sai na nance wayan kuma lokacin baki nan ne yasa ban faɗa Miki ba" Allah ya sani tana sananin son Rayyan fiye da yadda ake tunani duk cikin ƴaƴanta tafi son sa ko dan da ta haife sa bata sake haihuwa ba sai bayan 12 years. Ya ɗaura kansa a shoulder ɗinta yayi shiru tace "Me su Nisreen da Niswa suka maka da zaka dake su?" yayi shiru be ce mata komai ba ta ɗaga kansa ta karasa ɗaukan file ɗin da zata ɗauka sai sannan ta kalle sa sauke idon sa kasa yayi yace "Mummy dukan Leena sukayi har sai da ta fasa mata hanci Kinga yanzu ta tashi bata da lafiya" tace "Rayyan idan har kana so na daga yau na raba ka da Leena har abada ba ruwan ka da ita, tin da akan Leena kake dukan kanan ka" daga haka ta fara gaba yana biye da ita a baya suna fita parlor tana kallon sa tace "kayi breakfast?" yace "Eh" daga haka ta karasa fita shi kuma yana biye da ita kusan tare suka fita daga gidan Rayyan yana fita asibiti ya wuce duk wani abu da zai bukata ya ɗauka, ganin bayi da wani aki sosai ranan yasa ya fita yace wa abokin aikin sa idan wani abun ya taso shi baya nan daga haka ya wuce gida yana zuwa yayi sallama parlorn muryan Ammi yaji tace "shigo mana ya Rayyan" ya shiga ciki Ammi ta tashi tana biye da shi a baya yana shiga ɗakin Leena yaga Hajiya na zaune a gefen ta tana rokan ta da taci egg ɗin da ta soya mata tana kallon Rayyan ta tsuke fuska Murmushi yayi yace "Hajiya yau fushi kike da ni kuma? tace "A'a zo ka duba ta, ai Ni tunda naga Leena bata je ta gaishe ni ba nasan ba lafiya ba amma kai fa rabon ka da gida na tun jiya, ina ta damuwa ashe garau ɗin ka" ya haɗa alluran hannun sa ya ɗaga kai yana kallon Hajiya yace "toh ai tun jiya bana gidan nan ɗazu shigowa na a asibiti na kwana" ya gama hada abun da zai hada yana ma Leena Murmushi yace "Toh Leena bari muyi allura ko?" nan da nan ta fara hawaye tana girgiza masa kai ita bata so Ammi ta mata wani kallo tace "ko ki tsaya yayi Miki ko kuma ba zaki warke ba har ku fara exams ke kika sani" jin haka yasa ta tashi ta zauna Hajiya ta tashi ta fice tace "sai kuma na sake leko ki Lina" Ammi tana kallon Rayyan tace "Kaima Rayyan ji yadda kake abu, be like a man yadda zata ji shakkar yi maka gardama amma a hakan ne zaka ce zaka ma Leena Allura?" daga haka ta fice a ɗakin da kyar ya samu ya mata allura ta sha magani sannan ya kwantar da ita, a parlor ya samu Ammi na zaune tace "ka gama" yace "Eh, Allah ya bata lafiya" Ammi ta amsa da Amin mungode. Around 2 Rayyan ya sake zuwa daga office ya wuce yaje ya duba jikin Leena yaga da sauki zazzaɓin ma ya fara sauka, ya wuce part ɗinsu ya shiga da sallama Nisreen da Niswa suka gaishe sa ya amsa yace "kuna wani abu ne yanzu"?" duk suka ce A'a, yace "okay na baku 10 minutes ku shirya sai ku same Ni a wajan mota na" daga haka ya fice suka fara jin daɗi coz duk sanda yace musu zai fita da su toh shopping zai kai su tare da ice cream heaven ba'a ɗau lokacin ba sai gashi duk sun fito suka shige motar, Rayyan mall ya fara kai su yayi parking sannan ya kalli Niswa dake gaban motar yace "ku shiga ku ɗauki abunda zaku ɗauka" ya karasa maganar yana mika mata ATM card ɗinsa ta amsa tana murna tace "toh Yaya Rayyan" ta kama hannun Nisreen suka shige ciki shi kuma ya ciro wayar sa yana danna danne kamar wanda aka tuna wa abu da sauri ya sauka a motar ya rufe sannan ya shiga mall ɗin, inda yasan Leena na fara zuwa a mall ɗin yayi ya ɗauka mata