Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sukaji dan lokaci d’aya suka rikice! Kan kujera d’ayan ya hau ya dan daddaki p.o.p d’in wajen kamar yana knocking Daga nan yasa hannu ya d’an fara jaaaa! Kamar akwai mai taimaka mishi a take suka janye ya d’aura a kan kujera. Ladder, d’in da aka zuro mishi ne yasa muka gane akai wani a saman a cikin ceiling d’in. Sai da d’ayan ya cire wallet da wayar Junaidu ya yar a tsakar falon da bindigar da aka kashe CJ d’in da ita sannan ya ciccib’eshi ya fara haurawa da shi saman.. Yana gama hawa ragowar ma suka ciccib’i maka makan akwatunan da suke a parlourn da alama kud’ad’e ne a ciki suka bi bayanshi suka haye. Last one d’in ne ya d’auko dakin pop d’in da suka cire suka taimaka mishi suka jaa wajen suka rufe tsaff yadda duk k’urillar mutum bai isa ya gane wajen a fashe yake ba....” Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan yace “Ba yadda bamu yi da shi akan ya barmu mu tafi da Junaidu ba amman yace mana “kasancewar wanda aka kashe babban mutum ne! Wallahi an basu kwakkwarar doka akan kar a sakeshi har sai an gama case d’in! Kuma kafin ma a samu ayi settling a gama mourning rasuwar nan sai anyi wajen wata d’aya ko sama da haka. Guda biyu masu mask d’in an rasa su, dan waenda akayi fashin da su ragowar mutane ukun d’ayan tun a jiya aka ga gawar shi ba a san wa ya kashesa ba! Su kuma ragowar biyun awa biyu da suka wuce aka samesu da kyar a Bauchi An harbi d’ayan dan yayi attempting guduwa ne Shi kuma d’ayan yace ‘wallahi bai tab’a ganinsu ba bai san ya yanayin fuskarsu ta asali take ba! Dan tun a lokacin da suka zo musu da tayin aikin ma da mask a fuskokinsu….dan haka basu tab’a ganin fuskokinsu ba kuma basu damu da su gani d’in ba saboda su ta kud’in kawai suke kuma sunyi musu alk’awarin in dai aka yi fashin duk kud’in da aka samu nasu ne dan su ba zasu tab’a ko sisi a ciki ba, basa buk’ata......” Kuka Baba ya saka kafin yace “Yanzu kenan Junaidu a wannan waje zai yi ta zama kenan har sai an yankewa waenchan hukuncinshi?? Har zuwa yaushe kenan?” Ummu ce ta share hawayenta kafin tace “Wallahi Baba muma bamu sani ba. Kawai dai mu ci gaba da addu’a, dan na tabbatar addu armu ce da taimakon Ubangiji ya sa aka ga wannan b’oyayyiyar camerar! Kuma mutumin yayi min alk’awarin ba zai bari a bashi horo ba ko ta yaya. Dan a office d’in wani Abokin Ya Jamilu ma suka nuna mana suka ce zai ci gaba da zama. Sannan Ya Jamilu har yanzu yana chan yana dubawa in an samu rara anytime from now zasu iya tahowa, in kuma sun k’i yarda to sai dai mu yi hak’uri mutu ta addua. Dan mutumin yace zuwa gobe za‘a rufe ganin su sai ranar da za a fara zuwa kotu! So in dai Ya Jamilu bai dace a yau ba, sai dai mu jira ranar. Amman mutumin yayi mana alk’awari ya sake yi mana alkawari a kan ba zai bari a cutar da shi ko ya wahala ba..........” Sun yi zaman jira kam har washegari, da safe ganin Ya Jamilu ya dawo shi kad’ai yasa duk jikinsu yayi sanyi. Haka nan su Ummu suna ji suna gani washegari suka shirya suka tafi suka bar Junaidu a Lagos tare da addu’o’i bila adadin.. Dan da safe ma su Baba basu sare ba sai da suka koma sai dai ba yadda ba suyi ba amma aka hana