Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta murmushi ai dama tun farko mijin da take ta wa Leena fatan ta aura kenan, idan ko har haka ne bata damu da kyau ɗin sa ba yaje can ya aure ta talauci ya kashe su. Leena tayi shiru tana ta mamakin maganganun Rayyan dan ba kaɗan ba maganar ya dake ta, taya ma Malik zai ce yana son ta? Amma sai kuma ta samu kanta da rashin jin haushin sa, har Ammi tayi noticing ɗin ta tace "Leena tunanin me kike tun ɗazu? Da sauri Leena ta kalli Ammi sai kuma tace "Babu komai Ammi" Ammi tace "Okay, ashe ma kin fara ɓoye min abu ko?" Leena ta girgiza kai ta zauna ta fara narrating ma Ammi duk yadda suka yi da Rayyan, Ammi tace "Toh me a maganar nasa da har zaki ɗaga hankalin ki kina wasu tunani?" Leena tace "Toh Ammi ni nace masa ina son sa da har zai masa magana?" Ammi tayi murmushi tace "Toh yanzu wa zaki raina wa hankali kice ba son sa kike ba? Duk zuwan da yake kusan kullum da wayan da kuke yi shima duk cikin kiyayya ne?" Leena tayi shiru tana kallon wani wajan Ammi tace "Rayyan yayi min daidai, ko dan kina ganin Daddyn ku ya zuba miki ido bai ce komai bane? Tun yaushe mutumin nan yake shigo mishi gida amma ya kauda kan sa yanzu kuma kice ba son sa kike ba sai kuma a zuba muku ido sai yayi ta zuwa ke kuma kiyi ta fita kuna hira?" Leena ta sauke kan ta kasa tana wasa da fingers ɗinta daga haka Ammi ta mike ba tare da ta kara ce mata komai ba ta wuce dakin ta. Daran ranan haka Leena ta kasa bacci, maganganun Ammi da Rayyan ya dinga zuwa mata, ta rasa ya zata yi ta kauda tunanin nan amma ta kasa, kuma haushin Malik take ji da rashin kiran ta da baiyi ba through out ranan, ta jawo wayan ta ta kalli karfe 12pm ta ja tsuka ta rufe kanta da duvet dan ta samu bacci amma sai ta kasa, tayi ta juye juye daga karshe kawai ta sake jawo wayan ta ta rintse ido tayi dialing numbern sa yana ringing har ya katse bai ɗauka ba ta ja tsuka ta ajiye wayan, kawai taji wayan ta ya fara ringing da sauri ta ɗaga tana kallon sunan sa dake kan screen ɗin bata ɗaga ba har ya yanke, ya sake kira ta ɗauka takai kunne yayi sallama ta amsa masa daga haka tayi shiru, shima shirun yayi a hankali yace "Leena" tace "Shine ko kira babu?" Yace "I'm sorry, just that.." ta katse sa "Sorry for what? Don't tell me aiki kake or something else" yayi shiru ita ma shirun tayi can ya daure yace "I don't know ko Rayyan ya miki magana?" Tace "that's the reason ka daina kira na?" Yace "No, kawai dai ina fargaba ne" tace "Fargaba for what? Ka faɗa min, shi ne ba zaka iya faɗa min ba sai Yaya? So you don't trust the comfortability I have for you? Ba zaka iya approaching ɗina ba? Well duk lokacin da ka shirya then, Is left for you" daga haka ta katse kiran tayi shiru tana tunanin abubuwan da ta faɗa masa sai taji she really sounds dull ta taɓe baki daga haka bacci ya ɗauke ta. A bangaren Malik kuwa mamaki ma hana sa bacci yayi daga karshe ya shiga rubuta mata long message ya tura mata. Washe gari Ammi ta gama shirin ta cikin laffaya ga Nawaf ma da ta gama shirya sa tana zaune daga parlorn tace "Yanzu Leena tun ɗazu shine kika kasa shiryawa? Ba fa ke kika shirya Nawaf ba balle kice min kin tsaya shirya sa ne" tace Ammi gani fitowa fah" ba'a ɗau lokaci ba sai ga Leena ta fito tana sanye da Atamfa da Veil, Ammi tayi hanyar kofa da Nawaf a hannun ta, Nawaf ya juya yana kallon Leena yace "Amma come with us" ta tsaya ta rufe