favorite turaren ta sai zai bi wajan chocolate ya hadu da su Nisreen tana murmushi tace "yaya kaiman ka shigo ne?" ya yi mata Murmushi kawai duk wani abu da yasan Leena zata so sai daya ɗauka mata bayan sun biya kuɗi yace akai musu kayan booth ya buɗe aka zuba a ciki yana rike dana Leena yasa a gaban motar daga nan ya wuce da su ice cream heaven suka shiga tare yace "kuje ku ɗau abun da kuke so" ya ɗauka wa Leena sanin Mummy na son country yoghurt da pizza ya ɗauka mata basu suka koma gida ba sai daf Magrib yana parking duk suka sauka kana ganin su kasan suna cikin murna ya mika wa Niswa na Mummy yace "gashi ki fara kai na Mummy sannan sai ki zo ki ƙwashe naki ta amsa ta kama hanyar part ɗin su, Nisreen ta fara kai nata ciki itama ya ɗauki na Leena ganin ta zaune a kofar ɗakin yasan ta fito shan iska ne hakan yasa ya karasa yana inda take. Mummy da ta fito zata raka aminiyarta suka ci karo da su Niswa a bakin kofar parlorn ja baya suka yi suna Murmushi suka gaishe ta ta amsa tace "ai da bangan ku ba nake tambayar Mummyn ku" suna Murmushi suka ce Ya Rayyan ne ya fita da mu shopping. Rayyan na kallon Leena da har ta rame yace "Toh kinci abinci" ta girgiza masa kai yace "meyasa toh?" tana masa shagwaba tace "Ni ba zan iya cin abincin ba" tana gama faɗa ta ɗauke kanta dama Leena da shagwaba barin ma bata da lafiya ai an shiga uku dariya ma ta basa ta tashi ta mike ganin su Mummyn sa sun fito ita da kawar ta though ba wanda yayi noticing ɗinsu a cikin su, ya mika mata siyayyan da yayi mata yace "toh karɓa" ta karba tace "Tace Nagode" zata shiga ya riko ta hannu ya kai forehead ɗinta dan yaji temperature ɗinta karaf ya faɗa a idon aminiyar maman sa Leena suna haɗa ido da matar ta juya, Matar tace "Ke khadija wannan ba ita bace Agolan ta ku?" Lokacin da Mummy zata juya Leena na kan shigewa cikin parlorn shi kuma Rayyan ya jiya zai koma gun motar sa yayi kamar be gansu ba sai yanzu ya gane tafiyar da Leena tayi, ya tsana wannan matar saboda duk lokacin da tazo sai tayi causing matsala, Mummy ta kalle ta tace "itace, menene?" tace "Tab, haka yarinyar ta kara girma" Mummy tace "Tsawon kafa ne fa kawai amma ai age mate ɗin Nisreen ne" tace "waya ce Miki zallan tsawon kafa tayi, ke baki ganin halittun jikin ta ne chapɗin gashi har ta kusan fin Niswa a tsayi" Mummy tace "Ni ina nasani dake ba kare mata kallo nake ba" tace " Tohbmaganar gaskiya sai kin tashi sosai akan ɗan ki da wallahi ko ƙaffara ba zanyi ba ɗanki na son yarinyar nan dan ke baki ga kalan kallon da yake mata bane harda janta jikin sa fa yana shafa ta" Mummy tace "Rayyan ɗinne kuwa?" Tama Mummy wani kallo tace "gashi nan dai kina gani da idon ki Rayyan ɗin ya bar wajen ita kuma yarinyar ta shige ciki abunta, muna nan da ke wallahi wata rana zaki kirani kice min Rayyan zai aure ta" Mummy tace "ya isa dan Allah, bana son wannan misalin" Matar tace "Atoh kin san kuwa abinda yake so ubansa zai masa" Mummy tayi shiru sai kuma tace "Wallahi Ni yanzu abinda kika faɗa ne ya ɗaga min hankali, akan yarinyar nan fa Rayyan ya sha dukan kanansa kamar zai kashe su, abu idan nata ne sai Kinga rawar kafa" Matar tace "magana ta zata fito fili kuwa, waya sani ma ko uwarta ke kissa mata saboda ya aure ta Kinga sai su kama gidan da hujja sai yadda suka juya ta" kiran Sallahn da aka fara ne yasa Rayyan ya sauko a motar sa daidai lokacin da Daddy ya fito a part