hankali na idan na tuna bikin wai in 2 weeks time ne" Fu'ad ya dinga kallon sa cike da tausaya masa. Ayrah dake kwance tana waya har pass 11pm sai ga Layla ta shigo, Ayrah tace da wanda take wayan "Excuse me, I'll call back" ta dinga kallon yayar ta ta da ta shigo tace "Amma anty Layla ya kamata kima kanki fada, idan mune muke wannan yawace yawacen ya kamata ki tsawatar mana amma ace ke ne kike yi" Laylan ta sake baki tana kallon ta har ta gama magana ta wanke ta da mari tace "How dare you talk to me like that! Do you think I'm your mate or something? This is the first and last time you'll speak to me like that. Make sure you know what you're saying before you approach me, I'm not your mate Ayrah, Okay?" Ayrah ta rike kuncin ta tana kallon ta ta bangaje ta ta wuce dakin ta.*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
35.......
Yau wajan kwana 10 kenan da zuwan Leena da mijin ta Sadeeq Abuja, har mamakin yadda suka yi sabo da juna suke yi su, Sadeeq ya sha cewa 'They were made for each other'. Farkawan Leena kenan daga bacci, ta buɗe ido tana kallon kyakkyawan fuskan mijin na ta, yace "Ki daina kallo na kafin kyau na ya kare" dariya ta fara saboda bata ɗauka ya farka ba tace "Ni Karka min sharri, Honey" ta janye jikin ta a nashi, shima tashi yayi yana addu'an tashi a bacci, ta kalli agogon dakin da ke nuni da karfe 6:30am da sauri ta kalle sa tace "Honey, mun makkara fah", bayan sun idar da Sallah su kayi Morning zikr ɗin su tace "Good morning, Lee's Honey" ya ja hancin ta yace "Morning baby" ta langwabar da kai tace "Kaga da ka barni na fara girki da sai yanzu na daura maka ko da light food ne, yanzu kafin ka je ka saya mana breakfast zaka makkara" yace "Oh, so kike ki fara girki ki wahalar min da kanki?" ya ja hancin ta yace "Maybe sai kin haifa min yara goma masu kama da ke sai ki fara" ta harare sa ta mike tana ninke Hijab ɗin ta tace "Yara goma sai kace wata inji" yayi dariya tace "at least da ka bari na fara kaga irin wannan rana sai kawai na mana breakfast fah" yace "sai mu sha tea da snacks ko?". Bayan Sadeeq ya gama breakfast har bakin motar ta raka sa ta mika masa briefcase dinsa sai kallon ta yake yi sannan ya karba tana waving ɗin sa har ya fita, ta koma cikin gida. Bayan Rayyan yayi parking kofar gidan su Layla, ya kira ta a waya, tana ɗauka yace "Kiyi sauri zan wuce office ne" daga haka ya katse kiran ba'a dau lokaci ba sai gata ta fito sai wani sheki skin ɗinta yake yi, front seat ta buɗe ta shiga tayi kasa da murya ta gaishe sa ya amsa, hannun sa ya kai wajan da kafafun ta yake ya ɗauki ladan wajan ya mika mata yace "Here is it" ta karba tana Godiya, sai kuma tace "Wai da gaske kake dama ba zaka yi attending any events ba?" yace "Meyasa kike son na ringa repeating kai na ne?" tace "Well, ɗan anjima zan tafi saloon, da yamma kuma, zamu fara event" yace "tun daga yanzu?" tace "Kai baby, yau fah saura 4 days shine tun daga yanzu" yace "Okay" duk maganan nan gaban motar dinsa yake kallo ita kuma ta zuba masa idanun ta, ya ɗan kalle ta yace "Toh zan tafi ko?" tace "Okay, take care of yourself for me, please" daga haka ta sauka tana waving dinsa, shi kuma yaja motar sa yayi gaba. Daidai wani eatry Leena tayi parking moton ta, ta sauka ta shiga ciki tayi ordern abinci tace a takeaway za'a zuba mata, bayan ta karba ta kama hanyar inda Sadeeq yake aiki, a daidai organization ɗin su tayi parking, tun daga bakin gate gatekeeper suka fara gaishe ta saboda sun san matar Sadeeq ne, tun da take haduwa da mutane kowa with respect ke gaishe ta har ta haura first floor, knocking office dinsa tayi yace "Who is it?" tayi