Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da jin furucin Daddy. Daddy ya tsaya kallon evidence ɗin wanda aka sayar masa da gida, gashi kuma takardun gidan ne ba wai na bogi bane, Daddy kansa ya ɗaure dan da gaske komai na gidan ne amma waya sayar shine amsar da yake nema, Rayyan ma yayi shiru yana tunani, Daddy ya sa aka kwashe kayan na su yace su koma gidan sa da zama kafin nan, Malik yaki ganin har ran Daddy ya ɓaci sannan ya yarda, shi kuma gani yake kamar ba zai iya zama a cikin gidan su bane, yasan da kunya, yanzu addu'an sa bai wuce Allah ya sa ya samu aiki bane, ya bawa Leena rayuwar farin cikin dan yasan tayi kokari da shi. Bayan sun koma gidan Daddy da zama, an basu BQ, Daddy kuma yasa a masa binciken waya sayar da gidan shine kawai abin da yake bukatar sani. Bayan sati da komawar su gida, Leena ta fito daga part ɗin Hajiya ta wuce BQ inda yanzu suke da zama ita da mijin ta, tana shiga taji wayan ta na ringing da sauri ta karasa ta ɗauki wayan ganin Muhammad ke kiran ta yasa tayi receiving call ɗin, bayan sun gaisa Muhammad yace "Leena toh sai ku shirya yau, gobe ku taso zuwa nan Abuja dan jibi suke son ganin ku" Leena tace "Ya Muhammad ka manta ban yi makaranta ba, sai dai miji nane" yace "Kar ki damu, yanzu za'a iya ɗaukan ki a hakan saboda Daddy yayi magana kin san senator ne shiyasa, so da ke da mijin na ki duk zaku samu aiki amma ina so kina farawa dan Allah Leena ki koma school" Leena taji hawaye ya cika idon ta, addu'an ta kenan kwana biyun nan Allah ya bawa mijin ta aiki kawai ta tuna da Muhammad tana masa magana gashi ko sati bai ɗauka ba yace suje ana neman su, Muhammad ya katse mata tunani yace "Sai kun zo ɗin, ki gaida min mijin na ki" A hankali tace "Mungode" yayi sauri ya katse kiran dan baya bukatar godiyar ta, Leena ta fashe da kuka ta rasa me take ji, a haka Malik ya shigo ya ganta da sauri yayi kanta yace "SubhanAllah Meya same ki dear?" Tana share hawayen ta tace "Yanzu Muhammad ya kira Ni, wai gobe mu tashi zuwa Abuja, mu tafi da takardun mu jibi zamu yi submitting Application sannan su mana interview" Malik ya mata wani kallo yace "Who is Muhammad?" Da sauri ta gyara tace "Wani cousin ɗin Ammi ne fah" sai sannan ya sake fuskan sa yace "Toh Allah yasa mu samu, Allah ya kaimu" ta amsa da Amin ta fita zuwa bangaren Ammi dan ta sanar da ita abin da ake ciki.. Leena ta fito daga part ɗin Ammi, sannin Malik ya dawo dan baya yarda ya wuni a gidan sai ya lura goma ya wuce sannan sai ya dawo ko kuma da yamma ya dawo, tana cikin tafiya zuwa BQ ta tsinkayi muryan Rayyan "Hey Leena" ta juya sai kuma da murmushi shinfiɗe a fuskar ta ta karasa inda ya ke tace "Yaya ina wuni" Yace "Lafiya kalau" tace "Ya su Anty Layla da Leena na?" Yana murmushi dan yaga kamar ma Leenan tafi Layla kishin kara mata aure da yayi yace "Ba zaki tambaye ɗayar Antyn na ku ba?" Ta taɓe baki tace "Ni na santa ne? Ai gashi na tambaye wanda na sani" yayi murmushi yace "Yanzu Husnan ne baki sani ba? Tun da kina yarinya take zuwa gidan nan" ta taɓe baki sai kuma tace "Yauwa Yaya kasan me? Gobe fah zamu tafi Abuja jibi wai zamu je interview" jikin Rayyan yayi sanyi dan shi bai so hakan ba yaso ace shine yayi fighting mu su yace "wa zai kai ku?" Tace "I think motar tasha zamu bi, ko kuma mu tafi da nawa motar" ya Harare ta yace "Dama kin taɓa bin motar tasha ne? Lokacin da kike lafiya baki bi ba sai yanzu da kike da karamin ciki? See you" Leena