think dama ba so na kake yi ba, Nima offer ɗin Ya Rayyan na karɓa not that wai dan ina son ka" tayi shiru tana tunanin tura masa hakan shine daidai, ta kai hannun ta zata yi pressing sent kawai taga kiran sa kamar ba zata ɗauka ba sai kuma ta ɗauka ba tare da tace komai ba kawai taji yace "Ina compound Leena, ki fito ki same ni please" tayi shiru har sannan idon ta na kan message ɗin da zata tura masa, dake wayan na speaker, da sauri ta clearing abin da tayi typing, a hankali ta mike ta ɗauki hijab ɗinta, kallon agogo tayi taga pass 11pm, ta wuce ba kowa a parlorn dan Ammi tuni ta kwanta da jikan ta, ta buɗe kofar parlorn a hankali, ta hango sa zaune, ta karasa car park tana jin hawaye na taruwa a idon ta, ya mike yana kallon ta har ta karaso, yayi kasa da murya yace "I'm very sorry, wifey" Leena ta rufe fuskar ta tana kokarin tsayar da kukan ta, Malik duk ya rikice haka nan yake jin Leena kamar wani sassan jikin sa, ya rike hannun ta yana lekan fuskan ta yace "I'm sorry Leena, na san nayi laifi" tace "Ko ka tsaya kaji menene amma sai ka share Ni" yace "Ai ban isa ba, I'm sorry dan Allah" ta gyada masa kai tace "Ya shirye shirye yasu Umma?" Jikin Malik yayi sanyi to the core, a hankali yace "Lafiya kalau, Wifey" ta sauke idon ta kasa sai yau ta yarda suna kama yadda yake kallonta sai gani tayi kamar idon ta ne banne a fuskar sa, ta zauna shima ya zauna, basu daɗe sosai suna magana ba ya mike yace "Barin tafi dare nayi ki samu ki kwanta dan gobe babu baccin safe" tayi murmushi daga haka suka yi sallama. Tunda sassafe sai ga kawayen Mummy sun cika gidan, sai murna take kamar nata auren 'yar zata yi, tana kallon Hajiya Amina tace "Karfe nawa mai makeup ɗin zata zo ne?" Wata kawar ta tayi dariya tace "Wato Khadija baki canzawa yadda na sanki haka nan kike" duk suka kwashe da dariya Hajiya Amina tace "Wallahi sai kace anan ake bikin ina ji ko ita uwar Amaryan bata yi wannan gayyar ba" duk suka kwashe da dariya, Mummy ta mike tace "Ina zuwa" daga haka tayi part ɗin Daddy zata shiga sai ga Hajiya tana fitowa, ta masa mata da sauri har ta karasa fita tana dariya kana kallon ta kasan tana cikin farin ciki tace "Hajiya ina kwana, ya shirye shiryen bikin?" A takaice Hajiya tace "Lafiya" daga haka ta barta tsaye, ta shiga parlorn Daddy ta same sa na breakfast ta zauna gefen sa ta sake gaishe sa bayan ya amsa tace "Ka ga dear har an fara taruwa kuma atleast ya kamata ace ayi abinci saboda jama'a duk da karfe 2pm ne daura auren" Daddy yace "Toh ai ba za'a yi taro ba, haka Hauwa tace" Mummy tace "Amma dai gaskiya wannan ba yi bane, toh nikam har 'yan office ɗin mu sun fara taruwa ace za'ayi abun alkhairi kuma sai a hana inviting mutane, A'a hakan ba yi bane" Calmly Daddy yace "Toh me kike so yanzu?" Tace "wai zaka kawo kuɗi ne aje kasuwa tun yanzu a siyo kayan da za'a yi girki kafin lokacin daura auren" Daddy yace "Okay, kamar nawa zai isa?" Tace "1500k ma Is okay zan yi managing" yace "Okay then, zan miki transfer" ta mike tace "Allah kara buɗi" daga haka ta fita, dakin su Leena ta wuce ta shiga sannan tayi sallama, Ammi dake zaune parlorn suna magana da wata kawarta ta ɗaga kai tana kallon Mummy wanda sun yi wata ma basu haɗu ba, bayan ta zauna Ammi tace "Ina kwana, Maman Rayyan" Mummy na murmushi tace "Lafiya, ashe Abu fa har ya zo, kuma haka nan sai kice ba taro, ai na aka taɓa haka" Ammi tace "Aure bana farko ba? A'a ba sai an daura ma kowa nawi ba kawai su bi su da addu'a Shikenan" Mummy tace "A'a dai yanzu Daddyn su ya bada kuɗi, So, yanzu za'a je kasuwa, duk wanda zai zo ki barsa dan Allah, ai abun murna ne, so abinci kuma ba matsala bane a gidan nan, kuɗin kayan miya kuma Daddyn su ya bayar" Ammi tayi shiru sai kuma tace "Toh shikenan, Mun gode, sannu da kokari" Mummy tace "Me kuma na godiya" daga haka ta fita. Rayyan