muddun komai ya rushe wannan ba me sauki bane ko da 2weeks kike so za'ayi hakan". Niswa ta buɗe dakin nasa ta shiga sannan ta rufe ta tsaya tana kallon sa daga bakin kofar, shi kuma jin an buɗe dakin an shigo kuma beji alamar Mummy bace ko Daddy yasa ya buɗe ido dan kallon wanene, ya buɗe ido yana kallon Niswa da ta kafe sa da ido tun daga bakin kofar alamar menene ya mata da hannu hawaye taji ya taru a idon ta, ba zata juri kallon yayan nata a wannan sabon yanayin ba ta karasa har jikin gadon sa ta durkusa tana kallon sa kamar yadda shima kallon nata yake yi, tace "Yaya nasan saboda Leena zata yi aure yasa kake kwance ko?" ta karasa maganar hawaye na gangaro mata kallon ta yake ba ko kiftawa.....
Assalamu Alaikum, everyone!
Da fatan anyi sallah lafiya? Allah Ubangijin ya maimaita mana, yasa muna cikin bayin sa da yayi wa Rahama, Amin ya hayyu ya qayyum.
Share, please.
https://www.instagram.com/jiddatul_khayr_?igsh=MW8yeXBveXRlOTg5Yg==Follow the JIDDATUL-KHAYR BOOKSHELF DIARIES📚💕! channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vaq17Di3WHTWv5ju0w3Z
https://www.instagram.com/jiddatul_khayr_?igsh=MW8yeXBveXRlOTg5Yg==
26........
Tace "Me yasa baka ce min kana son ta ba? Da na taya ka fighting Ya Rayyan" ya kamo hannunta trying hard to hold his tears back girgiza mata kai yayi sannan ya mata Murmushi, ya tashi daga kwancen da yake yi ya jinki na da gadon ya rufe idon sa kaman me whisper yace "Everything will be alright, then." ta cire hannun ta a nasa ta mike tsaye still idon ta na kansa tace "I wish you speed recovery'?" sai sannan ya buɗe ido yana kallon ta She gave him a reassuring smile shima mayar mata yayi daga haka ta juya ta fita. Mami dake tsaye akan sa Jiddah kuma na zaune a bakin gadon da plate ɗin fruit a hannun ta shigowan Sultan kenan, Mami ta ɗan ɗaga murya tace "ba zaka bude baki ka min magana ba?" sai sannan ya ɗaga ido ya kalli Jidda da Sultan Mami ta fahimci meya ke nufi dan haka tace "we need privacy, please" Jiddah ta kalli Sultan sum sum suka tashi ta ajiye plate ɗin hannun ta suka fita Mami karasa bakin kofar ɗakin ta kulle sannan ta dawo tana kallon sa tace "Uhm, I'm all ears" sai sannan Sadeeq ya buɗa baki kamar me whispering ya fara Magana. Masu algaita sai aikin su suke, Manyan motoci ne suka dinga shiga layin gidan su Leena suna parking. Hajiya dake zaune a parlorn Ammi anty Binta ta kalle ta tace "Hajiya kamar sune suka iso" Hajiya tace "Toh, yi maza kije sai ki karaso da su Nan" kafin ta karasa har sun fara shigowa. Daga cousins ɗin Ammi har few neighbors ɗinsu suka zo taya su karɓan kayan lefen Leena, sake baki su kayi suna kallo ganin har sannan ba'a daina shigowa da akwatinan ba, ana cikin shigarwa sai ga Jiddah da Mami ma sun shigo. Ammi dake zaune a dakin ta, ta fita zuwa dakin Leena ta karasa har ciki tana kallon yadda a ƴan kwanaki biyun nan ta wani zabtare ta zauna bakin gadon ta tana kallon ta tace "Leena tunanin me kike haka ne wai?" Ammi daurewa kawai take yi bata son wannan sabon canzawan Leena, Leena ta kalli Ammi sai kuma tayi faking murmushi tace "bakomai Ammi" Ammi tace "ni zaki fara boyewa abu Leena?" Sai sannan taga Leena ta fara kuka same thing da Anty Binta ta mata haka Ammi ma ta mata janta tayi jikin ta ta bari har sai sanda tayi shiru dan kanta sannan Ammi tace "ina jin ki?" Leena tace "Nima ban san