tare da shi…
A take su Ya Jamilu suka kinkimeshi aka saka a mota
suka nufi asibiti dukkan su. Sai da Likitoci sukayi da gaske tukunna suka samu numfashin sa ya daidaita…
Bai farka ba sai bayan kwana hud’u amma ya samu stroke mai k’arfi dan hatta bakinshi da hancinshi sun koma b’angare daya a fuskarshi.
Idan ka ganshi abun tausayi dole kayi kuka, Likitocin ne suka yi ta basu kwarin guiwa akan zai dawo daidai da yardar Allah da taimokon therapy da excercise d’in da za’a d’aurashi akai.
A hankali ahankali zai dinga samun sauk’i in sha Allah.
Hakan kuwa akayi dan jikin nashi da kad’an kad’an ya fara gyaruwa…
Ya Usman kuwa shaye shaye ya fara gadan gadan babu kama hannun Yaro, cikin wata uku ya lalace gaba d’aya, tun iyayen basu fahimta ba har suka gane, Ya Usman wanda a daa yake fari tass yanzu kam sai ka k’ura ido tukunna zaka iya tantance hasken fatar tashi, dan sai dai a kirashi da chocolate colour, duk ya yamushe ya fige ya rame over!!! Da aka yi k’ok’arin hanashi sai ya nemi haukacewa, dan basu saniba ashe abun ya shiga jikinshi sosai, idan yazo sha ashe shi over dose ma yake yi!
Shiyasa yanzu abun yake neman tab’a kwakwalwasa, ko zuwa kayi kusa dashi idan bakayi masa ba sai dai kaji duka!! Wannan dalili ya sanya kowa yake tsoron rab’arsa, Sadiya! Kad’ai ce take iya zuwa inda yake, duk da kuwa itama d’in idan taje sai ya mareta ko yayi mata duka amman bata gajiya….ita zata je ta kai mishi abinci ta share mishi d’aki ta wanke mishi band’aki!. Tun Laraba da K’asimu suna hanata suna zaginta har suka daina badan suna so ba sai dan rashin kunyar da take zuba musu a duk lokacin da suka so hanatan kuma ba yadda za suyi da ita.
Watan Madu hud’u yana fama, da ikon Allah a wata na biyar ya warke dama anata samun cigaba a hankali a hankali. Bayan ya dawo gida hankalinshi yayi matuk’ar tashi da halin da yaga Usman shiyasa ya duk’ufa ya dinga yi mishi addu’o’i ta tofi, a hankali a hankali kafin wata d’aya shima Allah ya bashi lafiya amman dai kana ganinshi ka san yana cikin damuwa saboda lokuta da dama ma idan ka shiga sai dai ka tarar dashi yana kuka…
D’agawa K’asimu hankali da Sadiya tayi ne yasa ya taso ya zo wajen su Madu akan maganar ta da Usman d’in.
Da ‘to’ kawai suka bishi amman ko suna hauka baza su
bari su had’a Jini da K’asimu ba….dan a lokacin da Al’Amarin Maryam ya faru shi yafi kowa zak’ewa, kusan shi ya yayata maganar ma har kowa yaji, kuma ya tsaya tsayin daka saida aka hukunta Madu
(Da kyar ma aka barshi ya cigaba da sama a unguwar dan da cewa sukayi Madu sai ya bar unguwar).
Sannan sam K’asimu bashi da hali mai kyau!
Shima Usman duk da alkhairin da Sadiya tayi mishi hakan bai sa ya amince da auren ba, dan shi yanzu sana’a ma zai yi ya tara kud’i ya tafi Madina neman Maryam! Sai ya dawo da ita ko da bala’i ne.
Shiyasa ranar da Sadiya tazo mishi gyara, yaji tausayinta dan sai nan nan take yi dashi, dan haka ya yanke shawarar ‘gara ya fad’a mata gaskiya’ saboda a yanzu yana ganin mutunci ta ko ba komai ita ta kula dashi a lokacin da kowa ya k’i shi.
Zaunar da ita yayi ya fad’a mata cewa “shifa babu maganar aure a tsakaninsu, akwai abinda yasa a gabanshi, in ma saboda haka ne taketa kula dashi gara ma ta daina ta nemi wani suarayin tayi aurenta!. Amman yana mai tabbatar mata da bazai tab’a mantawa da irin alkhairin da tayi mishi ba, har abada!! Ya gode ya gode sosai.”
