Muhammad ya gama cika sa yace "Idan kuma kana so, tana da Sisters duk wacca kace kana so a cikin ƴaƴana zan baka Son" Muhammad tunawa da yadda Leena ta taɓa basa labari yadda Mummy da yaranta mata suka sata gaba tun lokacin yaji ya tsane su with passion, yace "Dama da wacca aka bani a gida, nace sai Leena" Daddy na patting bayan sa yace "It's Okay" Daddy ya raka sa har inda drivern Muhammad yayi parking shi ya buɗe masa car door din da kansa ya shiga har sannan Muhammad kana ganin yanayin sa kasan yana cikin damuwa ainun Daddy ya koma cikin gidan sa da tausayin Muhammad, tun daga inda yayi parking yake kallon su, dama ganin Motar a kofar gidan yasa yayi parking gaba da gidan nasu, tun da Daddy ya fito yana rike da hannun sa har ya sa shi a mota be ɗauke idon sa a kansu ba, kallon su yake ba kiftawa har Daddy ya koma cikin gida sannan suma suka bar wajan, be taɓa jin yanayin da yake ciki a yanzu ba, nan da nan idon sa yayi mugun ja, saboda tsab ya gane sa, dan yana yawan ganin a Quarters ɗin su Jiddah and she once told him shine Fiancee din Leena, be san sannan ya kunna motar a mugun speed ba yabar layi. Jidda da ke zaune ita kaɗai a gidan sai cook ɗin su, tana game a wayan ta taga credit alert kuma daga Sadeeq, kiran sa tayi yana daga wa tace "Ya Sadeeq alert ɗin mene?" Murya sa kamar mara lafiya yace "duk abinda ake bukata a kara a kwatinan nan Please ki samu kije mall yanzu duk ki tsiyo" tayi shiru tana mamaki yanzu kuma, murya shi taji yace "Please Jiddah, wani abun nake yanzu ba zan iya zuwa be ne, ko Sultan ki roka ya raka ki" tace "Sultan ai ya tafi aiki dama ni da kaine muke hutu ai ka manta shi a gari yake, it's Okay zamu tafi da mai aiki" yace "thank you, idan kuɗi be isa ba just call me" tace "toh" bayan ya kashe tana mamakin sa, yau kuma?" Daga haka ta mike zuwa sanar da Cook ɗin su ta shirya kafin itama tayi wanka". Daddy da ke kallon Ammi yace su Binta fah yaushe zasu koma?" tace "sun ce sai an kai Leena, saboda jiya Mami ta kira akan Saturday ɗin Leena zata tare inji Sadeeq, nan da sati dai za'a ce" yace "Okay, dama driver zan sa da su din dan Allah su samu su taimaka mana su mayar da kayan Lefen da suka kawo" sai yanzu Ammi ta tuna da maganar Lefe tace "Ai kuwa ya kamata a mayar, toh zan musu magana sai su shirya zuwa gobe" Daddy yace "toh barin leka office sai na dawo". Ammi ta shiga dakin ta taga fitowan Leena kenan daga wanka tana shafa lotion Ammi ta karasa jikin dressing mirror ta dauki comb ta shiga gyarawa Leena gashin ta daya har gitse, bayan ta gama tana kallon 'yarta ta cikin mirror tace "Ma sha Allah, ai hakan kin fi kyau amma kullum baki son kamawa" ta ɓata fuska tace "Toh ai Ammi da zafi ne" Ammi tace "lalaci dai, amma ina zafi anan, haka zaki nayi a gidan miji kai a hargitse" Leena ta kalli Ammi sai kuma tayi frowning face dinta nan take ta tunowa Ammi memories ɗin baya, yadda take mata shagwaɓa da yadda Abban Leena ke biye mata, sak fuskan Leena daya da baban ta, hatta bakin su ɗaya, kawai ta kawar da wannan tunanin, tana kallon Leena tace "kisa kaya barin baki waje idan kika gama zamu yi magana" daga haka ta fita daga dakin after some minutes sai ta kara komawa cikin dakin ta zauna tana facing