Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gramma duk ta rud’e. “Doctor mai ka fahimta yana damunta???” Granpa ya yi mishi tambayar yana dogara sandarshi yana mai k’arasowa wajen. Mik’ewa tsaye ya yi sannan ya zare farin glasses d’in idonsa ya d’an mutsitsika idon ya maida glass d’in kafin yace “Heart d’inta ke da matsala, and da alamar ya yi serious gaskiya tunda har ga jini,ban san dalilin da ya sanya ta b’oye ba ta gayawa kowa ba,but this is very serious,idan ba damuwa yanzu zan tafi da ita mu yi ECO, saboda mu san matakin d’auka,dan ba a d’aukar issue na heart irin wannan likely.” “A wanne asibiti za a sameka?” Granpa ya sake mishi tamabayar. Card d’insa ya mik’awa granpa mai d’auke da suna da address na diagnostic center d’inshi sannan yace “nan waje nane it’s a private place. I’m a consultant a AkTH,idan hankalinku ya fi kwanciya da chan sai ayi mata a chan d’in, dai nasu zai d’auki time kafin a gama. “Za a sameka a chan (nakan)nan da 1 hour,get every thing ready” “Ok sir,”shine abinda Doctor yace sannan ya juya ya fita. “Let me show him the door” Mom tace sannan ta bi bayanshi. A hankali ya k’arasa takowa inda suke kafin ya kalli gramma yace mata “Leave us” A hankali gramma ta mik’e ta juya ta fita. K’arasowa yayi ya zauna a kan kujerar da take zaune a gefenta kadan a kan kafet sannan yace “Since when kika yi realizing baki da lafiya??” “2 years ago”tace. “Wa kika fad’awa?” “Ba kowa.” “Mai ya yi causing abun?” Shiruu ta yi wannan karon. Zan b’ata miki rai Ummi,kin san ba na son kame kame da kyaliya. Hawaye ta share kafin tace “Abba ne”cikin sheshshek’ar kuka. Tari ta fara yi sai da ya d’ab tsagaita sannan ta ci gaba da magana “Ba ya bani time d’inshi,kullum cikin zancen Maryam yake,i tried very well inga na daidaita relationship d’inmu amman na kasa,yak’i ya bani had’in kai at the end ma gashi ya zo ya rabu da ni gaba d’aya. Inaji yana waya da Abokinsa wai ya san idan ya had’amu ni da Maryam ranar lahira da shanyayyen b’arin jiki zai tashi…..tunda yanzu ya samu chance d’in da zai iya maida ita…..kuma wai yana jin tausayina,gara ya sauwak’e mini inyi aure nima In samu wanda zai iya bani kulawa tun kafin lokaci ya k’ure. Granpa it’s like har yanzu suna tare a yanayin maganarsa.” Tana kaiwa nan ta fara tari irin na marasa lfy,abun tausayi. A hankali ta ji granpa ya dafa ta sannan yace “ki huta,ya isa haka.” Waya ya d’auka ya fara lalube sannan da kyar ya nemo numbershi,yayi mamaki da ya samu number dan ya jima basa waya…ko abu zai fad’a mishi sai dai ya gayawa Dad ya fad’a mishi, ko Abban ya kirashi domin ya gaidashi baya amsawa. Sometimes kuma yayi rejecting shiyasa tun yana kira har ya zo ya daina shima. Abba yana zaune Sudais yanata zuba masa surutu ya ji k’arar wayarshi,zaro ta yayi daga aljihun gaban rigarshi ya kalla screen d’in, k’ara kalla yayi ya d’ab bud’e idonshi…ganin da gaske ne yasa yayi saurin d’auka had’e da toshe wa Sudais baki “Assa...” Kafin ya k’arasa sallamar ya ji ance “Ina falona,ka sameni yanzu” Kit!! Ya ji an kashe wayar. Mik’ewa yayi a take sai dai da kyar k’afafuwansa suka