Kuka kawai yaga ta fashe mishi dashi, da kyar ya samu ya lallasheta, ta tashi ta tafi gida.
Tana zuwa gida ta tarar da Baba Laraba da dillaliya suna hira a tsakar gida da gudu ta fad’a kan Baba Laraba tana rusa kuka, nan ta koro mata abunda Ya Usman d’in yace..
Baba Laraba ce ta hauta da fada tana cewa “idan ita ba mayya baceba to ta hak’ura da Usman.”
Dillaliya ce ta katse su ta cewa Sadiyan “ta tashi ta tafi ta daina kuka” sannan ta matso kusa da Baaba Laraban ta rad’a mata wasu maganganu….
Bayan kwana uku da safe, sai ga Baaba Talatu tazo gidansu Sadiya, da yamma Baba Bashir da Ya Jamilu, duk akan neman auren Sadiya….har wani b’oyewa Modu suke yi. Shi kuwa Madu da yaji labari abun ya bashi mamaki amman daya je ya samu Usman yaga yadda shima ya haukace akan Sadiyar sai kawai ya biyesu aka shiga neman auren….
Wata biyu aka saka dan ana so a had’a dana Ya Jamilu, lokaci yana cika da ikon Allah aka sha biki aka d’aura aure.
Sadiya ta tare a gidanta wanda Baba Bashir da Madu suka bawa Ya Usman d’in anan bayan layi nasu, shi kuma Ya Jamilu dake ya samu sabon posting a Ibadan zai sake komawa yayi shekaru hakan yasanya ya d’auki amaryarsa suka tafi tare amman shima akwai gidanshi anan kusa da na Ya Usman d’in, sanin da yayi ba kwana kusa zai dawo garin ba ya sanyashi zuba haya...........
Bayan shekaru bakwai!.
Madina…
Wani d’an mini duplex ne mai d’auke da d’an k’aramin compound da 3 bedrooms 3 parlours sai kitchen da dining area, Maryam da Abba sukaje gani domin yanaso ya siya, a wannan lokacin apart from work na office yana business kala kala so Allah yayi mishi bud’i.
Bai yi wata k’iba ba saboda ba yanayin k’irarsa kenan ba amman ya murmure yayi haske yayi fresh kana ganinshi kaga hutu, kyawunshi ya sake fitowa .
Tsayawa fad’ad kyauwun da Maryam ta k’ara ma b’ata lokacine.
Suna tsaye a cikin gidan
yana magana da masu gidan da lawyer, ita kuwa in banda cika da batsewa ba abunda take yi, jira kawai take a tab’a ta ta fashe da kuka.
Daman already sun gama magana da ganin gidan a hoto Dan Abban ma ya tab’a zuwa sau d’aya yau ya kawo Maryam d’in ne akan idan gidan yayi mata sai a siya.
Koda ya tambayetan kuwa kawai d’aga kai tayi ba tare da tace k’ala ba.
Murmushi kawai yayi ya juya wajen mutanen…har da lauyanshi suka zo, shiyasa kawai aka fara cike cike bayan an gama suka karb’i keys suka nufi apartment d’insu dan suyi parking.
Kamar jira takeyi suna shiga tun a falo ta fara kuka tace “ita wallahi babu inda zata je kawai ya mayar da ita gida, tunda har yayi kud’in da zai iya siyan gida a nan ai zai iya nema mata jirgi taje Nigeria, kuma kwanaki tayita tambayarshi ‘ko waya yaje’ amma yace mata ‘waya bai je Nigeria ba’, nan kuwa waya yaje, jiya neighbour d’insu take ce mata akwai anty d’inta a Nigeria kullum sai sunyi waya.
Kuma tace landline ma yana iya tafiya sometimes…”
Abba tun yana yiwa rigimar tata dariya har ya daina dan yaga abun nata na yau dagskene, dan tace “wallahi ba inda zata je, ko Yaya ne ya kira.