su ganinshi.......... Haka nan suka dawo jiki duk a mace. Umma tayi kuka tayi kuka kamar ranta zai fita. Itama Jalila kamar mara lafiya. Duk gidan ma sai ya koma kamar na marasa lafiya in ka shigo sai ka d’auka rasuwa aka yi! Tun ba ma da su Kaka suka dawo suka sanar musu halin da ake ciki ba, sai kawai suka d’au kuka dukkansu, sai da Madu da Kaka suka tsawatar musu, sannan, suka ce “ai kamata ma yayi suyi murna, tunda an gano bashi da laifin komai, kawai dai d’an zama ne zai yi a wajen kafin a gama yanke hukunci daganan ya dawo gida in sha Allah.” Tukunna fa aka samu gidan ya d’an nutsu. ............. Nasarawa gra. Saturday. MT estate. A gajiye Auwal ya dawo yau dan aiki yayi mishi yawa! Kwana biyun nan. Saboda Granpa ya had’a mishi har da aikin Arshaad yace “ya dinga yi”, shi kuma son gwaninta baya so aga kasawar shi shiyasa yake aiki tuk’uru! Jiya ko rintsawa bai yi ba. Yana shiga ya gama parking motarsa kenan wayarsa ta hau ringing! Da farko kamar ba zai d’auka ba sai kuma ya lalumo wayar a sit d’in gefen shi inda ya jefata tun jiya da rana (idan zai tuna kenan) daga nan bai sake bi ta kanta ba! Hannunshi ya kai kan wayar yayi tsaki kafin yace “Wannan tsohon so yake yi ya kashe ni da aiki wallahi!”. Yana duba screen d’in sai yaga sunan ‘Micheal’ dan haka ya amsa yana kaiwa kunnenshi kafin yace “Talk to me Mik’e, just get straight to the point plss.” “Sir, I followed him day b4 yesterday and naga yaje wani unguwa, ban san sunan unguwar ba but zan gane zan iya kaika! I hid myself dan kar ya ganni. Yana fitowa naga ya d’auko waya yayi kira.. After kaman 5 minutes wata fine yellow girl! Ta fito da abaya maroon colour, the way he’s talking and smiling na san itace…. Suna tsaye wani ya zo a moto ya shiga gidan da Yarinyar ta fito. Bayan Arshaad ya tafi sai nake tunanin ya za ai in san sunanta ban sani ba, kawai sai wannan saurayi da ya shiga gidan naga ya fito ya zo wajen mai pos sunata hira sosai, i wanted to go and ask (mai pos) amman inaso sai saurayin ya bar wajen dan maybe ko brother d’inta ne kar inje inyi tambaya a gabanshi yasa question mark a kaina. To dai inata jira inata jira ashe nayi bacci a moto ban saniba..sai da gari yayi duhu na farka naji ana kiran sallah, me pos kuma ya tashi!.” Tsaki Auwal yayi sannan yace Ji banza, anyways your information will help meet me yanz…” Da sauri Mike ya katseshi yana dariya kafin yace “Sir, ai na koma jiya, na tambayo shiyasa ma kaga ban kiraka tun shekaran jiyan ba, i wanted to complete my job fully. Jiya da safe naje na samu mai pos d’in! Nace mishi ‘jiya nazo wucewa wata Yarinya da abaya maroon a nan gidan’ (na nuna mishi gidan) Sannan nace ‘naga ta jefar da takarda maybe bata sani ba, please meye sunanta zan aika In ce tazo ta karb’a.’ Da farko bai ganeba, dan ce mini ma yayi ‘bai ga wata Yarinya ta fito daga gidan ba jiya dan ya d’an fita!’ Sai da nace mishi ‘k’anwar wanda ya zauna suka yi ta hira jiya da ya fito daga gidan shima’. Tukunnan! Da farko cewa yayi In kawo takardan zai bata ni kuma na k’i yarda… Haka nan k’arshe dai ya hak’ura yace min sunanta ‘JALILA!’