suka fita suna zuwa part ɗin Daddy ta tsaya daga waje tana sallama, bata manta lokacin da tazo ɗakin Daddy zata nuna masa JSCE result ɗinta ba Mummy ta kama ta a parlorn sai da ta fasa mata baki har da jini, jikin ta kuwa sai da yayi jaa dan duka akan haka sai da suka yi faɗa da Daddy wanda hakan ya kara mata bakin jini a wajan ta shiyasa tun daga ranan bata kara attempting shiga ba kullum a waje take tsaya wa, kara sallama tayi taji Daddy be Amsa mata ba Ayaan yace "Addah, just go, I'll enter. Maybe Daddy is in the bedroom, that's why he didn't hear us" Leena ta girgiza kai bata son tafiya ta barshi a wajen dan anything can happen after some minutes sai ga Daddy ya fito zai kulle kofar da mamaki yake kallon Leena, Ayaan yace "Daddy tun ɗazu muke ta sallama" ya karasa gun Daddy, Daddy ya ɗaga sa sama yana dariya, Leena tace "Ina kwana" yace "Ina baki jin magana ko, Leena? Didn't I tell you that whenever you come here, you can just come in?" ta sunkuyar da kai tana wasa da fingers dinta tace "Daddy I'm sorry" yace "It's Okay " Ayaan dake hannun Daddy yace "bye" Leena ta juya jikin ta yayi ta wuce ciki, tana shiga gun wayan ta ta wuce Ammi na kallon ta ta kunna wayan ta ganin ba missed call balle SMS ta wuce dinning Ammi tace "idan kin gama breakfast ɗin ki wanke plates ɗin" tace "toh Ammi" tana gama breakfast ta wuce kitchen before 9am ta gama ta wuce ɗakin ta sake duba wayan ta tayi taga shiru. Bayan ta fito a wanka tasa kaya hakanan taji hawaye ya gangaro mata ta share ta ɗauki Littafin ta ta fara duba abubuwan da ta karanta kafin Zahra ta zo. Da yamma bayan ta dawo daga school ta gaishe da Ammi, Ammi tace "Leena ko zaki je ki gaishe da Mami yanzu, amma karni daɗe, gobe kuma sai kuje shopping tunda Sunday zasu dawo" Leena tayi shiru Ammi tace "naga ba dadi kin mata alkawarin Saturday zaki je" tace "Toh, Ammi" daga haka ta wuce dakin ta ɗaukan wayan ta tayi tana expecting ganin call ɗin sa nanma shiru, ta wuce ta chanza kaya sai gashi ta fito tana kallon Ammi tace "Ammi ina Ayaan?, sai mu tafi da shi" Ammi tace "Daddyn ku ya fita da shi" tace "toh barin tafi" Leena ta kama hanyar fita a bakin gate tayi clashing da Rayyan shi da kannan sa ko kallon su bata yi ba tayi wucewar ta da kafa ta karasa gidan su Mami gatekeeper ya buɗe mata gate ta shiga parlorn da sallama Mami na zaune a sofa Sadeeq yana kwance a 3 seater yana kallo Sultan shima yana zaune yana ba Mami labari, ta karasa jikin parlorn Leena tayi hugging ɗinta Mami tace "Ai yanzu Leena kin daina sona ai" tace "Wallahi Mami ba haka bane" Sultan yace "Iyyee, Wato yau dan Kinga Mami shine ko magana babu ko?" tana murmushi tace "Ai zan gaishe ku, barin gama da Mami na" Mami tace "Ah toh" sai sannan tace "Uncle Sultan ina wuni" yace "Lafiya kau, ya exams ɗin" tace "Alhamdulillah" ta ɗan leka Sadeeq dake kwance tana murmushi tace "Uncle Sadeeq" Sadeeq yayi kamar be ji ba Sultan ya taɓa sa yace "baka ji ana maka magana bane" wani kallo ya masa yace "Waye?" Sultan yace "Leena mana" Sadeeq yace "Can you tell me who she is?" ba Leena ba har Sultan sai da ya buɗe baki yana kallon sa Mami tace "kyale sa abun ki" ko juyowa be yi ba balle ya kalli direction ɗin sa Leena ta harare sa. sai kusa da Magrib Leena ta fito a ɗakin Mami a parlorn ta haɗu da su Sadeeq ko kallon direction ɗin sa bata yi ba tace "Uncle Sultan barin tafi" yace "so soon?" tayi dariya tace "it's almost Magrib fah" ya gyaɗa kai yace"wait barin kai ki" sai sannan Sadeeq ya kalli Sultan, Sultan ya wuce sa ya ɗauki keyn motar sa. Da Daddare bayan Leena tana part ɗin Hajiya suna hira Hajiya na bata labarin daa Leena tana ta dariya wayan ta ne ya fara ringing kallon screen ɗin tayi ganin Muhammad yasa da sauri ta ɗauki wayan tace "Hajiya sai da safe" tayi receiving call ɗin ta kai kunne tana sauri ta wuce part ɗinsu ko gama buɗe labulan parlorn bata yi ba zata fita Rayyan da zai shiga parlorn Hajiya kenan Leena ta fada jikin sa rike ta yayi sai da ta tsaisaita kanta sannan ta wuce sa ko kallon sa bata yi ba waya kare a kunnen ta, binta yayi da kallo yaga still waya na kare a kunnan ta, kara sa cikin parlorn yayi, Hajiya tace "ka gane min yarinyar nan, tun ɗazu fa take nan muke labarin mu, shikenan saurayin ta na kiran ta shine fa ta rikice ko kallo na bata yi ba ta tashi wai sai da safe" ta karasa maganan tana rike haɓa Rayyan yafi minti biyar yana kallon Hajiya kamar wani statue Hajiya tace "ya zaka zo ka sani gaba kamar wata ƴar iska?" Sai sannan Rayyan yace "Hajiya ita Leenan ne take da saurayi?" Hajiya tace "Toh kar tayi? yarinya Ma-shaa-Allah so kake tayi ta zama mana haka ta buɗe ido" ya sauke idon sa kasa without saying anything sai can yace "Sai da safe" Hajiya tace "ikon Allah! Amma lafiya ko? Ka shigo ka sani a gaba da kallo sai kuma ka tashi kace zaka tafi?" ba kalli Hajiya ba ya fice abin sa. Leena da ta ɗauki wayan Muhammad shiru tayi taki ce masa komai tana karasa cikin ɗakin ta ta faɗa kan gado still wayan na kunnen ta ta fara sheshsheka Muhammad yace"SubhanAllah what's wrong dear" kana jin muryan sa kasan yayi maganar cikin damuwa tace "shine yau throughout baka kira Ni ba?" Muhammad yayi shiru yace "Baby na ɗauka ai kamar ina takura ki ne, kuma wallahi yau na wuni ina aiki ne gashi ni ne nayi organizing zuwan su Abba na jibi" tayi shiru itama tasan duk lokacin da suke waya bata basa attention sbd bata da interest, yace "Baby" tace "Uhm" yace "I'm so sorry" tace "it's Okayy" yace "ko sai gobe na biyo su Abba, na zo bada hakuri tukun" tace "Ai nayi hakuri" ba Leena ta kwanta ba sai pass 12am suna ta hira da Muhammad ita kanta tayi mamakin chanza wanta. Yau Saturday, Daddy ya hayo masu aiki suka gyara gidan tass duk wani lungu da sakon gidan sai da aka gyara flowers akayi streaming, masu paint suma suka zo da kayan aikin su. Kamar karfe 10am Mummy ta fito daga kitchen tana kallon Rayyan dake aiki a system ɗin sa tace "Ni kam Rayyan meke faruwa ne a gidan nan" yace "wallahi