Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kuma ta daga kai tana ma Malik magana da hannu yazo kuma har sannan tana rike da Leena, tace "Yarima kazo mana" Malik ya karasa wajan Granny wanda ta haɗa da shi da Leena ta rungume su tana kuka, duk mutanen haraban wajan suka garzaya zuwa parlorn Daddy. Ban san ya ake yi ba nake long chapters two days ba, so please ayi min Voting Sannan a taya Ni Sharing. *AGOLA (Behind the palace walls)* *YOTA* Wattpad © Jiddatulkhayr Instagram © Jiddatulkhayr writes Chapter 68 A week later, Duk suna zaune a parlorn Daddy har ma da Mama ta tayi takanas dan jin ƙwaƙwaf, Rayyan ya mika wa Suhaif envelope ɗin hannun sa, shi kuma ya mikawa Family Doctor ɗin su, Dr. Saminu adjusted his glasses, cleared his throat slightly, then unfolded the paper slowly. Ga baki ɗaya parlorn was silent, especially Mummy tayi kuru dan ganin gwajin ba haka bane, All eyes were on him as he read aloud, "The DNA analysis reveals a 99.9% match between Malik and Baban Yarima... This confirms a biological parent-child relationship.’ Sai ya numfasa, duk parlon kallon Baban Suhaif da Malik suke cike da mamaki, Dr saminu glanced at Leena, Ammi taji bugun zuciyan ta ya tsananta, Dr saminu then continued, "Additionally, Leena’s DNA shows a strong genetic link with Hajiya Hauwa'u, known as Granny, indicating she belongs to the same family lineage. Ammi ta fashe da kuka, Malik ya dinga kallon Leena baya ko kiftawa, Umma ta kalli Malik sannan ta kalli Abbah, sai itama ta fashe da kuka, Granny ta sauka akan kujera tayi sujuda-shukr, Maman Malik ta tashi taje ta rungume Malik tana kuka kamar ranta zai fita, Malik felt a kind of peace and calmness wash over him, a feeling he had never experienced before, Without thinking, he wrapped his arms around her too, holding on tightly as if he never wanted to let go, Muryan ta na rawa tace "Yarima? Dama zan sake ganin ka?" Mai martaba yama Leena hannu akan ta je, ta kalli Ammi dake kuka sai kuma a hankali ta mike ta isa wajan sa, Granny bata yi wata-wata ba ta rungume Leena tana kuka mai tsuma zuciya, Mummy nan take taji wani zazzaɓi ya rufe ta, Rayyan kan sa ya mugun kulle wa, Does that mean Malik and Leena are actually siblings?, ya girgiza kai dan baya son ya fara believing nonsense thought ɗin sa, Mama ta furta "Alhamdu Lillah" tana kallon Mummy da ta gama haɗa zufa kamar wacca ta fito daga wanka, Suhaif ya taka har inda Maman sa ke rungume da ɗan-uwansa ya rungume su baki ɗaya yace "I'm truly happy to have you back with us" ya faɗa a hankali cike da kamewa a harshen sa sannan ya ɗaura "Alhamdulillah da Allah ya sake haɗa ka da mu a karo na biyu" Daddy ya kosa yaji meke faruwa dan gaba ɗaya a ruɗe yake kuma bai taɓa jin Ammi ta basa wani labarin game da Leena ba. Mai martaba yayi gyaran murya hakan yasa kowa nutsuwa, In very calm tongue ya fara magana duk da yawan shekarun sa hakan bai hana calmness ɗin sa bayyana ba yace "Nasan we all need karin bayani right? Dan nasan dole duk muna cikin ruɗani" yayi shiru, duk suka zuba masa ido, ya juya yana kallon Granny a hankali ya furta "Gare ki, Habibty na" Granny idon ta na kan Leena ta numfasa......! A cikin babban Masarautar Yola..