Sadeeq na gaba Sultan na baya suka shiga parlorn, Kallo ɗaya Sadeeq ya musu ya wuce dakin sa Sultan ya bisa da kallo haka Leena ma dan wannan ba halin sa bane tun da sukayi aure, bata ɗauke ido ba har ya shiga dakin sai sannan ta mayar da kallon ta kan Sultan tace "Sannun ku da zuwa, ina wuni" gaba ɗaya abinda Sadeeq yayi bai masa dadi ba ya ɗauke kansa yace "Lafiya Leena, ya jikin kuma?" tace "Alhamdulillah" kallon ta yake yi ganin hankalin ta baya kansa sai satan kofar dakin Sadeeq take yi da ido yasa ya mike yace "Leena I think zan wuce" Farida ma ta da ji wani iri ganin yadda Leena tayi ta rawan kafa dan zai zo harda su lalle da kitso duk da cikin ta ya tsufa a haka ta juri zaman, ta mike tana kallon Yayan nata tace "Ya Sultan bari kawai na bi ka sai kayi dropping ɗina gidan Mami" yace"dan kin ganni sai kuma kice zaki tafi? Kuma naga ko sallama da Sadeeq baku yi ba" tace "I know, yanzu zan masa sallama, dama kuma ina da niyyar tafiya ai saboda jibi zan koma Abuja, saboda screening din my" yace "Alright, ki gama sai ki same ni a mota" daga haka yama Leena sallama tace ya gaida Anty Jidda. Bayan Farida ta fito da akwatin ta Leena ta shiga dakin ta ta ɗauki siyayyan da tayi mata, da kyar ta karba, ta tsaya kofar dakin Sadeeq tace "Ya Sadeeq, I'm going" ya fito fuskar nan ta sa a tamke yake tace "Dama zan tafi ne" yace "I have your acc details zaki ji sako na" tayi godiya sannan ta karasa parlorn Leena na faking murmushi ta raka ta har bakin motar Sultan. Bayan ta dawo ta buɗe dakin Sadeeq ta shiga baya dakin amma tana jin alamar karan ruwa a toilet hakan yasa ta fahimci yana toilet din, ta zauna bakin gado tana jiran fitowar sa, tunda Sadeeq ya fito daga toilet kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa yana tsane ruwan kansa da dan karamin towel ya karasa jikin mirror, har sannan Leena na binsa da idanu Allah ya gani ɗaurewa kawai take yi dan ji tayi kamar zata yi kuka idan ma wani abun tayi masa ai sai ya faɗa mata amma sai ya share ta, ta mike ta fara tafiya inda yake da murmushi shinfiɗe a fuskar ta tace "Welcome back home, honey" wani kallo ya watsa mata yace "Excuse me, I want to wear my clothes" Leena ta sake baki tana kallon sa expression dinta ya koma shock tsawan da ya daka mata ne yasa da sauri ta juya ta fita, hawaye ya fara sauka a fuskan ta, dakyar ta wuce dakin ta ta zauna tana share hawayen da yaki tsaya mata. Layla ta fito rike da plate ɗin abinci a hannun ta kallon Rayyan dake aiki a system ɗin sa tayi har zata wuce shi sai kuma ta dawo parlorn ta tsaya a gaban sa tace "Amma ai kaji abinda Mummy tace ai" be tanka ta ba yi yayi kamar be sanda wata a wajan ba ta kuma cewa "Wai wannan wani irin wulakanci ne? Wallahi na gaji da halayyan ka Rayyan, na gaji" daga haka ta fashe da kuka ta zauna kasan carpet sai sannan Rayyan ya ture system ɗin da ke gefen sa, harga Allah halayyan ta ne baya so, dan ya san pure love take masa, yace "ke ko da yaushe kuka?" tana sheshsheka tace "Ko sau daya baka taɓa ɗauka na a matsayin matar ka ba, kullum kallon waccan aka cusa maka ita kake min" yace "Layla" ta lalle sa yace "Ba ke bace bana so, halaiyan ki ne bana so, duk abinda na hanaki bakya bari, ko sau nawa zan hana ki fita toh sai kin fita sallah kuma sai nayi da gaske kike tashi kiyi, a haka ne kike so na so ki?" ta ɗauke kanta dan shi kullum ana fara magana sai ya kawo wannan zancen, ita kawai zata tsanar da Mummy halin da take ciki ne, duk yadda Rayyan yayi ta mata magana haka nan ta share sa daga karshe ma barin wajan tayi. Gaba daya haka Leena ta wuni bata da wani walwala, dan tun dazu Sadeeq ko leko ta be yi ba, balle ya san ya take ko ɗan da ke cikin ta, ta