meke damuna ba Ammi, kawai dai na san I'm just Scared" Ammi tayi shiru tace "kun samu matsala ne da Muhammad ɗin?" Leena ta girgiza mata kai tace "ko dazu ma munyi waya" Ammi tace "baki son sa yanzu ko?" Leena ta girgiza mata kai kawai Ammi tace "ki kwantar da hankalin ki ba wani abu da zai faru in shaa Allah sai alkhairi kuma ina nan ina Miki addu'a, duk sanda kika ji wani abu ki ambaci Allah, kar ki bari bakin ki ya zauna babu ambaton Allah, kin ji?" Leena ta gyada mata kai" har sannan Leena na jikin Ammi sai yanzu taji tasamu natsuwa sosai suna nan a haka suka jiyo buɗa da ake sakewa a can compound ɗin. Akwatina set biyar suka kawo mata kuma ba wanda aka sa mata kaya me arha a ciki duk kaya ne masu tsadan gaske, har bakin mota suka raka su Hajiya sai hamdala take tayi bayan sun dawo suna kara ganin kayan for the second time, gate Man ya buɗe gate Mummy ta shigo da mota tayi parking Hajiya ganin haka yasa ta tashi tana kallon ta har ta sauka tace Khadija karaso kizo ki ga abun arziki, Mummy data ke rufe motar ta tayi magana kasa kasa tace "ji shigeyar matan nan" ganin mutane da ɗan dama yasa ta karasa wajan amma da ba dan su ba ba zata ba, lokacin da idon ta ya kallin yawan akwatina bata san sanda ta durkusa da sauri ba sakamakon kafar ta da taji ba zasu iya daukan ta ba, zufa taji ta ko inan ta, murmushin da take faking bata san sanda ya tafi ba sabar ruɗu bata san sanda tace "kuma shi hauka yake zai yi wannan akwatina sai kace shago zai buɗe mata?" Duk aka ɗago ana kallon ta sai kuma tayi realizing mema tace ashe, Jiddah kallo ɗaya ta mata ta ɗauke kai anty Binta tace "Zunzurutun soyayya ce nake faɗa Miki, wani hauka kuma sai kace bakin ciki ake ma ƴa? Kin san gidan daula zata shiga" Mummy ta mike tace "Kaya kam sunyi kyau, Allah sanya Alkhairi barin shiga na ɗan wasa ruwa kafin Magrib" Dakyar ta mike Anty Mairamah tace "Yo ai baki tsaya Kinga kaya ba" Mummy ta wuce ciki, ko kallon Nisreen dake zaune a parlorn dake mata sannun da zuwa bata yi ba direct dakin ta ta wuce tana shiga ta danna kofar ta zauna nan kasan dakin tayi tagumi sai kuma ta daura hannu a ka tace "Nashiga uku ni khadijatu" da sauri ta share hawayen daya gangaro mata hannun ta har rawa yake yi ta ciro wayan ta a jakka ta gwada danna kiran Aminiyarta sai kuma ya shiga tana daga wa Mummy bata bari tayi sallama ba ta fara cewa "yanzu dawowa na na tarar wallahi akwatin sai kace wanda shago za'a buɗe baki gani ba expensive trolleys nake faɗa Miki, ya zanyi ne wai? Hauka kawai ya rage nayi" tace "kice yarinya de tayi goshi, toh ai zamu ga ta yadda abun zai kasance" Mummy tace "tun farko nice nayi wauta, da tun lokacin nasa ta zama ƴar iskangari na gaske yadda ba wanda zai yi sha'awar aurenta ta balle ya tinkare ta sai de da iskanci, ni yanzu babban damuwa ta ki kira mutumin nan kice masa kawai ya kashe yarinyar kowa ya huta! Idan yaso sai a haɗa ta aure da Niswa" Fatima tace "wata Niswan kuma bayan ga yarta Layla" Mummy tayi shiru sai kuma tace "Naji ni yanzu damuwa ta ki kira sa yanzu dan Allah" tace "anyi an gama" tace"aikin ita uwar Tata da muka ce ya bari sai bayan biki za'ayi nata ki ce masa ya yayi yanzu kawai" daga haka ta katse kiran, ga ba daya duniyar ta mata zafi. Da Daddare Leena na kwance ta lulluɓe da duvet duk da yanzu aka idar da Isha'i ba wai dare yayi nisa bane wayan ta dake