shiru tana murmushi, ta sake knocking ya sake cewa "who is it?" taki magana , bayan ta sake knocking taji yaki amsa wa, ta dinga knocking Sadeeq yayi banza da ita, sanin ba zai amsa ba ta dinga dariya saboda komai na Sadeeq yana burgeta hankalin ta a kwance ta san 'yan mata ba ganin fuskan sa zasu yi ba, Ciro wayan ta tayi ta kira sa ya daga yace "Sweetheart, I miss you" tace "Toh buɗe min" yace "Ina?" tace "Office ɗin ka mana" ya katse kiran ya je ya buɗe mata ya sake baki yana kallon ta sai kuma ya masa mata ta shiga yace "Kamar kin san ina missing dinki" ta ajiye abincin akan table din gaban sa tace "Na san baka ci abinci ba ko? To gashi" ya langwabar da kai yana kallon ta yace "Sure, baby" tace "toh barin koma gida" ya mike sai kuma yaga tarin aikin dake kan table din sa yace "Oops da ba dan aiki ya min yawa ba, da na bikin mun koma gida tare" tace "Just take your time, Honey" daga haka ta fita tana kara jin son mijin nata har bargon jikin ta. Nisreen ta shiga parlorn na su da sallama, ta ajiye ghana-must-go ɗin hannun ta tace "Mummy ga ɗinkin nan" Mummy tace "Na Mother Eve din fah, Ya samu ya gama?" Nisreen tace "yana ciki" duk ta juye su nan kan kujera ta fara sorting nata out, Mummy ta dauki wani gown din dinner ɗinta tana kallo, Nisreen ta juya tana kallon Niswa da ko sau daya bata kalle su ba balle tayi magana akan nata dinkunan tace "Anty Niswa ba zaki duba na ki kayan ki gani ba?" Niswa taja tsaki Mummy ta sake baki tana kallon ta tace "Niswa bana son neman magana fah" daga haka Niswa ta mike ta wuce ɗakin su, Mummy ta bita da kallo, Nisreen tace "bari zan cire nata sai na kai mata" Mummy ta dauki nata tace "Ki kyale ta" daga haka ta wuce dakin ta da nata kayan a hannu, bayan Nisreen tabi Niswa daki da kayan tace "Ga naki kayan" sai sannan Niswa ta kalle ta tace "Toh ni nace a dinka min?" Nisreen tace "ashoben bikin Yaya ne fa? Niswa taja tsaki tace "Da kun san yadda na tsana Laylan nan wallahi ba wanda zai ce zai na min magana akan ta" Nisreen tace "ki daina fada haka kin san Mummy da Yaya ba zasuji dadi ba" Niswa tace "Dalla min shiru ke me kika tsani? Toh uban waya ce miki Yayan ma yana son ta ne? Wai fah akan ta har Mummy tabi bayan cin mutuncin da ta min wallahi idan naga dama sai na fadawa Daddy duk abinda ke faruwa a gidan nan inya so duk abunda zai faru ya faru, kowa ya huta shikenan ai" Nisree ta rufe bakin ta da hannun biyu tana kallon Niswa. Anyi decor cikin gidan nasu da balloons gurin har ya gaji da kyau tsabar yadda aka tsara sa ga wani babban banner dake rubuce da Layla's henna party, ga kuma friends dinta ta sukayi anko, Layla sai sheki ta keyi cikin shigar ta me kyau. Leena tana zaune a comfort zone ɗinta da ke cikin parlorn ta, a edge din parlon tayi creating wani waje ta gyara tayi arranging duk wani stuff da zata buka ta na creative writing ɗinta, ga kuma ɗan karamin bookshelf a gefe, ta mayar da hankalin ta kan rubutun poem da zata yi performing a wani organization, like kamar advertising zata musu, ji tayi an dafa ta ta baya a zabure ta mike tana kwala ihu da sauri Sadeeq ya rungume ta duk ya rike ce yace "I'm Sorry, baby" sai sannan tayi shiru tana maida numfashi leka fuskan ta yayi yace "Sorry, ban san zaki tsorata har haka ba" tace "ban fa ji shigowar ka bane, kuma ka zo da motar ka kuma?" yace "naga ai kinyi nisa cikin imagination world ɗinki, shiyasa ma baki ji shigowa ta ba" sai kuma ya fara dariya yace"ashe babyn tawa matsoraciya ce" ta zauna tana kallon sa, sai kuma ta mika masa papern da tayi rubutu tace "Taya ni gani ka ga ko akwai Abunda zan kara" ya karba yana mamaki irin talent