Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shiga, ya tada motar tukunna idanunta suka sauk’a akan Sadiya wadda take tsaye a k’ofar gidansu gaba d’aya hankalinta yana a kansu….. Tafiya mai d’an nisa sukayi dan Maryam kam kanta har ya juye abunka da wadda bata fita sosai, tana cikin y’an kalle kallenta suka iso wani tafkeken masallaci a d’an gaba kad’an akwai hotel… Wuce masallacin sukayi ya shiga cikin hotel d’in wanda ya gaji da had’uwa ga securities ta koina, ya nemi waje yayi parking. Babu yadda bai yi da ita akan ta fito ta shiga cikin hotel d’in saboda shi yanaso ya je ya samu limamin yayi mishi bayanin komai, kuma akwai y’an shirye shiryen da yake so ya fara so zai kama mata d’aki ita d’aya shikuma ya fara preparations amman tak’i tace “ita a mota zata jirashi har yaje ya dawo”, hakanan ba yadda ya iya ya kunna mata AC ya bata mukullin ya kwashi abubuwan da zai buk’ata. Sai da yaje wajen Limamin suka tattauna sannan ya fito ya tari motar haya ya shiga aikin gabanshi. Sai wajajen 12 tukunna ya dawo Maryam har tayi bacci ta tashi ga tsoro ga yunwa, yana zuwa ya kwankwasa, da kyar ta iya bud’e k’ofar ya shigo mata da abinci sannan yace bara yaje yayi Sallah idan an idar zai zo su wuce. Haka kuwa akayi sai wajen 2:00pm Time d’in masallacin kowa an watse tukunna ya dawo. Yana zuwa ya sa key sannan ya umarce ta da ta koma baya, bayan ta koma ya tada motar yaja suka isa bakin masallaci. Wani dattijo cikin alkyabba da rawani suka tsaya suka d’auka a bakin masallacin sannan suka hau titi, basu yi wani tafiya mai nisa ba suka gangara kan hanya suka shiga wani layi, a bakin wani gida sukayi horn aka bud’e gate d’in suka shiga. Bayan sunyi parking sun fito dattijon ya nuna musu babban parlourn gidan yace wa mai gadi “ya kaisu gurin Hajiya” Shi kuma ya nufi parlourn bak’i dan yanada bak’i. Matar mai kirki sosai bayan sun gaisa ta dinga yi musu hira aka kawo musu abinci kala kala, Maryam kam fitsarine yake neman yi mata illa ga Abba a wajen balle tace zata yi fitsari, Allah ya taimaketa matar ta shiga tambayarta “ko tayi sallah?” Da sauri ta mik’e tana cewa “a’a” Nan ta nuna mata d’aki ta shiga….sai da tayi sallah tukunna ta fito suna cikin cin abinci wannan dattijon ya shigo….. Sake gaisawa suka yi kafin ya juya ga matar tashi yace ne “Yakubu ne k’anin Yahaya, kin ganesa ai ko” Da mamaki matar take kallonshi, nan ta hau yi mishi tsiya tana cewa “baya ziyara.” Gyaran muryar da dattijon yayi ne ya katsesu, sannan ya kalli Abba yace “nayi waya da Yahaya yanzu ya tabbatar mini da abunda ka fad’a min d’azu, yace tare kukaje dashi jiya. Amman ni da zaku bi ta shawarata da ko Mahaifinta ko wani d’an uwanta a samu a wajen tukunna, ina ganin hakan zai fi, ko?”