iya d’aukar sa saboda sanyi da rawar da suke yi dama kuma ga yanayin rashin lafiyar da yake ciki. Ajiyar zuciya ya sauk’e,ya tattaro dukkanin kuzarinsa sannan ya fara tafiya a hankali domin amsa kiran mahaifin nashi. Gaban Ummi ne ya fara dukan uku uku gashi Mom bata kusa…dukda sunada mafitar abinda za su fad’a amman hakan bai hanata jin tsoro ba,da kyar ta samu ta saisaita kanta gudun kar granpa ya fahimci wani abu,dukda ta san shi ba mutum ba ne mai zurfafa bincike iyakar abinda akai akan idanunsa da shi yake aiki sannan bashi da time d’in bibiyar abinda bai shafeshi sosai ba above all ya yarda da Ummi yana ji da ita sosai ba ya son abinda zai b’ata mata rai ita kad’ai ce in abu ya shafeta yake sawa ya sauk’o daga dokin zuciya…….tana cikin wannan tunanin suka ji sallamar Abba. Granpa ne ya amsa sannan yace”k’araso ciki.” Shigowa ya yi, sannan ya k’araso inda ya ga Ummi a zaune ya nemi guri ya shima ya zauna a d’an gefenta kad’an. “Barka da yamma” shine abinda Abba yace da granpa, kanshi na kallon k’asa. Juyowa granpa ya yi ya kalleshi sannan yace “Ai ban yi tunanin har yanzu Ina da darajar da zaka gaidani ba.” Bai jira jin abinda zai ce masa ba ya d’aura “Bara in baka wani gajeran labari,dukda na san ka sani amman bara in sake maimaita maka.” Mik’ewa ya yi yana dogara sandarsa ya koma wajen da su Ummin suka shigo suka sameshi d’azu ya tsaya yana kallon waje,a hankali ya fara magana........... ……. “Asalina d’an k’asar Chad ne, mahaifin mahaifiyarmu ma haka,saidai mahaifiyarta ce ta fito daga yankin Niger,Agadaz. Mu biyu iyayen mu suka haifa a duniyar nan,da ni da d’an uwana…gudun hijira ya sanya muka baro k’asarmu ta haihuwa,domin a lokacin har kakanninmu sai da aka kashe da kyar muka tsira,kasancewar Fulani bamu da yawa a yankin ya sanya aka yi galaba akanmu. A lokacin inada shekaru tara a duniya d’an uwana kuma yanada 11,tun a hanya na lura mahaifin mu bashi da lafiya,da na tambaye shi sai yace mini gajiyar tafiya ne.. Yanayin gudun hijira ba abu bane mai sauk’i don ko ruwan da mutum zai sha ma aikine. Mahaifin mu ya zab’a mu bi ta Agadaz domin mu duba ko zamu had’u da dangin mahaifiyar mamana ko zasu taimaka mana akan mu tafi garin da bamu san kowa ba. Mahaifiyarmu ta so yin tirjiya akan gara mu bi ragowar mutanen rugarmu waenda suka yi saura, saboda ta san a wannan lokacin danginta kowa yayi nashi wurin sannan y’an uwanta idan ma za ta samu yanzu mutun d’aya ce, wadda take aure a chan, don mahaifiyar tata su uku aka haifa a gidansu kuma itace auta,Babbar yayyarsu a ghana take aure. K’in yarda da zancenta da mahaifinmu ya yi ne ya sanya muka nufi Agadaz Amma sai muka yi rashin sa’a muna zuwa aka tabbatar mana ciwon k’afa ya kamata an kaita Yemen neman magani. Da kyar wani makwafcinsu ya bamu gurin kwana da abinci mukai wanka da safe muka nufi marad’i,don Yemen akwai nisa sannan babu ko sisi a wajenmu, dayake mahaifinmu ya tab’a zuwa daura ya sanya shi cewa mu zo daura ko marad’i inyaso idan ya d’an samu aiki yayi ya tara kud’i daga baya sai mu tafi Yemen d’in mu dubota. kasancewar hanyar Sahara ce ko ina,yasanya