kyar ta mike ta daura alwala tazo ta gabatar da Isha'i, jin ba zata iya jure wannan sabon yanayin nasa ba ne yasa ta wuce dakin sa ko knocking bata yi ba ta buɗe ta same sa yana kwance kan gado yana kallon wani wajan Leena ta karasa har gaban sa zata durkusa nan kasa yayi saurin mikewa yace "daka ta" ta tsaya kallon sa ta buɗe baki za tayi magana yace mata "Out!" ta girgiza masa kai tace "i can't" ya sake mata wani tsawan a karo na biyu yace "I said out!" Wannan karan Leena ta gama taorata da lamarin sa dan wannan ba Sadeeq dinta bane tace "At least ka saurare ni mana Uncle" a harzike ya mike ya daka mata tsawa yace "har zan baki doka zaki tsaya min akai ki kiyi?" tace "But.." to her surprise ko bari ta karasa maganar be bari tayi ba ya sauke mata wani lafiyayyar mari a fuska, Leena ta dinga kallon sa ya kuma daga hannu zai mare ta ta ja baya tana kallon sa hawaye na tsintiri a fuskan ta, ta fita dakyar take iya ɗaga kafa. yunwan da take ji ne ya farkar da ita daga bacci daya fara ɗaukan ta kallon agogon tayi taga ashe ma dare baiyi ba dan 11pm ne ma ta sauka daga kan gadon a hankali da kyar take iya tafiya sabar yadda kafafun ta suka kumbura, tana fita a dakin ta ta gansa kwance kan resting chair ta ɗauke kanta ta ta karasa dinning buɗe kulolin wajen tayi taga ko taɓa abinci da ta kashe kanta wajan yi be yi ba, hawaye taji sun fara zuba a fuskan ta ta sa hannu ta share ta debi wanda zata iya ci sauran kuma ta sa a fridge, bayan ta fito a kitchen wannan karan baya parlorn jiki a sanyaye ta wuce dakin ta, wannan daren haka Leena ta yi shi ba tare da ta rintsa ba, dan bacci ma yaki ɗaukan ta, tana ta forcing kanta dan bata son tunani tunanin da take yi saboda tasan illar hakan. Bayan ta idar da sallar asuba tayi morning azkar ɗinta ta mike ta wuce kitchen ta fara hada masa breakfast bata dau lokaci ba ta kammala ta jera a dinning, ganin ya fito ya sa ta karasa cikin parlor ta duka tace "Good morning" Sadeeq dake gyaran neck tie ɗinsa ya daga kai yana kallon ta dan shi bai san tana wajan ba ma, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai, Leena ta tace "Dan Allah idan da wani abun da na maka ka fada min amma ka tausaya wa condition dina" ko kallon ta be yi ba ya dauki briefcase dinsa Leena tace "Toh ko da ba zaka min magana ba ga breakfast din ka is ready" haka ya fita ba tare da ya ko kalle ta ba. Leena tana tsaye a wajan kamar wata gunki, ta fashe da kuka ta zauna nan kasa sai da tayi mai isar ta sannan ta mike, ita yanzu ba abin ta faɗa wa Ammi bane hankalin ta ya tashi. tana cikin bacci taji an buga kofar da karfi ta farka a ɗan raza ne ta mike zaune tana kallon sa strictly yace "sakwara zaki girka min" Leena tace "toh" daga haka ta sauka akan gadon shi kuma ya wuce ya fita bayan ta shiga kitchen ganin garin ya kare yasa ta fito ta same sa a parlorn yana kallon Tv ta karasa har gaban sa ta duka tace "Babu garin fa ya kare" a takaice yace "sai kuma a gidan babu doya ko?" ta dinga kallon sa dan ita bata jin zata iya girka shi idan ba garin bane wani kallo da yake mata yasa ta mike ta wuce kitchen ɗin zata iya rantse wa wannan ba Sadeeq dinta bane, dan abinda zai sa ta wahala akai duk ya hanata ta girki ma da kyar ya yarda take dafa indomie, sai data bata lokaci tana girki, bayan ta fito ta ajiye a kulolin a dinning, sai gashi ya bude kofar parlorn ya shiga ya bari a bude tana kallon sa tace "Na gama" tsawa ya mata yace "Sai yanzu? Ke wacca irin mahaukaciya ce?" Sultan dake biye da shi a baya ya tsaya speechless baki a bude yana kallon Sadeeq, a ɗan harsige yace "Sadeeq are you alright?" Sadeeq yaja tsaki ya wuce daki, Sultan ya dinga kallon Leena data sunkuyar da kanta.