. A hankali cikin girmamawa Abba ya hau yi mishi bayanin komai…sai a yanzu matar take fahimtar ba amarya da ango baneba yet. Bayan ya kai aya ne dattijon ya sauk’e ajiyar zuciya sannan cike da gamsuwa da zancen nasa yace “ai shikenan!! In dai maza sun riga sun gama magana batun mata ba biyeshi akeyi ba…” Bai gama rufe baki ba wasu magidanta responsible su uku suka shigo, d’auke da huhunan goro da packs d’in alawowi. Zama d’ayan yayi sannan yace “Akaramakallahu barka da rana ga sak’on da kace in taho dashi nan.” Amsashi yayi sannan yayi mishi nuni da su ajjiye. Bayan sun ajjiye an gaggaisa anan yake shaida musu “Aure za a d’aura, za suyi shaida”. Nan suka amince. Limaminne ya umarci Yakubu da “ya kawo sadaki.” kamar jira yake, nan ya zaro dubu talatin a aljihun shi…a take aka gudanar da duk abunda ya kamata, Yakubu ya kanshi wakili, limamin nan kuma ya yiwa Maryama. A take a falon aka d’aura auren Yakubu Umar Farouk mai turare Da Maryam Muhammad Madu akan sadaki naira dubu talatin…. Aka raba goro da alaawa a y’an falon sannan aka kwashe ragowar domin rabawa In an fita masallaci dan har an fara kiraye kirayen sallar la’asar. A gidan suka yi har sallar Magrib…matar mai kirki tanata nan nan da Maryam, ita dai Maryam Allah Allah take su tafi dan ta k’agu su koma gida, dukda yadda gabanta ke ta fad’uwa amman dai tanaso taje ta tunkaresu a tura ta k’are!. Suna idar da Sallar Magrib d’in wani Yaro ya shigo d’akin da alamun d’an matar ne yace “wai ance Maryam ta fito zasu tafi.” Ai kuwa zumbur!! Haka ta mik’e har matar har tana tsokanarta….ita dai tayi mata godiya ta kimtsa suka fito tare da matar. Y’ar guntuwar nasiha mai ratsa jiki Limamin nan yayi musu sannan yai musu fatan alkhairi suka mik’e suka yiwa juna sallama suka nufi k’ofar fita daga parlourn. Abba ne a gaba sai Maryam wadda ke bi mishi baya bumper to bumper.. …goshi da k’irjinta ne taji sun bugu da gadon bayan shi sakamakon burkin da ya jaa ya tsaya chak! Lokaci guda, yak’i yayi gaba yak’i yayi baya. Daga yadda yake tsaye zaka iya ganin yadda jikinsa yake karkarwa sannan duk ya rikice tashi d’aya!. Magana yake son yi amman sai ya hau in ina sam ya gagara furta koda kalma d’aya mai ma’ana. Bata dawo daga mamakin abinda ya firgita Abba haka lokaci d’aya ba taji an d’auke shi da wani mahaukaciin marin da saida ya kai ga kaiwa k’asa ya tsugunna a gurin. Tsugunnawar da yayi ne ya bata damar ganin mutumin da yake gaban su ya tare k’ofar, kana ganinshi ba sai an fad’a maka ba ka san shine Mahaifin Abba, dogo ne sosai fari k’al kyakkyawa yana mugun kama da Abba da Yayanshi da suka zo tare jiya, sai dai shi ya d’an manyanta, kana gansinshi kaga tsohon dattijo. Muryarshi ce ta dawo da ita daga nazarin data tafi jin ya daka wata uwar tsawa yana cewa “Out of my way! stupid boy!!!”. Maryam bada ita ake ba amman da sauri ta matsa ta koma bayan matar gidan da itama duk ta rikice ta b’uya. Shima Abba da sauri ya tashi ya matsa yana shafa marin da aka yi mishi. Cike da k’asaita mahaifin nasu ya k’araso cikin parlourn Yayan Abba da wasu maza biyu suna binshi a baya, sai kuma wani Yaro matashi da kayan sojoji a jikinshi. Kujera inda wannan Limamin yake tsaye ya samu ya zauna ya d’aura k’afa d’aya kan d’aya, ko takalmin shi bai cire ba haka ya shigo mishi tsarkakakken falon da shi. Ahankali Limamin ya d’an zauna akan tum tum d’in kan kafet sannan yace “Barka da dare Daddie!”. Batare da ya amsa shi ba yace “Did u just got them married??.” Cike da kwarin guiwa yace mishi “Na’aam.” Gyara zamanshi yayi ya fuskanceshi da kyau kafin yace “D’ahiru you know I can sue you right??”