ringing a bedside drawer ta kai hannu ta ɗauka ganin Zahra ne ta daga bayan sun gaisa Zahra tace "Ɗazu na dawo gari, in shaa Allah gobe zan shigo, Amarya" Leena tace "toh Allah kaimu" daga haka sukayi sallama sai ga kiran Muhammad ya shigo ita duk tunanin ta Zahran ce ganin Muhammad yasa ta ɗaga tayi masa sallama a hankali ya amsa yace "is everything okay, babe?" tayi shiru yace "speak up please, dear" ta buɗe baki zata masa magana kawai taji ta fara kuka a ɗan ruɗe Muhammad yace "Menene kuma babe, please ki daina kuka kimin bayani" Leena ta kasa yin shiru ya runtse ido yana jin kukan ta har zuciya sai daya tsaya yace "Baby ko na bi Flight ne na zo yanzu?" ta girgiza masa ka kaman yana ganin ta tace "A'a, I'm okay" yace "Baby" tace "Uhm" yace "tell me bana son ki boye min komai, menene?" tace "Nima ban san ko menene ba, kawai tsoro nake ji" yayi kasa da murya yace "please ki ajiye wannan tsoron a gefe idan ta nine, na Miki alkawarin ba zaki taɓa nadaman aure na ba, just calm down, Okay?" tace "Tohm, Allah ya yarda" yace "kinci abinci?" tace "yanzu zanci" yace "je ki ci, zan kira ki anjima" daga haka suka yi sallama toilet ta wuce tayi alwala sannan ta shimfiɗa sallaya. Hajiya dake tsaye bakin parlorn su Nisreen hannun ta ɗauke da kula tana ta sallama ba wanda ya bi ta kanta har zata juya sai ga Niswa ta buɗe kofar tana gaishe ta Hajiya ta fara masifa tace "Sai ku kama ku garkame kofa kamar wanda za'a muku sata ayi ta doka sallama kuna jin mutun kuyi banza da shi" Niswa tace "kowa ya koma dakin sa ne shiyasa" Hajiya na mata wani kallo tace "toh ba zaki masa min na shiga bane ko yaya?" Niswa ta masa gefe Hajiya ta shiga bata tsaya ko ina ba sai dakin Rayyan, Niswa ta zauna anan parlorn tayi tagumi ita duk damuwar duniya ya ishe ta, Hajiya ta karasa har inda Rayyan yake kwance ta taɓa jikin sa Rayyan ya buɗe ido yana kallon ta ya tashi daga kwance da yake Hajiya ta sake Salati tace "yanzu su iyayen naka haka suka zuba maka ido wato ka karata a haka kenan ko me suke nufi ne?" kallon ta kawai ya ke yi ta ajiye kulan hannun ta tace gashi faten dankali ne da alayyahu nasan zaka so yace "ki samin dan kaɗan Hajiya" Hajiya ta zuba masa ta mika masa tace "kira min shi uban naka" kallon ta yake alamun ta basa wayan ta ya fito mata da numbern Daddyn tace "ai da Wayan ka zaka kira min shi tunda ni na bar nawa a can" ɗaukan Wayan sa yayi ya yi dialing numbern Daddy yana fara ringing ya mika mata ta karɓa Daddy na daga wa ko amsa sallamar sa bata yi ba tace "yanzu fisabilillah saboda shi Riyan ɗin ba rai gare sa ba shiyasa zaku ta zuba masa ido ba zaku kaisa asibiti ba? Ji fah yadda ya koma, wannan wani irin rayuwa ne?" Camly Daddy yace "bari na shigo Hajiya" tace "Toh ina dakin Riyan ɗin sai ka same ni anan" Rayyan ya kalle ta yace "Hajiya ni nafi son gidan saboda duk kulawan da za'a bani a asibiti shi nake samu anan balle ma ni na warke" Hajiya ta dinga hararan sa har ya karasa magana bata tanka sa ba, can ba da daɗewa ba sai ga Daddy ya shigo ya gaishe da Hajiya ta amsa masa tace "ku yanzu baku ganin yadda ya koma ne?" yace "Hajiya shi yaki a kaisa asibiti kuma duk wani abinda ake bukata ana masa, sai dai ki ce masa ya cire duk wani abu dake ransa ya mika wa Allah lamarin sa sai komai yaga yana tafiya masa daidai" Hajiya ta mike tace "Ni kam barin tafi can, dan bana yarda da