ta amsa Leena na kallon cikin kwanon tace "Hajiya shine kika samu dambu yau kika manta da Ni?" Hajiya tace "ji jaraba, toh ba shi akayi yau a gidan bane" Leena ta girgiza kanta ta zauna kan kujera tace "tun yaushe Mummy ta hana Masu aiki kawo mana abinci ko zuwa side ɗin mu ai ta hana su, shine Ammi kawai ta fara yi mana tace dama haka take so saboda taste ɗin baya mata daɗi" Hajiya ta rike haɓa tace "wai dama tun wancan cass ɗin da Daddyn ku ya shiga dama bata bari sun ci-gaba ba?" Leena tace "Eh fah, shine Ammi tace wa Daddy ba komai kawai zata na yin nata daban" Hajiya tace "Toh dama me Ammin ki zata yi da abincin gidan nan da kamar har yanzu su ke koya, abincin kullum ba daɗi idan kin ga naci abinci nayi nak toh na uwarki ce" ta karasa maganar tana mika ma Leena warmern dambu Leena ta karɓa tana washe baki tace "sai nayi sallah zan ci" ta ajiye a gefe sai kuma tace "Hajiya dama na zo ne na faɗa Miki sati me zuwa saukan mu" Hajiya tace "kinci jarabawar kenan?" Leena ta gƴaɗa kai Hajiya ta rangaɗa buɗa tace "yanzu ƴar nan kin Haddace izu sittin a kai?" Leena reaction din Hajiya kaɗai abun dariya ne ta fara dariya tace "Eh mana Hajiya" Hajiya tace "Chap gaskiya ko nawa Muhammad ya bada sadaki be faɗi ba dan yayi dacen mace" ambata Muhammad da Hajiya tayi ya sa gaban Leena ya faɗi ita har ta manta da wani Muhammad sai yanzu ma take tuna kalan missed calls ɗinsa da take gani gashi bata kira sa back ba tayi tagumi tana tunanai Hajiya tace "ke kuma Lafiya?" sai Sannan Leena ta kalle ta jin anan kiran sallah ta tashi ta wuce ban ɗakin Hajiya dake ciki Hajiya ta fara masifa "Ai kin san na tsana ana shigan min ban ɗaki, ke ba wanke wa mutun kika iya ba sai dai ki ɓata ki bar mutun da gƴara" duk mitan Hajiya sai da Leena tayi kamar bata ji ta ba ta shige abinta. Bayan Ammi ta idar da Sallah taja wayan ta tana kallon numbern daya kira ta dialing back tayi ba'a ɗaga ba sai ga numbern ya sake kiran ta back immediately Ammi ta ɗaga ta kai kunne daga ɗayan bangaren aka ce "Assalamu alaikum, Ammin." Ammi jin haka yasa ta amsa tace "Sorry ka kira ina sallah ne, shiyasa ban ɗaga ba" yace "Sure, sai dana kira nace kila awajan ku kun shiga sallah ne, I'm sorry" tace "bakomai, amma ban fahimci wanene ba" yayi shiru sai kuma yace "Muhammad ne, Ammi." Ammi tace "Muhammad kuma?" yace "Eh, your son-in-law from Abuja" sai sannan Ammi ta gane tace "Ayyah, Allah sarki ya kuke?" yace "Alhamdulillah" sai yayi shiru Ammi ta fahimci akwai Magana a bakin sa tace "Ina jin ka? Feel free and talk" yace "Ammi dama i just want to confirm.." sai yayi shiru ta fahimci kunya yake ji tace "kayi magana mana" yace "kwana biyu ne idan na kira Leena bata ɗauka so last Wayan mu tace min kanta na ciwo so bansan ko lafiya bane naga shirun yayi yawa ne kuma bansan gun wanda zanyi confirming ba" Ammi tace "Everything is alright! So Karka damu, kawai kwana biyun ne bata zama saboda kasan exams ɗin biyu take gana WAEC sai kuma na islamiyya" yace "Sure! Kawai ne I'm so disturbed ne da jin shirun kuma ba daɗi ban kira nayi confirming ba tunda ina da numbern ki, amma ba