yayi parking motar sa a parking space na gidan, Layla ta sauka da kyar dan yanzu tafiyar ma wahala yake mata, Rayyan yace "Barin wuce part ɗin Daddy" ta gyaɗa masa kai daga haka ta wuce part ɗin Mummy, da sallama ta shiga taga Mummy da few friends din Mama sun ci uban gayu sai shewa suke yi, Layla ta karasa cikin Parlorn ta gaishe da Mummy, Mummy ta amsa da fara'ar ta tace "Ya nawin jikin kuma?" Layla tace "Alhamdulillah" ta gaida sauran Mamas ɗin na ta, wata tace "Wannan ba 'yar Fatima bace?" Mummy na dariya tace "Itace, ai kin san ɗa na take aure" Layla ta girgiza kai dan ta san makirci ne ya kawo su, daga haka ta mike ta wuce part ɗin Ammi. Ammi tace "ki shiga tana ciki, taki breakfast ma ki mata magana kila ta ji naki" Layla na Murmushi ta mike ta wuce dakin da Leena ke ciki ta same ta kwance, Layla tace "Me zan gani haka?" Leena ta mike ta zauna tana murmushi tace "Ai da baki fito ba tunda kin yi nawi" tayi dariya tace "Ni na isa kin zuwa ne, ai sai Rayyan ya kullace Ni" murmushi kawai Leena tayi, Layla tace "Yana gan ki wani iri?" Tace "Ba zaki gane bane, wallahi gaba ɗaya a tsorace nake kamar a fasa auren haka nake ji, ga wata irin bugawan da zuciya ta yake yi kamar wani abu na shirin faruwa" Layla ta riko hannun ta ganin yadda take magana in breaking heart tongue tace "Ki daina haka Leena, addu'a kawai zaki yi, in shaa Allah duk abin da zai faru Alkhairi ne" a haka ta dinga kwantar mata da hankali. Bayan an gama abinci Mummy da kanta ta sa na Ammi idan tayi baki, ta kaiwa Hajiya, haka nan Hajiya taji abincin bai kwanta mata a rai ba, dan yadda Mummy ke behaving ya ba Hajiya shakku. Niswa ta gaida friends din Maman ta sannan ta wuce dakin Mummy ta zauna kan gado tana kokarin cire charger a jakkan ta sai ga Mummy ta buɗe dakin ta shiga, Niswa ta ɗaga kai tana kallon ta, Mummy tace "Me yasa zaki zo Niswa?" Niswa tace "Kawai dai Mummy, sannan ai at least Leena zata ji daɗi" Mummy ta taɓe baki tace "Bana so kina shiga mutane da wannan raman na ki ne wallahi" Niswa bata ce komai ba Mummy tayi saurin cewa "Zan so ki zauna har dare ki ga gidan da za'a kai Leena, ke ko gidan iyayen sa ba zaki iya minti ɗaya a cikin gidan ba, Kinga nashi gidan sai a hankali" Niswa na kallon Maman na ta tace "Mummy ina ba ke kika yi forcing auren ba ko?" Mummy ta hayyako mata "Nayi forcing kamar yaya? Dama can na san yaron ne?" Niswa ta bata hakuri, Mummy zata koma parlorn Niswa ma ta mike tace "I'm begging you Mummy, kar kiyi wani abu da zaki shiga hakkin wani" Mummy ta sake baki tana kallon ta sai kuma ta wuce ba tare da ta ce mata uffan ba, Niswan ma bangaren su Leena ta wuce, bayan ta gaishe da Ammi ta wuce dakin Leenan ta samu Layla da Zahra suna cikin ɗakin, tayi gaisuwa in jam'i Leena da Zahra kaɗai suka amsa ita kuma bata ko yarda ta kalli side ɗin Layla ba, tace "Leena ya shirye shirye?" Leena tayi murmushi kawai. Har sannan Mummy na mamakin rashin ganin Hajiya Fatima da bata yi ba. Kamar karfe 12:30pm Rayyan yayi sallama a kofar dakin su Leena, Ammi tace ya shiga amma yace A'a kawai a mika masa takardar gwajin, ba'a dau lokaci ba sai ga Layla ta fito ta mika masa yana karɓa ya juya saboda gudun kar ya ɓata lokaci. Ana idar da sallahr jumu'a aka daura auren Leena Abbah da Malik Areej, ko Leena ba zata nunawa Mummy murnan da tayi da auren nan ba. Leena na zaune duk jikin ta yayi mugun sanyi sai ga kiran Malik, ta rintse ido sannan tayi picking call ɗin na sa, da accent ɗin sa na larabci yace "Am I free to call you my wife?" Leena tayi shiru a hankali tace "Um" yace "May Allah bless our marriage with everlasting love until death parts us" a hankali tace "Amin ya Rabbi" ta sauke wayan ta katse kiran. Bayan an gama mata nasiha Mummy da ta sha makeup da few friends ɗinta tace ita zata kai ta hakan yasa Ammi bata sake cewa komai ba..
