sai ta rama dukan da aka mata akan Leena da kuma rashin kunya da ta mata har tasa ana mata dariya,
Hey, sis! Please hint the star at the corner.
_By Jiddatul-khayr writes
Chapter 7
Unfortunately Daddy ne yazo ɗaukan su hakan yasa Niswa ta hakura da abin da tayi niyyar yiwa Leena but taci Alwashin sai ta dake ta ko a gida ne, Daddy na parking duk suka sauka kowa ya wuce part ɗin su, Da yamma Leena ta fito a part ɗin Hajiya tana sanye da uniform ɗin Haddan su a jikin ta Hajiya ta fito tace "Ikon Allah, toh fita kikayi?" Leena tace "Hajiya gani fah a bakin kofar ɗakin ki, takalmi nake sawa, kin san yana da wahalan shiga ne" Hajiya ta fito tana mika mata takeaway ɗin hannun ta Leena ta karɓa tana washe baki tace "Laalaa dukka dambun nawa ne? Nagode Hajiya na" Hajiya tace "Yayan ku ne ya tsiya mana" daga haka Hajiya ta wuce ciki abunta Leena na gama saka takalmin ta ta mike kawai taga Niswa tana ni fo ta, taki masa wa ta ci gaba da tsayuwa a wajan tayi kamar tana gyaran takeaway ɗin hannun ta ne, Niswa na karaso ta tace "Shegiya waye a gaba na yanzu?" Leena tayi kamar bata san da mutun a wajan ba ta wanke ta da mari sannan ta hankaɗe ta ta faɗi har takeaway ɗin ya zuɓe a kasa Hajiya ta fito da sauri tana cewa "Uwar ki ta Miki da zaki dake ta Niswa? Ni fah bana son bakin halin kun nan wallahi" Niswa tace "Ai Hajiya ita ta fara kuma Ni ba sa'ar ta bace da zata na min rashin kunya ina kyale ta" Hajiya tace "yanzu ke ɗin ba rashin kunya kika min ba idan haka ne na dake ki mana, uwar ku duk ta shafa muku mugun halin ta wallahi, riyan ne kaɗai yayo hali na da ke Allah na son sa, kuma duk bakin cikin ku akan Lina saboda kun san ta fi ku ne" Niswa ta haɗe rai, Leena ta tashi a kasa tana karkaɗe jikin ta Hajiya ta kalli dambun da ta bata duk ya wase a kasa ta buɗe baki tana bin dambun naman da kallo Leena tace "Do your worst, Niswa. Do whatever suits you. But let's be clear, you're not me, and I'm not you – God forbid. Whatever Allah blesses me with is yours to envy, not collect, kinji?" Niswa na kallon Hajiya tace "Hajiya Kinga tana min rashin kunya ko? Har sunana take kira ba Anty fah?" Hajiya tace "A'a Ni banga komai ba, sannan ai dole ta ɗena kiran ki Anty tunda kin zubar da girma" Niswa ta saya tana huci Leena ta harare ta, Niswa ta kuma hankaɗe ta har sai ta Leena taji ciwo jini ya fara zuba a hancin ta Hajiya tace "Lalle Niswa har Ni zan Miki magana ki kuma hankaɗe ta toh wallahi bari yayan na ku yazo, bar min gida ki wuce can inda kika fito dan ni bana son halin mugunta" Hajiya ta kalli Leena da jini har ya fara fita a hancin ta tace "Na shiga uku, kalli yadda kika fasa mata hanci" Niswa ta juya ta kalle ta sannan ta wuce kamar zata tashi sama, a hanya taci karo da Ya Rayyan amma ko ta kansa bata yi ba ta wuce sa ya ɗan tsaya yana kallon ta sai kuma ya juya zai karasa part ɗin Hajiya ya kuma haɗuwa da Leena da har fuskar ta yayi mugun ja ga hancin ta jini yana zuba ya tsaya yace "Leena" itama bata ko kalle sa ba ta wuce abun ta ya karasa yaga Hajiya tana share dambun naman da ya zuɓe a kasa yace "Sannu da aiki Hajiya" ta kalle sai sai kuma tace "sannu riyan" ta karasa kwashe wa ta kai waist bin ta zuba already har Rayyan ya shiga parlorn ta yana jira ta karaso danna wayar sa ta same sa yana yi ya ɗaga kai ya gaishe ta ta amsa sai kuma tace "Riyan kasan me?" yace "ina jin ki Hajiya" tace "Gaskiya ka jama kannan ka kunne dan sun sa yarinyar nan a gaba haka kawai fah Niswa ta karaso nan ko kunyan ta bata ji ba ta fara dukan ta