. Ina barin wajennasa na nufi k’ofar gidan, nayi kamar naje gidan, na d’an jira kad’an. Da naga baya kallona na dawo na zo na shiga moto nayi tafiyana… Shiyasa tun jiya nake ta kiranka kai kuma baka amsa waya. i wanted to tell you akwai good news bu...” Auwal wanda surutun Michael ke neman k’ara mishi ciwon kai ne yace “Ok Mike, ai ka gama fad’a min all i want to hear ya isa haka!! Meet me nan da 30 minutes sai muje ka nuna min gidan!” Har zai kashe yaji Mike d’in yana d’an murmushi k’asa k’asa yana cewa “Sir about the money fa?” Da d’an k’arfi Auwal yace “Meet me nan da 30 minute!!!” Sannan ya kashe wayar. Da kyar yake tafiya dan sai yanzu baccin da bai yi jiya ba ya fara d’ibarsa! Yana isa side d’inshi kuwa wanka kawai yayi ya fad’a gado, a take yaji wani bacci mai mugun dad’i yana fisgar shi, gudun kar a katse mishi baccin shi yasa ya kwaso gaba d’aya wayoyinshi ya saka su a silent. Bai tashi ba sai pass 9! Da mik’a ya farka sannan ya wuce toilet…. Sai da ya d’an yi freshening up yayi alwala tukunna ya fito ya jero sallolin shi!. Yana idar wa ya hango d’aya daga cikin wayoyinshi tana haske. Tsaki yayi sannan ya nufi gadon yana zuwa yaga sunan ‘Granpa’ b’aro b’aro a kan screen d’in! Kafin ya d’auka har ta tsinke Da sauri ya d’auka wayar ya bud’e ga mamakinshi yaga wajen 30 misscalls! Tsaki yayi ganin wajen 20 duk na Mike ne. K’ok’arin dialing number Granpa yayi amman sai nashi kiran ya shigo! Hakan yasa ya d’auka bai kara a kunne ba ya saka ta a speaker. “Meet me, right now!” Kawai Granpa yace mishi sannan ya kashe wayar. Tsaki ya sake yi a karo na ba adadi sannan yace “D’an masu da bada order!” Yana ta k’unci haka nan ya shirya cikin pyjamas sky blue da d’an ratsin black, yayi mai kyau kuwa sosai. Wayarshi guda d’aya ya d’auka ya sanya a aljihu ya bar ragowan ya fito ya nufi side d’in Granpa. A compound d’inshi ya sameshi, a wani had’add’en garden haske ta koina tarr!!kamar rana. Daidaita kanshi yayi sannan ya d’an saki fuska kafin ya k’arasa wajenshi. Ko gaisuwarshi kuwa Granpa bai amsa ba ya rufeshi da fad’a! Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, sannan daga k’arshe yace “idan ba zai iya bane ya bar mishi company d’inshi ai daman ragowar ma ba shine yake kula mishi da su ba! Wannan d’in dama dan yaga a tsakaninsu (jikokinsa ) yake son bawa mutum d’aya shiyasa yake d’orasu a kai saboda yana so yaga ko zasu iya, but tunda yaga kamar ba lalle su iya d’inba! Kawai zai chanja shawara ya bawa Yahaya ko Yusuf dan ba zai yiu ya d’auki something that is so dear to him ya bayar a wrong hand ba! Company d’in is very dear to him ne it’s like something da suka yi shi da brother d’inshi. Bayaso Company d’in ya samu matsala ta koina shiyasa yake son bawa individual dan sai anfi kula da shi ta hakan, sab’anin idan mutum ya san ba nashi bane shi kad’ai, to ba lalle ya zage damtse kamar yadda zai yi idan nashi ne shi kad’ai ba. Yana buk’atar jajirtacce tsakanin shi(Auwal), Aslam ko Arshaad! Yana ganin su Dad yanzu girma ya fara zuwa musu, besides kuma duk akwai companies d’in da ta mallaka musu each, ba lalle su iya ba. To kuma gashi su d’in (jikokinsa) da ya kwallafa rai gashi suna k’ok’arin bashi kunya! Meye amfanin su? wish d’inshi na passing company