Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gagara tafiya jiya haka ta kasa bacci gidan Leena gave her a sleepless night, tana zaune tun ɗazu tana jiran kiran aminiyarta da tayi ta kira wayan a kashe yasa ta tura mata message. Leena da ke waya da Ammi tace "Toh Ammi ki ce su Anty Binta su zo mana" Ammi tace "Ai su Binta sun yi tafiya, amma gobe za su zo" tayi shiru sai kuma tace "Toh na zo na ɗauki Ayaan ɗin?" Ammi tace "Naga kamar fa ba hankali gare ki ba, yanzu idan nace ki zo sai ki zo?" Leena ta share hawayen da ya gangaro mata tace "Toh sai anjima Ammi" daga haka Ammi ta katse kiran. tun da tayi breakfast Ɗazu ta dawo dakin, ita kunyan Sadeeq ma ta fara ji, da ta tuna da shi, sai kuma tayi tagumi tana mamakin shi, toh dama haka ya ke ko dai ya canza ne, tana nan a haka har aka fara kiran Sallah tashi tayi ta wuce toilet, bayan ta idar da Sallah ta mike da sauri ta wuce dinning bata so idan ya dawo gidan yace zai bata da kansa, ta zuba abincin tana ci kawai taji an buɗe kofar parlorn kallon sa take har ya karasa cikin parlorn da sauri ta ɗauke  kanta, ya karasa dinning room din ya ajiye Ledan hannun sa,  idon sa a kanta ji tayi she's not comfortable yace "Okay, so you're eating already? You didn't wait for me to come back  so I can feed you?" ta ɗan kalle sa sai kuma tace "No, I'm just feeling hungry" yace "Then Why did you eat the rest of the breakfast? You should have waited for me. I would have brought us food" sai bata kuma ce masa komai ba, Ledan ya buɗe ya Ciro takeaway da ke ciki ya juye su a plate ya kai mata ɗayan gaban ta, ta ɗan kalle sa taga ita yake kallo da sauri ta ɗauke idon ta ta ɗauki wani plate ta rufe sai kuma ta mike wanting to leave the dinning area Sadeeq ya daga kansa yana kallon ta yace "Where are you going ?" tace "I'm satisfied" yace "Come back and finish your food" she frown her face tace "I'm telling you, I'm full" yace "Wait for me, let me finish eating. I've waited for you and even fed you, in the morning, now it's your turn to feed me so we can leave together" Leena ta sauke kanta kasa tana wasa da fingers ɗinta yace "I'm waiting for you" kuka zata fara masa yace "Okay, just wait for me, let me finish" ta koma ta zauna tana satan kallon yadda yake cin abincin is like da style ma yake ci, kusan duk sanda zata sata kallon sa sai taga shima ita yake kallo daga karshe ta daure taki kallon sa duk da jin idanun sa akan ta. Bayan ya gama ya mike itama tashi ta yi, tayi hanyar ɗakin ta yace "Wait, Are you not tired of sitting in the room? Why don't we take a walk around the compound? You're already wearing your veil, so let's go and see how it is" kallon sa kawai take ya tako har inda take ya kama hannun ta, ba ita ba hatta shi sai da yaji wani shock, kamar ta zare hannun ta amma be bata alama ba gaba daya jinta take wani iri a haka suka zaga cikin compound ɗin da kuma ɗakunan gidan, Lina didn't try to hide her joy, and she found herself savoring their stroll around the compound, feeling utterly relaxed in his presence, bayan sun dawo cikin parlorn still yana rike da ita akan sofa ya zauna kallon sa tayi sai kuma tayi murmushi ita ba zata iya zama kusa da shi ba, shima be san sanda yayi murmushin ba yace "zauna mana" da kyar ta iya zama yana kallon ta yace "Leena, Why didn't you love me?" ta sace kallon sa her eyes avoiding his tace "Did I