Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ki tsaya ki faɗa min me zanyi yanzu kuma?" Mama ta harare ta tace "Kina jin duk wanda suka taɓa kulla makirci asirin su ya tonu, sannan duk an sallame su, shine yanzu kike so na sake ? Ai sai ke dai ɗin ne amma inaaa banda ni Fatuu" daga haka itama ta fita. Share it Fisabilillah #Jiddatulkhayr 08110615256*AGOLA (Behind the palace walls)* *YOTA* Wattpad © Jiddatulkhayr Instagram © Jiddatulkhayr writes Chapter 73 Kafin Mai martaba da su Granny su tafi sai da suka cika gidan da abun arziki dan ba wanda bai samu abin arziki ba sai Mummy da taki fitowa ta musu sallama, Su Hajiya suka raka su jikin mota, Granny na rungume da Malik da Leena, Amira ma ta karasa ta rungume su ji take kamar za'a sake raba ta da ɗan ta, Amira tana kallon Malik cike da kauna tace "Suhail ina goben zaku zo ko?" Ya gƴaɗa mata kai yace "In Shaa Allah" Granny ta sakar musu murmushi tayi kissing hannun Leena da na Malik tace "Allah kawo mana ku lafiya, ka fin nan ma muma har mun dawo daga Niger ɗin tunda yanzu Yola zamu, kuma ba daɗewa zamu yi ba" Leena tace "Allah kai ku lafiya" Malik ma yace "Safe trip" tace "Amin" Suhaif ya sake rungume ɗan uwan sa yace "Can't wait to see you" daga haka duk suka shiga Mota, Daddy, Rayyan da kuma Malik suka raka su Airport, bayan sun sauka sun shiga cikin airport din, drivers ɗin su suka kama hanyar Yola, dama wasu kuma daga can Yolan sun kama hanyar Bauchi tun daren Jiya dan Mai martaba baya shiga bold ko kuma Motar da wata Masarautar zata aiko masa dan tun ba yanzu ba ya daina yarda da kowa daga Matar sa sai ɗan sa Abdallah, bayan tashin su su Daddy suka kama hanyar gida. Hajiya tace "Ikon Allah, Ni fah har sannan ina kallon abin nan kamar a mafarki ko kuma a Film, kalli yadda lokaci guda al'amura suka canza" Ammi tayi shiru tana kallon ta sai kuma tace "Hajiya Nima ban taɓa daukan haka abin yake ba duk da nasan cewa Abbah ba ɗan Mami bane dan lokacin ina da wayo aka tsince sa amma kuma nasan tabbas daga gidan masu hali ya fito" Hajiya tace "Ikon Allah, gaskiya a wannan zamanin samun kalan Mami da kuma su Umma ba da yawa ba kam, kalli yadda suka rike su cike da amana shiyasa Hausawa suka ce ɗa na kowa ne" Ammi tayi murmushi kawai sai kuma Hajiya ta kara magana tace "Kai har ma da iyayen ki na Nijar wallahi sun yi kokari, ace su ɗauki tsallaliyar budurwa kyakkyawa kamar ki su bawa wanda ba'a san assalin sa ba ai abin da mamaki" Ammi dai bata ce komai ba amma har sannan itama bata gama recovering daga shock ɗin da take ba but tasan tana ma Leena murnan haduwa da dangin mahaifinta sannan tana ma su Hajiya ma murna dan at least yanzu hankalin su zai kwanta tun da sunga jinin ɗan su duk da yanzu baya raye, Leena dai sai bin su take da idanu haka kawai take jin ta cikin wani peace sannan tasan auren Malik a gare ta alkhairi ne kuma haka Allah ya hukunta kila da tana gidan Sadeeq da bata kira Muhammad akan ya nema musu aiki ba balle har ta haɗu da Suhaif. A haka dai har su Daddy suka dawo gidan wanda har sannan yake avoiding eye contact da Malik dan yana ganin bai kyauta masa da bai nema masa aiki ba. Bayan sun shigo gidan suka wuce parlorn Daddy wanda har sannan su Hajiya suke ciki, Hajiya tana kallon su tace "Har jirgin nasu ya tashi kenan?" Daddy yace "Eh sun tashi" Hajiya ta kalli Malik ta kalli Leena tace "Ikon Allah, Ni wallahi sai yau naga kamar nasu, har ya ɓaci fah" Malik yayi murmushi Leena