Farouq ya gagara making any move saboda mamakin hakan, ya duka ya ɗago ta a hankali ya shiga rarrashin ta ta kwace kanta tayi baya tana kallon sa tace "Seems you're happy?" yace "I can't hide, gaskiya ban so kiyi aure ba, but hakan ba yana nufin zan sake nude vids din ki ba, how can you imagine zan yi murna da auren ki, idan kika yi aure na san ba lalle ki sake kula Ni ba" ta tsaya kallon sa tace "Farouq!" yace "sure, na so auren ki but kika ce A'a a lokacin, daga karshe na hakura har muka jefa kan mu a wannan hali, but saboda kishi ba zai sa nayi wani abu da zai ɓata miki suna ba, believe me, please" Niswa tana jin zuciyar ta na kuna, shima zaman yayi yana tunanin who is it, Niswa ta dinga kuka shi kuma ya rasa me zai ce mata balle tayi shiru a haka har bacci ya ɗauke ta, ya canza jallabiyar jikin sa zuwa jamfa sannan ya feshe jikin sa ta turare ya rage ACn dakin ya rufe ta da duvet sannan ya fita zuwa sallahr Magrib da ake kira. Layla da ke wasa da Abubakar ta kalli Ammi tace "Wallahi Ammi, kawai tayi ta ce masa Abubakar? Haba mana" Leena dai murmushi tayi ba tare da ta sa baki a hiran su ba, Ammi tace "Toh ai kema naga Maman sa ne kawai sai ki sa masa suna" tayi shiru kamar me tunani sai kuma tace "Rayyan" Ammi tayi murmushi tace "Sannu Layla" Leena kam abun dariya ma ya bata ba ta san sanda ta fara dariya sosai ba Ammi tayi ta kallon ta haka ma Anty Binta dan rabon da tayi dariya sun manta, ta takaita dariyar tace "Ke ma kina haihuwa sai a sa Leena ko, ba Shikenan ba tun da abun son kai ne" Layla tayi shiru tana kallon ta sai kuma ta ɗauke kai tace "Shikenan, ana kiran da Nawaf kawai" Leena tace "Better",. Mummy da hankalin ta yayi mugun tashi ganin har pass 8pm kuma har sannan wayan Niswan a kashe yake ga barazanar da Daddy ya mata na barin gidan sa idan har bata dawo da Niswa gidan nan ba ace ta kwana a waje ai ta kaɗai, Rayyan har ya fara tausayin mahaifiyar ta sa ganin yadda hankalin ta ya tashi Nisreen sai kuka ta keyi a hankali yace "Mummy just pray, duk inda take In Shaa Allah za'a same ta beside da kanta fa ta bar gidan ba wai sace ta aka yi ba" tana kallon Rayyan ta share hawayen da ya gangaro mata tace "Dan Allah Rayyan kayi duk yadda ya dace kaji?" ya gyada mata kai yace "Toh ki daina damun kan ki, barin sanar da Layla kawai ta kwana ana" da sauri tace "Je ka kawai bari da kaina Zanje dakin su Leenan nace mata ta kwana" ya girgiza mata kai yace "Ba sai kin je ba" daga haka ya fita ya Ciro wayan sa yayi dialing numbern ta. kiran Rayyan ne ya shigo wayan ta, tayi receiving dama tun dazu take ta kiran sa dan ya zo su tafi yanzu cikin na ta da ɗan sauki, a hankali tace "Hello" sai kuma ta kalli Ammi da sauri tace "Bangane ba? Niswan guduwa tayi ko mene?" sai kuma ta fara salati ta kashe wayan, Anty Binta tace "Niswan guduwa tayi?" Layla tace "wallahi yarinyar bata da kunya dama tun asali, kawai dai baku fahimta bane, toh gashi yanzu wai ba ta gidan, tun ɗazu ake ta neman ta ba'a ganta ba" Ammi tace "Bangane ba?" Anty Binta tace "Ta gudu kenan?" Ammi ta kalli Binta tace "Kee, bana son shashan ci me hakan kuma" Antyn Binta ta taɓe baki Layla tace"Abinda Ya Rayyan ɗin ya faɗa min yanzu kenan wai tun dazu ba'a ganta ba" Ammi ta mike da sauri anty Binta tace "Ammi ina zuwa kuma?" bata tanka ta ba tayi hanyar kofa sai kuma taci karo da Hajiya da zata shigo. Hajiya Fatima ta shigo gidan a