ko ina sannan ta bi su a baya da sauri, suna shiga compound ɗin su Mami suka ga Sadeeq na tsaye waya kare a kunnen sa, kallo ɗaya Leena ta masa ta ɗauke ka, ya sauke waya a kunnen sa  ya karasa inda suke ya ɗan duka yace "Ina wuni, Ammi" Ammi ta tsaya su gaisa, a takaice Leena tace masa "Ina wuni" daga haka ta wuce ciki ta bar su Ammi da suka tsaya gaisawa, ganin kallon yaron yake yasa Ammi tace "Nawaf je gun Daddyn ka ko?" daga haka Ammi ta bi bayan Leena, daga yaron yayi ya ɗaura sa kan bayan motar sa yana kallon sa cike da so da kauna yace "Ka Sanni?" Nawaf yana ta babbaka masa dariya kamar ya san sa, kissing ɗin sa yayi shima yana masa dariyar. Mami tace "yau kuma ina Baba na?" Ammi tace "yana wajan Baban sa a waje" Leena sai kallon jaririn Jiddah take. Har suka fito Sadeeq na rike da Nawaf suna ta shirmen su, Mami ta kalle sa tace "Toh zasu tafi, Malam" Ammi tace "A'a bar su idan sun gama hirar ai sai ya kawo sa" da sauri Sadeeq yace "Toh Shikenan Ammi" Leena dake baya ita da Jiddah a hankali yace "Leena" ta tsaya tana kallon sa yace "Thank you" tace "For?" sai kuma yayi diverting maganan yace "ya maganan school ɗin ki?" tace "Ban fara ba tukun, Maybe nayi Jamb this year" yace "Success, but please kar ki canza mind" kai kawai ta gyaɗa masa daga haka ta fita ba tare da ta sake kallon su ba, Nawaf yace "Amma bye". *AGOLA (Behind the palace walls)* 🫧 Wattpad @Jiddatulkhayr Instagram @Jiddatulkhayr writes Young talented writers association (YOTA) Chapter 59 Sa'adutu, Murjanatu, Aisha bint Sa'id, Daddy's princess, Noor and Co. I dedicate this page to you guys. Kwana biyun da suka wuce Ammi ta sa Leena a gaba, gashi gaba ɗaya tunanin ta ya tsaya cak, ta rasa exactly me zata yi, ga Malik da ya sata gaba, she thought haɗuwan ta da Sadeeq zai sa ya mata maganar komawan ta gidan sa but bata ga alamar hakan ba, ga kashin zuga da Ammi ta saka mata akan idan bata tsaida ɗaya ba zata sa Daddy ya mata magana, dan haka ta dage da addu'a kawai. Ta fito tana sanye da Jilbab, hannun ta ɗaya riƙe da hand bag ɗayan kuma tana rike da Nawaf, suna tafiya zuwa parking space, Nawaf ya cire hannun sa a nata bata kula sa ba ta cigaba ta tafiya, gate ɗin aka buɗe ta ɗan daga kanta ganin wanene, ga mamakin ta ta kalli Niswa ne, ta ɗauke kai ba tare da ta sake kallon wajan ba, ta buɗe kofar motar zata shiga kawai ta tsinci muryar Niswa "Hey! Leena" Leena ta daka ta da shiga motar ta juya sai kuma taga Niswan na mata murmushi kuma tana tun karo ta, hakan yasa itama ta sake fuska tace "Sannu, Anty Niswa" tana murmushi tace "Kina nan Lafiya, ya Babyn ki?" Ware ido tayi ganin Nawaf tace "Ohh, wow, has my little baby grown this much" ta ajiye jakkan ta a bayan motar Leena ta duka ta ɗauke shi tana kallon sa tayi kissing ɗin sa, ya fara mata murmushi ta sauke sa tana kallon Leena tace "Is like fita zaku yi ko?" Leena tace "Eh" tace "Toh sai kun dawo" daga haka ta wuce zuwa dakin su. Da sauri Umma ta dakar da Abbah tana kallon sa cike da mamaki tace "Inaa! Ai ba zai taɓa yuwa ba, gwara ma ya canza ra'ayin sa akan yarinyar nan" Abbah da mamaki yake kallon ta, ta mike daga kan tabarman da take tace "wallahi ba zan taɓa lamuntan Malik ya auri wannan yarinyar ba, ba zan taɓa yarda ba, toh shi me zai yi da bazawara? Ko yanzu sai na fito masa da mata wallahi, budurwa ma kuwa" Abbah ma ya mike yace "Toh ki sani tunda yace yana son ta shikenan, sannan