*Mai Martaba Modibbo Barkindo* sarkin Yola, Bafulatani ne na asali, daga zuriyar Fulani masu sarauta. Mutum ne mai hankali da natsuwa, da son talakawan sa, yana da Mata biyu, amma yana da ɗabi’ar nuna ƙaunar uwar gidan sa a fili, har a gaban fadawa da 'yan majalisar fada yakan nuna mata tsantsan so, dan ya kan kira ta da "Habibity", abin da ke ƙara tayar da gwiwar amaryar sa.*Gimbiya Hauwa’u*, uwar gida, mace ce mai tsantsar tarbiyya da halin natsuwa. Ita ce garkuwar gidan masarauta kuma jigon zaman lafiyar Sarki. Ta haifi ’yan biyu *Yarima Abdallah Modibbo  ɗan fari cikin 'yan biyu, Ana kiransa da "Yarima Mai shiru"* saboda yawan zama cikin natsuwa da rashin burin mulki. Shi ya fi son karatu da aikin office *Yarima Abdul-Aziz Modibbo ɗan biyu, mai kuzari da ƙwazo. Ana kiransa da *"Yarima Jallube"*, saboda irin rawar da ya ke takawa a fada da kuma sha’awarsa na gadon sarauta.*Gimbiya Zainabu*, amarya, mace ce mai zafin rai da ɗan hassada. Tana jin haushin cewa za a bar uwar gida ta haifi mai gadon Masarautar. Tana da yara biyu:*Karamin Yarima Usman* – ɗanta na fari. Ana kiransa da *"Yarima Fari"*, saboda siririyar fuskarsa da shigarsa mai kyau, Sai dai shima yana kishi da Yayun na sa. Tana da burin ganin shi ne zai gaji mahaifin sa. Sai *Gimbiya Indo* – ƙanwar Usman. Yarinyar da ke da natsuwa da biyayya, ta matuƙar shaku da Sarki. Ana kiranta da "Karama Gimbiya" a cikin fada. Masu tsatsuba a fada; Waliyi Musa Dankaka – ɗan uwan Sarki, wanda ke da ra’ayi cewa ‘ya’yan Hauwa’u ne suka fi cancanta da gadon sarauta. Fulani Rabi mai kula da gida, dafa abinci da ado. Ita ke cusa wa Gimbiya Zainabu shawara mai kaifi. Wasu daga cikin 'yan uwan Mai martaɓa duk suma basu goyon bayan yaran Hauwa`u da suke da gadon Masarautar, wanda hakan yasa suka haɗa kai da Zainabu suka ware Hauwa'u,. Wata rana Mai martaba na zaune duk suna zaune a gefen sa, ya kalli 'yan biyun nasa wanda Abdallah gaba ɗaya hankalin sa na kan wayar hannun sa, Hajiya Zainabu ta taɓe baki ganin kallon sha'awar da yake wa yaran sa kamar ita bata haifa masa yaran ba, Mai martaba a hankali furta "Yarima Abdallah" Abdallah ya janye idanun sa akan wayan hannunsa ya zuba wa Mahaifin na sa yace "Na'am Abbah na" Mai martaba yace "Kai ne Babba, kai ne kafi dace wa da Masarautar nan, kuma kai ne kake da aure, amma gaba ɗaya baka son wani abu daya shafi sarauta kalli kayan da ke jikin ka, baka kallon ɗan uwan ka Abdul-aziz ne?" Abdallah ya tsosa kansa yana kallon Mai martaba, dan shi a rayuwar sa bai fiye magana ba daga Mai martaba sai ɗan uwan sa ko kuma Ummin sa ta yadda mutane suke gane sa kenan dan ba karamin kama yake da ɗan-uwan nasa ba, a hankali yace "Ya Abbah na, a gafarce Ni, amma na sha faɗa bana son wannan Mulkin, akwai takura Ni kuma rayuwar 'yan ci nake bukata shi yasa nafi maida hankali na kan karatu da aikina" Mai martaba ya numfasa amma har sannan shi ɗin yake kallo