Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta tsinci kanta da kasa bashi amsa…ta ga yawan maganarsa turanci ne, kar taje ta bashi amsa da Hausa ya kasa ganewa kuma tana tsoron yin turanci dan ba wani iyawa ta yi ba, kar taje yayi mata dariya kamar yadda su Ya Jalila suke mata a duk lokacin da ta yi turanci. Ganin ta yi shiru yasa ya fara tunanin ko bata jin turancin ne domin kuwa yanayin duk’unk’unennen hijabinta da kod’add’en zanin jikinta kad’ai sun isa su fad’awa mutum ita d’in ba wata shahararriyar y’ar Boko bace ba. Dan haka ya yanke shawarar maimaita mata tambayar da Hausa. “Me ya saka ki kuka??” Da mamaki a fuskarta, ta ke kallon sa jin Hausar tasa tarr!! A ranta tace “To ko dai koya yayi??” Dan tabbas ita dai ta san wannan ba bahaushe bane ba, ko dai balarabe ko kuma d’an India , Saboda yanayin cikar gashin kansa, gashi a kwance sai kyalli yakeyi, shigen na larabawa, gashi fari sosai, dukda cewa itama bakinta pink ne amman ta san nashi ya fi nata zama pink sosai, ga hancinshi mai kyau d’an dogo, sannan idanunsa irin manyan nan kuma a kwance dogaye, kuma wani ikon Allah yanayin shape na gashin girarsu iri d’aya..ba irin cika d’innan ne da girarba, amman shape d’inta na medium arch ya fito sosai…… Shi kam Arshaad zuwa yanzu ya fara tunanin ko dai kurma ce Yarinyar nan?! To amman kuma ai d’azu har gaida shi ta yi. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya sake ce mata “Umm?” Yana mai tsare ta da idanuwa dan yaga kamar ba ta ji na farkon ba. K’asa ta yi da kanta ta fara wasa da y’an yatsun hannunta kafin tace “Ya Ja’afar ne yace in siyo mishi zob’o, na manta gidan, tun Ina Yarinya aka hanani zuwa, kuma yanzu na b’ata.“ Ta yi maganar tana share siririn hawayen da ya zubo mata da bayan hannunta. Shi kam he don’t know Y amman yanayin maganarta burgesa yake yi, komai nata a nutse take yinsa, ya dad’e bai ga mace mai magana cikin nutsuwa da kamewa ba kamar ita. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ganin ta d’ago kai ta kalleshi a karo na biyu bayan gama yi masa maganar, sai kuma ta sake yin k’asa da kanta ta cigaba da goge hawayen. Wani white handkerchief ya zaro daga cikin aljihunsa ya mik’a mata. Da farko k’in karb’a ta yi sai da yace “Ungo ki goge fuskar ki,ya b’aci da yawa da hawaye, Yara za su yi miki dariya.” Tukunna a hankali ta sanya hannu ta karb’a ta fara goge fuskarta tana lumshe idanu saboda wani fitinannan k’amshi da yake shigar mata hanci. Sai da ta goge hawayen tass sannan yace “Zo,mu je ga mota sai in kaiki Gida.” A hankali ta girgiza masa kai sannan tace “Ban san ka ba, ba zan shiga motar ka ba.” Wani d’an cute smile ya yi, kafin yace “To in tarar miki napep za ki shiga??” Da sauri ta d’aga mishi kai alamar ‘eh’. Smiling ya yi har sai da hak’oransa suka d’an baiyyana, sannan yace “To shi a ina kika sanshi? me napep d’in!” Rau rau ta yi da idanunta, har za ta yi magana sai kuma tayi shiru tana wasa da yatsun hannunta, dan bata da amsar da za ta bashi. Ganin hakan yasa yayi locking motanshi daga inda yake da key d’in, sannan ya fara tafiya yace “mu je In saka ki a napep d’in.” Da saurinta ta bi bayanshi…a hanyar yake tambayar ta sunan ta, tace masa “Huda.” Basu wani dad’e suna tafiyar ba, tun kafin su fita a kwandila suka samu napep, ta fad’a mishi inda zai kaita ta shiga. D’an sunkuyowa ya yi yana kallonta a cikin napep d’in…ji yake kamar kar su rabu amma da ya tuna ya ji sunan layin Gidan nasu yanzun har ma da d’an guntun kwatancenta da ta yiwa mai napep d’in duk ya haddace. Sai kawai yace mata “ki gaida gida da su Mama.” Daga haka ya zaro 1k a aljihunshi ya bawa mai napep d’in, kafin ya yi waving nata yana smiling suka yi gaba suka barshi a wajen. Har ya isa inda motarshi take ya shiga ya ja yai gaba, yana smiling. Ita kuwa Huda mamakin kyau da had’uwa da gayunshi take ta yi, dukda ta san su Ya Junaidu ma kyawawa ne sosai amman wannan kam ya fi su, gashi da kirki. Ahaka suka shigo layin su, ta nuna k’ofar gidansu aka ajjiyeta. K’irgo y’an chanji mai napep d’in ya yi(950), har ta d’an yi gaba ya kirata ta dawo ya mik’a mata. Sai a lokacin ta ji gabanta ya fad’i domin kuwa ta san tabbas ba za ta b’oyewa Mama abunda ya faru ba, gashi kuma har da sakota a napep har k’ofar gida, ta ina za ta fara bayani, waye shi?? ya aka yi ma ta sake da shi haka bayan jan kunnen da Mama ta sha yi mata a kan maza!? Mai ya sa duk wannan tunanin ba su zo mata ba d’azu??. Muryar mai napep d’in ce ta katse mata tunanin da take yi “Ungo mana, ko bakya so?” D’aga mishi kai ta yi a hankali tace “Ka rik’e na bar maka.” Daga haka ta juya ta nufi gida da sauri. Tana d’ago kanta gabanta ya fad’i da k’arfi sakamokon had’a ido da suka yi da Baba ya hard’e hannayenshi a k’irji ya jingina da jikin bangon gidan da tafin kafarshi kwaya d’aya da bayanshi, yana kallonta yana kallon mai napep d’in. Da sauri ya d’ago daga jinginar da ya yi ya zira silifas d’insa guda d’ayan wanda ya cire ya jingina da k’afar, ya tunkari mai napep d’in da yake shirin buga mashin d’insa ko gaisuwarta bai amsa mata ba. A hankali ta tura k’auren ta shiga…tun daga soro ta fara jiyo maganar Jalila da Umma, Umma tanata masifa Jalila na zugata, tana ida shiga tsakar gidan kuwa ta hango Mama a zaune a bakin k’ofar d’akinsu tana kuka, Ya Junaidu ya durk’usa a ta gefenta da alama hak’uri yake bata, Umma sai ce masa take yi “shanyayye!! ya tashi a wajen kafin ranshi ya b’aci!!” Jalila kuma tana cewa “ai dama ya fi son Mama a kan Umman tasu. Sallamarta ce ta sanya duk suka juyo suka zuba mata idanu. Ganin Mamanta na kuka yasa da sauri ta yi inda take ta durk’usa a gabanta ta saka hannu ta hau share mata hawaye. D’an kama hannunta Mama ta yi sannan ta goge hawayen da d’ayan hannunta kafin tace “Daga ina kike? ya aka yi kika dad’e? Jalila tace Ina fita kema kika fita.” Mama ta jero mata tambayoyin tana kafeta da idanu. Za a wani tsaya ana yi mana kukan munafurci kamar ba ki san Ina ta tafi ba!! Kawai ke dai kice baki san waye saurayin ba amman sarai kin san me ta je ta yi.” Cewar Umma sannan ta d’aura da cewa “Yo Allah na tuba daman Yaran yanzu ka haifo su ta hanya mai kyau ma ya aka k’are, ballantana ta hanyar da ba ta dace ba!!”