har sai da taga ta fasa mata hanci sannan ta zubar mata da dambun da ka tsaya mana, Ni abun da ya dame ni ma shine ko ta saya ta kwashe min Abunda ta zubar min A'a kawai tayi wucewar ta abunta" Rayyan ya kura ma Hajiya ido har ta karasa magana Hajiya ta kalle sa tace "Ji gantalelle, toh me kuma na kura min ido da kayi?" Yace "Hajiya kika ce ita ta fasa mata hanci?" Hajiya tace "toh na maka karyan dana saba" yace "kiyi hakuri ba haka nake nufi ba" daga haka ya mike. Leena na shiga parlorn ta haɗu da Ammi, Ammi tace "lafiya Leena? Me ya same ki? Kuma ya baki tafi Haddan ba?" Leena ta wuce ɗakin ta, ta ajiye hijab ɗinta da har ya ɓaci a kan gado sannan ta wuce toilet Ammi ganin ta shiga ɗakin ta yasa ta tashi ta bi ta har cikin toilet ɗin ta taya ta wanke fuskan ta, mata wanka gaba ɗaya tayi sannan ta kama hannun ta suka fito tana kallon ƴarta da tausayi tace "sune suka ji miki ciwo ko?" Leena tace "Eh Ammi, saboda abinda ya faru ɗazu a school shine yanzu ta dake ni, Hajiya na mata magana amma ta share ta ma" Ammi ta rungume ta tana tausayin ƴar nata tace "Toh bayan a school ɗinma naga ba laifin ki bane ai" kana ganin fuskan Ammi kasan ranta a bace yake Leena tace "Ammi dama kene kike hanani rama abinda suke mun, toh yanzu kam zan fara ramawa saboda hakan ne yasa kullum suke cin zali na" ta karasa maganan tana me fashewa da kuka Ammi ta fara lallashin ta Sallama Rayyan yayi a bakin kofar na su Ammi ta sake ta sannan ta koma parlorn tana me amsa masa sallama sai daya shiga kuma ya fara jin kunyan Ammi yama rasa mema zai ce mata sai yace "Am dama Ammi ina so naga Leena ne" Ammi ta koma ɗaki ta kira Leena har yanzu kana ganin fuskan ta kasan ran Ammi a bace Leena na fitowa Ammi ta wuce ɗakin Leena ta ɗauki uniform ɗin nata ta wuce laundry dan wanke mata, yana kallon Leena yace "Leena tell me everything nasan baki min karya me ya haɗa ki ke dasu Niswa" ta fara narrating masa tun abinda ya faru daga school har zuwa yanzu kana ganin sa kasan ransa yayi mugun ɓaci ya tashi without saying anything to her ya fice a ɗakin part ɗinsu ya wuce Luckily Mummy bata nan ɗakin sa ya wuce ya ɗauko belt ya wuce ɗakin su Niswa yanda ya buɗe kofar da karfi yasa duk suka juya suna kallon sa Niswa tayi saurin cewa "Yaya wallahi karya take maka" wani kallo ya wurga mata key yasa ma kofar yadda ba zasu iya guduwa ba ya zane Niswa yadda ransa ya ke so tana ta ihu tana basa hakuri Nisreen kam ta tsorata iya tsorata sai kuka take ya juya yana kallon ta yace "wato harda ke ko?" ta girgiza masa kai tana basa hakuri yace "kina karama kina munafurci ba" zuba mata belt guda uku yayi yace "sa'an ki ɗaya ke karama ce but next time ki gwada zaki sha mamaki na" kuka take tayi yace kuna jina duk suka gyaɗa masa kai yace "wallahi daga yau ko kallon Banza kuka sake ma Leena wallahi sai na muku abinda ya fi haka" daga haka ya buɗe kofar ya fita ya barshi suna ta kuka zai fita daga gidan yaga gatekeeper na buɗe gate yasan Mummy ce zata shigo da mota da sauri ya buya a bayan ɗakin mai gadi har ta shigo da motar tayi parking yana ji masu gadi na gaishe ta Amma ta share su tayi wucewar ta sannan Rayyan ya sauke ajiyan zuciya ya fito a inda ya ɓuya ya karasa gate ya musu sannu da aiki sannan ya wuce masallacin unguwar yana jira lokacin Magrib ta karasa tunanin yadda yau zasu kaya da Mummy ne kawai yake yi da sauri ya cire wayar sa yasa a DND Qur'an ya ɗauko ya fara karantawa. Mummy da ta gama cika tayi fam sai trying numbern Rayyan take baya tafiya ta kuma kallon