da kike maganar bazawara ina son ki san cewa fiyayyan halitta da bazawara ya fara, dan haka baki isa haramta masa ita ba" daga haka ya wuce ya bar gidan dan yanzu masifar Umman ya fara gajiya da shi. Mummy ta zuba wa Niswa ido ganin yadda ta rame kamar ba ita ba tace "Niswa kina cin abincin kuwa?" Niswa tayi murmushi tace "Eh, Mummy" Mummy tace "Har yanzu zaman naku ba daɗi ne?" ta girgiza kai tace "Ni fah bani da matsala da shi, kawai dai baya son nace zan fita, matsala ta yanzu kuma da gidan su ne, amma shi kam bayi da matsala" Mummy tayi shiru tana kallon 'yar na ta yadda ta koma ba wannan tsaurin ta koma wani shiru shiru da ita. Da yamma Niswa ta shiga sashin Hajiya, Hajiya ta sake baki tana kallon Niswa da mamaki, Niswa ta gashe da Hajiya, Hajiya ta amsa tana kallon yadda gaba ɗaya ta bar Niswan da ta sani a baya, ta kara mata nasiha daga haka ta mata sallama.  Leena na ba Ammi labari gani tayi Ammin na sha mata kamshi saboda maganar nan, murmushi kawai tayi, ta yi kamar bata ma fahimci me Ammin ke nufi ba, sallaman Niswa suka jiyo, Ammi ta amsa mata bayan ta shiga ta gaishe da Ammi, Ammi ta amsa mata, tace "Ashe har Babyn ya girma, nikam girman sa ya ban mamaki" Ammi tayi dariya tace "kila dan baki ganin sa ne" Leena ta lura tun shigowan ta take kallon ta sai dai bata ɗaga ido da niyyar kallon ta ba sai taga kallon nata take a hankali tace "Leena kin kara kyau, kuma kinyi kiɓa, Ma Shaa Allah" Leena tace "Kai Anty Niswa" murmushi kawai ta yi, Ammi nata mamakin ta dan a da kam ko kallo Ammin bata ishe ta ba balle gaisuwa, ta mike tana kallon Ammi tace "Zan tafi, Ammi" Ammi ta mike tace "Ki tsaya ina zuwa" daga haka ta shige dakin ta bata daɗe ba sai gashi ta fito rike da laida, tace "Ga shi kin zo bani da komai sai turare ne" tana murmushi tama Ammi godiya daga haka ta fita Ammi ta kalli Leena tace "Ki raka ta ko da gate mana" Leena tace "Kamar site ɗin Daddy zata fa". Daddy ba karamin jin dadin sauyin Niswa ba yaji sai dai yaji wani iri ganin yadda ta lalace. Mummy ta fito daga backyard zata ɗaki da sauri Harisu yace "Hajiya" Mummy ta bi compound ɗin da kallo ganin ba kowa yasa ta tsaya har ya karasa, ya duka yana gaishe ta, ta dakatar da shi tace "Bani amsar sako na kawai" yace "Okay.. Dama na bibiye sa ne, har unguwar su naje nasan gidan su, sannan yaron gaskiya basu da kuɗi dan ɗan karamin gida ne gare su, ga kuma shi ke ɗauke da nawin iyayen sa, bayan haka kuma 'yan unguwar sai zagin sa suke ganin yadda suke fama da bakin talauci amma sai yana saka kaya mai kyau akan ya ci ma cikin sa wanda wasu suke ganin kamar yaudarar 'yan mata yake yi" tace "kana da tabbacin abinda kake faɗa?" Yace "kwarai ma kuwa Hajiya, har gidan su fa nace miki naje, kuna naga shigan sa gidan, wallahi ba ma zaki yarda a gidan yake ba Shiyasa mutanen unguwar suka ce yaudara gare sa" Mummy tayi wani murmushi tace "Nagode da wannan sakon" ganin zata juya ta shiga yayi saurin tsayar da ita bayan ta tsaya yace "Hajiya kuma duk sanda zai zo gidan nan ma machine yake zuwa" tace "Naji, ka saurari sako na" daga haka ta shige ciki, hamdalah ta fara yi, ita at this point zata iya hakura da ta cusawa Layla bakin ciki gwara kawai ya auri Leena da yaudaran. Malik ya shiga cikin gidan na su da sallama a bakin sa, Umma kaɗai ya gani zaune a ɗan sakar gidan na su, da ɗan karamin radiyo tana saurara, Kallon Malik da tayi yasa ta kashe