d’in to an individual from generation to generation ya tashi a aiki kenan? Gaba d’ayan su basu da amfani daga shi har Arshaad, har gara ma Aslam wanda dukda tarin aikin da yayi mishi yawa hakan bai sa ya nuna gazawa ba a b’angaren kula da branch na company d’in nasu da yake a chan! Aiki yake yi tuk’uru bil hakk’i da gaskiya! Su kuwa a nan daga b’arawo sai mai son jiki.” Sai da Granpa yayi mishi tatas!! tukunna ya tashi ya barshi a wajen ko kallonshi bai kuma yi ba, ballantana ya tsaya sauraron hak’urin da yake ta faman bashi. Auwal ji yayi kamar ya shak’e kanshi da kanshi tsabar takaici! He tried so much for all this amman sai da abu ya kusan zuwa gangara zai fara nuna gajiyawa a time d’in da ya kamata ya zage damtse?! Tabbas maganar Babansa (Daddy) da yake cewa “babban companyn Granpa… Ya tab’a cewa kyautar shi zai yi a mutum d’aya tak! To amman ba lalle a tsakanin su brothers su uku zai bawa ba, tunda company d’in flour n su a hannunshi( Yusuf) yake, na textiles kuma Dad (Yahaya) ne akai a chan Abuja shiyasa ma bai cika zama ba, na oils kuma Abba (Ya’akub) ne dudda yanzu an cireshi an sake bawa Daddy( Yusuf) d’in shiyasa ma aiki yayi mishi yawa. To wannan babban na MAI TURARE and Co. wanda har a Uk suna da branch tabbas kyautar shi zai yi amman a tsakanin jikokin su uku, duk mai rabo.” Gaskiya ce kenan? A hankali Auwal ya sauk’e ajiyar zuciya, yace “Daa chan, da na d’auki maganar under probability ma nayi k’arfi da k’arfe wajen ganin na mallaki company d’in, ballantana yanzu da naji daga bakin oga kwata kwata ai sai inda k’arfi na ya k’are!.” Juyawa yayi ya kalli hanyar da Granpa ya bi ya wuce.. Murmushi yayi kafin yace “Old man, you may be older but I’m smarter.. Lokacin da zaka sauk’o daga fushin nan ma, baka sani ba.” Yana gana fad’in haka ya juya ya wuce tare da plans barkatai a ranshi. Ko da yaje kwanciya ma sai da ya gama shirya yadda zai wanke kanshi a wajen Granpa ta hanyar yin aiki tuk’uru ba tare da an saka shi ba ma! Dan ya samu ya dawo da martabar shi a idon Granpa, sai wajen 12:30 bayan ya zab’i dandatsetsiyar shaddar da zai saka gobe idan zai je wajen Jalila, tukunna na ya kwanta........ 1:00am a airport tayiwa Arshaad, duk da kuwa sun yi waya ba da jimawa ba yace mishi “sun samu delay gashi akwai transit so sai 2:30 flight din zai yi landing a Kano!.” Amman tun 12 ya shirya da kyar ya bari 1:00 d’in ma tayi, ya fita. Kamar yadda Aslam ya fad’a masa ‘2:30 am’ d’in tana yi, Arshaad d’in ya isa wajen arrivals ya tsaya. Har ya d’an fara gajiya dan ya fi 20 minutes a tsaye kuma sai kiran shi yake yi baya d’auka! D’ago wayar shi yayi a karo na ba adadi da niyyar sake kiran nashi sai kuma ya sauk’e wayar yana kallon setin shi ya hau murmushi…. Sanye yake cikin normal sleeve golden color ta ciki, ta waje kuma ya d’aura slim fit suit a kai white colour, takalminshi da wandonshi suma duk white sai agogon hannunsa ne shi kuma ya kasance gold jaguar special edition!. Dogo ne, dan ya fi Arshaad tsayi.. Sannan kyakkyawane ajin farko! Hasken fatarshi bai kai na Arshaad ba, amman dai shima ba bak’i bane ba. Yana da doguwar fuska wadda take zagaye da lallausan saje da gashin baki, baki