Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
amman tanada dirin jiki mai kyau sannan tanada gashi wanda ya sauk’o har kan kafad’arta, sai dai sam waennan qualities na Sadiya basu d’ad’a Usman da k’asa ba hasalima shi ya tsane ta kwata kwata bata kwanta mishi ba.. A cewarshi Yarinyar bata da kamun kai, ga munafurci irin na Ubanta dan sarai ya san ita ta shiga tsakanin Maryam da Zainab, shiyasa daya ga nacin nata yana neman yi mishi yawa ya had’asu ita da Zainab d’in ya ci ubansu, tun daga ranar ya samu sa’ida. Sai dai fa dukda hakan da yayi sam soyyarshi a zuciyar Sadiya ba abinda ya ragu sai ma k’aruwa da tayi…. Da wannan tunanin Zainab wadda ta saci hanya ta isa gidansu sadiya, bayan sun gaisa da Baba Laraba ta tambaye ta Ina Sadiya tace mata “Tana d’aki”. Tana shiga ta sameta a kwance tana bacci, jijjigata Zainab ta shiga yi har sai da ta farka sannan ta shiga koro mata halinda ake ciki A ranar Zainab ta sake gasgata soyayyar Usman a zuciyar Sadiya domin kuwa kuka ta dinga yi harda ihu kamar wata y’ar k’aramar Yarinya da kyar suka lallasheta ita da Baba Laraba bayan ta shigo Zainab ta gaya mata halin da ake ciki. kafin ta bar gidan kuwa zazzab’i ne mai zafi ya rufe Sadiya dan ko idanunta bata iya bud’ewa. Satin Sadiya uku tana rashin lafiya, idan ka ganta sai ka tausaya mata, duk ta rame ta fita a haiyyacinta, har shagon d’inkin Usman taje tai sallama da shi daya fito tayita masa kuka, ganin da yayi abun nata na gaske ne yasa ya lallasheta ya rakata gida, wannan itace rana 1 daya mata magana mai dad’i shiyasa tana dawowa gida har mamakinta Laraba ta dinga yi saboda yadda ta ware kamar ba ita ba. Hutun makaranta ya k’are! su Maryam an fara shirin komawa, wannan karan Baba Bashir ne ya yi musu provision da kyar Madu ya bari kuwa. Ranar Lahadi Usman da Madu suka maidasu makaranta. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 10 Ranar Monday aka yi chanjen aji, sannan da yamma aka nad’a shadow prefects wanda a ciki har da Maryam, Maryam ta so an bawa Zainab itama domin zuwa yanzu Maryam ta lura a duk lokacin da ta samu abu Zainab d’in bata samuba ne suke samun matsala da ita. Duk da k’ok’arin ganin an zauna lafiya da Maryam d’in take yi hakan bai hana Zainab kyarar ta ba kasancewar hostel d’aya suke room d’aya aji d’aya kuma seat d’aya. washegari Tuesday, suna zaune suna jiran first period na English, English theacher d’in ya shigo tare da wani kyakkyawan saurayi sanye cikin khakin sa na nysc, kusan duk matan ajin ido suka zuba mishi…. Har suka k’araso bakin board suka tsaya da shi da English teacher d’in idanunsu na a kanshi, shi kam bai ma san suna yi ba don idanunsa suna a k’asa yana kallon k’asa yayinda su kuma ko fahimtar bayanin English teacher wanda yake cewa “ga sabon copper shi zai dinga yi musu English a yanzu for 10 months, daganan idan ya gama service d’inshi ya tafi aiki zai dawo hannunshi kamar farko” basa yi, har sai da yace “Are u guys with me??” Da d’an k’arfi, tukunna hankulansu ya dawo jikinsu, suka ce “Yes sir.” Banda Zainab wadda tayi mutuwar zaune, dan a lokaci d’aya ta ji bawan