Please hint the star at the corner.
*AGOLA (Behind the palace walls)* 🫧
*HAUWA JIBRIN SULAIMAN*
*Jiddatul-khayr*✍🏼
*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION*
*Chapter 40*
Jiddah tace "ina jin ka dear" Sultan yayi shiru yana kallon waje daya Jiddah ta kura masa ido, ya gyara zaman sa yace "Jiddah, bana tunanin Leena tana jin dadin auren ta" Jiddah ta masa wani kallon tace "bangane ba?" yace "Ranan da nayi dropping Sadeeq a gidan sa Leena ta fito da niyyan tarban sa but unfortunately Sadeeq ko kallon ta be yi ba ya wuce ciki, and can you imagine Jiya a gaba na yake mata ihu kuma yake kiran ta da jahila" Jiddah ta sake baki tana kallon sa sai kuma ta girgiza kai tace "bana tunanin Ya Sadeeq zai aikata haka" Sultan yace "ya zanna faɗa miki abinda idanuwa na suka gane min kice A'a" tayi shiru amma still kana kallonta kasan she was totally confused yace "Please zaki je gidan, ki sa ido dan lura da halin da take ciki, inma ya kama You can even ask her, ko dan condition dinta" Jiddah ta gyada masa kai, duk sai take ji ba lafiya ba hakanan. Zuwa yanzu Leena ta gama tsare wa da lamarin Sadeeq har bata son haduwa da shi, ita yanzu damuwar ta ma idan labour ya kamata cikin dare ya zata yi gashi bata son ɗagawa Ammi hankali. Jiddah ta shiga parlorn su da sallama Mami dake zaune tana cika wani files na wajan aiki ta daga kai tana kallon ta har ta karasa cikin parlorn bayan sun gaisa, can Mami ta daga idon ta akan system ɗin gaban ta tana kallon Jiddah tace "An samu waccan za'a kaiwa Leena?" Jiddah tace "A'a ai waɗannan kin ce sunyi yara sai dai dattijiwa" Mami tace "Sure, na fi son Dattijiwa saboda abubuwa da yawa" Jiddah tace "zan kara mata magana muji me ake ciki" Mami tace "Toh shikenan, Nima nayi kwana biyu ban leka Leenan ba wallahi" Jiddah tace "Nima zan je can na duba ta anjima" daga haka ta bar Mami anan parlorn ta wuce dakin ta bata dade ba ta fito tace "Mami barin tafi" Mami tace "Dama ba wuni kika zo min ba?" Jiddah tayi dariya tace "zan dawo gobe, yanzun ma gidan Ya Sadeeq zani na biyo nan" bata kai ga karasa rufe baki ba sai ga Sadeeq ya shigo parlorn da sallama, ya gaida Mami ciki ciki ko amsa gaisuwar Jiddah be yi ba ya wuce sama, Leena ta bisa da kallo. Knocking da Jiddah ta dinga yi yasa Leena farkawa a bacci, da kyar ta mike ta fita compound ɗin, bayan ta buɗe taga ashe Jiddah ne, ta kirkiri murmushi ta masa mata baya ta shiga, bayan sun shiga parlorn suka gaisa Leena ta mike tace "barin kawo miki ruwa" Jiddah tace "No, daga gidan Mami nake yanzu ma zan koma gida" Leena ta wuce tace "Eh, duk da haka" daga haka ta wuce kitchen ta dauko mata ruwa, Jiddah sai kallon ta take yi ganin yadda Leena ta koma wani iri ba walwala tattare da ita, Jiddah tace "Leena" Leena ta kalle ta Jiddah ta koma kusa da ita tace "Meke damun ki, Please? Leena ta girgiza kai tana murmushi tace "Bakomai fah" Jiddah ta girgiza kai ta e "kar mu fara haka dake, wallahi akwai Leena, i can see, toh me amfanin boyewar?" Leena da har hawaye ya fara cika idon ta tana kokarin mayar da shi baya tace "Babu fah" Jiddah ta zuba mata ido tace "ki daina kallon na a matsayin kanwar Ya Sadeeq, ki kalle ni a matsayin Aunt ɗin ki na da" Leena bata san sanda ta fashe da kuka