tace "Amma ai na fi shi kyau" Rayyan yace "Ta ina kenan?" Ta kalle sa sai kuma ta ɗauke kai tana turo baki, Malik ya miƙe tsaye sai kuma ya fita, Leena ta bi parlorn da kallo ganin ba mai kallon ta itama ta mike tabi bayan Malik, Hajiya ta rike haɓa tace "Ikon Allah, yaran yanzun ba kunya gare su ba, ji agaban mu zata bi mijin ta" Leena da har tayi bakin kofa ta ɓata rai ta juyo kamar zata yi kuka ta tsaya kallon Hajiya, Rayyan ya dinga dariya Daddy yace "Tafi abin ki, tsokanar ki take" Ammi tayi murmushi dan itama reaction din Leena ya bata kunya, daga haka Leena ta fita ba tare da ta sake bi ta kan Hajiya ba. A parlor ta same sa yana zaune, ta karasa ciki ta zauna gefen sa tace "I still can't believe this" ya Kalle ta yace "Nima, duk da yadda mutane ke magana but ban ɗauka abin har haka ba though since from day one nake jin ki kamar wani bangare na jiki na, kamar kece wall ɗina" tace "Alhamdulillah ina mana murna most especially kai dan Ni na san Abbah na sannan nasan Ammi, kai ne abin tausayi" ya girgiza mata kai yace "But yanzu zan gansu ai, but Abbah fah? Allah masa rahama" tace "Amin". Da yamma Hajiya ta doka sallama a kofar dakin su Leena, Leena ta fito tana gaishe ta tace "Toh sai ki faɗa wa ɗan uwan naki zamu je duba jikin ɗan ki tunda Kinga zaku tafi cikin dangin uban ku baku ma san rannan zuwan ku ba, dama akan zamu je duba sa sai ga Mai martaba da tawagar sa" Leena ta gƴaɗa kai, Hajiya tace "Ji wani iskanci kuma, har yanzu dai ba canzawa zaki yi ba, ki buɗa baki kice toh ne sai ki wani gyaɗa min kai?" Leena tayi dariya tace "Toh Hajiya naji, barin shirya" daga haka Hajiya ta wuce dakin Ammi dan faɗa mata sakon. Mummy sai zufa take yi, ta gama rasa yadda zata ɓullowa wannan al'amarin, Hajiya Amina tace "Ki fah kwantar da hankalin ki, komai zai tafi yadda kike so" Mummy tace "Wani kwantar da hankalin? Ai sai naga aikin nan ya kammalu zan kwantar da hankalina, Ni dai yanzu dan Allah ki samu kije min" Hajiya Amina tace "Toh amma da ta nikam yanzu ki hakura da kishiyar ki da 'yarta a fara gyara naki auren tunda har kince ga abin da Mahaifiyar sa tace akan ki" Mummy tace "Shikenan sai na zuba ido suna walwala?" Hajiya Amina tace "Kinga idan kina ga kamar ba kokari nake miki ba toh kije da kanki" da sauri Mummy tace "Toh shikenan naji, ko nawa ake bukata just let me know" a haka suka yi sallama ta share zufan goshin ta ta ajiye wayan ta tallabi chin dinta tana kallon waje daya, tasan Hajiya Fatima ne kaɗai zata iya tsaya mata a mata aiki na gaskiya kuma sannan komai ya warware yadda take so amma gashi yanzu sun sami misunderstanding wannan Hajiya Aminan kuma ta kaita wajan wasu amma aikin su bai kai na Hajiya Fatima ba dan sometimes asara ma kawai take dan bata ganin Result, ta sake share hawayen ta ta miƙe tana zaga dakin dan ganin me kuma zata sake yi yanzu. Layla ta riƙe haɓa tace "Kai Mama?" Mama tace "Karya zan miki kenan" Layla tace "Abin ne da mamaki gaskiya, chap ɗin" Mama tace "Wallahi fah" Layla tace "Ban faɗa miki tun farko ba Mama? Nace yadda Mummy ta dake sai Leena ta aure sa wallahi sai tayi nadama dan Ni kam wallahi tun farkon ganina da shi nasan cewa ba daga karamin gida ya fito ba" Mama tace "Ai baki ga idon shegiyar ba" Layla ta kwashe da dariya tace "Kaiii wallahi zan so naga Mummy, Allah sarki ashe shi da Leena cousins kenan?" Mama tace "Iko fah na Ubangiji kenan, gashi ya sake haɗa su waje guda, shiyasa wallahi mugunta be yi