wai na kira ne dan nace bata picking call ɗina ba" Ammi tace "na fahimce ka Karka damu" yace "Okay, Ma. Thank you" Ammi tace "The pleasure is mine, indeed" daga haka ya katse kiran Ammi tayi shiru for almost 5 minutes ita kaɗai tasa wannan ta kunce tasa wancan. Bayan Leena ta idar da Sallah kulan dambun ta ta ɗauka ta juye a plate din Hajiya ta koma cikin parlorn ta zauna tana ci Rayyan yayi sallama ta ɗaga kai tana kallon sa yace "baza ki amsa ba?" tace "Wa'alaikumus salaam, ina wuni" yace "Lafiya our little Hafiza" gani tayi har ya ɗan chanza mata compare yadda yake a asibiti ya zauna yana ganin yadda take cin dambun da hannu tace "Yaya ka duba ka gani?" yace "Uhm nagani har nayi replying ɗin ki back, tho Ni ba za'a sanmin dambun bane?" ta kai bakin ta tace "toh ai a gidan ku akayi Nima Hajiya ne ta bani" ta kare maganar tana mika masa plate ɗin ya girgiza kai yace "sai dai idan ke zaki bani hannu na ba kyau" tayi shiru tana tunani tace "toh ai ba spoon anan" yace "Eh dama da hannun zaki bani" ta ɗeba ta kai masa bakin ya karɓa sai da hada da yatsan ta da sauri ta cire akan idon Hajiya da ta fito ta ɗauke kai ta fara masifa ita kaɗai Rayyan ya kalle ta Leena kuma ta cigaba da cin abincin ta Hajiya ta karasa cikin parlorn tace "Ni dai gaskiya zaki daina shigo min ɗaki tunda komai kika ɗauka ba zaki mayar wajan sa ba" Leena ta turo baki taki kallon ta Hajiya taci gaba "Haka jiya bani da niyyar fita da yamma kika sa na raka ki asibiti wajan Rayyan zaki kai masa abinci kika ce muna zuwa zaki bani kaza amma har yanzu shiru kin mayar da Ni ban san me nake yi ba" Leena sai yanzu ma ta tuna ashe tama Hajiya Alkawarin kaza ta fara dariya Rayyan yace "wani iri kike so Hajiya a biya ki kayan ki?" Tace "Ni dai ko wani iri amma nafi son ban karus" Rayyan yace "toh ai Ni zaki sa na tsaya miki ba ita ba saboda ai bata aiki ita ina zata samu kuɗi" Hajiya tace "ba saurayin ta ɗan Minista ba ne Nasan ko yana turo mata" nan da Nan mood ɗin Rayyan ya canza and Leena can see it Dan haka dama ta gama cin dambu ta kai ma Hajiya kwanon ta kitchen ta wuce sashin su Hajiya na kallon Rayyan da ya jinjina da kansa tace "ka gani dai da idon ka ta gama ci taje ta ajiye min a kitchen" a hankali yace "toh Hajiya ina masu aiki kisa su wanke mana" tace "kai yanzu ka taɓa gani na bawa masu aiki sun wanke min kwanuka? Ai ko sun yi sai na sake wanke wa?" Yayi shiru be ce mata komai ba tace "yanzu kuma kaza ta ta dawo hannun ka" ya mike yace "barin je masallaci daga nan sai na biya na tsiyo Miki" daga haka ya fita. Leena na shiga parlorn ta ga Ammi na zaune ranta a ɓace nan da Nan Leena taji gaban ta ya tsinke Ammi na mata wani kallo tace "Leena, when was the last time you spoke to Muhammad?" Leena jin tambayar tayi har tsakiyar kanta kamar wacca aka cakkawa mashi tayi shiru tana kallon Ammi Ammi shouted at her "what nonsense is this? I'm talking to you, and you're looking at me like that? Ke kurma ce ban sani ba?" Leena taji kuka ya zo mata bata san sanda ta fashe da shi ba tace "Ammi, I think it's been 3 days now" Ammi tayi Wani murmushi tace "well