. Wannan karon murmushi Limamin yayi, kafin yace “A tsarinka zaka iya suing d’ina, amman a musulunce ba zaka iya ba, dan Yahaya ma magabacinshine, dan haka kuwa kaga ba zaka iya suing d’ina ba!. Bayaga haka, Abba iya shi kad’ai ya isa yiwa kanshi wakili….” “I’ll get back to you later.” shine kawai abinda Granpa yace dashi cikin katseshi sannan ya mik’e ya isa gaban Abba ya tsaya. Hannunshi ya mik’a baya alamun yana so a mik’o mishi wani abun, da sauri Daniel ya zaro wasu takardu da international passport ya mik’o mishi. Ajiyar zuciya ya sauk’e, kafin yace “Abba, d’azu da Dahiru ya kira Yayanku muna tare!. Jiya na bawa Yayan naka sak’o nace ya fad’a maka, ashe bai gaya maka ba, right?” Bai jira jin amsar shi ba ya cigaba “I’m really disappointed in you, and bana so inyi punishing d’inka harshly which is why I’m doing this… Take this!” Yayi maganar yana mai mik’a mishi passport d’in hannun shi. Jiki a mace Abba yasa hannu ya karb’a, passport d’inshi ne da wasu takardun da bai gama dubawa ya gano na menene ba muryar Mahaifin nashi tasa ya maida hankalinshi gareshi jin yana cewa “Ga passport d’inka, nayi k’ok’ari wajen ganin na had’a har da na amaryar taka in yi muku tare, amman sai na fahimci ita d’in y’ar gidan talakawa ce bata tab’a fita koina ba, so wannan aikinkane yanzu zaka yishi, tunda kaika kwaso ta. Na baka 5 hours ka bar k’asar nan! Bana son ganin ka…ba zan iya zama a country d’aya da kai ba. Abba ko labari idan ka ji zanje k’asar da kake, to ka tabbatar ka bar wajen ko kuma duk yadda zaka yi to ka tabbata bamu had’u ba. I don’t think zan iya yafe maka laifin da kayi min sannan bana son in yi punishing naka harshly kuma na san indai Ina ganin fuskarka ko kuma kana kusa dani to tabbas zan yi maka abunda ba zaka tab’a mantawa ba. So, as you can see I’m doing my very best to stay calm! All I want from u shine ‘wannan ya zama last time da idona zai ga naka!! You want freedom right? Kana so kayi abinda kakeso ka auri wadda kakeso ko? Well, Abba ga freedom nan! I’m giving it to you….Idan ka kuskura muka had’u, ko kak’i barin k’asar nan, u pretty much know wat I’m capable of! Dan wallahi i promise sai nayi making life d’inka a living hell!!. Kayi addua In iya yafe abinda kayi mini kafin In mutu, maybe I can forgive and call u back.” Har ya juya zai fita, sai kuma ya dawo ya zo inda su Maryam suke ya tsaya, cikin kakkausar murya yace “Maryam!” Maryam jikinta har tsuma yakeyi, cikin sake b’oyewa a bayan matar liman kamar zai daketa ne, tace “Naa ‘aa mm.” Cike da tsana yake kallonta kafin yace “D’a na kikeso ko? A kanshi kika bar iyayenki kika gudo kika aure ko? Well congratulations to you, da shigowa familyn MT! But let me assure you! Wallahi karnukan family d’ina sai sun fiki daraja! Sannan ko bayan raina ban amince Y’ay’anki suyi bearing family name d’ina ba. Kuma inaso ki sani, zan iya yafewa Abba kamar yadda na fad’a amman ke kam nida ke karki kuskura ki bari muga juna suma kuma Y’ay’anki haka, bana so su zo ko kusa da inda nake ma talkless of mu had’u da su. Idan kika kiyaye wannan watak’ilan ki zauna lafiya, idan kuwa baki kiyaye ba to kinga mahaifinki da mahaifiyarki da wannan k’anwar taki, I’ll make sure na kulle su a prison d’in da ko kusa dashi baki isa zuwa ba ballantana ma kiyi tunanin fito dasu, this is my promise to you!!” Yana gama fad’in haka ya bawa Daniel umarnin ‘ya kai Maryam da Abba suyi preparations d’in tafiya sannan ya ajjiye su a airport, within 5 hours!’