Leena ta rike hannayen ta tace "Leena ki faɗa min me damuwar ki? har yanzu baki san cewa Allah be ƙaddara Muhammad ba mijin ki bane" ta tsunkuyar da kanta tace "Ammi ai na riga da Nasan haka Nima kai na inason naga na daina tunanin sa ma, kawai dai da ba'a daura min Uncle Sadeeq bane" Ammi na kallon ta still tace "Saboda me? Leena Kiga kaunar da ƴan gidan su suke nuna Miki, tun kafin su san mu, ji yadda suka rike min ke lokacin tafiya na Niger, Leena shine ke zaki ki jinin su? me shi Sadeeq din ya nema ya rasa?" Leena ta sauke kanta kasa tace "Ammi shi fah baya so na, ko da yaushe baya son kula ni, dama Uncle Sultan ne sai Anty Jidda mu ke shiri" Ammi tace "baki fahimce sa bane, ni kuma inaga kamar nature ɗinsa ne haka Leena, da baya son ki ba zai nema a basa ke ba, dan Mami sai da tayi ta roko na akan a daura da Sadeeq dan ta dade da fahimtar yana son ki, kuma da bakin sa ma ya faɗa mata" Leena ta tsaya kallon Ammi jin wai Sadeeq da kansa yace yana son ta. sai kusan karfe biyar Jiddah ta dawo gida likis ita da mai aikin su suna shiga kuma suka ga Sultan har ya dawo daga aiki da alama ya sake wanka fita zai yi ganin su ya sa ya tsaya, Jidda ta buɗe bayan booth din motar mai aiki ta fara kwasa tana kai wa ciki, Sultan ya karasa har inda ta ke yace "daga ina kuma, kayan nan fah?" tace "wallahi Yaya ne fah ya sani wannan aikin, na gama wahala yau nake baka labari" Sultan ya sake baki yana kallon ta sai kuma yayi dariya yace "kin san yanzu haka shine ya dame rayuwa ta wai nazo can gidan nasa, ina wajan aiki ma ya dame rayuwa ta wai anemo masa masu aiki" Jiddah tace "baka ji yadda baya na ke min ba, Allah saboda Leena ce shiyasa na fita" yana kallon ta yace "toh Nima raka ni mana" ta dade kirji tace "ina?" yace "gidan Sadeeq din mana, muje muga kiran menene" tace "Allah kiyaye hanya amma ni na gama wahala ta yanzu" da kyar yayi convincing dinta ta yarda Amma sai da ya jira ta sake wanka taci abincin kafin suka fita, basu suka isa gidan nasa ba sai Magrib har wasu masallatai sun idar, Bayan Sultan yayi parking a kofar gidan suna kan sauka sai ga Sadeeq daga masallaci kusa da su yana tahowa alamar dai anan yayi Magrib, bayan ya karasa inda suke yace "Jiddah kin gama?" tace "eh, amma sai ka biya ni" Sultan yace "Uban me zaka nuna mana kasa muka taho da magrib ɗin nan" ya buɗe gate ɗin gidan ya shiga suma suna biye da shi a baya tun daga bakin gate suke kallon yadda gidan ta sake zama wata sabuwa suna shiga parlorn daga Jiddah har Sultan sake baki su kayi suna kallon sa Jiddah tace "yaushe akayi jere?" yana shafa kansa yace "Ɗazu masu Company suka zo suka yi" Sultan yana ta rike dariyar sa Sadeeq dake kallon Jiddah yace "an sa Everything a gidan, yanzu zaki je ki taho da ita?" Sultan da ya mike zaije yayi alwala ya jiyo da sauri jin furucin Sadeeq suka kalla juna da Jiddah kamar hadin baki suka fashe da dariya Jiddah harda hawaye tace "aina aka taba yin haka?" Sultan yace "yaushe kuma ka canza ra'ayi, kace shiyasa baka ji zafin girgiza acc dinka ba yau kenan" ko kallon su be sake yi ba, shi da da hali ma yaushe zai kula su ai sai de yaje ya dauko ta ya kawo ta da kansa.
Thank you Noor Imaan
*AGOLA (Behind the palace walls)*
31......