. Da k’arfi Mama ta runtse idanunta wasu zafafan hawaye suka shiga tsiyayo mata… Umma bata damu ba ta ci gaba da cewa “Sannan sai ki dinga goya mata baya tana abubuwan da ta ga dama idan anyi magana ki ce sharri aka yi mata saboda bakin ku d’aya ko?? Kina samu tana kawo miki taro da sisi.” Hudan ce ta mik’e ta k’arasa kusa da Umma tace “Umma dan Allah ki yi shiru kinga fa maganar ki yadda take saka Mama kuka.” D’an zaro idanu Umma ta yi kafin tace “Eh lalle Yarinyar nan kin rik’a!!!! Ko da yake ba zan ga laifin ki ba, yanzu ai gani kike yi daidai kike da ni tunda duk abinda na sani kema kin sanshi, zafin ciwon nak’uda kawai ya rage.…..” Da sauri Mama itama ta mik’e ta k’arasa daff da Umma ta ce “Dan Allah dan annabi Sadiya ya isa haka! Za kisa Yarinya ta san abunda shekarunta ma basu kai ba, tun d’azu kinata aibantata da bakinki kuma yanzu kin zo kina irin wannan maganar a gaban Yara saboda Allah.” Mamaki ne ya cika Umma saboda ta dad’e ba ta ga b’acin ran Mama kamar haka ba, cikin matsowa kusa da sosai itama tace “Lalle Maryam!! na jinjina miki. Son y’arki ya rufe miki ido har kina gaya mini magana dan na fad’i gaskiya??”. Mama bata bari ta k’arasa ba tace “Wallahi ba gaskiya kika fad’a ba!” Sannan ta juya ta kamo hannun Huda wadda take ta kuka ganin ana fad’a a kanta, ta kawo ta gaban Umma tace “Zan iya dafa Al Qur’ani akan sharri kuke yi mata, Allah ne shaida ta na san kalar tarbiyyar da na yi mata. Idan kuma kina da shedar da zaki tabbatar da abinda kike cewa gaskiya ne to Bismillah Ina sauraron ki.” Hudan garin k’ok’arin goge hawaye bata saniba handkarcheif d’in da Arshaad ya bata ya fad’o k’asa! Karaf! kuwa a kan idon Jalila, da sauri ta k’araso inda ta ga handkarcheif d’in ya fad’i,har tana gurd’ewa. Duk sai suka zubawa inda ta nufa ido, cikin sauri ta durk’usa ta d’auka,sai a lokacin Hudan ta lura aikuwa ta fara rarraba ido gabanta na mugun fad’uwa kana ganin ta ka ga mara gaskiya. K’arasowa Jalilan ta yi kusa da Mama, dai dai fuskarta ta d’ago handkerchief d’in ta yi mata fifita da shi a dai dai setin fuskarta kafin tace “kowa dai ya ga lokacinda ya fad’o daga hannun Huda ko? Tambayata a nan itace ‘shin a ina kamila nitsatstsiya Huda ta samu handkerchief mai kyau haka da k’amshin turare wanda na tabbata na maza ne?’.” Ya Junaidu wanda kishi ya turnuk’e sa a take ne, yace “Kawo in gani!” Mik’a masa ta yi ya k’arasa warewa…Farine tas! Hanky d’in, kana gani ka ga had’add’en personalize handkerchief, ta chan k’asa an rubuta ‘AY’ da wani had’add’en glitter gold, ga uban k’amshin da yake ta zubawa na had’add’en designer perfume. Da kyar ya samu ya d’an yi controlling temper d’inshi tukunna ya kalli Huda yace “na waye???