sai juye juye take akan gadon daga karshe ta mike zaune tana kallon Niswa data kifa kanta da resting chair ɗin ɗakin ta dinga kallon ta cike da takaicin a ranta tace toh dama ba tayi tunanin wannan ranan bane har ta fara aikata laifin or yanzu kukan me take yi, daga karshe taja tsaki ta dauki duvet ɗin ta da pillow ta wuce parlor dan ba karamin bacci take ji ba, rabon data samu bacci tun da bikin ya gabato. Niswa ta bita da kallo sai kuma ta mike ta wuce kan gadon, ɗaukan wayan ta tayi ta yi dialing numbern Farouq har ya yanke bai ɗauka ba ta kuma kiran sa kamar zai yanke sai kuma ya ɗaga yace "Baby" ta share hawayen fuskan ta tace "Uhm" yace "Are you still crying? Ko kuma wani abu ya sake faruwa ne?" ta girgiza kanta tana jin relief saboda yanzu shine kaɗai wanda yake mata magana in very calm way and she's ready to spend the rest of her life with him, a hankali tace "kai ma kasan dole zan samu pressure a gida, and still Daddy yaki min faɗa balle duka na, kuma wannan silent ɗin nasa ba kyau cos I knw him, yanzu ma cewa yayi dole aure zai mana nan da 2weeks, I'm so disturbed Farouq" Farouq yayi shiru meanwhile kuma yana tunanin me ta gama faɗa masa ta katse masa tunanin sa tace "Hello" yace "Yes, dear" tace "kayi shiru" yayi murmushi yace "No, ina realizing ne" tace "Toh baka ce komai ba?" yace "Sure, zance dear" a hankali kamar me raɗa tace "Farouq" yace "Na'am" tace "kana so na?" yace "Sure! I do love you" tace "zaka aure ni?" ta karasa maganar kamar me raɗa, yayi shiru for a while, tace "Why the mute, Farouq?" yace "Uhm, ina jin ki?" tace "Since you love me, kawai muyi aure! ka ji?" yayi wani irin murmushi mai wuyar fassara sannan yace "Niswa" tace "ina jin ka" yace "I'm sorry, that was then" Sabar shock Niswa tayi shiru ta ma gagara magana dakyar ta nemi strength tace "bangane that was then ba?" yace "Sure, a baya ne na so ki Niswa, not now da na gama sanin ki, I'm sorry ba zan taɓa auren mace irin ki ba, baki da qualities ɗin matan da nake so, ba zan iya auren ki ba" Niswa ta ji bugun zuciyan ta na bugawa da karfi sannan ta gagara ma sanin what exactly take ji at that moment, me zata ce masa dan she ne last hope ɗin ta ta fara furta 'innalillahi wa'inna ilahi raji'un' a zuciyar ta hawaye Masu zafi suna sauka kan kuncin ta tace "But amma kai ma kasan yadda ka same ni ko? Kasan kuma ba wanda nake kulawa sai kai, kasan bani da lokacin wani duk abin da nake yi kuma kana sane, shine yanzu zaka ki ni? har zaka iya guje min?" yaja dogon tsaki yace "Look bitch girl, don't even think about saying we know each other balle ma kiyi tunanin ko kin taɓa gani na, got it?" daga haka ya katse kiran, ta cire wayan daga kunnen ta ganin dagaske kashe wayan yayi maganganun daya gaya mata ne har sannan ta gagara believing wai Farouq ne zai faɗa mata? bata san sanda ta ɗaura hannun a ka ba ta fashe da sabon kuka.
Yana tsaye a bakin kofar dakin Ammi yana jiran ta, bata ɗau lokacin ba sai ga ta tana buɗe kofar parlorn, jin haka ya karasa jikin kofar bayan ta buɗe ya kalle ta from head to toe yace "sai kuma ki fito haka?" ta kalli sleeping dress ɗin jikin ta ta kalli compound ɗin gidan da babu kowa dan dare yayi sosai sai kuma ta tura baki tace "yanzu wa yake kallo na bayan kai" yace "Ya jikin?" ta langwabar tace "Alhamdulillah" mika mata maganin hannun sa yayi yace "make sure kin sha" ta gƴaɗa masa kai, yace "toh, good night kar Ammi tayi faɗa" ya kare maganar da wasa, itama ƴar dariyar tayi tace "waya ce ma Ammi na nan? Ai ta bar mana part ɗin ta" yace "Alright, sweet dreams" daga haka ya juya ita kuma ta koma ciki ta kulle musu kofar.