Har suka bar gidan Sadeeq yaki kula Jiddah da Sultan suma ko ta kansa basu bi ba suka kama hanya abin su suka tafi. Jiddah dake zaune gefen Mai tace "Mami kiji min fa an taɓa haka ne, kuma ai ana zuwa godiya toh shi yaje ne" Mami tace "toh in banda abun sa ai wannan ba abun fushi bane ni sai da kaina naje na sanar da Ammin ta yace gobe zata tare, shi kuma sai ya hakura goben kawai tunda suma zasu so ace su ɗan kimtsa tukun, da yamma kuma shi da su Sultan sai suje godiya" sallama suka yi alamar sun dawo daga sallar isha'i ne anan parlorn suka tarar da su bayan sun zauna suka gaishe da Mami, Mami na kallon Sadeeq tace "Ka ce yaushe kake son ta tare?" ya ɗan saci kallon Mami sai kuma ya sauke kai, da ya tuna yaga Muhammad a kofar gidan sai yaji hankalin shi ya tashi yace "Mami yau" Mami ta sake baki tana kallon Sadeeq da shock tace "ban gane yau ba?" Sultan and Jiddah couldn't help but burst out laughing Mami ta musu wani kallo wanda hakan yasa sukayi shiru amma suna kunshe dariyar su Mami na kallon Sadeeq tace "Sadeeq, To 9pm fah yanzu, kuma haka kawai sai aje ace a baka mata, kaje godiyan da ango ke yi ne na al'ada?" sai yanzu shima yaji yayi sounding so dull yace "toh Mami ko gobe da safe" duk mamakin Sadeeq ya cika Mami tace "Toh zan fada musu" daga haka ya mike ko kallon Sultan dake masa magana be kula sa ba ya haura stairs. Muhammad dake zaune duk kallon sa suke cike da tausayi Nimrah tace "Toh Meyasa zasu aura mata wani?" Nawaal tace "Lallai, baki san abin da ciwo bane yanzu kila wani ɗan-uwan ta ne saboda tausayi yace zai aure ta" daga Ummu har Abbah duk sun zauna Lost of thoughts can Ummi tace "kai ma baka jin magana da ka hakura ace ku tafi tare da Uncle dinka atleast su san ba wai ki kayi ba" Muhammad yace "Shi mijin Maman nata ma ya tausaya min" Sai sannan Abbah ya kalle sa yace "i think zaka koma Netherlands kafin kayi healing " Muhammad yayi shiru dan shima yasan idan yayi nisa da gida abin zai zo masa da sauki than yana nan Nawaal tace "Wallahi ai Ummi da kin bari yayi amfani da back to sender din, In shaa Allah, Allah zai saka masa". Bayan Mami ta sanar da Ammi, Ammi ta sanar da su Anty Binta tace "bari nake da kaina na fadawa Hajiya kar sai gobe taji ranta ya ɓaci" daga haka ta wuce sashen Hajiya. Washe gari bayan Leena ta idar da Sallah Ammi ta zauna gefen ta tana kallon ta tace "Leena in shaa Allah, anjima za'a kai ki" Leena tace "Dan Allah ba yanzu ba Ammi " ta rike hannun Ammi cikin lallami, Ammi tace "ba yanda muka iya ne Leena, shi Sadeeq din ne da kansa ya bukata kuma kinga yanzu yafi mu karfi a kan ki" Leena ta fara kuka Ammi ta mike ta fita ta barta a wajan, Anty Binta tayi ta rarrashin Leena da bata baki har nasiha ta mata amma ina Leena gaba daya bata gane kan zancen ta kukan ta kawai take yi. Da yamma Sadeeq da few friends din sa suka shiga gidan su Leena gaisuwan angwaye, bayan sun gaishe da Ammi suka wuce part ɗin Hajiya, Hajiya tayi ta sa musu Albarka tayi wa Sadeeq nasiha mai ratsa jiki kuma ta gwada masa dole sai yayi hakuri da Leena saboda ita yarinya ce, kuma nasihan yayi tasiri akan sa, dan ya ratsa shi, wata cousin ɗin Daddy ne tace saura part ɗin Mummy ganin idanun su yasa Hajiya bata ce komai ba, suka ajiye gift ɗin da suka kawo mata suka wuce part ɗin Mummy, bayan sun shiga suka gaishe ta Mummy na zaune tana girgiza kafa cike da kasaita tace "toh waye angon a cikin ku?" Sadeeq da kansa ke kasa ya daga yana kallon ta hakan abinda tayi wa Leena few years back