“ Ya yi mata tambayar yana tsareta da manyan idanuwanshi da suka fara chanja kala. Shiru Huda tayi ta fara goge hawayenta da suke zuba a yanzun babu k’akk’autawa. Mama ma da gabanta yake ta fad’uwa tana kiran sunan Allah da k’ok’arin kawar da mugun tunani akan y’artata tace “Huda tambayar ki fa akeyi, kin yi shiru ki bamu amsa!” Baba wanda ya shigo yanzu ne yace “Ku barta ai ba zata tab’a cewa komai ba! Gani nan, ni ne zan baku amsa!.” BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 08. Duk juyowa suka yi suna kallonshi da mamaki a kan fuskokinsu. K’arasowa yayi ya kalli Mama yace “Nace miki Yarinyar nan yawonta ta tafi irin wanda kika yi amma kin k’aryata ni ko?? To mai adaidaita sahun da ya kawota shi na bi na tsare na tambaya ya kuma tabbatar mini da cewa ‘Ita da wani saurayi dogo fari tass suka tsaida shi a wajen kwandila, bayan ta shiga har yana ce mata ta gaida su Mama har ya bada dubu d’aya a kawota, da mai napep d’in ya bata chanji tace ta bar masa.’ Haka akayi ko ba haka ba?” Ya k’arashe tambayar yana kallon Huda wadda jikinta a yanzu yake mugun karkarwa ga hawaye sai zuba sukeyi ta gagara controlling d’insu. Mama ce ta k’arasa ta kamo hannunta ta share mata hawaye sannan a hankali tace “Huda da gaske ne abinda mai napep ya fad’awa Baban ku? Dan Allah kar kiyi mini k’arya.” Addua Mama take yi a ranta Hudan tace mata ‘A’a’ amman sai taga tana d’aga mata kai alamar ‘Eh’. Wata uwar gud’a Umma ta rangad’a sannan tace “Huda Allah dai ya yi miki albarka, gwara da kika fara fitowa fili kina fad’in gaskiya, yanzu sai a daina janta d’aki a na b’oyewa.. Don kowa yanzu ya san hali! har shi Junaidu mai goya mata baya yau kam ya ji kuma ya gani. A bi dai a hankali kar a kwaso k’anjamau.” A fusace Mama tace “Bana son mugun alkaba’i, dan an ganta da wani sai kuma akace wani abun ke tsakaninsu?? Ki fad’i alkhairi ko ki yi shiru mana! Mai ya kawo maganar k’anjamau a nan?” Baba ne yace “Wallahi Maryam zan yi mugun sab’a miki!!! Ya da girman mu kina raina mana hankali? Uban mai ya had’ata da shi to da har ya sako ta a adaidaita sahu? To bari kiji in gaya miki!! Malam Iro mai kayan Miya da kika rainawa arzik’i kika hana shi auranta, yanzu zan je ince ya turo!! Dan ba zan zauna Yarinya ta lalata mini gida ba. Amman kafin nan sai na sauya mata kamanni ta yadda shi kansa d’an iskan saurayin nata ba zai iya ganeta ba, kuma gobe ko ance ta je ba za ta je ba.” Junaidu ne ya sha gaban sa ganin ya yo kan Hudan, kafin yace “Baba a yi bincike dan Allah, kar a yi saurin yanke hukunci.” Cikin fushi Umma tace “tou shanyayye!! binciken me kuma bayan wanda akayi?” Da sauri yace “Umma mu tambaye ta mana mu ji, kina gani fa bata b’oyewa kowa ba ta fad’i gaskiya bata k’aryata mai adaidaita sahun ba, ko?” Yanzu wannan munafukar Yarinyar za ka tambaya??? Kuma kana zaton za ta fad’i gaskiya? Tou Bismillah bari mu ji.” Umman tace tana mai gyara tsayuwarta da d’aurin d’ankwalinta. Ahankali cikin nutsuwa Junaidu ya tambaye ta “hanky d’in na waye? sannan waye wannan mutumin da aka gansu tare,a ina ta sanshi?” Amsa d’aya ta iya bashi, “hanky d’in na mutumin ne amman ita wallahi ba ta sanshi ba.” Ta kuma bashi labarin tun daga yadda kare ya biyo ta har lokacin da ya sakota a adaidaita….. Dariya Umma da Jalila suka saka kafin Jalila tace “Lalle Huda kin cika tantiriyar mak’aryaciya!” Junaidu kuwa ganin raina masa hankali ma zata yi yasa ya jefar da hanky d’in kawai ya