Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ɗaya sai yaji wani iri saboda Umma, bayan ya fita ya jiyo muryan Abbah, ya juya ganin Abbah ne yasa ya juya zuwa inda yake, Abbah ya dafa kafaɗar sa yace "Malik, Karka damu komai zai wuce, ina ji a jiki na auren nan akwai Alkhairi, kar kace zaka canza ra'ayin ka Saboda Mahaifiyar ka, ka tausaya wa yarinyar ko dan jarabawar aure da ya same ta kuma ka ga marainiya ce, Nasan mahaifiyar ka na hakan ne dan ka janye, amma da kanta zata sauko kar ka damu" Malik ya gyaɗa masa kai, Abbah yace "Allah maka Albarka" ya amsa da Amin daga haka ya kama hanya. Mummy tayi parking motar ta a farkon Layin unguwar na su, tana ta bin wajajen da kallon gƴama ta jingina kanta da jikin kujeran motar ganin wanda take jira bata hango ta ba, tsaki taja ganin tana bata mata lokacin, ɗaukan wayar tayi ta kira matan, yana fara ringing ta ɗaga tace "Hajiya gani fa a hanya yanzu haka ma ina hango motar ki" daga haka Mummy ta katse kiran ba'a dau lokaci ba sai ga matar, kwankwasa motar tayi, Mummy ta cire lock ta sauke windown tace "shigo" matar na murmushi ta buɗe ta shiga, Mummy taji numfashin ta na shirin ɗaukewa saboda yadda jikin matan ke tashi, Matan tace "Ina kwana Hajiya, Kinga na daɗe ko? Ta baya na bi saboda bana son aga ina shiga Mota ina fita a fara saka ido shi..." Mummy ta katse ta tace "Dan Allah yi sauri kiyi maganar da ya kawo ni" tace "Toh dai yanzu abun da ake ciki shine mahaifiyar sa bata son auren kuma tace sai dai bayan ran ta ne za'ayi auren" Mummy tace "Ita asali me dalilin ta na dake wa akan hakan?" tace "Toh bamu dai sani ba, amma ko jiya da na shiga gidan naji tana mita, kuma kamar ance yarinyar da zai aura suna da kuɗi kuma selebiriti ce, Inaga saboda haka ne" Mummy tace "amma kun gwada mata maganar?" tace "Chap, ai ki raba ni da ita, daga sa baki na ta kusan mari na sabar masifa" Mummy tace "Naji" ta buɗe Jakkan ta ta fito da dubu goma ta mika mata tace "sauka, sai na sake neman ki, ki cigaba da binciko min komai" matar ta fara Godiya tana washe baki a haka ta sauka tana mata kirari, Mummy ta sauke ajiyar zuciya ta buɗe motar ta yatsar da miyau, tana tada motar ta bar unguwar. Niswa dake kitchen tana girki tana waya da Farouq sai dariya take, knocking taji ake yi a kofar parlorn hakan yasa tace "ana knocking kofa dear, barin je na duba, sai ka dawo bye" bata jira cewar sa ba daga haka ta yanke kiran ta goge hannun ta da towel ta fita zuwa parlorn, sai da numfashin ta ya kusan ɗauke wa ganin Mummy ce da Na'ila, muryan Mummy ya dawo da ita daga tunanin data faɗa, "Toh ba zaki bamu hanya bane ko ta kanki zamu shige?" Fuskar Mummy a tamke ta kare maganar, Niswa ta masa mata da sauri tana kirkiran murmushi tace "Sannu da zuwa, Mummy" Mummy bata amsa mata ba ta wuce cikin parlorn Na'ila na biye da ita a baya, Niswa ta rufe kofar duk jikin ta yayi sanyi ta karasa parlorn ta zauna tace "Sanni da zuwa Mummy, Ina wuni" Mummy tace "Fine, ina Umar ɗin?" tace "Baya gida sai dai anything yanzu zai dawo" ta juya ta kalli Na'ila dake danna waya kamar bata san da zaman ta a wajan ba, a hankali tace "Sannun Sister Na'ila" ta ɗan yatsina fuska tace "Ohh" Niswa ta sauke kanta kasa sai kuma ta mike ta wuce kitchen bata ɓa ta lokaci ba ta dawo parlorn rike da tray ta cika musu da snacks, ta duka ta ajiye a gaban Mummy, Mummy tace "Ni kam banda ci da kwanciya banga wani aikin da kike ba? Yanzu fah