ba, ai labarin Leena da Malik ya taba min zuciya wallahi Ni kam na gama shiryuwa kuma ina gode Allah da bai ɗauki rai na ba ina bin bokaye da masu tsubbu" Layla tace "Dama Ni duk iskanci na ban yarda su'ke bayarwa ba" Mama tace "Toh gashi wanda suka kulla tun can da ma gashi asirin su ya tonu, balle kai da baka da wata gata dama" Layla tace "Allah kyauta, Amma kin sanar da Hajiya abubuwan da Mummy ta dinga aikatawa tun farkon auren Ammi?" Mama tace "A'a ban tona mata asiri ba, na kyale ta da halin ta" Layla tace "But why Mama? Kar ta cigaba da halin ta ne kuma, Kinga fah kince akwai sanda Daddy yafi shekara baya ko kallon Ammi" Mama tace "Kinga Layla, a labarin dangin Leena da naji na koya abubuwa da yawa, Ni ba zan tona mata asiri ba taje ita da Allah balle ma Hajiya ta rantse sai ta bar mata gidan ɗan ta, Kinsan ko gaishe da Hajiya fah bata yi sai ta shafe wata guda bata bi ta kan Hajiya ba balle ta gaishe ta" Layla ta gyaɗa kai tana mamakin Mummy. Hajiya ta fito rike da hannun Ayaan ba'a ɗau lokaci ba sai ga Ammi ta fito Leena na bayan ta a haka suka nufi gate, bayan sun shiga compound ɗin su Mami sai ga Nawaf da ya fito waje shan iska shi da Baban sa da gudu yayi kan Leena yace "Amma" Leena ta duka ya faɗa jikin ta tana dariya kamar yadda yake dariya tayi kissing ɗin sa ta ɗauke sa, Ammi tace "Baki da hankali ne zaki ɗaga sa sama ko baki san condition ɗin da kike ciki bane?" Leena taji kunya sai kuma ta sauke sa dan ita bata ɗauka Ammi ta san tana da ciki ba, Hajiya tace "Eh lallai yaro kam ya warke har hankalin mu ya tashi" Har sannan Leena na wasa da shi tana masa murmushi, Sadeeq ya karasa inda suke ya duka yana gaishe da su Hajiya, Leena ta Kalle sa tace "Ina wuni" yace "Lafiya kalau, ai ɗazu nake cewa za'a kawo miki shi hutu" Murmushi kawai tayi suka wuce ciki. Suna shiga parlorn Mami Leena ta Kalli Farida har da gudun ta ta wuce dakin Mami, Jiddah tayi dariya bayan sun gaisa, duk yadda Ammi taso karɓan Nawaf a hannun Leena ki yayi, Ammi ta dungura kansa tace "Naga Uwar taka ma bata wahala kamar yadda na wahala da kai ba" Leena dai sai dariya take yi, Hajiya tace "Ashe ya samu sauki, ai muka ce zaku jimu shiru bamu sake zuwa duban sa bane muka ce bari dai mu zo tunda Leena ma gobe zata yi tafiya" Mami tace "Ayyah wallahi babu komai, ai yaji sauki dama akan zai zo muku hutu ma" Hajiya tace "Ayyah, har mun shirya da zamu zo kwatsam sai ga Wani Manyya motoci sun shigo mana gida ashe daga faɗar Yola ne duk muka tsaya kallon ikon Allah dan mukam mun ɗauka ai wani rankafefen laifi muka aikata ashe wai Leena da mijin ta ɗan uwa ne sannan daga masarautar suke kai munga abin al'ajabi da mun daɗe bamu ga kamar sa ba" Ammi ta sake baki tana kallon Hajiya da Mamaki Leena tayi murmushi dama bata cire sammani daga Hajiya ba dan tasan saf sai kowa ya gama jin wannan labarin, Mami duk da bata gama fahimta ba tace "Ma Shaa Allah, na musu murna wlh" Leena tana kallon Jiddah da mamaki sai kuma tace "Lalle ma Farida" daga haka ta wuce dakin Mami da ta ga Faridan ta shiga ɗazu, ta buɗe kofar, Farida dake zaune bakin gado tana danna waya jin an buɗe kofar ɗakin yasa ta ɗaga kai ta kalli kofar ganin Leena ne ke tsaye yasa da sauri ta mike zata hanyar toilet Leena tayi sauri ta sha gaban ta tace "Sannu Farida" Farida ta sauke idon ta kasa ta gagara haɗa ido da ita Leena tace "Dan kin auri Sadeeq shine kike gudu na? Sai kace ina tare da Sadeeq din ne balle kice da