radiyon, Malik ya karasa har inda take zaune ya zauna yana gaishe ta, daga masa hannu tayi ta mike tsaye tace "wato Malik zaka iya zaɓan abun da bana so kace lalle shi kake so?" Malik ya fahimci Abbah kenan ya mata maganan, haka nan yasa ya saukar da kansa Umma ta cigaba "ina maka magana zaka min shiru? Har nice zaka bijirewa magana ta? Tun da na nuna maka bana son yarinyar nan ka nuna kai kuma nan kake son ta, Uban me take da shi da sauran matan ba su da shi" yadda take magana da karfi yasa a hankali yace "kiyi hakuri Umma" tace "idan har mata kake so zan shiga gari na nemo maka wacca ta fita da komai" ya ɗaga tsaya yana kallon ta, toh ita ina ta santa da har zata nemo masa wacca ta fita ɗin? A hankali yace "Umma dan Allah akwai abin da ta miki ne? Naga tun kafin kisan ita wacece kika tsane ta, balle kiji nayi maganar ta sai nan da nan ran ki ya ɓaci" tace "Okay, dan ban isa da kai bane yasa kake tuhuma na?" Daga haka ta wuce ciki da sauri ya bita dan duk duniya baya jin akwai wani abu da zai iya ɓata wa Mahaifiyar sa rai ya hakura. Da Daddare Mummy na zaune gefen Daddy shi kuma yana dinner, duk da ba wani sake mata yake ba amma hakan baya sa ya tauye mata hakkin ta, bayan ya gama cin abincin a hankali tace "Yallabai ina da wata magana" ya zuba mata ido alamar yana jin ta" a hankali tace "dama wata magana ce naga yana yawa a unguwar nan, kuma shine nace ya kamata na sanar da kai duk da ban san ya zaka ɗauki maganar ba amma kuma nima ba wai na san da hakan ba ne sai kwanan nan da magana ya fara yawo shine na sa ido dan gasgatar wa, kuma naga hakan ne" yace "Bar wannan baya nan, ina son kallon news, just go straight to the point" tace "Okay, regarding wanda ke zuwa wajan Leena ne, kaga yadda ake magana kuwa? fin shekara kenan, idan ma auren ta zai yi gwara kawai ya fito da wannan zuwan na sa, kasan yarinya karama ace da zauranci bai yi ba" Daddy ko uffan bai ce mata ba ta dinga kallon sa ganin yadda ko amsa ta bai yi ba, but deep down him yasan gaskiya take faɗa, atleast ya basa chance tunda shima witness ne almost a year yake ganin sa. Leena har tayi shirin kwanciya taji karar message duk tunanin ta Muhammad ne daya sako ta gaba kwana biyun nan, hakan yasa bata kula wayar bama har sai da zata kwanta ta jawo wayan dan ganin content ɗin sai kuma taga Malik ne, har sannan baya iya kiran ta sai dai ya tura mata da message bayan ta gama karanta message ɗin nasa ta ja tsaki sai kuma ta ɗauki wayan ta shiga typing masa idan har ba zai iya kiranta ko kuma fuskantar ta ba toh kada ya sake neman ta, bayan ta tura kamar da minti 2 sai ga kiran sa, ta dinga hararan wayar kamar wanda wayan ne ya mata laifi. Tun da gari ya waye Mummy ta shirya da wuri ko breakfast bata jira ba balle ta haɗawa Daddy breakfast duk da kwanan ɗakin ta ne, ta fita har sannan 'yan gidan basu gama tashi ba dan babu kowa compound ɗin, bayan ta fita a daidai gidan kawar ta Hajiya Fatima tayi parking, Hajiya Fatima da ta fito daga dakin ta zata kitchen ta tsaya kallon Mummy da mamaki sai kuma ta kalli agogo tace "Lafiya?" Mummy na murmushi ta karasa cikin parlorn tace "wallahi kalau, magana fa zamu yi dan ba ta waya bace yasa na zo kafin lokacin office yayi" Mama ta dawo tsakin parlorn tana kwalawa Ayrah kira, bata ɗau lokaci ba ta fito, Mama tace "Je ki karasa breakfast ɗin kar kiyi latti tunda lectures ɗin safe gare ki" ta amsa da toh ta gaishe da