wajan shekara guda kenan" Niswa da rashin fahimta ta kalle ta sai kuma bata ce komai ba, Sallamar Farouq suka jiyo, tun da ya shiga ya tsaya daga bakin kofar yana kallon su da mamaki, Mummy ta mike ganin sa tace "dan an maka magana ranan shine ka ɗauke kafa a gida ko? Yau wajan satin ka nawa baka taka ko da kofar gida ba? Toh nazo faɗa maka ko zaka mutu ne sai dai ka mutu a cikin satin nan mahaifinka zai kai goron tambayar ka gidan su Fatima-Zahra" with shock yake kallon Mummy, Niswa taji hawaye ya cika idon ta ta sauke kanta kasa ba tare da ta bari wani yayi noticing ba, Farouq yace "Please Mummy kar ki.." ta katse sa, "Idan har ba zaka karbi zaɓi na bane sai ka fada min, yarinyar nan ba wanda bai san ta so wanta ba, yarinya mai hankali da kamala, ga tarbiyya, idan har zaka iya zama da wata macen karya kace ba zaka iya zama da ita ba, ko kana so ko baka so next month bikin ka, kuma ina son ka tanadar da wajan da zaka ajiye ta kuma kasan mahaifiyar ta ba karfi gare ta ba dan haka kayan kitchen kawai zasu yi sai ka fara siyan furnitures, period na gama magana" tana kallon Na'ila dake taunan chewing gum tace "Kee! Tatso mu tafi" daga haka ta fita fuuu, Farouq dakyar ya iya bin su da kallo sai kuma ya mayar da kallon sa ga Niswa da har sannan take duke a kasa, ya fuzar da isakan bakin sa sannan ya karasa dinning ya zauna yayi tagumi. Ta kalli Malik sai kuma tayi murmushi tace "wai me yasa kake damun kan ka ne? Kana da good future tunda har kayi karatu, wata rana sai ka sha mamakin yadda Allah zai mayar da kai, kuma ina jin a jiki na zaka samu sauyin wajan aiki very soon" yayi murmushi yace "Ina dai jin wani iri ne, You don't deserve someone like me, poor me, kawai dai ina da tsaurin ido ne da har nace ina son ki" ta masa wani kallo sai kuma yayi murmushi yace "Yes, I'm telling you, ai maganar gaskiya ne" sai kuma yayi making serious face yace "but please zaki iya zama da ni?" ta dinga masa wani kallo yace "No Leena, yana da kyau na tambaya, duba da yadda ni na taso da kuma yadda kika taso ba ɗaya bane, kin saba cin mai kyau, kin saba saka mai tsada, kin saba hawan mai tsada" tace "Well, ka je ka samu Daddy yanzu tun kafin ya fita kace masa ka fasa aure na, ba shikenan ba" sai da yayi dariya yadda tayi sounding yace "I'm sorry, princess" taki ko kallon inda yake da kyar dai ya lallaɓa ta ta sake fuskan ta. Leena na girki a kitchen, Ammi kuma ta gama wa Nawaf wankan yamma tana shirya sa, wayan Leena dake ringing a hannun Ayaan yayi silencing wayan ya cigaba da game ɗin, Ammi tace "zaka tashi ka kai mata ko sai na dake ka? Kai ba dama kana game da wayan mutum ana kira sai kana sa silent saboda ga ka baka so ana interrupting ɗin ka ko?" Sai ga Leena ta fito a kitchen ta karasa cikin parlorn tana "bani waya ta" kafin ya mika mata har ya yanke, ta zauna sai kuma ta buɗe baki ganin Zahra ce, Ammi tace "who?" Tace "wallahi Zahra ce Ammi" Ammi tace "Allah sarki, wallahi bata da zuciya ne, ni yaushe ma zan cigaba da bin ki idan nine ita? Yanzu sai ki faɗa mata maganar bikin na ki ai, kafin ki manta " tana murmushi ta gyada kai, bayan ta kira ta back Zahra ta ɗauka, tun kafin tayi magana Leena tace "Dan Allah kar ki ce wani abu nasan banda kirki" Zahra tayi dariya tace "kin hutar da ni kam tunda kin san halin na ki, toh ya kwana biyu? Ya Nawaf kuma" Leena ta amsa sai kuma tace "Dama fah ina son kiran ki wallahi" Zahra tace "Uhum, meya