Tunda yanzu ai duk k’arshen shekara yana zuwa dubasu, kuma k’arshen shekara ya zo dan haka ya taho mata da numbern su Shuwa ita ko waya ne ta samu tayi dasu, kafin taje gaskiya hak’urin ta ya k’are!.”
A b’angaren Abba kuwa, duk zuwan da Yayan nasu zaiyi, sai yayi yunk’urin binsa su koma, amman sai Yayan nashi ya hanashi, saboda ba sau d’aya ba Granpa ya kan gaya mishi ‘in dai yaje Madina suka yi tsautsayin had’uwa da Abba to ya gaya masa yana nan akan bakarshi babu abinda ya chanja’, kasancewar ya san yanayin aikin Yahayan a chan yake kuma yana zuwa akai akai(ambassador) shiyasa ba yadda ya iya ya san dole wani lokacin zasu had’u, kuma ya fad’a ya sake maimaitawa yace ta kan Maryam d’in zai fara.
Duk lokacin da Granpa zai zo Madina kuwa sai ya aikawa Abban da sak’o, hakanan In ba lokacin hajji bane zai d’auki Maryam ya d’au leave a wajen aiki su bar k’asar gaba d’aya..
Volume d’in kukan nata data k’ara ne ya katse mishi tunani.
Kallonta yayi cike da tausayi ba tare da yace mata komai ba
ya hau tunowa shekara biyu da suka wuce shi da kanshi ya rok’i Yayan nashi akan yaje wajen Madu ya kirasu su gaisa da Maryam d’in ko hankalinta zai d’an kwanta.
Hannu bibbiyu Madu ya karb’i Yahaya, amman ga mamakinsa daya ce ‘bari ya kira waya su gaisa da Maryam
sai Madun ya nuna mishi bai ma san wa yake nufi ba!.
Duk hak’urin duniyar nan Yahaya ya bashi tare da bayani da k’ok’arin lalllab’a shi da fahimtar dashi, amman furr!! Madu yace “shi bashi da wata y’a mai suna ‘Maryam’.
Y’a d’aya tak Allah ya bashi a duniyar nan kuma sunanta ‘Bilkisu’.
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
19
Jiki a mace haka Alhaji Yahaya ya tashi ya fito, Madu har wajen mota ya raka shi yana mai sake yi mishi godiyar taimakon da yayi musu shekarun baya da suka wuce na Usman.
Bayan Yahayan ya koma ne ya d’au waya ya shaidawa Abba halin da ake ciki.
Hankalin Abba ba k’aramin tashi yayi ba a wannan lokacin, idan ya kalli Maryam sai yaji gaba d’aya tausayinta ya rufeshi. Dan, in dai ya fahimta to Mahaifinta disowing d’inta yayi kenan!
Duk sai yaji haushin kansa dan a ganinshi shine ya ja mata…
Baya son gaya mata komai a yanzu, yafi so sai ya lallab’a Granpa ya barshi ya koma Nigeria in yaso sai suje tare da shi da Yayansa har ma da Limamin da ya d’aura musu aure ya tayasu bawa Madun hak’uri.
Amman yanzu idan taji ta waya ko ta tafi Nigerian ita kad’ai ta samu wannan labarin
ya san it’ll break her!!.
Da kyar ya samu ya lallab’ata tayi shiru bayan yace mata “idan Yaya zai taho k’arshen watan nan zai zo mata da numbar Madu.
Karshen wata nayi Yaya yazo, kamar kullum tare da matarsa da d’anshi mai shekara bakwai mai sunan Abba ana kiranshi da ‘ASLAM’.
Maryam ita ta zab’a mishi suna Aslam, dan bayan an rad’a mishi sunan YAKUBU, sai
Yayan ya tura musu sak’o yace Abba ya nemi sunan da za ana kiranshi dashi, shi kuma Abba ya cewa Maryam ta zab’a mishi…a wannan lokacin lokacin watanninsu shida da zuwa Madina aka haifi Aslam.
Aslam ya shak’u da Maryam sosai, dan kamar yadda Abba ya fad’a suna yin shekara Yayansa ya fara bibiyar shi duk k’arshen shekara kuwa sai yazo, tun yana zuwa shi kad’ai har ya fara zuwa da Aslam da Mamansa.