gigice, direct parlorn Mummy ta shiga tana kallon yadda kawar ta tayi wani iri ta karasa da sauri tace "Aminiyata, Bangane zancen baku ga Niswa ba?" Mummy ta share hawayen da ya gangaro mata na babu adadi tace "Ni yanzu damuwa ta ace barazanar mutuwar aure na da Daddyn su ya min ne yafi kona mun rai" tana kai wa nan ta fashe da kuka, Hajiya Fatima ta buga ashar tace "ke kika ɓatar da ita da har zai miki barazanar mutuwar auren ki? Lalle ma mutumin nan, toh a jin sa baki fi shi shiga damuwa bane?". Tun dazu yana zaune a dakin amma ya kasa yin wani abu sai ma ido da ya zuba mata yana kallon ta motsi ta fara sai kuma a hankali ta tashi a baccin da ta dinga sha, a hankali ta fara bin dakin da kallo tana haɗa ido da Farouq nan take memoryn ta ya dawo gare ta, ta mike tsaye toilet ta wuce ta wanke fuskan ta ta fito sai kuma ta tsaya kallon sa ganin kallon ta yake yi Camly yace "Baby, tell me waya sending message ɗin? sannan i need to know the background too, zan yi wani bincike ne and duk wanda ke da hannu he must reap what he sow" tana kallon sa tace "I can't recall the background, and kamar a nan ne Oho, and numbern sender din kuma ban sani ba dan a wayan Daddy ne" yayi shiru yana kallon waje daya, yace "kiyi Sallah, kici abinci zan mayar da ke gida it's already late" ta zauna tayi tagumi yana kallon ta cike da tausayi tace "I'm going no where" yayi murmushi kawai dan yasan yanzu dole za'a fara neman ta barin da yau take notice, yace "amma kin taba samun matsala da wani ko wata ne?" ta girgiza masa kai tace "Faɗa Kum.." Layla ta fado mata a rai ta kalle sa da sauri tace "Sure! Matar Yaya na bata so na" maganar da ta faɗa mata ne ɗa zu kafin ta fito ya faɗo mata tace "wallahi ita ce, dan ta cemin 'this is just the star, and it's a deal'" zai yi magana amma ina har tayi Hanyar kofa da zafin nama yayi sauri ya riko ta yace "Wait barin kai ki" tace "No, zan tafi da kaina, cos I must kill her, yau sai tasan da Ni take" daga har ta wuce duhun da ta gani a compound ne ya bata mamaki dan bata ɗauka dare yayi ba, ta tuna babu waya a hannun ta ta koma ciki ta wuce sa taje ta dauki wayar ta fito ba tare da ta sake kallon sa ba..
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
Wattpad © Jiddatulkhayr
Young talented writers association (YOTA)
Chapter 53
____Har wajan karfe goma Niswa bata gidan, zuwa sannan Mummy hankalin ta yayi mugun tashi, Hajiya Fatima sai calming ɗin ta down take yi, Rayyan sai bata positive thoughts yake yi dan ya kwantar mata da hankali, Ammi ce tayi sallama duk suka ɗaga kai suna kallon ta ta karasa cikin parlorn, bayan ta zauna tana kallon su a hankali tace "Ashe abin da ya faru kenan?" Hajiya Fatima ta gyaɗa mata kai tace "Wallahi fah" Ammi na kallon ta tace "Why not ayi tracking ɗin ta tunda ba za'a rasa cewa ta fita da wayar ta ba" Mummy ta share hawayen ta tace "Shegiyar ba ta kashe wayan ta ba, ni Niswa zata sa cikin matsala?" Ammi tace "Ki daina faɗin haka, ke uwa ce kawai ki bita da addu'a, sannan Allah ya dawo da ita gida cikin aminci" a hankali Mummy tace "Amin", Layla ce tayi sallama Rayyan na biye da ita a baya, har ta fara bacci Mama ta kira ta a waya akan itama tana cikin gidan shine ta fito sai kuma ta haɗu da Rayyan a compound ɗin, Mummy ta dinga kallon su har suka karasa cikin parlorn, Layla ta zauna gefen Mama tana mata ya hanya, Mummy na kallon Rayyan tace "Baba na