ke dawo masa yaji ya kagu su bar parlorn wani abokin sa yace "wannan ne" ya karasa maganar yana pointing Sadeeq tace "Oh Ayyah, toh sai dai kayi hakuri da yarinyar fa, kasan de cewa yarinya ce kamar yadda ake cewa a gidan nan komai tayi na rashin jin ba'a magana sai ace yarinya ce, toh dai shawara ta anan sai ka haɗa da hakuri, kar kuma ka ce zaka kashe kan ka wajan kashe kudin a hidimar tarewan nan dan basu da godiya dan tun da tazo gidan nan a matsayin agola baka gani ba duk hakuri muke amma ko shi Daddyn na su basu gode masa" duk kallon ta suke da mamaki Sadeeq ya mike yace"Sai anjima" ko friends dinsa be jira ba ya fita suma duk suka mata sallama ta bi su da harara. Bayan Zahra ta shigo ta gaishe da su Anty Mairamah Ammi dake kallon ta tace "ki shiga tana dakin na ne" Zahra ta shiga ta karasa har inda Leena ke zaune ta hada kai da gwiwa tana sheshsheka Zahra tace "Haba ke kuwa Leena, sai kace baki san wanda aka aura Miki shi ba" Leena ta share hawayen ta, ta ɗago tana kallon wani direction Zahra tace "ke ma kin san Sadeeq be yi kama da wanda zai cutar da ke ba, wallahi dama hakura kikayi da kukan nan ki godewa Allah da yasa hakan ya faru, dan duk nan ba wanda zai ce yasan halin Muhammad ɗin 100% so Kinga bamu san bad side ɗin sa ba kuma dama ba'a zuwa neman aure da bad side, shi kuma wanda kika aura an san shi for more than years" Leena ko kallon Zahra ta ki yi. Hajiya da ta gama tsara tafiyar tana kallon Ammi tace "ina ga yana da kyau ace Khadija zata bi mu kar ta kullace mu tace ba'a sata a lamarin ba" Ammi bata so ba amma tunda Hajiya da kanta ne tayi magana yasa ta yi shiru, saboda kai Leena da za'a yasa su Anty Binta ba su mayar da kayan lefen a ranan ba. Bayan sallahn Magrib motoci ne jere a kofar gida Daddy, Jidda da su Anty Binta suka shirya Leena turare kuma sai kace da shi aka mata wanka Jiddah na kallon Leena tace "Leena wanan kukan kuma fah? Dan Allah ki daina nuna tsoron Ya Sadeeq har haka, nasha faɗa Miki Ya Sadeeq yana son ki amma kin ki yarda" Anty Binta ji take kamar ta ɗauke Leena da mari saboda takaici. Ammi barin gidan tayi dan ba zata iya ganin take up ɗin her very own daughter ba, Zahra tayi mata whisper a kunne "Please Leena ki daina wannan kukan, Jiddah ba zata ji dadi ba" Leena ko kula ta bata yi ba. Hajiya da ta koma sashen Mummy ta tsaya musu a kai sai ga Mummy da yaran ta suma sun fito duk sun yi kyau ma shaa Allah, Anty Binta da Mairamah sai hararan kasan ido suke mu su, anan parlorn Ammi Leena dake zaune cikin lafayan da aka rufe mata har fuska ta karasa ciki, Mummy ta fara magana "Leena zaman aure zaman hakuri ne, yi nayi bari na bari, duk muma da hakan aka fara" ta kama hannun Leena dake kara sautin kukan nata Jiddah nata kallon wulakancin rike Amarya da Ummu tayi, mota daya aka sa amarya da Mummy da Hajiya gaban motar kuma Zahra ne. Duk sai da sauran motocin suka tashi kafin na amarya ma ya tashi, ya SubhanAllah a daidai kofar gidan motocin sukayi parking, amma motar amarya har cikin compound ya shiga, dukkan su sai bin compound ɗin suke da kallo da mamaki sabar tsaruwan gidan basu tashi ruɗewa ba sai da suka shiga cikin parlorn wanda sai ka rantse wannan parlorn a kasar waje yake, Hassadan Mummy da yaranta ƙarara ya bayyana a kan fuskokin su, dan nan take annurin fuskar su ta ɗauke, Hajiya tace "wannan gida sai kace a Saudiya take" kowa nata fadin albarkacin bakin sa, Anty Binta da Jiddah suka kama hannun Leena suka kaita cikin bedroom ɗin da suke tunanin