Niswa ta dinga kiran wani layin baya ɗaga wa ta sake kiran for the countless times, ta sake dialing har zai katse sai kuma taji an ɗauka ta sauke ajiyar zuciya tace "Sorry na hana ka bacci ko?" yace "Not at all, kin san bana bacci da wuri ai, just that bana kusa da wayar ne" tace "Okay, ina neman favor ne" yace "Ina jin ki, idan har bai fi karfi na ba" tace "Wannan yarinyar da ranan kace min kasan wata friend ɗin ta" yace "That stubborn girl?" tace "Eh ita" yace "Then, what is it?" tace "Ina son sanin duk rayuwar da tayi before, sannan kuma da duk wadda take mu'amala" yayi shiru for almost 30sec sai kuma yace "Hope all is well?" tace "Sure!" daga haka ta fara masa narrating duk abubuwan da suka faru.
Da safe, sai wajajen karfe 7am Rayyan ya shigo gidan, dakin Daddy ya wuce, bayan ya shiga Daddy ya daga kai yana kallon sa, ga kuma Ammi dake gefen sa, ya karasa ciki ya zauna ya gaishe su, bayan sun amsa Ammi ta miƙe, Daddy ya kalle ta yace "ina zaki?" tayi murmushi tace "barin je na ga ko sun ɗaura breakfast" ya gyaɗa mata kai, while ita kuma bata son tana shiga maganar su ne dan yadda taga Rayyan tasan maganar Niswan ne har sannan, kuma suna bukatar privacy, bayan fitan ta Rayyan yana kallon Daddy yace "Jiya da daddare mutumin da nasa ya min aiki akan sa ya gama komai, har ya mika ma wani lawyer da muka dauka case ɗin" Daddy yace "Good job, Allah maka Albarka" yace "Amin, ina ga kafin ya fita office zasu kai masa sammaci, amma kuma bai fiye zama a gidan iyayen sa ba dan su suna Millennium City ne shi kuma yana da gida a Malali ne which am sure nan yarinyar nan take zuwa" ya kare maganar cike da takaicin ta, Daddy yace "it's Okay ai, I'm ready to spend ko wani irin amount ne dan ba zan yarda ace ya lalata ta kuma yaki ta ba, idan ya so suje can duk rayuwar da za suyi dama su suka zaɓa hakan dan nasan ba lalle yace zai so ta yanzu ba" Rayyan yace "Ai bai isa bane Daddy, dan Nima I'm ready to spend" Daddy ya numfasa.
Bayan ya shiga parlorn su dan breakfast ya samu Mummy zaune a Parlorn ya gaishe ta a takaice ba tare da ya tsaya as usual ba itama ta amsa masa a dakile dan taji haushin sa ainun da har bai dauki mataki akan gaya mata magana da Layla tayi ba, Nisreen tace "Yaya ina kwana, jiya baka yi dinner ba" ya gyaɗa mata kai yace "Lafiya kalau" ya wuce dinning ɗin dan yin breakfast, Niswa ma ta fito da Niyyar shan tea dan ba dan yunwan da take ji ba ba zata fito ba saboda ko yadda taga rana haka taga dare jiyan, saboda spaced out da tayi har ta isa dinning area bata san Rayyan na zaune a wajan ba kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kan sa tana kallon sa ta sauke idon ta kasa a hankali tace "Ina kwana Yaya" sai da ya dauki some seconds kafin a takaice yace "Lafiya" haka nan taji ba daɗi tasan ba yadda za'a yi yaji Daddyn zubar ma Layla cikin da tayi ta ɗauki karamin flask ta juya zuwa dakin su, Mummy ta bita da kallo har ta shiga, bayan Rayyan ya gama serving kansa zai fara ci sai ga kiran Layla ya daga yakai kunne , bayan sun gaisa yace "Layla ko Ki sha magani ko na haɗa ki da Ammi" jin furucin sa yasa Mummy ɗaga kai da sauri tana kallon sa, in other side Layla tace "Toh gashi a nan mun gama breakfast zaka zo ka karɓa ne ko na kawo maka dan kasan bana son kana cin abincin can" ya kalli abincin gaban sa ya tuna da abinda Hajiya ta sanar da shi ya ture plate ɗin gefe yace "Thank God, kin kira da wuri wallahi har nayi serving kai na zan fara breakfast ɗin kika kira ni, barin zo na karɓa kawai" daga haka ya mike, shi har ga Allah yama manta da Mummy a parlorn yana katse kiran kuma text message ɗin barrister ya shigo masa so yana kan dubawa yana tafiya har ya fita a parlorn ba tare da yayi noticing ɗin Mummy dake zaune ba, ita kuwa tun sanda ya ambaci Layla da Ammi ta zura masa ido bayan last furucin sa ta sake baki ta bisa da kallo har ya fita, sai yanzu ta sake yarda da cewa Layla ta zama mata karfen wiya.