ta ji kunya ya lulluɓe ta "Zan duba if there's available flight mu gani" tace "Toh Shikenan, Mun gode" daga haka ta karasa. Da safe bayan sun ma Ammi da Hajiya sallama sai da suka biya gidan Umma wanda tayi ta musu addu'ar nasara da kuma Allah ya tsare su. Bayan flight ɗin su yayi landing, drivern da Muhammad ya tura shine ya je ya ɗauke su, a kofar wani apartment yayi parking, Malik ya sauka sannan ya riko ta ta sauka, ya kwashe musu trolley ɗin sannan suka jera tare zuwa cikin apartment ɗin. Leena na zaune akan gado kafafun ta na kasa, Malik na duke a kasan yana masa mata su dan ƙafan sun ɗan kumbura, tace "Twin, yanzu Ni dan Allah me za'a bani bayan ba karatu nayi ba?" Ya Kalle ta sai kuma yace "Kin san yanzu yana yin kasan it depends on Who you know ne, kuma ai kince Mutumin senator ne so yasan yadda zai yi ai" ta gƴaɗa masa kai yace "Sai dai gaskiya dole ki koma school, saboda Karki ji daɗin kuɗin ki manta makaranta" tayi dariya. Washe gari da safe drivern da ya ɗauko su a airport shine ya sake zuwa, bayan yayi dropping ɗin su a wani babban organization suka sauka, ta Ciro wayan ta a jakka ta mika masa tace "Gashi, call him sai ya faɗa maka inda zamu nufa" Malik ya karɓi wayan da take mika masa, baya ya gama magana da Muhammad ya mika mata wayan, hannun ta ya rike suka nufa ciki, dake ko wani office da suna a jikin, a haka har suka haura second floor, wata mata ta karasa wajan su tace "Hello! Are you the ones Sir Muhammad said would be coming?" Leena tace "Yes, Ma" tace "Alright then, welcome! Come with me, please" suka bi bayan ta, a wani babban office ta kai su tace "Oga is in his office having breakfast, Once he's done, he will let you know so you can go in" Malik yace "Alright, thank you" daga haka matar ta fita a office ɗin, su kuma suna zaune a ciki sannan akwai wani office a cikin inda suke, wanda suke kyautata zaton shine office ɗin da take magana akai, after like 30 minutes ya buga kararrawa wanda hakan yasa wata PA ɗin sa fitowa a wani office ta karasa ciki da sauri ba'a dau lokaci ba ta fito tana kallon Malik tace "Sir, Ma, zaku iya shiga" suka miƙe suka shiga office ɗin nasa, Mutumin yana kallon system ɗin gaban sa, Matashi ne amma daga gani kuɗi ya zauna masa, Leena ta kalli mutumin sai kuma ta kalli Malik haka nan taji zuciyar ta ya tsinke ganin kaman da suke yi, Malik kuma shi tunanin sa ai ɗan uwan Leena ne, dole kila suyi kama, da hannu Mutumin ya nuna musu kujera su zauna wanda har sannan bai ɗago ba, gaishe shi da Malik yayi yasa ya janye idon sa akan system ɗin zuwa gare su, da sauri ya mike tsaye yana kallon Malik cike da mamaki bakin sa na rawa ya furta "Yarima!!!" Malik da Leena suka kalli juna, ya mayar da kallon sa kan Leena yace "Lil sis?" Idan ban samu more reaction da yawa ba mu da update sai Monday, thank you. *BEHIND THE PALACE WALLS* *YOTA* Wattpad © Jiddatulkhayr Instagram © Jiddatulkhayr writes Chapter 67 Let's dive into the 'The palace walls' Leena was sitting, but she was lost in thought, gaba ɗaya kan ta ya kulle waye kuma Lil sis?, sannan kuma bata gane wai Malik Yarima ba ne, quite sure yana mugun kama da Malik, toh ita kuma me nata?, ko dai da wani abu da bata sani bane dan kowa yana cewa tana kama da Malik, ta kalli Malik da shima yayi nisa cikin tunanin sa, shima a wajan Malik ɗin hakan ne, one thing da ya kawo doubt a lamarin gaba ɗaya, yadda sometimes Umma ke ɓoye masa abu, toh Leena