done Leena, You must move on from him since you have Rayyan now, right?" Leena da ke share hawayen ta ta ɗaga kai da sauri tana kallon Ammi jin abinda ta ce da sauri ta girgiza kai tace "wallahi ba haka bane" Ammi tace "haka ne mana, 3 day da kika ce min ba lokacin bane kika zan cook ɗin Rayyan ba? ba lokacin bane? Shiyasa baki da time ɗin Muhammad balle ki ɗauki kiran sa, lokacin da Rayyan yake share ki ina har idan Muhammad be kira ba hankalin ki tashi yake yi kin dinga duba waya amma lokaci ɗaya ki canza ki bar bawan Allah da shiga damuwa, its okay, Leena" Leena na girgiza kai tace "Please don't misinterpret me, Ammi. Wallahi thats not the reason, ba haka bane" Ammi tace "Leena, I think I'll set boundaries between you and Rayyan" da sauri Leena ta ɗurku sa ta rike kafafun Ammi tace "Ammi dan Allah kiyi hakuri, kar kiyi min haka" Ammi with shock take kallon Leena tace "Tabbas ya tabbata zargi na, kije ki tattara kayan ki zaki koma Niger, ba zaki ci-gaba da zama da Ni anan ba, kije duk wahalan da zaki sha ko zasu baki ke kika sani, Leena. Kije idan har Muhammad yaga zai iya auren ki toh a ɗaura auren sai yaje ya dauko ki, idan kuma zaɓi da kika ma kanki ne fine ai yanzu kin girma zaki iya zabar ma kanki abin da ya dace da ke" ta kwace kafan ta tayi hanyar ɗakin ta Leena ta fashe da masanan cin kuka bata taɓa shiga tashin hankali irin na yanzu ba, tabi Ammi ta bata hakuri ma ta gagara sai da tayi kukan ta me isar ta har hawaye ya kafe mata sannan tayi kokarin tashi dan niyar yin Sallahn isha'i.
Rayyan yayi sallama ɗakin Hajiya ya shiga ya mika mata yace "yanzu dai zaki daina magana tunda an kawo Miki" tace "ai dama alkawari tayi min ba da banayi magana ba" ya mike yace "toh sai da safe" tace "zauna za muyi magana" ya zauna yana kallon ta ta ajiye kazan ta a gefe tace "yanzu kuma me yasa kuka fara shiri bayan shekarun nan kamar masu aljanu" kallon Hajiya yake yi sai kuma yace "tun da ɗin ma ba wai da son raina na daina mata magana ba" tace "Toh amma ai yanzu sai da zata yi aure ku tsira wannan sabon rayuwan Rayyan? Kai fa Babba ne idan Ita Linan yarinya ce? Ko baka san hakan ba kyau bane zaka ce min" yayi shiru be ce mata komai ba sai kuma yana kallon ta yace "Toh Hajiya me yasa zaku ba wani ita bayan kinsan ina son ta" Hajiya ta sake baki tana kallon sa da mamaki tace "A'a ban sani ba, toh taya zan sani bayan baka faɗa min ba zan san abun da ke zuciyan ka ne?" Yayi shiru tace "kana ji na ko Rayyan, har ga Allah na so ka da Leena abaya amma daga baya dana ga ka daina mata Magana abin yayi ta damuna idan ba zaka manta ba har kiran ka nayi na maka magana akai amma ka mayar dani ƴar iska" Rayyan yayi shiru sai yanzu yake ganin illan hanasa magana da mummy tayi Hajiya tace "yanzu kuma kasan cewa haramun ne ka ce zaka neme ta bayan har an bata ma wani shi kuma ya bada sadakin ta" Rayyan be ce mata komai ba sai kallon one direction da ke yi ga kuma wani boiling da yake inside Hajiya ta gama maganganun ta wanda shi baya ma sauraron ta dan hankalin shi baya jikin shi sam ya kalli Hajiya yace "sai da safe" ya mike sannan ya fita.