ba Jiddah ta barta tayi me isar ta sannan tayi shiru duk yadda Jiddah taso Leena ta fada mata haka nan taki cewa komai daga karshe ta hakura a haka ta koma gida bayan Sultan ya zo ya ɗauke ta. Mami ta fito daga dakin ta around 8pm taga har sannan Sadeeq na gidan tace "kai Malama Ko ka manta kana da iyali ne zaka tare min a gida tun ɗazu" a takaice yace "Na sani" Mami tace "Amma kasan awannan stage ɗin ne ba'a son ana barin ta ita kadai?" Sadeeq bai tanka mata ba ya wuce dinning Mami tace "toh Karka sake kara min ko minti biyu ne a gida" daga haka ta wuce dakin ta, Sadeeq ji yayi ya tsane ta with passion ko hada roof daya da ita baya so. Mami tayi shiru tafi minti biyu a haka, har sai da Jiddah ta ciri wayan a kunnen ta, ta ɗauka wayan ya yanke ne, ganin yana reading yasa ta fahimci bata kashe ba, Jiddah tace "Mami" Mami tace "Uhm, wato shi yasa ya wuni min a gida? Ni zai zuba wa kasa a ido daga basa yarinya sai ya fara wulakanta ta, Har ya isa?" Jiddah tace "kawai ki sa masa ido zaki gani da kan ki ma" daga haka sukayi sallama. Rayyan da ke kwance kan 3 seater gaba ɗaya yaji duniyar ma ta masa zafi shi sai yanzu ne ma yake kara tsanar Layla kuma yake jin haushin abinda mahaifiyar sa ta masa, tun karfe 8pm ya dawo gida amma yanzu wajan 12am ne bata gida, dan bata ma san ya dawo ba, wato ma siyasa ta kira sa da yake a asibiti zai kwana shiyasa tayi fitar ta, yana ta tunani iri da kala yaji alamar tana buɗe kofar parlorn bayan ta shiga cikin parlorn ta kunna wutan nan nan da nan haske ya garwaye parlorn kallon Rayyan da tayi kwance yasa ta tsaka ihu sai kuma ta toshe bakin ta da sauri jikin ta ya fara bari ta buɗi baki tace "ba.ba.. kace zaka.. kwa kwana a asibiti.. ba" Rayyan tun da ya mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa be sake bari yaga direction ɗin ta ba, da kyar ta iya ɗaurewa ta shiga dakin ta bata ma san ta ina zata fara ba, gashi wani ɗan iskan kaya ne a jikin ta balle tace daga unguwa take, zama tayi a bakin gado tana ta tunani iri da kala. Yau tunda safe Sadeeq ya bar gidan Leena tana fatan kar ya dawo gidan irin na jiya sai dare, bayan ta gama aikin ta ta koma parlorn ta fara rubutun ta dan kawai ta ɗaukewa kanta damuwar da take ciki, ringing ɗin da wayan ta ya fara ne yasa ta mike taje ta ɗauka ganin Zahra yasa ɗaga kiran, Zahra tace "ina kofar gidan ki" Leena ta kashe wayan ta fita dan shigowa da Zahran. Asma wani kallo take ma Layla tace "Ni wallahi ban san yaushe kika zama haka ba, kamar ba Laylan da na sani ba, har yaushe zaki bari namiji ya ke baki pressure?" Layla tayi shiru, Asma taja tsaki tace "ba dole ya raina ki ba, shakkar sa karara a fuskan ki, ai samun waje yayi, kin gama submitting masa kanki har ya fahimci kina mugun son sa" Layla ta numfashi tace "Ba zaki fahimce ni bane Amsa, Ni yanzu ya Zanyi wallahi tun jiya da daddare har yau da ya fita ko cikan ki be cemin ba, bana son wannan shirun nasa atleast ai ko faɗa ne ya min na samu salama" Asma tace "Kina da kayan takaici wallahi, toh sai kiyi ta zama a gida kamar me takaba? Iskanci ma guri ya samu" buɗe kofar da akayi yasa suka daga kai suna kallon sa, kamar ba Rayyan ba, har tsakiyan parlorn ya karasa yana kallon Asma with serious face yace "Look! Bana