Allah n ya tafi da imanin ta. Kasancewar Madu da Bashir sun gayawa Malaman su su dinga zaunar da su sit d’aya ita da Maryam ya sanya akoda yaushe suna tare, hakanan wani lokacin zainab sai ta kawo jaka ta saka a tsakiyar su wai kar jikin Maryam ya goge ta ta kwashi bak’in jini, Amman yau kam zainab bata san lokacin da ta kamo hannun Maryam da k’arfi ba! Ita maryam d’inma tsorata ta yi dan kwata kwata hankalinta baya ajin, ya tafi ga takardar da take hannun ta tanata bitar debate d’in da za suyi da safen nan, kawai ta ji an damk’o hannunta kamar za a karya ta. Kallonta ta yi amman sai ta ga hankalinta gaba d’aya baya tare da ita, wani wajen ma daban take kalla. Da sauri ta kalli inda zainab take kallo ta ga englishi teacher yana ta zuba bayani a gaban board da wani balarabe a gefen sa da koren kaya a jikin sa….dan haka ta juyo gareta cikin kulawa tace “Zainab menene?” Kallon ta zainab d’in ta yi sannan tace “Maryam kinga wannan kyakkyawa ko?. Dama haka ake ji a lokacin da ka ga wanda kake so? kinji yadda k’irjina yake bugawa kuwa? haka kike ji idan kika kalli ya Usman?” Ta yi mata tambayar tana mai sake kallon saitin da copper d’in yake. Wani farin ciki ne ya lullub’e Maryam dan rabon da zainab ta yi mata magana mai tsaho haka har ta manta…dan haka ta saki wani k’ayataccen murmushin da ya sake fito da ainihin kyawun fuskarta sannan ta d’ago kanta domin ta kalla wanda y’ar uwarta ta haukace a kai haka cikin lokaci k’ank’ani. Tana d’ago kan nata dai dai shikuma English teacher ya mik’a masa chalk yana cewa “introduce yourself to them.” Karb’a yayi sannan ya d’ago daidai ita kuma Maryam ta juyo tana murmushi a take idanunsu suka sark’e a cikin na juna! Bai san ya aka yi ba kawai ya ji chalk d’in dake hannunsa ya fad’i k’asa! Lokaci d’aya zuciyarsa ta hau bugawa da sauri da sauri…. Itama Maryam kusan hakan ne a nata b’angaren, jin yadda zuciyarta ke bugawa gashi ya tsareta da manyan idanuwanshi farare k’al masu kama dana mai jin bacci, hakan ya sanya ta saurin sunkuyar da kanta k’asa. Maganar Mr Solomon ce ta dawo da shi daga duniyar daya tsinci kanshi a ciki dak’ik’un k’alilan da suka wuce. Chalk d’in da ya yar yaga yana mik’a mishi sannan ya sake cewa “introduce yourself to your students.” A hankali ya saka hannunshi ya karb’a sannan ya sake juyawa ya kalli inda Maryam take a ranshi yana adduar Allah yasa ta sake d’agowa ya kalli fuskarta, domin kuwa baya jin akwai abinda ba zai tab’a gundurar sa a duniyarnan kamar kallon fuskar wannan extraordinary beautiful young lady d’in ba. Ganin tak’i d’agowa ne yasa shi juyawa…a hankali ya k’arasa jikin black board d’in ya rubutu sunan shi kamar haka ‘YAKUBU UMAR FAROUK M.T’ Sannan ya juyo ya kalli students d’in yace “that’s my name, but u can all call me ‘ABBA’ I’m your new English Teacher....” Cikin nutsuwa ya karanto musu tsarinshi kamar ‘baya son surutu a aji sannan yana son in ya bada assighment a dinga maida hankali ana yi......’ Sai da ya gama tukunna Solomon yace “akwai debate d’in da ya basu as an assignment group A B and C”. sannan ya mik’a mishi textbooks d’in da suke hannunshi ya juya ya fita…. Cikin kwarewa da nutsuwa Abba yake koyar da su, sun nutsu kuwa suna fahimta sosai don duk hankalin su yana a kanshi, sai da ya gama yace “Ina masu debate?” Maryam ita take representing group A, dan haka ta mik’e tsaye. A hankali cikin sauk’e ajiyar zuciya yake kallon ta, kafin ya janye idanunsa ya mayar kan group leaders d’in B and C da suka mik’e sannan yace “su fito gaban board”. Topic d’in yana magana ne a kan who is more responsible a karatun Yara A, parents B, teachers C kuma both. Maryam itace mai parents. Haka suka dunga mahawarar a tsakanin su har kowa ya kawo gaba d’aya points d’inshi. Points d’in da Maryam ta kawo ko kai shed’an ne dole ka san itace winner! Danhaka ya bawa group d’inta 10/15 ragowar groups biyun kuma ya basu 6. Bayan sun koma seats d’insu sun zauna ya tambayesu ko “akwai mai question”, sukace “a’a”hakan yasa ya tattare books d’inshi, ya duba time table yaga sai Friday shida ya sake shigowa ajin. Daga haka ya yi musu sallama ya fita. Ai kuwa kamar jira sukeyi yana fita kowacce ta hau tofa albarkacin bakinta, wasu su ce balarabe ne wasu suce d’an India wasu kuma pakistan, gashi daga ganin sa ka san d’an masu kud’i ne! Nan ajin ya haukace da zancen sa har sai da malamar next period ta shigo tukunna aka samu ajin ya nutsu da zancenshi. Kafin kwana biyu, gaba d’aya makarantar ta d’au zancen copper Abba balarabe (sunan da suka saka mishi kenan) Hatta junior section ba’a barsu a baya ba, masu love letters suma yi suke yi su je su zira ta saman glass d’in motasa Inda yake d’an bari kad’an a zuge saboda iska ya d’an dinga shiga. Zainab tun ranar da ta fara ganinsa ta haukace bata da labari sai na Abba, hannuta kuwa kullum da kalar design d’in da za ayi da biro a cikin heart d’in a rubuta ‘Abba’ duk inda kuwa akace Fridays Mondays ko Tuesdays ( ranakun da suke da English kenan) hakanan za ta rambad’a kwalliya ta yi skipping assembly kuma, dan kar a goge mata. Kamar yadda y’an makaranta suka haukace da ganinsa hakanan shima zuciyarsa ta haukace tunda ya ga Maryam. Yau satin sa biyu da fara koyar da su kuma zuwa wannan lokaci kam ya gama fahimtar son Maryam yake yi domin kuwa tun ranar farko daya ganta ya rasa nutsuwarshi gaba d’aya bashi da burin da ya wuce yayi ta ganinta, har Allah Allah yake ranar da zai shiga ajinsu ta yi ya samu ya sake sakata a idanunsa. Through out this week ko me yake yi kawai tunanin ta yake yi. Ganin da yayi yana b’atawa kanshi lokaci yasa kawai ya yanke shawarar gaya mata in his next period, dukda kuwa yana fargabar mai amsarta za ta kasance, duba da yanayin k’arancin shekarunta amma kuma ya san ‘a bari ya huce shi ke kawo rabon wani.’ Yau Monday!! kasancewar Abba ba’a staff quarters yake da zama ba..gida ne guda mahaifin shi ya siya mishi saboda service d’in da aka turo shi…ya sanya ya tashi da sassafe dan baya son ya makara, kuma akwai d’an tazara tsakaninsu da makarantar. Har yayi wanka yayi breakfast yana murmushi jifa jifa shi kad’ai, kawai idan ya tuna zai ganta yau sai yaji wani farin ciki ya lulllub’eshi . Duk saurin shi kuwa sai da aka gama assembly tukunna ya samu ya zo. Zainab yau sneaking ta yi bataje assembly ba saboda ta shafa jambaki da powder ga kwalli ta saka kuma ta san indai aka ganta to punishment ne bayan an sakata ta goge. Y’an aji suna fara shigowa suka ganta a zaune, wata classmate d’insu ce tace “wato yau sneaking kika kuma yi ko?Hmm bai ma fa san kina yi ba! Dan ko kallonki baya yi.” Dariya tayi kafin ta sake cewa “tou shadow sai ki rubuta sunan y’ar uwarki, a cikin masu sneaking in dai ba son kai bane abun” Ta yi maganar referring to Maryam. Ko gama zama ba su yi ba Abba ya shigo ajin hakan yasa zainab ta had’iye masifar da ta taso mata take shirin juyewa classmate d’in tasu tahau murmushi tana kallonsa. Cikin dabara ya kalli wajen zaman Maryam yaga tana goge wajen zaman ta da duster kafin a hankali cikin nutsuwarta ta zauna sannan ta fara yiwa Zainab magana a hankali… Ajiyar zuciya ya sauk’e a hankali sannan ya amsa gaisuwar da suka shiga yi masa. Bayan ya kammala duk abunda ya kamata yace dasu “su ciro takarda zai yi test”. Hakan kuwa aka yi…. Lokaci yana cika ba tare da ya b’atawa kanshi lokaci ba ya kalli Maryam yace “ta tattare gaba d’aya papers d’in ta kai mishi office.” Sai da ya ga fitarta tukunna ya bi ta a baya. Jin kamar mutum a bayan ta yasa ta juyo, ganin shine ya sanya ta d’an tsaya sai da yayi gaba tukunna ta bishi a baya saboda daman ko taje Admin d’in sai tayi tambaya tunda ba sanin office d’insa tayi ba. Office d’inshi kusan shine na k’arshe a jerin k’ananun offices d’in da suke wajen…suna zuwa ya saka hannu cikin aljihun wandonshi ya zaro key ya bud’e ya tura ya shiga sannan a hankali yace mata “Bismillah”. Sallama tayi ta shiga…office d’in d’an k’arami ne, sai dai ya had’u sosai, sai k’amshi yake fitarwa, ga wata k’ofa a gefe wanda tanada tabbacin toilet ne…. Maganar sa ce ta dawo da ita daga duniyar k’arewa office d’in nasa kallo data tafi, jin yana cewa “Zauna mana, ga seat.” A hankali ta ajjiye takardun a kan tebur sannan ta girgiza kai ta juya za ta fita taji yace “I order u to sit.” Sai da tayi kusan 1 minute sannan ta zo ta zauna kan kujerar da take facing tashi benci ne kawai a tsakaninsu. Sai da ya d’an sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “from which state are you ?” “Kano” ta bashi amsa. “Which area??” “Gandun albasa” Ta fad’a a tak’aice. “Are u sure?” Yai mata tambayar kafin yace “cos banga alama ba, at all” Da mamaki ta kalleshi, kafin tace “U too” Sannan ta mik’e tace “Please sir zan tafi muna da test.” Mik’ewa shima yayi yana murmushi kafin yace “sai yaushe? Ba kiyi mini kwatancen gidanku ba balle in kawo miki ziyara idan an yi hutu, ko bakya so in zo???