Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
k’arasowa bakin k’ofar falon taji fad’uwar da gabanta yake yi ya tsananta!! Da kyar ta iya saisaita kanta tayi knocking, ta ciki taji muryar Baba Bashir yana cewa “ta shigo” Hannu tasa ta murza handle d’in k’ofar sannan ta tura had’e da tura kai ta shiga, kanta a k’asa. Haka nan ta kasa d’agowa sakamokon yadda zuciyar ta ke bugawa sosai sosai, sai da ta samu waje ta zauna tukunna ta d’ago kanta da niyyar gaishesu...... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 14 idanunta suka sark’e a cikin na Abba wanda ya kafeta da ido ko alamar kyaftawa bayayi..... Mutumin dake zauna a gefen sa mai tsananin kama da shi ne taji yana cewa “Ma sha Allah, mun sameki lafiya??” Cikin d’an jin kunya ta sunkuyar da kanta sannan tace “ina wuni.” Yana murmushi ya amsa mata, Ita kuma ta juya ta gaida Madu da Baba Bashir, sannan ta gaida Abba wanda ya kasa daina kallonta, ko kunya ta kasa hanashi kallonta a gaban iyayenta. Da kyar ya iya cewa “Lafiya” Wanda ba ma kowa ne ya ji ba sai ita d’in da take kallon fuskarsa. Madu ne yayi gyaran murya sannan ya fara magana “Maryama wannan shine Yayan Abba” Yayi maganar yana nuna wannan mutumin da yake zaune a gefen Abba. Jinjina kai Maryam tayi sannan ta sake gaidashi kanta a k’asa Murmushi shima yayi ya sake amsawa dan a gaskiya Maryam ta burge shi, yanayin nutsuwa da hankalinta sun burgeshi. Madu ne ya cigaba da cewa “Lokacin da muka dawo daga hajji mun baku labarin wani bawan Allah da ya taimakemu aka tseratar da Usman ko?” Jinjina kai ta kuma yi. Ajiyar zuciya Madu ya sauk’e kafin yace “To gashi nan a zaune” yayi maganar yana sake nuna mata Yayan Abba, da sauri ta d’ago ta sake kallonshi wanda shi kuma a yanzu Abba yake kallo har yana d’an tab’ashi da alama nuni yake yi masa da ‘kallon ya isa haka’. Modu ne ya d’aura da cewa “Sunanshi, Alhaji Yahaya Umar Farouk mai turare, d’azun nan aka yi sallama ana son ganina, abun mamaki ina fita sai na ganshi, mutumin da muke nema ruwa a jallo sai gashi yau har gida. Daman ni tun ranar da naga Abba a makarantar ku naso tambayarshi saboda tsananin kama da naga sunayi, amman kasancewar yadda abubuwa suka kasance a ranar ya sanya ban samu dama ba.” Alhaji Yahaya ne yayi gyaran murya sannan yace “Ina mai baku hak’uri, da kuma rok’on mu manta da wanchan zancen har Abada! Saboda hakan ba abune mai maana ba especially idan muka yi duba da yanayin hankali da tarbiyyar Yaran. Laifin su d’aya da suka yi shine da suka tsaya kula juna a makaranta, kowa yasan hakan sab’a doka ne, wanda hakan ne ya sanya ma maganar ta samu gurbi. Ban san waye ya had’a kuma ya fad’i wannan labarin ba amman tabbas na san k’arya ne…. Mu uku mahaifin mu ya haifa a duniyar nan, bani da d’an uwa mafi kusanci dani kamar Abba, shiyasa ko a lokacin da nayi aure ma tare muka tare a chan part d’ina dashi kuma har yau a gidana yake…. na san abinda Abba zai yi na san wanda ba zai yi ba, dukda ance ba a shedar mutum amma ni kam zan shedi Abba a duk inda yake. Na hanashi fita ne tun dawowarshi ba dan komaiba sai dan