muka wahala babu ruwa babu abinci kowannenmu idan ka kalla a wahale yake Shiyasa da zaran mahaifinmu ya nemo d’an abinci ko abun sha sai ya bamu mu ci yace mana shi ya ci a hanya saboda yana gudun kar wani abun ya samemu dan a ganinsa laifinshi ne saboda babu yadda mahaifiyar mu batayi da shi ba akan mu bi tawagar y’an hijira mu gudu tare amman ya k’i. A lokacin naga amfanin ilimi domin da muka k’arasa marad’i babu wanda yake jin yarenmu, sannan muma bama jin nasu, sannan bama jin turanci ballantana mu yi communicating da su. Hakanan muka kwana a y’ar kasuwarsu da kyar mai k’osai ta bamu sadaka mukaci,da safe muka samu wanda zaije daura ya tausayamana muka bishi a motar katakon shi (kiya kiya ). Ga wahala ga yunwa ga kuma yin tafiya mai nisa a kiya kiya a wannan lokacin ba dadi . Tun kafin mu k’arasa mahaifinmu ya fara jijjiga idanunsa suka k’akk’afe, muna isa garin aka taimaka mana muka yi asibiti da shi, ba a jimaba Allah ya karb’i ransa ta sanadin rashin abinci likitoci suka tabbatar mana da cewa ya shiga hypoglycemia ne, sannan bai samu taimakon gaggawa akan lokaci ba. A lokacin bamu san kowa ba, ganin haka yasa Likitan ya nemo mutane aka sallaci mahaifin mu aka kaishi gidanshi na gaskiya, bayan ya tabbatar da mu Musulmai ne. Bayan an dawo daga mak’abarta lokacin tafiyar sa gida yayi still ya ga bamu da niyyar tashi, dan haka ya zo ya sami Mamanmu yace mata idan ba damuwa mu bishi gidanshi, kafin a san ya za a yi. Muna isa gidan kuwa matar sa tace ba za ta rik’e mutum uku ba sai dai a kaimu gidan marayu da ni da d’an uwana In yaso ita mamanmu ta dinga mata wanke wanke da shara. A lokacin rigima ce ta b’arke tsakanin Likitan nan da matarshi, domin ita tace ‘ba za ta rik’e tsintacciyar mage ba ai ya ma yi sa’a da ta yarda za ra d’auki Maman namu aiki’ Shi kuma ya dage akan sai mun zauna ai daman ba yau ta saba yi mishi irin haka ba! Taya yana miji amman ita ace ita za ta dinga zartar da hukunci. Rigima suka hau yi sosai,har ta kai ya fara ik’irarin rabuwa da ita. Ganin hakan ya sanya Maman mu tace”Ta yarda a kaimu gidan marayun In yaso idan ta yi aikin ko na wata hud’u ne ta d’an tara kud’i sai ta fara sana ‘a taje ta d’auko mu ta kama haya.’ Hakan kuwa aka yi muna kuka muna komai aka kaimu gidan marayu…. Maman mu mace ce da baka iya gane tak’memen abun da yake cikin zuciyar ta amman zan iya cewa a wannan lokacin na ga tsananin tashin hankali da k’unci a fuskarta domin kuwa itama harda kukanta. Every weekend take zuwa ta dubo mu A lokacin ne kuma yayana duk da k’arancin shekarun shi ya dage wajen koyan sana‘a, dan zan iya cewa duk wata sana ar da ake koyarwa a gidan marayun nan babu wadda bai iya ba,ba ya isheshen bacci kullum cikin aiki,idan nace mishi ya huta yakan ce mini ‘ba dan kanshi yakeyi ba,saboda ni da mama yakeso ya yi sana’a ya tara kud’i ni da shi mu koma makaranta sannan ya siya mana gida.’ A kullum maganarshi kenan. Tun muna Yara mun kasance masu tsananin k’aunar juna,soyayyar da yayana yake yi mini ba kad’an bace ba,ba ya son ya ga rai na a b’ace duk da kuwa ni d’in na kasance Miskili ne amman in dai ina tare da shi sai ya san yadda yasa na ware sosai saboda baya bari na ma har sai ya ga Ina dariya. Kamar yadda mahaifinmu ya dinga sacrifice yana bamu abincin da ya samu(lokacin gudun hijira)haka shima ya dinga yi mini a gidan marayu,gashi ya hanani aikin komai,shi yake had’awa nawa da nashi ya yi,zan iya cewa ni kam ban san wahalar gidan marayu ba kwata kwata. Mun shafe wata uku a gidan Marayu muna neman shiga na hud’u. Ranar wata lahadi muka tashi mukai wanka da sassafe muna jiran mahaifiyarmu,kasancewar ranar zuwanta kenan amman har yamma bata iso ba,sai da daddare wannan Likita ya xo ya tura aka kiramu. Muna fitowa da ya had’a idanu da mu kawai sai naga ya fashe da kuka,da sauri muka k’araso gabanshi muka hau tambayarshi amman sai bai amsa mana ba kawai ya cewa shugaban wajen yayi checking namu out zai tafi da mu. Sai da muka je gidan nasa muka gane dalilin kukanshi…ciwon zuciya mahaifiyarmu take fama da shi tun watanni uku da suka shud’e tanata nuk’u nuk’u babu wanda ta fad’awa yau kuma da safe ta yanke jiki ta fad’i jininta yai high sosai,babu irin taimakon da basu bata ba amman rai yayi halinshi. A ranar kam mun sha kuka iya kuka hatta wannan matar Likita sai da ta tausaya mana. A ranar sadakar uku ne kuma ta tada balli tace ‘sai dai mijin ta ya nemi wani wajen ko ya kama mana haya mu koma dan ba zai barta da Yara maza a gida ba bayan ita mata ne nata kuma k’anana, ai mu maza ne ko aikin k’arfi ne za mu iya mu samu mu rik’e kanmu.’ Hakan kuwa akayi Sai dai kud’in da mahaifiyarmu ta tara bai isa kama haya ba balle a had’a da Sana’a. Shawara Likita suka yi da yayana aka kama haya shima sai da ya cika mana. Gefen gidan wata tsohuwa da y’ar jikarta aka kama mana haya, sannan Likitan ya bata amanar mu. Kasancewar Yayana ya iya sana a kala kala ya sanya yake fita sana a,Allah kuwa ya sanya mishi albarka domin duk abinda yayi ko ya tab’a sai ka ga bud’u da karb’uwa ta koina dukda kuwa k’arancin shekarunshi..hakan ya sanya masu shago suka rik’esa kowa yanaso ya yi aiki da shi. Acikin shekaru biyar yaya ya bud’e shagon d’inkin sa,da wajen had’a hula da takalma, da turarurruka,sannan ya koma makaranta nima yasaka ni a makaranta,kuma cikin ikon Allah har gidan wannan y’ar tsohuwa shi yake ciyarwa,domin ta zame mana kamar uwa jikarta kuma y’ar uwa Likita kuma ya kan zo duk wata ya duba mu,haka nan muka zama kamar family. A lokacin da shekaru na suka ja,naje na samu yayana da batun inaso inyi aure don a lokacin ina matuk’ar k’aunar mahaifiyarku, kuma babanta har ya fara shirin maganar zai bata wani d’an uwanta za ai musu aure, to a wannan lokacin shima d’an uwana Ashe yanada tashi budurwa harya gama hada kudin lefe da na siyan gida da komai amman ganin yadda hankali na ya tashi yasanya ya bani kudin lefen muka je ya siya mini gida da duk wani abun da za a buk’ata, sannan ya bani wajen had’a turarenshi a matsayin kyauta yace in kula da Iyalina da shi. Both mahaifiyar ku da budurwar da yayana yake nema, y’ay’an masu kud’i ne neman auren su ba abu ne mai sauk’i ba hakan ya sanya da yayana ya nemi da a k’ara mishi lokaci