Dan Abba d’aga mishi hankali yayi akan ‘yazo mishi da takwaranshi ya gansa.
Ai kuwa ranar da aka fara zuwa dashi Yaron yaga gata a wajen Maryam da Abba, shi yasa ya saba dasu sosai, yana son Maryam over itama tana son Yaron gashi yana da hankali. Mamanshi ma tanada kirki, dukda cewa ta girmi Maryam d’in amman hakan bai hanata k’ulla k’awance da Maryam dan tashi d’aya taji Maryam d’in ta kwanta mata a rai. D’ayar matar Yaya kuwa (amaryarsa) so d’aya aka zo da ita, ita ma ta haihu a lokacin d’anta d’aya sunansa ‘Muhammad (Arshaad) amma bata zo da shi ba. Tunda matar ta zo Maryam d’in ta lura y’ar rainin wayo ce, dan sai wani cika da batsewa take yi sannan tak’i sakewa da Maryam kwata kwata, idan aka zauna ana magana kuwa bata da labari sai na company’s da kadarorin Mahaifinta, bama ta cika yin magana da Hausa ba.! Ita Maryam a tunaninta maybe
ko dan ta san uwar gidan Yaya (Maman Aslam) k’awarta ce shiyasa ta had’a take kishin harda ita.
Sai bayan tafiyar su ne take tambayar Abba “Wai shin
mecece matsalar amaryar Yaya da ita ne? Dan ta fahimci bata sonta.”
Abba bai b’oye mata ba yace “ai best friend d’in Zainab ce (cousin d’inshi da ake so ya aura), sannan y’ar Abokin Granpa ce, shine ma ya had’a auren tun da dad’ewa a lokacin Allah bai bawa Maman Aslam haihuwa ba, a tunaninsu bata haihuwa, to ita kuma Maman Arshaad d’in sai mahaifinta yace “sai ta kammala karatunta wanda saura shekaru uku ta kammala”!
Anyi komai an saka rana, Maman Aslam ita tayi ta k’arfafawa Yaya guiwa a kan auren dan bata son abinda zai jawo matsala tsakaninshi da Granpa kuma ita a nata tunanin ko da gaskene bata haihuwar! Amman cikin ikon Allah ba a yi shekara da yin baikon Yaya da Maman Arshaad ba! Maman Aslam ta haifi Aslam.
Murna a wajen Yaya ba a magana dan yana mugun son matarshi a tunaninshi mahaifin nasu zai janye batun auren.
Sai dai kuma Maman Arshaad tana kammala karatunta aka d’aura aure tare dana d’ayan brother d’insu Yaya Yusuf wanda ya auri cousin d’in Zainab ne shima, ta b’angaren Uwa.”
Maryam ba k’aramin tashin hankali ta shiga ba data gama jin bayanin Abba. Dan sai da Abban yayi dana sanin bata labarin..
Daman chan rashin haihuwa shine main problem d’insu gashi kuma yanzu taji wagga zance!! ‘Kar fa taje itama Granpa yasa ayi mata kishiya!!!’
Da kyar Abba ya lallab’ata amman shi kansa a chan k’asan zuciyarshi hankalinshi ba a kwance yake ba..
Shi bama ta Granpa yake ba, a rayuwarshi bashi da burin daya wuce yaga jininsu shi da Maryam.…..
Tunda su Yaya suka iso aka gaggaisa, Maryam take ta faman kasa kunne amman bataji Yaya yayi mata maganar wata number ba.
Karshe dai cire kunya tayi ta tambaya.
Shiruu, Yaya yayi, kafin ya umarcesu da ‘su basu waje’.
Sai da suka fara tattaunawa shi da Abba tukunna Shi da kanshi ya kirata ya lallab’ata yace “Dan Allah ta k’ara hak’uri sunada dalili…watarana zata je ta gansu, in sha Allah.”
Da kyar dan tana jin kunyar Yaya sosai ta iya tausar kanta
sannan ta hak’ura
Abba kuma ya duk’ufa da adduar ‘Allah ya daura shi akan Granpa’ ......
Bayan Shekara uku!..
Abba yana zaune suna hira da Maryam, Granpa ya kirashi a waya…
Da kyar Abba ya iya d’aukar wayar saboda bai san me zai ji ba.