saboda ita Yarinyar, saboda na san ko wanne Uba idan aka fad’i irin wannan maganar akan y’arsa dole zai d’au zafi ba kad’an ba, so shiyasa na hanashi zuwa nace masa ya d’an bari abubuwa su lafa tukunna sai mu zo, dan already daman na saka a raina zamu zo neman aurenta, dan a duk fad’in duniyar nan bata da mijin da yafi dacewa ta aura kamar Abba. Sannan Abba ya tabbatar mini da soyayyar ta a cikin zuciyarshi, nutsuwa da hankalinta duk ya gamsu dasu sai a lokacin ne ma yake fad’a mini ashe lokacin da yayi rashin lafiya har na taho ban samu munyi sallamaba wai duk a ta dalilin ya nemi gidan nan ne bai samu ba. Kuma ya fahimtar dani Yarinyar da aka zab’a mishi a gida sam baya sonta, ko ya aureta ba zasu zauna lafiya ba, shiyasa naga ya dace muje mu samu Mahaifin mu muyi mishi bayani yadda zai fahimta tukunnan muzo nan To amman kuma jiya sai ya zo mini a hargitse wai jibi za a d’aurawa Maryam aure!! Da na koreshi nace ‘ya jira har sai lokacin da na d’iba mishi yaga maryam d’in yayi tukunna zamuzo’ dan ni a tunanina kawai fad’a yakeyi ba wani aure, dan naga ya k’agu ya ganta d’in A take ya sume min, da kyar ya farfad’o yau da safe, bayan Likita ya tabbatar mana jinin shi ne ya hau saboda damuwar da take neman yi mishi illa, shiyasa a take na saka shi yayi wanka ya d’an ci abinci ko mai d’akina ma ban samu damar gayawa ba muka taho.. A labarin Maryam, ta gayawa Abba cewa ka ce ranar Jumaah zaka aurar da ita, so a iya yadda na fahimta watak’il baka riga kun tsaida mijin ba,ko? Saboda haka gamu nan mun zo neman aurenta ban sani ba ko za a amince a bamu… …….Very short ya d’an basu biography d’in familyn ‘Mai turare’.” Dayake sanannen family ne, nan suka ce “ai suna jin ma sunan familyn..” Baba Bashir ne yace “Alhaaji munji abinda yake tafe da kai, amman kafin komai da farko muna so mu fara yi maka godiya!! Mun gode sosai da taimakon da kayi kwanakin baya, Allah ya saka da alkhairi. Sannan magana ta biyu, ni dai kamar uba nake a wajen Maryam dan haka na bawa Abba ita halak malak!! Idan Allah ya kaimu gobe Jummah indai a shirye kuke za’a d’aura aure, sai dai In wani mugun hali muka ji a kansa (dan za muyi bincike kamar yadda ake yi In sha Allah) amman bayaga haka gobe iwar haka bi’izinillahi ta’ala an d’aura musu aure.” Da sauri Madu ya kalle shi, kafin yace “Bashir maganar Usman fa, ya zamu yi?”. Murmushi Baba Bashir yayi sannan yace “kar muso kanmu anan mana, Usman fa shi kad’ai yake son Maryam ita bata sonshi, wannan Yaron kuma” yayi magana yana nuna Abba sannan yace “yana sonta itama shi takeso. Sannan abu na biyu, wannan bawan Allah” ya nuna Yayan Abba sannan yace “Tun ranar da ya taimaki Usman muke son sake ganinshi dan mu gode mishi, yau gashi Allah ya kawoshi yana neman abu a wajenmu! Mai zamu tsaya jira???? Ka tuna shine fa silar fitar da Usman a wanchan had’arin wanda ba dan an gano gaskiya ba, da watak‘ila babu Usman a doron k’asa yanzu. Kuma dani da kai duk na san auren nan nasu sai yafi kwantar mana da hankali, saboda abubuwa da dama..” Shiruuu! Madu yayi…..tabbas duk abinda Baba Bashir ya fad’a