. Yana gama fad’in haka ya juya ya nufi hanyar fita, yana mai yiwa Limamin alk’awarin dawowa idan ya samu lokacinshi, dan ba zai barshi haka ba wallahi!…. Kuka Maryam ta dinga yi kamar ranta zai fita. Tsoro gaba d’aya duk ya rufeta!! Tayaya za a ce babu ita babu family d’in Mijinta waenda sune garkuwar y’ay’anta?? da wanne dangin y’ay’anta za suyi tutiya idan sun taso? dan ba a ado da dangi d’aya! Daman Abba ya san haka mahaifinshi yake amman shine bai sanar mata ba?? Tukunnan ma taya za a fara tunanin barin ta k’asar nan har abada?? Dan in har lissafinta ya bata daidai ana nufin ita da Abban zasu tafi……. Waennan al’amura da tunanin ne suka kuma hargitsa ta, ta dinga rusa kuka ko sauraronsu Abba da suke ta bata hak’uri bata yi… Daniel ne ya d’an rankwafo kan Abba yayi gyaran murya sannan ya nuna mishi agogon hannunshi, harararshi Abban yayi sannan ya mik’e ya fita Daniel d’in yabi bayan shi suka hau shirye shirye gadan gadan. Bai sha wahalar yi mata passport ba, daman yanada k’aramin hotonta daya cira a file tun suna makaranta, amman da aka zo kan visa ba k’aramin wahala ya sha ba, duk inda yaje ‘embassy’s d’in Kano’ sai ace visar gari dole sai mutum ya jira. Dakyar ya samu Yayanshi ya kulashi dan shima duk ya tsorace kar Mahaifin nasu ya juyo kanshi..Nacin da Abban ya dinga yi masa ne yasa ya amsa wayar da cook d’in gidan yaketa rok’on shi ya karb’a, yana karb’a Abba ya kwararo mishi abubuwan da yake da buk’ata….. Da kyar da taimakon sa da taimakon kuma wani baban Abokinsa Maryam ta samu visiting visar Madina, amman shima sai nan da 7 days jirgin zai tashi kuma a Lagos, gashi sauran 1 hour 5 hours d’in da aka bashi ya cika. Da sauri ya shiga nema musu wani ticket d’in daga Kano zuwa Lagos. Aka yi sa’a kuwa ya samu da wuri, zai tashi in the next 20 minutes, a lokacin sauran 15 minutes time d’in da Mahaifinsa ya basu ya cika. A gurguje suka samu suka k’araso gidan Limamin shi da Daniel wanda yake ta binshi a baya yana nuna mishi agogo duk bayan minti talatin, Abba ji yake kamar ya shek’e sa amman kuma sanin da yayi ba laifinshi bane shima saka shi akayi kuma bai isa ya hukuntashiba yasa kawai ya rabu da shi. Yana shigowa a gurguje suka had’u da Limam suka nufi d’akin da Maryam take. Ai anan kuwa ta birkice!! Ta dinga kuka tace “wallahi babu inda zata je, idan ma zata tafi tou sai taje taga su Shuwa tayi musu sallama sun saka mata albarka.” Tabbas sun san ta fisu gaskiya ata koina amman zuwa unguwar su Shuwa ma kad’ai sai ya d’auki minti ashiri bare dawowa, nan kuwa suna kusa sosai da airport… Daga Liman har Abba hadda ma matar Liman d’in duk sun rikice rok’on Maryam kawai suke suna lallab’ata suna mata nasiha akan tayi hak’uri ta bi mijinta su tafi watarana sa dawo…amman fur tak’i!!. Daniel ne yayi knocking ya shigo, har Abba zai yi mishi masifa dan ya ishesa! Sai yaga ya mik’o mishi envelope. Sai da yasa hannu ya karb’a