saboda nutsuwar sa da hankalin sa yafi cancanci da ya hau kan kujerar sarautar fiye da ɗan-uwan na sa, ganin kallon da Mai martaba ke masa yasa a hankali yace "A gafarce Ni" Mai martaba yace "Abdallah ina ganin har yanzu baka gama tunani ba, zan cigaba da baka lokaci har sanda zaka fahimci menene Sarautar" Hajiya Hauwa'u tace "Ranka shi daɗe, a gani na tunda Abdullah ya furta baya so, ga kuma ɗan-uwan sa dake son duk wani abu da ya shafi sarauta gani na zai fi dace wa da shi" caraf Hajiya Zainabu tace "Abdallah aka ce ba Abdul-aziz ba, sannan ku bari idan har Abdallahn baya so ai shikenan, amma kiyi ta cusawa 'ya`yan ki" Mai martaba yayi gyaran murya ya mata wani kallo wanda hakan yasa tayi shiru Hajiya Hauwau tace "Kiyi hakuri idan magana ta tayi zafi" Abdul-aziz ya juya yana kallon Ummin sa sai kuma ya miƙe yace "Ummi kin mata laifi ne da har zaki bata hakuri? Ko kuma Shikenan ke baki isa kiyi magana akan ra'ayin ki ba?" daga haka ya bar parlorn, Abdallah ma ya mike ya bar parlorn duk Mai martaba yana kallon su amma bai ce kala ba wanda hakan be yi ma Yarima Usman daɗi ba. A yammacin wannan ranan Yarima Usman yayi sashin Mahaifiyarsa, a bakin kofar jakadiyar ta zube tana gaishe sa ba tare da ya amsa ba ya shige ciki, duk jakadan da suke ciki suka miƙe suka bar ɗakin, Hajiya Zainabu dake zaune tana shan fruit gefen ta kuma Gimbiya Indo ce, hankalin ta na kan chatting ta ɗaga kai ta kalli Yayan nata a hankali ta furta "Hey you" a takaice yace "Fine" Mahaifiyar ta su ta ajiye bowl ɗin hannunta tana kallon sa cike da so tace "Yarima mai jiran gado" da sauri Gimbiya Indo ta ɗaga kai tana kallon Mahaifiyar tasu sai kuma ta taɓe baki, shi kuma Yarima Usman murmushi yayi ya zauna gefen ta yace "Umma kina ganin hakan zai iya tabbata kuwa? Ko baki ga kamar Mai martaba baya kaunar na hau kan Mulkin bane?" ta ajiye sauran berries ɗin hannunta cikin bowl ɗin sa tace "Yarima kenan, kana ganin hakan ba zai kasance gaskiya bane? Toh barin faɗa maka wani abu, da ace su waziri da Fulani basu goyan bayana ne sai nace da kamar wuya, amma muddin suma basu kaunar wancan ɗakin su gaje sa ai shikenan" Gimbiya Indo ta ajiye wayan hannun ta tana kallon su tace "A gafarce Ni, Amma hakan tamkar son kanmu da yawa mukayi, maganar gaskiya an haifi su Yarima Abdallah tun kafin Mai martaba ya san zai aure ki Umma amma ace yanzu sai mu tsaya kishi Dan yana son Yarima Abdallah ya hau kan kujerar?" Wani kallon da Yarima yake mata yasa ta ɗauke idon ta akan sa, Umma tace "Toh uwar masu gaskiyar duniya, naga har yanzu Mai martaba bai ɗaukan ku da daraja kamar ba  'ya'yan sa ba, amma kina ganin yadda yake nunawa Hauwa'u da 'ƴaƴan ta soyayya a gaban jama'a" Gimbiya Indo ta mike tace "Duk da haka mu kar mu shiga hakkin su" Yarima ya yunkuri da sauri ta fita tana kiran jakadiyar ta. Yarima ya maida kallon sa ga Umma yace "Umma ya kamata kiyi duk yadda zaki yi kafin lokaci ya kure" ta shafa kansa tace "Baka da matsala" washe gari da safe mai martaba yana zaune Hajiya Hauwau ta shiga da breakfast ɗin sa ta zauna