say that?" yace "Yes, you said you wouldn't love me, kin tuna?" She corrected him, "I said I don't like you because you're often arrogant and you rarely talk to me, sometimes, even when I greet you, you didn't respond" yayi shiru yana kallon ta, ta cigaba "It's Only Uncle Sultan....." he cut her off, his voice raised in anger "Stopp!!! I don't want to hear it" tunawa da cewa tsawa ya mata da sauri yayi composing kansa, ya kai hannun sa fuskanta yana shafawa yace "I'm sorry Baby, I didn't mean to shout at you, it's just that I didn't want you to mention any other men's name" ta buɗe baki zata yi magana, He leaned in and kissed her deeply, their lips entwined in a romantic, French kiss, da sauri ya mike tsaye ya juya mata baya, ita kuma da sauri ta kifa kanta da sofan yace "it's almost Asr, kije kije kiyi sallah" daga haka ya fita, Leena taji hawaye na sauka mata, ta tashi gaba ɗaya jikin ta ba kwari ta wuce cikin dakin ta sai data jingina da kofa ta tsaya for almost 5 minutes, ta fara tunanin abubuwan da suka faru tun daga safe har zuwa sanda wannan incident ɗin ya faru, gaban mirror ta wuce tana kallon lips din ta, gani take kamar zata ga lips ɗinsa a jikin nata dan har sannan shock be gama barin ta ba, This was her first kiss in life, it was first time someone had kissed her so deeply, mamakin kanta take mai makon taji haushin sa sai kuma taji akasin haka, jin har an fara tada kabbara a masallaci yasa ta mike ta wuce toilet da thoughts kala da iri a ranta. Mummy da ke tsaye akan sa tace "Ba magana nake maka bane Rayyan? So ban isa da kai ba kake nufi?" yayi kasa da muryan sa yace "Mummy kwatakwata baki fahimta na" ya mike tsaye yace "Naji bari zanje yanzu" tace "Toh ko kai fah, kace ina gaishe su" bayan fita sa Niswa tace "Amma Meyasa Mummy kike son hada Yaya da wannan yarinyar da tuntuni ta zubar da mutuncinta?" Mummy tace "Toh dama yanzu a wannan zamanin ai ƴan mata ɗaɗɗaya ne masu zuwa gidan miji da mutuncin su" Niswa ta sake baki tana kallon Maman nata tace "Yanzu kin yarda Yaya ya aure ta a hakan?" Mummy tace "Toh karya aure ta? Naga rufa mata asiri zai yi, kuma ke yanzu dan Allah waya gaya Miki cewa tana yawo?, kawai daga ganin nace tana son kwalliya da son waye wa sai ki mata sharri" Niswa tace "Ko ƙaffara ba zan yi ba yarinyar nan na yawo" Mummy tace "ke Meyasa kike haka ne wai? Ina jiya da Daddare kuka kika dinga yi da kika ga gidan Leena, toh yanzu ba uwar nata bane zata kai ma malamin nan bukatun naki, so kike mu gwada musu bakin hali ta cire hannun ta a lamari mu, karfa ki manta Aminiyata ce tun muna ƴan mata" Niswa tace "Toh ai sai yanzu kikayi baya ni, ni yanzu damuwa ta na samu ya fara kula ni, dan yanzu naga Sadeeq din ma ya fi Muhammad haduwa ashe" ta taɓe baki tunawa da tayi inda Leena ke zaune yanzu. Bayan yayi parking a kofar gidan su, ya rasa ta ina ma zai fara ya sauka daga motar sa ganin wani yaro yasa ya kira sa, yaron yace "gani" Rayyan yana so ya tuna yama sunanta, shi yama manta yace "ka shiga gidan nan kace ana sallama a waje" yaron yace "toh" bayan ya fito yace "ance wai waye ne kuma wa ake nema" yace "kace Rayyan ne" yaron ya fito yace "wai ka shiga" daga haka yaron ya bar wajan shi be shiga ba yana ta tsaye jikin motar sa sai ga last born din Aminiyar Maman sa wanda ba zata wuce sa'ar Nisreen ba tace "Wai ka shigo ciki" yana biye da ita har ta