har sannan babu wani abu da aka samu wanda zai nuna inda take ko?" Ya sauke ajiyan zuciya yace "Mummy har yanzu suna aiki ne akai, sannan duk inda take za su sanar da mu, in shaa Allah" ta mike ita bata so zuwan sa gida yanzu ba, yana kallon Layla yace "ɗa zu na shigo miki da maganin ki, hope abdominal pain ɗin da sauki" kai kawai ta gyaɗa masa tana gyara kwanciyar ta a jikin Mama, daga haka Rayyan ya wuce ɗakin sa, Mummy tace "Layla toh kin ci abinci ne?" tace "Eh naci a ɗakin Ammi, sai dai ina son na sha tea" daga haka ta mike ta wuce dinning, Ammi dai tayi shiru tana tunani, kamar daga sama sai ga Niswa, kamar wadda aka jefo ta haka ta faɗo musu, duk suka mike tsaye suna kallon ta da mamaki, bata ma gama kula da mutanen dake parlorn ba duk hankalin ta ya koma kan Layla da ke dinning tana shan tea, Mummy ta furta "Niswa" Layla ta ɗaga kai da sauri jin an ambaci sunan Niswa, ta mike a dinning ɗin ta fara tafiya zuwa cikin parlorn rike da cup din tea a hannun ta, da gudu Niswa tayi kanta, ba shiri kawai Layla taji an yar da ita kasa, da sauri Niswa ta hau cikin ta ta fara kai mata duka ta ko ina, dake ta je mata ba zata shiyasa ta samu nasarar kada ta, Mummy ta yi kan su da gudu tana cewa "Niswa kina lafiya kuwa?" tana kokarin jan Niswan, Niswa tace "Ni zaki sa a fasa aure na? Wallahi naki auren ma sai ya mutu wlh" Hajiya Fatima ta karasa wajan ba shiri ta sauke wa Niswa mari amma gani tayi kamar ta kara mata energy ne hakan yasa ta tsala ihuuu wanda hakan yasa ba shiri Rayyan da Nisreen fitowa a ɗakin su da gudu, Ammi tana kokarin jan Niswan ganin zata ma Layla illa, da gudu Rayyan ya karasa wajan ba shiri da kafa ya buga Niswa kamar kwallon wanda hakan yasa ta tsinci kanta a gefe, Ammi ta ɗaga Layla, Layla ta kwace kanta a hannun Ammi mug cup ɗin hannun ta daya faɗi gefe ta ɗauka ta buga mata kai, ta sake kai mata wani dukan akai wanda hakan yasa Niswa sake fadi kasa, Mama kam ta kasa magana, ganin haka yasa Mummy tace "Toh Rayyan ba zaka raba su bane" wani kallo Layla tama Mummy tace "lokacin da ta kada ni kasa kinyi Magana ne?" ganin haka yasa Niswa mikewa ta dauki flower vase zata sake kwaɗa mata, Rayyan ya buga hannun ta ya da karfi hakan yasa vase ɗin ya faɗi "Are you mad??" Layla ta ji wani jiri yana shirin dibar ta tayi baya zata fadi Ammi ta riko ta da sauri sai ga jini ya ɓalle mata yana bin kafar ta, Ammi tace "Innalillahi, Rayyan ka duba matar ka" Hajiya Fatima ta tsaya with shock tana kallon ƴar nata, hakan yasa Rayyan ya juya zuwa gun Niswa ya zare belt ɗin sa ya fara dukan ta kamar wadda aka aiko sa, Mummy tace "Rayyan" ya ɗaga mata hannu yace "Enough!!!" sai da ta tsorata, Ammi ta ajiye ta ta karasa har inda Rayyan yake ta rike sa tace "Rayya ka fara duba condition ɗin matar ka, ka zo mu kaita asibiti, kar ta zubar da jini sosai" sai sannan ya sake ta ya ja baya ko kallon Mummy be yi ba, Hajiya Fatima ta karasa wajan tana kallon Ammi tace "a haka za'a kai ta? does it feel like a miscarriage?" Rayyan ya karasa wajan, ya sa hannu ya daga ta cak, dakin sa ya wuce da ita, tsabar yadda Layla ta sha wahala kuma abun kamar a mafarki yasa ko hawaye be ɗigo daga idanun ta ba, sai daya gama gyara mata jiki sannan ya fito ya wuce dakin su Niswa bude wardrobe ɗin ta yayi ya ɗauki wani Abayan ta ya fito ya wuce ɗakin sa, bayan ya gama shirya ta ya fito rike da ita, Mama ta bi bayan sa da