babu k’arya a ciki, dan haka shima ya yanke shawarar ya bi bayan Baba Bashir d’in a take! Juyowa yayi ya fuskanci Maryam sannan yace “Maryama kina sonshi ko?” Dariya Baba Bashir da Yayan Abba suka yi sannan Baba Bashir yace “Kaima dai neman magana kake yi.” Murmushi yayi kafin yace “kawai ina son inji ta bakinta ne, ta fad’a a gaban kowa.” Sannan ya sake maimaita mata tambayar……cikin jin nauyi a hankali ta d’aga kanta alamar ‘eh’. “Alhamdulillah” shine abinda Madu yace, sannan shima ya tabbatarwa Abba ya bashi Maryam… Yace “Ba sai ya wani had’a lefe ba sadaki kawai suke buk’ata su zo da shi gobe.” Yayan Abban ne yace “Maganar b’oye b’oye babu ita a tsakaninmu kuma ni mutum ne daman straight forward…. A gaskiya! Ba lalle mahaifinmu ya yarda da d’aurin auren a gobe ba, duba da yadda ya riga yayi wa Abban mata kuma a yau zamu gaya mishi d’aurin auren, na san za a d’an kai ruwa rana, watak’ila yace sai nan da sati biyu dan zai d’anyi gayyata… Amman wannan duk ba matsala baceba, za azo a goben ko iya mu uku ne in sha Allah zamu d’aura auren, dan na lura Madu yana so ayi auren a gobe, inyaso daga baya sai a sake sabon aure mai taro idan mahaifinmu ya tsayar da rana…..” A hakan kuwa aka bar maganar. Murna a wajen Abba ba’a magana, dan ko kunya bayaji, haka nan ya zage ya dinga jero godiya ga su Madu, har sai da Baba Bashir ya fara tsokanarshi……: Sallamar Maryam suka yi ta tafi su kuma suka ci gaba da hirar su cikin mutunta juna kafin daga baya suka yiwa juna sallama suka tafi akan gobe za’a had’u a masallaci in sha Allah….. Da kyar Alhaji Yahaya ya lallashi Abba ya hak’ura ya bishi suka tafi saboda da shi ya dage ne akan sai ya ga Maryam tukunna zai tafi….. Shuwa da ragowar mutane sai bin Maryam suke da kallo, Yarinyar da take ta koke koke akan ita bata son auren, amman dubeta yanzu yadda ta ware dan ko makaho idan yaji muryarta sai ya tabbatar da tana cikin farin ciki, haka nan aka sakata a lalle aka yi kaulu lafiya tanata washe baki kamar ba itaba. Bayan sallar isha kowa ya watse….Madu da Baba Bashir suka nemi ganin Ya Usman, Baaba Talatau Ya Jamilu, Maman Shuwa, Shuwa da y’an uwanta..... SHARE PLS. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 15 Ba tare da b’ata lokaci ba Baba Bashir ya fad’a musu duk abinda ya faru d’azu… Tun kafin ya k’arasa Baaba Talatu tace “zancen banza ma kenan!!! Ai indai gaskiya za a bi to haramun ne neman aure a cikin aure”. Cikin b’acin rai Baba Bashir yace “waye kenan yake yi miki zancen banzan?? Sannan ban gane maganarki ta ‘neman aure cikin aure’ ba! Shin a tsakanin ni ko Madu waye kika tab’a ji ya cewa Usman ya bashi Maryam?? Shiyasa fa d’azu na kyaleku ban kiraku ba, dukda yadda na so ace ke da Shuwa kun zo kun yiwa mutumin nan godiyar abinda ya yiwa Usman kwanakin baya, amman kawai sai na fasa domin na san k’aramar kwakwalwa gareku, indai kuka lura shine yayan Abba sai kunsa munji kunya…” “Ko kuma dai an so shirya munafurci shiyasa aka k’i kiran nasu ba!” Maman Shuwa ta fad’i hakan sannan ta mik’e tace “Madu na lura ba zaka iya tsawatarwa Yarinyar nan ba! Ba