Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
hakuri ce, irin su kadan ne a duniya, Allah shiga lamarin ta da ƴarta" Daddy be iya cewa komai ba, ta ajiye kaskon hannun ta ta fara zuba hayakin a ciki, sai kuma tace "toh sai ka taso kazo kayi na wankan" yace "Hajiya ki bani maganin zan yi anjima" ta masa wani kallo tace "Saboda matar ka ta samu damar hana ka?" daga haka ya mike. Leena na komawa part din su ta sami wayan ta na ringing ta ajiye Babyn a gadon sa kafin ta karasa har ya yanke, ta ɗauka tana kallon missed call ɗin Malik, tsaki tayi dan yanzu kuma abun nasa ya koma takura. Bayan sun koma gida, toilet ya wuce yayi wanka sai da ya gama sannan yayi amfani da maganin da Hajiya ta basa da be yi believing ba amma ganin da gaske aka raba Leena da mijin ta hakan ya basa tsoro, dama kuma kiran da Hajiya ta masa kenan dan ta basa magani, ya dauki lokaci sannan ya fito, samun Layla yayi har ta gama gyara dakin tasa turaren wuta sakar masa murmushi tayi ta ajiye abin hannun ta akan dressing mirror tace "bari na daura mana dinner" yace "ki bari zamu fita mu ci" ta tsaya kallon sa yace "Sure, we're going out on a date, ko baki so ne?" tace "Ina so kai, abinda ban samu ba tun a waje" yayi murmushi jin yadda tayi sounding. Niswa tace "Wallahi Mummy idan baki tashi tsaye da gaske ba sai Layla ta saki kuka" Mummy tace "Naga alama kam Niswa, wallahi da na san haka ne da tun farko ban cusa masa ita ba" Niswa ta taɓe baki tace "Gashi kuwa yanzu kamar ya fara son ta, dan na gani a idon sa" Mummy tayi tagumi Niswa ta cigaba tace "Dan wulakanci wai ta haɗa kai da su Leena?" Mummy tace "gashi uwar ta har sannan bata bari na nayi magana da malamin nan, ko da munje a waje take bari na balle na kai masa Sunan Laylan" Niswa tayi dariya tace "Hajiya Mama ba daga nan ba". Da Daddare bayan Ammi ta gama gyara dakin ta, tasa turaren wuta, tana kan kunna mosquito coil taji an buɗe kofar dakin duk zaton ta Ayaan ne yasa bata juyo ba amma Kamshin da ya dake hancin ta ne, the smell that she is obsessed with, kafin ta kai ga juyawa ya rungume ta ta baya, tayi shiru tana tunanin yaushe rabon ta da shi, a hankali yace "I'm sorry wife, nasan ban kyauta ba" Ammi tace "wani abun ya faru ne?" ya juyo da ita yana facing dinta yace "Your silence is killing me, Dan Allah kice duk abinda kin san zaki huce, dear" Ammi ta girgiza masa kai tace "It's Okay" yace "I'm sorry, I'm so sorry, please! Kin san haka kawai ba zanyi ignoring dinki ba" Ammi bata ce koma ba ta janye jikin ta ta cigaba da kunna coil ɗin ta ajiye a spot din sa ta mike taga har sannan kallon ta yake yi yace "amma kin san you're my all time favorite, kimin uzuri mana" tace "Bakomai wallahi" yace "Wallahi na kasa hada ido da Leena nasan zata yi tunanin dan bani bane mahaifinta ko?" ya karasa jikin gadon ya zauna yana bin Ammi da kallo dan yayi missing ɗinta ba kadan ba, yadda take magana da shi, yadda take basa shawara, yadda take kwantar masa da hankali, uwa uba ga safta da iya girki, a hankali Ammi tace "A'a akan me zata dauka? Ai a baya baka rage ta da komai ba, so kar kayi tunanin haka" Daddy ya jingina kansa da gadon yana kallon sama. Washe gari bayan ta gama shirya Ayaan har driver ya kai sa, haka nan Daddy wai sai dai da kanta zata yi feeding dinsa, ta kalli parlorn da sauri sai kuma ta tura masa plate ɗin abinci gaban sa tace "idan 'yarka ta ganmu fa, kar ka manta ka zama kaka fa" ya buɗe