haɗa masa, tana serving ɗin sa amma idon sa akan ta yake, yana mamakin yau wajan shekaru nawa amma bata taɓa yarda masu aiki su dafa masa abinci ba, da kanta take masa, bayan ta gama serving nasa tace "Ranka shi daɗe na gama" ya sakar mata murmushi ya riko hannun ta yace "Har da wasu ranka shi daɗe ba kowa anan fah" itama murmushi ta sakar masa, Yarima Abdallah da Abdul-aziz ne suka shigo, hakan yasa Hajiya Hauwa'u kokarin cire hannun ta ana Mai martaba, kallon ta har sannan yake da mamaki yana kara mamakin kunyar ta har sannan, Su Abdallah basu ma gwanda sun ga wani abun bama sai ma zama da suka yi suna gaishe su, kana ganin su kasan daga gym suke, bayan sun amsa Mai martaba yace "Ku kun karya ne?" Abdul-aziz kaɗai yayi magana yace "A'a Abbahn mu, yanzu zamu tafi sai munyi wanka kafin mu yi" yace "Okay, na ɗauka ko zaku jona ni ne" basu sake cewa komai ba suka miƙe, Mai martaɓa yayi gyaran murya hakan yasa duk suka koma suka zauna suna kallon sa, dan sun san akwai abun da yake son faɗa musu ne yasa yayi gyaran murya, yana kallon su cike da kauna yace "Yanzu kai Abdul-aziz da kake son sarauta a haka zamu baka baka da aure?" Ya tsosa kansa yana kallon Abba sai kuma yayi murmushi, Mai martaba yace "A ce ɗan uwan ka yana da Mata har da 'ɗa amma kai kayi shiru, ko dan kaga bana cewa komai ne? Gaskiya idan har baka fito da mata ba Habibity zan sa ta kawo maka koma wacece, in kuma ba haka ba ba lalle ka wakilci Masarautar nan ba, dan kasan dokar Masarautar" ya gyaɗa kai yace "Zan yi making effort Abbah" daga haka suka fita zuwa sashin su, duk fadawan sai zube wa suke suna gaishe su amma Yarima Abdul-aziz kaɗai ke amsa wa, dan shi Abdallah takura ya ɗauki hakan, bayan sun karasa part ɗin nasa Abdallah na kallon Abdul-aziz yace "i think gobe zan tafi US" Abdul-aziz yace "Ban gane ba? Shine sai yanzu zaka sanar da Ni? Kila ko Mai martaba bai sani ba?" Ya numfasa sai kuma ya kama hanyar toilet yace "Eh, I have to go, almost a month banje naga Suhaif da Mamar sa" Abdul-aziz ya taɓe baki ya zauna yana danna wayarsa yana mamakin hali irin na 'yan biyun nasa. Duk suna zaune suna son ganin yadda plan ɗin su zai kasance Waziri yace "Gaskiya har yanzu muna wasa, dan ma taimakon da Allah yayi mana Abdallahn baya son Mulkin amma ai da tuni Mai martaba ya sauka ya  basa" Fulani ta ɗaura tace "Ni fah gani nake har yanzu muna ganganci da maganar nan bamu wani ɗaukar sa da muhimmanci ba amma idan ba haka ba ai da tuni an wuce wajan" Umma ta daura "Toh waya ce Hauwa'u n haka ta barsa? Kun taɓa ganin yaga laifin ta ko sau ɗaya? Kamar yadda kasan ita an halittota bata kuskure" ta karasa maganar tana jan tsaki, waziri yace "Ainihin mulkin nan a ɗakin mu yake, ba shi ya kamata ya gada ba, amma Mahaifin mu ya zaɓe sa tun kan ya mutu wai saboda shine yafi hankali" Fulani ta mike tace "ya kamata gobe ba jibi ba mu garzaya kauyen nan dole Mutumin nan yayi mana aiki cikin hanzari dan nagaji da zama da kuma kallon bakin ciki" Umma tace " Allah ya kaimu goben, sai mu ga ya ake ciki da farko tukun nan". Fulani