zaki koma gida bane?" tace "Mun yi waya yace yana hanya yanzu zai karaso mu tafi" ta gyada kai tace "ki gaishe min da shi" tace "Toh" ta mayar da kanta kan abinda take a waya Mummy ta raka ta, bayan ta dawo ta samu Layla na kwance akan 3 seater, Mummy ko kallo bata ishe ta ba ta wuce ciki haka nan taji Layla ta fice mata arai, Layla ko daga kanta bata yi ba balle tasan da Mummy, Niswa ta fito ɗaukan system ɗin ta dake chargy a parlorn, ta harare Layla da bata ma san da fitowan ta ba ma. Rayyan yayi parking a kofar gidan sannan yace "Sai da safe Ammi" Ammi ta masa godiya ta wuce ciki, duk yadda Rayyan yaso ya samu Layla a waya amma gaba ɗaya ya kasa samun ta, ya sauka a motar yana shiga compound ɗin muryan Mummy da kawarta sai Niswa ne yaji ya fara echoing in his mind, dakyar ya karasa har kofar dakin su luckily ita kadai ce a parlorn, yayi karfin halin cewa "Ki fito mu tafi" Jin muryan sa Layla ta mike ta dau jakkan ta dama ta gama shiri shi take jira ko sallama bata ma su Mummy ba ta fita, ganin ba zai shiga ba hakan ya mata daɗi ba kadan ba tace "Dear mu tafi ko?" ya fara tafiya tana biye da shi a baya. Zuwa yanzu Sadeeq ya ji dama dama, Mami gani take abun kamar a mafarki ne, Jiddah tana girgiza kafa tace "Ai wallahi koma waye ne ya masa wannan bakin abun wallahi sai ya gani daga kansa har kan 'ya'ya da jikoki" Mami tace "Amma na hana ki ko Jiddah" Jiddah ta tashi tace "Mami sai dai fah kiyi hakuri dan wallahi har na gama biyan kudin da za'a min aiki" daga haka ta wuce ciki. Hajiya tace "inma zaki cire wannan tsohon mijin naki a rai gwara ki gaggauta cire sa kafin ki ja ma kan ki hawan jini, naga kaf dangin sa kin gansu anan ne?" Anty Binta ta gyara zama tace "Ah toh, gwara ma ki faɗa mata Hajiya, kila taji maganar ki dan naga kamar Ni ba fahimta na take ba". Niswa ta taɓe baki tace "Ai ni tun farko sai da na gwada bana son ta kwatakwata amma inaa gani kike ina kishi da Yaya na" Mummy ta sauke ajiyan zuciya tace "ban taba sanin haka halin ta yake ba, har Ni zata buda baki tace min haka?" Niswa tace "wai kuma a hakan dan ita kuke wahala ba, ai gashi tun kafin aje ko ina ta fara gwada miki halin ta, kuma Uwar ta bata yi magana ba sai ma dariya da tayi tana goyon bayan 'yarta" Mummy tana girgiza kafa dan bil hakki Layla ta bata mata rai tace "toh yaushe ta tafi kuma?" Niswa tace "Yaushe dama zata mana sallama". Bayan sallah isha'i Sultan ya shigo gidan dakin da Sadeeq yake ya karasa ya samu Mami da Jiddah ma suna dakin, yana kallon sa ya masa ya jiki Sadeeq ya amsa masa kawai, Mami ta mike ta fita ta musu alama da su biyo ta duk suka mike suka masa Allah karasa sauki, Anan parlorn suka haɗu da Mami suka zauna suna jinta Mami tace "Ni yanzu haka zamu zuba ido ba zamu duba yarinyar nan ba?" Sultan yace "Gaskiya ya kamata, da da hali ma ace harda Sadeeq din Mami" Jidda ta girgiza kai tace "Ina