hannun sa alamar ina ruwan sa yace "Ai zata koya ne daga gare mu, itama sai take ma mijin ta" Ammi tayi yar dariya ta mike ganin da gaske yaki breakfast ga kuma Binta da Leena dake zaune a Parlorn, bayan ya gama breakfast yace ta raka sa, tana rike da briefcase dinsa ta raka sa har jikin motar sa, sai tsokar ta yake yi duk da taki biye masa amma tana murmushi, tunda Mummy ta fito idon ta akan su, har ta gagara controlling kanta, bayan Daddy yayi hugging Ammi zai shiga motar sa, ganin haka yasa Mummy sake jakkan hannun ta duk juyawa suka yi, ganinta yasa suka ɗauke kai ba wanda ya kara bi ta kanta, barin ma Daddy da yake jin tsanar ta a ran shi. gaba daya a wajan aiki Mummy ta kasa samun nutsuwa, sai faɗa take da sauran ma'aikatan wajan daga karshe ma gida kawai ta dawo dan ta kasa sukuni, kuma tayi ta kiran aminiyarta amma baya shiga. A haka Mummy tayi rayuwa kwana biyun nan a gidan Daddy bata da wani peace of mind, sai ma baccin da bata iya yi da daddare, ga baki sun fara taruwa saboda bikin Niswa da ake shirin yi. Oops! Where am I even going to start, My lovely dearest? Well, Assalamu alaikum, mutanen arziki, I'm a bit busy today, so today's chapter will be shorter than usual, ayi hakuri da hakan, thank you. Hauwa Jibrin Sulaiman (Jiddatul-khayr) *AGOLA (Behind the palace walls)* 🫧 Wattpad © Jiddatulkhayr Young talented writers association (YOTA) Chapter 49&50 _________Ammi dake kallon Anty Jiddah da Farida tace "bari a tashe ta ai la'asar ma tayi" Anty Jiddah ta mike tana kallon Ammi tace "A'a kar a tashe ta Ammi, bari kawai mu tafi, kawai dai idan ta tashi ace Farida ce ta zo gaishe ta" Ammi tace "ba ayi haka ba kam, ace tun daga wani gari ta zo gaishe ta ace kuma bata ganta ba?" daga haka ta wuce ciki, Anty Jiddah ta koma ta zauna, Farida sai kallon Babyn take yi, ba'a dau lokaci ba sai ga Ammi ta fito Leena na biye da ita a baya, ta sake baki tana kallon Farida sai kuma ta karasa cikin parlorn tayi hugging ɗinta tace "Sister Farida yaushe a gari?" Farida tayi murmushi tace "Jiya na shigo da daddare nace barin zo ganin Baby" ta zauna, bayan sun gaisa basu dade ba suka ce za su tafi, Leena ta mike ta raka su har gate, da take dawowa taga sai kallon ta ake ana magana kasa-kasa dake gidan yanzu ya fara cika, duk da yadda taji wani iri amma sai ta ɗauke kanta tana kallon kasa har ta karasa part din su, Ammi tace "an kira ki" ta karɓi wayan da Ammi ke mika mata ta kalli kiran Malik ne, ta ajiye wayan ba tare da ta sake bin kan kiran ba, tunda suka fara event Leena ko da wasa ba ta taɓa fita ko da compound ɗin ba, saboda duk sanda ta fita indai ta haɗu da wani na Mummy toh sai sun jefa mata magana akan mutuwar auren ta hakan yasa ko bakin kofa bata yarda ta taka, kuma Hajiya bata damu da ta sa suna shiga cikin su ba, Niswa tayi bridal shower wanda kuɗin da aka barar bana wasa bane, hakan ya sake tabbatarwa mutane ba karamin mutum Niswa zata aura ba, yau tun da safe Niswa ta bar gidan su ta koma gidan Kanwar Mummy, gaba ɗaya gidan sai hada hada ake yi, hatta bangaren Hajiya a cike yake da cousins ɗin Daddy da yaran su da suma sukayi takanas dan halartar bikin. Mummy tayi dariya tace "Wallahi kaman kin sani, ina aurar da Niswa ai burina ya cika" Kawar ta Maryan tace "Toh ba zaki kai ma ita kishiyar taki gate pass ɗin bane? Karfa aje can ayi barin kuɗi Kinga idanun su bai kalla ba balle bakin ciki ya kama su" tayi dariya tace "Wallahi kin kawo shawara, ai kuwa da kai na zan shiga na ba su". Daddy ya shiga parlorn da sallama, Anty Binta ta amsa ta mike zata dakin Leena yace "kawo shi" daga haka ta mika masa Babyn ta wuce ciki, Ammi jin muryan sa yasa ta fito tana murmushi yace "Madam yunwa nake ji" Ammi ta karasa ta karbi Babyn tace "Muje ka ci" dinning suka karasa tare suna hirar su, bayan ya gama ya mike yace "I think sai dare kawai zanna shigowa gida cos naga gidan yanzu a cike ya ke" ta gyada masa kai tace "Hakan ma it's okay ai" Sallamar Mummy suka jiyo, Mummy bata yarda an bata izini ba ta kusa kanta wani irin jiri ne taji yana neman ɗeban ta har wani dishi dishi take gani, dan bata yi expecting ganin Daddy ba, Daddy yayi ma Ammi sallama daga haka ya fita ba tare da ya bi takan Mummy ba, da kyar ta iya daurewa ta zauna akan cushion ɗin tana faking murmushi, cos yanzu har ta fara manta da wani bakin cikin da Daddy ya fara kunsa mata ba sai yanzu da ta shigo kuma taji damuwar ta ya dawo sabo, Ammi ta katse mata tunanin ta da cewa "Mun wuni lafiya ya taro?" tayi murmushi tace "Alhamdulillah, dama na kawo muku kati ne nace kar kuce ba'a fada muku ba" Ammi ta karbi gate pass ɗin data ke mika mata tana kallon tace "Allah ya sanya Alkhairi" idon ta nakan jaririn da Ammi ta ajiye a gadon sa tace "ina Leenan?" Ammi ta kwalawa Leena kira bayan Leena ta fito fuskar ta ba yabo ba fallasa tace "Ina wuni" Mummy tace "Lafiya Leena" sai kuma ta buga uban tagumi tace "Oh Ni Khadija yanzu fisabilillah yarinya karama Kamar Leenan nan ace an maida ta bazawara? ai shi yasa sometimes auren wurin nan babu alkhairi kwatakwata tattare da shi" Leena ta mike ba tare da ta amsa mata ba Ammi kuma kallon ta kawai ta tsaya yi da mamaki, Mummy tayi saurin cewa "Amma Leena kema baki tsaya kinyi tunani bane kika aure sa? Ko dai gudun kar ace an fasa auren ki yasa kika amince da auren sa? Ashe dai gidan su basu gaji arziki ba" kamar daga sama sai ga Anty Binta ta fito tace "Toh idan Allah ya kaddari abu babu bai canza ta, ko da kuwa suna son junan su kamar su cinye ne tunda aure tsakanin su ya kare ai shikenan dole su rabu" Mummy ta tabe baki tace "Ai wata sa'in naci ne ke jawo hakan" ta mike zata fita sai ga Layla na shigowa da sallama a bakin ta Mummy ta tsaya kallon ta sai kuma tayi yake sau daya Layla ta kalli Mummy tace "Ina wuni" Mummy tayi banza da ita ta fita ba tare da ta sake kallon su ba, Layla ta gaishe da Ammi da Anty Binta daga haka ta wuce dakin Leena, Anty Binta tace "wallahi munafurci ne ya kawo ta nan" Ammi ta mike ba tare da ta ce komai ba Anty Binta tace "Ammi wallahi duk ke kike kyale matar nan" Ammi ta ajiye katin hannun ta akan Centre table Anty Binta ta ɗauka tana kallon tace "Allah ya kiyaye wanin mu ya halarci wajan taron nan" Ammi bata ce mata komai ba ta wuce dakin ta", Layla tayi hamma, Leena tace "Toh ki hau gadon mana kamar bacci kike ji fah" tace "Wallahi baccin ne ma, dan jiya ban samu nayi ba gashi yau an hanani saboda tsinanniyar auren nan" taja tsuka ta kwanta akan sallaya, ita dai Leena bata ce mata komai ba. wata cousin ɗin Daddy tana kallon Hajiya tace "Hajiya ya naga baki fara shiryawa ba naji ance da wuri za'a je wajan event ɗin dan naji wai kamar motoci ma sun fara zuwa" Hajiya tace "Toh ni kuma tsofe tsofe da Ni zan kama hanya wai da sunan event? A'a ba dai Ni ba kam" tace "Toh ai Hajiya naga kin je na Rayyan ma balle wannan da kamu