wuluk! Yana da madaidaitan idanuwa masu oval shape da straight cikakkiyar gira, hancinshi dogo ne sosai kamar yadda yanayin fuskar tashi take.. Sai d’an mitsitsin bakinshi wanda ya k’arawa fuskar tashi tsari da ainahin kyau mai aji!. Tafe yake yana jan d’an matsakaicin trolley d’inshi yana amsa waya. Magana yake yi amman kamar baya so yayi…da alama ma bai lura da Arshaad d’inba K’arasawa yayi towards inda yake dede lokacin yana hanging up call d’in. Ji yayi anyi hugging d’inshi kawai, wanda ko bai ga waye ba ya san Arshaad ne “Welcome back bro” yace mishi kafin ya cika shi yana murmushi yace “I miss u, a lot.” Kallonshi Aslam yayi, a hankali yace “mee too”. Trolley d’in tasa Arshaad ya karb’a suka k’arasa mota Arshaad d’in yana tambayarshi “ya uk?”. “Alhamdulillah” kawai Aslam d’in ya iya cewa. A haka suka k’arasa motar suka shiga suka zauna Arshaad ne ke ta magana Aslam kuma daga ‘ummm’ sai ‘um um’ k’arshema ajiyar zuciya ya sauk’e daga haka ya d’an jingina kanshi ya runtse idanuwanshi… Ganin haka yasa Arshaad d’in yin shiru shima bai sake cewa komai ba har suka iso. Gidansu Aslam suka nufa direct! Arshaad ya d’anyi horn kad’an. Mai gadi ne ya d’an lek’o ganin motar yasa shi saurin bud’ewa ba tare da tmbayar dalilin zuwanshi da mota cikin dare ba. A hankali ya k’arasa da motar kamar baya so yayi parking d’inta a parking space kafin yad’an kalleshi, in a calm voice yace “Mun iso.” “Tnx” Kawai Aslam yace bayan ya d’ago ya bud’e idanuwan nashi sannan ya fara k’ok’arin bud’e motar… A hankali Arshaad yace “Are you sure a nan zaka sauk’a?! Ka zo kawai muje chan mana, a side d’ina akwai rooms sai ka zab’i d’aya.” Juyowa Aslam d’in yayi ya kalleshi sannan yace “I’m good, open the door pls it’s late.” “Well, you don’t seems good!! Ina lura da mood d’inka tun d’azu ai, you look disturbed and scared! Ka zo muje gobe sai a san abun yi!” Arshaad d’in ya fad’a cikin d’an tsare gida. Komawa kawai ya ga Aslam d’in yayi ya kwantar da kanshi a jikin seat d’in sannan ya mayar da idanuwansa ya lumshe. Ganin haka kawai yasa Arshaad ya bud’e mishi lock d’in, dan ya san tunda Aslam d’in yayi haka to idan zasu dauwwama a nan shi fa ya gama magana kenan!. Yana bud’e mishi kuwa ya sa k’afa ya fice… fitowa Arshaad d’in yayi shima ya zagaya ya d’auko mishi trolley d’inshi. Har bakin main door na parlour d’in ya rakoshi tukunna yace “Zan juya daga nan” Hannu kawai ya saka ya karb’i trolley d’in sannan yace , “Thankyou Arshaad.” Har Arshaad ya juya zai tafi sai kuma ya juyo yace “You sure about this??” “Yeah” kawai Aslam yace mishi sannan ya k’arasa ya danna door bell. Ya jima a wajen sosai tukunna wata y’ar dattijuwa mara jiki sosai tazo ta bud’e k’ofar. Tana ganin shi tace “ai kuwa kai d’inne, tun d’azu nake ta lek’owa ta ramin nan inaso in tabbatar! D’an albarka….” Sai kuma kawai ta fad’a jikin shi ta fashe da kuka. Murmushi yayi sannan ya d’an yi tapping bayan ta alamun rarrashi kafin yace “Kin tare ni a k’ofa ko dai in koma ne? Daman Arshaad sai tallar ‘inje In kwana a gidansu’ yake ta yi min.” Da sauri ta cika shi tana d’an murmushi, sannan ta bashi hanya ya wuce…. “Home sweet home” shine abinda ya furta