ƴaran nata mata tace "wallahi yau sai Rayyan ya zaɓa ko Ni Ko wannan matar, ina har nine Rayyan zai iya dukan ku akan yarinyar dana fi tsana duk duniya, tun dana gwada bana son yarinyar nan kuma shi ya fara son ta" sake dialing number din nasa tayi taga baya shiga ta fita a part ɗin tana huci ta wuce part ɗin Hajiya dan tasan yawanci idan baya dakin sa toh yana dakin Hajiya ne, ta shiga parlorn Hajiya da sallama Hajiya ta amsa tana mamakin yadda taga kalar Mummy, Mummy ta gaishe ta Hajiya ta amsa da fara'ar ta tace Hajiya na ɗauka Rayyan yana nan ne ko dai kin aike sa ne?" Hajiya tace "A'a dai baya nan dan tun ɗazu daya shigo nan kuma sai ya fita to be sake shigowa ba" daga haka tace "sai anjima to" ta tashi ta fice, shigan Mummy part din Hajiya Daddy ya dawo gidan ita kuma saboda ɓacin rai bata ma lura da motan sa a parking space ba, kawai ta wuce part ɗin su Leena ta ban kaɗe kofar parlorn ta tsaya nan bakin kofa Mummy dake kunna burner a parlorn ta ɗaga kai ta kalle ta Mummy tace "Ina Agolar ƴar ta ki take? Wato saboda sunyi faɗa shine ta haɗa karya da gaskiya ta faɗawa yayan su dan ta shiga tsakanin su kamar yadda kika shiga tsakani na da shi ko? to ki haja ma ƴarki kunne dan wallahi ba ita ba harke sai kinyi dana sanin shigowa gidan nan, sannan abu na biyu idan ma lashe min zuciyan ɗa kika yi toh kinyi kaɗan dan yanzu zan ɗau mataki" Sai sannan Ammi ta kalle ta a ranta tana ji wannan lokacin ba zata iya kyale Mummy ba saboda itama ranta ya ɓaci da yadda suka fasawa ƴarta hanci tace "Toh ai idan kin isa da naki ɗan ai naga ba sai kin zo nan kina ɗaɗɗaga jijiyoyin wuya ba tun a ɗaki zaki tanƙwara sa" Mummy tace "Lalle har Ni zaki mayarwa Magana" Mummy ta shige cikin parlorn da zuciya sai kuma tayi turus ganin Daddy a zaune a dining room yana kallonta Daddy yace "A'a karaso mana" ta juya zata fita yace "wai ke meyasa Khadija kwatakwata baki son peace, You don't want peace to reign, Why?" ta juya tayi wuce war ta ko ta kansa bata bi ba ita yanzu damuwar ta ta haɗu da Rayyan ne. Daddy ya juya yana kallon Ammi yace "Hauwa nasan ki da hakuri Please ki kara akan na da kin ji sirbajo na" Murmushi Ammi tayi bata ce komai ba, kiran Magrib da akeyi ne yasa Daddy wuce wa masallaci. Ko da aka idar da Sallah Daddy ya hango Rayyan da hannu ya masa alama da ya zo hakan yasa ya karasa yana tsosa kansa Daddy na kallon sa yace "yau kuma meya faru?" Yayi narrating duk abinda ya sani yace "Daddy idan kana ganin ba haka bane just ask Hajiya a gabanta akayi komai" yace "No wonder Banga Leena ba, it's okay" daga haka yace "tashi mu tafi" yace "Daddy zan saya ma Hajiya abu ne a can bakin hanya daga haka ya tashi ya fita sai yanzu yaji haushin rashin fita da mota da beyi ba amma yanzu ko gigin wasa yasan ba zai iya shiga gidan nan ba har sai Mummy ta huce, ciro wayar sa yayi a Aljihun sa zai kira wani abokin sa to his own surprised yaga missed calls ɗin mummy wajan 18 hamdala yayi da ya sa wayar a DND tunani ya fara ko ya tafi asibitin su ne yaga shi ba zai iya kwanan asibitin ba kawai ya kira friend ɗinsa fu'ad yana ɗauka wa yace "how far fu'ad? Kana gida ne?" Fu'ad yace "Eh ina gida, zaka zone?" yace "Eh" daga haka ya mayar da wayan sa cikin Aljihun sa ya tare taxi ya Kaisa har kofan gidan, yana isa ya kira fu'ad, ya fito yazo ya same sa da masu gadi suna gaisawa fu'ad yace "kai fa ka iya munafurci gidan ne kullum idan kazo sai kayi tayi kamar bakon ka" Rayyan na dariya yace "Toh kawai saina kusa kaina ciki?" Daga haka suka kama hanyar BQ Rayyan yace "Wait, barin fara gashe da Mama tukun" fu'ad yace "Toh, muje" Sallama fu'ad yayi ya shiga tukun yace "Mama ga Rayyan yazo gaishe ki" tace "Toh ya shigo mana" yace "Toh ai sai ka shigo an baka izini ustazi" ya karasa maganar in funny tongue, Rayyan ya shiga parlorn da sallama daga Mama sai kanwar fu'ad Hasna ya zauna nan kasan carpet yana gaishe ta ta amsa da fara'ar ta tace "yau kuma wani rana ga Rayyan anan gidan" ya shafa kansa ɗan rabon sa da gidan ya ɗan jima kuma Fu'ad aini hin abokin sa ne tunna yaranta yace "wallahi Mama abubuwa ne suka ɗan sani gaba kwanan nan ga kuma aiki" fu'ad yace ba wanin na! Rayyan ya ɗan harare sa Mama tace "To Allah yayi jagora ade dunga zumunci dai" yana murmushi ya amsa gaisuwar Hasna tace "Yaya ina wuni" Ya amsa da fara'a yace "Lafiya kalau, ya karatu?" tace "Alhamdu Lillah" yace "Ma shaa Allah" daga haka yace "Mama bari mu shiga ciki" tace "Toh shikenan" suna fita Hasna ta tashi da gudu tayi cikin gidan ta ban kaɗe kofar Husna ta juyo tace "ke dalla wata irin mahaukaciya ce ke" tace "dalla Albishir na kawo Miki" tace "mene?" Hasna tace "Ya Rayyan ne yazo gidan nan" Husna tace "really? Wayyo Allah na". Rayyan yace "kai anan fa zan kwana sai gobe na koma gida" fu'ad yace "kace zuwan naka da biyu mana" Rayyan ya ɗan yi dariya yace "Not at all" Husna ce tayi sallama a kofar dakin sannan ta shiga taci uban wanka ga wani kamshi da take zuba wa kallo daya Rayyan ya mata sannan ya ɗauke kansa shi abinda yasa baya son zuwa gidan saboda Husnan nan ne Fu'ad ya mata wani kallo ganin yadda ta yi wani shiga ga kamshin da take yi , Nan ta zauna kan cushion ta wani karya murya tace "ya Rayyan ina wuni" ya amsa idon sa na kan wayan hannun sa tace "me za'a kawo maka ne?" ya ɗan kalle ta jin yadda take magana sai fari take da ido shi abun dariya ma ya basa amma ya maze yace "thank you, Husna. Daga gida nake so karki damu. Kiran sallahn isha da aka fara yi yasa ya kalli fu'ad yace "mu tafi masallaci ko" kai kawai fu'ad ya gyaɗa masa dan shi ya sani wannan iskan cin da Husna take idan taga Rayyan, gashi yana magana Mama zata hayyaya ko masa tace ina ruwan sa Husna tace "sai kun dawo kafin nan barin ɗaura muku abinci". Bayan Daddy ya dawo daga sallan isha'i ya shiga ɗakin sa ɗauko abu sai ga Mummy ta bi sa ta zauna bakin gadon sa tace "Daddyn Rayyan ina son muyi wata magana ne" ya juya ya bata full attention ɗin sa yace "ina jin ki dear" tace "Naga kowa yayi wasi da maganar ne babu me yinta shine nace barin zo na same ka da ita" yace "am all ears , just go ahead" tace "dama maganan auren Rayyan ne naga Kai baka ce komai ba gidan su yarinyar ma sunyi shiru, shine nace tunda tambaya akayi kawai yanzu kuje a sa rana, dan ni wallahi na gaji da Rayyan a cikin gidan nan" Daddy yace "In shaa Allah zan muje a sana ranan, amma zance kin gaji da shi a gidan nan kina uwa be kamata ki faɗa haka ba saboda bacin rai, kuma a wannan lamari Ni banga laifi yaron nan ba, sai dai akasarin laifin nasu Nisreen ne sai dai ban san wani kalan ɗaukan mata ki yayi ba, zan ja masa kunne, kema ki jama ƴaƴan ki kunne su fita harkar Leena, ke kuma ki kama girman ki dan Kinga tun sirbajo bata tanka miki yanzu harta fara Kinga wata rana zaki ji kunya sannan kuma me na zuwa har part ɗinta idan banda jama kai raini?" Tace "ai kasan matar ka ƴar gold ce baka kwanar a taba maka ita" daga haka ta mike ta fita tana kudirin sati 4 kawai za'a sa na tare wa dan ita ba zata iya juran ganin Rayyan yana iya dukan kannansa akan Leena...