ne" Hajiya tace "Toh ba Zanje ba, nace ba zan je ba ko? Ko zaki sani dole ne?" ta mike tace "Kiyi hakuri Hajiya duk abin bai kai nan ba" daga haka ta bar Hajiya a dakin ta dan yanzu kallon Hajiya ta gama tsufa take abu kaɗan sai ta har zuka. Ganin lokacin yayi har an fara fita yasa Mummy kiran Layla, Layla da bacci yayi daɗi tasa kiran a silent ta cigaba da baccin ta, Hajiya Fatima tana kallon Mummy tace "Ki kuma kiran ta karfa tasa mu makkara a fara taro bamu" Mummy tace "Ai ina ga sun shanye ta ne, nace miki fa ɗazu kafin ki zo da ido na naga tana shiga parlorn na su wlh" Hajiya Fatima tayi tsuka tace "Dan Allah mu tafi ita taji wajan idan bata zo ba" daga haka Mummy ta saka wayar ta a ɗan karamin fos ɗin hannun ta me shegen kyau, ba karamin kyau ta sha ba, kana ganin ta kaga uwar Amarya. kukan da Babyn Leena ya fara yasa ta farkawa da sauri ta jawo sa jikin ta tana dan girgiza sa dan ya koma baccin da yake yi, ganin ba komawa zai yi ba kawai ta tashi itama ɗaukan sa tayi ta fara feeding dinsa kallon agogo da ke nuni da karfe huɗu tayi sai kuma ta juya tana kallon Layla da mamaki sai dai kuma bata ce komai ba, Ammi ce ta leko tace "Aah dama bacci Laylan ke yi?" Leena ta gyada mata kai Ammi tace "Ai da kin tashe ta" daga haka ta tashi Layla, bayan ta farka Ammi tace "Layla karfe 4 fa yayi naga kuma tun dazu kuma mutanan gidan ke tafiya fa" Layla ta murja idanun ta tace "Toh Ammi yanzu zan shirya" daga haka Ammi ta bar bakin kofar, ta jawo wayan ta tana kallon missed call ɗin Mummy da Maman ta sai kuma wannan numbern mutumin da ya kira ta ranan, ɗan Satan kallon Leena tayi ganin ba direction ɗin ta take kallo ba yasa ta sauke ajiyan zuciya ta kashe wayan baki daya dan bata bukatar ya sake kiran ta yanzu, tace "ya tashi ne?" Leena tace "Eh fah, ban jima da kwanciyar ba fa amma Kinga ya tashe Ni" tayi murmushi tace "me ku ke ce masa?" Leena tace "Babu" Layla ta mike tsaye tace "Haba ke kuwa, sai kace You're not famous, ai kamata yayi ace a waye kike dan Allah sa masa nickname me daɗi" Leena Murmushi kawai tayi ba tare da ta ce mata komai ba, kayan jikin ta take cirewa da niyyar shiga wanka tace "Toh ke ba zaki bane?" Leena tace "ba fa muyi 40days ba fa" ta gyada mata kai tace "Wallahi na manta ne" sai kuma ta ja tsaki tace "yanzu sai ya zama magana idan mutun bai yi attending ba, beside bana son Rayyan yaji ba daɗi ne amma da ta sune wallahi ba Zanje bikin shegiyar nan ba" Leena bata ce mata komai ba har ta gama cire kayan cikin ta ta wuce toilet. Sai bayan Magrib suka gama kamun su, kowa sai san Barka yake dan biki kam an yi shi bana kananun mutane ba, duk suka dawo gida lilis, Mummy kam bragging din da take zaka ɗauka su suka kashe wannan uban kuɗaɗen, ta faɗa ta maimaita Yadda aka bada kudin buɗan kai 20mil. Niswa da few friends ɗinta suna zaune duk suma sun gaji barin ma Niswa, wata friend dinta tace "Kai Niswa ai na kika samu miji irin wannan?" yar dariya tayi tace "God sent am" duk dariya sukayi, wata tace "gist us please" tace "toh nace me kuma? Nima da farko wallahi na ɗauka yaudara ta zaiyi shiyasa ko faɗa banyi ba" wata tace "amma suna da Bala'in kuɗi, ko da yake Prince ne ai" Niswa tace "Hmm Kinga yadda yake spending min? Toh da farko har na fara tsoron kudin sa amma tun da suka zo gaisuwa anan aka san wanene shi, ke most of the furnitures ɗin na a jikin shi na cire" duk suna mamakin yadda suka gansa da kuma familyn sa dan