Mummy dake tsaye akan Niswa ta sake baki jin furucin ta, tace "Mummy ai ba karya bane, tun farko ke kayi mistake din bawa Yaya Layla, wallahi ko ƙaffara ba zan yi ba da kin hakura ya auri Leena da yanzu duk hankalin mu a kwance kika dake lalle sai Layla ai yanzu kina gani, kuma wallahi kar take kallon ku, kika sake kika sa Daddy ya ɗau mataki akan maganar nan sunan auren ki macacce" Mummy ta samu waje ta zauna sai yanzu ta hango abun da tun abaya bata hango ba, tace "wallahi kinyi magana with sence" Niswa ta share hawayen ta tace "Dan haka ki daina blaming ɗinta ke kika fara causing komai, da yanzu Leena ce zata tona min asiri ne?" Mummy ta sauke mata mari tace "Yanzu Ni zakiyi blaming? wato ma nice nayi causing komai? Idan har baki yi ba komai tsanar da ta miki ta isa ta sa a fasa auren ki ne? waya jefa ki cikin wannan halin? Ko dan Kinga har sannan ban ce miki komai ba" Niswa na shash-sheka tace "Mummy kin taɓa ce mana this and that are good? Kin taɓa ce mana wannan ba abu me kyau ba ne? Kin taɓa cewa kuje islamiyya dan dole idan muka ki? Amma Leena fah? haka Ammi tayi treating ɗin ta?, a cire son zuciya duk hassada da kyashi muke mata but she gets everything, nutsuwa, hankali da kuma addinin" Mummy tana mata wani kallo Niswa ta cigaba tace "Nima ban taɓa tunanin ganin kai na a wannan yanayin ba, ban taɓa ɗauka zan yi Wannan rayuwar ba, but I believe one thing, hakan ya zo ne a kaddara ta, kuma na san ba yadda zan kauce mata, da ace ina da sanin addini me yawa kila da nayi ma kai na addu'a, da Allah ya tsare ni daga haka" Mummy ta sake wanke ta da mari ta mike ta bar ɗakin zuciyar ta na kuna, Niswa ta kwanta kan tile tana kuka sosai bata taɓa expecting Farouq for once zai guje ta ba.
Bayan sun tabbatar da gidan ba kowa duba da gatekeeper ɗin sa yace yau ba a gidan ya kwana ba suka koma motar su, kiran Rayyan ne dake dakin Daddy ya shigo ɗaya daga cikin su, ya ɗauka, Rayyan yace "kun same sa?" Barristern yace "Yanzu haka muna gidan sa na Malali ne, baya nan so zamu wuce can gidan su ne, Ko da baya nan zamu bada message ɗin ma iyayen sa" Rayyan yace "Alright" daga haka sukayi sallama, dayan lawyern ya ja motar suka bar street ɗin.