nata ne, bayan sun shiga Jiddah tayi ta aikin rarrashin Leena Anty Binta ta fara masifa tace "Shegiya sai kace wanda aka kawo ki gidan yankan kai" Jiddah tace "Easy Madam, ya zaki wani sa matar yayana a gaba ne?" ta rungume Leena dake zaune tana kallon Binta tace "ba zaki gane bane, tun asali ita da shi ba shiri suke ba kuma tsoron sa kamar take yi amma kuma haka nature ɗinsa yake dan yana mugun son ta" Zahra ta shigo dakin tana ma Leena magana a kunne, Anty Mairamah tana son shiga ciki amma bata son ta ba Mummy da ranar chance ɗin yin wani aika aika dan ido sosai ta sa musu Mummy wai zata buɗe dakin Sadeeq Anty Mairamah tace "A'a nan dakin mijin ta ne" Mummy tace "toh hanamu gani zakiyi?" ta murɗa handle din taji a kulle sannan ta dawo cikin parlorn ta zauna Anty Mairamah taji daɗin kulle wa da aka yi, Mummy bata taɓa jin tsanar da tayi wa Leena da Ammin ta ba irin na yau kawai controlling kanta take. Bayan Jiddah ta cire Wayan a kunnan ta tana kallon Binta tace "Toh kinji ango ko, wai mu fito a mayar da mu" anty Binta na dariya tace "mu tafi tun kafin ya shigo ya tsaya mana aka yana koran mu" Zahra tayi hugging Leena tayi mata magana a hankali duk suka mike Leena ta yaye mayafin kanta tana kallon jIdda tace "har dake ne anty Jiddah? Ai tare zamu kwana ba?" tace "Eh bari na raka su sai na dawo" bayan duk sun fita Mummy sai cika take tana bosewa, Niswa har da hawayen ta, Jiddah taje inda Sadeeq da Sultan sai few friends dinsa suke tsaye tana gaishe su sannan tace "Ya Sadeeq minti biyu mana" Sultan yace "Wallahi ki sashi a hanya Jiddah" ko kallon su be yi ba da kamar ba zai je ba sai kuma ya bi ta bayan sun ɗanyi nisa da su yana kallon ta alamar ita ya ke jiran ta fadi abinda zata ce tace"Ya Sadeeq kaga dai Leena yarinya ce, wannan halin ko'in kula in dan Allah ka canza, ka ga yanzu duk tunanin ta Wallahi baka son ta ne saboda yadda kake yi mata, please dont be harsh on her" yace "Kin gama min faɗan?" tayi ƴar dariya tace "wai ina gwada maka halinmu mu mata ne, kasan muna son caring" daga haka ya juya abinsa, jIddah ganin su Sultan sunyi hanyar gate ta bi bayan su da sauri dan kar a manta da ita. Sadeeq na shiga parlorn ya zauna nan kan sofa can kuma ya soso kanshi sai kuma ya mike, dakin da aka sa Leena nan ya wuce sai da ya tsaya for some minutes kafin ya iya ɗaurewa ya buɗe dakin ya shiga har sannan Leena na kuka jin an buɗe kofa ta daga kanta da sauri anan bakin kofa ta gansa ta mike tsaye da sauri tana kallon bayan sa hoping zata ga Jiddah at the same time tana share hawayen ta, tace "ina Anty jiddahn?" yace "Jiddah ai na aura da zaki ganta anan" nan da nan Leena ta fara wani sabon kukan yace "kin yi sallah ne?" Kai kawai ta girgiza masa daga haka ya juya ya fita, dakin da ke kusa da nata yasa key ya buɗe ya shiga sai bayan wajan 1 hour ya fito a dakin sa Ledan da ke kan center table ya ɗauka ya wuce ɗakin na ta ya buɗe da alama har tayi wanka ta canza kaya dan dogon hijab ne jikin ta ta takure a can edge din gado jin ya buɗe kofar, da sauri ta kulle idon ta ya karasa har cikin daki for the first time in her life taji yace "Leena!" yi tayi kamar bacci ta ke ya kuma cewa "Leena, wake up and grab something to eat, I know you didn't have dinner" Leena sabar mamakin sa bata san sanda ta mike ta zauna tana kallon sa ba sai kuma ta tuna ashe tayi pretending tana bacci ne da sauri ta sauke idon ta kasa ganin yadda yake kallon ta tace "I'm really not hungry" ya ajiye Ledan hannun sa akan stool ya juya