ga ba lallai sai da shi ba, zamu iya zuwa mu ɗin, dan yau fah wajan 3days kenan" Mami tace "Toh gobe sai ku shigo sai mu tafi asibitin" suka amsa da Amin Mami tayi murmushin takaici tace "haɗa ido da su ma kaɗai aiki ne". Duk suna zaune a ɗan karamin compound ɗin su suna shan iska suna hira gwanin ban sha'awa, Malik ya kalli mahaifin na sa jin abinda yace yayi murmushi yace "لا بأس يا أبي (it's nothing Abbah)" Abbah ya masa wani kallo cike da kaunar ɗan nasa yace "ستخبرني بالحقيقة بنفسك (You will tell me the truth yourself)" Malik yayi wani murmushi sai dai kuma bai ce komai ba Abbah yace "أين الفتاة التي حدثتني عنها؟ (Ina yarinyar da ka min maganan ta?)" Umma duk da ba wani larabci take ji sosai ba amma ta fahimci magana kamar na Leena Abbahn ya sako wa 'ɗan sa ta haɗe rai kamar bata san me dariya ba, Malik ya ɗan kalle ta sai kuma ya mayar da kallon sa ga Abbahn sa yace "هي موجودة، لكنني لم أتمكن من رؤيتها بعد، فقط أنا قلق وأريد أن أعرف حالها. (Tana nan Abbah, but I haven’t been able to see her yet, kawai na damu na san halin da take ciki ne" Umma ta mike tace "Ai sai kuyi ta yi" daga haka ta shige ciki, Abbah ya bita da kallo, Malik yayi shiru, shi ya rasa dalilin da yasa da zaran ya dauko maganar Leena Umma ke bata rai. Tun bayan da suka dawo gida kaya kawai ta canza ta wuce kitchen, haka nan taji tana farin ciki, ko dan yau ya kula ta ne bata sani ba, ta wuce dakin Rayyan tayi knocking sannan ta buɗe tana kallon yadda ya kura wa waje daya ido tasan daga gani tunani yake yi, ya juyo yana kallon ta tace "Am nace ko pasta zan daura? Ko kuma wanne zan girka" ya mike zaune daga kwancen da yake yi yace "No need, I'm full" ta dinga kallon sa kamar zata yi kuka sai kuma yace "Okay, ina tunanin pasta ɗin ma is okay" ta juya ta fita bata dau wani lokaci sosai ba ta gama girkin ta ta zuba a warmer ta ajiye a dinning sannan ta wuce toilet tayi wanka ta sa sleepwear ta feshe jikinta da different varieties of perfume har zata fita kuma sai ta tuna kanta ba hula kuma ya faɗa mata ya tsana rashin sa hula da take yi da sauri ta juya ta koma dakin ta dauki hula ta saka, dakin sa ta wuce, tayi knocking sannan ta shiga still yadda ta barsa dazu haka nan yake tace "Amma babe kana lafiya?" ya juya yana kallon ta murmushi ta masa atleast yau ya sauko, tace "Abincin fah is ready" ya nuna mata wajan shi yace "Ki zo za muyi magana ne" da sauri Layla ta karasa tana murmushi, kallon ta yake yi sai kuma yace "I'm begging you Layla, kar ki boye min komai" ta gyada masa kai tace "Wlhi gaskiya zan fada maka, Menene?".
Jiddatul-khayr
08110615256
https://chat.whatsapp.com/K7dFXrl6zm1IG82QJyPjuV?mode=ac_c
Assalamu alaikum! jama’a! Kuna buƙatar sayen Data, Airtime, biya kudin wuta, ko siyan WAEC Scratch Card cikin sauki da arha?
To ku zo kuyi aiki da HADJIBS DATA SERVICES – inda muke ba ku sabis cikin sauki da amana.