Su huɗu suke zaune kan dinning ɗin suna breakfast gwanin ban sha'awa suna hirar su, Farouq da familyn sa kenan, shi da Kanwar sa sai kuma iyayensu, Baban na su ya ɗaga kai yace "Gaskiya Umar wallahi duk wacca na aura maka it's Okay, na gaji da maka magana" Kanwar sa Na'ila tace "Wallahi Daddy ka aurar da shi kawai kowa ma ya huta, dan bana jin Yaya na da budurwa ma" Farouq ya juya da sauri yana kallon ta ya tamke fuska yace "kee ina wasa da ke?" Mummy na kallon sa tace "daga ta faɗa gaskiya? to kabar min auta ta sarara dan Allah" Daddyn su yace "Toh ai autar na ki ma na kusan cewa tabar min gida, ina duk mate ɗin ta suna aure amma kullum sai kiyi ta saka mata cewa ita karama ce" Na'ila ta kalli Daddy tace "I'm just 23 fah, Daddy" sallamar gatekeeper suka jiyo daga parlorn Daddy kaɗai ya amsa yace "Alhaji wasu mutane biyu ne wai suna neman ka ko kuma Alhaji karami" Daddy yace "waye su?" yace "wallahi ban san su ba, amma suna dai sanye da kalar kayan da masu aiki a banki suke sakawa" yace "It's Okay, kace su shigo compound ɗin gani fitowa" daga haka ya juya zuwa isar da sakon sa, Daddyn Farouq ya mike yana goge bakin sa yace "barin duba ko su waye ne" daga haka ya wuce, da mamaki shimfiɗa a fuskar sa ya karasa wajan su, bayan sun gaisa suka ciro IDcard ɗin su suka nuna masa tare da kuma mishi bayanin meya kawo su, with shock yake kallon su sai kuma ya daure yace "Sure, ɗa nane hope ba matsala?" suka mika masu envelope ɗin hannun su suka ce idan ba damuwa ka isar mana da sakon nan zuwa gare sa, ya karɓa suka masa godiya daga haka suka juya suka fita, haka nan yaji hankalin shi ya tashi sai kuma ya juya ya koma parlorn na sa, briefly ya musu bayanin me ya kawo su, Farouq yaji hankalin shi ya tashi, yana mika ma Farouq envelope ɗin Mummy ta kwace da sauri ta buɗe tana karanta contents ɗin ciki, ta sauri ta ɗaga kai tana kallon Farouq, wanda Daddyn ma kallon nasa yake yi, Na'ila tace "Sammaci kuma daga court? amma ko sun fara hauka ne? Ko dai ba nan zasu kawo ba?" Farouq ya fara jin zufa na karyo masa strictly Daddy ke kallon sa yace "Umar karya kace min baka san akan menene ba, dan baka nuna wani shock da jin maganar ba, so what is it?" ya girgiza ma Daddy kai ba tare da yace komai ba, yana mamakin dama Niswa tasan gidan su ne ko kuma tracking ɗin sa akayi.
Bayan kwana biyu, Daddy ya fito yana tsaye a compound yana waya sai ga Rayyan da ya sako Niswa a gaba sun fito daga part din Mummy suna tahowa inda Daddy yake tsaye, bayan sun kara sa duk suka shiga motar bayan Rayyan ya data motar yana kallon Niswa dake bayan motar yace "Saura idan anje ki tsaya kina rufe baki kiki bayani ko yace ba haka bane kiyi shiru, dan wallahi tun a wajan zan fara dukan ki kamar jaka" bata ce komai ba haka Daddy ma.
Lemme see 60 reaction🤭
Hauwa Jibrin Sulaiman
Jiddatul-khayr__ 08110615256
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
Wattpad © Jiddatulkhayr
Young talented writers association (YOTA)
Chapter 55
According to the court's ruling, aligned with principles of Islamic law, Daddy's family was granted a favorable verdict. Daddy bai yarda an bar court ɗin ba ba tare da an ɗaure auren with the assurance of zata tare a week ɗin, tun a hanya da Niswa ta kifa kanta take kuka ta rasa gane what exactly take feeling, is it murna ko kuma akasin haka, daga Daddy har Rayyan ba wanda yace mata kala, dama Daddy har sannan magana baya shiga tsakanin su daga ta gaishe shi, a takaice zai amsa shikenan, bayan Rayyan yayi parking Daddy ya buɗe kofar motar ya sauka, Rayyan ma ya sauka ba tare da sun kula Niswa dake kuka a bayan motar ba, Rayyan ya fara