baki gashi na barsu su kadai" tana kai wa nan tayi hanyar fita sai kuma ta dawo dakin tana kallon Rayyan tace "Riyan kayi ta addu'a Abunda ba rabon ka ba baza ka taba samu ba kaji?" Rayyan ya gyaɗa mata kai kawai saboda zuwa sannan har ya fara gajiya da surutun ta tayi musu sallama ta fita tunawa da tayi da baki yasa ta fara tafiya da sauri dan Hajiya kwata kwata bata yarda da mutane. Daddy na kallon sa yace "Kana addu'an kuwa?" yace "Eh, in shaa Allah" daga haka yace "toh sai da safe, Allah sauwake" ya ja masa kofar daki. kusan cin karo yayi da Mummy a dinning kallonta yake ganin gaba ɗaya kwana biyun nan she's not herself ya wuce ya fita ita kuma ta banka kofar dakin su Niswa ta shiga ganin haka yasa Niswa ta mike tana kallon ta tace "Allah sa lafiya dai Mummy?" Mummy tace "Ni zaki ba wa kunya Niswa? Ashe abinda kika wa Mutumin nan kenan? Toh gashi ran Aminiyata ya baci ta kira tana ta magana akai, wallahi ko ki koma kina kula sa ko Kiga abinda zan Miki" Niswa tace "ina yanzu kowa sai mamakin mijin da Leena ta samu ake yi sai nine zan kula wannan? Ni ina ruwa na da kudin sa, ita kawar taki ta bawa daya daga cikin ƴaƴan ta mana" Mummy ta sake baki tana kallon Niswa mug ɗin dake kusa da ita ta ɗauka Niswa na ganin haka ta mike da gudu tayi hanyar toilet sanda Mummy ta wurga kuma be same ta ba dan har ta shige, kulle toilet din tayi ta fara rusa kuka ita ba zata aure wannan ba, tunda ta ke jin maganar auren Leena bata taɓa biin hankalin ta ya tashi ba sai ɗazu da ta gwada searching mijin da Leena zai aura a IG ji take ba zata iya bari Leena ta mallake sa ba kuma tayi alƙawarin ko da bayan bikin ne ba zata fasa bibiyan sa ba, dan tun lokacin ta tura masa da messages kuma ba zata hakura ba dan ita ce tayi deserving not Leena, bayan some minutes ta share hawayen ta tasan sannan Mummy bata nan ta buɗe kofar a hankali ta fito tasa ma kofar su key, ita data san haka ne da ta taimakawa Yayan ta ya samu Leena ita kuma ta makalewa MD, daukar wayan ta tayi ta shiga IG hoping yaga sakon ta. Har sannan Leena taji bacci ya kasa daukan ta gashi bata so tayi wani abinda zai sa Anty Binta ta gane ba bacci take ba, kuma Muhammad yace ze kira amma har sannan be kira ba, ta ja wayan ta ta shiga Whatsapp hoping zata ga Muhammad online tana masa magana taga message ɗin yayi delivered taji hankalin ta ya ɗan kwanta at least ba zai barta ita ɗaya ba, har wajan 10 min bata ga yayi replying dinta back ba dama ta san sa da barin data always On ta shiga call log dinta tayi dialing numbern sa har ya gama ringing be ɗauka ba ta sake kira nan ma be ɗauka ba sai kawai ta kashe wayan ta kwanta, tana son tayi forcing kanta tayi bacci dan tasan gobe da sassafe zata tafi kitso da Lalle. Wani irin zabura yayi lokacin guda har sai daya kusa faɗuwa kasa, da kyar ya iya rike kansa, wani sabon tururi yake ji wanda hakan sabon yana yi ne game da shi ya runtse idon sa amma sai kuma ya gagara addu'an da ke bakin sa....
Join me on Wattpad: a free, mobile app for reading and sharing stories. https://www.wattpad.com/user/jiddatulkhayr?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp.w4b&utm_campaign=invitefriends
Follow the JIDDATUL-KHAYR BOOKSHELF DIARIES📚💕! channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vaq17Di3WHTWv5ju0w3Z
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
27........