dinta yace "baby, everything is great" tace "gobe ina performing next tomorrow sai tafiya Kaduna ko?" Kai kawai ya gƴaɗa mata, daga haka ya wuce ciki, itama ta ajiye papern ta mike tabi bayan sa. Mummy da take tsaye akan Rayyan tace "Toh yanzu saura kamin Transfer din 1 mil ko?" ba shi ba hatta Niswa saida ta daga kai tana kallon Mummy sai kuma ta taɓe baki saboda karban kudin Mummy yanzu ya fara yawa, Rayyan yace "1 mil kuma Mummy?" tace "Eh mana, ko baka ji bane zaka kuma tambaya ta?" ya girgiza kai yace "me kuma za'ayi da wannan kudin?" tace "Okay, tambaya ta kake sai na baka amsa kafin ka bani kuɗin?" Niswa tana ta Allah, Allah karya sa Rayyan ya bada, Rayyan yace "Wai dama naji ko important abu ne saboda ba kudin yanzu a waje na" ta masa wani kallo yace "I'm telling you, Mummy, bani da kudi" ta mike tace "toh ai shikenan, dama Hajiya Fatima ne ke bukata wai zasu kara ma masu organizing mother's Eve" daga haka ta wuce ciki Niswa tayi kasa da murya tace "Yaya wallahi gwara da baka bada ba, dan Allah duk sanda Mummy zata ce ka bada kace baka da kudi, taya dan rainin hankali su kama wajan event kuma suce babu kudi" kallon ta kawai yake har ta kai aya daga haka ya mike ya fita. Jiddah ce take knocking a kofar gidan su Sadeeq, Leena dake jikin Sadeeq ta kalle sa tace "kamar fah knocking akeyi" be tanka ta ba ya ci-gaba da cika file da yake yi a wayan sa ta mayar da kanta kan chest ɗin sa sanin kuma ba zai ce wani abun ba, sake knocking akayi tace " Honey kamar fah knocking akeyi" ya ajiye wayan hannun sa ya dago da kanta yana kallon ta yace "akan ki ake knocking ɗin?" tace "How?" yayi kissing dinsa yace "then, sai kiyi kamar baki ji ba, koma waye ne ya koma ba zai ɓata min wannan precious moments din ba" ta kwanta abunta tayi kasa da murya tace "kasan anty Jidda tace idan ta samu lokacin zata zo min ne" yace "Who is she?" tayi dariya tace "haba mana" yace "Ohh toh uwar me Jiddahn zata Miki? tayi wucewar ta kawai, yanzu kila Sultan ya koma Kaduna ne" tace "Ya zo ne?" yace "Eh" tace "shine be zo mana ba" yace "Nine ban so ba" tayi shiru taga kamar akan ta har Sultan be yarda da shi ba can tace "Amma kamar they love each other ko?" yace "ki bar munafukai tun suna yara suke son juna, dalilin da yasa ya dawo gidan mu kenan, sai daga baya suka yi fada har ya kai daga baya Sultan ya fara neman wata zai aura ganin Jiddah taki sauransa amma da ta ga maganar zai yi karfi Jiddah ta fara masa hauka har sai daya janye maganar" tayi shiru tana tunani yace "maganar da nake faɗa miki bai wani daɗe ba" tace "Nima zan so ganin sun yi aure, cos sun dace kuma kana ganin su kasan suna son junan su" yace "Uhm" duk maganar da suke yi ba'a daina knocking kofar ba, wayan sa ya fara ringing ya kalli me kiran yace "Inaga Jiddahn ne dan itace ke kiran" Leena ta sauka a jikin sa tace "inje in buɗe?" ya harare ta yace "idan ita da wani katon ne kuma fah?" Leena tayi dariya tana kallon sa har ya fita, yana budewa kuwa yaga Jiddah, babu alamar wasa a fuskar sa ya amsa gaisuwar da take masa, tayi dariya tace "Haba Yaya na toh me na daure min fuska da kake min kwana biyu?" Shi kam tuni ya shige ciki Leena ta fito dan tun zuwan su Abuja yau ne rana ta farko da zasu fara haduwa, Jiddah ta dinga kallon Leena ganin yadda ta kara wani haske tana wani glowing ga kuma kiɓan da ta kara. Bayan Leena ta karasa cikin parlorn ta gaishe ta Jiddah tana murmushi tace "Lafiya klau Anty Leena" Leena tace "Dan Allah anty Jiddah ki daina kira na da Anty" tace "Toh ai kin zama antyn ne tunda kina auren Ya Sadeeq" ta karasa maganar tana murmushi. Washe gari misalin ƙarfe 2:30pm