Nima Mummy ban sani ba, kawai dai naga Daddy yasa na kira masa masu paint zuwa na kuma naga anata sanitation" tayi shiru tace "kuma baka tambaye sa ba?" ya girgiza kansa yace "A'a ban tambaye sa ba" sai ga Nisreen ta shigo tace "Mummy wai yau muna da manyan baki?" Mummy dake kallon ta tace "waya fada Miki?" tace "Chap ai Mummy ki fita cikin compound ki ga yadda ake gyaran gidan nan, shine na tambaye Hajiya tace wai Abokanan Daddy ƴan siyasa ne zasu zo masa" Mummy tace"Ikon Allah, toh Daddyn naku be faɗa min ba" daga haka ta kama hanyar ɗakin ta at least taji hankalin ta ya ɗan kwanta akan da zu. Ammi ta mika wa Leena list ɗin hannun ta tace "ku fara zuwa wajen Chef Siyama ku bata list ɗin abinci da snacks ɗin da zata yi gobe, sannan sai ku wuce supermarket" Leena tace "toh Ammi" Ammi tace "kice mata na kira ta wayan akashe tana kunna wa ta kira Ni back" Leena tace "In shaa Allah" Leena na kallon Zahra tace "Mu tafi Zahra" Zahra ta tashi suka fita a compound suka haɗu da Rayyan da zai fita shima kallo daya Leena ta masa ta ɗauke kanta haɗa ido yayi da Zahra haka taji ba zata iya cin dry ba tace "Ina kwana " yace "Lafiya" daga haka ya wuce parking space. A bakin street ɗinsu suka tsaya suna jiran taxi sai ga Rayyan ya zo zai wuce sai kuma ya tsaya ya sauke glass ɗinsa yace "ina zaku" Zahra zata yi magana Leena ta riga ta tace "thank you, Muna jiran wani" kallon Leena yake ba kiftawa sai kuma yaja motar sa yayi gaba. A layin gidan abincin Chef Siyama taxi ya tsaya suka sauka suna kallon layin to figure out gidan nata opposite ɗin inda suka sauka su ka ga maza guda Uku kuma duk kallon Leena suke yi suna magana Zahra tace "Ke Leena kin san waɗannan mazan ne? Leena tace "dan Allah ki dena kallon su Zahra" dube duben gidan suka yi Zahra tace "karshe fa Leena sai mun tambaye mazan nan fah" Leena taja ta tsaya tace "sai dai ke ki tambaye su amma Ni ba zan tambaye su ba" Zahra ta karasa kusa da su tayi sallama suka amsa mata tace "Gidan abincin Chef Siyama muke nema Please" dayan yace ai next street ne ba wannan ba" sai sannan dayan yayi saurin cewa "Dan Allah wancan ƴar uwan ki ce" tace "Eh" yace "basu kama da wannan Malik ɗin" sai sannan Zahra ta kalle sa, ta sake baki with shock written all over her face, kallon sa take babu kiftawa da badan wannan na miji bane kuma dan babba bane zata iya rantse wa identical twin ɗin Leena ne, his eyebrows, lips ɗinsa, yadda idon sa yake, da yadda yake starring one place sak irin na Leena, bakin ta na shaking tace "Wallahi Allah kamar identical twin ɗin ta" sai sannan Malik ya ɗaga kai yana kallon Zahra......
[5/28, 7:39 PM] Jiddatulkhayr writes: *AGOLA (Behind the palace walls)*
17.........