tana tafiya cike da kasaita zata sashin ta, wata Dattijiwa daga cikin dattijen gidan da suke aiki ta fito rike da ruwa ta watsa, tsausayi yasa ruwan ya zuɓe a jikin Fulani, Matar ta sake baki tana kallon Fulani dan itama bata ɗauka tana tahowa ba, da sauri ta zuɓe kasa ta fara bata hakuri "Tuba nake Ran ki shi dade wallahi ban kula bane" Fulani ta sake baki tana kallon ta bata yi wata wata ba ta ɗauke ta da mari, akan idon Hajiya Hauwa'u, ta sake baki tana kallon Fulani da mamaki dan a ƙalla matar ta haife ta koma tayi jika da ita, ta ɗaga hannu zata sake marin ta Hajiya Hauwa'u tace "Haba Fulani, ai zaki tausaya mata ko albarkacin tsufan ta, Dattijiwan tana duke kasa hawaye na sauka kan kuncin ta, a fusace Fulani tace"Ke babu ruwan ki, ki kama mutuncin ki kafin na gwada miki halina" Hajiya Hauwa'u ta bar wajan tana Allah wadare da halin Fulani. Toh Ni dai naga kulawa, Alhamdulillah thank you guys, Amma ni nace muku nayi left ɗin channel ɗina😂🤦🏽‍♀️💔 naga sai kira ake ta min da lots DM wai nayi left, but Shaa Nagode da kula wa A tayani Sharing saboda masu naima #Jiddatulkhayr 08110615257*AGOLA (Behind the palace walls)* *YOTA* Wattpad © Jiddatulkhayr Instagram © Jiddatulkhayr writes Chapter 69 Hajiya Zainabu na zaune a ɗan karamin ɗakin, ga Fulani a gefen ta suna jiran jin mai Mutumin gaban su zai ce musu, Fulani tayi nisa cikin tunanin, tunanin da yanzu ita ce ainahin Fulani, amma aka hana a hannun Mai gidan ta zuwa kan Mai martaba Modibbo, wani tsaki taja a fili wanda hakan yasa Sarauniya Zainabu kallon ta, tace "Ya dai Fulani?" Ta kalli Mutumin dake gaban su sai kuma tace "Ni na kosa duk yadda za'a yi kawai ayi da Mutanen nan" ɗagowan Mutumin yasa suka Kalle sa suna jiran jin me zai ce, da muryan sa wanda babu daɗin saurara ya fara magana "Gaskiya Mai martaba Modibbo yana da babban lakani a jikin sa wanda idan har aka dage sai an masa wani abu toh gaskiya aiki na zai lalace sannan kuma ku kanku zaku iya rasa ran ku idan kuka masa, saboda tauraron sa na da karfi" suka kalli juna a take, Sarauniya Zainabu tace "Kinga tashi mu koma idan ya so sai muyi wani tunanin da ban amma banga ta rasa rai na ba, dan ban shirya mutuwa yanzu ba" Fulani ta mike duk jikin ta babu karfi. Gimbiya Indo na zaune tare da Mahaifin ta sai basa labari take, wanda kawai sai dai yayi murmushi ko kuma ya bita da eh ko A'a, waziri ne ya shigo, sai kirari yake ma Mai martaba, kallon sa ta dinga yi da mamaki kamar bashi ne wanda yake son ganin bayan Abban na ta ba, bayan fitan sa ta numfasa ta zuba wa Abba ido kamar mai raɗa tace "Abbah nasan baka yarda da kowa amma dan Allah ka sake kara rashin yardan ka da mutane ko da kuwa waye ne" Mai martaba yayi murmushi dan yasan daman yasan waziri ba son sa yake ba, sai kuma ya Kalle ta ya sakar mata murmushi, ita ma mayar masa tayi tana tunanin ko zata faɗa masa kudurin wasu daga cikin masarautar akan sa amma idan ta tuna harda Mahaifiyar ta sai jikin ta yayi sanyi. Sarauniya Hauwa'u ta shige part ɗin 'ya'yan na ta, Abdallah na haɗa kayan sa a box ga kuma