son sake ganin ko da shadow ɗin ki ne a gidan nan, Get out!" ta mike tsaye ta sake baki tana kallon sa za tayi magana Layla ta rike ta daga haka Rayyan ya wuce ciki, Asma ta ƙwace hannun ta a na Layla tace "So, dama haka kike zaune da wannan? Wallahi kinji kunya" she grabbed her bag Layla tace "Haba Asma" tana kallon cikin idon ta tayi wani murmushi tace "Baki ji me yace bane? Zan yi magana kuma kika hanani, so what exactly do you want me to do?" Layla tayi shiru so speechless, Asma tace "Kin gama down grading kan ki Layla, ban sa yaushe kika canza ba, Allah ya kiyaye namiji ya dinga controlling dina this way kuma na tsaya kallon sa" daga haka ta fita Layla ta zauna kan kujera tayi tagumi. Tun daya shiga street ɗinsu yake jin ɓacin ran shi yana tsanan ta, a daidai gate yayi parking motar dan baya jin zai iya shiga da motar ganin abu kawai zai dauka, bayan yayi parking ya sauka ya shiga cikin gidan, dakin sa ya wuce direct. Leena da ke kwance a dakin ta tun bayan tafiyan Zahra bata sake yarda ta fito ba, sai yunwan da ya kaɗa mata hankali yasa ta mike, har ta kama handle ɗin kofar zata buɗe taji shigowan Sadeeq yasa ta fasa budewa tana tsaye jikin kofar har taji shigan sa dakin sa. Ya dauki duk dakardun da zai yi amfani da su ya kai mota har zai tada mota sai ya tuna ya bar system ɗin akan gado kawai ya shiga gidan ba tare da ya kulle gate ba, jin fitar da sa yasa Leena fitowa ta wuce dinning area bata kai ga karasa zama ba sai gashi ya shiga parlorn, kallon ta da yayi ya sake jin wata tsanar ta har cikin ran shi, ya tamke fuska, kamar be san meye murmushi ba, Leena ta fara addu'a a ranta, ya karasa dinning Leena ta sauke kanta kasa yace "Who the hell are you da har zaki min amfani da cup ?" Leena ta kalli cup din da ke kan dinning ta san neman magana yake dan ita ba abinda ta taɓa, kai kawai ta girgiza masa hawaye har ya fara sintiri a fuskar ta, ya mata wani tsawan yace "Daga gidan ku ne kika zo da dinning ɗin?" jiki a tsanyaye ta sauka, mari ya kai mata yace "Ina Miki magana zaki min shiru?" Leena ta fashe da kuka tace "Dan Allah kai ba zaka tausaya min bane? Wannan wani irin rashin imaani ne?" wani marin zai sauke mata suka jiyo Ihuun Mami daga bayan su "Are you mad Sadeeq?" ta karasa dinning ɗin rai bace ta sauke masa wani wawan mari sai da ya dauki sekonni sannan ya daga jajayen idon sa ya zuba mata sake kai masa wani marin ta yi, ya rike kuncin sa kamar me raɗa yace "Mami! you just slapped me?" tace "So, you even have the gut of asking me, right?" yayi murmushi daga haka ya wuce ta fuu ya fita, Mami ta mayar da kallon ta gun Leena da har ta durgusa kasa, Mami mamakin Sadeeq ya cika ta, ta gagara yarda da abinda idanun ta suka nuna mata just now, wato da badan Allah yasa sun manta gate a buɗe ba ba lalle ta san me ke faruwa ba, ta karasa har inda Leena take durkushe ta ɗago ta tace "Daughter" har sannan hawaye na sauka idon ta Mami ta share mata hawayen tana rike da hannun ta suka koma parlorn, ita bata ma son ta tambaye ta Meya faru dan ita koma menene ai bai kamata ya daga hannu har ya dake ta ba, ai ko ba dan ita ba ko albarkacin cikin ta sai ya daga mata kafa. Bayan Mami ta zaunar da Leena tana kallon yadda ta lalace tace "Meyasa