Mummy da ta gama serving Daddy tayi kasa da murya tace "baka ce komai ba yallabai" yace "yanzu an daina yayi zuwa wani gari siyyaya kawai order za kuyi a kawo muku" ta kashe murya tace "Haba Alhaji, siyayyan bikin ƴarta ne fa! Kuma ta roke ni, taya zan ce mata A'a, da safe zamu shiga Kano da yamma mu dawo dan da Flight zamu dawo" Daddy na mamaki hali irin na Khadija sai in tana bukatar abu ne kawai take zama very calm yace "it's Okay, Allah tsare hanya" tace "Amin, Nagode dear". Leena tun lokacin da tayi idar da sallahn isha'i bata tashi akan sallayan ba tana nan wajan damuwa ya mata yawa tasa wannan ta sa wancan wani lokaci taji hawaye yana sauka kan kunci ta ta share a haka take har pass 10pm wayan ta ne yake ta ringing ta ta tashi tana kallon wayan sai kuma ta karasa ta ɗauka amma kafin tayi receiving call ɗin ya katse Rayyan ne taga ya kira ta dawo ta zauna kan sallayan wani kiran ne ya shigo taji bata da wani interest ɗin magana da shi yanzu zata yi silencing wayan taga ashe Muhammad ne kamar ba zata ɗauka ba sai kuma ta ɗauka ta kai kunne sallama yayi ta amsa tace "good evening!" tana ji ya sauke ajiyan zuciya yace "Baby How have you been?" tace "I'm doing great" yace "Alhamdulillah! yanzu naji hankali na ya ɗan kwanta, Baby. I'm so disturbed kwana biyun nan, a office sai da aka ban pass na kwana biyu wai naje na huta sabon yadda nake treating Kowa kamar su suka hana ni magana da ke baby" sai kuma taji ba daɗi abinda ta masa yawan ci yana kira bata kusa ne amma bata taɓa bin kiran back ba, tayi kokari dan kar ya gane tana cikin damuwa tace "I'm so sorry, exams nake yi bana zama a gida ne shiyasa, and ya wanci kuma yanzu da wuri nake bacci, amma da ko text sai na maka" yace "No, no, no, baby don't street yourself for me please, me na kuma bayani, tunda you're fine, I'm glad" tayi shiru shima shirun yayi sai yace "toh barin barki Kiyi baccin ko" tace "thank you". gani take kamar gari ba zai waye mata ba, ta rasa ya zata yi dama idan ta shiga damuwa ɗakin Ammi ne comfort zone ɗinta, ta shiga rubutawa Ammi sako tana rubutawa tana hawaye a haka ta gama rubuta mata tayi sending, ta saba idan da ne Ammi zata leko ta tace kinyi addu'a? Kinsa maganin sauro? Kinyi this and that amma yau ko motsin Ammi bata ji ba tasan ran ta ya ɓaci sosai ne.
Do hints the star at the corner, please.
Thank you, and Happy reading!
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
22......
Tun da ta idar da sallar asuba tana nan kan sallayan ta gagara tashi saboda wani ciwo da kanta ya keyi, ta san da abaya ne toh tabbas da warhaka kam Ammi tazo ta duba ko tayi Sallah asuba amma yau Ammi ko ta kanta bata bi ba, tana nan kwance har taji dawowan Daddy daga masallaci. Daddy yace da Ayaan "toh je Ammi ta shirya ka ko" ya gƴada masa kai Ammi ta fito jin muryan sa ta gaishe sa ya masa yace "ina Leena? Jiya ta kawo min IVn su nace zan nema ta kuma na sha'afa" Ammi tace "waya san mata" yana kallon ta yace "bangane ba?" tace "ban san ko tana sashin Hajiya ba ne" Leena ta daure ta fito tana kallon Daddy ta gaishe shi be amsa ba, sai kallon ta da yake yi yace "Me yake damun ki?" daga haka Ammi ta kama hannun Ayaan tace "mu je na shirya ka ko" Leena ta sauke idon ta kasa ganin kallon da Daddy yake mata kamar wani me son gano wani abu ta tace "Babu kawai na kwana da ciwon kai ne" Daddy ya mike yace "barin ma Ya'yan ku magana kafin ya fita sai ya duba ki" ta gƴaɗa masa kai kawai yace "Nawa kike bukata na waliman ki?" tayi shiru yace "ko bakiyi list ba ne?" tace "Eh" yace "toh ki bari idan kika ji sauki sai ki rubuta Kiyi totally sai ki faɗa min amount ɗin" tace "Toh, Nagode Daddy" daga haka ya wuce sashin Uwar gidan sa. Leena har sannan tana tsaye a wajan ta gagara motsi daga karshe dai tabi Ammi kitchen ta tsaya a bakin kofa tace "Ammi dan Allah Kiyi hakuri" Ammi bata juyo ba tace "Wani abu ya faru ne?" Leena tayi shiru bata ce komai ba kuma bata bar bakin kofar ba sai sannan Ammi ta juyo ta kalle ta tace "Niger ɗin ne baki son komawa?" Leena ta girgiza kai sabbin hawaye suka ka fara sintiri a fuskar ta tace "Wallahi ba dan shi bane Ammi, damuwa ta yadda kika share ni ne, idan har komawa ta can ɗin zai saki farin ciki toh barin ki komawan ba" ta kare maganar tana me fashewa da kuka Ammi struggles to hold back tears bata juyo ba amma Chak ta tsaya da aikin da take yi tana jin kukan Leena har zuciyar ta She can't fake her feelings, her love for her daughter surpasses everything. She feels her pain deeply, and as someone who values the best for her child, she wants to protect her from getting hurt by Mummy. That's why she's setting boundaries between her and Rayyan. Leena's passions become hers, and above all, she adores her daughter.