💼 Muna sayar da:
✅ MTN, GLO, AIRTEL, 9MOBILE DATA
✅ Airtime na kowane network
✅ Biya na wutar lantarki (NEPA)
✅ WAEC Scratch Card
✅ Cable TV: DStv, GOtv, Startimes
👩💼 Zaka iya bude account naka kyauta a dandalinmu kuma ka fara sana’arka nan take, ka rika siyarwa da riba.
🤑 Ma’ana: kana siye da wholesale, kana saida da retail!
💻 Ga link ɗin rajista:
👉 https://hadjibsdata.com.ng/mobile/login/
📲 Muna da App a Play Store da App Store – saukar da shi yanzu!
📞 Tuntuɓi mu: 07017133099
📍 HADJIBS DATA SERVICES – Sabis na gaskiya cikin sauki!
Assalamu alaikum! jama’a! Kuna buƙatar sayen Data, Airtime, biya kudin wuta, ko siyan WAEC Scratch Card cikin sauki da arha?
To ku zo kuyi aiki da HADJIBS DATA SERVICES – inda muke ba ku sabis cikin sauki da amana.
💼 Muna sayar da:
✅ MTN, GLO, AIRTEL, 9MOBILE DATA
✅ Airtime na kowane network
✅ Biya na wutar lantarki (NEPA)
✅ WAEC Scratch Card
✅ Cable TV: DStv, GOtv, Startimes
👩💼 Zaka iya bude account naka kyauta a dandalinmu kuma ka fara sana’arka nan take, ka rika siyarwa da riba.
🤑 Ma’ana: kana siye da wholesale, kana saida da retail!
💻 Ga link ɗin rajista:
👉 https://hadjibsdata.com.ng/mobile/login/
📲 Muna da App a Play Store da App Store – saukar da shi yanzu!
📞 Tuntuɓi mu: 07017133099
📍 HADJIBS DATA SERVICES – Sabis na gaskiya cikin sauki!
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
Hauwa Jibrin Sulaiman
(Jiddatul-khayr)
Wattpad © Jiddatulkhayr
Young talent writers association
Chapter 46
____Yayi shiru yana kallon ta ta marairace masa tace "I'm all ears, please" yace "I don't want you to hide anything from me about what's going on, I know you know about it" ta gyara zama tana masa dirty look tace "Promise me that if I tell you the truth, you'll start loving me" gyada mata kai yayi har sannan tana kallon sa yace "I've made a promise" ta kwanta a jikin sa tana wasa da fingers ɗinta a hankali tace "Everything you heard is true, dan nasan kaji komai" shirun da taji yayi ne yasa ta daga kanta tana kallon sa yace "Layla ki faɗa min duk abin da ban sani ba" ta sauke idon ta kasa dan ita har cikin ranta taji haushin kashe wa Leena aure da suka yi dan ba ta so Rayyan yace zai koma mata a karo na biyu, tayi shiru tana tunani tajiyo muryan sa yace "Layla" ta sake kallon sa yace "Ina jinki" ita fah She didn't bother to reveal their secret, a hankali tace "duk planning ɗin Mummy ne da Mama, duk wani abu da ke faruwa if It's not normal toh definitely suna da hannu" Rayyan yayi shiru da bai cire rai da jin hakan ba, tunawa da Hajiya da ta basa magani yayi, lokaci guda ya tuna lokacin da ko laifin Layla ya daina gani, ya sauke ajiyan zuciya dan tunawa da alkawarin da yama Laylan, ya san zai iya canza ta tunda har tana son sa kuma zata na fada masa duk wani next move din su, ai it's enough hakan kuma, tausayin Leena yake ji da mijin ta har cikin ran sa dan tun day one yaga soyayyar Leena a idon sa, tace "Zauwji" ya kalle ta tace "Dan Allah ka fara so na" yace "ai ina son ki" ta girgiza masa kai tace "Wallahi