“ Da sauri ta d’aga mishi kai alamar ‘eh’. With surprise yace “Y” “Nothing” Kawai ta iya ce mishi sannan ta sunkuyar da kanta k’asa, tana adduar Allah yasa ya bata izinin tafiya, dan bata san daliliba in dai suna waje d’aya ji take tamkar zuciyarta za ta faso k’irjinta ne ta fito waje, tsabar bugawa. Abba fahimtar da yayi kamar yana yin komai cikin sauri..kar kuma yaje ta k’i shi idan taga zalamarshi…hakan ya sanya ba dan ya gamsu da shawarar da zuciyarshi ta bashi ba kawai ya bata izinin tafiya. Ai kuwa da sauri ta juya ta fita a office d’in. Zama yayi a kan kujerar sa, sannan ya bud’a hannunshi kafin ya kaisu duka biyu bayan k’eyarsa kamar zai yi filo da su… Lumshe idanuwanshi yayi sannan ya fara tunanin duk wani possible hanya da zai b yayi getting close to her, dan ya lura he needs her attention first. A bakin Admin block d’in taci karo da Zainab tana ta faman kai kawo, tana hango ta kuwa ta iso tana tambayarta inda office d’in nashi yake..kwatance Maryam d’in tayi mata daga haka tayi gaba, bata san ya sukayi ba.... A b’angaren Abba kuwa, a da k’arfe 2 yake tashi ya tafi gidanshi, amman yanzu voluntarily yayi exceeding time d’inshi har 10 pm (Time d’in tashi daga night prep) ko tsoron hanya baya yi, hakanan yacewa mai principal kawai zai dinga supervising evening and night prep, Friday kuma zai samu aji ya dinga k’ari a sms. Da murna kuwa principal d’in ta yarda, dan yace ba sai an bashi ko sisi ba. Kasancewar Maryam shadow ce ya sanya ba a ajin su take night prep ba, a jss2 take zama tana supervising d’insu. Tana zaune kawai ta ji kamar an shigo tana kallon k’ofa kuwa suka yi ido biyu….kujerar teacher ya janyo ya kawo dai dai gefen sit d’inta ya ajjiye sannan ya zauna kafin yace mata “Good evening ma.” Da sauri ta kalleshi sai kuma ta yi k’asa da kanta tace “evening sir.” Murmushi yayi kafin yace “na takura ki ko?” Girgiza kanta kawai tayi ta ci gaba da karatunta… Jifa jifa yake mata hira har aka tashi. Tun daga ranar kuwa haka kullum zai shigo ajin da sunan supervising zai yi amman su daya kamata ace sun hana Yara surutu har a tashi bakin Abba baya yin shiru na minti goma. A haka har aka yi sati… Yau friday Maryam tanata murna ba zasu had’u ba atleast zuciyarta sa ta huta da bugawa da take yi. Sai dai kuma tana zuwa sms d’in ta ganshi a bakin gate na main mosque yana tarar y’an makara, ai kuwa ganin tazo a makare ba k’aramin dad’i yayi masa ba, sai da ya bawa kowa punishment sannan ya juyo ya fara tanbayarta “mai yasa ta makara bayan tana matsayin shadow?” Uzurinta ta fad’a mishi…maimakon ya barta ta tafi ko yayi punishing nata, instead, sai kawai ya hau tambayarta ajin da take. Yaso ace itama d’aliba ce amman sai ya ji tace “ajin y’an Izu 60 take koyarwa, thou he was amazed.” Ganin zata makara sosai ya sanya ya barta ta shiga taje wajen d’alibanta…. Sai da ya samu ajin da tabarmar su take facing tata tukunna yace su zai koyar...... Idan ana maganar ‘Nacii!!’ tou shi Abba yake yiwa Maryam, tun bata sakewa da shi har ta fara, dan ya iya labarin ban dariya, sannan yana burgeta , thou har yanzu bata gama sanin ma’anar bugawar da zuciyarta keyi idan suna tare ba. Ahaka aka shafe 3 weeks. Kamar kullum yau ma suna zaune a night prep yana bata labarin Mahaifin sa….tanata mamaki saboda ita dai ita da Mahaifinta they are like best friends sab’anin shi dan a yadda yake bada labarin Mahaifin nasa kamar wani boss na horror movie, he is not even close to him kwata kwata kuma wai a haka duk cikin y’aya’ansa yafi sonshi, saboda ya ci sunan mahaifinsa