sauri, Ammi itama fitan tayi duk jikin ta yayi sanyi sai yanzu ta fahimci dalilin da yasa Layla zama a dakin ta duk lokacin da ta zo gidan, bayan ta shiga ta samu har su Leena sun yi bacci dan haka ta wuce dakin ta tayi wa Ayaan addu'a ta fito sanye da Hijab ɗin ta ta wuce sashin Daddy, sai data tsorata ganin yanayin da yake ci, ta yaye bargon jikin sa tana kallon sa tace "Me yasa baka yi magana an kai ka asibiti ba? Kalli yadda kake fama da fever" da sauri ta ɗauki wayan sa tayi dialing numbern Rayyan yace "wa zaki kira?" tace "Rayyan mana, dama asibiti zai kai matar sa yanzu sai ya haɗa da kai" yana kallon ta yace "Me yasa mi matar na sa?" tace "Wallahi yanzu fah Niswa ta dawo gidan nan Shikenan sai ta kama Layla da faɗa har Layla ta fara bleeding" sai kuma tayi realizing me take cewa da sauri ta rufe bakin ta tana kallon sa, zata ɗauki wayar na sa yayi sauri ya karɓa yace "No, need! Zan kira doctor na da safe" ta tsaya kallon sa sai dai bata ce komai. Rayyan gudu kawai yake yi, dan yana jin bai taɓa jin ɓacin rai irin na wannan lokacin ba, yana addu'an kar Allah yasa ya hadu da Niswa har sai sanda ranshi yayi sanyi dan yana ganin zai iya karya ta a yadda yake ji. Bayan gari ya waye, dake ana hutun school shiyasa Ammi bata ɗaga Ayaan a bacci ba kawai ta wuce ta ɗaura breakfast, Anty Binta ta fito tana kallon ta tace "Ammi yau kuma lafiya kike girki da sassafe? tace "Asibiti zan bada akai ma Layla" tace "wata Laylan kuma?" Ammi ta faɗa mata abun da ya faru, Anty Binta tace "Amma anya Niswan nan bata shan wani abu?" Ammi tace "ki mata fatan sauki mana" Anty Binta ta taɓe baki ta karɓi girkin a hannun Ammi, ita kuma ta wuce ɗakin Leena dan ma Nawaf wanka. Da sallama ta shiga parlorn Daddy ta samu Hajiya na gefen sa tana masifan kar a kashe mata ɗanta da bakin ciki, Ammi ta ajiye tray da ta jera masa breakfast ɗin a akai sannan ta gaishe da Hajiya, Hajiya ta amsa tace "Ashe abun da ya faru jiya da daddare kenan?" Ammi tayi murmushi kawai ta duka ta fara hada ma Daddy tea, ta ɗan kalli hannun sa dake makale da drip din sai kuma ta mayar da kallon ta kansa tace "Ya jikin?" yace "Alhamdulillah" tace "zan iya zuwa na duba jikin Laylan?" yace "Why not mana, ai yana da kyau ace anje" Hajiya tace "Daɗin abun sakanin su ne, suje can za su karata". Ammi ta mike tace "ba zan daɗe ba, ko kana bukatar abu?" yace "No" daga haka ta fita. Hajiya Fatima tun da abun nan ya faru sai daga baya abun yayi mugun tsaya mata a rai, taji haushin kan ta da bata dauki wani kwakkwaran mata ki ba, sai tsaki take ta ja sannan tayi madallah da fasa auren Niswa da aka yi dan tana ta mamaki har gari ya waye Mummy bata kira ta ba. Mummy ta fito a ɗakin ta bayan mai aiki ta gama shirya musu breakfast ɗin a dinning, tana tsaye tace da mai aikin ta kira mata su, ba'a ɗau lokaci ba sai gasu sun fito Niswa na tsanye da Hijab, bayan sun karasa dinning ɗin suka gaishe ta Niswa har sannan idon ta na kasa, Mummy tace "ya naga idon ki a kumbure?" Nisreen tace "Ai bata yi bacci ba ne, kuka ta dinga yi da daddare" Mummy ta fara serving kanta ba tare da tace komai ba sai kuma can ta ɗaga kai tana kallon Niswa tace "yanzu tunda ba kukan kike ba kiyi min bayani yadda zan gane" Niswa ta kalle ta sai kuma ta sauke idon ta kasa tace "Eh, dama tun lokacin da muka samu sa'insa tayi alkawarin sai ta sani kuka, and jiya ta shigo nan da yamma tace mun 'dama