juya ya fita ranshi a mugun b’ace…..A hanyar fita suka had’u da Ya Jaafar yana shirin shigowa shi kuma, yana tafe yana tangad’i. Yana shigowa ya hango Mama a gaban Huda ta na k’ok’arin kare ta daga dukan da Baba yake shirin yi mata tana kuka tana bashi hak’uri..saboda ita har ga Allah ta yarda da labarin da Hudan ta basu. Da saurinshi ya k’araso yace “Ke dan ubanki Ina zob’o na???tun jiya na k’i shan ruwa ke nake jira, Jalila tace mini tun jiya da yamma muka aikeki, a gidan ubanwa kika kwana?” Ita Hudan sai yanzu ma ta tuna da kud’in aiken kuma indai za ta iya tuna a inda ta zubar to a wajen gudun kare ne…. Hak’uri ta shiga bashi tana cewa “Bata ga gidan mai tuwo tuwo ba, ta duba duk wani lungu da sak’o na Gabdun Albasa. Sannan kud’in sun fad’i, ya yi hak’uri dan Allah.” Zancenta na kud’in sun zube kawai ya iya fahimta, dan haka ya yo kanta zai daketa nan ma Mama ta kuma karewa, ta hau rok’on Baba tana cewa “Dan Allah ka bawa Jaafar hak’uri, ka ga a yanayin da yake ciki, baya cikin hankalinshi kar ya je ya ji mata ciwo.” Umma ganin kamar Mama za ta yi nasara a kan Baba ne yasa ta sanya gaba d’ayan k’arfin ta ta ja Mama ta cilla ta gefe har saida ta fad’i k’asa. Ya Jaafar kamar jira yake yi ya hango wani tsohon katako a gefe kawai ya nufe shi ya d’akko. Mama na ganin haka ta fara k’ok’arin mik’ewa da sauri ta nufi inda suke amma kafin ta k’araso har ya bugawa Hudan a cikinta da dukkan rogowan k’arfinsa. Aikuwa dukan ya shige ta ba kad’an ba, k’usoshin da suke jikin katakon suka chaketa wanda hakan ya sanya jini ya fara zuba, a take ta fad’i a wajen ta sume. Sai da numfashin Mama ya d’auke da jinta da ganinta na y’an sakanni tukunna a hankali ta taka ta k’araso ta durk’usa ta fashe da kuka, tana dudduba ta tana neman pulse….. Da sauri ta mik’e ta nufi d’aki ta bud’e jakarta ta zaro waya ta hau kiran Ummu.… Shi kuwa Ya Ja’afar yana ganin ta sume, shi ya d’aukama ko ta mutu ne, dan haka ya kwasa a guje ya yi waje. Umma da Jalila kuwa d’akinsu suka nufa, haka shima Baba….babu wanda yace uffan a cikinsu. Ummu, an ci sa’a har yanzu suna gidan Hajiya Shuwa, dan ya fi kusa da asibitin, shiyasa suka zauna a nan gudun kar su koma gida ciwon Sumayyan ya sake tasowa. Suna cikin hira ta ji k’arar wayarta, ganin sunan Mama wanda tayi saving da sister a kan screen d’in ya sanya ta yin murmushi kafin ta d’auka tana mai cewa “Mama jikin nata fa da sauk’i, ki kwantar da hankalinki bacci ma takeyi yanz....” Jin sheshshek’ar kuka yasa tace “Me ya faru? Ya naji kamar kina kuka??”. Salati ta fara lokacin da Mama ta fara gaya mata halin da Hudan take ciki… ba ta tsaya jin ba’asi ba ta zaro mayafinta ta yi waje, ganin hakan ya sanya Sakina biyo ta. A bakin gate suka ci karo da Madu, ganin yanayinta ya sanya shi tambayarta “mai ya fati?” shi a tunaninsa ma ko jikin Sumayyan ne…nan ta hau gaya mishi abunda ya samu Hudan….Shiruuu! yayi ba tare da yace komai ba, chan kuma a hankali ya rab’a ta gefenta ya wuce cikin gida. Wani siririn kuka Mama ta sake fashewa da shi sarai Ummu ta san ta ji yadda sukayi da Madu yanzu da