kallon farko zaka san cewa kudi ya zauna musu, dan ba sai sun yi bayani ba, wata friend dinta da tun ɗazu bata sa baki ba a maganar na su ita ce tace "Wallahi ban so ace yau Friday bane, dama Jiya akayi Event ɗin nan da yanzu mun caske kudin mu a hannu, 20mil? ai ba wasa ba" nan suka fara hauka suna dariya. Yau da ya kasance ranan daura aure, tun asuba Niswa ke waya da mijin ta Ashraft, kallon karfe bakwai yayi tace "kasan yanzu zan fara zuwa gida daga can sai na wuce wajan makeup ɗin, kai kuma daga daura auren sai ka zo idan mun gama hotuna sai na tafi gida tunda kasan dole acan za'a dauke ni" yace "Uhm baby, yanzu dai in barki kenan?" tayi murmushi tace "ka ga makeup na ɗaukan lokacin" yace "Okay, sai munyi waya" daga haka ta kashe tana kallon friend dinta da ta sata a gaba tana harararta tace "ke Malama ai na gama wayan yanzu ko?" tace "Ke kika sani, Kinsan yana da kyau ace duk abinda zaki yi kiyi da wuri saboda karfe biyu suka ce jirgin naku zai tashi ko?" Niswa ta mike tace haka ne fa, brush din ta da ta sa masa toothpaste ta ɗauka ta wuce toilet. Ganin part ɗin Ammi ba kowa hakan yasa Daddy anan yayi breakfast dinsa ya dauki babban riga da ya musu anko shida Ayaan yace "Madam dan Allah ki shirya Ayaan cikin kayan nan" Ammi tace "Toh shikenan" daga haka ya fita zuwa nasa bangaren dan shirya wa. Manyan kuloli da aka gama hada hadaddiyar breakfast wa dangin miji Niswa Mummy ta fito tasa driver ya kwashe su tana fada masa idan ya isa hotel ɗin da suka sauka ya kira drivern su ya fito ya kai musu breakfast din, daga haka ya wuce. Dakyar Rayyan ya samu ya lallaɓa Layla ta yarda zata gidan Mummy, sai narke masa take yi wai bata da lafiya, kasan marar ta na damun ta, bayan yayi parking tare suka sauka, har part din Ammi, bayan yayi sallama Ammi tace Su shigo, bayan sun gaisa Ammi na kallon Layla tace "baki jin dadi ne?" ta girgiza mata kai tace "Kawai dai ciki na ne ke ɗan ciwo" Ammi tace "Allah ya sauwake" Rayyan yace "Ammi zan samu breakfast?" Ammi tace "kadan ne wanda ya rage, shima sauran na Daddyn ku ne bari Binta ta daura maka" yace "No, na Daddyn ma is Okay zan haɗa da tea" dan yanzu ya daina cin duk wani da ya fito daga sashin su, dan Hajiya ta hana sa ga kuma Layla ma, Leena ce ta fito sanye da Hijab tana rike da Babyn ta ya mike ya karasa har inda take ya karbi Babyn ya koma ya zauna yana ma Babyn wasa, Leena tace "Yaya ina kwana" ya daga kai yana kallon ta sai dai bai amsa ba Layla tace "gaishe ka fa take yi" a takaice yace mata "Na sani" Leena ta kura masa ido ya kalle ta yace "Kina kuka kenan har yanzu?" ta girgiza masa kai yace "Toh tunanin me kike yi?" ta ɗan kalle sa sai kuma ta ɗauke kanta tace "Babu fa" yace "kamar yaya zaki ce min babu gashi kin wani rame" Ammi da ta gama hada masa tea a dinning area tace "Ahtoh kai ma ka tambaye ta" tayi shiru tana wasa da fingers ɗinta Layla ta mike ta wuce dakin Leena dan ita yanzu ba kanta zasu gane ba, Ammi tace kaje ka karya Rayyan" ta karbi dan hannun nasa tana cewa "Wallahi Ni da Binta ba irin bakin da bamu ba ma yarinyar nan daga karshe hakura mukayi" yace "we need to talk Leena, bari a gama taron nan" daga haka ya karasa dinning ita kuma ta wuce dakin ta, tana kallon Layla data kwata a kasa tace "ga gado amma sai kiyi ta kwanciya a kasa?" Layla tace "Kinga wallahi kasan yafi min daɗi ne, beside ga ciwon cikin da ya sani a gaba". Yadda Mummy tayi Bala'in kyau tasha