bin Daddy a baya, bayan sun karasa har parlorn Daddy, Daddy ya zauna yana kallon sa yace "Weldon" murmushi kawai Rayyan yayi, Daddy yace "Hope yau zaka ɗauki matar ka ku bar min gida?" ya shafa kansa yana murmushi yace "Toh Shikenan, Daddy" yace "Better" daga haka ya mike yace "let me have some rest" ya wuce ciki, shi kuma Rayyan ya mike ya fita zuwa part ɗin su, tun a hanya Hajiya ta kalle sa ta kwala masa kira kafin ya karasa shiga, jin muryan ta yasa ya juya zuwa wajan ta ya gaishe ta, ta amsa masa tace "Riyan ya kase ɗin kuma?" yace "Alhamdulillah, dan har an ɗaura musu aure" Hajiya tace "Ah toh, dan ba zai cuce mu ba" daga haka ta juya tana mita ita kaɗai. Bayan duk sun shiga parlorn sun zauna Daddyn Farouq shi ko a jikin sa dan abin da Daddy yayi shine ko wani abu na gari zai yi dan haka he don't care tun farko me ya kai Farouq ɗin ɓata musu yarinya, Mummy ce ta sauko daga stairs da saurin ta tana kallon su, ta kalli Farouq da yayi nisa cikin tunani ya jin gina da cushion haka nan Mummy taji hankalin ta bai kwanta ba, tace "What's the status of the case?" Daddy ya kalle ta yace "Alhamdulillah! Komai ya tafi daidai kamar yadda yake a shara'an ce" tace "I didn't get you" yace "Well! So, an ɗaura auren nasu, ai dama soyayya ce ta kai su ba? So court ta yanke hukunci dole ya aure ta?" Mummy ta samu waje ta zauna tsabar yadda taji kamar jiri ne ke shirin ɗibar ta tace "Kamar ya an aura masa ita?" yace "Kamar yadda kike tunani mana" tsumbul ta mike tsaye, har sannan kuma Farouq bai buɗe idon sa ba, amma yana jin duk conversation ɗin na su, tace "wallahi ba zaiyu ba, taya za'a aura masa wacca bata da tarbiyya" yace "Kamar yadda naki ɗan ma bayi da tarbiyya ba" Na'ila ta fito daga ɗakin ta tana kallon kamar abun a mafarki, Mummy tace "Toh wallahi sai ya tsake ta, dan banyi Na'am da ita a matsayin surkuwa ba" kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai ya fara tafiya sama yace "Idan kika kuskura kika kashe mata aure ki tabbatar naki auren kika kashe, kuma lokacin da kika basa go ahead ɗin ya fara nasa rayuwar a wani waje da nayi magana kice a other country ba haka akeyi ba ya malleki hankalin kan sa, he can build his own life, so, here's the result" daga haka ya shige ɗakin sa, Mummy ta koma ta zauna har sannan bata daina mamakin maganar da Daddy ya faɗa mata ba, wato saboda wannan bad bitch ɗin za'a ce auren ta zai mutu? Auren da yanzu take shekara na 34yrs a kanta shine lokaci ɗaya za'a datse mata, tayi wani murmushi ta miƙe zuwa sama, Na'ila ta kalli Yayan na ta daga haka ta koma ɗaki, Farouq ya san idan ta kuɗi ne su Daddy basu isa suyi winning ba just that Baban sa na supporting ne. Da yamma Rayyan ya shiga ya gaishe da Ammi, Ammi tace "Ashe an aura auren Niswan?" yace "Eh wallahi" Ammi tace "Toh Allah haɗa kan su ya basu zaman lafiya" yace "Amin, Ammi" daga haka ta mike zuwa ɗakin ta ba'a ɗau lokaci ba sai ga Layla ta fito rike da Nawaf kallo ɗaya ta masa ta turo baki ta zauna rike da Babyn yayi kasa da murya yace "Toh 'yar Ammi ko na tafi na barki anan ne?" tayi dariya tace "Oho" sai ga Leena ta fito rike da jakkan Layla, Rayyan yace "Ke Layla sai ki barta da ɗaukan Jakkan?" Layla tace "A'a ita fah ta ɗauka amma ban sata ba" yana kallon Leena da take gaishe sa yace "Ba an hana ki ɗaukan abu mai nawi ba?" ta kalli Jakkan sai kuma tayi dariya tace "yanzu ɗan wannan jakka ai ba nawi gare sa ba" yace "ke kika sani" Ammi ta fito da wani babban Nylo bag wanda ta cika cikin da abubuwa ta mika wa Layla, Layla na Murmushi ta girgiza kai tace "A'a wallahi Ammi" Ammi ta mata wani kallo ta ajiye laidan tace "idan