kaisa parlorn su, ya shiga da sallama ya zauna sai ga Hajiya Fatima ta shigo parlorn tana kallon sa ya gaishe ta ta amsa masa da fara'a tace "Mummyn ku tayi ta cewa zaka zo kuma shiru, nace toh wani irin aure kuma zaku yi ba tare da tun a waje ka nuna kulawa ba" yana sosa keya yace "Mama kin san bani da lafiya ne, toh shiyasa komai sai a hankali yanzun" tace "hakane, Allah sauwake" ta mike tace "inaga shiri take amma zata shigo yanzu" kanwar Layla tazo ta jera masa fruit da ruwa, can sai ga Layla ta fito tana zuba kamshi, wai wani catwalk take yi, gashi ta sha kyau, tun da ta fito idon ta akan sa har ta karasa inda yake zaune, Rayyan be tashi mamaki ba sai daya ganta zaune a Kujeran da yake zama tace "Yayan mu" kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa ya fara danna dannen a wayan sa yace "How are you?" cikin Murya ta me daɗi tace "I'm good, toh me kuma daga fara zuwan ka sai ka fara danna waya as if ba hira ka zo ba" ya janye wayan yana kallon ta ta wani lankwashar da kai tace "Haba mana, baby" yace "bakya jin wani iri da kika zauna anan? ya kamata ki gwada min ke macace, da kunya aka san ku" tace "Look, I'm not teen anymore, sannan na gama degree dina 4 years back, so ya kake so ka mayar da ni kamar yanzu na gama secondary school" yace "Okay! Haka ne kuma fah" daga haka be saka ce mata komai ba, ya mike itama ta mike da sauri tace "kar kace min tafiya zaka yi?" Yace "Sure, ina da abin yi ne" tace "ai wannan wulakanci ne, ko fah kallo na baka yi ba balle ka yaba wa kwalliya ta, sannan kana ta danna waya sai kace abinda ka zo yi kenan" yana kallon ta yace "Oh really? Then I'm sorry" daga haka ya kama hanyar fita, ta sha gaban sa ta zare wayan sa dake gaban aljihun rigar sa, tana kallon sa tace "Passcode " shi rashin kunyan ta mamaki yake ba sa yace "Leena" tana saka wa ya buɗe tasa numbern ta tayi saving sannan ta kira layin yana shiga ta kashe ta mika masa tace "Tun da kai ba zaka karba number ta ba, shine ni na saka maka" yace "Well" sannan ya fita, ta bisa da harara, Anan compound yaga Hajiya Fatima yace "toh sai anjima Mama " tace "har ka fito kuma? yace "Eh" tace "toh fah! Ai gani nake kayi saurin fitowa ko dai da matsala ne?" ya girgiza kai yace "wallahi ba komai, wajan aiki zan wuce shiyasa" tace "Oh toh, Allah tsare, ka gaishe min da ita Maman naku" yace "In shaa Allah". Layla na kallon Maman ta tace "Wallahi Mama duk ku kuka ja min raini, wai ni zai kalla ido na tsabar rashin mutunci zai ce wai an san mace da kunya toh ce masa akayi I'm still teen, karfa ya manta ba wani shekaru masu yawa ya ban ba fah" Hajiya Fatima tace "Shi Rayyan dinne yace Miki haka?" tace "Toh karya zan Miki, kuma duk ku kuka jamin raini kila kin faɗawa muguwar uwarta sa cewa ni nake so ya aure ni, ita kuma ta kama ta fada masa" wani kallo ta mata tace "kina tunanin zan fada mata ne?, ai ni na gwada cewa kawai ayi haɗin gida ne" Layla tace "wallahi yaci sa'an ina mugun son sa ne amma da yaga rashin kunya da hujja sai na goge masa hadda da gaske yasan cewa Eh lallai wannan Layla ce" tace "Kiyi hakuri zan sanar da ita uwar nasa nace ya zo amma ko wani magana be shiga sakanin ku ba" tace "da ya fi kuwa, dan ta ja masa kunne, kuma ni banji zan hakura da shi ba" Hajiya Fatima tace "ki kwantar da hankalin ki, ina me tabbatar Miki daga shi har uwar ta sa basu isa su ce zasu gujewa auren