kafin a hankali ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya, sannan ya d’an lumshe idanuwanshi da suka fara chanja launi a hankali ya bud’e su. Murmushi ‘Gwaggo Asabe’ tayi tana k’ara girmama k’ok’ari da k’arfin hali irin na Aslam! Sarai take hango abubuwa barkatai a idanunshi amman shi k’ok’ari ma yake ya b’oye har da janta da wasa duk dan kar ta gane kuma ta damu. “Dad, yana Abuja ko?” Taji muryar shi. “Eh” tace, sannan tace zauna in kawo maka wani abun ka d’an sakawa cikin naka, ko?”. Har tayi hanyar kitchen yayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa “No, I’m full fa. Naci abinci sosai a jirgi, sai dai gobe da safe pls ayi min d’an wake, i miss it.” Murmushi tayi bayan ta juyo sannan tace “Tam shikenan Aslam, sannu ko” Har yayi hanyar side d’inshi dake a nan k’asan, sai kuma ya juyo yace “Ta fara baccin dare kenan! Na ji shiru” Ajiyar zuciya Gwaggo Asabe ta sauk’e kafin tace “Bata dad’e da yi ba, dan ko minti ashirin bana jin anyi, shiyasa ma ka tarar dani idanuna biyu. Amman dai gaskiya yau kusan shekara biyar ai na fada maka tun a waya, wannan koke koken duk babu, har takan zauna ayi hira da ita fa wasu lokutan, matsalar sai an sauk’k’o k’asa! Tana yin ido biyu da b’angaren ka zata fara!”. Da sauri Aslam yace “Bara inje in yi wanka.” Bai jira jin me zata ce ba ya tura sliding glass door d’in side d’in nashi ya shige sannan ya mayar ya rufe…… Bayan yayi wanka ya sha tea. Kwata kwata sai ya kasa bacci, hakan yaasa kawai ya mik’e ya fito daga side d’in nashi, parlourn ba kowa hakan na nufin Gwaggo Asabe har tayi bacci kenan dan duk bulbs d’in ma an kashe su. K’arasawa yayi Inda staircase na hannun dama yake sannan ya kama ya fara hawa… A hankali yake kallon parlourn yana nan yadda ya sanshi! Da sauri ya runtse idonuwanshi ya tsaya cak! Sakamokon wasu memories da suka fara flashin….. Sai da yayi y’an addu’o’i sannan nutsawarshi ta dawo, ya samu ya ci gaba da tafiya. A hankali ya k’arasa inda bedroom d’inta yake! Sai da ya sauk’e tagwayen ajjiyar zuciya kafin yasa hannu a kan handle d’in ya d’an murd’a a ransa yana adduar ‘Allah yasa a bud’e ne’ Aikuwa yana murd’awa k’ofar ta bud’u!. Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan ya kutsa kai ya shige d’akin tare da mayar da k’ofar ya rufeta.... BULAMA ✍️. So da Buri Free Book 30 D’akin da d’an duhu amman ba chan sosai ba sakamokon side lamps d’in da suke a kunne wanda hakan ya bashi daman hango ta kwance a kan gadon. A hankali ya k’arasa ya zauna a gefen gadon. A kwance take, rigingine.. pillows wajen uku aka d’aura kanta a kai hannayenta duka biyu tayi folding d’insu a kan cikinta! Kalar fata ta iri d’ayane da ta Aslam, sai dai shi ya d’an fi ta haske kad’an. Babu d’ankwali a kanta, wanda hakan ya bawa gashin kanta damar baiyyana wanda yake nan rabinsa bak’i rabi furfura! Mai santsi da shek’i had’e da tsaho sosai. Shekarunta ba zasu wuce hamsin ba…kallo d’aya tak! Zakayi mata ka gano kyakkyawa ce ajin farko. Yanayin hancinta ne Aslam d’in ya d’auko sai dai nata har ya d’an so yafi nashi tsayi da tsaruwa amma saboda yanayin na Yarinta yasa za’a iya cewa ya fita kyau..... Hannunshi ya saka ya kamo