kuma fah?, sai sannan ya ɗaga kai ya kalle ta yaga ita ɗin ma shi take kallo, ya kalli agogon ɗakin sai kuma ya mike yace "Kar mu rasa flight ɗin mu, Habibty" ta miƙe itama jiki a sanyaye ta fara haɗa kayan su. Suhaif dake zaune a office ɗin sa gaba ɗaya ya rasa wani tunani zai yi, ji yake kamar Malik zai gudu masa a karo na biyu, ya share hawayen daya gangaro masa, wayan sa ne ya fara ringing, kallon Granny ne yasa yayi picking, tana zaune Babban parlorn ta kamar ko da yaushe littafi a hannun ta kana ganin ta kasan tana cikin tashin hankali, ga mai martaba zaune shima a gefen ta, sai wata mata da take mid 50s ɗinta wanda tun ɗazu sai kuka take yi, Mai martaba yana ta basu baki wanda yana cewa abi komai a hankali, jin Suhaif yayi picking call ɗin tace "Suhaif kar su bace mana a karo na biyu" Suhaif yace "Granny na karɓa address ɗin su, sannan ina da access da su yanzu ba zasu ɓace mana ba" Granny tace "Ka dawo gida yanzu, ka duba available flight ka dawo" yace "Toh Shikenan" daga haka ya katse kiran. Bayan gateman ya buɗe mata gate ɗin yana gaishe ta ta amsa a takaice sannan ta shiga cikin compound ɗin, Hasna da ta fito daga part ɗin ta, daga gani fita zata yi ta ɗan risina tace "Ina wuni Mama" Mama tace "Lafiya kalau, Hasna, fita zaki yi kenan" Hasna na Murmushi tace "Eh Mama" daga haka ta kama hanyar shiga main gidan tana cewa "Toh Allah ya tsare" Hasna kuma tayi bakin gate. Bayan Mama ta shiga parlorn Layla, sai ga Layla ta fito daga kitchen tana kallon Mama sai ta fara dariya, Mama tace "wannan wani irin shashanci ne? Ko dama lafiyar ki?" Layla ta karasa cikin parlorn ta fashe da dariya tace "Wallahi Mama kawai so nake na ganki" Mama ta ja tsaki ta karasa parlorn ta zauna, tana gaishe ta, Tace "Leena fah?" tace "Tana ciki tana bacci, bari na ɗauko ta" daga haka ta wuce ciki sai gata ta fito rike da Leena ta mika ma Mama, sai kuma ta zauna, Can Layla tace "Mama kina ji an kore su Leena a gidan su?" Mama tace "kamar ya an kore su? Ba gidan Daddyn suke ba?" Layla tace "Ah toh, toh dai watsi akayi da kayan su a titi wai an sayar da gidan shine Mai gidan yace yana bukatar gidan sa" Mama tace "ikon Allah toh waya sayar?" Layla tayi dariya tace "Mama ai kema kin san halin kawar ki, wallahi zan iya rantse wa ita ce ta sayar saboda taga yadda Leena zata yi kuma ina da ya kinin ita ce ma tasa aka kore sa a aiki" Mama tace "Ina mamakin yadda kika san halin ta har haka, wallahi tun muna yara take da halin Mugunta, sannan Mamar Leenan nan wallahi tun tana amarya take kai ta gun bokaye" Layla tace"Mama kenan, taya ba zan san halin ta ba, wallahi tun yadda take supporting auren nasa da walakin, amma Mama abun ya isa haka mana, dan Allah kiyi wani abu akai" Mama tace "Ki kyale ta, har sannan ina rike da ita a rai, ace haihuwar fari, 'yar ki ko shekara bata yi ba tasa dole sai da yayi miki kishiya ita kuma da aka mata kishiyar naga har sannan tana faɗa akai, kuma wannan Aminan ne ke zuga ta" Layla tace "Kin ce tun Maman Leena na amarya take zaluntar ta Kinga yanzu Leenan ma bata barta ba dan Allah Mama kiyi wani abu" tace "Ki kwantar da hankalin ki Layla, takanas zanje gidan na zube gaban Hajiya da ita kanta Maman Leenan ke harma da Daddyn nasu saf zan iya na dinga sharara kuka ina cewa su yafe min, sharrin shaidan ne yasa na zuba ido Khadija na cutar da su nayi shiru, komai tun daga A to Z zan faɗa musu" Layla ta kyalkyale da dariya tace "Do so, please