nan ba" Layla tace "Nikam Mama sati hudun yayi min yawa" Ayrah dake kallon ta tace "Ikon Allah" ta juya tace "wallahi uban ki zanci a gidan nan idan kina shiga harka ta" daga haka ta wuce ciki ta dauko wani jakkan ta dama already ta shirya ta kama hanyar fita, Mama tace "ina zaki" tace "Gidan kawata" daga haka ta fita Ayrah tace "Mama amma fitan Addah be yi yawa ba?" tace "Kinga tace ki fita a harkar ta, toh bana son gulman" daga haka ta wuce daki". Har Rayyan ya karasa gida be daina mamakin Layla ba. Bayan ya dawo daga sallar Magrib, tun Ɗazu da ya fita sallan la'asar be kuma dawowa ba sai yanzu, dakin Leena ya wuce, Leena da ke kwance tana game yaji an buɗe dakin da sauri ta mike ta zauna amma bata yarda sun haɗa ido ba ta sauke kafafun ta kasa tace "Ina wuni, welcome back" ya karasa har ciki ya zauna bakin gadon shima yace "Thank you, dama you're so caring haka, wife?" ji take kamar ta sauka har sannan bata yarda sun haɗa ido ba ya kama hannun ta yace "Wife, ki shirya, I'm taking you out on a date" sai sannan ta daga kai ta kalle sa ya sakar mata murmushi, taga haka ya mike zuwa dakin sa, yana fita ta shiga wanka bayan ta fita ta sa Maroon Abaya daya haska mata farin fatanta, daga eye pencil sai lips tick tayi using, ta dauki Black hand bag ta wani Black flate shoe sai kallon kanta take a mirror ita kanta tasan tayi kyau, ta ɗauki wayan ta tasa cikin hand bag dinta ta fita parlorn yayi daidai da fitowan sa, tun da ya fito har ya karasa cikin parlorn idon sa na kanta, itama kallon nasa take yi yau ne rana ta farko da ta fara masa wannan kallo taga ashe ya ma fi Ex ɗin ta kyau, da sauri ta kawar da tunanin saboda duk sanda ta tuna sai tayi kuka, yana karasa inda take kawai taji ya yi hugging dinga ja baya tayi tana cire hannun sa, yayi murmushi yace "Ma Shaa Allah, Baby you're damn cute, too beautiful" tana wasa da handbag dinta tace "You're handsome, too" ya ware ido yace "Oh really, No, no, ban kai ki ba" daga haka ya kama hannun ta suka fita, har parking space su ka tafi a haka, duk da ba wanda yayi magana a cikin su, ya buɗe mata front seat yace "Get in" ta kalle sa sai kuma ta shiga. Ko da suka isa sun ki cin abinci a cikin restaurant ɗin suka tafi can baya inda few couples suke zuwa, Wajen so beautiful, lights ɗin dake haska wajen very dim ne, kasan wajan kuma irin kasa ne me laushi wanda ko kana taka sa ba takalmi ba zaka ɗauka shi kake ta kawa ba, sai cool down dake dauke da decor a jikin sa, kusan ko wanne da mutane akai kuma majority Lovebirds ne, aka nuna musu inda za su zauna, su ka karasa still holding her hand, ita sai sunkuyar da kai take yi, ji take kowa su yake kallo, bayan sun zauna aka jera musu dishes da suka yi order, kafin su fara ci Sadeeq ya jawo ta jikin sa ya fara musu hoto ita kunya ya cika ta ta janye jikin ta ya kalle ta yace "Oh bakauyiya" tace "Dama kana jin Hausa haka?" yayi dariya yace "No, ai ni ba bahaushe bane" ta girgiza kai tace "i thought baka ji irin deep ɗin nan, ko da yake ban taɓa ma ganin kana magana dayawa ba sai yau" be san sanda ya fara dariya ba yace "Ji sharri wai sai yau" ya dauki wani stick na Nama ya kai mata baki, ta buɗe zata karɓa. Tun daga ɗan nesa ya kafe su da ido shi duk mamaki ya cika sa, ganin zai sa mata abu a baki da sauri ya ja hannun Jiddah yace "taya ni kallo wancan ba Sadeeq da Leena bane?" Jiddah sake baki tayi tana kallon su sai kuma ta fara dariya tace "jiya fa aka kaita, wato zuwa yanzu har sun fara shiri?" Sultan yace "Munafukai dama raina mana hankali su ke" Jiddah tace "barin je please, na gaishe da me cewa 'who is she?" duk suka kwashe da dariya.. *AGOLA (Behind the palace walls)* 🫧 33........ Har ta mike Sultan ya jawo ta tana kallon sa da alamar tambaya yace "Toh me amfanin zuwan? Ki kyale su kawai" Jiddah ta dinga kallon sa sai kuma ta zauna tace "Ni wallahi na so na gwada masa mun gan sa ai" yace "Toh ke ina ruwan ki? Ba matar sa bace yanzu" Jiddah tayi dariya. Bayan sun gama da dinner yayi clearing bill din sun, su na tafiya ba wanda ke ce da dan uwansa komai, Leena ta kwace hannun ta a cikin na shi ta koma bayan sa tana ɓoye kanta a jikin shi, da mamaki ya juya yana kallonta yace "What?" ta daura yatsan ta a bakin sa alamar yayi shiru, sai kuma ta nuna masa gaban su, Sultan ne da Jiddah suke fita a wajen sai labari suke suna dariya, ya kalle su sai kuma ya mayar da kallon sa kanta shi kam ma abun dariya ya bashi, kawai ya kama hannun ta da niyar su cigaba da tafiya ta kwace hannun ta tayi baya da sauri ganin Jiddah kamar zata jiyo, ya rungume hannu ya tsaya yana kallon ikon Allah, sai da Jiddah suka bar wajan sannan ta karasa inda ya ke yace "Why are you hiding?" tace "toh kawai sai su ganmu" ya gyara tsayuwar sa yace "Okay, toh kar su ganmu, ko?" ta gyada masa kai yayi murmushi yace "Ashe da na musu magana, sai su ganmu da hujja" har suka karasa jikin motar Leena taki masa magana shima be kuma ce mata komai ba. Bayan sun isa gida Leena ta riga sa shiga ciki, dakin ta ta wuce direct ta shiga toilet tayi alwala zata shimfiɗa sallaya sai gashi shima ya shigo da alama dai alwalan yayi , ya jasu sallar isha'i bayan sun idar Sadeeq ya bar ɗakin, Leena ta wuce toilet tayi wanka, bayan ta fito kamar jiya tana cikin shafa lotion sai ga Sadeeq ya shigo, da sauri ta sunkuya kasa tace "Excuse me, kaya nake sawa" Sadeeq yayi banza da ita ya zauna bakin gadon yana danna wayan sa, ta kuma maimaitawa ko alamar kallon ta be yi ba balle tasa ran zai amsa mata ta tura masa baki ta ja kayan ta dake kan stool da gudu ta shige toilet din tasa kayan ta, bayan ta fito daga toilet taga wannan kara yana kan gadon ne gaba daya ya kishin giɗa yana danna wayan sa ta saci kallon sa sai kuma ta wuce gaban mirror ta fesa turare, tana nan tsaye jikin mirror tana wasa da fingers dinta tana so tace masa zata kwanta amma ta gagara taga ya mike suna haɗa ido ya sakar mata murmushi, ta sauke wani ajiyan zuciya ita tunanin ta fita zai yi sai taga yayi hanyar toilet dinta haka nan taji hankalin ta ya tashi tace "En.. Uncle Sadeeq, nan kuma zaka shiga?" har ya sa kafan sa a toilet sai kuma ya juyo ya fita ya wuce ɗakin sa, ta karasa ta cire hijab ɗin jikin ta ta fara gyaran gadon, to her surprise sai ta gansa ya shigo rike da towel da shower gel ɗinsa a hannun sa dayan hannun nasa kuma rike da Pajamas ɗin sa ya zuba su nan bakin gado sabar yadda Leena ta ruɗe da ganin ya sake dawowa tama manta cewa Sleepwear ne a jikin ta, mara hannu da sauri tace "Uncle Sadeeq, toilet dinka ba ruwa ne zaka yi wanka anan?" daf zai shiga kenan sai ya juya yana kallon ta yace "Kar na shiga ne?" ta rasa me zata ce sai kuma tace "em.. wai dama nan ban kunna water heater din bane so ruwan da sanyi" kallon da yake mata ne yasa ta