Ko amsa gaisuwarshi Granpa bai yi ba kawai ya sanar da shi
mahaifiyarshi bata da lafiya, tana son ganinsa…
Har zai yi hangin up, sai kuma yace
“Don’t come here with your wife!!”
Tukunna ya kashe wayar.
Tsabar farin ciki sai da hawaye suka gangaro a idanun Abba.
A hankali ya share hawayen sannan ya d’au waya ya kira Yayanshi, yana d’auka yace “Yaya it works, i’m coming home!.”
“Alhamdulillah” shine abunda Yayan yace kafin murya k’asa k’asa yace “amman fa kayi sauri, dan Granpa yana shirin neman kwararren Likita a dubata!! Kar muje ya gano wani abun.”
“In sha Allah, zuwa nan da dare kuyi expecting d’inmu.” Cewar Abba.
Maryam wadda ke gefen sa ce ta fara tsalle tana murna bayan ya kashe wayar.
Cikin murnar da take yi ne tace
“I wonder why! Bamu yi tunanin wannan plan d’inba all this time. Let me go and start parking….”
A hankali shi kuma yace “let me start the preparations..”
Da murna ta haye sama,
Abba kuwa da farko yayi farinciki amman bai san daliliba haka nan kawai sai yaji baya so su tafi kwata kwata.
Jiki a mace ya mik’e ya fita ya hau shirye shirye…
Basu samu jirgi a ranar ba sai a washegari suka bi jirgin 8:00am.
1:30pm, jirginsu yayi landing a gida Nigeria.
Yaya ne da Aslam a lokacin suka zo d’aukar su, ba gidan Granpa suka nufa ba,direct daga airport d’in suka nufi gidansu Maryam.
Wani farin ciki take ji yana ratsa zuciyarta tun tasowarsu har kawo yanzu barema da taga anzo unguwar su.
Suna shigowa layin su ta fashe da kukan murna, komai ya chanja kamar ba unguwar ba, gidansu da na Baba Bashir an d’aura bene an sake gyarawa da kyar ta iya gane gidajen.
Tun kafin a gama parking ta bud’e mota ta fito da gudu ta shiga cikin gida.
Da wata fara kyakkyawar budurwa ta fara cin karo a tsakar gida tana shanyar kayan makaranta, da wani Yaro kyakkyawa a gefenta yanata zuba mata surutu yana tayata shanyar kayan, a k’alla Yaron zai kai shekaru tara a duniya. Ragowan kayan cikin bokitin ta kwashe sannan ta mik’awa Yaron bokitin ta ce “Jaafar! Ungo bokitinan kaishi chan baya sai kazo kaje ka siyowa Jalila alawarta, naji har ta fara rigima.”
Kalar tausayi Yaron da aka kira da Jaafar yayi sannan yace “Anty Bilkisu nima harda tawa zan siyo ko?”.
Murmushi tayi sannan ta d’an sunkuyo kanshi kamar zatayi ruku’u ta kama kumatunshi kafin tace “Yaya babba!! kai baka san ka girma bako?”.
Rau rau yayi da ido kamar zai yi kuka hakan yasa tace “to shikenan harda kai, sai ka had’a har da na Junaidu shima ka siyo da shi kafin ya zo ya fara zuba mini mita.”
Tsalle Jaafar d’in yayi kafin ya d’auki bokitin ya nufi bayan gidan da gudu yana cewa
“To Anty Bilkisu mun gode ganinan zuwa inje in siyo yanzun nan.”
Maryam mamaki takeyi..kenan wannan Bilkisu k’anwarta ce?? tabbas ga kamanninta nan kuwa! Wannan inda ace a hanya suka had’u ai ba zata iya gane ta ba! Ta girma sosai kamar ba ita ba, ta zama budurwa…
Mamaki sosai take yi, irin wannan girma haka? anya kuwa itace ko dai wata Bilkisu ce? Koda yake shekara goma ai ba nan kusa ba….
D’an matsowa tayi kusa da Bilkisu wadda ta bi bayan Jaafar da kallo tana murmushi.