Ba lalle wannan chaptern ya ma kowa daɗi ba, but muyi accepting yadda hakan ya zo mana, thank you.
#Jiddatulkhayr
08110615256*AGOLA (Behind the palace walls)*
Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes
Young talented writers association (YOTA)
Chapter 64
Hajiya na jin wai Mummy ce zata kai Amarya da sauri ta mike, dakin ta ta wuce ta ɗauki Laffayan ta ta ɗaura, lokacin har wata friend ɗin Ammi da Mummy suna rike da ita, Mummy ganin Hajiya ta tunkaro su taji ranta yayi bala'in ɓaci, Ammi kuwa ganin Hajiya yasa hankalin ta ya kwanta. Mummy sai murmushi take a cikin motar, Drivern da ya ke driving ɗin su nai ya fara shiga Malali, layin manya gidaje, Mummy sai bin wajen take da kallo tana Allah, Allah su bar unguwar, kawai taga motar su ya parka a wani Babban gida, Mummy ta sake baki tace "Ha'a driver, ya zaka parka mu anan tun bamu karasa gidan amaryan ba?" Yace "Hajiya nan ne gidan na ta" Mummy ta sake kallon gidan sannan tace "A'a dai kayi ɓatan hanya, kalli wannan gida da uban kyau kace shine gidan?" Hajiya tace "Bangane me kike nufi ba Hadiza?" Mummy ta fara zufa, dan bata son da fara imagining wannan wai shine gidan Leena ba, ai gwara ta zauna gidan Sadeeq yau dubu, Driver ɗin ya juya bayan sa ya kalli sauran motar da suka raka su a bayan sa hakan ya sake tabbatar da cewa gidan ne, har sannan Hajiya bata daina kallon Mummy ta mamaki ba, duk suka sauka, Leena da kanta ke duke Hajiya ta sauko da ita, Kawayen Mummy da suke baya ma suka sassauko, kawayen Mummy sai bin gidan suke da kallo dan suma abun ya basu mamaki amma ba halin magana saboda Hajiya da ke wajan, bayan sun shiga gidan Mummy ji tayi kamar numfashin ta zai ɗauke sabar yadda gidan ya gaji da kyau ga furnitures masu tsadan gaskiya. Bayan sun ajiye amarya a Parlorn ta Hajiya ta kalle Mummy da kawayen ta da suke bin cikin parlorn da kallo tace "Zamu iya tafiya, tunda ba wai yarinya bace ko kuma auren ta na farko bane sai mu tafi ko?" Ta saka musu ido ta yadda ba wanda zai iya wani abu a cikin su. Wata kawar Mummy tayi karfin halin cewa "Kuma nan ne gidan na ta? To ina miji kuma?" Hajiya ta mata wani kallo tace "Yana kofar gidan, jira yake mu bar masa gida ya shigo ai" ta ja bakin ta tayi shiru Mummy ta goge zufan fuskanta tace "Amma abun da mamaki, yaron fa kowa ya san gidan su kuma ba wai aiki a babban waje yake yi ba amma kalli gidan da ya kama? Ko dai da wani abu da bamu sani bane?" Hajiya tace "Ni kam ko da wani abu ne a zuciyar ki da bamu sani bane Hadiza?" Hajiya Amina ta buga kafar Mummy da sauri, Mummy tace yake tace "Inaa, kawai dai ina taya ta murna ne" Hajiya tace "Muje" duk suka mike har sannan ba su gaji da kallon gidan ba, a compound suka samu Malik da wasu few friends din sa, ya karasa ya gaishe su, Mummy ta dinga kallon sa haka sauran friends din na ta ma, bayan sun shiga motar, motar su Hajiya yayi gaba wanda Mummy ke ciki, motar su Hajiya Amina kuma na biye da su, Hajiya Amina tace "Kambala'i! Amma wallahi ansha da Khadija" duk suka kwashe da dariya, Hajiya Amina tace "Ni fa wallahi dana ga mutumin nan ko wuka za'a samin a wuya ba zan yarda bashi da kuɗi ba, kalli yadda skin ɗin sa ke shinning" wata friend ɗin Mummy tace "ku gayawa Khadija gaskiya, ta ajiye makaman hannun ta