A taimaka amin voting mana
Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes
Chapter 8
Alhamdu Lillah
Washe gari, Friday! ana idar da Sallah ya zauna yayi lazimin shi tare suka koma gida da Fu'ad suka shiga suka gaida Mama sannan suka koma BQ in da ɗakin Fu'ad yake, suna shiga Rayyan ya Kuma komawa kan gado yana dannan wayan sa sai can ya tashi ya zauna yana kallon Fu'ad yace "Yau short day ne, gashi zan tafi office, yanzu kuma idan nayi wanka anan ban san kayan da zan sa ba, so, I think zan tafi gida kawai" Fu'ad yace "ka tsaya kayi breakfast mana idan ya so sai mu fita tare nayi dropping ɗinka" Rayyan yayi shiru yana tunanin yanzu ta'ina ma zai fara shiga gidan yanzu idan ya koma yasan Mummy na nan shi kuma ya fi so ya koma lokacin da bata nan idan ya so ita ta zo ta same sa, tunawa da yayi da kayan sa a wajen me Laundry yasa ya tashi yana kallon Fu'ad yace "ban keyn motar ka zanje na karɓo kayan na awajen mai wanki" Fu'ad yace "da sassafen nan?" ya karasa maganar yana mika masa keyn, ya amsa ya fice. Ammi ta sake leka ɗakin Leena taga har sannan tana kwance tace "Leena makarantar fah? Ko ba zaki je bane ina tashin ki kina komawa ɗin" tashi tayi ta zauna tana murza idon ta tace "Ammi ni bazan je school yau ba" lokacin da take ba Ammi amsa Already ta bar wajan ma taje tana sa abincin da ta dafa mata a lunch box ɗinta, Ammi ta shigo da niyyar ta taya ta ta shirya amma kuma still ta kuma kallon Leena kwance ta karasa ta tana cewa "Leena yau dai lafiyan ki klau kuwa?" ta yaye duvet ɗin dake jikin ta ta taɓa jikin ta taji da zafi tana kallon ta tace "Baki da lafiya ne?" ta gyaɗa mata kai tace "yau ba zan iya zuwa school ba" Ammi tace "Toh shikenan barin ma yayanku magana idan zai rubuta magani ne ba sai muje asibiti ba fine" daga haka ta gyara mata kwanciyar ta ta rufe ta sannan ta fita taci gaba da aikin da take yi. Husna ce ta shiga ɗakin yayan nata hoping zata ga Rayyan ajiye tray ɗin hannunta dake ɗauke da breakfast ɗin da ta kawo musu tayi, ta ɗaga kai tana kallon yayan ta tace "Yaya ina Ya Rayyan ɗin?" Sai sannan ya ɗaga kai ya mata wani irin kallo yace "ke wacca irin yarinya ce mara kamun kai, kina tunanin a haka ne zaki burge sa Look! Rayyan ya tsana irin mata masu halin ki, and I'm warming you wallahi kika sake idan ya dawo kika shigo nan kina wannan abun naki zan iya kakkaryaki" wani irin kallo take masa ta kasan ido ta tashi kenan zata fita sai ga Rayyan ya shigo da sallama ja da baya tayi tana washe baki sannan ta gaishe sa kallo ɗaya Rayyan yayi mata sannan yace "yau ba lectures ne?" tayi fari da ido tace "sai 10am muke da shi" daga haka be kuma ce mata komai ba yayi wuce War sa cikin dakin ya shiga toilet, bayan ya gama shiri ya fito Fu'ad na kallon sa yace "shikenan ai yau ka gama min da turare, kai gashi fesawan hauka kake yi" Rayyan yace "Dalla ba wani fesawan kirki nayi ba fa". Nisreen da Niswa suka fito a sashen su suka karasa wajan motar suka shige Nisreen tace "Anty, Leena ba zata je bane? Naga yau mun riga ta shiri ne" Niswa tace "toh ke ina ruwan