ayi ta magana kana ji ba zaka ce komai ba" yace "toh Hajiya duk yanda kika ce ayi hakan kawai" bayan ya gama waya da Hajiya ya ɗaura kansa akan desk din office ɗin sa be san me taka meme idan zai ganta ba shi yanzu tunanin sa idan mahaifiyar yarinyar ta iso gari yau ya zasu ce mata?. Mai gadin ya buɗe musu gate din gidan fita su kayi acikin gidan da mugun speed sai kuma wanda ke tuka motar ya fara reversing motar da hankali ya dawo baya Sadeeq yana kallon Sultan yace kai kuma lafiya sai da ya tsaya sannan ya juya yana kallon inda Sultan din ke kallo, tsaki Sadeeq yaja Sultan yace "Look at how peacefully she's sleeping" Sadeeq responded, "what businesses do you have with her" Sultan yaja motar suka tafi. Hajiya ta kuma kiran Rayyan for, numerous times yana ɗaga wa tace "Riyan ka ganta" yace "No Hajiya, barin kuma fita nama rasa inda zan tafi neman ta ne" daga haka ya katse kiran ya cife a cikin asibitin na su, Hajiya taji hankalin ta ya fara tashi gashi uwar yarinyar na ganin girman ta, tsoron ta kar uwar Leena ta dawo yau toh suce mata me? kiran Daddy tayi a waya tace "Kana ina ne wai? Gashi mun kusan shiga bakin duniya, Ni yanzu idan uwar yarinyar nan ta dawo kasar nan me zamu ce mata?" Daddy yace "Hajiya me yake faruwa ne ban gane ba?" tace "Gaskiya toh idan ba wai wani abu kwakkwara kake ba toh ka dawo yanzu wallahi" Daddy yaji hankalin ya ya ɗan tashi dan Hajiya bata fiye masa wannan kira tace ya dawo gida ba. Har su Sultan suka dawo daga inda suka tafi Leena na nan wajan but this time around jin karan motar su yasa ta buɗe ido tana mutawa Sultan ya dawo daidai da inda take ya tsaya da mota yana kallon ta yace "Hey little girl" tace "Good afternoon, uncle" ta fada tana kokarin gyara jakkan ta zipping yace "What are you doing here? And you look exhausted, is everything alright?" ta girgiza masa She replied to him "I can't find our house" His expression is one of surprise yace "how?" tace "i just don't" ya kalli Sadeeq dake danna wayar sa yayi kamar be ma san dasu a wajan ba ya sake maida kallon sa kanta yace "So, what brings you here" She replied "Uncle, I want to go back home, but I haven't seen our house and I'm tired, so I'm sitting here to rest" Sadeeq yace "malam na gaji da ajiye Ni anan da kayi fah" Sultan yace "ɗan rainin hankali ba gashi mun karaso gidan ba ai zaka iya sauka ka shiga" Leena na kallon Sultan tace "I don't like your brother" Sultan ya kwashe da dariya wani kallo Sadeeq ya watsa mata to his surprise yaga kallon idon sa take ba alamar tsoro Sultan yace "I'm coming" karasa shiga da motan cikin gidan yayi sannan yayi parking Sadeeq ko kallon sa be yi ba ya wuce cikin gidan abun sa Sultan ya karasa gate ya shigo da Leena "Uncle, can you take me home?" yace "Sure! a wani street gidan ku yake?" tace "I don't know" kallonta ya tsaya yi tace "do help me, please?" yace "how?" ta mai alama da bata sani ba itama, har cikin parlorn su ya kai ta yace "ki zauna ana, bari nayi lunch sai na kaiki school din naku a duba min address dinki" ta gyaɗa masa kai tace "Uncle What time is it?" yace "pass 3" ta rufe bakin ta da sauri tana gwala ido yace "What?" tace "Na bar gida before 8am fah" sadeeq ya fito a daki yana kallon Sultan da mamaki yace "Continue attending to the stranger" yayi wuce War sa kitchen, Sultan ya maida kallon sa gun Leena yace "Tell me how?" Leena ta fada masa everything ya tashi yana girgiza kai Sadeeq daya fito a kitchen yana jin su yace "What do you plan to do now" Sultan yace "I know I won't take her back home until tomorrow. That way, they'll notice she's missing, I'm not worried about her father taking action against the stepmother" Leen tace no please kamar zata yi kuka tace "Ya Rayyan zai damu, Hajiya ma Daddy too" dakyar sukayi convincing dinta zasu mayar da ita anjima. Sadeeq ya jona wayan shi a chargy ya fita, Sultan kuma tunda ya haura sama be sauko ba Leena ta gama cin abinci da aka bata taje ta cire wayan Sadeeq a chargy ta buɗe wayan ta shiga Camera ta ajiye akan kujera yadda bazai faɗi ba ta fara video. Hankalin daddy yayi mugun tashi daya gama jin maganganun da Hajiya ta fada masa yace "Hajiya meyasa tun jiya ba'a sanar dani abun da ake ciki ba" daga haka ya fice a parlorn ta kiran Rayyan yayi yana ɗaga wa yace "Rayyan ka dawo gida yanzu" yana katse kiran ya kira wani friend dinsa D.P.O. sadeeq bayan ya dawo ya wuce sama abun sa me yankawa Leena ba duk tunanin sa wayan sultan ne a hannun ta. Sallama akayi a bakin kofar parlorn Leena ta daga kai tana kallon budurwan da ta shigo, Leena tace "Sannu da zuwa" tana murmushi tace "thank you" daga haka ta wuce dakin dake cikin parlorn.