ɗin Hajiya ya jira sa har ya karaso inda yake sannan suka jera suka fita be yarda yaga inda suke ba. Matar tace "ki bari kawai sai munyi waya" Mummy tace "toh shikenan" daga haka ta koma cikin gida. Mummy na serving Daddy bayan ta gama ta ɗaga kai tana kallon sa tace "baka ce komai ba akan maganar da muka yi da kai, kuma naga weekend zamu shiga kar ace har ya wuce baka yi wani abu akai ba har a shiga week days" yace "maganar me kuma?" Mummy ta tsaya shakeke tana kallon sa tace "wai har ka manta? Maganar sa date ɗin Rayyan mana" yace "Ohh Okay, bari zanyi magana da shi anjima sai ya tsanar da su ko da jibi Sunday in Allah ya kaimu sai mu tafi" tace "Toh Allah ya yarda, Amma dan Allah kar a wani sa long time" yace "wannan kuma bari muji ta bakin shi Rayyan ɗin" tace "Toh ai shine ya roka hakan". Around 9pm Daddy ya kira Rayyan,Rayyan ya shigo da sallama ya zauna yana kallon Daddy yace "Gani Daddy" Daddy ya ajiye jaridar hannun sa yace "kunyi magana da yarinyar ne?" yace "wani yarinya kuma?" Daddy ya masa wani kallo yace "wanda zaka aura mana" wani bugawa zuciyarsa tayi a wannan lokacin yace "Toh maganar me kuma Daddy zan mata?" yace "Bana son shashan ci, ba kai ka turo mahaifiyar ku akan asa bikin not too long ba? So you have to let her parents know, first" zufa ne suka fara zirya a fuskan sa da kyar yace "Daddy Ni bance mata komai ba, infact ma Ni da yarinyar bamu magana ma yanzu haka, she has totally changed shiyasa" Daddy na kallon sa yace "what do you mean, tho?" yace "I'm sorry to say Daddy Amma yanzu na fasa auren ta" Daddy yace "Toh wa kake so yanzu? Kasan ba wai zaka ci gaba da zama haka ba ko?" Ya gyda masa kai yace "Daddy wanda nake so ba lalle su ɓan ita yanzu ba, amma soon zata yi paper, idan tayi zan same ka" Daddy yace"tho tashi ka tafi zan ma Maman na ku bayani" Rayyan yana shiga ɗakin sa ya jin gina da wall ɗin ya rufe idon sa yana sauke numfashi a hankali
Yes, I trust you sister. You're a true supporter, so please help me and share this with others
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
Chapter 9
Alhamdu Lillah
Mummy na kallo Daddy sakeke sai kuma ta girgiza kai tace "sai kuma ka kyale shi haka nan?" yace "toh me zan ce masa kuma? yace basu magana ma da yarinyar yanzu" tace "toh zuba masa ido zamu yi haka nan?" yace "Idan lokacin sa yayi za'ayi ba mu'isa mu tsallake ba" ta gyaɗa kai tana kallon Daddy da takaicin sa ya cika ta, ya lalle ta sai kuma yace "Beside ma yace ai akwai wanda yake so" tace "waye ita ɗin, aina take ?" yace "how will I know, Khadija? gani yayi ta mike yace "ina kuma zaki?" tace "ɗakin Rayyan mana" yace "Ni banga dalilin za yasa kika dage sai ansa bikin sa kwanan nan ba, ki bar yaro ya huta, it's already pass 10pm fah, haba ke kuwa". Washe gari, Saturday, Ammi na idar da azkar ɗinta ta ninke prayer mat ɗin ta ajiye ɗakin Leena ta nufa ta shiga cikin ɗakin taga har sannan tana bacci taba ta tayi sai Leena ta buɗe ido Ammi ta mata Murmushi tace "tashi kiyi sallah ko?" gyada mata kai kawai tayi Ammi ta taimaka mata ta tashi tace "ya jikin?" tace "Da sauki" tace "meke Miki ciwo yanzu?" ta girgiza kai tace "yanzu ba inda yake min ciwo kawai dai baki nane har yanzu ɗaci" Ammi ta kai ta toilet tayi wanka sannan tayi alwala suka fito Ammi ta shinfiɗa mata sallaya tace "toh yi sallah kafin nan barin je ɗaura miki breakfast, me zaki ci?" Leena tayi shiru