Kamar tana jin tsoro a hankali ta sa hannu ta tab’a ta tace
“Bilkisu”
Bilkisu jin an dafata an kira sunanta da kamar muryar da ta sani wadda ba zata tab’a mancewa ba yasa ta waiwayowa, aikuwa tana ganin Maryam ta gane ta!! Da sauri ta k’arasa juyowa tace “Ya Maryam!!! Sai kuma ta fad’a jikinta da gudu ta fashe da kuka tace “Ya Maryam kece da gaske…..”
Itama Maryam d’in kuka ta sake fashewa dashi tana d’aga mata kai alamun ‘eh’.
Da kyar ta iya zaro ta a jikinta ta shiga girgiza mata kai tana share mata hawaye alamun tayi shiru, dan farin ciki ma ya hanata magana.
Fitowar Shuwa da Baabaa Talatu yayi daidai da k’arasowar su Abba cikin gidan …
“Karka kuskura ka k’araso nan!!!, ka d’auketa ku koma inda kuka fito bama buk’atar ku!!”
Muryar Shuwa ta daki dodon kunnuwansu.
Da sauri Maryam ta cika Bilkisu ta nufi Shuwa da nufin rungumeta amman tana k’arasawa Shuwa ta d’auketa da mari!
Cikin b’acin rai tace mata “idan kika yi gangancin tab’ani wallahi saina illataki!! Wai Yakubu baka jina ne?! Nace ka zo ka d’auketa ku bar nan tunkafin raina ya b’aci!!!”.
Da mamaki cikin zazzaro ido Maryam take kallonta kafin ta kai k’asa ta fashe da wani marayan kuka gwanin ban tausayi…
Gyaran murya Yayan Abba yayi zaiyi magana nan ma ta katse shi ta hanyar cewa
“Ina ganin mutuncin ka, kar kayi abunda zai saka ni zuba maka rashin mutunci a tsakar gidan nan!”.
Baaba Talatu ce ta fara lallashinta amman Shuwa tayi burus tace “wallahi sai sun fitar da Maryam a cikin gidan.”
Kusan a tare duk suka sauk’e ajiyar zuciya tare da yin hamdala sakamokon jin muryar Madu da Ya Usman a waje, suna k’ok’arin bud’e gate. A tunanin su Madu zai tsawatarwa Shuwa amma koda ya zo, kamar yanda ya gayawa Alhaji Yahaya, haka ya sake tabbatarwa jama’a cewa “shi bashi da wata y’a Maryam, wannan baiwar Allah n kuma”yayi maganar yana nuna Maryam da aketa ce mishi yayi hak’uri ga Maryam ya yafe mata, yace “shi bai tab’a ganin ta a rayuwarshi ba.”
Daga k’arshe abunda Madu yayi musu hatta Shuwa sai da jikinta yayi sanyi, dan Yara ya kirawo yace “su jefe su idan sunk’i fita!!”
Kowa mamaki ne ya kama shi dan wannan kwata kwata ba d’abiar Madu baceba, shiyasa tun kafin a jefe su Ya Usman da Baaba Talatu suka d’aga Maryam suka yi gidansu da ita, dan Madu yace “wallahi ko k’ofar falon shi ba zata k’arasaba.!”
Suma su Abba haka suka juya suka fita, da kyar suka iya janye Aslam wanda yake ta kurma ihun ‘shi sai ya bi Anty Maryam, ba za a barta anan ba!’
Ahaka dai suka tafi suna mamakin abunda suke tunanin zai yi sauk’i, ga yadda ya kasance! Ya zama babban case.
Sai bayan kwana uku tukunna Abba ya samu ya zo yaga Maryam.
Da ta ganshi sai da gabanta ya fad’i hankalinta ya tashi dan gaba d’aya ya rame ya fita a haiyyacin shi a cikin kwana uku kacal!. A take ta hau tambayarshi ‘mai ya faru?!’ duk ta rikice, dukda kuwa itama tana fama da tata damuwar dan y’an unguwa sai yamud’id’i akeyi da ita akan cewa ‘ba aure tayiba, saurayi tabi, yanzu kuma ya gaji da ita ya dawo da ita’.
Sadiya har wani shishshige mata take yi, kasancewar yanzu babu Zainab tayi aure da yaranta biyu ta na Kaduna, kuma duk Yara mate d’insu ba a kusa suke aureba.