Yes, I trust you sister. You're a true supporter, so please help me and share this with others
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
_By Jiddatul-khayr_
~Book 1~
Chapter 4
Tana chanza kayan ta ta fito daga dakin ta wuce kitchen ta ɗebo abinci har ta fito Leena na jikin waya tana ta maganganun ta Jidda ta tsaya tana kallon ta saboda yarinya ta burge ta tace "Hey! Baby girl, zo mu ci abinci" girgiza mata kai tayi sannan tace "is this Your house?" Jidda tace "yes, it is" tace "toh Brother dinki ya bani abincin naci" jidda taji yarinyar tana burge ta kawai ta karaso cikin parlorn ta zauna a kujeran da ke kallon na Leena, Leena tace "Oops na bata video ɗina ashe banyi pause ba nake ta magana da ke" jidda tace "sorry, then" Leena ta ɗaga kai tana kallon ta tace "Are those two brothers yours?" Jidda na murmushi tace "Yes, sweetheart" She replied "I didn't like the other one, but I like the one who gives me food" jidda tayi dariya tace "Is it because you're a foodie?" Ta girgiza kanta tace "No, it's because he brought me into your house and treated me kindly. The tall one, though was harsh, so I didn't like him" sadeeq da Sultan dake saukowa a stairs zasu ball Leena ta karasa maganar daidai saukan su jidda ta ringa dariya ta fahimci ƴaƴan nata har ya gwadawa Leena halin sa dan tasa cousin ɗinta bai da wannan hali, Leena ta juya da sauri jin dariyan Sultan fuskan sadeeq ta ɗan kalla taga ya ɗaure fuska da sauri ta tashi taje jikin jidda ta zauna sai kuma ta kai bakin ta kunnan jidda tace "kinga fuskan sa ko Ni tsoro ma yake bani" jidda ta ajiye abincin hannun ta da sauri tana dariya gudun kar ta zubar suna karaso cikin parlorn Leena ta ɗauke kanta tana karatu a hankali Sultan yace "Hey girl" tana murmushi tace "Sannu uncle" Sadeeq yaje wajan chargy zai ɗau waya yaga ba wayan sa ya juya yana kallon Sultan yace "Dude ka cire min waya na ne a chargy?" yace "Not at all" Leena ta kalli jidda da sauri sai kuma ta kalle su ita tama manta cewa a chargy ta ciro wayan a hankali tace "here is it" wani kallo Sadeeq ya watsa mata" Sultan ya karasa ya karɓa a hannun ta" yace "ka bari ta kawo da kanta mana" yana mika masa yace "it's okay tunda na karbo muje kar muyi latti" ya karba wayan sai yana duba percent yaga 20 da sauri ya juya yana kallon ta yace "wato tun ɗazu kika cire min ko? Wait karde a waya ta kika ringa haukan dana gani kina yi" a hankali tace "I'm sorry, Amma ba hauka ba ne" Sultan sai dariya yake ya ja sa suka fita tana kallon Jidda tace "sam min wayan ki mana" Daddy na zaune a station absent-minded, yayi nisa cikin tunanin da yake Rayyan ya dafa sa yace "Daddy yamma yayi ka wuce gida kawai, zanna informing dinka duk wani abu daya taso" sauke ajiyan zuciya yayi yace "Okay Rayyan" mikewa yayi sannan yayi sallama da friend din nasa be tsaya ko ina ba direct gida yayi yana shiga street ɗinsu sai ga motar Mummy ma ya kuso kai yana bin nasa a baya yayi horn mai gadi ya zo da gudu ya buɗe masa yana tambayar sa ko an ganta girgiza masa kai kawai Daddy yayi saboda yanzu baya son wani magana yana shiga da mota ita ma ta shigo da nata motan bayan ya gama parking ya buɗe motar ya sauka sai ya kama hanyar part ɗinsa ba tare da ya tsaya ba Mummy kallon yana yin sa yasa