Mama" Mama tace "kina wasa da Ni kenan, gobe zan tafi gidan na su". Bayan Leena sun sauka Rayyan ne ya ɗauko su daga airport wanda har sannan dukkan su kansu a kulle, bayan yayi parking Malik dake gaban motar ya dube sa yace "Sannu da kokari mun gode" Rayyan yace "Haba sai kace wani abun kuma? Bakomai wallahi" ya zaga ta inda Leena take ya buɗe mata sannan ta sauka, kayan su dake bayan motar ya buɗe ya dauka musu suka wuce cikin gidan, Bayan sun shiga nan in da suke sai ga Ayaan yana sallama, Leena ta amsa ta amsa tace "Ayaan shigo mana" Ayaan ya shiga hannun sa rike da warmers, Malik ya miƙe ya karba yace "Kace da Ammi mun gode" Ayaan yace "Toh" sai kuma ya gaishe su, Leena tace "Baka je school bane?" Yace "Ai munyi Hutu" tace "Ma Shaa Allah" daga haka ya juya ya fita. Rayyan ya daga wayan sa dake ringing yakai kunne, bayan sun gaisa Lawyern ya faɗa masa bayanan wanda ya sayar da gidan, Rayyan was totally shock, yama gagara magana dan baya ma son yayi believing wanda aka faɗa masa, har mutumin ya gama masa bayani Rayyan ya kasa cewa komai, mutumin ganin haka ya ɗauka ko Rayyan baya ji ne daga karshe ya katse ya shiga kiran Daddy, Rayyan ya jinginar da kansa jikin motar ya lumshe ido yana jin yadda zuciyarsa ke kuma, taya Mummy zata yi haka just because she hate her. Bayan Leena ta gama huta wa, ta mike   zuwa ɗakin Ammi, ta shiga da sallama, Ammi ta ɗaga kai tana kallon ta har ta karasa cikin ta zauna, Ammi tace "Ya hanya kuma?" Tace "Alhamdulillah Ammi, Ina wuni" Ammi tace "Lafiya Klau" Leena tace "Ammi wani abu nake son tambayar ki" Ammi tace "Ina jin ki Leena" Leena ta rasa ta ina zata fara ma Ammi bayanin abin da ke ranta, sai kuma tace "Ammi da gaske Ni da Malik muna kama ne?" Ammi tace "Eh, kuna yana yi dai" Leena ta cigaba da kallon Ammi, Ammi tace "Menene?" Leena tace "Ammi toh dangin Abbah na fah?" Ammi ta dinga kallon ta sai kuma ta sauke idon ta kasa ta kasa cewa komai, Leena tace "Ammi dan Allah ina so na sani ne" sai sannan Ammi ta ɗaga ido ta kalle ta tace "Shi Malik ɗin ne ya aiko ki ki tambaye Ni?" Ta girgiza kai da sauri tace "Wallahi Ammi ba shi bane" Ammi tace "Me yasa toh baki taɓa tambaya ta ba sai yau?" Leena ta numfasa tace "Wallahi Ammi wani abu ne ya fara wanda ya ɗaure min kai" Ammi tace "Me abun?" Leena tace "Ammi bayan tafiyar mu Abuja ne, mutumin da muka je office ɗin sa yana kallo mu ya rikice ya miƙe tsaye yana pointing Malik ya furta 'Yarima' Ni kuma yace min 'Lil sis' so wallahi gaba ɗaya na zama so confused" Ammi na kallon Leena bata ko kyafta ido, ta share zufan daya taru mata tana kallon Leena har sannan, Leena tace "Ammi abin da ya ɗaure min kai wallahi baki ga kaman da suke da Ya Malik ba, Ni wallahi na ɗauka ma 'yan biyu ne, shi kuma Ya Malik wai nine nake kama da mutumin" Ammi da tayi nisa cikin tunani tace "Amma akwai abun da mutumin ya faɗa muku bayan wannan?" Leena ta girgiza kai, Ammi ta miƙe bata son Leena taga hawayen ta ta juya mata baya tace "Ban san me zan ce miki ba, but koma menene Allah ya mana mai kyau" daga haka ta wuce ciki tana share hawayen ta, Leena ta bita da kallo tana jin zuciyar ta na karye wa, hakan yana nufin Ammi ta san wani abu ne? And tambayar da ta ma Ammi shi kaɗai take buƙatar sanin amsar sa, daga haka ta miƙe zuwa part ɗin Hajiya dan ta ce mata sun iso, a compound ta haɗu da Mummy kamar zata wuce sai kuma taji ba zata iya ba, tace "Ina wuni Mummy" Mummy da dawowan