baki taɓa faɗa min ko Jiddah ba abinda Sadeeq ke miki kenan?" Leena na share hawayen daya ki tsaya mata tace "Mami a baya ba halin sa bane shiyasa" Mami tace "wuce ki dauko kayan ki, sai yasan darajar ki kafin ki dawo gidan nan" Leena bata so ba amma atleast tasan da wani abu ya taso ga Mami kusa. Mami dake zaune a dakin ta tana waya da Jiddah tace "Jiddah ba zan iya barin ta agidan ba, na dawo da ita gida na, ace matar ka tana da tsohon ciki har zaka iya daga hannu ka mare ta?" Jiddah tace "Hmm Nima da farko da Ya Sultan ya faɗa min Mami ban yarda ba, sai fah da naje naga yanayin ta tana cikin damuwa shi yasa ma na fara yarda duk da mun san ba halin sa bane" yadda Mami take boiling bata ma son tayi magana, da scene ɗin yayi flashing a idon ta sai taji duk duniya ba wanda ya taba mata munin abu kamar Sadeeq, tace "Ki kyale ni kawai Jiddah, ina son rest" daga haka ta katse kiran. Dakin da Jiddah take kafin ta yi aure nan Mami ta buɗe ta shiga ta na kallon Leena dake kwance tace "Daughter, zaki iya cin jallof ɗin ko a girka miki wani abun? Leena da damuwar duniya ya mata yawa tace "zan iya ci Mami" daga haka ta fita ta kulle mata kofa, ba'a dau lokaci ba sai gata ta kuma buɗe dakin har kan gado Mami ta kai mata abinci zata dauka Mami tace "No, yi zaman ki anan" Leena ta ja kulan ta buɗe ta fara zuba wanda zata ci a plate. Har ta gama ci Mami bata bar dakin ba, ta mika mata ruwa ta karba ta sha tana kallon Mami tace "Thank you, Mami" Mami ta kama hannun ta tana kallon ta tace "Daughter bana son ki boye mini komai, ina son sanin everything" nan take Leena ta ji hawaye har sun soma zuba a idon ta. Jiddah da take kallon Sultan tace "Wallahi ni fah Ya Sultan gani nake Ya Sadeeq ya fara shan wani abu dan ba haka nan ba" Sultan yace "Bana tunanin Sadeeq zai iya fara shan wani abu ko da kuwa anan gaba ne, cos I knw who is Sadeeq, ba abinda ya fi tsana ma sama da shaye-shaye shiyasa ko flavors bai yarda da su ba" Jiddah tace "But still it's not normal" yace "Sure! it's not, shiyasa nake so nayi magana da shi". Hajiya Fatima tace "Toh uban me kike so na miki yanzu?" Layla ta share hawayen ta tace "Mama ko fah kula ni yanzu ya daina" Hajiya Fatima tace "Toh ai shikenan, Allah kyauta" Layla ta dinga kallon ta tace "Mama na kawo miki damuwa ta kice haka?" ta mike tsaye ta dauki jakkan ta zata fita Hajiya Fatima tace "Dawo ki zauna Layla" wani kallo take ma mahaifiyar ta ta sannan ta zauna amma taki kallon direction ɗin ta, Hajiya Fatima tace "Ko da yaushe na Miki magana akan sa sai ki nuna baki so, amma ai ke ma kin san sai da muka je wajan malamai aka rufe bakin sa yadda ba zai ma mahaifiyar sa musu ba" Layla ta katse ta tace "Toh yanzu Mama meya kawo wannan maganar kuma?" tace "Wai na tuna Miki baya ne, naga kin manta ne, shiyasa da zaran zan fara magana sai ki ce baki so ana masa asiri, gashi yanzu kina kuka wiwiwi saboda asirin ya karye, duk da cewa baki sani ba bayan auren ma ina biyan malalmai suna cusa mi shi son ki" Layla tace "Toh yanzu me za'ayi?" tace "Hakuri zaki yi na wani lokaci kadan, aiki za'a fara har sai Rayyan ya rabu da kowa a kanki" Sai sannan Layla ta fara murmushi tace "wallahi, can't
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 50