yadda Madun ya nuna halin ko’in kula da lamarin…. Shiru kawai ta yi ta cigaba da tafiya da sauri domin ta je ta iske su ita da Hudan akan lokaci tunda yanzu shine priority. Sauri takeyi still da wayar kare a kunnanta dan ta cewa Maman “kar ta kashe har ta k’araso.” A bakin layin suka ci karo da Junaidu, ganin ta da yayi a hargitse yasa ya shiga tambayar ta “mai ya faru??” Ce masa kawai ta yi “Ya nemo mai adaidata ya kawo k’ofar gidan Baba yanzun nan.” Da farko kamar ba zai yi ba, domin kuwa shi Yaji! ma yake shirin yiwa gidan gaba d’aya saboda kwata kwata baya son ya had’u da Huda don idan yana ganin ta kishi zai iya sakawa ya bubbugeta, shi kuma baya son hakan ta faru. Dan haka ya yanke shawarar barin gidan for some time. Ji yayi zuciyar shi tana bashi shawarar ya yi abinda Ummun tace dan haka kawai ya nufi titi.... Ummu sai da ta zo shiga gidan tukunna ta lura da Sakina, dan haka a tare suka kutsa kai suka shige. Suna isa tsakar gidan kuwa suka hango Hudan a kwance malale cikin jini, ga wani makeken katako a kwance a kan cikinta ragowanshi kuma yana jan k’asa, kanta a kan cinyar Mama wadda taketa kuka tana rik’e da waya a kunnenta dayan hannun kuma tana ta shafa kan Hudan. Kukan da Sakina ta fashe da shi ne ya janyo hankalin ta garesu, aikuwa ganin y’ar uwarta yasa ta fashe da wani sabon kuka abun tausayi. Ummu ma bata san lokacin da ta fara kukan ba, Sakina kam da gudu ta k’arasa inda suke ta hau kiran sunan “Huda!” Jin kamar k’arar adaidaita sahu ne yasa Ummu juyawa tana addua Allah yasa Junaidu ne, aikuwa a soro suka had’u da shi yace mata “mai napep d’in yana waje” sannan ya juya zai fita, da sauri tace “dan Allah Junaidu zo ka taya mu d’aukar Huda.“ Da mamaki yake kallonta sai kuma kawai ya bita suka shiga ciki…gabanshi ne yayi mugun fad’uwa da ganin halin da Hudan take ciki, da gudu shima ya k’arasa yana kiran sunan ta yana tambayar Mama “mai ya faru?” Duk a lokaci d’aya. Da kyar Mama ta iya ce mishi “Ja’afar ne.” A zabure ya mik’e ransa a b’ace zai yi waje Ummu ta taro shi, tace “Yanzu ba lokacin wannan bane ba, mu ji da lafiyarta tukunna.” “Sakina, d’auko zanin gado ko wani babban hijabi mu samu mu raba ta da wannan mugun katakon, mu danne jinin sai mu kaita asibiti.” Hakan kuwa aka yi… Daga nan suka kinkimeta da taimakon Junaidu aka sakata a napep aka nufi asibitin kusa da su dan emergency ne…. Sai da Umma da Jalila suka ji fitarsu tukunna suka sauk’e ajiyar zuciya a tare Jalila ta saka dariya kafin tace”Ai ko banza ta wahala!. Da farko fa amma tsorata nayi Umma dan wallahi na d’auka ta mutu ne, sai da na ga Mama ta duba hannunta da wuyan ta tace ‘Alhamdulillah’ tukunnan hankalina ya d’an kwanta, amman da har na fara shirin guduwa wallahi.” Umma ce tace “ke dalla chan rufe min baki!!! Banza kawai!! kina nan zaune gashi ita har ta yo saurayi mai kud’i!, ke kina fama da malamin maths wanda sai dai yayi ta lissafa uban kud’ad’e amma ba zai iya baki ko sisi ba. Wannan kuwa kina gani kin san mai kudi ne, kalli kyallen da ya bata, k’amshin turaren jiki duk ya cika gidan nan. Tunda na dawo