ta gidan kenan ta tsaya tana kallon ta da fara'a a fuskar ta abin da Leena bata taɓa gain ta mata ba knn tace "Lafiya kalau Leena, ashe abin da ya faru kenan?" Leena na Murmushi tace "Eh wallahi" Mummy na kallon ta tace "Ai Matsalar auren talaka kenan, ke kuma naga kin fi bin jajayan fata, amma in banda abin ki me ya kaiki auren fakiri? Yanzu gashi kin jibge mana a gida" Leena tayi murmushi kawai amma maganar ta ya dake ta, ta ɗan Kalle ta tana son tafiya Mummy tayi saurin cewa "Yanzu shi baya kunyar zama cikin sirkan sa? Abun da mamaki wlhi, toh Allah ya kyauta, amma kam ace duk gadarar kyaun kin nan ki kare gidan talaka? Ko da yake naga kakan nin naki na Niger ma talakawa ne Ammin ki ne kamar ta auri me kudi ko? Shi yasa abin ba zai dame ku ba" Leena da taji ranta ya gaba ɓaci bata san sanda ta bar wajan ba tayi hanyar ɗakin Hajiya. Da yamma Hajiya ta doka sallama a kofar dakin Ammi, Ammi ta fito ganin Hajiya tace "Ahh Hajiya ki shigo mana" Hajiya tace "A'a Kinga ba zama ya kawo ni ba, ace yanzu fisabilillah yaron nan baida Lafiya ace tun da muka duba shi sau ɗaya Shikenan?" Ammi tace "Wallahi Hajiya ina tunanin sa amma kar suga kamar muna musu zarya ne a gida" Hajiya ta rike Haba tace "Toh wallahi ki kiya ye Ni" Ammi tayi dariya tace "Toh zan je" Hajiya tace "A'a wannan ba maganar zaki je bane, ki shiga ki sa kayan ki, Leena ma yanzu ta bar waje na nace tace ta shirya nima kayan zan saka sai muje duk gaba ɗayan mu Kinga ai zasu san mun damu da shi" Ammi tace "Toh shikenan barin sa kaya" daga haka ta shige ciki, Hajiya kuma ta wuce sashin ta. Hajiya Amina tayi sallama, Mummy dake cin abinci a parlorn ta amsa mata, ta shiga cike daga gani kasan gulma ce ta kawo ta, Mummy ta dinga dariya tace "Kai Amina kina son gulma haka?" Hajiya Amina tace "Toh wallahi ban daɗe da shigowa garin nan ba, cewa nayi idan ban zo nan ba hankali na ba zai kwanta ba" Mummy tace "Ah toh, da kinyi missing" tafawa suka yi suna shekewa da dariya, Hajiya Amina tace "Can you imagine, na haɗu da Fatima ta ɗauke min kai, ina da niyyar mata magana naga tayi kamar bata sanni ba shi yasa na kama kaina Nima amma abun da mamaki wallahi" Mummy tace "Toh ai sai tayi, ke kika biye mata da har zaki mata magana yanzu ai maganin ki" Hajiya Amina tace "wallahi Banga laifin ta ba, ni na ja ma kaina". Daddy bai taɓa jin ransa yayi mugun baci ba irin na wannan ranan, akan meyasa Khadija zata masa haka? Gidan nata ne da har zata sayar dan taga yadda Malik zai yi, ya shiga motar sa a zuciye yana jin komai ma zai iya faruwa dan bai damu bama, tuki yake amma yana tunanin hukunci da zai dauka. Hajiya ta fito ga Leena a bayan ta sai Ammi dake rike da hannun Ayaan zasu je gidan Mami duba Nawaf, anan compound suka haɗu da Mummy ta fito raka kawarta Hajiya Amina sai shekewa suke da dariya kamar basu gansu ba, buɗe gate ɗin mai gadi yayi Daddy ya shigo da motar sa ko gama parking bai yi ba ya sauka, Hajiya ta kalle Ammi ganin yadda Daddy ke huci, sai ga Mama ta shigo gidan ita ma, ganin kowa a compound ɗin tayi hamdala dan yayi mata daidai, hakan ne zai sa ta fasa kwan kowa yaji warin, Daddy yayi kan Mummy kamar zai tashi sama yana huci dan shi hankalin sa baya kan Hajiya Amina infact bai ma ganta ba, Mummy ta ja baya ganin yanayin sa tace "Lafiya?" Daddy da karfi ya fara magana yace "Akan wani dalilin zaki tsayar min da gida sannan kisa a kore su daga gidan???" Rayyan da buɗe gate ɗin