faru, just tell me, Dan nasan da dalili" Leena tayi dariya itace "Dama fah this coming Friday za'a ɗaura auren na" Zahra ta buɗe ido tace "Wow, really? Are you for real please?" Leena tayi murmushi tace "Sure!" Zahra tace This coming Friday? Kenan four days to go?" Leena tace "Eh, abun ne yazo a haka Shiyasa wallahi" tace "Ayyah, gidan Baban Nawaf zaki koma?" Leena tayi murmushi tace "Nope, ba gidan sa bane?" Tace "Ya Rain" abin ya bawa Leena dariya, sai da tayi mai isar ta sannan tace "ke kuma ji tunanin da kike yi" tace "Toh ai I've to ask ko?" Leena tace "Sure, amma ba su bane dan wannan kam saurayi ne bai taɓa aure ba" Zahra tace "Oh Ma Shaa Allah, Allah sa hakan ne mafi alkhairi" tace "Amin ya Rabbi, My friend" tace "Event fah?" Leena tayi dariya tace "Sai kace budurwa? Bazawara da nake fah, Toh dai babu wani event ɗin da za'ayi daga ɗaura aure Shikenan, shima haka yace" Zahra tace "see you, wai bazawara, toh ai dan naga kince saurayi ne dama" tace "A'a" suka ɗan yi hira sai kuma daga haka suka yi Sallama. Ammi da ta shiga cikin ta bar Nawaf, ya karasa wajan Leena jin ta gama waya yana mika mata hannu yace "Amma phone" Ayaan yace "A'a ka tsaya idan na gama zan baka" ta Harare Ayaan tace "kai baka san ka girma ba sai ka hana masa" ta mika wa Nawaf ta mike zata shiga ɗakin ta taji wayan na ringing, Nawaf ya mika mata, ta dinga kallon screen ɗin wayan ba ko kiftawa at the same time mamaki ne karara rubuce a fuskar ta, she ne the least wanda zata kawo hakan a ran ta, zuciyar ta ya fara bugawa da karfi har ya yanke bata gama recovering ba, ya sake kira Nawaf yace "Amma pick" sai sannan ta dawo daga duniyar tunanin da ta faɗa, ta tsaya kallon ɗan na ta ta karɓa zata yi picking ya sake yan ke wa. You guys are discouraging me, Shiyasa har na kasa long page yau, at least kuyi motivating ɗina with lots vote mana? Ko mu tafi hutu ne my Dudes? Jiddatulkhayr 08110615256*AGOLA (Behind the palace walls)* Wattpad © Jiddatulkhayr Instagram © Jiddatulkhayr writes Young talented writers association (YOTA) Chapter 61 Bayan Rayyan yayi parking a layin su Malik, wayan shi dake gaban aljihun sa ya ciro, dialing numbern Malik yayi yana ɗaga wa yace "Malik gani a layin na ku, so ka fito dan ban gane gidan ba" daga ɗayan bangaren Malik yace "Alright, I'm coming" daga haka Rayyan ya katse kiran ba'a ɗau lokaci ba sai ga Malik ya fito daga cikin gidan su, ta cikin motar sa Rayyan ke kallon sa hakan yasa ya ɗan yi gaba kaɗan sannan yayi parking ya sauka, Malik ya karasa inda yake ya mika masa hannun suka yi sallama, Rayyan yace "Da ma akan maganar mune shine nace barin zo, ban san ko kunyi magana da ita ba ko kuɗin akwatin zaka bata ko siyayyan da kan ka zaka yi i don't know which" Malik yace "ta ce bata son kuɗin already kuma dama ina da wasu kayan dana tara" Rayyan ya gyaɗa kai yace "Okay, na fahimta, dama bana so muyi magana acan Shiyasa ba biyo ka nan, so your acc details please" Malik yayi murmushi yace "No need, thank you" Rayyan yace "I'm sorry if what I said sounded awkward or somehow unpleasant, kawai dai naga nayi alkawari ne" Malik yayi murmushi yace "Not at all, kawai dai dan naga na gama haɗa akwatin ne" Rayyan ya dinga kallon sa sai kuma yace "Okay, kuɗin sadakin toh idan baka bukatar na akwatin" wani murmushi ya sake yace "Please ka daina damun kan ka, it's my responsibility not urs, I'm grateful for your kind" Rayyan yayi shiru yana kallon