kowa sai shirin tafiya wajan Mother's Eve ya keyi, Amarya kuma ta wuce shagon makeup. Hajiya tayi Sallama a kofar parlorn Ammi, Ammi ta amsa ta fito ta buɗe mata kofar tana kallonta yadda tasha kyau cikin kaya na alfarma tace "Sirbajo ke ba zaki wajan ebent ɗin bane ?" Ammi tayi shiru harga Allah bata da niyyar zuwa tace "Toh Hajiya bari na shirya" Hajiya tace "Toh ko ke fah, amma gaskiya kiyi sauri" daga haka Ammi ta wuce ciki dan shirya wa. Mummy ta sake baki tana kallon Niswa da ta fito daga kitchen rike da plate ɗin chips kuma zallan gajeran wando ne jikin ta sai riga mara hannu, Mummy tace "ke Niswa dama baki je wajan makeup ɗin bane?" Niswa ta yamutsa fuska tace "Eh, kuma banjin zan tafi saboda kai na na ciwo" Mummy tace "wallahi Niswa zan gwada Miki bad side of me fah, dan ubanki kamar hassada kike da Yayan naki? to wallahi ki shiga kisa kaya ga wadda zata min makeup sai ta mana tare" Niswa ta yamutsa fuska, Mummy tace "Wallahi kar kiyi, zaki sha mamaki na ina faɗa Miki" daga haka ta karasa wajan wadda zata mata makeup, tun kafin a gamawa Mummy sai ga Niswa ta fito ta zauna, ita dan tana gudun kar Mummy tayi maganin ta yasa kawai ta shirya ta fito. Wajan event har ya kaji da tsaruwa da kyau, event ake gudanar wa irin ta masu hannu da shuri, Mummy kam ta gagara tsayuwa waje daya sai washe baki take yi, Hajiya Fatima kam ba'a Magana, ba Ammi ba hatta Hajiya sai da tayi na daman attending event ɗin dan wani kallo ake musu na kaskanci, bayan bride na hotuna da sisters ɗinta Mummy ta karasa har inda Niswa take tace "Niswa wallahi ki shiga hankalin ki, baki ganin yadda ake ta kiran ku ne kina zaune? Wato zaki gwadawa duniya cewa kina da mugun hali ko?"Niswa ta mike ba tare da taga mahaifiyar ta ta ba ta wuce wajan da ake hotuna da amarya, Nisreen ta washe baki tace "yauwa Anty Niswa ba muyi da ke ba" Niswa na karasa wajan ta tsaya za'a musu hoto Layla tace "Ya dai?" Niswa tace "Kamar ya dai?" Layla tace "Ni sa'ar ki ce ko kuma kinga mate ɗinki ne anan da zaki hada kafada da ita?" Wata kawarta tace "kar dai ita ce kanwar tashi mara kunya?" Niswa ta ja dogon tsaki daga haka tabar wajan, Layla tace "Uban yarinyar nan zanci ina faɗa Miki" kawar ta tace "kar ki bata mood dinkin saboda ita Please". Hajiya ta mike tana kallon Ammi tace "tashi mu tafi Sirbajo, wallahi zasu san da Ni suke yi" Ammi ta mike dama ita gudun wulakanci take shiyasa da farko bata so zuwa ba, a hanya Hajiya ta dinga masifa tace "Wallahi dama tun ba yau ba matar nan ta raina Ni, kawai ina kauda kaine yanzun ma saboda Riyan ne nazo amma Ni ina zuwa Abinda ya shafe ta? Ko da ace ƴaƴanta mata ne ba zuwa zan yi ba" tayi shiru tana mamaki yadda Mummy da wasu kawayan ta suka musu, Hajiya tayi ƙwafa tace "gaba tafi baya yawa ai" tunda Layla ta dizga Niswa bata kara tsayawa a cikin Hall ɗin ba ko second ba tayi ba ta fita abin ta. Ganin kamar be ma ji shigowan sa ba ya ɗan buga table din gaban sa Rayyan daya ke zaune a Kujeran office dinsa yans kallon sama spaced out yayi sauri kallon sa, sai kuma yayi murmushi yace "Fu'ad" Fu'ad yace "Karfa ka jefa kanka cikin damuwa fah, you're a man, kana da wani Alternative, so please be strong" Rayyan ya shafa kansa yana murmushi yace "Just that" sai kuma yayi shiru Fu'ad yace "Whatsoever ya kamata ka sama kanka salama, da ace kai macace sai ka shiga wannan damuwar so tunda Allah ya baka zabi ai shikenan" Rayyan ya sauke ajiyan zuciya yace "Thank you for reminding me this, Fu'ad. In shaa Allah zan de na.*AGOLA (Behind the palace walls)* 🫧
_Wannan page ɗin na sadaukar wa Whatsapp group Fans din Leena, Ina godiya matuƙa_
36......