nace miki it's a deal, and it's just that start' tayi dariya sai kuma ta fita" Mummy tayi ta kallon ta tace "Me yasa baki sanar da Ni ba tun farko?" Niswa tace "Ai ba ɗauka abun zai yi tasiri bane kuma duk lokacin da na fara magana akan ta sai kiyi ta jin haushi kina ganin kamar bana kyautawa ko dan bana son ta ne" Mummy tayi shiru daga haka ta miƙe ta wuce ɗakin ta tana mai kara jin tsanar ta har ranta. Ammi ba karamin tausayin Layla taji ba, Layla ta kifa kanta a jikin Ammi dake zaune akan gadon da akayi admitting ɗin ta, Ammi tace "Toh me na kukan Layla? So kike kan ki yayi ciwo ko ki jama kan ki wani ciwon na daban?" ta girgiza ma Ammi kai, Mama dake gefe tana kallon su tace "Dan Allah Maman Lina ki mata magana kila taji na ki, tun dazu banda kuka ba abinda take yi" Ammi ta kalli Layla dake jikin ta tace "Toh Layla ya zamu yi? Allah bai ƙaddara cikin zai rayuwa ba, Allah yasa mai ceto ne ya baki masu Albarka" A hankali tace "Amin", Bayan Ammi ta tafi, Mama na kallon Layla tace "Amma ke Layla Meyasa kika yi hakan?" Ayrah da bata daɗe da zuwa ba ta kalli Mama da sauri tace "Whatsoever hakan bai bata damar daga hannu ta taɓa Yaya ba, ai yanzu a matsayin Yayan ta take, wallahi naji na tsane Niswan nan" Mama tayi shiru tana kallon su Layla tace "Toh karya na mata? ko ba ita bace a videon? kuma wallahi har sannan ko nadama banyi ba kuma bani da ranan nadama, kuma sai ta san ni ta zubar wa ciki" Mama tace "Yanzu haka ina tara Uwar ta ne, ace tun jiya abu ya faru, babu ita balle ta kira ko waya? sai kishiyar ta ne zata nuna damuwa? " Layla ta taɓe baki "Ai wallahi Ammi na da kirki sosai, wallahi Mama kun cuci rayuwar Matan nan, kuji tsoron ranan da Allah zai saka mata" har sannan tana kan gadon amma bakin ta bai yi shiru ba, Ayrah tace "Toh yanzu ya zaki yi idan suka faɗa wa Daddyn su da Rayyan ɗin ke kika sa aka fasa auren ta fah?" Layla tayi wani murmushi tace"Wallahi fata na kenan, babu abun da zan mance from A to Z ban faɗa ba, sannan kuma ita Niswan sharri na mata? ai ba sharri bane, kawai na ramawa Leena ne, auren ta na farko an fasa, na biyun ma sun kashe mata aure sannan sun cire ta a ran mijin, kee komai fa faɗa zan yi dan baki na ba sakata" Mama ta dinga kallon Layla ta mamaki dan ita bata ɗauka har Laylan ta san hakan ba. Ammi dake gefen da Hajiya sai Brothern sa Usmanu, yanzu jikin nasa da ɗan sauki, Daddy yace "Eh kayi gaskiya, dama nima yadda nayi ta ji ne jiyan yasa na kasa magana amma zuwa anjima da yamma idan na sake warware wa zan tara dukka gidan sannan na faɗi hukunci da na yanke" Usmanu yace "ai gwara hakan, yaran yanzun ne wallahi sai a hankali, musamman ba'a sa musu ido sai kaga sun sauya hali" Hajiya tace "Toh ba dole ba Uwar ma tarbiyya bai ishe ta ba balle a kai ga maganar 'ya'ya". Layla dake makale da Rayyan sai shagwaba take zuba masa ita bata taɓa zaton zai iya ɗaga hankalin sa har haka a kan ta ba sai Jiya, kuma taga yadda hankalin sa yayi mugun tashi da aka kasa saving ciki shikenan kuma ta fara masa shagwaba, shi kuma ya ɗauka duk a cikin pain ne sai fama rarrashin da bata hakuri yake yi. Bayan duk sun hadu a babban parlorn Daddy, Daddy dake rike da Nawaf amma yana jingine da kansa yana jin duk abinda kawu Usmanu ke faɗa, bayan ya gama ne Daddy ya gyara zaman sa with serious face ya fara magana yace "Niswa" Niswa dake rakuɓe a gefe sai da gaban ta ya faɗi da wannan