zaka iya tirsasa mata tayi abinda ya dace ba, a k’a‘ida fa babu ita a hurumin zab’arwa kanta mijin aure, ku iyayenta ku ya kamata ku zab’ar mata. Allah na tuba yaushe ma Maryam d’in ta NuNa ne wai? Da har ta san wani soyayya?. Daman ni tunda naga sauyi a tattare da ita d’azun na san da wata a k’asa!. Son da kake yi mata ya sanya baka son ganin b’acin ranta kwata kwata, to inaso ka sani wannan Maryam d’in da kake shagwab’awa ko bayan raina zaka ce na fad’a maka ‘Wallahi sai ta kunyataka!!’ Ai shi Yaro ba a yi masa haka kwata kwata. Taya ma za ayi ka bari ta auri wanda suka gama lalacewa a waje? Allah na tuba Yaro ka auresa da mutuncinka ma ya aka k’are ballantana wanda ya sanka tun a waje?? Ai ni wallahi na ma ga k’ok’arin wannan Yaro Usman da ya amince zai aureta, ga mahaifiyarshi itama y’ar albarka bata k’i jininka ba!! Ana k’ok’arin a rufa maka asiri, kana son tonawa kanka asiri da hannunka. Ba Baki zan yiwa Maryam ba amman duk daren dad’ewa indai wanchan Yaron zata aura to kuwa auren ba zai d’aure ba! Sai ta dawo gida kuma sai kun yi dana sani!!!”. Madu kasa jurewa yayi dan haka yace “Inna na rok’e ki da girman Allah kiyi shiru!! A matsayinki na Babba ba a so ki dinga mugun alkaba’i haka!! Kawai ki bita da fatan alkhairi…” A hasale Innar tace “Ank’i a bita da fatan alkhairin!!! Ai sai mutum yaso alkhairi tukunna za a bishi da alkhairi! Masifa kuke son janyowa kanku kai da ita k’iri k’iri!!! Yaron nan ko bincike na tabbata ba kuyi ba….Kai nan kaga mai arzik’i ko? Shine zaka fake da wani wai ‘Yayansa ya taimaki Usman’, ai taimako daban neman aure daban. Wannan karon Baba Bashir ne yace “Inna tunda suka zo suka tafi muke bincike akan shi, kuma bamu samu wani mugun abu a kanshi ba kowa alkhairi yake fad’a.” Cikin fad’a sosai Innar ta katseshi ta hanyar cewa “Amman tabbas yau na tabbatar Yaran nan baku da hankali wallahi!!! Binciken wuni d’aya shine Bincike????” Madu ne yace “ai ba a son tsananta bincike ko a addini!” Ga mamakin su kawai sai sukaga Inna ta fashe da kuka a cewarta wai ‘Madu da Bashir sun rainata! taya za a yi tana fad’a suna mayar mata saikace sun samu sa’ar su!?. Nan ta hargitse musu harda cewa “Sister’s din Shuwa su shirya a daren nan zasu wuce Maiduguri ba zata sake kwana a gidan Madu ba!! Dan yaga ba itace ta haifeshiba shiyasa zai yi mata rashin kunya a gaban Yara, kuma sai ta kira Babansu, zata gaya mishi duk halin da ake ciki, wallahi indai tanada rai ba zata bari Maryam ta auri wanchan Yaron da suka gama lalacewa ba, shagwab’ar ai tayi yawa!! Taya Yarinya tayi laifi kuma still lallab’ata akeyi sai abunda takeso tukunna shi za ayi mata??. Madu ne yau har da yi mata rashin kunya duk akan y’arsa???” Da kyar su Shuwa suka d’an lallab’ata ta sassauta kukan, sannan ta hak’ura da tafiya amman tace ‘tabbas maganar auren Maryam da Abba babu ita indai tana raye! Dan sai ta hukunta Maryam akan laifin ta, da fari taso ta kyaleta amman yanzu ubanta ya janyo mata.” Hayaniyar su ta sanya har su Maryam d’ib da ke a d’aki suka d’an firfito. Tarin da Ya Usman ya hau yi ne ya karkato da