Leena ta fara hada kayan ta, tunda Sadeeq ya kalle ta sau daya bai sake kallon direction dinta, ta gama parking kayan ta tayi zipping akwatin, ta ɗaga ta kai gefe, sai sannan ta zauna tana kallon sa tace "Toh kai naga baka hada kayan ka ba? Ko da safe zaka hada?" ya shafa kansa yana kallonta yace "Toh ai babu available flight to Kaduna" tace "Toh sai mu tafi da mota kawai" yace "A'a bana son ki wahala" tace "Toh ai na taɓa zuwa Abuja ma a mota banji na gaji ba" yace "Shiiiit, Stop stressing yourself out by taking on too much" ta ɗan bata rai tana kallon sa ya mata Murmushi kawai daga haka ya kwanta, Leena ta dinga kallon sa dama taga take taken sa kamar baya son komawan nasu, wayar ta ta ɗauka and checked if there were available flight to Kaduna for tomorrow, ganin Akwai kuma karfe 10:00am zai tashi ta ringa kallon Sadeeq, ta buɗe baki zata yi magana kawai sai kuka Sadeeq ya mike yace "Me kuma?" da sauri ya karasa wajan ta tace "Ni ka kyale Ni, bayan ga available flight kace babu?" ya fara sosa kanshi dan be yi expecting zata duba ba, yace "to be honest with you dear, bana son tafiyan ki Kaduna a wannan week din" tace "Why?" yace "Kawai haka nan, ki bari sai next week kawai In-Shaa-Allah sai mu tafi" daga haka ya mike ta bi sa da kallo harya fita, tayi tagumi dama ita har mamaki ta yi da yace zasu Kaduna dan ta lura kwatakwata baya kaunar wani ya raɓe ta, balle ma da yaji bikin Rayyan ake yi, ita kuma ba dan shi take son zuwa ba just that tayi missing Ammi ne. Yau ranan daura auren Layla da angon ta Rayyan, kuma da daddare za suyi dinner. Daddy da yake part ɗin Ammi yana breakfast, bayan ya gama yana kallon ta yace "Amma zaki wajan dinnern Rayyan ɗin ko?" ta girgiza masa kai tace ba fa najin dadi, zazzaɓi nake ji. So, bana tunanin zan iya zuwa" ya mike yace "Okay, Amma ya kamata ki je asibiti, ina ga ni daga nan idan nayi wanka zan wuce wajan daura auren ne sai kuma reception" tace "Toh Allah ba su zaman lafiya" yace "Amin" daga haka ya fita, ita kuma ta dauki kulan abinci da ta sawa Hajiya ta fita da shi, cikin compound ɗin a cike yake da jama'a ana ta hada hada, wasu kuwa suna bakin murhu suna girki, a haka Ammi ta wuce ba tare ta tabi ta kan kowa ba, a kofar dakin Hajiya tayi sallama duk parlon a cike yake da baki 'yan uwan Daddy, Ammi ta shiga ta gaishe da mutanen parlorn sannan ta wuce bedroom ɗin Hajiya ta same ta tana zaune da wata Kanwar ta ta gaishe su duk suka amsa mata ta ajiye mata kulan, Hajiya tace "Ai kuwa na gode, yanzu dama na gama shan tea gani nayi kamar sun ma manta da mu a gidan yau, shiyasa Sa'adatu kawai ta daura musu abin da za suyi ƙarin kumollo" Ammi tace "kila ta sha'afa ne, hidiman mutane da yawa sai a hankali" Hajiya tayi murmushi tace "baki san halin Khadija ba ne, dama ba son samin take ba, duk da cewa ba ita ke girkin ba, balle yau data ga jama'a, ai ko dan su sai ta zubo" Kanwar Hajiya ta mike tace "idan akayi shiru ma ai tayi nasara ne babban kula zan ɗauka na kai nace a zuba na sashin Hajiya, tunda dan ɗanta muka taru anan" daga haka Hajiya Rabi ta fita, Ammi dai bata ce komai