ya sake shiryawa, mahaifin ta ya k’i amincewa barema da ya ji k’aninsa zai yi aure sai ya yi tunanin raina musu hankali yake son yi… haka nan yanaji yana gani aka aurar da ita kuma ya b’oye mini don ya san ba zan bari ba shi kuma ya fi son ya fi son farin cikina akan nashi. Shi ya wuce mini gaba ya tabbatar na auri Maijiddah , Likita ya yi mini wakili. Bayan nan muka ci gaba da karatu da business gadan gadan,Yaya iyakacinshi masters amman ni har PHD sai da ya tabbatar nayi, ya rik’e gaba d’aya companies d’in harda na turare na daya bani wanda a lokacin ya bunk’asa , yace zai iya inje inyi karatun nawa. Yaya bai yi aure ba,sai bayan shekaru goma mutane sunata gulmace gulmace amman ya toshe kunnuwanshi,saboda shi tunda aka aurar da wacce yake so aure ya fice mishi akai. Sai da na saka baki ni da Likita tukun ya yarda ya yi auren a lokacin har kai an Haifa. Matar Likita wadda ta dinga m korarmu a gidanta itace ta kawo d’aya a cikin y’ay’anta tace ‘ta bashi ya aura’. Don a lokacin Yaya yayi kud’i na ban mamaki,sai kuma akayi dace ya yarda don yana ganin ta ta kwanta mishi,sannan kuma ko da ace bayaso yaci ace ya karb’i y’ar Likita a matsayin mata ko dan halaccin ubanta. Tunda na yi aure nake burin in haifi y’a mace, sannan ina son in saka mata sunan Mahaifiyarmu, amman Allah bai bani ba, da kai da Yusuf da Yahaya Allah ya bani. Bayan auren Yaya kuwa da shekara d’aya aka haifi Zainab(Ummi) Da ni da Yaya ban san wa ya fi wani sonta ba gashi sunan mahaifiyarmu gareta. A lokacin ne kuma Yaya suka yi wani accident wanda akai mishi aiki aka tabbatar mana magudanar kwayayan haihuwanshi sun sami matsala,ba zai sake haihuwa ba! Mun girgiza sosai amman kasancewar mu masu tawakkali ne sai muka mik’awa Ubangiji lamuranmu muka rungumi k’addara. Abu d’aya muka sa a gaba shine faranta ran Ummi,Yaya ya tab’a gaya mini yana neman kud’ine saboda faranta raina da na mahaifiyarmu amman hakan bata faruba a b’angaren mahaifiyarmu domin mun rasa ta tun kafin ta ji dad’in da muka so bata,shiyasa yayi alk’awarin d’aura dukkan wani gata na duniyar nan akan tilon y’ar sa tunda takwarar ta ce,ya kance idan ya ga Ummi tana dariya gani yake yi kamar mahaifiyarmu ya sanya farinciki, domin kusan halinsu d’aya dan itama Ummi tun tana da shekaru biyu da y’an watanni muka fahimci tanada nuk’u nuk’u da b’oye abu a rai. Shiyasa ya zama har y’ar rige rige muke ni da Yaya wajen cika mata burinta,muddin ta furta. Shekararta biyar a duniya Yaya da Likita suka tafi Abuja,a hanyar su ta dawowa suka yi wani mummunan hatsari!! Likita tun a lokacin ya cika sai da aka kawoshi emergency yanata cewa yana son ganina… a lokacin Ina office aka sanar mini ana san ganina a asibiti tun a lokacin gabana ya fara fad’uwa,Ina zuwa kuwa a reception aka ce mini ai y’an uwanane suka yi hatsari d’ayan ya rasu d’ayan kuma yana wanchan d’akin aka min nuni da d’akin da Yayana yake ciki… A gigice na shiga inda yake,ina ganinshi cikin jini nai kanshi da gudu na rik’esa ina kuka. Dukda halin da yake ciki bai hanashi lallashi ba,sai da ya ga na yi shiru tukunnan ya kamo hannuna duka