nata sannan ya d’aura d’ayan hannun nasa a kai ya dunk’ule a hankali ya saka guiwowin hannayenshi a kan gadon for sopport kafin ya d’aura fuskarshi a kan hannayen nasu ! Tunani ya fara ‘rabonshi da ita yau shekaru bakwai! Kenan.... ........Tun lokacin da psychiatric Doctor d’inta yace musu “the last option d’in da suke dashi shine a kulle su a d’aki d’aya, daga ita sai shi sannan a d’aure hannayenta da k’afafuwanta gudun kar ta cutar da shi ko ita kanta. Hatta abinci ana so ya zamana shi ne zai dinga bata a baki, yayi mata alwala yayi mata komai for 24 hours! May be daga hakan tayi snapping out, ta dawo cikin hankalinta.” Tun a 12 hours Aslam ya ga ba zai iya ba domin kuwa tak’i chin abinci kuma daga ya matso kusa da ita sai ihu! K’arshe ma suma ta fara yi… Gaba d’aya duk ta firgice. Ganin haka yasa ya d’auki waya ya kira Dad wanda shima d’in jin da yayi tanata suma yasa yace “bara ya zo ya gani.” Sannan ya kira Doctor, shima Doctor d’in yace gashi nan zuwa. Dad d’in yana zuwa yayi knocking k’ofa Aslam ya bud’e, basu ankara ba kafin ya shigo ta taho da gudu ta hankad’o Aslam d’in waje ashe ta kunce hannayenta ba tare da ta bari ya lura ba! A take ta saka key… Ba suyi wata wata ba Aslam ya fara k’ok’arin b’alla k’ofar Dad kuma ya tafi ya d’auko spare key!…Amman ko da ya zo ya saka k’ofar k’in bud’uwa tayi sakamokon barin key d’in da tayi a jiki ta ciki.. Suna cikin kiciniyar bud’ewa suka ji k’arar fad’uwar abu kamar kujera, a rikice Aslam yayi kan 3 seater d’in da take a parlourn ya cewa Dad “ya zo ya kama mishi”. Haka suka kinkimi kujerar da kyar, suka yi kan k’ofar da gudu da k’arfi suka buga! Allah ya taimake su kuwa ta bud’u…. Aslam kasa motsi yayi sakamokon ganin k’afafuwanta a sama suna lilo kanta kuma tayi hanging a jikin chandelier d’in d’akin, sai dai k’afafuwan nata still suna d’an motsi!!. Dad ne yayi k’arfin halin shiga da gudu ya d’auki kujerar data taka ta sak’ale kan nata ta yar! Ya saita mata ya d’aura kafafun nata a kai sannan ya hau ya kunto ta, sai dai zuwa wannan lokacin bata motsi!. Shi dai Aslam duhu kawai ya fara gani daga nan bai sake sanin inda kanshi yake ba. Sai da ya farfad’o tukunna ya fahimci ashe suma yayi… Yana farfad’owa Dad da Arshaad suka yo kanshi suna tambayar shi jiki… Cikin tsananin tashin hankali , muryarshi tana rawa yace “Dad ta mutu ko? Shikenan nayi silar mutuwar mahaifiyata!!” Da sauri Dad yace mishi “Bata mutu ba Aslam, suma kawai tayi.” A tunanin Aslam kwantar mishi da hankali kawai Dad yake k’ok’arin yi, shiyasa yak’i yarda da zancenshi har sai da Dad d’in ya kaishi ya ganta ta window tana zaune Gwaggo Asabe tana bata abinci a baki hannunta kuma ana mata k’arin ruwa!. Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan yace “Alhamdulillah” Ba a dad’e bai aka yi discharging d’inshi.. Auna komawa gida ko gama dedeta parking d’in mota bai bari Dad yayi ba, ya fito cikin hanzari ya nufi cikin gidan.. A d’akinsa Dad ya sameshi…yanata kiciniyar had’a kayayyakinsa, gaba d’aya ya sauk’o da akwatina ya hargitsa d’akin da alamun komai da komai yake son tattarawa dan hatta games d’insa suka har yayi parking nasu a daban.! Da sauri

Chapter 25 of 32