ba, can kuma ta mike tace "Hajiya toh barin leka su" Hajiya tayi godiya, Ammi ta shiga har cikin parlorn Mummy, kannan Mummy sai wani kallon kaskanci suke mata amma bata damu ba ta zauna a dinning tunda taga jama'a ne a parlorn kuma wasu kamar breakfast su ke, Niswa ce ta fito daga dakin Rayyan Ammi tace "Yauwa Niswa ina Mummyn na ku" tace "Tana ciki" Ammi tace "Ko zaki mata magana" har ta fara tafiya kuma sai ta koma zata ma Mummy magana, bayan ta shiga da sallama da alama magana mai mahimmanci suke tattaunawa Niswan tace "Anty ne ke Miki magana" Mummy ta mata wani kallo tace waye kuma Anty?" Niswan tace "Maman Leena mana" autar su Mummy ce tace "Toh ke baki ganin magana muke ne da ba zaki ce mata tayi wucewar ta ba" Niswan tace "tsawan me kuma kike min? Ni nawa ba aika bane" daga haka ta fita ta banka kofar, autar su ta daga kai tana kallon Mummy tace "Anty Khadija ni Niswa zata ma haka?" Mummy tace "kiyi hakuri, Nima kaina lamarin Niswa tsoro ya fara bani, wallahi ko shakka ta bata yi yanzu, yadda nake controlling Rayyan idan ita ce wallahi ko rabin yadda nake masa ba zata ɗauka ba" tace "Hmm, kin zaune kuma? Kika san ko ita kishiyar taki ce ta mata wani abu dan ta zama fitsararriya?" Mummy tayi shiru sai kuma ta mike tace "Barin je Naji uban me ya kawo ta". Bayan an daura auren Layla da Rayyan. wata Kanwar mahaifiyarta ce ta shiga cikin compound ɗin tana rangaɗa buɗa tana cewa an daura, wata kawar Layla tace "dan Allah kuyi shiru kamar an daura ake cewa" duk suka yi shiru nan suka jiyo abinda take fada suka fara taya Layla murna, Layla sanin Rayyan ba kiranta zai yi ba ta dauki wayan ta ta kira sa har ya katse bai ɗauka ba ta ajiye wayan mai makeup ta cigaba da mata makeup sai kuma wayan ta ya fara ringing da sauri ta ɗauka ganin Rayyan ne tayi sallama hadi ta cewa "Ango na" Rayyan yace "Naga kin kira ni" tayi shiru sai kuma tace "Ai kamata yayi ace kai ka fara kira na" yace "It's Okay, tunda gashi ke kin kira, right? Layla taji haushin amsa da ya bata amma ba daman ta gaya masa bakar magana ko dan friends dinga da ke zaune a gefen ta tace "Okay angon Layla, sai an jima" tun kafin ta karasa magana ya katse kiran. Leena ta ɗauki kiran da Mami take mata, bayan sun gaisa Mami tace "Amma za ku zo ɗin kuwa daughter?" Leena tace "A'a Mami, yace wai sai next week ne" tace "Okay, ai dana ga har pass 5 nace barin tambaya, na ɗauka za kiyi attending bikin Yayan na ki ai" Leena tayi murmushi kawai Mami tace "Toh Allah kaimu next week din, sai ku dawo tare da Jiddah dan itama tace zata dawo gida next week" Leena tace "Toh in shaa Allah Mami" Mami tace "Allah kawo ku lafiya" Leena tace "Ameen Mami". da Daddare ko da Mummy ta masawa Niswan sai ta shirya taje wajan dinner, Niswa ta kira saurayin ta akan ya zo ya ɗauke ta, ba'a dade ba sai kuwa ya karasa har kofar gidan su lokacin har an fara zuwa dinner, ta fito cikin ankon ta ko ta kan autar su Mummy dake faman saka takalmin ta bata bi ba tayi ficewar ta, ta fita ta ga motar sa a parke a kofar neighbors ɗinsu ta karasa ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 50