fahimci she's half naked da sauri ta sukuna nan da nan taji hawaye ya fara zuba mata, yace "It's Okay, dama na fi so nayi da na sanyin ne" daga haka ya shiga tashi tayi da sauri ta dau hijab dinta ta saka, tana gama gyaran gadon ta suguna a kasa tana jiran ya fita sai ta kwanta, bata tashi sanin Sadeeq ya wuce tunanin ta ba sai da ta gansa ya fito a toilet daga shi sai towel dake daure a kugunsa, Ga Muscles dinsa sun fito rada raɗa abinka da me gym, bata san sanda ta kwalla ihu ba ta rufe fuskan ta da Hijab ɗin jikin ta, sau daya ya kalle ta yayi murmushi ya ɗauke kansa tana ji yayi mata amfani da perfumes ɗinta still taki ɗagowa tsoron sa ma ta fara ji, bayan ya gama shirin sa cikin Pajamas dinsa ya kashe wutan dakin ya bar dim light ya rufe musu kofa sannan a hankali ya tako ya kwanta kan gadon, Leena ta ɗauka fita yayi tana tura baki ta mike kallon kan gadon ta fara yi kamar zata yi kuka ta dauki wayan ta ta haska be san sanda ya fara dariya ba Leena tayi kamar zata yi kuka tace "Toh kuma anan zaka kwana yau?" yace "A'a ba yau kadai ba, ai dama anan zanna kwana" ya karasa maganar yadda itama tayi cikin kwaikwayon murya ta, Leena ta ɗauki pillow ta koma kasa ta kwanta bayan some minutes Sadeeq ya shammace ta ji kawai tayi ya daga ta sama tana ta kokarin sauka amma ta kasa ya ajiye ta nan saman gadon. Bayan ya fito a wanka yasa Sleepwear dinsa ya kwanta yana duba numbern da yayi ta kiran sa gani yayi da 'Heart owner' Rayyan mamakin yaushe yayi saving wani number da wannan sunan? yana shiga message yaga wannan numbern still ta masa message ko karanta contents ɗin be yi ba nan da nan ya tuna cewa ashe Layla ce tsaki yaja ya kashe wayan sa sannan yayi addu'a ya kwanta. Washe gari har karfe 11 na safe Sadeeq na aikin rarrashin Leena, amma kamar kara tunzura ta yake yi, gashi yana son ya fita babu dama, ta masa magana ma taki ko breakfast yayi ta bata hakuri ta ɗanyi amma ko kulasa bata yi, daga karshe tagumi yayi yana kallon ta cike da tausaya mata. Ammi ta fito daga dakin ta jin su Binta sun dawo tana murmushi tayi hugging ɗinsu suma hugging ɗin nata suka yi, Ammi tace "sannu kun sha hanya" Anty Mairamah tace "danma Abban nasa yace sai dai mu biyo jirgi" Anty Binta ta daura "Wallahi Ammi mutanan nan suna da kirki, baki ga yadda suka karbe mu ba, da fah cewa suka yi ba zasu karbi lefen ba dan Daddy yayi magana ne" Ammi tace "Allah sarki" tace "Ummin sa tace yanzu motar da ya bata gift ai ya zama na ta tuntuni, toh me na kawowa sai kace kuna rike da mu har yanzu" Ammi tace "Self-conscious ne, gani za su yi tayi kamar muna rike da su" tace "wallahi, shiyasa da Daddy yace kar a dawo da lefen suka yi shiru, suka ce toh gold ɗin rabon Leena ne, mu kuma aka bamu 1Mil wai musha ruwa a hanya" Ammi tayi tagumi tana jin su. Tun da garin Allah ya waye Layla take ta kiran sa be daga ba kuma har sannan bata daina damun sa ba, wani colleague dinsa ya kalle me kiran sannan ya mayar da duban sa kan Rayyan yace "Anyi faɗa da Madam kenan" Rayyan ya kalle sa sai kuma ya jawo wayan sa ya kira ta back yana fara ringing ta daga ta kashe murya tace "Haba sweetie, bayan baka kira ni ba, ina kira kuma kaki daga wayan?" yace "Look Layla, ina wajan aiki ne, so duk lokacin da nake asibiti kuma duk wani lokaci ba nawa bane, ki gane wannan" ta sake kashe masa murya tace "Haba Habibi, sai kace

Chapter 21 of 50