tana gama parking tabi bayan sa yana shiga part din zai kulle Mummy tace "Amma lafiya Alhaji?" Kallon daya wasa mata ne yasa tasha jinin jikin ta juyawa tayi ta wuce part ɗin ta a parlor ta samu Nisreen da Niswa suna kallo shigan ta yasa duk suka ɗaga kai suna kallon ta Niswa ta tashi taje ta karɓa jakkan hannun ta bayan Mummy ta zauna Niswa tace "Mummy kin san me yake faruwa a gidan nan kuwa?" Mummy taji zuciyan ta ya tsinke tace "me yake faruwa ɗin" Niswa tace "Wai fah Leena ce ta ɓata tun safe da muka fita itama ta fita wai zata makaranta a kafa" Mummy tace "ta ɓata kamar yaya?" Nisreen tace "Tun safe ta bar gida kuma bata isa school ba har yaya sai daya tafi school dan yayi confirming amma bata je ba" Mummy ta ja dogon tsaki tace "Dama shiyasa Daddyn ku ya wani shareni akan ta, Lalle ma mutumin nan" daga haka ta tashi ta wuce ciki Niswa tace "Allah yasa a same ta" Mummy ta jiyo ta wasa mata wani kallo tace "I'm sorry Mummy but wallahi Daddy ya damu sosai kar wani abu ya same sa kuma" tace "Toh ya same sa ɗin mana wani ya ɗaura masa wahalan? Ba shi ya ɗaura wa kansa ba? Toh shi ya sani" daga haka ta shige dakin ta Nisreen tace "Wallahi dazu baki ga yaya bane kamar zai dake ni" Niswa tace "Dalla kimin shiru". Daf Magrib sai ga Maman su Sadeeq ta dawo da sallama ta shigo parlorn tun da ta shigo idon ta ke kan Leena da take video a wayan Jidda ganin ta da Leena tayi yasa ta kashe wayan ta sauka a kan cushion din ta zauna nan kasan carpet tace "ina wuni" tace "Lafiya, tashi ki zauna abunki a kujeran kinji" sai ta gyaɗa mata kai ta koma kan kujeran sai ga jidda ta fito tana ma Mamin ta sannu da zuwa bayan sun gaisa jidda tace "Kai amma Mami kunyi dare" tace "Wallahi abun su ɗin ne is not organized" daga haka ta wuce ɗakin ta dan canza kaya gashi ana ta kiraye kirayen sallah, sai kusan to 7pm Mami ta fito a dakin ta sai ga jidda da Leena suma sun fito Mami na kallon Jidda tace "Jidda wannan ƴar waye ne kuma?" jidda tace "wallahi nima ban sani ba Mami" Mami ta haɗa rai tace "ban gane ba" jidda tace "Nima na dawo a school na ganta ya sadeeq da ya Sultan ne suka kawo ta" Mami tace "suna ina yanzu ɗin?" tace "Tunda suka fita ɗazu da yamma da kayan ball basu dawo ba" daga haka Mami ta wuce kitchen. Daddy ta inda yake shiga ba tana yake fita ba "wannan ai selfish ne taya zaki hana yarinya zuwa makaranta saboda da mugunta, akan ki take zama agidan? me ta tare Miki yarinyar karama ki tsaya kina wasting time ɗinki wai ke kina kishi da ita wannan ai hauka ne" Hajiya tace "Wallahi baka ga fuskar yarinyar nan bane jiya wallahi da uwarsa zata ga fuskar ƴarta jiya wallahi sai tayi kuka kila ma tace bazata iya zaman gidan nan ba" Mummy sai hararan Hajiya ta kasa take yi Daddy yace "Wallahi Khadija akan missing ɗin yarinyar nan zaki iya barin gidan nan dan bazan iya zama roof daya da mugu ba, Hajiya tace "Hakuri zakayi in shaa Allah za'a same ta zuwa safe, kayi hakuri wannan ihun da kake yi har idan ba'a ci Sa'a ba har makwafta zasu iya ji. Daga haka Daddy ya wuce masallaci dan yaji ana kokarin sallan isha'i Hajiya tace "bari na koma can part Dina Nima dan banga ta zama ba, mu mikawa Ubangijin mu kukan mu" tana juyawa mummy ta zuba mata hararan sannan ta tashi ta shiga parlorn ta tace "Niswa mi ko min waya ta a daki na" Niswa ta ɗauko ta mika mata mummy Rayyan ta kira yana ɗaukan watan tace "Sannu Rayyan, ai kanwar uwar kace ta ɓata da har yanzu ka kasa dawowa gida, kama manta da yunwan cikin ka" yace "Mummy I think ba zan dawo yanzu ba, abinci kuma yanzu zan tsiya injira ne inji me police ɗin zasu ce mana kuma" Mummy tace "Ni kake cewa ba zaka dawo yanzu ba? Toh umurni nake baka da ka dawo" yayi shiru sai kuma yace "Mummy ki duba halin da yarinyar zata shiga beside ma Daddy ne yace na zauna na jira me zamu ji next" tace "Toh wallahi nan da 15 minutes na baka ya maka a gida, shi uban naku tunda shi ya ji ya gani ya auro uwarta sai ya kwana a waje yana neman ta, saura karka dawo Rayyan wallahi zaka sha mamaki na" daga haka ta katse kiran. Sai wajan karfe tara Sadeeq da Sultan suka dawo gidan already Jidda ta canza mata kaya ta bata wani ringan ta top ta cire mata uniform har tayi bacci abunta, suna shiga parlorn suka ga Mummy da jidda na zaune sai yanzu Sultan ya tuna da Mummy yaji kaban sa ya faɗin bin parlorn yayi da kallo baiga Leena ba karasa cikin parlorn su kayi suka zauna a nan kasan carpet suka gaishe ta ta amsa musu da fara'a tana tambayar su ya aiki sun tashi zasu tafi tace ku zauna ina da magana da ku duk suka dawo suka zauna tana kallon su tace wancan yarinya kuma yarinyar waye ne?" Sultan ya juya yana kallon Sadeeq while sadeeq yayi kamar ba dashi ake magana ba dan shi gaba daya ya mayar da hankalin sa kan Tv dake aiki Sultan yace "Mami yarinyar ta ɓata ne, so bata san gidan su ba" kallon sa take baki buɗe tace "ban gane ba Sultan" yace "mun tsince ta ne Mami, toh gudun kar ta faɗa hannun wanda ba na gari ba yasa muka kawo ta nan" tace "A nan kenan zata yi ta zama?" yace "A'a Mami, gobe dama zamu kaita Makarantar su tunda ta san makarantar acan sai muyi musu bayani sai su bamu address din gidan nasu" Mami tace "Amma kuma da hankali, tun yaushe kuka tsince ta and where?" Sultan ya mata bayanin everything da kuma maganan da Leena ta fada musu Mami ta fara faɗa kamar zata dake su "Yanzu ya familyn ɗinta za suyi, idan kune aka tsince kanwarku a barta har sai washegari yaya zakuji, idan wani abu ya same su kuma fah?" fada Mami take kamar ba gobe daga karshe tace "a fitar mata da Leena a daren suje sune mo inda gidan su yake dan baza ta laminci wannan rubbish shawaran da suka ba kan su ba dakyar suka bata hakuri har da jidda akan a bari gobe da sassafe zasu nema gidan su Mami tace "Wallahi ban san baku da lissafi ba sai yau, kwata kwata na raina ma wayon ku" ta tashi ta wuce dakin ta ɗan ranta yayi mugun ɓaci Sadeeq na kallon Sultan yace "Abunda nake ta gudu kenan gashi an haɗa dani" Sultan yace "ji munafuki inace da ta gama bamu lbrn ta nace mu bari sai gobe ai cewa kayi it's okay" daga haka sadeeq ya mike yayi wucewar sa jidda ta kalli Sultan tace "Ya Sultan wallahi naji tausayin yarinyar kamar tayi ta zama ana" yace "Toh kije ki fadawa Mami hakan" ta rufe bakin ta tace "rufamin asiri" yayi dariya yace "kina ganin yanda ran Mami ya ɓaci zaki kawo wannan shawaran" daga haka yace "good night" ya wuce ɗakin sa. Rayyan bashi ya isa gida ba sai kusan 10 na dare yana zuwa yayi part din Hajiya yana sallama ta fito da sauri tace "Riyan an same ta