baka yi" yace "ba wai ke bane bana so, kawai halayyar ki ne bana so, kuma idan na hanaki abu bakya bari" kallon sa take tace "Wallahi ina bari, kuma ai kai ya kamata ka canza Ni" yace "Meyasa kika zubar da ciki?" jin tambayar sa tayi har ƙwaƙwalwar kanta ta sauke kanta da sauri dan bata taɓa expecting zai fahimci hakan ba tunawa da shi likita ne sai kuma jikin ta yayi sanyi tace "ba yin kaina bane, Mummy ce tace zan tsufa da wuri, and I regret my action" Rayyan kallon ta yake ba kiftawa, gani yake kamar kawai mahaifiyar sa haifan sa tayi ba tare da tana son shi ba, yasan son da yake nunawa Leena ya sa aka tsane ta, ganin yanayin Layla yace "Muje kar abinci ya huce" ta sauka daga jikin sa tana jin hawaye na sauka kan kuncin ta, Rayyan ya jawo ta jikin sa yace "C'mon, kuka kuma?" Shi tun lokacin da yake mata wannan kallon ya fahimci hakan amma da ke baya son ta sai yaji abin bai dame sa ba, yana rike da ita suka wuce dinning. Washe gari tun kafin karfe 8am housegirl ɗin Mami da ita kanta Mamin sun gama hada breakfast da zasu kai ma Leena asibiti, harda su kai da ƙafan Sa da suka dafa, Mami ta wuce dakin ta dan yi wanka, bata dau lokaci ba ta fito tana mitan har sannan su Jiddah basu karaso ba, fita tayi a dakin ta wuce dakin Jiddah tana kallon kanwar late husband dinta ta shiga dakin ta zauna tace "Hajiya ko zaki shirya ne kafin yaran su karaso, dan Ni na gama shiryawa" ta mike akan darduman da take ta ninke tace "Toh shikenan barin shiga wanka yanzu" Mami ta fita a daki zata shiga dakin ta sai taji sallamar su Sultan ta koma cikin parlorn bayan sun gaishe ta suna tambayar jikin Sadeeq Mami tace "Ni wallahi gaba ɗaya abin mamaki yake bani, yanzu fah haka kamar ba shi ba ya warke tass, sai dai matsalar sa tunanin da yasa a gaba ne" Jiddah tace "ba dole ba, ai cuta kam an cuce sa wallahi" Sultan yace "amma kinyi magana da shi Mami?" Mami ta girgiza kai kawai, Sultan yace "ya kamata kuwa, saboda maganar da zai fada miki ma kaɗai zai iya healing ɗin sa" Mami tace "Haka ne" daga haka Sultan ya mike yace "barin duba sa" Jiddah ma ta mike ta bi bayan sa, Mami ta sauke ajiyan zuciya ta wuce dakin ta, bayan sun shiga Sadeeq take zaune kan dadduman yana karatun Alqur'ani ya sallame ya ajiye Qur'anin ya ju ya yana kallon su suka gaishe sa suna masa ya jiki a takaice yace "Alhamdulillah" Jiddah yace "amma idan ka warware zaka duba Leenan ko?" Sadeeq yayi murmushin takaici yace "A'a" Jiddah tace "A'a kuma?" kai kawai ya gyada mata ta kalli Sultan da sauri sai kuma ta sake mayar da kallon ta ga Sadeeq da har ya ninke darduman ya koma kan resting chair dake dakin sa, Sultan yace "amma ya kama ta kuwa, atleast ai ɗan ka ne, hakan bai kamata ba" Sadeeq yace "A tunanin ka zan iya sake hada ido da ita ne? When I think that there's no marriage between us now, it really hurts me a lot, wallahi ji nake kamar na ɓace kawai sabar raɗaɗi" Sultan yace "ban gane ba? Kamar ya ba aure tsakanin ku?" Sadeeq ya kalle sa yace "ko baka ji ance ta haihu bane?" yace "Toh hakura zaka yi da ita ko me kake nufi?" ya girgiza kan sa yace "i can still remember yadda na sake ta, tana kuka asking for help Amma ko a jiki na" yayi shiru for some seconds sannan ya cigaba "I don't know what the future holds, but I'm praying for the best" daga Jiddah har Sultan sai da suka ji tausayin sa na ratsa su, duk da cewa ba halin sa bane, Mami ne ta buɗe kofar dakin tace "Toh sai ku fito ko? Ku ake jira" duk suka mike jiki a sanyaye Mami na kallon Sadeeq tace "zaka bukaci wani abu kafin mu dawo?" Ya girgiza mata kai yana kallon Jiddah yace "kiyi min kissing Babyn on my behalf" Jiddah taji kwalla ya taru mata da sauri ta fita dan zata iya fashe wa da kuka Sultan ma duk sai yaji ba daɗi, Mami ta dinga kallon ɗan nata cike da tausayi daga haka ta juya ta bi bayan su Jiddah da har sun fita. Ammi ta dinga kallon Daddy da har sannan yaki ce mata komai, tace "Magana fah nake maka" yace "and so?" ta sake baki tana kallon sa daga haka kawai ta mike ba tare da ta sake kula sa ba, bayan ta isa bakin gate tana kallon gatekeeper tace "Sannu Baba" yace "yauwa Hajiya, kin fito kenan, ya me jiki kuma?" tace "Alhamdulillah" yace "ina wannan mutumin da ya kawo ta ranan?" Ammi tace "wani mutum kuma?" yace "wanda dai ya kawo ta gida ranan, toh kusan kullum sai ya zo wai yana son sanin ya jikin nata Ni kuma nace wallahi ban sani ba amma har sannan baku dawo gida ba" Ammi tace "Ayyah, jiki kam da sauki kawai dai sun rike ta ne saboda aiki da aka mata" yace "Allah kara lafiya" suna magana Mummy tazo fita daga gidan da motar ta ita da Niswa tayi horn mai gadi ya buɗe musu gate Ammi ta matsa gefe har suka fita kuma ba wanda yace mata kala itama bata damu ba kamar a baya idan ba su mata magana ba sai tayi ta damun kan ta, bayan ya rufe gate tace "Dama fah driver nake nema, yayi nisa ne?" Yace ai "tun daya kai Ayaan makaranta ya wuce ɗakin sa yana bacci" Ammi tace "dan yi masa magana mana asibiti zai kai Ni" da sauri mai gadi yayi sashin su don kira mata driver ita kuma ta wuce cikin gida da dauko basket ɗin da ta gama hada musu breakfast tana mamakin Daddy har sannan, yanzu tama daina hawa motar gidan sai dai ta hau motar da akama Leena gift, bayan ta fito ta samu har ya wuce parking space yana warming motar ta karasa wajan ya karɓe kayan hannun ta yasa a bayan motar yana gaishe ta. Bayan sun isa asibitin Jiddah ta ciro wayan ta dan kiran Binta taji suna ta ina amma sai bata ga numbern ta ba tana kallon Mami tace "Mami wallahi banga numbern ta ba, toh ko da me nayi saving Oho" Sultan ya Ciro wayan sa ya kira Rayyan buga daya Rayyan ya dauka bayan sun gaisa yace "Dan Allah ko zaka iya fada mana inda Leena ke kwance?" yace "Okay" bayan ya faɗa masa suka sauka Mami sai sannan ta kara jin nauyin su, duk tafiya suke jiki a sanyaye. Hajiya sai faman banbami take wa Leena, Anty Binta tace "Toh ba zaki ba sa bane?" tana share hawayen ta ta ɗauki babyn Anty Binta na tsaye a kanta, ta lulluɓe jikin ta da Babban veil sannan ta fara breastfeeding