sa kenan ya tsaya kallon Daddy wato shima ya samu labarin kenan da sauri ya dafe kansa dan baya son ace sun samu matsala, jin furucin Daddy yasa Leena ta kalli Ammi da Hajiya, Ammi tace "Mu tafi Hajiya kar yamma yayi" Hajiya ta mata wani kallo tace "Kina jin abin da ke faruwa zaki ce mu tafi?" Daddy na kallon Mummy da wani expression yace "Ba zaki bani amsa ba?" Ta ɗan kalli mutanen compound ɗin sai kuma ta marairace masa tace "Haba dear, ka tsaya kaji mai ya faru amma sai ka hauni da faɗa a cikin mutane? Idan ba kuma Ni na sayar ba fah? Na tabbata wannan makircin matar ka ne" Daddy ya ɗaga hannu zai mare ta sai kuma ya sauke da sauri, Mummy wani kallo take masa, Hajiya Fatima ta matso kusa ta zube gaban Daddy ta fashe da kuka hakan yasa hankalin Mummy tashi tace "Ke kuma me haka? Ki tashi mu shiga ciki" ta karasa zata ɗago ta Mama ta warfe hannun ta, su Ammi dai suna tsaye suna kallon ikon Allah, Nisreen kuma jin hayaniya yasa ta fito dama tazo gida weekend, Mama ta fara kuka tana "Dan Allah Baban Rayyan ka yafe min" Daddy da mamaki yake kallon ta dan reaction ɗinta abin mamaki ne, Hakan yasa ke ɗaga wa Mummy hankalin, Hajiya ta gyara tsayuwar ta tace "wannan matar makira ce, kawar Khadija ce tun budurci, yanzu haka kila ta zo tonan asiri ne", Daddy yace "Please ki tashi, sannan yafiyar me kike magana akai? Kin min laifi ne?" Mama ta fara share hawayen tana sheshsheka tace "wallahi, tun da ka auri Maman Leena babu abin da be faru a gidan nan ba, yanzu na tuba kafin na mutu shine nake son kai, Hajiya, Maman Leenan, da ita kanta Leenan ku yafe min, kai hatta har da Rayyan ma ina so duk ku yafe min", Gatekeeper da gudu ya wangale gate ɗin motoci suka shigo compound ɗin wanda hakan yasa duk suka ɗaga kai suna kallon su da mamaki, dogare ne suka fara fitowa da gudu suka je suka buɗewa Granny kofar motar ta sauka, ga jakadiyar ta ma ta sauka daga wani motar ta karasa inda take da gudu, wasu daga cikin dogare suka wuce buɗewa mai martaba, Sannan sai ga wata mata wanda har sannan idon ta yayi mugun ja, ga kuma wani namiji da yake mid 60s ɗin sa, Ammi zuciyar ta ne ya fara bugawa da karfi ganin yadda gaba ɗaya mutanen suke kama da Leena, sai ga Suhaif wanda shima ya sauka kana ganin sa kaga Malik, hakan yasa Ammi taji kamar ba zata iya tsayuwa ba, Mummy tsabar yadda ta galalo ido waje zaka ɗauka wani abun ne ya faru, ta dinga bin mutanen da kallo dan kana ganin su kasan tabbas jinin su Leena da Malik ne, sannan kuma ka san cewa daga gidan sarauta suke, Malik da ya shigo gidan ganin su yasa zai juya, wannan matar da take mid 50s ɗinta ta kwala masa kira "Yarima!" cak Malik ya tsaya sai kuma ya juyo da gudu ta ta karasa wajan ta rungume sa tana mai fashe wa da kuka tace "Yarima kai ne wannan?" Mummy bata san sanda ta zauna dirshen a kasa ba, mai martaba ya taka har inda Daddy yake ya mika masa hannu, haka nan Daddy yaji shakkar sa da kimar sa ya mamaye sa, Mai martaba yace "Kai ne mai gidan?" Daddy yayi gathering courage yace "Eh nine" yace "Da farko ina mai baka hakuri shigo maka gida ba tare da izinin ka ba sannan har muka taso muka zo ba tare da consent ɗin ka ba" Daddy yace "ba koma"  Mai martaba yace "Idan babu damuwa ina son zamu yi magana mai muhimmanci ne, ko zamu samu karɓuwa?" Daddy ya gƴaɗa masa kai yana nuna musu hanyar parlorn sa, Granny tana hango Leena ta karasa wajan ta ta rungume ta tana mai fashewa da kuka, sai

Chapter 43 of 50