sa, Malik dake kallon wani waje ya juya jin shirun Rayyan ɗin, ganin kallon sa yake yi yasa ya sake masa murmushi yace "I'm sorry, but bana bukata ne, ai da ina bukata da zan karɓa" Rayyan yace "Ok, sai anjima" daga haka ya juya zuwa motar sa, Malik ya sauke ajiyan zuciya sai kuma ya koma cikin gidan su. Farouq yayi parking a compound ɗin gidan su, ya sauka duk yana hoping Daddy yana nan, bayan ya sauka a hankali ya fara tafiya zuwa cikin gidan, bayan ya shiga da sallama ya samu babu kowa a parlorn as usual dan haka ya haura sama, a corridor yaci karo da Na'ila ta ja baya tace "Yaya Ina kwana" ko kallon ta be yi ba ya wuce zuwa ɗakin Mummy, ta bisa da kallon sai kuma ta taɓe baki ta sauka downstairs. Mummy ta daga kanta dan kallon waya shigo mata ɗaki, sake baki tayi tana kallon sa sai kuma tayi murmushi tace "Ko dai ɓatan hanya kayi?" Ya zauna kan sofan ɗakin nata yace "Ina kwana, Mummy" tace "Lafiya kalau" sai kuma ya jingina jikin sa da bango yayi shiru yana kallon wani gu, can yace "Mummy dan Allah ki taimaka min, kin san bani da ra'ayin zama da mata biyu, ki janye maganar nan Please" tace "Saboda a ture kake har yanzu ko?" Yace "Mummy please, consider me, beside ko magana bamu yi" tace "Dama ka san da baka son zama da mata biyu shine ka auri wancan? Kai ma kasan dole ka bi zaɓi na" yace "Mummy dan Allah yaushe kika kawo zaɓin ki? Ina sai bayan aure na ne, and zafin da kike ma Niswa ya kamata ki ɗan sarara mata" tace "Abu ɗaya tak zaka yi dan na sarara mata shine ka kara aure, kai bama shawarar ka nake nema ba, dan already an gama maganar har an tsayar da rana, Inaga Daddyn ku ya manta ne bai faɗa maka ba" daga haka ta fice daga ɗakin ta bar sa nan zaune. Bayan Mummy ta parka motar ta, Hajiya Amina ta kyalkyale da dariya tace "Gaskiya Fatima baki da kirki wallahi, dama nan ne unguwar ta su Shiyasa kika dage sai ta aure sa" Mummy tayi dariya tace "Dama mijin da ya dace ta aura kenan, Kinga tana aurar sa, sai na koma kan uwar nata ma, itama sai ta bar min gida ko kuma ta bi duniya Ni ban damu ba" suka kwashe da dariya daga haka suka sauka, a kofar gidan su Malik suka yi sallama, Umma dake share tsakar gidan ta amsa tace "su waye ne?" Hajiya Amina tace "Baki ne" tace "Toh Bismillah" su Mummy suka shiga cikin gidan suna yatsina fuska, Umma ta shinfiɗa musu tabarma suka zauna bayan sun gaisa sai Umma tace "Amma sai dai ban gane ku ba ne" Mummy tayi murmushi tace "Eh baki san mu ba gaskiya" tace "Ok, Allah sarki! Amma me ke tafe da ku?" Mummy ta gyara zama tace "Dama akan auren da ɗan ki zai yi ne, munji labarin wai kina so a fasa auren dan baki son yarinyar, shine muka yi takanas muka ce bari mu zo" Hajiya Amina ta karɓe zancen ganin kamar Mummy bata kan line da suka tsara tace "kina ji ko Baaba, wallahi yarinyar marainiyace ga mijin ta na farko ya wulakanta ta da ciki sanan ya sake ta, yanzu kuma ta kwallafa rai a kan ɗan ki, mu kuma jami'an fararen kaya ne, sannan muna aiki da masu taimakawa waɗanda suke neman taimako, ki tausaya mata ki bari ayi auren nan, ko zata samu farin cikin, gata tana fama da ciwon zuciya" Umma tayi kankan da idanu tana kallon su cike da rashin kirki, Mummy ta ɗaura "Kinga idan har kika yarda munyi alkawarin baki tukuicin dubu dari biyar 500k" Umma ta mike tana murmushi tace "Toh dan uban ku baku isa canza min ra'ayi ba, kuka ce ku su waye? Kai ko Sarkin garin nan ne bai isa ba balle ku, kun ɗauka