Zahra bata taɓa shiga ruɗani irin na yau ba, ganin kallon da Malik ke mata yasa bakin ta na rawa tace "Ina wuni" ɗauke kansa yayi daga kallon ta kuma be amsa mata ba juyawa tayi ta koma inda Leena ke jiran ta, Leena tace "kinje kin sake musu fuska kuna magana, kawai ki tambaye abu shine zaki daɗe?" Zahra ta rike hannun Leena tace "Dan Allah kizo mu karasa wajan su kiga abin da yasa na ruɗe" Leena ta kwace hannun ta da karfi tace "Dan Allah muyi abinda ya kawo mu" Zahra tace "gidan na next line ne, Dan Allah Leena kizo muje ki gansa" Leena taja baya ta tsaya tana kallon ta da mamaki sai kuma ta kama tafiya Zahra ta bita tace "wani me kama da ke na gani" Leena ta harare ta Zahra tace "Wallahi Leena He's the spitting image of you" Leena ta tsaya tana kallon ta hangaga sai kuma tace "You must be joking, Allah ma ya sauwake" Zahra tace "toh kin gansa ne kike cewa hakan? Toh barin faɗa Miki in ba sai dana ruɗe ba, kin san Allah? Like two peas in a pod" Leena tayi dariya tace "A'a ki ma ce 1 pea muke" Zahra tace "Allah ya haɗa ku wata rana zaki yarda da abinda nake faɗa Miki" suna shiga next line suka hango signboard ɗin a kofar gidan abincin Chef Siyama suka shiga cikin babban gidan suka same ta tana koyawa student ɗinta abinci, tana kallon su ta basu kujera suka zauna bayan sun gaishe ta Leena ta mika mata list ɗin hannunta tace "Ammi na ta kira ki wayan ki akashe, wannan list ɗin ordern da tayi na gobe" Chef Siyama tace"Oh Okay, kar de ke ƴar sirbajo ce? Yanzu muka yi waya" Leena na Murmushi ta gyaɗa kai tace "ikon Allah, gashi ke ɗinma Ma shaa Allah sai dai baki kama da Ammin naki, ita ana ganin ta zaka gane buzuwace" Wata budurwa da tun shigowan Leena take kallon ta tace "Dan Allah amma ke kanwar Uncle Malik ne?" Leena ta kalle ta Zahra tace "Ahtoh gwara ta baki amsa" Leena tace "banda yaya ni, ban ma san shi ba" yarinyar tace "Ikon Allah" ta kalli ƴar uwan ta da mamaki tace "ke baki ga kamar nasu ba?" tace "ai ban ganta ba sai da kikayi magana, wallahi sai ka rantse shine a hijab badan shi ɗin Babba bane" ta kare maganar tana dariya. Dawowan Daddy yayi daidai dana Rayyan, tare suka karasa har sashen su Rayyan, ya zauna akan cushion yace "Yima Maman ku magana" daga haka Rayyan ya shiga mata magana suka fito tare tana kallon sa ta zauna kujeran dake opposite ɗin sa tace "Gani" yayi gyaran murya yace "Dama nace barin sanar Miki anjima in shaa Allah za'a kawo goron tambayar Leena" Mummy da Rayyan har haɗa baki suka yi wajan cewa 'goron Leena? Daddy yace "in shaa Allah" Rayyan ya fara jin kansa na juya masa ɗakin ma gaba ɗaya gani yayi ya masa duhu, haka zalika wajan Mummy wanda har yanzu shock ɗin bai barta ba, ta gagara magana Daddy na kallon Rayyan yace "Anjima zaka je ɗauko su" daga haka Mummy ta tashi ta wuce ciki wanda ko kaɗan ba zata iya faɗin exactly me take ji ba, Rayyan ya dafa kansa da hannu bibbiyu Daddy yace "Lafiya Rayyan? Sai sannan ya ɗaga kansa ya kalli Daddy da jajayan idon sa Daddy yace "Are you Alright?" ya gyaɗa masa kai daga haka ya tashi ya fita a parlorn Daddy ya bishi da kallo, ba inda Rayyan ya tsaya sai part ɗin Hajiya har zai shiga kuma sai ya fasa ya koma part ɗinsu, zai shiga sai yaga Daddy zai fito yaja baya saida Daddy ya fito sannan ya shiga, ɗakin sa