ki da Ita? Driver na karaso wa wallahi tafiya zamu yi" Nisreen ta rufe bakin da hannayen ta da sauri tace "Kin manta me yaya yace?" tace "ai bata isa tace dukan ta nayi ba kuma waya hana ta fitowa da wuri" sai ga driver ya karaso Nisreen na kallon sa tace "Tafiya zamu yi yanzu" yace "Okay, dama gani nayi kamar baku gama haduwa ba ne" tace "kayi Abunda nace maka kawai" daga haka ya shiga ya tada motar suka bar gidan. Suna cikin breakfast yaji wayan sa na ringing dubawa yayi yaga Ammi ke kiran sa ya katse kiran sai ya kira ta back tana daukawa ya gaishe ta ta amsa tace "Ka fita ne Rayyan?" yayi shiru sai kuma yace "Menene Ammi?" tace "Dama Leena ce bata jin daɗi nace ko zaka Duba ta kafin ka fita" yace "bani gida amma yanzu zan karaso na dubanta ɗin" daga haka ta masa sallama. Tare da Fu'ad suka fita akan Fu'ad zai yi dropping ɗin sa suna hanya daidai mashigan unguwar ta su suka yi clashing da motar Mummy amma ita hankalin ta na kan gaban ta ne sai da Rayyan ya sauke ajiyan zuciya dama can baya so ya haɗu da ita a gidan dan zata iya hana shi duba Leena a bakin gate ɗin gidan su Fu'ad yayi parking Rayyan na kallon sa yace "Thank you guy, sai munyi waya" fu'ad yace "Okay, ka gaida su Mummy" daga haka ya shiga cikin gidan yana amsa gaisuwar da masu gadi ke masa direct part ɗin su Leena ya wuce yana bakin kofa parlorn yayi sallama Ammi ta amsa masa tace "shigo mana" yana shiga parlorn tace "mu wuce ciki kawai" yana shiga ya ganta kwance ya ɗan taɓa ta yaji jikin nata yayi mugun zafi yace "Ammi tun yaushe ne ta fara jin jikin?" Ammi tace "tace min tun jiya da daddare ne ya fara mata Amma Ni kuma sai da safe take faɗa min, ban ma ɗauka jikin yayi serious ba sai da nake bata breakfast haka ta dinga amai yanzu tayi ya kai sau uku" yana kallon Leena yace "ina ke Miki ciwo" ta fara pointing masa wajajan da take jin ciwo da hannun ta" Rayyan ya tashi yana kallon Ammi yace "Ammi barin je sai na kawo abubuwan da za'a mata magani" tace "Toh" yana fita parlor zai fita ya ci karo da Daddy ya gaishe sa ya amsa masa yace "ka duba Leena ɗin?" yace "Eh, yanzu zanje na dawo da abubuwan da ake bukata dan sai an sa mata ruwa ma" Daddy yace "Okay" Rayyan ya fice daga parlorn ido huɗu yayi da Mummy da tayi mantuwa tazo ɗauka ji yayi kamar kasa ya tsage ya shige da kyar ya iya kirkiran Murmushi ya bi bayan ta tana buɗe kofar parlorn ta juya tana kallon sa tace "bashi kake bi na da zaka biyo NI ka tsare ni?" Dariya yayi yace "kai Mummy bashi kuma? Na shigo ɗazu zan gaishe ki sai kuma naga gidan a kulle" bata ce masa komai ba har ta karasa buɗe gidan ta shiga still yana biye da ita a baya yace "yanzu fah zuwa na, ina shigowa Daddy yace inje in duba Leena bata da lafiya shine muka karasa part ɗin nasu tare" still bata ce masa a komai ba har ta wuce ɗakin ta shima ya bi ta ya rike hannunta yana kallon idon ta yace "Mummy fushi kike dani ko? Sorry jiya na bar waya na a gida Ni kuma saboda kira na da akayi ana nema na urgent a asibiti da zan tafi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 50