kunya amma ace har aure na sake toh me abun kunya?" Farida ta ɗan Kalle ta dan ta ɗauka ta first maganganu zata gaya mata, a hankali tace "I'm sorry Amma kunyar ki nake ji, gani nake kamar naci amanar ki duk da Nima bawai ina son shi bane su Mami da Mamana suka hada kayan su" Leena ta riko hannun ta tace "Ki daina min wannan kallon dan Allah, dan Ni kam tuni na manta da shi balle ma Kinga har aure na sake, dama rabon Nawaf ne ya kawo ni gidan sa, kuma ki daina masa kallon wanda haɗa ku aka yi saboda Sadeeq bashi da matsala ko ɗaya zaki ji dadin zama da shi in shaa Allah" Farida ta gyaɗa mata kai tace "Thank you Anty Leena" daga haka Leena ta koma parlorn ta samu har su Ammi sun tashi zasu tafi da sauri tabi bayan su. Washe gari da safe sai ga Niswa da Zahra sun zo mata sallama, Zahra tana kallon Leena dake breakfast a parlorn Ammi tace "Ahaf, kin tuna?" Leena tace "Me kenan?" Zahra tace "Lokacin da nace kuna kama?" Leena tayi dariya ta cigaba da breakfast ɗin ta Zahra tace "Nace miki kuna kama kamar wasu Twins kika ce idona baya aiki ne, toh yanzu kin tabbatar idon na ki ne baya aiki" Leena tayi murmushi kawai, Niswa tace "Congratulations Leena" Leena tace "Thank you Anty Niswa", bayan ta gama shiri har Malik ya dawo daga gidan Umma hakan yasa suka fita compound wajan da mota da zai kaisu airport suka karasa sai ga Layla da Hasna, Leena ta karasa da sauri taje ta rungume Layla sai kuma ta sake ta ta karɓi Leena dake hannun Rayyan tana ma yarinyar dariya, Ta gaishe da Layla ta amsa tana mata murna magana suke suna dariya sai kuma taji ba daɗi data share Hasna dan takan tuna lokacin da suke zuwa gidan su da Fu'ad sai Hasna na mata wani gani gani dan lokacin gani take Rayyan na son Leena shiyasa baya kula ta, Leena ta mayar da kallon ta ga Hasna tace "Anty Hasna ina wuni" Hasna ta jiyo da murmushi akan fuskanta ta amsa mata, Hajiya ta miƙa mata wani roban dambun kaza guda biyu tace "Kinga Wannan na Mai martaba ne" Leena tace "Toh" sai kuma ta sake miƙa mata wani tace "Wannan kuma na ganni suke ce mata ko me Oho" Ayaan ya fara dariya yace "Granny ake cewa" tace "Uwaka, nayi da kai?" sai kuma ta mayar da kallon ta ga Leena tace "Idan kinje ki basu kice inji kakar ki, sannan kafin lokacin Hajjin mu yayi zanzo na gaishe su da kai na" Leena tace "In Shaa Allah" Hajiya Amina da ta shigo gidan ne yasa duk suka bita da kallo wanda bata ce musu ko cikan ku ba, daga haka duk suka shiga Mota Rayyan yana tuka ɗaya dayan kuma driver ke ja daga haka suka fita daga compound ɗin , Ammi sai yanzu take jin Leena tayi aure dan gani take shikenan ita da 'yarta yanzu kuma sai ziyara, Hajiya ta kalli Ammi sai kuma ta juya kan Daddy tana kallon sa tace masa "Yanzu kuma saura ka sauwake wa bakar matar naka da ta raina Ni"... A taya Ni Sharing dan Allah *AGOLA (Behind the palace walls)* *YOTA* Wattpad © Jiddatulkhayr Instagram © Jiddatulkhayr writes Chapter 74 With shock Daddy ke kallon Hajiya dan ɓai ɗauka zata iya faɗin hakan ba yace "But Hajiya ai naga kamar yanzu idan na rabu da ita ban kyauta mata ba duba da yadda sufa ya fara tunkaro ta" Hajiya ta riƙe haɓa tana kallon sa da mamaki tace "Amma duk tsawon zaman ku tare zaka ce baka san ta raina Ni bane? Ko kuma baka kallon ko gaisuwa baya shiga tsakanina da ita balle yaranta dan gwamma Rayyan kaɗai ke gaishe Ni sai kuma bayan da Niswa tayi aure" Ammi ta juya ta koma part ɗin ta jiki a sanyaye dan ba kaɗan ba Hajiya ta bata