ya wuce yana shiga yasa key nan wajan ya tsulale tsabar yadda yake ji garin na juya masa. Bayan Leena sun fito a taxi suka kama hanyar shiga cikin mall ɗin Zahra sai zuba take Leena hankalin ta kwatakwata baya gurun hankalin ta ya tafi can wani duniyar daban tana gaba Zahra na biye da ita a baya a daidai Entrance door Leena taji tayi karo da mutun da sauri taja baya ta ɗaga kanta da niyyar Bama wanda ta bige hakuri, Hakurin nata makalewa yayi daidai lokacin da taji wani bugun zuciya shima hakan ne a gurin sa sun ɗauki some secs a haka suna starring each other, Maganar Zahra ce ya dawo da su daga duniyar shock da suka faɗa tace "Leena are you, Okay" sai sannan Leena ta bashi hanya bata san sanda tace "Sorry" ba, Zahra ta zaro ido dan ganin sa da tayi awajan, shi kuma ya sauka ya ci-gaba da tafiyan sa as gentle as he is. Zahra tace "Mukam Leena ko dai gamo yau muka yi ne?" Leena har sannan tana ɓari tace "Dan Allah mubar maganan nan" Zahra ta taɓe baki, har suka gama sayyayan da za suyi Leena kwatakwata bata da nutsuwa. Mummy da take ta kiran Fatima bata ɗaukawa hakan yasa tayi ji fa da watan nata ta rasa meke mata daɗi a duniyar toh ina ma zata yanzu?, zama tayi a bakin gado tayi nisa a tunanin da take. Ammi da kawarta Zainab ba abinda suka mance basu haɗa musu naci ko na sha ba Zainab tace "Ai kuwa rahama na Ubangiji duk kin ka da mutun Idan Allah ya bashi ba yadda zakayi" Ammi tace "Allah kyauta kawai ya shiryar damu". Daddy ya dinga kiran Rayyan baya ɗauka hakan ya bawa Daddy haushi yana kallon Amininsa yace "Ni Rayyan zai sa naji kunya? taya zan sa driver kaɗai yaje ɗauko su, ai sai su ga kamar ban karrama su ba" Aminin nasa yace "barin kira Farouq idan yana nan kawai sai su tafi tare da naka driver ɗin" daga haka ya fara dialing Numbern ɗan nasa. Mummy dai na zaune inda take tun ɗazu, ringing ɗin wayan ta taji a wajan da ta yar da shi da sauri ta karasa ganin Fatima yasa ta ɗauka ta kai kunne muryan ta na shaking tace "Fatima na mutu na lalace, ke da kika ce min zaki zo har yanzu shiru? Toh wallahi yanzu za'a kawo gaisuwar yarinyar nan" tace "Kiyi hakuri gani nan na kusa karasowa" daga haka ta katse kiran tana share zufan da yake gangaro mata a fuska. Leena na kwance sai waya take da Muhammad, Zahra na gefen ta tana game daga karshe ajiye wayar tayi a gefe tana kallon shagwaba da Leena take zuba masa, Zahra ta gyaɗa mata kai tace "Shegiya kika ce min baki son sa" tayi mata maganar kamar raɗa Leena ta harare ta ta ɗauke kai taci gaba da wayan ta, Hajiya ta doka sallama Ammi da Anty zainab suka amsa ta karasa cikin parlorn tana ma Ammi godiyan kayan daɗin da ta kawo mata, Ammi tace "Wallahi bakomai Hajiya, Hajiya tace "ina Linan take ne wai?" Ammi tace "tana ɗakin ta" daga haka ta wuce ɗakin Leena Hajiya ta sake baki tana kallon Leena, Leena kuma ganin Hajiya yas ta tashi daga kwance da take yi ta cire wayan a kunnen ta tana turo baki Hajiya tace "Eh lalle kam, yaran yanzu Allah ba kunya gare ku