Daddy yana shiga yaga Niswa na kwance kan 3 seater tana chatting ganin sa yasa ta tashi ta zauna ta gaishe shi ya amsa yace "yau ba lectures ne Niswa?" Kai ta gƴada tace "Dama lectures daya gare ni kuma lecturern ba zai zo ba" yace "Okay" Rayyan ne ya shigo ya gaishe da Daddy, Daddy ya amsa yace "yauwa dama Leena bata jin dadi ne so kafin ka fita ka duba ta" akan kunnan Mummy da ta fito wanda har ta gama shirin tafiya, Rayyan na kallon Daddy yace "Daddy me yake damun ta ne?" yace "Ta tashi ne da ciwon kai" wuff Mummy tace "Duk garin nan babu asibiti ne da sai Rayyan zai duba ta?" Daddy yace "ke Meyasa kullum baki son zaman lafiya?, shi Rayyan ɗin laifi ne idan ya duba ta, idan su Niswa ne zaki hana shi duba su ne?" tace "toh ai su ba ɗaya suke ba, taya ma zaka fara haɗa wata shegiyar agola da yaran gida" Daddy yayi murmushi yace "Ke musulma ce Khadija, ya kamata kisan cewa itama yarinyar bada son ta ta zama hakan ba, kamata yayi ki godewa Allah daya barni Kuma ya barki akan ƴaƴan ki, dan dukkan mu ba dabaran mu bane" bata son su fara samun issues da safen nan saboda yanzu burin ta ta samu tayi tafiyar da ke gaban ta, ta wuce dan yi breakfast. Ammi tace "Toh na haɗa Miki tea ne?" ta girgiza kai tace "zan ci wannan ɗin" Sallamar Rayyan suka ji daga bakin kofa Ammi ta ɗaga kai tana kallon kofar sai kuma ta amsa masa tace "shigo mana Rayyan" Leena ta sauke kanta kasa tana wasa da fingers ɗinta Rayyan da ya shiga parlorn ba zai iya tuna When last ya shigo ba, hakan yasa yaji nawin Ammi sosai, kunya kawai yaji ya kamasa Ammi dake dinning room ita da Leena ta tashi ta karasa cikin parlorn ya gaishe ta kansa a kasa ta amsa tana tambayar sa ya karfin jikin yace "alhamdulillah, dama Daddy ne yace nazo na duba Leena kafin na fita aiki" Ammi tace "Okay" ta mayar da duban ta kan Leena tace "Leena ki karaso ga Rayyan zai duba ki wai" daga haka ta wuce dakin ta Leena ta karasa cikin parlorn idon ta a kasa tace "Good morning" be amsa mata ba yace "What's wrong with you?" he asked, touching her forehead to check her temperature tace "Ba fah komai ba ne, It's just a slight headache, and I'm feeling okay now" yace "But your temperature is high" tayi shiru yace "Leena!" sai sannan ta kalle sa yace "Mene ne?" tace "bakomai dagaske, kan da sauki wallahi" yace "bari toh zan kawo Miki magani kafin na fita" tace "Thank you". Leena na shan magani ta kwanta sai bacci, bacci da bata samu tayi in peace jiya ba shine yanzu ta samu. Rayyan yana kallon Mummy da ta fito da wani ɗan babban jakka a hannun ta ya tashi ya je zai karba jakkan tace "A'a ka bari ba sai ka wahala ba" kallon Mummyn nasa ya ke yace "Toh barin kai ki airport sai na wuce aiki" da sauri ta kalle sa tace "A'a yi wuce War ka zan hau bolt" yace "bolt kuma Mummy? kuma fa ai ba abinda zanyi yanzu" tace "aikin fah?" yace "kin san yau zanyi resuming so ba lalle su ɗauka zan yi resuming yau ɗin ba" ya karasa maganar zai karɓa jakkan hannunta yana cewa "barin kai ki kawai" ta hatsalo masa tace "Toh sannu uba na, ina ce maka A'a kana son takura ni, toh ba zanje ba, shikenan" da mamaki yake kallon Mummy toh yanzu kuma me yayi zafi a maganar sa, ita da ko da wasa bata yarda ta shiga bolt amma