Wayan ta ne ya fara ringing kafin ta kai ga buɗe ido har ya yanke mikewa zaune tayi ta kalli agogon ɗakin da ke nuni da karfe 6:30am da sauri ta fara murza ido bata san ta makkara har haka ba ɗaukan wayan tayi dan ganin wanene, ganin Aminiyarta ne zata yi dialing back sai ga wani kiran yana shigowa, ɗauka tayi ta kai kunne kafin ta kai ga magana Aminiyarta ta riga ta tace "wajajen sha biyun daren jiya mutumin nan ya kira wai aiki ya fara, so yanzu zaki bada Miliyan daya" Mummy tayi shiru dan yanzu ko tsisi bata magani, dan kusan kullum sai ta kashe kusan hakan Aminiyar ta tace "Hello!" da sauri Mummy tace "Toh, shikenan yaushe ake bukata?" tace "yanzu yace yake so" Mummy ta mike tace "barin yi sallah zaki jini" tunani ta fara ko ta shiga kasuwa ta sayar da gold dinta ne, da wannan tunanin ta shige ban ɗaki. Zahra ce tayi sallama Ammi ta amsa mata ta gaishe ta Ammi tace "Yaushe kika dawo Zahra?" tana murmushi tace "Jiya Ammi" Ammi tace "Ayyah sannu da zuwa, ki shiga ciki suna can" tace "Toh, Ammi" tana shiga ta same su Anty Binta ta gaishe su suka amsa tace "Leena fah?" Anty Binta tace "tana wanka" bata daɗe ba sai ga Leena ta fito bata san sanda taji wani relief ba da taga Zahra tace "na ɗauka ai ba zaki iya fitowa da sassafe ba ai" Zahra tayi dariya tace "Na'isa Amarya?" Leena ta Harare ta daga haka ta fara shiri cikin sauri tana gamawa ta saka hijab ɗinta ta daura Niqab tana kallon Zahra tace "Muje ko?" Zahra ta mike Anty Binta tace "Ya maganar me lallen mu ɗin" Leena tace "mun kara magana tace zata shigo amma sai karfe 9am" daga haka suka fita tayiwa Ammi sallama. Daddy yadda ya ganta hakanan yasan da magana a bakin ta yadda tayi wani calm da ita dama sai tana da bukata take zama very calm yace "Yau ba zaki office bane?" ta ɗan kalle sai sai kuma tace "zani mana" yace "Okay, naga baki fara shiri bane har pass 7am" tayi kasa da murya tace "Dama yallabai, 1 mil zaka taimaka min da shi yanzu?" Daddy ya dinga kallon ta baya kiftawa sai kuma yace "Me zakiyi har da 1 mil?" tace "ina son zanyi Using ne" Daddy yana kallon ta yana son studying dinta, ai yasan tana da kudi toh ina suke me ze sa ba zata yi using ba? duk tunanin sa ya tafi kan kila saboda kayan daki da yayi wa Leena ne take son itama ta fara zaran kudi a jikin sa, tana kallon sa tace "kayi shiru baka ce komai ba" yace "Khadija kiyi hakuri gaskiya ba zaki samu wannan kudin yanzu ba, Kinga dai na gama kashe kudaɗen wajan biki kuma kinga ba'a ma gama ba" ta mike tana masa wani kallo tace "Amma dake ai wancan matar taka ka ɗauke ta ƴar gold ce ji rawan kafan da kake yi a bikin ƴarta, ji uban kayan daki da ka mata kowa sai magana yake dan na tambaye ka miliyan daya shine zaka tsaya kana kallo na ka na bani wani banza Excuse ɗin ka" daga haka ta ja tsaki ta fice Daddy ya girgiza kai ita ko kunya ma bata ji idan tana neman abu zata kashe murya amma idan akasin haka ne maganar arziki ba zata haɗa ku ba. Mummy tayi shiru tana tunani gashi inda take zuwa tsayan gold a kasuwa ba su fitowa sai 10 na safe balle tace zata jira gashi Fatima ta addabe ta da kira wai mutumin yace zai lalata aikin idan ba suyi sauri sun tura kudin ba, sake checking account balance dinta tayi for the countless times taga duk abinda ke ciki be kai 200k ba duk kudin sun tafi a hanyar aikin da ake mata. Buɗe dakin Rayyan tayi ta shiga ita sai yanzu ma ta tuna da shi yana kallon ta ya gaishe ta ta amsa tace "ya jikin naka kuma?" yace "da sauki Mummy, yau ba aiki ne?" tace "yanzu zan tafi" ya gyada mata kai tace "kasan me, 1 Mil nake son kamin transfer yanzu wani abu nake son yi kuma kudina ba zai kai ba" yace "Toh shikenan, a wani account ɗinkin zan sa?" tace "Samin a Opay" daga haka ta fita shi kuma yaja wayan shi zai mata transfer yaga datan shi ashe ya kare, Daddy ya shigo duba