Babyn, Hajiya tace "Da ke haka aka miki ai ba zaki ganu ba" bata sake cewa kowa komai ba, knocking ɗin kofar da akayi ne yasa suka juya suna kallon kofar Hajiya tace "a bude yake" Jiddah tayi karfi halin buɗe wa ta shiga da sallama su Mami na biye da su a baya, Leena kallo ɗaya ta musu ta ɗauke kanta nan da nan taji hawaye na taruwa a idon ta kamar yadda Hajiya ke kallon su haka anty Binta ma, bayan sun Zazzauna Kanwar mahaifinsu ne ta gaida Hajiya, Hajiya ta amsa a dakile tana kallon wani wajan, suma duk suka gaishe ta amma ba wadda ta sake wa fuska, Anty Binta ta gaishe su suna tambayar ta ya me jiki, a hankali Leena ta gaishe da Mami da Baabar su Sadeeq, Mami ta amsa tana tambayar ta ya jiki, tace da sauki, bayan sun gaisa da su Sultan suma duk ya jikin suka mata, haka nan Leena bata ji dadin reaction din Hajiya ba, Mami kuma tayi farin cikin rashin Ammi da basu yi ba dan ji take kamar ba zata iya haɗa ido da ita ba, Anty Binta ta mike ta karasa wajan Leena, Leena ta gyara jikin ta sannan ta mika mata Baby, ta karba ta kaiwa su Mami, Mami ta dinga kallon fuskan Babyn taji hawaye ya cika mata ido ganin Babyn take yi kamar sanda ta haifi Sadeeq haka sak ya ke shima, ta masa addu'a ta mika wa Sultan shima kallon kyakkyawan fuskan Babyn yake yi, Baabar su ta karba tana addu'a, a hankali Jiddah ta karba itama tana kare wa Babyn kallo, kuma duk babu mai cewa komai, Sultan na kallon Anty Binta yace "An masa hudu ba ne?" Caraf Hajiya ta bada amsa "Toh kai sai aka ce maka ba'ayi ba sai ka yarda?" Ba Leena ba har anty Binta taji ba daɗi Sultan yayi murmushi kawai yace "me sunan Babyn?" kafin anty Binta tayi magana Hajiya ta kuma riga ta "Toh ita dai Linan wai Abubakar za'a kuma saka masa" ta karasa maganar tana tagumi dan ita wannan lamarin na bata mamaki, duk sai da jikin su yayi sanyi jin wai an sawa Babyn Abubakar, Ammi ne ta buɗe kofar dakin da sallama, Mami taji kamar ta nitse, ranan da ta roki Ammi wai a daura auren da ɗan ta Sadeeq wannan scene ɗin ne ya dawo mata sai kuma taji jikin ta ya kara sanyi, Ammi ta gwada kamar ba komai duk da sakin 'ƴarta da akayi ya mata ciwo ba kadan ba, amma ta dake suka gaisa cikin mutunci Ammi ta ajiye musu basket ɗin hannun ta tana kallon Binta tace "ki hada mata breakfast din Binta" Mami ta kalli Jiddah tace "Kinga mun manta namu basket ɗin a mota kawo Babyn kije ki dauko" Mami ta karba tana kare masa kallo ba'a dau lokaci ba sai gata ta dawo, Jiddah ta dinga taba Mami da kafa dan tayi bayani amma Mami tayi kamar bata gane ba, can tana kallon Binta tace "sister Binta ko zamu iya magana?" da sauri Hajiya ta mayar da kallon ta ga Binta tana son kallon reaction din ta, Binta ta mike suka fita a dakin, Jiddah ta mata bayanin duk abinda da ya faru, jikin Binta yayi sanyi har ta kasa magana, bayan sun koma ɗakin asibitin, Mami na kallon Jiddah ta mika wa Anty Binta babyn suka mike suka musu sallama. Bayan fitan su Hajiya tace "ji wani jaraba kuma, sun zo su tayar mata da hankali ne?" Ammi ta sauke ajiyar