yau kuma tace bolt zata hau, komawa da baya yayi yace "I'm sorry, Amma ba wai da wani manufa na fada hakan ba, Allah tsare hanya ya dawo da ku lafiya" tace "Amin" daga haka ta fita, Rayyan ya tsaya jim sai kuma ya fita. Me adaidaita tsawu ya tsaya a bakin tashar, Mummy ta sauka ta mika masa kuɗin sa, gate ɗin tasha ta karasa ta tsaya ta ciro wayan ta tana kiran Aminiyarta bugu biyu ta ɗauka tace "Nima gani nan karaso wa" bayan ta kashe ko minti biyar ba'a yi ba sai ga me napep ya tsaya ta sauko ta mika masa kudin sa sannan ta karasa wajan da kawarta take tana dariyar Mugunta tace "Shegiya da yanzu wani aikin kirki ne cewa zakiyi yayi safe amma wai harda rigani zuwa" ta karasa maganar cikin shekiyan ci Mummy tayi dariya tace "baki san yadda nake gagara bacci bane gashi kullum waye wan gari sai naji kamar nayi hauka idan na tuna bikin na matsowa kusa" shiga cikin tashar suka yi, wajan motar wani kauye suka karasa. Leena na farkawa taja wayan ta da niyyar ganin karfe nawa ne text ɗin Muhammad taci karo da shi murmushi tayi sannan ta tashi, yanzu ta ɗanji dama dama ko dan yadda Ammi ta sauko ne oho, sauka tayi a gadon ta gyara ɗakin sannan ta wuce ban daki tayi wanka ta chanza kaya ta ɗauki wayan nata tana sake karanta sakon sa replying ɗinsa back tayi sannan ta jona wayan a chargy ta fita zuwa parlor ganin Daddy tayi da Ammi suna zaune daga gani soyayya suke sha abin su zata wuce Daddy yace "ya jikin naki dai Daughter" kanta a kasa tace "Alhamduida da sauki yanzu" Ammi na kallon ta cike da tausayi harga Allah duk duniya ba wnada take so fiye da Leena, hakan da take mata kuma so ne ba wai taki ta bane, itama ta san ba zata taɓa iya mayar da ita Niger ba tana kallon ta tace "Toh ki sake breakfast ɗin mana ai yanzu zaki iya yi tunda jikin da sauki" ta gƴada mata kai tace "barin je na gaishe da Hajiya kar tace yau naki leko ta dama jiya munyi faɗa" Daddy na dariya yace "kinyi list ɗin ne?" tace "A'a" yace "Dama me da me zaki buka ne?" tace "Dama ɗinki zanyi na ranan, da wanda zan sa a wajan taron da kuma.wanda zansa a gida, sai memo, sai kuma masu deco da zasu zo gida suyi" Daddy yace "okay, In sha Allah zuwa anjima zan Miki transfer, tace "Toh, Nagode Daddy, Allah kara buɗi" yace "Amin" daga haka ta wuce ɗakin Hajiya tana shiga taga Hajiya na yagan kaza nan da Nan har ta manta da wani damuwan da ke damu ta tace "Kai wallahi, Allah yana so" Hajiya ta kalle ta tace "ke kuma me haka" ta zauna dirshen a gaban Hajiya tace "toh ban nawa mana" Hajiya tace "dama baki je jarabawar bane? da ban ganki da safe ba" tace "na tashi ba lafiya ne sai da Yaya yamin allura tukun" duk maganan da tayi tana kallon cikin plate ɗin hannu Hajiya, Hajiya ta ɗauki fuka fiki ta mika mata Leena ta ɓata rai ganin abin da take bata bayan ga manyan soka a ciki Hajiya tace "idan ba zaki karba ba wallahi zaki rasa" Leena tace "toh bayan kadan kika bani ai wannan ba abinda zai min" Leena ta fake idon Hajiya ta ɗauke cinya da gudu ta kama hanyar fita Hajiya ta sake baki tana kallon ta Leena bata tsaya ba sai a kofar ɗakin su dan tasan tana shiga Ammi taga yana yin ta zata mata faɗa dan ta hana ta gudu sai da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 50