ne… Hayaniyar wasu Yara ne ya juyo da hankalinsu suna waigawa kuwa suka ga ana dambe! Da sauri ta tashi ta isa wajen, shima ganin hakan yasa ya biyota….garin k’ok’arin raba damben d’ayar Yarinyar jin an rik’e hannunta ta d’auka y’an class d’insu ne nan ta buge hannun Maryam d’in da k’arfi!! wanda bai sauk’a a koina ba sai a kan louvers na window kuma daman a fashe yake, nan da nan kuwa ta yanke jini ya fara tsiyaya… Abba bai san lokacin da ya finciko Yarinyar ya wanka mata marin da har sai da ta fad’i kasa itama gefen bakinta ya fashe, sannan yayi sauri ya kamo hannun Maryam, ganin jini ta koina yana zuba duk ya ma rud’e bai san lokacin daya kama k’asan rigar shaddar jikinsa ba ya yaga ya kamo hannun ya d’aure da kyallen sannan ya fara janta yana cewa “ta zo su tafi clinic, a dubata.” Duk ya rikice, dan har kwalla Maryam ta hango ya taru a idanunsa. Suna fita suka had’u da prep mistress d’in hakan yasa suka d’unguma har ita aka je akayi mata dressing, a tafin hannuta ta yanke amman Allah ya taimaka ba’ai mata d’inki ba. Har sukaje suka dawo yana jera mata sannu ko motsi tayi sai ya tambayi “mai takeso?” Har bakin unity gate ya rakata tukunna ya juya dan a lokacin an tashi daga prep. Kusan bai samu yayi ishashhsen bacci ba, juyi kawai ya dinga yi yana Allah Allah gari ya waye. Allah ya taimaka ma washegari za ta kasance Tuesday ne, so yanada su har double period. Kamar kullum yau ma Zainab tayi kwalliyarta suna zaune suna jiran shigowarshi, yau kamar da rashin mutunci ta tashi dan sai hararar Maryam take yi, tana fama yada mata magana har da cewa “ idan ma za ta ware gara ta ware tun wuri dan ba abinda za ta tayata da shi.” Ita dai maryam ta yi shiru tana fama da zugin da hannunta ke yi mata, ga idanunta da suka yi jaa, dan jiya bata samu isheshshen bacci ba. Shigowarsa ce ta sanya ajin yin shiru kowa ta maida hankalin ta gareshi, shi kam yau k’arara kowa sai da ya lura da kalar kallon da yake yiwa Maryam dan tunda ya shigo daga bak’in k’ofa ya kafeta da idanu har ya isa inda bench d’inshi yake, garin kallon ta ma har da d’an yin tuntub’e. Ganin tak’i d’agowa ta kalleshi yasa kawai ya amsa gaisuwar y’an aji sannan ya fara lesson..dictation ya fara kamar kullum dan baya musu note a board amma yaga Maryam d’in ta kasa yi, k’ok’ari takeyi ta rubuta da hannun hagu amma ta gagara, ganin tana neman fama ciwonta ga ciwon kan da ya addabeta yasa kawai ta tura littafin gefe ta kifa kanta a benchi. Abba kam zuwa yanzu ji yake kamar ya kori gaba daya y’an ajin ya lallasheta, ganin gaba d’aya hankalinshi baya ajin kar yaje ya fara musu dictating shirme yasa yayi rounding up, sannan yace “akwai mai question?” Mutane uku ne suka yi question ciki harda Zainab tanata faman karairaya, shi bai ma san tana yi ba, ya bata amsa daga haka yace “Let’s call it a day”. Sai a lokacin Maryam ta d’ago ta juya ta tambayi wata classmate d’insu ta ara mata note d’inta, bayan ta mik’o mata ta had’a da nata ta ajjiye a kan bench, duk a kan idonsa.. Har ya yi hanyar fita sai kuma kawai ya dawo ya d’auki littafin nata da na wadda ta karb’a za ta kwafa d’in, ya juya ya fita da sauri. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 11 Yana fita y’an ajin suka fara tofa albarkacin bakin su, har da masu cewa ‘ai tayi sneaking ta shigo da waya dan da gani free call suka kwana suna yi jiya shiyasa daga ita har shi idanuwansu suka nuna alamun rashin barci. Wata Ramlat wadda hostel d’insu d’aya kuma k’awar Zainab ce k’ut da k’ut tace “Tab! Yanzu girman kai zai k’aru, su o’o ba’a da had’add’en saurayi ma ana kallon mutane a kan hanci, ballantana yanzu anyi..” D’agowa Zainab tayi ta kalleta a take tayi shiru bata k’ara cewa uffanba. Abinda ya bawa Maryam mamaki shine har suka koma hostel, aka yi lesson na evening, suka sake fitowa night prep kwata kwata Zainab bata ce mata uffan akan maganar ba. Sai dai kawai ta ga tanata yawan kallonta. Straight jss2 ta nufa tana shiga ta gansa a zaune a gefen sit d’inta kamar ko yaushe. Yana jin shigowa ya d’ago kai ya kafeta da ido har ta k’araso ta zauna ta gaidashi. A hankali ya amsa sannan yace “Ya hannun??” Itama a hankali tace “ da sauk’i.” Sannan ta fara k’ok’arin bud’e jakarta domin da d’auko littafi ta samu ta fara karatu. Littattafan d’azu ya mik’o mata yace “gashi, gobe sai ki bata nata ko?!” D’agowa ta yi ta kalleshi sannan ta d’auka littafin ta bud’a da niyyar ta d’an k’ok’arta ta kwafa, saboda Yarinyar har ta fara mata maganar littafinta wai ‘tanaso za tai karatu’, amma kawai sai ta ga wani had’add’en rubutu ya baiyyana daga dai dai inda suka tsaya, dubawa tayi tai comparing da na k’awar tata taga Note d’in nata ya zama complete, kallonshi tayi taga shima Itan yake kallo da murmushi a kan fuskarshi kafin yace “Ko ban iya rubutu ba?”. Bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba saboda yadda yayi maganar yana wani langab’ar da kansa, kuma harga Allah tayi mugun jin dad’in taya ta d’in da yayi dan bata san ya za tayi ba, bata da wanda zata rok’a ya tayata dan kusan kaff y’an class da room d’insu daga safe zuwa yanzu kamar haushin ta duk suke ji wanda ita bata san dalilin su na Jin haushin nata ba. Ganin tana murmushi kawai ya tsaya yana ta kallon ta dan ji yake kamar kar ta daina. A hankali ganin ya kafe ta da ido tace “Ni ka daina kallo na.” D’auke idanunsa yayi daga fuskanta yana murmushi….idanunsa suka kai kan hannun rigarta, dayake da d’an jini jini a jiki tun na jiya, har zai tambayeta dalilin da ya sanya bata wankeba sai ya tuna da hannunta, kuma a yadda take da shiru shiru d’innan ya san ba zata iya saka Junior wanki ba. Dan haka kawai sai yace mata “Ki dinga kawo kayan wankin ki zan na kai miki wajen wanki har zuwa lokacin da zaki warke .” Murmushi kawai tayi tace mishi “to” Sannna yace duk note d’in da bata yi ba ta kawo, da kyar ta bashi na physics, ragowar kuma tace “za ta k’ok’arta da hannun hagu.” Har aka tashi suna hira yau kam ta sake dashi, hakan kuwa yayi mishi dad’i sosai. Washegari kam da bata zo da wankin nata ba taga b’acin ransa matuk’a, dan kicin kicin yayi, kuma ko da aka tashi da kyar ya yarda ta tafi bayan ya sanya ta ta rantse akan washegari za ta kawo.” Hakan kuwa

Chapter 8 of 32