sannan Daniel d’in yace “driver d’in Daddie ne ya kawo yanzun nan yace wai a baka.” Jikin Abba har rawa yake yi haka yasa hannu ya zaro takardar ya fara karantawa… “Sauran minti goma jirginku ya tashi, yanzu munzo wucewa na sake ganin motar Daniel a k’ofar gidan Liman, which means baka tafi ba and still kuna ma gidan, jirginku zai tashi in the next 10 minutes, I know maybe nan da 7 minutes zaku iya isa airport, which means zaku k’ara 2 minutes akan time d’ina…. Already daman d’azu mun tafi da motarka, tunda ni na siya maka! Kayanka da credentials d’inka da Yahaya ya had’a maka suna boot d’in motar Daniel… Ina umartarka da ka bawa Daniel atms d’inka da komai na kadara ya taho mini da su… If u like ku ci gaba da wasting time, and I’ll not hasitate to keep punishing u. Ina sane da duk wani single movement d’inka.” Kawai gani sukayi Abba ya durk’usa a gaban Maryam ya kama hannayenta duka biyu ya fashe da kuka, cikin kukan yake rok’onta yana “Dan Allah dan Annabi Maryama ki tashi mu tafi yanzu shine abu mafi amfani, duk tirjiyarki a k’arshe tafiya zamu yi…. wannan b’ata lokacin da muke yi baki san abubuwan da kike janyo mini ba, zamu dawo idan nayi settling I promise!!!” Kuka yake yi kamar k’aramin Yaro, hakan yasa Liman shima ya ci gaba da lallab’ata tareda yi mata zazzafar nasiha mai ratsa jiki…. Jikinta duk yayi sanyi hakan yasa tace “zata tafi amman sai yayi mata alk’awarin zasu dawo very soon, kuma hadda su Liman za aje a bawa su Shuwa hak’uri.” Duk suka amince hakan yasa suka mik’e da sauri sukayi hanyar fita, su Liman suna ta binsu da fatan alkhairi haka suka shiga mota suka tafi, sai sauri sukeyi, dan tuni lokaci yayi.! Allah ne ma ya taimakemusu aka d’an samu delay da tuni sunyi missing flight d’insu. A gurguje ya had’a duk wani abun da Granpa yace ya bada. Ya bawa Daniel d’in yace “ya bashi” sannan suka hau layi. Sai da Daniel ya tabbatar yaga tashin girjinsu tukunna ya juya ya koma mota ya nufi gida da tunani barkatai a ransa….. SHARE PLS. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 17 Hakanan yana ji yana gani ya bayar da komai ya d’auki d’an briefcase d’inshi na credentials d’insa suka wuce Lagos. Yaso su zauna a Lagos d’in har zuwa lokacin da Mahaifin nasa zai d’an sauk’o daga fushin da yayi. Amman ranar da suka cika kwana biyar a garin! Granpa yayi musu chune! Y’an sanda suka zo suka tafi dasu…aka dinga bincikensu akan laifin da basu san dashi ba. Kwanan su d’aya a station daga k’arshe wani police ya kawowa Abba takarda, yana dubawa yaga sak’on Granpa d’in ne ‘shine ya saka aka kamasu! As a punishment na 5 days d’in da suka k’ara, sannan he should either choose barin k’asar ko kuma zaman station dan zai saka suyi ta zama a wajen ne har abada ba tare da sun san laifin su ba.’ A take Abba ya zab’i tafiya, yayi signing inda aka nuna mishi dan Maryam har ta fara zazzab’i sakamokon sauro da wahalar wajen, shi kansa da yake Namiji daurewa kawai yake yi. Suna fitowa ya mayar da ita masauk’in su ya fita y’ar buga buga dan kud’in da Yaya ya saka mishi a gaban suitecase d’in credentials d’insa sun k’are tass. Bai wani samu kud’i sosai ba har dare haka ya dawo, gashi jirginsu 4:00am zai tashi. Tunda ya tashi Maryam yace “ta fara shiri” take faman yi mishi kukan data mayar sanaarta tun ranar da aka d’aura musu aure. A haka suka isa airport har ana d’an kallonsu… Bayan y’an bincike…jirginsu ya d’aga zuwa k’asa mai tsarki. Tun kukan Maryam yana iya fita har muryarta tazo ta dishashe, ji take yi kamar ta rufe Abba da duka!!! Duk shine ya ja mata shiyasa duk faman aikin lallashin ta da yake ta yi ta yi banza dashi ta k’i kulashi, shi kam babu abunda yake yi sai aikin lallashi dukda kuwa shima kamar ya fashe da kukan haka yake ji, saboda in suka sauk’a bai ma san ta ina zai fara ba, duk wani means na kud’i an kwace a hannunshi! Gashi bai san tayaya zai samu aiki ba, ga iyali a tare dashi…tabbas ya zame masa dole ya tashi ya nemi abunyi Suturarsu kanta kwata kwata set bibbiyu ne dasu, daga waenda suka baro Kano dasu a jikinsu sai waenda ya saya musu set d’aya d’aya a Lagos….. Yana cikin wannan tunanin jirgin su ya sauk’a a garin Madina. Maryam ya d’an tab’a a hankali wadda bacci ya fara kwasa. A hankali ta bud’e idanuwanta da suka kumbura suka k’ank’ance suka yi jaaa. “Mun iso.” Shine abunda yace mata sannan ya fara k’ok’arin mik’ewa itama ya kama hannunta ya mik’ar da ita suka bi ayarin y’an jirgin da suke ta sauk’a, suma suka sauk’a. Bayan an gama sauk’a mutane suka nufi wajen d’aukar kayansu.. Su kuwa su Abba suite case d’inshi ce kawai garesu, tana da d’an girma shiyasa ta cinye har ragowan kayansu set d’aya d’aya. Waje ya samu ya zauna ya fara duba suitecase d’in, bayan sun fito, kamar yana neman wani abu. Allah yaso su kuwa akwai y’an chanji a ciki…so da yawa idan Yayanshi zai zo yakan biyoshi su taho tare yayi masa rakiya dan yana son garin, ya tuna lokacin daya dawo da kud’in yana taso ya chanja su bai samu time ba haka ya hak’ura ya d’aga k’asan suitecase d’in credentials d’in nashi ya saka. Shiyasa yanzu da wannan ranar ta fad’o mishi a rai ya duk’ufa yana dubawa had’e da adduar Allah yasa har yanzu kud’in suna nan, ai kuwa ya tsince su yadda ya barsu. Abun hawa ya fara nema musu, da kyar kuwa ya samu, daganan yace “a kaisu wani d’an hotel haka mai d’an saffa saffa.” Suna zuwa ya kama d’aki d’aya. Sai da ya kai Maryam d’akin yace mata “tayi wanka ta huta” tukunna ya fito domin ya siyo abinci, acikin hotel d’in ya siyo abincin, sannan bai yarda ya bar wajen ba sai da ya samu aiki a restaurant d’in cikin hotel d’in, bayan ya nuna musu takardunsa kuma sunji yana jin larabci suka bashi aikin ‘waiter’!! Bai wani damu da k’ask’ancin aikin ba ya amsa yana mai farin ciki. Yana dawowa da abincin ya tarar da Maryam a yadda ya barta tana kuka, hawaye ne ke fita kawai amman ba sauti tsabar yadda muryarta ta disashe. Da sauri ya k’araso ya d’agata ya zaunar sannan ya ci gaba da aikin lallashi. Da kyar ta yadda taci abinci sannan ta shiga tayi wanka ta fito. Shima mik’ewa yayi yaje yayo wankan sannan ya fito ya tarar da ita a zaune ta mayar da kayanta. A hankali ba tareda ta kalle shi ba tace “Inane gabas? Zanyi sallah.” Shima kayan nashi ya maida sannan yaje ya d’aga window ya hau duba garin Alk’iblar masallacin da ya hango ya duba kafin ya zo ya nuna mata. D’ankwalinta ta