Abdul-aziz yana zaune yana danna wayan sa, duk ɗaga kai suka yi suna kallon ta har ta karasa ciki ta zauna, duk suka gaishe ta tana kallon Abdallah tace "Kai kuma ina zuwa haka?" Yayi murmushi yace "Ummi US zan tafi" ta masa wani kallo tace "Da ban shigo ba ba zaka faɗa min ba kenan?" Ya sosa kansa yace "No Ummi, dama ina da niyyar yanzu na shigo na sanar da ke wallahi" tace "Hmmm, I can see" yayi murmushi yace "I think zan tafi na dawo da Amira, ta gama exams ɗin ta jiya so Kuma bana son ta haihu a can" tace "Ai dama shiru na maka taya Zaka ce ta haihu a US bayan ba wanin ta a can ɗin ba" ta kalli Abdul-aziz tace "Baba na Yarima" ya kalli Ummin sa sai kuma yayi murmushi, tace "Ya ake ciki ne? Ko dai baka ji me Mai martaba yace maka ba ne" ya ajiye wayan hannun sa yace "Dan Allah Ummi ku daina min maganar aure, duk sanda na shirya zan faɗa muku, ko kuma nace duk sanda lokaci na yayi" ta harare sa tace "Kai da mai Martaba ai, kuma kaji me yace maka, ace ɗan uwan ka da yake miskili ma ya fara tara iyalen amma kana nan kayi shiru ban jin ma kana da budurwa" yayi dariya, Abdallah ya mike yana kallon Ummi yace "Bari naje na ma Mai martaba maganar tafiya na yanzu" Ummin ma mike wa tayi tana kallon sa tace "Gaskiya ya kama ta kam" daga haka ta fita, jakadiyar ta dake waje tana jiran ta dan basu shiga sashin su Yarima ko da wasa, ta fara bin bayan Ummi. Waziri wani irin kallo yake musu kamar zai dake su rai ɓace yace "Idan aka ce aiki ba zai yi akan shi Mai martaba ba toh akan yaran nasa kuma fah? Wannan wani irin shirme ne da rashin tunani Fisabilillah, daga anyi magana sai ku gwada a bar komai a hannun ku zaku yi handle while ba tunani gare ku ba" Fulani ta ja saki tana kallon Sarauniya Zainabu tace "Nifah tun kafin na gama processing maganar sa ta mike ta jani waje amma ku ma kun san ba wai rashin tunani ne da Ni ba" Yarima Usman ya ɗaura "A gani na ko, dama tun farko ba kan Mai martaba ya kamata ayi aiki ba, dama kan Yarima Mai shiru da kuma Yarima Jallube, su ya kamata ayi wa aiki, musamman Yarima Jallube yadda yake zakalkalewa a cikin Masarautar nan, yana gwada shine wanda zai gaje kujerar, dan gwamma shi Abdallah baya so, beside shi ba'a isa a masa dole ba" Hajiya Zainabu ta ɗaga kan ta tana kallon ɗan nata da irin nasa basirar, Waziri yace "ka kawo magana mai muhimmanci kuwa, sai dai shi Abdul-aziz na kallon mutane da daraja kamar ba kamar ɗan uwan nasa da yake kallon mu a matsayin ba kowa ba" Sarauniya Zainabu ta ɗaura "Dole zamu koma wa Mutumin nan, sai kuma mu faɗa masa yadda muke bukata". Yarima Abdallah ne da Yarima Abdul-aziz suka tun karo ɗakin Mahaifiyar su, Jakadan da suke ciki wata daga cikin su tace "Gasu Yarima Mai shiru suna karaso wa" hakan yasa duk suka mike suka fita, yayi daidai da lokacin da suka karaso, duk suka duke suna gaishe su, Yarima Abdul-aziz ne kaɗai ya ke amsa musu wanda tuni Abdallah ya shige cikin dakin Mahaifiyar na su, Ummi na kallon identical twins ɗin ta cike da sha'awa har suka karasa ciki, ta shafa kan su tace "Allah muku Albarka" duk