mamaki bata dau zata kawo wannan babban hukunci ba amma da ta tuna yadda Mummy tayi ta treating Hajiya sai tayi shiru dan Hajiya bata da wani say gwamma ma bayan da aka auro ta itake kai mata abinci. Hajiya tana kallon Daddy daya sauke idon sa kasa tace "Muhammadu ba zaka iya abin da nace maka bane?" Ya girgiza kai yace "Ba wai ba zan iya bane Hajiya kawai dai..." Ta katse sa "Shikenan tunda ban isa da kai ba daga haka ta juya zata bar wajan, yayi saurin shan gaban ta ya duka yana rike ta kafafun ta yace "kiyi Hakuri Hajiya ba wai ba zan iya bane, amma tunda kince haka yanzu zan aiwatar da abin da kika so" daga haka ya miƙe har Sannan bata sake kallon sa ba tayi wucewar ta ciki, Daddy kuma ya karasa sashin Mummy ya kai hannu zai buɗe yaga parlorn a buɗe yake hakan yasa ya shiga parlorn kansa tsaye sai dai yana jiyo muryan mutane biyu daga dakin Mummy. Hajiya Amina ta ma Mummy wani kallo tace "Daɗi na dake gaggawa" Mummy tace "Hmm ba zaki taɓa fahimta bane yanzu shegiyar Uwar san nan nake so a fara nane min bakin ta sannan kuma duk abin da zata ce masa idan ba nawa maganar bane toh ba zai bi ba, ita kuma Uwar Leenan asa tsanar ta a zuciyar sa har ya sake ta" Hajiya Amina tace "Baki da damuwa dan yanzu haka ma ya fara aiki nake gaya miki, ai dama matsalar tun farko da ya haɗa ki da Uwar sa ce amma yanzu da kansa zai ce ba zai iya zama da ita ba dole wani gidan zai nema mata ko ta koma kauye" Mummy tayi wani dariya sai kuma tace "Toh ya za'ayi da Leena? Nifah na haɗa auren nan" sai kuma tayi tagumi tace "Ai naga ta kaina dole ma a raba auren nan tunda Ni na haɗa idan ya so yazo ya auri Nisreen ɗina" Hajiya Amina tayi dariya tace "Sai dake wato ma ya auri Nisreen?" Tace "Wallahi toh Ni ina ruwa na" Hajiya Amina ta miƙa mata wani kullin laida tace "Toh ki tabbatar dai Daddyn su yaci, ki haɗa a cikin abinci" Mummy ta karɓa tace "Yanzu ma zan shiga na dafa masa Lunch Kinga sai na zuba" tace "Sure" ta dauki jakkan ta ta rataya Mummy tace "Please ki sake tunatar da shi muhimman abubuwan sune, Ya sake matar sa sannan a rufe bakin shegiyar uwar nasa sai kuma ya kora ta koda kauye ne ko kuma ya nema mata wani gidan sai ita kuma Leenan a haɗa faɗa sakanin ta da Malik ɗin yaji ya tsane ta har su rabu daga baya kuma yace Nisreen yake so" Hajiya Amina tayi dariya tabi hanyar fita tana cewa "Sai da ke, wato kin jima kina abu, yau wajan shekaru 20 fah, Chap sai dai ke ɗin matar M...." Maganar tane ya kafe ganin Daddy a bakin kofar yana tsaye yana jin duk conversation ɗin na su, Mummy dake bayan ta tace "Karasa mana, Ai gidan nan nawa ce Ni kaɗai kamar yadda nake tun farko" tana kallon Hajiya Amina tace "Mu tafi mana" zata kama hannun ta ganin reaction ɗinta kawai taga Daddy tsaye a bakin kofar, bata san sanda ta kwala kara da duka kan kafafun ta ba sai kuma ta miƙe tayi wajan sa cike da shagwaba tace "Yaushe kazo dear?" zata kwanta jikin sa ya sauke mata marin daya sa taga stars hakan yasa Hajiya Amina ja baya da sauri dan ta fahimci ya gama jin su, Mummy ta ɗaga kanta zata yi magana hawaye na sauka kan kuncin ta yace "Hold on, kije na sake ki" Mummy tayi wani ihu a gigice kamar zata yi hauka tana kallon sa sai kuma da sauri ta duka kasa ta rike kafar nasa tana kuka tana cewa "Dan Allah ka rufa min asiri, duk abin da kaji tsausayi ne" Daddy ya kwace kafar sa yana mata wani irin kallo yace "Make sure kin kwashe komai naki kin bar min gida cos ba zan lamunci ganin ki a