yana kallon ta yace "Don't make me repeat myself, just come down and take the food" daga haka ya juya ya fita, itama mamakin yadda yayi magana take dama yana magana haka daga karshe ta mike ta sauka dama yunwa take ji, duba ledodin tayi na chips kawai ta ɗauka taci ta bar kazan a wajan. Washe gari da asuba bayan yayi alwala kafin ya tafi masallaci ya buɗe dakin ta da niyyar tashin ta sai yaga already tana toilet ma. tun da Leena ta idar da Sallah ta fara bacci, zuwa Sannan ta fara jin jikin ta Alhamdulillah. Kamar karfe 9 Sultan ya kira Sadeeq, Sadeeq da gama shirin sa kenan yana gaban dressing mirror ya daga kiran Sultan, ya ɗaga, Sultan yace "ina waje" daga haka ya katse kiran, bayan ya buɗe gate ya karasa inda Sultan yayi parking, mika masa hannun yayi bayan sun gaisa Sadeeq yace "ba zaka shigo bane?" Sultan yace "Wa ne ni, A'a abinci Mami ta aiko ni na kawo" daga haka ya sauka ya buɗe back seat ya fito da basket yana mika wa Sadeeq yace "toh Ango a gaishe min da Amarya" Sadeeq ko tanka sa be yi ba, ya wuce ciki Sultan na dariya ya shige motan sa. Bayan ya shiga ya ajiye basket ɗin a dinning room, dakin Leena ya wuce ya buɗe Leena da ke gaban dressing mirror tana shafa lotion iya towel ne ke jikin ta ganin ya buɗe kofar a ruɗe ta mike ta wuce bayan wardrobe da gudu, Sadeeq be san sanda murmushi ya kubuce masa ba, rabon da yayi wannan murmushi ba zai ce ba, ita kuma ta bata fuska tana kukunin taya zaina buɗe mata kofa ba tare da knocking ba, yace "Well, idan kin sa kayan ki fito muyi breakfast" bata amsa shi ba yana fita da gudu taje ta sawa kofar key tana jin haushin shigo mata da yayi, bayan ta gama ta zauna bakin gado tana tunani sake zuwa da yayi zai buɗe dakin yaji a kulle yayi knocking yasa a hankali ta karasa ta buɗe wani kallo yake mata hakan yasa ta sauke kanta kasa tace "ina kwana" be amsa mata ba sai gaba da yayi itama fitowan tayi daga dakin ta tsaya anan parlorn bayan ya zauna a dinning ya daga kai yana kallon ta yace "na zo na dauko ki ne?" ta fara tafiya a hankali, bayan ta zauna, gaba ɗaya gani tayi she's not comfortable da shi a wajan, shi da kansa yayi serving mu su ya tura mata plate ɗin ta gaban ta, da kyar take iya diba nan ma sai ta fake idon sa kafin zata kai bakin har ya gama bata ci yakai spoon hudu ba, bayan ya gama ya dawo kujeran dake gefen ta ya dauki abinci ya diba ya kai bakin ta ita kallon sa take da mamaki ya bata fuska yace "buɗe bakin ki?" ta fara girgiza masa kai tace "zan ci da kai na" kallon da ya mata ne yasa bata san sanda ta buɗe bakin ba, a haka har ya man feeding din ta.
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
_Ina matukar kaunar ku mutanen arziki, Nagode da ganin reactions din ku, comment dinku shike kara motivating ɗina, Allah bar kauna._
*I dedicate this to Layla and Rayyan's Fans*
32......
Nawaal da ke gefen sa sai basa labari take yi bata son barin sa shi kadai saboda kar ya samu chance ɗin tunani Abbah ne ya buɗe dakin Ummu na biye da shi a baya, Abbah handed him his ticket, passport, and travel papers, ensuring he had everything needed for the flight to Netherlands, godiya yayi wa Abba Nawaal tayi hugging ɗin sa tace "Ya MD, Have a nice journey, I wish I could take you to the airport, but I have lectures today" murmushi kawai ya mata Ummi na kallon sa cike da tausayin sa, gaba ɗaya gani take kamar ba Muhammad ɗin ta ba ne wannan. Mummy da ke zagaye parlorn ta, yau ko office ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 50