Mummy sannan ta wuce kitchen, Mummy ta dawo kusa da Mama tace "Kina ji, wani ne yake zuwa wajan Leena yau kusan shekara gudu, idan kin gansa zaki ɗauka balarabe ne ko kuma ɗan gidan shugaban kasa tsabar yadda yake ji da kansa, Ni kuma nasa a min bincike akan sa ashe ɗan gidan talakawa ne, da naso nace Malamin ya raba ta da shi amma ganin ance min ga yanayin sa shine nace kar ayi komai a kansa sai ma son da za'a kara musu suji suna son juna kamar za su mutu idan ba ɗaya" Mama ta dinga kallon ta da mamaki tace "Amma ke ya akayi kika san ɗan talakawa ne?" tayi dariya tace "Harisu na sa yayi min bincike, ashe wai haka yake yaudarar 'yan mata saboda kyan sa while gidan su ko karen gidan mu ba zamu sa a wannan gidan ba, Ni har kama da Leenan ma naga yake yi" Mama tayi murmushi tace "Toh ba damuwa, zan sanar da shi kawai ayi auren na su ko? Amma zaki sha kudi" tana murmushi tace "kudi ba matsala bace" sai kuma ta ɗaura "Da fa Hajiya Amina cewa tayi kawai na sa Rayyan ya aure ta har na masa magana sai kuwa naga wannan mutumin" Mama ta dinga kallon ta ba ko kiftawa tsabar mamaki, da har ranta bata ji zata kai sunan Leena gun Malami ba amma yanzu lamarin Mummy ya fara bata tsoro, wato 'yar ta ko haihuwa bata yi ba za'a fara Maganan mata kishiya, ganin Mama ta faɗa duniyar tunani yasa da sauri Mummy realizing me ta gama faɗa har sai da shock ya ɗan bayyana a fuskar ta sai kuma tayi murmushi tace "kinsan da fir nace ban yarda ba amma sai ta nuna min cewa wata uku kawai za suyi ya sake ta shikenan" Mama na mata wani kallo tace "a tunanin ki kin isa ki sa ya sake ta ne a wata uku? Kuma kinsan dama yana son ta, a kaddara ace ciki ya shiga ki bar ganin biyayyar da Rayyan yake miki wallahi saf zai rufe ido ya gwada miki cewa ba zai rabu da ita ba" Mummy tayi yake tace "Allah ma ya kiyaye na hada jini da ita" sai kuma ta mike tana kallon agogo tace "Kinga barin wuce office kar na makkara". Daddy yayi shiru yana sauraron Rayyan, sai kuma ya gyara zama yace "amma da kuka yi magana mai ya ce maka?" yace "ya gwada min yana son ta da aure ne kuma ita ma da na mata magana tana son sa Shiyasa naga zaman nata haka bai kamata ba" Daddy yace "But planing ɗina fa ta koma makaranta ne Rayyan, ace duk yara na mata sun yi karatu banda ita?" Rayyan yace "Daddy aure baya hana karatu, kawai taje tayi a gidan sa idan yaso mu sai mu cigaba da ɗaukan nawin ta" Daddy yace "Okay, zan yi magana da ita Sirbajo sannan kuma kace wa yaron ina son ganin sa" ya gyaɗa kai yace "Da na so ta koma gidan mijin ta ne wallahi, amma Sadeeq ɗin nan ɗan rai nin hankali ne, dama tun farko ba magana muke ba sai da ɗan uwan sa, Daddy can you imagine mun haɗu a masallaci ina da niyyar masa magana ya ɗauke kai ya bar masallacin Shiyasa kawai na yanke shawarar tayi aure karma ta ɗauka yana da niyyar dawo da ita" Daddy yace "kayi abun da ya dace Rayyan, haka nake son ganin kana tsayawa a lamarin kannan ka, amma da na ɗauka ko kai ne zaka aure ta Shiyasa ban yi ma magana ba" Rayyan yayi murmushi yace "Daddy a barta da wannan sannan mu bita da addu'a tunda naga tana son sa" Daddy yace "it's true". Layla was totally shock da abin da Mama ta gama gaya mata tace "Mama wai matar nan ita a rayuwar ta bata so taga wani yana walwala ne? Ni yanzu uban me na tare mata take son ya auri Leena?" Har muryan ta ya fara breaking, Mama tace "Yanzu kam ai shikenan, sannan karma kisa abun