Haka nan zata zo ta zauna tayi ta bugar cikinta batasan sarai Maryam d’in ta gane me take yi ba, dan indai ta zo ta tafi to sai taji sabon zance ya fito a unguwa.
Gashi kuma Madu kwata kwata yak’i magana wanda shine ya kamata ace ya ya fito ya gayawa mutane aurene ya kaita Madina, amman sam yak’i cewa komai ya nad’e
hannu yayi shiru sai zaginta akeyi.
Gaba d’aya hankalinta a tashe yake, sai kuma ganin halin da Abbanta yake a ciki ya sake d’aga mata hankali….shiyasa ko duguwar gaisuwa bata bari sunyi ba tahau jera mishi tambayoyi….
Bai b’oye mata ba, nan ya hau kwararo mata bayanin halinda ake ciki
.....Suna tunanin sun yiwa Granpa wayo ashe ya san plan d’insu…da gangan ya bar su suka dawo gida.! Ummi(Zainab) cousin d’insa wadda aka tab’a cewa ya aura ya gudu! Wai itace ta gama phd d’inta yanzu shine za ‘a d’aura musu aure next week .......
Maryam mutuwar zaune tayi da jin wannan sabon tashin hankali, dan kwata kwata kasa motsawa tayi sai da ya tab’a ta tukunna ta fashe da kuka…
Ba k’aramin tashi hankalinshi ya shiga ba….
Tashi d’aya ya hau ce mata “kawai ta d’auko passport d’inta su gudu kamar yadda suka yi da farko.”
Bata kuka shi ba duk maganar da yake ta faman yi sai da ta ji zuciyarta ta d’anyi sauk’i tukunna tace “babu inda zan koma in bar su Shuwa suna fushi da ni haka!
Ka je ka auri cousin d’in naka Abba ba komai ai daman kai Mijin mata hud’u ne,
Allah ya sanya alkhairi.”
Tana gama fad’in haka tayi saurin ce mishi “ya tafi sai da safe.” Tun kafin ya kuma tsayar da ita tayi cikin gida da gudu
tana kuka.
Da kyar Baaba Talatu ta lallab’ata ta fad’a mata halinda ake ciki, ba k’aramin tausayamata tayi ba kuwa, dan har saida ta kusan yin fad’a da Shuwa a wannan ranar saboda Maryam d’in tana cikin gaya mata Shuwa ta shigo, nan itama take jin abunda yake faruwa
b’udar bakin Shuwan sai cewa tayi “Allah ya k’ara.”
Maganar ta bakanta ran Baaba Talatu sosai!! Taya kina uwa zaki na yiwa y’ar wannan maganar?.
K’arshe dai Shuwa bata zauna a gidan ba ta tashi ta tafi.
Tun wannan ranar Abba bai sake dawowa ba.!
Shiru da kad’aici nan suka taru suka yiwa Maryam yawa dan da farko Bilkisu tana d’an lek’o mata ashe itama sauran sati biyu bikinta lokacin da d’in Maryam ta dawo,
Y’an Maiduguri suna zuwa kuwa aka hanata zuwa dan had’uwa akayi har Shuwa aka had’e wa Maryam kai kamar ba ita ta haifeta ba.
Wani abun ma sai ranar da akayi bikin Bilkisu Maryam taga abu dan dangin Shuwa kakaf suma nunawa suka yi basu santa ba, waenda taci
sa’a suka kulata kuwa! Yada
mata magana suka dinga yi.
Da akazo za a kai Bilkisu gidanta har Maryam ta shiga mota Shuwa ta fito da ita a gaban mutane, kunya da bak’in ciki suka sanya ta kawai ta koma cikin gida tana kuka, tun daga ranar kuwa rashin lafiya tace ‘bismillahi’
ko abinci bata iya ci......
Yau kusan sati biyu kenan, da abun ya Ishi Baaba Talatu nan ta kwasheta sukayi asibiti. Suna zuwa bayan y’an gwaje gwaje aka tabbatar da Maryam tana da ciki wata d’aya.
Maryam duk kunyar ta kasa b’oye murnar da take ciki tayi ita kuwa Baaba Taraba kamar tayi mata kuka dan bata sani ba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 32