biyu yana d’an tari da nishi da kyar... Kalmarshi ta k’arshe itace Dan Allah dan Annabi ka kula mini da Zainab ka bata duk wani farin cikin da kake da iko ga amanarta nan na bar maka sannan ya yi kalmar shahada daganan na ji jikinshi ya sake idanunsa suna kallon sama. A lokacin na yi kuka mai yawa dan na rasa rabin jiki na sannan bani da kowa bani da wani bani da elder mai kula da ni. Maraicin sai ya dawo mini sabo fil.” …… Hawaye granpa ya share ya gyara tsayuwar shi yace “Ko mutuwar iyayena ban ji ta ba kamar yadda na ji ta Yaya..na yi alk’awarin faranta mishi ko bayan ranshi ko da kuwa ace hakan zai sanya in karya tawa k’aidar. Ga matarka nan,ko ka san tana d’auke da ciwon zuciya???” Ya yi maganar tare da juyowa yana kallon Abba wanda ya juya a razane yana kallon Ummi da kamar mamaki a fuskar shi. Juyawa granpa ya yi ya ci gaba da cewa “U won Yakubu, ka yi amfani da weakness d’ina and ka ci nasara a kaina! This time around,zan iya yafe maka laifin da ka yi mini tunda na ga alamar so kake ka dawo da baya yanzu. Komai ya wuce!!sannan ka rushe maganar tashinka daga estate d’innan babu ita. Abu d’aya zuwa biyu zan baka umarni shine “Ka maida matarka yanzunnan, sannan ka kaita asibiti ga katin nan,Dr yana chan yana jiranku. And Kamar yadda na fad’a maka a baya,babu kai ba Maryam,amma in dai har ka shiryawa tsinuwa ta to bismillah Ka je ka bibiyi rayuwarta.... SHARE PLS. BULAMA✍️ So da Buri Free Book 06 Shiru Abba ya yi yana so ya gano inda kalmar ‘ka maida ita!’ Ta nufa,dan bai gane ba. Fusata granpa ya yi jin yadda yayi masa shiru Dan haka ya daka mishi tsawa ta hanyar cewa “Ko baka ji na ne Abba!!!” Tuni Abba ya hau cewa “to granpa in shaa Allah..yanzu yanzu….” Duk ya bi ya rikice. Ganin hakan ya sanya Ummi share fuskarta da ta jik’e da hawaye ta faki idon granpa ganin ba su yake kallo ba ya sanya ta d’an tab’a Abba tace “Ka taso mu tafi,yake nufi.” Kallon ta Abba ya yi sannan ya mik’e ya ce “taso mu tafi.” Dan ba ya so ya fara zazzage mata ta cikinsa a gaban granpa. Har ya juya sai kuma ya dawo ya zo ta gaban granpa ya tsugunna yace “Dan Allah ka yi hak’uri na san na yi maka laifi, ka yafe mini, in shaa Allah duk abinda kace inyi zan yi daga yau ba zan sake k’etare umarnin ka ba.” Kusan 1 minute tukunna granpa ya juyo ya kalleshi sannan yace “Yafe maka da na yi ba wai yana nufin na manta da abunda ka yi bane,na yafe maka ne saboda ni kaina in samu peace of mind na zama a same environment da kai tunda ka zame mini dole, it’s all for Ummi’s sake, so idan kanada hankali do your best to keep her happy hakan ne zai sa ka gujewa b’acin rai na, ka samu mu rabu lfy. Yana gama fad’in haka ya juya ya fara dogara sandarshi har ya kai k’ofar d’akin shi ya juyo yace mata idan bai yi abunda nace ba, ko kuma ya yi trying anything stupid ki zo ki sameni.” Daga nan ya shige ya barsu a palon. Kallon ta kawai Abba yake yi, ji yake kamar ya shak’e ta ya huta, gashi ya yiwa granpa alk’awari…idan ya fahimci kalmar granpa ta ‘ka maida ita’ Tabbas Yaji Ummi ta yo Ta karkad’e zani ta kawo k’arar sa kenan. Sannan for her sake ne ma aka hak’ura