talauci zai sa na yarda da banzan kuɗin ku ne ko me?, ku fitar min a gidan kafin na tara muku jama'a, mara sa hankali kawai" yadda ta kare maganar da karfi kuma a tsawace yasa suka kalli juna Mummy tayi saurin cewa "amma kin san idan da rabo haka rabo zai kashe ki a banza, dan baki isa hana auren nan ba?" Umma ta fara musu ihuu da sauri Mummy da Hajiya Amina suka mike ba shiru suka fita suna mamakin ta, bayan sun shiga Mota suna maida numfashi Hajiya Amina tace "Amma naga basu kama kwatakwata fah? Gata baka gata da muni, amma shi ga haske ga kyau" Mummy tace "Baban sa ya ɗauko ai, baki ga Baban na sa bane, babu abu da ya bari na Baban, kai amma matar nan ta bani mamaki" Hajiya Amina tace "Mamaki ɗaya ko biyu? wallahi kamar me ciwon hauka" Mummy tayi dariya tace "ashe talaucin nasu ya kai haka?" Suka kwashe da dariya Mummy ta tada motar suka bar unguwar. Tun bayan tafiyar su Mummy abun duniya ya dame Umma, ta zauna tayi tagumi tana bitar maganar Mummy na karshe, wato rabo zai iya ɗaukan ta, tayi shiru tana bin compound ɗin na su da kallo, tana tunanin zuci, tasan tabbas haka ne, rabo zai iya ɗaukan ta gashi duk haukan da take dan ganin kar ayi auren amma yau saura kwana uku a ɗaura auren, ta dafe kirjin ta da sauri. Mummy dake zaune tana ta tunanin yanayin gidan su Malik sai kuma ta fara dariya taji wayan ta na ringing, ta tashi daga kan gadon da take ta je ta dauki wayan da ke gaba mirror ganin Niswa ne yasa ta yi receiving call ɗin, bayan sun gaisa tace "Niswa amma lafiya? Naji muryan ki wani irin kamar me shirin kuka" Niswa tace "Mummy Farouq zai kara aure, Maman sa ce tace dole yayi yanzu haka har an sayar da ranan bikin" ta karasa maganar in breaking heart ta fashe da kuka Mummy tayi shiru dan bata taɓa ɗauka abun har ya kai haka ba tace "Kika ce aure zai yi yanzu?" Niswa na sheshsheka tace "Mummy da farko na ɗauka abun ba zai dame Ni ba, amma sai da naga har an tsaida rana, shima baya so amma tace sai bayan ranta ne kawai ba za'ayi auren ba" Mummy ta fara salati ita gaba ɗaya she's just speechless ta'ina ma zata fara yanzu? A hankali tace "kiyi shiru nasan maganin ta, yanzu kar ki nuna komai da kanta zata janye dan uban ta" Niswa tace "Me zaki yi Mummy?" Tace "zan fadawa Malamin nan ne" Niswa tace "Bana so Mummy, wannan shirka ne, Shiyasa Allah yake barin mu da wayon mu, yanzu kin taɓa ganin Ammi ko yaran ta na shiga matsala? Saboda sun rike Allah ne" Mummy tace "Dan uban ki Ni zaki ce zaki wa wa'azi? Ina yanzu dan ke ne zan kai, kuma ai wannan ba boka bane balle ki ce shirka, da kike maganar Ammi kuma ita tun daga nijar ake mata aiki" a hankali Niswa tace "Ni gaskiya Mummy bana so, all what I know Layla ce ta cuce ni, gashi duk basu kallona da mutunci, Kanwar sa kam ko gaishe Ni bata yi, idan kuma na gaishe ta sai tace min 'ohh' kiji wulakanci fa" Mummy tayi shiru sai kuma tace "Ai kuwa Layla zata ci uban ta idan har aka miki kishiya, dan yanzu ta gama raina Ni bata kallona da mutunci balle kima, ranan ma ta zo yarinyar nan ko minti biyar bata yi ba ta koma dakin su Lina har dare sai da Rayyan ya zo daukan ta sannan zata min sallama" Niswa tace "Mama ki kyale ta kawai, Ni yanzu tsoro ma nake ji, wallahi ba rayuwar club da bata yi ba amma yanzu hankalin ta kwance" Mummy tace "shine zaki ce na kyale ta? Yadda aka miki haka ita ma za'a mata, ga Kanwar Fu'ad Husna, ai tana mugun son sa" Niswa bata kara cewa komai ba daga