hankalinsu gareshi, gaba d’aya suka nufe shi….kafin su k’arasa har ya zub’e ya fad’i a wajen sumamme…. Nan kuwa Baaba Talatu ta fashe da kuka, tashi d’aya ta rikice! Hankalin kowa a tashe aka fara k’ok’arin kinkimarshi..ganin baya motsi ko kad’an kamar gawa, ya sanya Baba Talatu ta juyo a zafafe tayi kan Maryam wadda take k’ok’arin k’arasowa wajen, tana matsowa kawai ta d’auketa da mari!! Ta fara magana cikin kuka “Maryam mai nayi miki a rayuwar nan in banda alkhairi da kike shirin yi mini gib’i a rayuwa?? Tun tasowarki banda soyayya muraran babu abinda nake nuna miki har iyau, mai Usman yayi miki a rayuwa haka? Muguwa kawai!! Wallahi idan wani abun ya samu d’ana ba zan tab’a yafe miki ba!!.” Madu ne ya katsesu ta hanyar cewa su d’an matsa su bawa Usman d’in iska sannan ya umarci Ya Jamilu da ’ya d’auko mishi makullin motar shi a d’aki’. Da Baba Bashir da Madu ne suka d’auki Ya Usman, suka yi waje dashi, Ya Jamilu kuma ya fito da mukulli ya bi bayan su da gudu, ganin haka yasa suma su Shuwa suka bi bayansu…. Da kyar aka lallab’a Baaba Talatu ta hak’ura bata bisu ba. Tunda suka koma cikin gidan kuwa Baaba Talatu take kuka, su Innaa da Shuwa kuwa in banda tsigale Maryam ba abinda suke yi…Shuwa ta tabbatar mata ta sake tabbatar mata cewa ‘muddin ta auri Abba to sai dai ta nemi wata uwar amma ba ita ba!!!’ A daren Innaa ta kira Baban su Shuwa a landline d’in gidan ta sanar masa komai! Yayinda shi kuma ya tabbatar mata da ‘in shaa Allah, gobe da sassafe idan Allah ya kaimu zai taho.’ Sai bayan awa hud’u, tukunna Madu da Baba Bashir suka dawo daga asibiti.. Nan suke gaya musu cewa “an kwantar da Ya Usman, Ya Jamilu yana tare da shi and the bad news is ‘ya samu stroke!!’ A sakamokon jinin shi da yayi mugun hawa.” Kukan da Baaba Talatu take yi sai ta baka tausayi, haka itama Shuwa. Gaba d’aya duk sai Maryam taji ba dad’i.. Gidan ranar babu wanda ya runtsa, da sassafe suka yi shirin zuwa dubo Usman har Maryam amman k’iri k’iri da Shuwa da Baaba Talatu suka hanata bin su… Bayan sun tafi da awa d’aya tana zaune gidan shiru duk ba dad’i ga damuwa tashin hankali da tunani, daga ita sai y’an tsoffin da su Innaa suka taho dasu. Sallama aketa kwad’awa a waje, hakan yasa ta sanya hijabi ta fita. Wani Yaro ta gani a tsaye bayan ta bud’e k’ofar gate d’in, Yaron ya kalleta sannan yace “Wai Maryam taje inji Abba.” Sai da gabanta ya yanke ya fad’i…abun ya bata mamaki ‘Abba da sassafen nan?, to Allah dai yasa lafiya.’ Ko cikin gida bata komaba, ta k’arasa gaban motar inda ta hango shi a tsaye cikin shigar shadda tazarce fara k’al tayi masa mugun kyau!!. Cikin kulawa ya amsa bayan ta gaidashi, sannan a hankali yace “Baki da lafiya ne? Naga idanuwanki duk sun kumbura.” Kwallar da ta zubo mata ta sa hannu ta share sannan ta shiga koro mishi abubuwan da suka faru tun daga jiya har izuwa yanzu bata b’oye masa komai ba. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e sannan yace “Maryam kin yarda dani?.” A hankali ta d’aga mishi kai alamar ‘eh’ Cike da bata umarni yace “Inaso yanzu! Ki shiga cikin gida, duk wani abunda zaki buk’ata ki d’ebo ki zo dasu, zamu d’anyi tafiya ne, maybe sai nan da shekara d’aya ko d’aya da rabi tukunna zamu dawo.” Cikin rashin fahimta da d’an tsoron daya bayyana akan fuskarta tace “Tafiya kuma? Zuwa Ina? Kai da wa?.” Ba tare da b’ata lokaci ba, yace “Ni da ke! K’asar nan zamu bari bayan an d’aura mana aure yau! In sha Allah.” Da sauri ta shiga ja da baya tana girgiza kai kafin tace “Kana nufin fa mu gudu kenan!! Abba mai yayi zafi har haka??” Da sauri ranshi a b’ace yace “Maryam komai ma yayi zafi!! Babu abunda bai yi zafi ba.! Kinga idan na saka k’afa na bar k’ofar gidan nan naku a yau batare da kin bini ba, to ki tabbata ba zaki sake ganina ba har abada!! Ta b’angaren ki ta b’angarena ko ina yayi zafi!! Ya kamata mu tashi mu tsayawa kanmu, saboda iyayenmu basu damu da farin cikinmu ba.” D’an sassauta murya yayi sannan yace “Jiya bayan mun bar gidan nan, direct wajen mahaifina mukaje. Bayan Yaya ya gama yi mishi bayani, Ina tunanin goyon bayanshi amman sai naji yace ‘Shi bai hanani in aureki ba, amman tabbas sai na fara auran cousin sister d’ina wadda ya zab’a mini tukunna bayan shekara biyar sai in aureki!’. Maryam ko a duniyar matattu muke na tabbatar idan na barki nan da kwana biyar ma to kina gidan Usman. Mahaifiyata itama ta goyawa Mahaifina baya d’ari bisa d’ari! Yaya shi kuma wanda nake tunanin zamuzo ni da shi a d’aura mana auren dashi a yau, shima ya juya mini baya. Dan Mahaifinmu d’aki ya kirashi suka shige, bayan ya fito dana yi mishi magana yace mini ‘kawai in hak’ura!!!’. Maryam, ya kikeso inyi?? still ba zaki yarda ki bini ba?.” Cikin kuka Maryam tace “Tunda nake a rayuwata ban tab’a ganin Hajiya da Abba suna fad’a ba sai da zancen mu ya fara! Bana son zama silar lalacewar zaman lafiyar su. Abba kawai muyi abinda suke so, watarana za muga alkahiri.” Wannan karon hawayene suka zubo daga idanun Abba “A hankali yace “Maryama, ko da ace mun auri waenda iyayen namu suka zab’a mana abun bazai yi kyau ba!! Domin kuwa za muyi ta cusgunawa Abokanan zaman namu ne muna d’ibarwa kawunanmu zunubai a wajen Allah, kuma case an dinga yin shi kenan watak’il ma k’arshe a lalata zumuncin gaba d’aya! Ga uban zunubin da za muyi ta d’iba a wajen mahaliccinmu, especially ma ke da kike a matsayin mace dan na tabbatar ba zaki iya yiwa Usman cikkkiyar biyayya ba sannan inaso ki rantse mini yanzu akan ‘shin bayan kin auresa ba zaki dinga tunaninaba?!”. Da sauri ta runtse idanunta. Bai jira jin me zata ce ba ya cigaba “to ki sani duk wani tunanin ko wish ko feeling da kika samu a kaina kina da zunubi!. Ni kuma na tabbatar Idan na auri Zainab (cousin sister d’insa) to tabbas ba za muyi sati ba zan saketa, idan kuma aka tilastamin zama da ita na tabbatar tsakanina da mahaifina sai dai kallo daga nesa, domin kuwa na dinga bak’anta mata kenan shi kuma ba zamu shirya da shi ba muddin zan yi hakan and na tabbatar ba zan tab’a iya zaman aure da ita ba!. Me kenan aka yi a nan Maryam?? Mun lalata rayuwarmu fa kenan mun lalata ta Abokanan zaman mu. A yanzu inaso ki rufe idanunki, karki duba kowa a duniyar