shimfid’a tayi sallar walha…. Yana zaune ya baza takardu yana dubawa dan neman mafita..ta ida sallarta ta nemi waje ta kwanta yana ta duba tarkadun shi da had’a su waje d’aya a haka barci ya saceta don tunda suka je station basu samu nutsuwa ba. Kiran sallar azahar ne ya tayar da ita. Tana juyawa taga Abba shima yana baccin a inda ta barshi da takardun shi a baje da alamun ma a zaune yayi baccin wahalan… Zuciya da abunda take so sai taji gaba d’aya ya bata tausayi. A hankali ta k’arasa taje ta durk’usa a gabanshi tana k’are mishi kallo, kana ganin yanayin fuskarshi ka san ba dad’in baccin yakeji ba kawai dai yana yinsa ne. Hannu ta saka ta d’an tab’a gefen inda yake jingine. A hankali ya bud’e idanuwanshi, ganin ya farka yasa da sauri ta mik’e tana cewa “ka tashi kayi sallah”daga haka ta fad’a toilet ta yo alwallah. Tana fitowa shima ya shiga bai fito ba saida ya sake yin wanka. A zaune ya tadda ita tayi shiru da alamun tunani take yi. A gurguje ya shirya, ya tada sallah. Bayan ya idar da sallah ne ya zo ya kwashe ragowar chanjin da suka yi sannan ya juya ya fita. Bai wani dad’e ba ya dawo da abinci da y’ar rigar da suka bashi da hula. A hankali ya zo ya zauna a kusa da ita. Da farko kamar ba zata yi mishi magana ba sai kuma tace “Ina wuni.” Amsawa yayi, sannan yace “Ga abinci nan, d’azu naso gaya miki zan fara yi musu aiki a restaurant saboda kinga muna buk’atar kud’i a hannunmu, amman sai naga kinata kuka. Zan d’an fita yanzu In k’aro mana kaya ko set bibbiyu ne kafin muga abinda Allah zai yi. Zan fara neman wani aikin. Kiyi hak’uri yanzu muji da yadda zamu yi surviving… In sha after that immediately zan san yadda zan yi ko ke kad’ai ce kije ki wajen su Abba kinji ko?” A hankali ta d’aga mishi kai sannan ta mik’e. Gani tayi shima ya mik’e sannan ya kamo hannayenta. D’agowa tayi ta kalleshi taga shima itam yake kallo, a hankali yace “That’s all? Babu irin adduar ‘Allah ya bada sa’a dinnan? Maryama, kuma still har yanzu ranki a b’ace yake.” “Allah ya bada sa’a.” tace, sannan tayi niyyar matsawa amman furr! Ya k’i ya tare hanya, shifa sai tayi murmushi kuma tayi mishi addua tukunna zai fita. Hakanan ba yadda ta iya ta k’ak’alo murmushi tayi sannan ta yi mishi addu’ar. A hankali yasa hannu yayi hugging d’inta yafi 5 minutes tukunna ya sauk’e ajiyar zuciya yace “Ameen.” Sannan ya juya ya fita. Sai yamma tukunna ya dawo ya kawo mata abinci, kana ganinshi a gajiye yake dan restaurant d’in ana cika sosai kasancewar a hanyar airport d’in yake kuma shi kad’ai ne sannan daman basuda waiter sai shi kad’ai. Sallah kawai yayi ya d’an ci abincin kad’an sannan yace “mata zai koma.” Gaba d’aya se sai tausayinshi ya sake kamata. Ganin ya tsaya yasa tace “a dawo lafiya.” “Ameen” yace, kafin yace “Murmushin fa??.” Wannan karon ba k’ak’alo shi tayi ba, ji tayi kawai ya sub’uce mata. Sai k’arfe goma sha d’aya na dare ya dawo. Kamar yadda yayi alk’awari da kaya ya taho musu dashi.. AlQurani mai kyau irin mai pieces d’innan izu sittin amman duk izu biyar a rabe ya siyo, da inner wears d’inta set biyu, sai abaya da hijab. Shi kuma ya siyawa kanshi gajeran wando da jallabiya Sai lotion, brush da

Chapter 13 of 32