kawai, dan wallahi wannan halin nata wata rana zai kai ta ya baro ta" a haka dai har suka karasa gida akayi dropping ɗin su. Hajiya ta sauka ta wuce cikin gidan, Mummy tun da ta sauka bata ko kalli Hajiya ba ta wuce sashin ta kamar zata tashi sama, tana shiga ta kafa kiran Rayyan a waya. Bayan fitan su Mummy Leena ta yaye veil ɗin kanta tana bin parlorn da kallo, dan tun suna cikin mota yadda Mummy ke magana yasa take Allah Allah a kaita ta kalli me Mummy ke magana akai, still Leena ta tsaya kamar statue tana bin parlorn da kallo, bata taɓa shiga shock haka ba a rayuwar ta, buɗe kofar akayi ta ɗaga kai tana kallon sa, murmushi ɗauke a fuskan sa. Dakyar Rayyan ya samu yayi parking motar sa a kofar gidan su, da sauri ya shige gidan saboda yadda Mummy ta ɗaga masa hankali da kira akan tana neman sa, yana shiga parlorn ya ganta tsaye hakan yasa zuciyarsa kusan bugawa yadda yagan ta yasan something is bad yace "Mummy is everything alright?" ya karasa maganar hankalin sa tashi, Mummy tana kallon sa tace "Rayyan kace min wanda zai auri Leena ba shi da kuɗi kuma har iyayen sa ma basu da hali?" Rayyan ya sauke ajiyan zuciya dan ba kadan zuciyan sa ya tsinke ba, ya zauna yana kallon mahaifiyar ta sa yace "Sure! Hakane maganar" ta matsa tsawa tace "Karya kake? Har Ni zaka ma karya Rayyan?" yace "Wallahi ba karya nake miki ba Mummy" tace "Shine naga gidan da aka kaita har yafi gidan mijin ta na da kyau? Su da suke da gidajen man fetur ma kenan?" Rayyan yana kallon Mummy da mamaki a hankali yace "A'a wannan ba gidan sa bane, ɗaya daga cikin gidajen Daddy ne ya basu su zauna a ciki" Mummy ta dafe kirjin ta tana gwalo ido tace "Gidan Daddyn ku ne wannan wai? Furnitures ɗin kuma fah?" Yace "Gidan Daddy wanda aka gama renovating sannan furnitures kuma ban sani ba" Tace "Bansan Daddyn ku bashi da tunani ba sai yau, yanzu sai ya dauki gida ya ba wata Agola? Gashi da yara?" Calmly Rayyan yace "Me aciki Mummy? Duk ai muna da wajan zama na rufin asiri sannan ita kadai ce wanda ta auri wanda bayi da shi shine Daddy ya tausaya mata, kuma yace zai samar masa aiki ai ba wani abun bane Mummy" Mummy ta ja dogon tsaki tace "Dan Allah ka bar min gida" daga haka ta wuce dakin ta kamar wacca zata hadiye zuciya ta mutu dan bakin ciki, ta dauki wayan ta zata kira Hajiya Fatima sai sannan ta tuna ashe ko inviting ɗin ta bata yi ba bayan ita ta bata kuɗin da ta kaiwa Malamin dan ya sa Leena ta so Malik, cilli tayi da wayan ta zauna kasan dakin tana jin wani baƙin ciki. Leena na kallon Malik da wani expression tace "Tell me, gidan nan kuma fah?" Ya sauke ajiyan zuciya dan bai san Daddy bai sanar da ita ba, a hankali yace "I thought Daddy ya sanar da kee, yace mu zauna anan kafin har Allah ya hore min, so da ban so karɓan offern ba but ba yadda za'a yi nama Daddy garda ma" Leena ta share hawayen fuskan ta tace "Allah sarki Daddy, Allah saka masa" a hankali yace "Amin". Sadeeq kamar zai yi hauka duk ya burkice musu, Sultan yace "Mistake da kake yi a rayuwa sai kace ba komai zaka yi magana akai ba, kuma hakan bayi bane" Mami tace "Wallahi ban so da Leena táyi aure ba, amma yadda naga idan wai ba'a yi mishi magana ba shi ba zai iya buɗe baki yace wani abu ba shiyasa na zuba masa ido" Jiddah tace "And to