baya Mummy ta katse kiran. Malik na zaune gaban Abban sa, Abbah yace "Ina rokon ka Malik kada ka karɓi komai daga gare su hakan zai iya ja maka rashin kima da daraja a idanun su" Malik yayi murmushi yace " Abbah ka manta ɗanka Malik Areej ne? Sai dai ko ba ni ba, amma ba zan karɓa ba Abbah" Abbah yace "Tabbas na san ka Malik, kawai dai ina sake maka tuni ne" ya gyaɗa kai yace "Na sani Abbah" Abbah yace "Allah maka Albarka" yace "Amin Ya Abbah na" dukkan su da accent ɗin larabci su ke magana. Leena tun a hanya take jin wayan ta ke vibrating amma ta share akan idan ta koma gida zata kira back, tana ta sauri ta koma gida saboda ta san Malik na hanya, a hankali ta furta to ko dai ya iso ne?, Nawaf ya kwace hannun sa a nata yace "Amma I'm tired" ta tsaya kallon sa sai kuma ta duka tace "Idan ka sake cewa na barka zaka yi tafiya da kan ka sai na mare ka" ya tsaya yana mata dariya dan duk da be fahimci me take nufi ba amma ta basa dariya shagala tayi da kallon sa, dan babu abu daya da ya bari na Baban sa especially idan yana dariya, sai kuma tuna da Jiya ya kira ta, ta faɗa duniyar tunani tama manta a kan titi su ke kuma ta na duke a kasa, Nawaf ya kama hancin ta da sauri ta dawo daga duniyar tunanin tana kallon street ɗin dan tabbatar da babu wanda ya kalle ta, Nawaf ya fara dariya ganin yadda take kalle kalle tace "Oya hau baya na, let me back you" ya zaga ta bayan ta ya hau ta mike da shi a haka ta isa gida. Ammi dake zaune tana karanta wani lissafin ta ɗaga kai tana kallon su sai kuma ta fara dariya tace "yau kuma kece da goyo?" Leena ta zauna akan kujerar bayan ta sauke shi tace "Wallahi Ammi dan dole nayi, ai Ni na gama fita da shi" tace "sai da na ce miki ki barshi amma kika ce A'a" tace "Ai kuwa kin san sa da son mutane wallahi haka nan ya ɗaga wa 'yan gidan hankali, wai sai an dauke sa suka dinga biye masa" Ammi tace "Ma Shaa Allah, yau ɗaya amma har kin fara glowing kuwa" Leena ta mike tace "Allah Ammi da ba dan kin matsa ba bazan yi ba, Kinga yadda take jirja Ni kamar nace mata bana son jiki na" daga haka ta wuce dakin ta dan shirya wa kafin Malik ya karaso, tunawa da an kira ta a waya tayi, ta ciro wayan a cikin jakka tana duba wa, sake baki tayi ganin Sadeeq ne, ta zauna bakin gadon tayi tagumi, toh Meyasa yanzu ya fara kiran ta kuma? Tama manta da wani Malik yana hanya ta faɗa duniyar tunanin ta. Malik ya kalle ta yace "dagaske akwai abun da ke damun ki, kawai kinki faɗa min ne" tace "Babu komai fah, amma mayasa kace haka?" Yayi murmushi yace "tun jiya ina lura da ke Leena, gaba ɗaya kamar bake ba, sai dai kiyi shiru ki yi ta kallon wani wajan ko kuma ki dinga sounding min wani iri, Are you sure ba abinda ke damun ki?" Ta girgiza masa kai tace "I'm good, ba abin da yake damuna kuma banga abin da kake faɗan ba, dan nasan ban canza ba" Malik yayi murmushi yace "ko dai kina tunanin yadda zaki kasance a gida na, ba kalar rayuwar da kika tsaba ba? Ba cikin gatan ki ba?" Sai sannan ta masa wani kallo ta mike tace "idan har zaka cigaba da kallona a haka toh kar ka sake zuwa waje na" ya mike shima yace "Afwan, Habibty na" tace "Naji, kaje kiran da Daddy ya maka, barin wuce ciki" yace "Okay" daga haka ta wuce ciki, shi kuma ya ciro wayan sa a aljihun sa yayi dialing numbern Daddy yana fara ringing Daddy yayi picking, bayan ya gaishe sa yace "gani a compound Daddy" Daddy yace "Ah toh ka karaso mana" daga haka ya

Chapter 39 of 50