Zuciya tace "ai dama ya kamata su zo Hajiya, tunda yanzu maganar lafiya ake" Hajiya tace "Toh dama ke me kika sani Hauwa? Ina haka kike ko da yaushe baki canzawa jiya iya yau, shiyasa kishiyar ki ta samu galaba akan ki" Ammi kawai tayi murmushi dan ko Hauwa da Hajiya ta kira tasan ranta ya ɓaci ne, anty Binta tace "Toh ai baku san me Kanwar nasa ta ce min ba" sai kuma ta juya ta kalli Leena dake cin abincin gaban ta a hankali. Bayan kwana biyu, babu irin siyayyan da Mami da yaran ta suka mance ba suyi wa Leena da jaririn ta ba, har hakan ya sa Hajiya ta ɗan sauko, a bangaren Rayyan ma kuwa ba'a barsa a baya ba dan shima ya taka rawar gani ba kadan ba, har sannan kuma Sadeeq ya kasa zuwa ganin Baby duk da kuwa san da yake ya sa Babyn a idon sa, bikin Niswa kuwa saura kwana goma, Mummy kuma har sannan bata zo ko da sau daya ta duba Leena da jiki ba hakan yasa Hajiya kara tsanar ta. Yau tun safe Anty Binta ta mayar da wasu kayan da suke amfani a asibiti gida, dan yau za'a sallame su, bayan Rayyan yayi parking motar sa Layla ta buɗe kofar ta sauka shima saukan yayi, bayan sun shiga dakin da sallama duk suka amsa masa ya gaishe da su Hajiya suka amsa yace "Ammi ina Leenan?" Ammi tace "tana toilet ne" yace "ayyah" Layla ta gaishe da su Hajiya, Hajiya na kallon Rayyan tace "Dama ai yana da kyau kana shigo da ita pamili dan ta san mu, muma mu santa, amma kullum bata shiga cikin mu kamar matar ɓoye" Layla murmushi kawai tayi Ammi ta mika mata Babyn ta karba tana kare masa kallo kawai taji hawaye ya cika mata ido lokacin daya kuma taji son Babyn har cikin zuciyar ta, sai yanzu taji haushin zubar da cikin da ta yi, Anty Binta ta buɗe kofar toilet ta fito Leena na biye da ita a baya, Leena ta gaishe da Rayyan, tana kallon Layla dake kallon Babyn hannun ta with passion tace "Ina wuni" Layla ta kalle ta tace "Lafiya, ya jikin kuma" tace "Alhamdulillah" bayan fitan Rayyan ba'a dau lokaci sosai ba sai gashi ya dawo yana kallon Ammi yace "An sallame ta yanzu". Bayan yayi parking motar a kofar gidan su duk suka sauka har sannan Layla na rike da Babyn Anty Binta ta so karba amma Ammi ganin yadda Laylan take makale da Babyn yasa tace a bar mata kawai, bayan sun shiga compound ɗin, Niswa data fito daga sashin Daddy ta sake baki tana kallon su da mamaki, har parlorn Ammi suka karasa, Ammi tace "Layla ko a baki Babyn ne?" Murmushi kawai tayi, Ammi tace "Allah baki ke ma" a hankali tace "Amin" Hajiya ta mike ta wuce zuwa sashin ta, Rayyan ya mike yana ganin Leena yace "ki dai tabbatar kina shan magani" a hankali tace "Tohm, Nagode" ya mike ya fita. Niswa na shiga parlorn bata ga Mummy ba ta wuce dakin ta ta buɗe, da sauri Mummy dake rike da wani abu a hannun ta ta mayar da hannun nata baya tana son ganin wanene tace "Sai ki shigo min dakin ba sallama?" Niswa tace "Mummy kin san me na gani yanzu?" Mummy tace "Meya faru?" tace "Wallahi Ya Rayyan da Layla na gani suna raka su Leena sashin su,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 30 Chapter of 50