be sincere maganar karɓan Nawaf kamar za'a shiga hakkin ta" duk maganar da akeyi Sadeeq bai kalle su ba, daga karshe ma mike wa yayi ya wuce sama ya bar su. Bayan kwana biyu, Mummy na zaune gefen Daddy da ke breakfast tana ta jan sa da hira, maganar da yayi ne ta karshe ya tsaya mata a rai, ta dake tace "Amma Daddyn yara bangane haka za'a bar mijin Leena ba?" Daddy daya gama breakfast din sa ya mike yace "Eh, ai Kinga idan har an kyale sa haka nan bamu kyauta ba tunda muna da hanyar sauya masa wajan aiki, dama tuni mun gama magana da Rayyan akan samar masa wani aikin" Mummy ta dake tace "Ai kam hakan yayi Alhaji" daga haka ya mata sallama ya fita. Tun fitan Daddy, Mummy ta dinga kiran Rayyan a waya baya ɗaga wa sai gashi can ya kira ta back ta ɗauka tace "Ina ta kira kana ina ne wai?" Yace "Mummy a asibiti muka kwana Layla ce ta haihu" to his surprise sai ji yayi tace "Okay, dama ina son na sanar da kai ne babu ruwan ka akan neman ma mijin Layla aiki" yayi shiru har sai da tace "Baka ji nane wai?" Yace "Ina ji, but Mummy mai hakan zai yi, naga taimako ne kuma ai dan Leena da Ammi zamu yi hakan" Mummy tayi masa wani tsawa "Har zan kawo magana kana jayayya da Ni Rayyan? Toh wallahi ban yafe maka ba idan har baka cire bakin ka a maganar nan ba" Rayyan yayi shiru yace "Idan kuma Daddy ya saka ni fah Mummy? Please kiyi hakuri ki janye bakin da kika min" kit ta katse kiran, Rayyan ya cire wayan a kunnen sa yana kallon screen ɗin, tunani iri da kala ne ke yawo masa a kai. Leena na zaune akan cabinet tana kallon Malik dake wanke waste plate a sink sai dariya take masa, ya juya yana kallon yadda take dariya sai kuma ya juya ya cigaba da wanke plates ɗin yace "Oho, Ni dai all what I knw na fiki iya wa" ta masa hararan wasa tace "A hakan? Chap sannu ko" ya wanke last plate Sannan ya fara clearing wajan ta sauka zata taya sa yace "Nace miki bana son kina sa mun hannu a duty na, ki bari idan naki ya zo ba zan taimaka miki ba" tace "Hutu na" tare suka fito a kitchen ɗin yace "Kiyi sauri ki shirya kar muyi yamma" tace "Alright" daga haka ta wuce dakin ta, shi kuma ya koma kitchen ya dauko food basket da suka jera da warmers a ciki ya kai bakin kofa ya ajiye sannan ya wuce cikin na sa dakin, ba'a dau lokaci ba sai gata ta fito dama tayi wanka kaya kawai zata sa, shima ya fito, ta dauki keyn motar ta ta mika masa, ya girgiza mata kai yace "Kawai kiyi driving ɗin mu" daga haka yayi gaba ba tare da ya jira ta ba, itama fitan tayi ta bisa a baya, yana sa basket ɗin a bayan mota ta saka masa keyn a hannun sa tace "Wai mayasa kake min haka ne" murmushi yayi yace "I'm sorry, then", A hanya sai labari suke idanun sa na kan titin, Ita kuma sai kallon sa take yi, can ya ɗaga gira ɗaya yace "Yes na miki kyau ne?" 'yar dariya tayi tace "Let me confess, wallahi kayi kyau" yace "You too, You are so adorable and beautiful wollah" ta harare sa, ta dauki wayar ta tace ya ɗan jiyo, yana jiyo wa ta musu hoto sai Kuma ta tsaya kallon hoton tace "Ikon Allah" yace "What?" Tace "Wallahi muna kama, Ni sai yanzu na gani a hoton nan" yace "No, bamu kama, kin fini kyau fah" daidai yana parking a kofar gidan su, ta sauka shima ya sauka, yaune rana ta farko da zata fara haduwa da parents ɗin sa, ya dauki basket