gwalagwala kaɗai ya isa ya nuna maka cewa Uwar amarya ce wannan, Hajiya Fatima ba ba'a barta a baya ba, Yadda Nisreen tayi kyau itama sai ka ɗauka amarya ce. A bangaren amarya Niswa kuwa yadda tayi kyau tana stunning ba sai an fada maka wacece ita ba, kuma kasan ba karamin gida zata shiga ba, dan kaya mai bala'in tsada ta saka, harta makeup artist din sai kallon Niswa take yi tana 'Awww' Friends dinta sai daukan ta hoto suke tun kafin ango da photographer su iso, tsadaddan motar da ango da ya bayar dan yawo da ita yana parke a bakin kofar makeup shop din, tafiya take kamar ba zata taka kasa ba, a haka suka bar shagon, drivern da gudu ya karasa ya buɗe mata motar ta shiga friends dinta ma duk shigan suka yi, be tsaya ko ina ba sai kofar gidan su, kowa ya sake baki sai kwallon ta yake yadda ita kadai sai wani sheki na musamman take, tun daga nan suka fara daukar hotuna. Screaming hannun sa yayi da karfi har sai da jijiyoyin jikin sa suka tashi raɗaraɗa a jikin sa, ya sake shiga Whatsapp dinsa for the countless times yana kallon videos da aka turo masa babu ko kiftawa, buga wayar yayi da kasa ya hura iska a bakin sa ya dunkule hannun sa ya dake iska yace "Why Niswaaa??" Idon sa yayi mugun ja, cousin ɗin sa dake zaune tun dazu shima speechless ya mike ya na kallon dan uwan nasa cike da tausayi yace "Prince pls calm down, kar ka jima kan ka ciwo" yadda ya juya yana kallon sa hakan yasa shima masa baya da sauri. Daddy ya kalli agogon hannun sa sannan ya kalli Rayyan shi dai kawai yayi shiru dan gaba ɗaya sai yaji hankalin sa yayi mugun tashi, abinda ya faru lokacin daura auren Leena ne kawai ya fado masa a kai, da sauri ya dafe bangon ya zauna yana Salati a hankali, Rayyan ya kalle sa yace "Is everything alright, Daddy?" Ayaan ma sai kallon Baban nasa yake dan kana ganin sa kasan akwai abun da ke damun sa a wannan moment ɗin, yana kallon Rayyan yace "Rayyan ba kuyi waya da su bane?" Rayyan yace "da zu dai munyi waya da Ashraft ɗin, sannan kuma ai an kai musu breakfast" Daddy yace "kalli agogo, time fah yayi ba kowa nasa" Rayyan yayi shiru shima dan yanzu ya fahimci me Daddy yake nufi, kallon body guard din su yasa Daddy sauke ajiyan zuciya, Rayyan da yaji shigowan messages wayan sa duk tunanin sa Layla ce yasa ya shiga Whatsapp ɗin sa, wani sabon numbern da ya gani haka nan yaji zuciyar sa sinke wa yana shiga yaga videos ne wajan 10, fara kallon da yayi yasa ya kifa wayan sa ba shiri yana rintsa idanun sa ya fara salati, Daddy duk hankalin sa na kan dan aiken, bayan ya isar masa da sakon su Daddy yaji wani sanyi na shigar sa, toh me zai duba a Whatsapp ɗin bayan yasan karshen sa a kuma yadda aka yi wa Leena, amma hakan yasa ya daure ya kunna wayan nasa kallon sabon layin da messages ɗin sa ya shigo ya tsaya yi amma ya gagara buɗewa. Assalamu Alaikum, daga ina ma zan fara? Kunyar ku ma nake ji gaskiya, well! Jina shiru da ku ka yi jinya wata dan matsala aka samu, amma ina fatan zaku yi enjoying wannan chapter din, Thank you. Naga ruwan votes please. *AGOLA (Behind the palace walls)* Wattpad © Jiddatulkhayr Young talented writers association (YOTA) Chapter 51 He was extremely shocked and deeply disappointed in her because he never saw this coming from her, mike wa tsaye yayi ba tare da ya kalli Rayyan ba, ya ɗan juya ya kalli colleagues ɗin sa da wasu few friends din sa dake tsaye suna magana, ya juya a hankali ya wuce

Chapter 32 of 50