kiran da ya mata, ta ɗaga kai ta ɗan kalle sa amma ta kasa amsa masa ya ci-gaba "we're all here because of you, zaki ba Yayan ku duk bayan nan mutumin nan" ya maida kallon sa ga Rayyan yace "kai kuma za muyi magana anjima" Rayyan ya gyaɗa masa kai ya ci-gaba "Daga ke har Nisreen babu wacca zata karamin 2weeks a gida" da sauri Nisreen ta ɗaga kai ta kalle sa amma ganin face da Daddy ya saka yasa ta kasa magana haka ma Mummy da har zata yi magana amma sai taji shakkar sa, yace "Babu wata yarinyar da zata cigaba da zama min a gida, balle kuyi ta rashin tarbiyya har Allah ya kama ni da laifin nan, tunda har Uwar ku bata san saka ido akan yara ba, imagine wai yau zan iya samun a cikin 'Ya'ya wacca zata aikata hakan?" ya tsaya da maganar yana Salati, Hajiya ta kalle sa tace "toh me kuma zaka yi da shi mutumin da har zaka bukaci Sanin abu game da shi" Daddy ya kalle ta yace "Saboda shi zai aure ta, dole nema ya aure ta ko suna son juna ko basu son juna a haka za'a yi auren, tunda suka iya zama babu aure tare dole da aure ma su zauna tare" Niswa ta daga kai tana ta kallon Daddy dake ma Hajiya bayani ganin zai juyo ta sauke kanta kasa hawaye suka fara tsintiri a kuncin ta, bata san specific me yasa ta kukan ba amma ta tsinci kanta da jin haushin kan ta. Bayan Mummy da yaranta sun koma part ɗinsu, Niswa banda kuka ba abinda take yi, a parlor suka ga Layla na kwance inda Rayyan ya ajiye ta, har sannan magana bai shiga tsakanin Mummy da Rayyan ɗin balle Layla, Mummy ta tsaya kallon ta sai kuma ta kalli Rayyan dake bayan ta yana ce mata ta taso taje bangaren Ammi ta huta, Mummy tace "Dole Daddyn ku ya dauki mataki, wallahi ba zan laminci wannan lamarin ba, dole sai ka rabu da ita ko kuma ka kara aure, dama ina jira ya samu nutsuwa na sanar masa so anjima zan fayyace masa komai" Layla ta kama hannun Rayyan, da gangan tayi kamar zata faɗi Rayyan da sauri ya taro ta jikin sa, Layla na kallon kwayar idon Mummy tace "Wait.. wai ko kin manta cewa koya nayi nima?" Rayyan ya mata tsawa ta fashe da kuka, hakan yasa yana rike da ita su ka fita zuwa side ɗin Ammi. Mummy ta zama kamar statue a wajan tana mamakin Layla, wani abu ne ya tokare ta a throat ɗin ta, bata san sanda ta fara kuka ba kawai tsintar kanta tayi hawaye na bin kuncin ta.
Jiddatul-khayr
08110615256
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
Wattpad © Jiddatulkhayr
Young talented writers association (YOTA)
Chapter 54
_____Rayyan dake kwance a ɗakin sa har sannan ya kasa bacci, duk abubuwan da suka faru has been vividly flashing in his mind, ya runtse idon sa, he still can't believe, haushin Niswa da yake ji is growing stronger now, wayan sa dake ringing ne yasa ya mike ya ɗauka, ganin mai kiran yasa ba tare da ɓata lokaci ba yayi receiving, daga ɗayan ɓangaren yace "Sir, Everything is done, iyayen nasa ma anan kaduna suke, suna Millennium city! So, I left everything in the barrister's hands" Rayyan ya gyaɗa kai cike da fahimta sai kuma ya sauke ajiyan zuciya yace "Okay! It's a great job, thank you, but please kar ka kira Daddy da safe zan sanar masa da komai, cos yanzu yana bukatar hutu" yace "In Shaa Allah, sir" daga haka ya katse kiran ya jima zaune yana tunanin Layla daga karshe ya mike.
Nisreen yanzu har kukan da Niswa take yi ya fara bata haushi, gashi ta hana ta bacci,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 34 Chapter of 50