zai ci gaba da zama a estate d’in…. Muryarta ce ta katse masa tunani “Doctor is waiting” Kawai tace ta kama hanyar fita tana d’an tafiya da kyar tana tari irin na marasa lafiya. Ta zo daff da fita kenan ta ji muryar gramma tana kiran Abba. Da k’arfi Ummi ta runtse idanunta domin ta san yanzu kam k’arya ta ta k’are. Kamar kuwa yadda ta yi zato gramma tana k’arasowa ta rufe Abba da fad’a akan sakin da ya yi, sannan ta hau bada umarnin ya maida ita nan take kuma karya k’ara. A rikice yake kallon gramma sannan ya juya a fusace yana kallon Ummi wadda kana ganinta ka ga mara gaskiya…gashi babu Mom a wajen bare ta ceceta, fahimtar rashin gaskiya k’arara a kan fuskarta ne ya sanya kawai ya juya ga gramma ya fara k’ok’arin fahimtar da ita. Hakan ne ya bata damar zaro wayar ta ta hau kiran Mom a rikice. Abba kuwa hak’uri ya hau bata yana ta rantsuwa a kan “shi bai san da wata maganar saki ba ma, wato shiyasa granpa ya zuciya sosai!! Haba no wonder Ai kuwa yanzu sai an koma wajen granpa an wanke shi wallahi” Ya k’arashe maganar a fusace yana kallon Ummi. A fusace itama gramma ta cillo masa takardar hannu nata tana cewa “Wallahi zan yi matuk’ar b’ata maka,bana son rainin hankali, ko a mafarki In aka tasheni na san rubutunka kai da y’an uwan ka.” Durk’usawa ya yi ya fara k’ok’arin d’aukar takardar yana kallon gramma a ransa yana cewa ‘yanzu kam ya samu mafita k’arya Ummi ta k’are!! Dama ace cewa ta yi a baki ya fad’a mata tou da da sauk’i, a rubuce kuwa ai ko hauka ake dole a gano inda rubutu ya bambam ta.’ Hannu ya kai kan takardar ya d’auka,bai kalla ba sai da ya mik’e… A take gabansa ya yi mugun fad’uwa ya k’urawa takardar idanu yana k’ok’arin tuno yaushe ya rubuta…. Tilastawa kwakwalwarshin da ya yi ne ya haddasa masa jiri ya tafi yuuuu zai fad’i. Da sauri Likita da suka shigo tare da Mom yanzu ya yi saurin taroshi yana “Be careful,wat happen again??” Ya yi maganar yana kallon su gramma. Mom kuwa rufe Ummi tayi da fad’a sosai tana cewa “Wai ke Zainab so kike ki k’arasa shi ne? Baki ji abinda Likita ya fad’a bane? Ina ce magana ta riga ta wuce? dan na tabbatar granpa ya sanya shi ya mayar da ke! To hayaniyar kuma ta mecece? “. Kuka Ummi ta saka sannan tace”Adama cewa fa yayi wai bashi baneba.” Ajiyar zuciya Likita ya sauk’e kafin yace ki kwantar da hankalinki,ba shi d’in bane” Da mamaki duk suke kallonshi. Ajiyar zuciya ya sake sauk’ewa sannan ya ci gaba “Yanzu haka takardun nan na dawo zan baku,inata sauri d’azu na hawo ba tare da itaba. Ban so shi Abban ya sani ba gudun abunda ka iya zuwa ya dawo but now I have no choice..” Hannu gramma ta mik’a mishi sannan tace “bani nan” Cikin ladabi ya mik’a mata ta saka hannu ta karb’a, Abba bai yi wata wata ba ya lek’a suka hau karantawa suna dubawa a tare. Sai da suka gama tukunna gramma d’in ta kalleshi da alamun buk’atar Karin bayani. Gyaran murya Likitan ya yi yace “Tabbas hakane,results d’in basu gama had’uwa ba sai d’azu da safe, daman a yadda na gansa yana behaving lokacin a asibiti na yi tunanin hakan shiyasa na yanke shawarar yi masa waennan tests d’in and

Chapter 4 of 32