tana nazari sai kuma tace "Zan sha ice cream ɗin da Yaya Rain ya kawo min jiya" tace "Abinci fa?" tace "Sandwich" daga haka Ammi ta mike ta fita. Rayyan yayi sallama a bakin kofar parlorn Hajiya ta amsa masa tace "Riyan shigo mana ya shiga ya zauna ya jira har ta karasa lazimin ta sannan ta karaso cikin parlorn yana kallon ta ya gaishe ta ta amsa masa tana tambayar sa ya aiki ya amsa da Alhamdulillah tana kallon sa kamar wacca ta tuna abu ta fara washe baki tace "ashe za'a je sa ranan bikin ka" da sauri ya kalle ta da kyar ya samu yayi healing daga Abunda yake ji jiya yanzu kuma Hajiya zata fama masa, ya girgiza kai yace "A'a dama Mummy ne tace ya kamata aje sa rana bata san Ni da yarinyar ko magana ba muyi ba" tace "kamar yaya kenan?" yace "kawai dai yanzu ta daina min magana sannan ta siro da wasu dabi'u da ba nata ba" Hajiya tace "Atoh, Ni tunda ka taɓa kawo ta nan bata min ba kwatakwata kar nayi magana ka killaceni" daga haka yayi shiru ta kura masa ido tace "toh yanzu an fasa wannan ɗin kenan" ya gyaɗa mata kai tace "toh yanzu da wa za'ayi?" yace "ba yanzu za'ayi ba Hajiya" tace "tambayar ka fah yarinyar nake yi?" ya ɗan kalle ta sannan ya mayar da kallon sa wani direction yace "yarinyar bata karasa girma ba, amma tana gama secondary school zaku san ta" daga haka ya miƙe Hajiya tace "Toh ai na take?" yace "Hajiya barin fita zan duba jikin Leena daga nan zan wuce gymnasium yau Saturday ne" Hajiya ta tsaya kallon sa tace "zaka zo nan neman kindirmo ai, zanyi maganin ka" ya fice abin sa kamar be ji ta ba. Direct a kofar su Ammi yayi sallama Ammi tazo ta buɗe masa kofar ta koma ciki shiga yayi yana kallon wani direction yace "ina kwana Ammi" ta amsa masa yace "ya jikin Leena ɗin? Hope da sauki yanzu" tace "Eh Alhamdulillah dan yanzu takan ci abinci bata amarwa amma sai dai bata ci daya" yace "zata ji sauki in shaa Allah" ta nuna masa kofar ɗakin tace "toh ka karasa mana" ya karasa ya shiga Leena da jin muryan sa ta kulle ido da sauri ya shiga ɗakin yaga tana bacci Murmushi yayi ya karasa cikin ɗakin ya dauki sauran alluran da ya ajiye jiya a saman walldrope ya haɗa sannan ya karasa inda take still idon ta a kulle ta kasan ido ya kalli bakin kofar ganin Ammi bata nan ya kai hannun sa fuskarta da hankali kaman mai raɗa yace "Leena, don't pretend you're sleeping; I know you too well" bata san sanda tayi murmushi ba ta tashi ta zauna tana kallon sa cikin shagwaba tace "I don't think I need the injection; I'm feeling fine Yaya Rain" hararan ta yayi yace "Haba baby girl, this will be the last injection, and then you'll be all set. Exams are coming up soon, so i want you to be healthy and do well" ta turo masa baki da kyar ya lallaɓa ta ya mata ta fara sheshshekan kuka yace "c'mon, you're not baby anymore fa" ta juya masa baya ya kwashe kwalɓan alluran daya fasa yace "toh ni zan tafi" ta juya tana kallon sa tace "zan bika" yace "gym zan tafi, ki bari da yamma sai mu fita ki kaga layin nan zaki ɗanji dama dama" ta gyada masa kai kawai, daga haka ya fita yayi ma Ammi Sallama. Wajajen karfe takwas Ammi na kwance a ɗakin ta ta rasa me ke mata daɗi haka nan take jin ta ba lafiya amma kuma ta rasa meke damun ta sallaman Hajiya da taji yasa ta amsa ta fito already Hajiya har ta shigo parlorn Ammi ta gaishe ta ta amsa Hajiya tace "ina ita Leena daman faten wake na dafo mata naga bata son komai idan bata