ba, mu fa lokacin mu idan aka ce za'a kawo gaisuwar mu toh guduwa muke bamu tsayawa, ko runfa bamu haɗawa da iyayen mu" Leena ta turo maku tace "toh ai ku naga lokacin ku daban muma daban" tana karasa maganar ta wuce toilet da gudu tabar Hajiya baki buɗe Zahra banda dariya ba abinda take yi, Hajiya ta fito parlor tace "Tabbas yau Lina ta faɗa min magana" Anty Zahra ta fara dariya tace "toh ai Hajiya gaskiya ta faɗa" ta karasa maganar tana dariya daga haka Hajiya ta fita tana cewa "ai zaki zo daki na". Motoci da suka amsa motoci kusan goma ajere suka shigo layin su Leena banda motocin securities da suke biye da su, Nan cikin layin suka samu waje sukayi parking karan jiniya ya cika unguwar aminin Daddy ne ya fita har kofar gidan ya shigo da su direct parlorn Daddy wasu daga cikin securities suka sauke akwati set biyu suka shigo da su amma basu shigar ɗakin Daddy ba nan bakin kofar parlorn suka bari, bayan sunyi gaisuwa nan suka fara bayanin game da zuwan su. Fatima ta karasa layin amma ganin motoci sun cika layi ba wajan shiga yasa ta tsaya ta kira Mummy, Mummy da ta tsaya tana leke ta jikin windown dakin ta taji karan kira ta ɗauka da sauri Fatima tace "gani na shigo amma layin naku ba wajan parking fah, me yake faruwa ne a unguwar" Mummy with cracking voice tace "ke de ki bari, wallahi wanda suka kawo gaisuwar yarinyar nan ne, na shiga uku na nikam" Fatima ta gwalo ido tace "tab wallahi wannan ba kananun mutane bane, barin karaso da kafa kawai" daga haka tayi parking. Hajiya dake compound ta sake baki ta koma ciki tana kabbara. Sun so asa bikin nan da 3 weeks Daddy yace "Duba da yadda kuka ce yarinyar ba zata zauna a garin nan ba, kuma kunga tana kan SSCE ne, gashi zata yi saukan Haddah nan da 3 weeks ɗin, gama exams ɗinta ma zai kai wannan lokacin why not asa bikin nan da 5 weeks". Anty Zahra tasa securities ɗin suka karasa da abincin cikin parlorn Daddy. Fatima ta shiga parlorn da sallama Mummy ta fito da sauri Fatima tana kallon Mummy tace "Kambala'iiiii, toh da kyar ace ba ɗan gwamna ƴar nan zata aura ba, Kinga cikin unguwan nan kuwa? Kai kilama shugaban kasa ne" ta karasa magana tana rike haɓa sai kuma tace "Lalle da kyar idan ba abunda nake tunanin bane, chap shiyasa naga Daddyn su Rayyan ɗin ya kuma gƴara gida nan" Mummy tace "Yanzu meye mafita? Wallahi ina faɗa Miki zuciyata kamar zata bugu, na rasa inda zansa raina, Abu ɗaya kawai na sani, da rai na bazan taɓa bari ayi auren nan ba" Fatima tayi dariya tace "Kinsan ko hauka kike baki isa hana wannan auren ba ko? Dan idan kuɗi ne daga gani ba zaki taɓa hada mijin ki da su ba" Mummy tayi shiru Fatima tace "Mafita ɗaya ne, idan har zaki yarda" Mummy tace "idan har za'a fasa I'm ready". Anty Zainab tace "Kai sirbajo aina Leena ta haɗu da wannan mutumin?" Ammi tace "tafiyan ta Abuja yin wannan poem ɗin ne fa ta haɗu da shi acan" Anty zainab tace "Allah mai iko, toh Allah tabbatar mana da Alkhairin sa". Duk suka fito a parlorn kowa da annuri a fuskan