nan, karma kiyi tunanin akwai wata halitta bayan mu biyu kacal a duniya! I want you to be selfish Maryam just for today for my sake! Mu so kanmu fiye da kowa mu sanya kanmu a farin ciki, na tabbatar miki, bayan an d’aura mana aure zamu dawo mu basu hak’uri, komai zai dawo dai dai in sha Allah, koma waye yake fushi damu daga baya za kiga ya daina, an dawo an zauna lafiya da kowa. Please Maryama, pleaseeee. SHARE PLS. BULAMA ✍️ So Da Buri Free Book 16 Cikin sheshshek’ar kuka Maryam tace “Hajiya fa fushi takeyi dani, yanzu idan na gudu zata kuma jin haushi na.” Hannu biyu Abba ya d’aura a kansa, kafin yace “O my God!!Maryam da wanne yare kikeso in yi miki bayani ne?? Ko bayan auren ki da Usman zata ci gaba da jin haushin ki ne….in dai kika auri Usman to kun yi ta janyo fad’a kenan a tsakanin iyayenku har azo a lalata zumuncin…” A hankali ya matso kusa da ita yace “Nace miki kar ki duba kowa yanzu, just ki duba mu biyu kawai, and trust me! Please Maryam, this is the right thing to do….” Cikin share hawaye tace “Abbana fa?” “Abban ki ya riga ya zab’a miki ni, so Abbanki ba zai ji haushin komai ba, this is his choice Maryama. Itama Hajiyan blackmailing d’inta aka yi, sannan kunyan Baaba Talatu take ji shiyasa amman da zarar mun yi aure idan taga kina cikin farin ciki tuni zata manta da komai! Burin ko wacce uwa taga farin cikin Y’arta Maryam i assure you Usman cannot give you the happiness you deserve!.” Ya k’arashe maganar kamar zai fashe da kuka.. Shiruu, tayi tana tunani.. Tabbas duk abinda Abba ya fad’a haka ne sannan ta yarda dashi d’ari bisa d’ari! Cikin katse mata tunani a hankali taji yace “muje..idan komai ya d’an lafa na yi miki alk’awari zamu dawo mu bawa su Hajiya hak’uri, na san zata hak’ura in sha Allah. Abba kuwa na san shikam farin ciki ma zaiy yi, dan munyi abunda ake k’ok’arin hanasa, wanda hakan shine zab’in shi. Na tabbatar idan mijin Innarku ya zo ba zai bari a d’aura aurenmu ba, kuma Inna da kanta kinji tace ba zata tab’a bari muyi aureba wanda na tabbatar Abba ba zai tab’a iya shallake umarnin su ba.” Cike da gamsuwa da maganganunsa Maryam ta hau d’aga kai alamar amincewa kafin tace “Amman zamu dawo anjima mu gansu, ko iya Abba ne shi kad’ai, na san ya san yadda zaiyi ya lallab’a Hajiya Shuwa watak’l ta hak’ura, kayi mini wannan alk’awarin?”. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Nayi miki! Amman nima kiyi mini alk’awari idan mun gama ganinsu, anjiman zamu wuce, saboda ina so in yin nesa da mahaifina ko da na wata d’aya ne. Ba zan iya fuskantarshi a yanzu ba, dan ban san hukuncin da zai yanke mini ba.” Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace “Na yarda!.” Ahankali yace “Alhamdulillah”sannan ya juya ya bud’e mata gaban mota. Har ta wuce ta shiga, ta zauna sai kuma ta juyo ta kalleshi yana shirin rufe mata k’ofar tace “Abba, kana ganin ba matsala?” Murmushi yayi sannan yace “Yes Maryam, in shaa Allah, just trust me please..” “Na yi, amma dan Allah kar ka sa in yi dana sani” Murmushi yayi yace “i promise, I won’t!”. Sai da ya juyo ya

Chapter 12 of 32