kike ta ce mini kin had’a bomb in jira yau burinmu zai cika ashe ke shirme kika had’a ban sanib..” Cikin katseta Jalila tace “Wallahi Umma da gaske ni plan d’ina shine Ya Ja’afar ya zaneta sannan ta yi dare sosai tunda kinga ai ba lalle ta gane gidan ba tunda ta dad’e bata je ba, sannan ita kuma Mama idan ta ji mun aiketa gidan ai kinga ranta zai b’aci Daganan ni kuma inyi ta fad’an maganganu a kanta yadda Mama zata ji haushi ta fusata. Ni sam ban yi tunanin za ta yo saurayi b...” “Aikuwa gashi ta yo kuma mai kud’i, kina jin kan zanjen nata kin san Yaron sonta yake yi.” Cewar Umma. Shiru Jalila ta yi kamar mai tunani chan kuma tace “Umma kema kin yarda da labarin da ta bayar kenan?” “To ai shine gaskiya.” Inji Umma, kafin ta d’aura da “idan ba hakan ba ta Ina wachchar gab’uwar Yarinyar ta san wani zuwa wajen saurayi??? Ni yanzu babban tashin hankalina kar ya zo ya zubewa Babanku kud’i kin san halinshi in dai yaga kud’i, mu je ya yarda ya bashi ita! Gashi ita kuma wawiya ta yi kwatancen gidan nan kuma nasan ya ji, zai zo….” Shiru duk sukayi Umma in banda huci ba abunda take yi kana ganinta ka san hankalinta a mugun tashe yake sannan tayi zurfi cikin tunani. Me ta tuna? Allah kad’ai ya sani, haka nan ta fara murmushi kafin tace “Allah ya kawoshi lafiya.” Kawai, ta fad’i hakan still da murmushi a fusakarta. Jalila dai ba fahimtarta ta yi ba, hakan yasa ta hau gado ta kwanta tana sinsinar k’amshin jikin handkerchief d’in a haka bacci ya yi awon gaba da ita, ta bar Umma tanata faman tufka da warwara. A chan asibiti kuwa, suna zuwa aka yi emergency da Huda. Likitoci suka rufu a kanta, Allah sarki Junaidu har da kukan sa shima Ummu da Sakina suma suna taya Mama..Har sai da wata nurse ta zo ta fara musu fad’a tana cewa “Addua za ku yi mata ba kuka ba, sanna kai kana Namiji kana kuka wa zai basu hak’uri??” Tukunnan a hankali Junaidu ya mik’e ya fice ya nufi masallaci Su Mama suma suka shiga k’ok’arin tsayar da kukan su, suna masu addu’ar Allah ya bata lfy ya kawo mata sassauci, dukda hawayen ba daina zuba yayi ba. Sai da aka yi! aka yi!! Tukunna suka tsayar da jinin, da kyar suka fito wajen awan su 4, dan numfashinta k’in daidaituwa ya yi da farko. Likitan ne yace “su godewa Allah k’usoshin basu tab’a komai ba. An yi mata tetanus da duk wani abunda ya kamata, an kaita d’akin hutawa za su iya zuwa.” Daga haka ya mik’a musu takardar bill. Cikin mutuwar jiki Mama ta fara k’ok’arin mik’a hannu za ta karb’a, Ummu ta yi saurin amsa tana dubawa, kafin ta cewa Sakina “ta hau Napep ya kaita gidan Hajiya Shuwa ta fad’a musu halin da ake ciki ita da su Baabaa Talatu sannan ta d’auko mata jakarta da atm d’inta.” A take Sakina ta wuce. Wasu zafafan hawayene suka zubowa Mama, a hankali tasa hannuta ta goge sannan ta mik’e ta nufi d’akin da aka yi musu kwatance, inda Hudan take. Ummu kawai binta ta yi a baya dan ta san abinda ya zo mata rai yanzun har yasa ta kasa yi mata magana. Kusan a tare suka shiga d’akin, Ummu ta zauna wajen k’afarta ita kuma Mama ta zauna a kan kujerar dake kusa da kanta a gefen

Chapter 6 of 32