kuwa" yana girgiza kai ya karasa shiga cikin parlorn ya zauna Hajiya tace"Toh mu de mun shiga uku wallahi, Ɗazu kuwa Hauwa ta bugo waya daga Nijar, suka gaisa da Daddyn ku tana tambayar sa ina Lina, yace baya gida, kila jikin ta ya bata ne, Daddyn ku shine ransa ya ɓaci wallahi duk kawaicin sa sai daya ma Uwarki faɗa, gashi kamar dai gobe ne Uwar Linan zata zo" Rayyan daya gaji da jin surutun ta tana ambaton Uwar Leena zata dawo ya ɗaga kai da sauri yana kallon ta yace "haka tace Hajiya?" tace "Eh fah, ai shiyasa Baban ku ransa ya ɓaci matuka" wani zufa ne ya fara karyo masa kawai ya miƙe tace "ina zaka?" yace "wallahi gani nake polisawan nan ba wani aiki suke ba Hajiya" tace "ai kam ace har yanzu shiru harda gidajen rediyo sai da aka sanar amma har yanzu shiru" fita yayi daga parlorn na ta a hanya yaci karo da Daddy dake waya tsayawa yayi har Daddy ya karasa wayan sannan yana kallon sa yace "Daddy akwai wani information ne?" yace "No Rayyan, wallahi na gaji da halin mahaifiyar ku, tun ba yau ba take abunda ta ga dama ina ɗauke kai amma ita sai tana amfani da wannan daman tana taka mutane, me yarinyar nan tayi mata yarinya karama da ita, kalli lokacin da tayi tafiya haka uwar Leena ta rike ku kamar ita ta haife ku, yanzu me zan ce mata idan ta karaso garin nan" ya karasa maganan so pissed off, Rayyan yayi ajiyan zuciya yace "Daddy ka koma ka kwanta, kana bukatar rest" yace "Ana bukatar hoton Leena gashi Ni bani da shi, kuma karna tambayi sirbajo ta fara zargi dan ɗazu ta tambayeni ita nace bani gida ne" Rayyan ya ciro wayan sa yace "Barin tura maka hoton nata" daga haka ya tura masa. Washe gari da asuba jidda ta tashi sallah bayan ta idar sai kuma ta tashe Leena, Leena na idar da Sallah ta kama azkar jidda nata kallonta da mamaki tana gama wa tace "Anty jidda ina kwana" tace "lafiya klau Leena" Leena tace "ina wancan Uncle ɗin?" Jiddah tace "Wanda kikayi video a wayan sa" tace "God forbid in neme shi, dayan uncle din" jidda na murmushi tace "ohh ya Sultan?" ta gyaɗa mata kai tace "Toh ya zo ya kaini gidan mu dama yace yau zai kaini kuma kar Ammi na ta dawo daga bana nan" jidda na kallon ta tace "baki son nan ko?" ta girgiza kai tace "ai zanna zuwa Miki weekend" jidda tace "Toh shikenan, bari su dawo a masallaci sai ya kai ki" tace "Toh" jidda tace "yauwa Leena waya koya miki wannan abubuwan da kikayi a waya na jiya sai dana zo kwanciya kawai na gansu very interesting wallahi, Leena tace "No one, Amma Abbah na na da shi yake supporting dina ina yi" jidda tace "keep soaring dear, abu me kyau ne kinji" tace "thank you" Jiddah tace "muje mu gaishe da Mami kinji" tare suka tafi ɗakin Mami sukayi knocking Mami tace "come in" tare suka shiga bayan sun gama gaisawa da Jiddah Leena tace "Mami ina kwana" tana kallon ta tace "Lafiya, a wani unguwa gidan ku yake ?" tace "Ni ba ban sani ba amma nasan layin gidan" Mami tace "wani makarantar kike?" tace "A international nake" Mami ta kuma cewa "Toh ina Maman ki?" tace "ta tafi Nijar inji Hajiya" tace "Toh ya akayi kika ɓata?" tayi narrating exactly yadda Sultan yayi mata narrating Mami ta gyada kai alamar gamsuwa dan yarinyar bata da wayon da zata kirkira labari, Mami tace "Toh tashi ku tafi" bayan sun fita sai ga su Sultan sun dawo a