da lafiya sai shi" Ammi ta gyaɗa mata kai tace "Sannu Hajiya, tana ma cikin ɗakin nata" dan yanzu Ammi bata wani son surutu, Hajiya ta shiga taga tana bacci ta fito tace "idan ta tashi sai ta sha yanzu naga tana bacci ne" Ammi tace "Toh shikenan, Allah saka Hajiya" daga haka Hajiya ta kama hanya ta fita ita kuma Ammi ta koma ɗakin ta ta kwanta. Wajajen karfe goma sai ga Rayyan ya dawo daga Gym yayi sallama ya shige parlorn ganin Mummy yasa ya tsaya yace "Mummy ɗazu ai na shigo zan gaishe ki naji a kulle nace yau Saturday kila kina hutawa ne" tace "Sure!" yace "ina kwana mummy, kin tashi lafiya" tace "Alhamdulillah, zauna nayi serving ɗinka" yana kallon ta yayi murmushi yace "A haka Mummy? Kalli yadda zufa ke ɗinga daga jiki na barin je nayi wanka sai na dawo" tace "toh before then, Rayyan me yasa ka fasa auren Anisa?" yace "Ohh Mummy, yarinyar ta chanza ba yadda na santa da ba and yanzu kafin na hakura da ita ita ta fara hakura da Ni dan har ce min tayi she's not interested yanzu kuma, so Kinga bani da laifi" tace "toh wa kace wa Daddyn ku kana so?" yace "wata ce, amma ba lalle iyayen ta su yarda su ba Ni ita yanzu ba" tace "saboda me?" yace "because she's still teen, Mummy" Mummy kallon sa take yi bata ko kiftawa kamar me son gano wani abu jin shiru da Rayyan yaji tayi yasa ya ɗaga kansa ya kalle ta tace "kuma dole sai ita zaka aura? Ina Husna kanwar abokin ka da ta nace maka why not ita akan yarinyar da kake magane, wato sa'an su Niswa fah" yace "Mummy bana son Husna, bata da kamun kai, baki ga yadda take exposing kanta a social media ba" tace "Ga ƴaƴan aminiyarta dukkan su uku mata ne sai wanda ka zaɓa aciki bari zan mata magana" da sauri ya ɗaga kai yana kallon ta matar da ya tsana alakarta da Naman sa ace ya auri ƴarta God forbid yace "Mummy kinsan ba zan iya auren ɗaya daga cikin ƴaƴan ta ba, kiyi hakuri kawai" tayi shiru tana kallon sa yace "but Mummy me yasa kike so kiga nayi aure ne all of a sudden" tace "Mate ɗinka nawa suke yi, shiyasa" yayi shiru yace "barin shiga zan yi wanka kafin na fito" tace "Okay, but ka sani Maganan be mutu ba Rayyan dole zaka fitar da mata ko na fitar ma". Ya shiga ciki da tunani iri da kala suna yawo a ransa. Jidda tace "Ya Sadeeq na jira ka idan zaka fita sai kayi dropping ɗina a gidan su Leena" yace "waye haka?" ta kalli Sultan da yake murmushi sai kuma ta sake kallon sa tace "wannan little baby da tazo gidan nan mana few days back?" Sai sannan ya ɗa ga kansa ya kalle ta yace "dama akwai wacca tazo gidan nan ne few days back ban sani ba? ta juya ta kalli Sultan sai taga Mummy da yanzu fitowar ta a ɗakin ta da sakon da zata ba Leena, Mummy ta harare sa tace "ki ta ɓata bakin ki ma Sadeeq" ta karba turaren tace "ta gode Mummy" daga haka Sadeeq ya mike ya haura sama Jidda tace "ɗan rainin hankali ne wallahi ya Sadeeq din nan" sai yanzu Sultan ya fashe da dariyar daya ke kunshewa Tun tuni yace "Kin san I caught him watching her videos countless times" Jidda ta zara ido tace "When? bayan na goge a wayan sa" Sultan na dariya yace "harda recycle bin kika goge?" tace "No" yace "definitely ya dawo da su ne" tace "kasan ranan da muka kai ta ina zuwa a lectures nace ya ban wayan sa zan tura videos ɗinta saboda idan na koma zan turawa maman ta sai ya fara masifa ashe be shiga ya gansu ba da kyar na bashi hakuri ya yarda na tura sai na goge, kai amma da mamakin ya