yaso karki ɗauka" Rayyan yace "Idan bata so Ni kam ɗauka zan yi" duk suka yi dariya Ammi tace "Layla sai ki dage da azkar ɗin, sannan kar ki manta da abubuwan da na sanar da ke" tace "in shaa Allah, Ammi" daga haka Ammi ta wuce ciki, Rayyan zai karbi Nawaf Layla taki, daga karshe hakura yayi suka wuce ɗakin Hajiya Leena sai duk taji wani iri duk da ba magana suke ba amma ta fahimci Layla is so nice, bayan su gaishe da Hajiya, Rayyan yace "Hajiya dama sallama zamu miki yanzu zamu wuce gida" Hajiya tace "Aiho, Allah sarki!" Sai kuma ta kalli Leena ta kuma kalli Nawaf dake hannun Layla tace "Ok, Ashe har da Leenan zaka tafi ko? ko dai an baka ita ne?" Leena tana ma Hajiya wani kallo tace "Sai kuma haka kawai a basa ni?" Rayyan ya fara dariyan reaction din Leena, Layla kuma ba zaka gane me take ciki ba dan fuskan ta ba yabo ba fallasa, Hajiya tace "Toh na sani ne? naga ga ɗanki hannun Lailan sannan naga ga jakka a hannun ki" Leena ta mike tace "Wallahi tsufa ne" Rayyan ya dinga dariya duk suka fito ta raka su, zasu shiga part ɗin Mummy Leena ta ja baya ta tsaya Rayyan ya juya yana kallon ta yace "ya kika tsaya kuma?" Leena tayi murmushi tace "Zan jira ku anan kawai" Layla ta mata alama da kar ta shiga, duk yadda Rayyan ya sata ta shiga amma haka taki daga karshe ya kyale ta nan tsaye har suka fito, taga Rayyan ya ɗaure fuska sai kuma bata ji dadin hakan ba bayan ta raka su har mota tace "Ya Rain kayi hakuri" bai san sanda yayi murmushi ba yace "Wai har yanzu baki iya faɗin Rayyan bane" tace "just that ya kama baki na ne wallahi" ta karɓi ɗan ta a hannun Layla tace "Anty Layla yaushe zaki sake zuwa?" Rayyan yace "ba za ta sake zuwa ba duk mai son ganin ta ya biyo ta" Layla tace "kyale sa, zan dawo kwanan nan kinji?" Leena ta ɗaga musu hannu tana musu bye-bye har suka fita. Bayan kwana biyu, bayan Daddy da Daddyn Farouq sun yi magana har Daddy yasa aka je akayi mata jere duk da gidan nasa ma da furnitures, da yamma Daddy na tsaye akan Niswa dake ta faman kuka yace "idan kika yarda na karaso har wajan nan zaki sha mamaki na" dakyar ta mike, Mummy tace "Haba mana, taya za'a ce kai zaka kaita? Ka bari idan aka gama shirya ta sai a samu mata su kai ta ai haka ake yi amma ina aka taɓa irin haka?" wani kallo ya wurga mata yace "Toh addini haka yace, ko kina da ja ne?" tayi shiru ta koma ta zauna amma har sannan ranta a mugun ɓace yake, ya karasa ya rike hannun ta ya wuce da ita sashin Hajiya, Hajiya ta ɗaga kai tana kallon sa tace "Ya haka kuma?" yace "ɗakin ta zan kai ta idan da abin da zaki ce mata ne to" Hajiya tace "Gaskiya kam, dan nima Jiya nace zaman uban me take mana a gida" tana kallon Niswa tace "Ni dai babu abin da zance miki sai dai shawara ta gare ki idan har kika ce zakiyi koyi da rayuwar auren mahaifiyar ki toh tabbas zaki sha wahala, biyayya da kuma girmama 'yan uwan sa ba gazawa bane, sannan kiyi abin da ya sa ki wanda kuma ya hana ki sai ki hakura, Allah ya maku zaman lafiya" har sannan Niswa tana sheshsheka a duke, Daddy yace "Ta so mu tafi" ta mike zata fita suka ci karo da Ammi itama tana kokarin shiga rike da kula a hannun ta, ta ja baya tana kallon Daddy tace "Lafiya?" yace "Zan kai ta gidan ta ne" Ammi tace "Toh Allah haɗa kan su ya basu zaman lafiya" a takaice yace "Amin" a kofar gidan Farouq Daddy yayi parking, ya sauka sai da yama Niswa tsawa sannan ta sauka kuma har sannan tana kuka, yana rike da hannun ta suka shiga cikin compound ɗin bayan mai gadi ya buɗe musu, Farouq ya fito har sannan yana jin nawin Daddy dan baya iya haɗa ido
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 35 Chapter of 50