ɗin yana gaba tana biye da shi a baya har suka shiga cikin gidan da sallama, Umma da Abbah dake compound duk suka daga kai suka kalle su, Nan da nan murmushi fuskan Umma ya washe cos bata taɓa ɗauka kamar nasu haka yayi sosai ba, Abbah da ba wai yana da magana bane amma hakan sai da ya basa mamaki ya dinga kallon su har suka karasa kan tabarman da suke, A hankali Leena ta sake musu sallama, Abbah kaɗai ya amsa Malik ya ajiye basket ɗin a parlorn sannan ya fito ya zauna kan wani kujera, Leena ta gaida Abbah, ya amsa mata da fara'a, ta juya tana kallon Umma, da sauri Umma ta sauke idon ta daga na Leena tana avoiding eye contact da ita ta amsa mata gaisuwar ba yabo ba fallasa, Umma ta mike tace "Mu shiga ciki ko?" Leena ta mike, haka Malik ma duk suka bi bayan Umma. har Leena suka fito bayan Magrib zasu koma gida Umma taki yarda su haɗa ido wanda hakan yayi matukar ba Malik mamaki, sannan yayi mamakin sauyin Umma cikin sauri haka. A hanya Malik ya ɗan kalli Leena dake hamma yace "Ko zamu karasa gidan Ammi ne ta bamu ɗan mu yau" Leena ta ɗan kalle sa sai kuma tayi dariya tace "Ai Ammi ba lalle ta yarda ta bata Nawaf yanzu ba" yace "Ai rokon ta zamu yi" tace "Dan Allah ka bari ko nan da sati ne" yace "Deal?" Tace "Sure!" Ya tsaya a hanya yayi mata siyayyar kayan zaki sannan suka wuce gidan. Abbah na kallon Umma da ta buga uban tagumi yace "wallahi Ni gaskiya yau wannan al'amarin ya bani tsoro ba kaɗan ba" Umma tace "Wallahi tun ban ganta ba dama ban so ace tazo kusa da mu ba, amma gaskiya ban ɗauka har abun ya kai haka ba" Abbah yace "Gaskiya ina ga zai yi kyau ace mu san familyn ta" Umma ta masa wani kallo tace "ban gane ba?" Yayi shiru ba tare da ya ce mata komai ba
Tun farkon labarin na gina sa ne akan Malik da Leena, So! Muyi hakuri har zuwa karshen labarin, Nagode.
#jiddatulkhayr
08110615256*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes
YOTA
Chapter 65
I Dedicated this chapter to Sadeeq's fans
Leena tayi parking a kofar gidan Rayyan, ta juya tana kallon Malik dake kallon ta tace "Idan ka gama kallon kyan nawa sai mu shiga ko?" ya Harare ta yace "Where's the beauty?" Tayi 'yar dariya tace "Abun da ya kawo ka kenan" ya ɗaga kira ɗaya sama yace "Sure" daga haka ya buɗe motar ya sauka itama ta sauka, bayan sun shiga suka samu Mama na zaune a Parlorn rike da jaririyar Layla, duk gaishe ta suka yi ta amsa musu da fara'a Leena tace "Anty Laylan fah?" Mama tace "Tana ciki" tana rufe baki sai ga Layla ta fito Rayyan na bayan ta, buɗe ido yayi ganin su, Layla ta karasa cikin parlorn tana cewa "Amarya waya ai ke ki fitowa?" Leena tayi dariya tace "Na zo ganin Leena" Layla da rashin fahimta tace "Bangane ba?" Leena na Murmushi tace "Toh ban manta deal ɗin mu ba, your first daughter is named Leena, and you’ll name her after me, just like we agreed" Rayyan ya fara dariya ganin how serious she is, Layla ma dariyan ta fara tace "Sannu da kokari" Mama tace "Ah toh idan har da agreement ba zan yarda na bi bayan rashin gaskiya ba" Leena ta gyada kai tace "Yauwa Mama" Layla tace "Amma haka muka yi?" Ta karasa maganar in funny tongue, Leena ta gyara zama tana kallon Mama tace "Mama kinga haka nan wai sai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 41 Chapter of 50