Sadeeq zan kwana, imagine fah wai waye ita?" Sultan yace "Kaɗan daga aikin sa kenan" Mummy ta tashi ta wuce ciki abunta sai ga Sadeeq ya kuma shan wanka ya fito jidda ta ɗauke kai Sultan yace "wajan ɗaura aure zaka ne? naga ka kuma wani wankan gashi yau dama Saturday ne" ko kallon Sultan be yi ba balle Sultan yasa ran zai basa amsa, ɗaukan Apple ɗaya yayi dake kan Centre table yayi hanyar kofa ya fice Jiddah na kallon Sultan tace "duk kai ka jamin Ya Sultan wai na bisa ya rage min hanya" sai da Sadeeq ya shiga motar sa sannan ya danna mata horn, Sultan yace "yana kiran ki fa" tace "kyale sa Ni ba inda zanje na fasa zuwa da shi ɗin" sai gashi tun kan ta rufe baki ya kira ta a waya ɗaukawa tayi tasa a handsfree tace "ina ji" yace "ke dalla Ni sa'an ki ne da zaki bari ina jiran ki?" ta kalli Sultan jin abin da yayan nata yace tace "toh ai baka ce zaka kaini ɗin ba" daga haka ya katse kiran ta tashi tana kallon Sultan tace "ya Sultan na tafi, i wish tare zamu tafi" yace "zan zo ɗaukan ki sai mu gaisa da ita" ta wuce ɗakin Mami ta mata sallama sannan ta wuce ta fita buɗe gaban motar tayi ta shiga bai ko kalle ta ba yace "Ina ne gidan nasu ya ke?" tace "ita wa ɗin?" ya juya ya mata wani kallo yace "if you're not ready, get out" ta kusan fashewa da dariya da kyar ta kunshe tace masa "Sorry big bro, na dauka tambaya ta za kayi ina zaka yi dropping ɗina" kai hannun yayi zai buɗe mata kofa ta fita masa da kyar ta basa hakuri tace street F suke bai sake tanka mata ba suna shiga layi tace masa "Ya sadeeq daidai wancan gidan zan sauka parking yayi without looking at her, wani direction daban yake kallo ta sauka tace "thank you Y Sadeeq" ta buɗe motar zata fita to her own surprised taji yace "yaushe zaki fito? Or just call me idan kin gama" ta juya tana kallon sa sakake saboda shi baya kai mutun waje kuma ya dawo da kai gida balle yadda ta riga masa hauka yace "Ke zaki sauka ne ko sai na saukar da ke" da sauri ta sauka tana kallon sa tace "thank you" yaja motar sa yayi gaba ta karasa bakin gate ɗin ta konkwasa gatekeeper ya buɗe gate ɗin ta gaishe sa ya amsa yace "wa kika ko nema?" tace "wajan Leena na zo" yace "Okay, tho ki shigo" ya karasa buɗe gate ɗin ta shiga tana kallon sa tace "dan Allah ina ne part ɗin su?" yace "wancan na hannun hagun ki shi zaki shiga" tana kallon sa tace "Nagode" ta karasa kofar parlorn tayi sallama Ammi da ta fito daga kitchen ta karaso kofar parlorn tana amsa sallaman ta buɗe tana kallon ta sai kuma ta masa mata tace "shigo mana" ta karasa cikin parlorn tana gaishe ta Ammi ta amsa da fara'a tace "Sai dai ban gane ki ba" tana murmushi tace "Eh baki sanni ba, wajan Leena na zo" Amma tace "Lafiya dai ina? tace "Eh lafiya klau, dama tace zata zo min a weekend ne toh na san ba lalle ta zo ba shine na zo mata yanzu" Ammi da ta kasa gane maganar tace "Muje tana ɗakin ta, dake ba lafiya dake da shi ba" Ammi na gaba Jidda na baya suka shiga Leena dake kwance tace "Laaa Anty Jidda" Jidda na murmushi ta karasa tayi hugging ɗinta tace "Me yake damun ki Leena?" Ammi tace "Ayyah, ai sai kice min ke malamar su ne" Jidda ta kalli Ammi da rashin fahimta Leena tace "A'a fah Ammi ba malaman mu bane" at this point kan Ammi ya kulle ta koma parlorn ta barsu a ciki bayan sun gaisa Leena tace "Ina Nice Uncle da wicked Uncle" Jidda na dariya. Jidda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 50