shi yaga jikin da ɗan sauki yanzu yana taba goshin shi dan yaji temperature ɗin sai ga Mummy ta kuma buɗe kofar dakin tace "Rayyan ba zaka turomin ba ne, kaima?" yace "Mummy, datan nawa ne ya kare, ki buɗe min hotspot sai na tsaya data sai na Miki transfer din" Daddy kallon ta kawai yake daga inda take tsaye a bakin kofar, ta buɗe masa Rayyan ya mata transfer a take tace "Ya shigo, Allah maka Albarka" daga haka ta kulle masa kofar ta wuce parking space. Leena da ake wanke mata kai ta sake dialing numbern Muhammad har yanzu baya picking call dinta, zuwa yanzu ta fara damuwa dan be taɓa mata haka ba, infact tana kira zai bari ya yanke sai kuma immediately ya kira ta back amma tun juya take kiran sa yaki daga wa kuma ko message dinsa bata gani ba as usual Kuma hakan be taɓa faruwa ba, she looks so disturbed Zahra tayi dariya tace "Haba amarya ai kya bar shi ya huta mana, kika san ko suna ta hidima acan ya bar wayan a daki ne, kalli yadda kika wani ruɗe" Leena ta sake baki tana kallon ta ita bata ɗauka har Zahra ta fahimci abun da ke damun ta bama ta Harare ta ta ɗauke kai, me mata gyaran gashi tace "A'a barta tayi waya da ango ta" Zahra ta kwashe da dariya ita bata san yaushe Leena ta koma haka ba. Mutumin da suke gaban sa ya mika musu magani a bakar leda yace Wannan kuma ki tabbatar kinsa a abinci gidan yadda kowa zai ci, toh hakan zai sa yarinya kowa ya tsane ta tayi bakin jini a idon mutane daga ita har uwar ta ta" Mummy ta mika hannun dama zata karɓa ya daka mata tsawa yace "ba'a aiki da hannun dama anan" jiki na bari tana murmushi ta mika matsa hannun hagu ta karba, a hanyan su ta dawowa gida Mummy tace "ke baki ga yanda hankali na ya kwanta lokacin da ya hasko mana yaron na ta fama da kansa ba" duk suka kwashe da dariya Aminiyarta tace "yanzu kuma maganar auren Rayyan da Layla zamu fara facing, kuma banji kince min wani abu ba" tace "ki kwantar da hankalin ki yau ina komawa gida maganar da zan ɗago kenan, jikin nasa yau din naga da ɗan sauki ai" . Gaba ɗaya Ummi ta tsorata da lamarin Muhammad, tana kallon Nawaal tace "yanzu mu Muhammad yake son tonawa asiri a duniyan nan" Nawaal ta share hawayen ta tace "Ummi ko ƙaffara ba zan yi ba wallahi Muhammad ba haka nan yake faɗin abun ba kin sa ba, kamar fa baya hankalin sa ne, amma kiyi shiru muga zuwa anjima kar Abba yaji zancen nan, muyi ta addu'a kawai". Ba Zahra ba hatta wanda ke saloon ɗin sai kallon Leena suke ganin yadda red and black henna ya mata mugun kyau ga yadda take ta wani sheki kana ganin ta kasan amarya ce Amma gaba ɗaya hankalin Leena be kwanta da wannan shirun Muhammad ba ace yau har Magrib be kira ba ana gobe daura auren su. Basu suka koma gida ba sai wajajen karfe takwas na dare, su Anty Binta Suna ta yaba kyan Lallen Ammi nata lura da yanayin ta amma dai ta dangan ta hakan da cewa ko wacca amarya takan sinci kanta a haka, dakin ta ta wuce. Har 12 na dare ba kiran Muhammad, Leena ta shiga toilet ta kulle ta fashe da kuka sai da tayi me isarta sannan ta rubuta masa message tana gamawa ta tura masa ta wanke fuskan ta ta fito. Rana bata karya sai dai uwar ɗa taji kunya, yau Saturday ranan ɗaura auren Leena da angon ta Muhammad kenan, tun asuba aka hura wuta aka daura breakfast, Anty Jidda ana idar da asuba ta shigo gidan, kallon yanayin Leena yasa tayi ta bata baki dan ta ɗauka tunanin barin gida take, Anty Mairamah dake bakin murhu ta daura tukunyan ruwa ta koma ciki dan kiran Binta da Jiddah su taya ta kulla alalen da aka kawo a wajan markade. Mummy tana idar da Sallah ta dauki kullin maganin jiya dama ta daure a bakin riganta gudun karya bata, ta fito compound tana bin ko ina da kallo ganin ba kowa saboda ko haske garin be gama yi ba backyard ɗin Mummy ta nufa inda aka hura
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 50