gida na ba" daga haka ya fita part ɗin sa ya wuce yana jin zuciyar sa na wani irin zafi. Bayan jirgin su Leena ya sauka a airport dake cikin jihar Yola, wannan ne karo na farko da Leena ta fara zuwa garin, wasu Manyan motoci ne ke fake waje guda wanda sai ka ɗauka wasu manyar kasa aka zo ɗauka, wani ke leading ɗinsu har suka karasa wajan motar daga Malik har Leena suna mamakin irin tarban da za'a musu duba da yadda motoci ke jiran su sai kace sun kai goma, bayan sun shiga mota ɗaya sannan ta fara tafiya sai kuma escort ɗin motocin suka fara bin su a baya, a cikin Masarautar Yola aka parka motocin, suka sauka wanda duk mutanen dake Safa da marwa a cikin Masarautar suka fara dukawa suna gaishe su, tun kafin su isa kofar Babban parlorn Masarautar Leena suka kalli Granny da ahalinta sun fito duk suna tsaye, Granny ta karasa ta rungume su, tayi cikin parlorn dasu a hannun ta duk kowa ya juya ya bi bayan su zuwa parlorn kowa da murmushi a fuskar sa,  parlorn a cike yake da 'yan uwa kowa sai magana suke musu wanda zuwa sannan har sun gaji da amsa wa, Buɗe kofar parlorn aka yi ya shigo ciki fuskar sa ɗauke da murmushi, wani zabura Leena tayi ta miƙe tana kallon sa without second thought tayi kansa da gudu ta rungume sa tace "Abbah!" Kawai yaji hawaye ya cika idon sa amma yana kokarin hana kansa zuba, duk parlon kallon su ake cike da tausayi, Hajiya tana kallon Malik tayi karfin halin cewa "Suhail, Baban ka ne" Suhail ya kalli Mutumin dake kama da Leena sai kuma ya kalli Hajiya, Leena lokaci guda jikin ta yayi sanyi ta juya tana kallon Hajiya sai kuma ta tuna cewa  Twin bro din Abbahn tane ta sake fashewa da kuka ya fara patting bayan ta ya tallabo fuskanta yana kallon ta ya gagara magana amma fuskar ɗan-uwansa yake kallo ya sakar mata murmushi yana rike da hannun ta ya karasa cikin parlorn ya buɗewa Malik hannu alamar yazk, Malik yayi shiru a jikin sa sai kuma ya tsinci kansa so emotional, hawaye kawai ya fara dan bai taɓa zaton wannan ranan ba, nan take yaji wani irin calmness na shigar sa, anan ya tabbatar da tabbas wannan Mahaifinsa ne dan ya lura yadda yake magana da kuma yadda yake murmushin sa irin nasa ne, Hajiya Amira ta karasa itama ta rungume su baki ɗaya, yana rike da su ya zauna sai ga Hajiya Indo ta shigo fuskar ta cike da fara'a tana "Ina yaran nawa suke?" ta karasa ta rungume su, can Hajiya tace "Toh ku tashi kuje kuyi wanka kuyi sallah sai kuzo muyi lunch ko?" 'yar Gimbiya Indo wacca ake kira da 'Khadija' ta miƙe tana cewa "Ni zan kai su" sai ga wasu 'yan uwan nasu ma sun mike kowa yana cewa shine zai nuna musu bangaren su, daga karshe Khadija ta kai su. Bayan sun fito duk suka wuce suka yi lunch tare, Leena har mamakin yadda ake nan nan da su take yi dan ba karamin soyayya suke nuna musu ba. Da Daddare aka shirya wani gagarumin liyafa saboda Leena da Malik wanda kowa ya fi son yaga yana jikin su, aka ci aka sha dan sai da Masarautar tasan da wannan liyafan har wanda suke wajan ta ma sai da aka dinga sadaka wa almajirai da marasa karfi. Duk a gajiye suka koma parlorn, Khadija na rike da hannun Leena sai ga wasu 'yan uwan nasu mata biyu suma sun shigo, Batul da Umaima, Hajiya na kallon su tace "Kuje ku kwanta nasan Leena ta gaji" Malik dake gefen dan uwansa ya ɗan saci kallon Leena sai kuma ya kalli Hajiya, Leena ta mike ta bi bayan su Khadija wanda duk suka ki tafiya dakin su wai da ita zasu kwanta, ai wannan ranan Leena anan

Chapter 47 of 50