suka amsa da 'Amin' Abdul-aziz yace "Yanzu zan kaisa Airport ne Ummi" ta numfasa tace "Allah ya kai ka Lafiya Abdallah, ya dawo da ku gida Lafiya" Abdallah ya rungume ta yace "Amin Ummi" tana kallon su tace "Ku cigaba da addu'a duk da Nima ina muku, kar kuyi wasa da daily Azkar ɗin ku, saboda shine garkuwar musulmi, dan haka nake so na sake tunatar da ku dan addu'a ne yasa har yanzu muke cikin gidan nan duk da yadda muke ganin tsanar mu a idon mutane, Kuma kowa ya san muguntan gidan sarauta, dan haka mu sake dagewa" duk suka amsa mata, ta cigaba da basu shawarwari kamar yadda ta saba daga haka ta musu addu'a, Abdallah ya mike shima Abdul-aziz ya mike suka nufi kofa dan gudun kar Abdallah yayi missing flight ɗin sa. Gimbiya Indo na zaune tana kallon jakadiyar ta Mai bata shawara wanda a kalla zata haife ta ko tayi jika da ita, tace "Kina ji, Ni har ga Allah bana bin bayan karya, maganar gaskiya lokacin da aka haifi su Yarima Abdallah ko auren Umman mu fah ba'a yi ba, toh na rasa gane dalilin da yasa basu son Yarima Abdallah ya gaje Masarautar nan, bayan shine ya dace da ya gaje" Jakadiyar ta ta numfasa tace "Allah kara miki tsawon rai Gimbiya, a kullum ina Alfahari da Allah yasa ke kika fahimci gaskiyar hakan, kuma Ni a gani na su waziri na wasa da hankalin Sarauniya Zainabu ne, dan suma ba zasu so a dauki Mulki a bawa Yarima Usman ba, bayan sun san Sarautar daga dakin su ya fito aka ba Mai martaba Modibbo, wallahi kamar suna using ɗin ta ne dan ta haka ne kadai zasu iya cimma Mai martaba da kuma su Yarima Mai shiru" Gimbiya Indo ta gyaɗa kai cike da fahimta tace "Amma ke kinsan dalilin barin Mulkin a hannunsu zuwa hannun Abba na?" Ta gyaɗa kai tace "kwarai kuwa, Kinga tun ina shekara goma nake cikin Masarautar nan, wanda yanzu wajan shekaru na Arba'in ina zaune a cikin ta, nasan ciki da wajan ta, nasan munafunka ta, tun ban san halin mutanan cikin ta ba har nayi karatun haddan ta, da suwa ke rayuwa a cikin ta" ta numfasa sai kuma ta ɗaura tace "Abun da yasa tsohon Mai martaba kafin rasuwar sa yace "baya kaunar bayan mutuwarsa a ba 'yan dakin su waziri Mulkin saboda a lokacin suna da mugun ta, ga su da bin Mata, sannan kuma suna shaye shaye, wanda hakan ya kusa taɓa musu ƙwaƙwalwa, tsohon Mai martaba yayi dogon rubutu wanda dattawan kasa suka sa hannu akai, yace ko bayan ransa Mulki a bawa Modibbo, wanda shi kaɗai ne a wajan mahaifiyar sa, su kuma su maza biyu ne da mata uku amma gaba ɗaya sun lalata rayuwar su saboda kudi ne kawai ke ruɗar su, wanda a lokacin hakan ya kawo babban rikici da kuma gaba wanda har sannan waziri da su fulani ke rike da abin a ransu har sannan, shi kuma dayan ɗan-uwan waziri, akan shaye shayen ya mutu, dan yayi ta ne ba kaɗan ba wanda har ya taɓa wasu daga cikin kayan cikin sa, an kai sa India a masa aiki toh acan ya mutu, wannan ne dalilin da yasa kika ga waziri ya rage sha saboda gudun haka, a lokacin Mahaifiyar su Yarima Mai shiru ta dage tukuru akan mijin ta da addu'a dan a lokacin ko wani Litinin da Alhamis zaki samu tana

Chapter 44 of 50