sa Har bakin mota Daddy ya raka su, bayan sun jiyo sun kama hanya Aminin Daddy yace "Nima barin tafi ba sai na koma ciki ba" duk yadda Daddy yaso ya dawo ciki amma yaki yace "toh ai Abunda ya kawo mu mun gama" haka Daddy ya kyale sa shima ya juya". Leena da ta fito ɗaukan ruwa tana jikin fridge jin muryan Daddy na magana yasa ta sunkuya da sauri, Daddy na kallon Sirbajo yace "Ku fito sai ku ga kayan, kuyi yadda za'ayi da su". Hajiya ta gwalo ido tana kabbar tace "Tabbas Allah yaga marai cin Lina, ji goro sai kace wanda zamu buɗe Sufamaket?". Dakyar Fatima ta lallaɓa Mummy akan suzo su ga kaya ko da na second ne kar ace suna hassada tunda Daddy da kansa yayi magana. Bayan sun karasa Mummy ta kasa yarda da abinda idon ta ke gani Fatima banda gyada kai ba abin da take yi duk sun kasa magana Hajiya tace "ikon Allah kalli yadda harda akwati set biyu kuma wai duk acikin goron tambaya? Chap ai a wannan marran sai dai ɗan ministan kam? take Mummy da Fatima suka kalli juna Mummy taji kamar ba zata iya tsayuwa ba, take ta juya ta kama hanyar ɗakin ta, ganin garin ma take yana juya mata, Fatima tayi yake tace "Eh lalle yarinya kam tayi goshi" daga haka ta juya itama. Hajiya ta taɓe baki. Sai can Magrib Anty zainab ta tafi, Zahra ma sai kusan Magrib ta tafi Ammi ta bata kuɗin mota ta ɗeba mata snacks ta haɗa mata da turare da sabulu. Bayan Daddy ya dawo daga Magrib yaga be ga Rayyan ba ya shiga parlorn Mummy ya haɗu da Niswa yace "Ina yayan ku?" tace "Bangan sa ba tun ɗazu" ɗakin sa ya karasa ya tura kofan yaji a kulle Mummy da ta fito daga kitchen Daddy ya kale ta yace "ina Rayyan?" tace "Rabo na da shi tun da rana" daga haka ya juya ya fita. Mummy ta zauna nan kujera tayi tagumi ta rasa yadda zata sa ranta taji daɗi da ta tuna Shawarar Fatima sai yaji dama dama Niswa ta kalle ta tace "Mummy baki da lafiya ne?" Mummy ta juya tace "Dan uwar ki ki tashi ki ban waje kafin ranki ya ɓaci" tsimsim Niswa ta tashi, ɗakin su ta wuce taga Nisreen na Assignment, Nisreen tace "Anty Niswa, me yake damun Mummy?" tace "Nima ina zan sani? ba tare muka dawo gidan nan muka same ta haka ba?" daga haka ta jawo wayan ta tayi dialing numbern Rayyan har ya katse be ɗauka ba ta kuma dialing still ba amsa ta ajiye wayan. Ammi dake kallon Leena tace "Toh me na kukan?" tana share hawayen ta tace "Ammi toh Meyasa za'a sa 5 weeks? Kuma ba'a Kaduna zan zauna ba, Ni kuma Ammi bana son nayi nisa dake?" Ammi tace "Naga a Abujan ma ga Antyn ki Jiddah, ai atleast akwai wanda kika sani kuma naga gasu Sadeeq duk sun ɗauke ki a matsayin kanwa ko bana kusa dake zasu taimake ki idan taimakon kike nema beside ma Allah ba zai sa hakan ma ya faru ba tunda kina addu'a kuma nima ina Miki" ta gyada kai sai kuma tace "Ammi toh maganar 5 weeks ɗin kice a ɗaga asa 1 year" ta karasa maganar tana fashewa da kuka Ammi ta dinga kallon ta sai kuma tace "wallahi abin naki iskanci ne, anan idan har Muhammad
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 50