a ranki balle ya dame ki" ta gyaɗa kai tace "Ba zan sa ba, in shaa Allah" sai kuma tace "Mama kin san Allah wannan Malik ɗin karya ake mata da aka ce bayi da kuɗi, ko kuma ba dai gidan su aka je ba, dan wallahi baki gan sa bane, ai da nake zuwa gidan ina ganin yana zuwa wajan Leena" Mama tace "Toh ai a gidan kike ganin sa, hakan ba shine zai nuna ainahin sa ba" Layla tayi wani murmushi tace "Toh Mama ki san abinda baki sani ba, Malik da kike gani ina following ɗin sa, dake yana following Leena so ya shigo min a suggestion Ni kuma na fara following ɗin sa a IG, Mama gayan nan bai yi kama da ɗan talakawa ba, beside kuma har kama suke da Leena" Mama tace "itama haka tace wai suna kama" Layla tace "Mama kiyi shiru da bakin ki, Ni fah da ban san Ammi ba sai nace ko Leena ba 'yar ta bace duba da yadda basu kama duk da Ammin ma kyakkyawa ce" Mama tace "kamar ya?" Layla tace "Ni fah ina zargin wannan kamar ɗan lekan asiri ne ko kuma nace da wata manufa, Shiyasa nace ki cire hannun ki a lamarin nan kuma dan Allah ko da wasa kar ki sanar mata" Mama tayi shiru tana mamakin maganganun Layla a haka dai suka rabu. Jiddatulkhayr 08110615256*AGOLA (Behind the palace walls)* 🫧 Wattpad @Jiddatulkhayr Instagram @Jiddatulkhayr writes Young talented writers association (YOTA) Chapter 60 Tunda Layla ta zo she has been dragging her into conversations, and it seems like she wants to know something about Malik, Leena tayi murmushi jin me ta gama faɗa, Layla tace "I'm telling you, this isn't something to joke about, wallahi kawai just marry him, ban san ya yaran ku zasu zama ba, kila ace daga Saudi suke ma" Leena, who was tired of listening to her talk tace "Yanzu kam ai shikenan tunda har Abbahn sa ya samu Daddy" daga haka ta cigaba da sawa Nawaf kaya, dan ita gani tayi everything Layla does seems driven by jealousy, and ita kam ta daɗe da cire Rayyan a ran ta, tun kafin auren ta da Sadeeq, tana gama sa masa kaya tace "Je ka wajan Ammi" ya juya ya fita, ta kalli Layla da murmushi a fuskar ta tace "Bari na ɗan kwanta kai na na min ciwo" daga haka ta haura gado duk da ba wai bacci take ji ba kawai tana avoiding magana da Laylar ne, daga haka Layla ta mike ta bi bayan Nawaf tana kiran sa. Tun bayan tsayar da maganan bikin ta da Malik jikin ta ya gama tsanyi, ta rasa meke damun ta, Rayuwar ta da Sadeeq shi ke sake zuwa mata, haka nan sai tayi ta kuka, but...She doesn't know what the future holds for her, Amma tana fatan Allah ya wuce lamarin ta, kuma she hopes that Malik will be a source of blessings in her life. Yau wajan sati guda kenan Umma bata kula Malik, duk yadda yaso ya bata hakuri bata basa wannan door ɗin, abin na damun sa but ya san ba zai iya rabuwa da Leena ba, saboda He is so much at peace with her. Kamar kullum yau ma, bayan ya gama shirin fita aiki ya karasa har parlorn, ita da Abbah su na zaune suna breakfast, wanda har Abbahn ma ta canza masa sai dai shi be gwaɗa mata ya fahimci hakan ba, Malik ya karasa ya zauna kan wani kujera dake parlorn yace "Umma, Abbah zan fita aiki" Abbah kaɗai yace "Toh Allah bada sa'a" ya juya yana kallon Umma yace "Umma zan fita aiki" sai sannan tace "Naji ai" sai duk jikin sa yayi sanyi yace "Dan Allah Umma kiyi hakuri" tace "kamin wani laifin ne?" Kai kawai ya girgiza mata, Abbah yace "tashi ka je Allah maka Albarka" ya amsa da Amin sannan ya kama hanyar fita amma gaba

Chapter 38 of 50