masallaci suka shigo gaishe ta tace "Toh Allah ya tashe mu lafiya, yanzu sai ku kama hanyar da zaku mayar da yarinyar nan gidan su" Sultan yace "Mami ki bari 7am yayi sai mu kai ta" tace "saboda jiya na muku Alfarman a bari da safe" ya bata hakuri daga haka sukayi mata sallama suka fita a daki suka ci karo da Jiddah a parlorn ta fito daga kitchen yana kallonta yace "ki shirya ta yanzu please" gaishe su tayi sannan sadeeq ya wuce ɗaki shi kuma Sultan ya zauna nan parlorn yana jiran ta Jidda tace "Toh gaskiya tare zamu tafi ina son ganin gidan su saboda ina son yarinyar" daga haka ta wuce cikin daki dan shirya ta Sultan yaji wani relief at least idan suka tafi da Jiddah abun zai ɗanzo da sauki than shi kaɗai na miji ya mayar da ita. Jidda ta shirya suka fito tare sallama takai Leena tama Mami, Mami na kallon Jiddah tace "lectures din yau ɗin fah?" tace "sai around 2pm ne Mami" daga haka tace Allah bada sa'a Sultan ma ya leko yayi mata sallama ta fito ta raka su har waje tace "kasan me zaka ce, maganar ka ya zama guda daya banda chanza baki" yace "in shaa Allah" Jiddah ta kama hannun Leena suka shige mota Sultan yayi horn mai gadi ya buɗe masa gate suka fita daga gidan Leena tace "ina wicked uncle ɗin can?" Daga Jidda har Sultan sai da sukayi dariya yace "barin kira Miki shi a waya". Bayan Daddy sun dawo daga sallah part ɗin Hajiya suka wuce shida Rayyan bayan sun gaisa suna kara jajanta abunda ya faru kenan Rayyan ya tashi yace "ina zuwa" yana fita ya wuce parking space ɗaukar motar sa yayi aka buɗe masa gate ya tsaya yana amsa gaisuwar su. Layin da suka bi dan kama hanyar makarantar su Leena, Leena tasa ihu tace "ga can gidan mu Nice Uncle, wancan ma motar Ya Rain din mune zai fita, kila Ni zai je nema ko?" ta juya da sauri tana kallon Jiddah Sultan ya rage speed din motar zuciyar na bugawa addu'a yake Allah yasa su fahimce su.
Yes, I trust you sister. You're a true supporter, so please help me and share this with others
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
Chapter 5
Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes
Bayan sun gama gaisawa yaja motar zai tafi Sultan yayi masa horn, Rayyan ya tsaya da motar Leena ta buɗe kofar ta fita Rayyan was utterly speechless, he couldn't believe what his eyes were telling him. Was it really Leena standing in front of him? sai kuma da sauri ya buɗe motar ya sauka Leena tazo da gudu ta kama sa ya dur kusa a akan kneel ɗin sa yana kallon ta He hugged her tight, sighed, and said, "Leena, is this really you?" ya sauke ajiyan zuciya ya kuma cewa "Alhamdulillah" dariya ya bata bata san sanda ta fara ba she replied confidently, "it's me, Do you miss me this way?" He noddle and said, "Not only me Leena, but everyone" ta gyaɗa masa kai tayi shiru tana tunanin Ammin ta ya yanke mata tunanin ta he asked, "where have you been since yesterday, and who showed you the way to come back home Leena?" Sai yanzu ta tuna ashe she's not alone da sauri ta juya tana nuna masa Jidda da Sultan da already sun ma fito a motar ya karasa ya mika ma Sultan hannu bayan sun gaisa Sultan ya faɗa masa briefly ɗin abunda ya faru Rayyan yana gyaɗa kai yace "Toh mu shiga ciki mana" da farko
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 50