Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta nufi hanyar kitchen,suka barshi a tsaye a wajen..... Su Auwal suna shiga main parlour ya yi hanyar staircases d’in da yake a hannun dama,da alama ata nan side d’insa yake. “We’re not finished.” Ya ji muryan Mom d’insa. Juyowa ya yi ya kalle ta sannan yace “Let me freshen up first,Ina zuwa . Ya fara hawa stairs d’in da d’an sauri. “What did u do??” Ya ji ta sake tambayar shi. “A peck.” kawai yace mata, da ga haka ya ci gaba ta tafiyar sa ba tare da ya juyo ba. BULAMA✍️ So da Buri Free Book 04 A nan ya tafi ya barta a tsaye kamar wata statue, kana ganin fuskarta ka san ranta a b’ace yake, ita sam! ta kasa gane kan Auwal kwata kwata,bata son halayyar nan tashi, kalli yanzu k’iri k’iri ya had’a uwa da d’anta fad’a, shikuma Arshaad ta tabbata kunyar ta ce ta sanya ya k’i cewa komai,gashi Daddy ya rok’eta akan dan Allah su taru ita da shi su dinga rufama d’ansu asiri…shi kad’ai Allah ya basu su daina yayata wasu halayyarshi da kansu a cikin family, domin kuwa duk ranar da aka yi rashin sa’a granpa ya ji to tabbas kashin Auwal ya bushe…. Tana cikin wannan tunanin ta ji an dafa ta…tana juyowa suka had’a ido da Mijinta Alhaji Yusuf MT murmushi ta yi kafin tace “Daddy yaushe ka dawo?” Sai da ya d’an k’ura mata ido kafin yace “Auwal ne ko?” Murmushin ta sake yi sannan tace”amsa tambaya da tambaya, are we??” Sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya ya yi kafin ya fara magana”Ta windown kitchen na hangoku Ina waya da doctorn ABBA, shine na fita ta k’aramar k’ofa na rufe na tsaya a k’aramin compound saboda bana son Auwal ya ji ni. Kin san yadda suke shi da granpa,ba k’aramin aikin sa bane ya kwashe komai ya fad’a mishi Tunda ya san in dai da granpa a case babu abinda zan iya yi masa.” Shiru yayi da alamun damuwa a kan fuskarsa kafin ya sauk’e ajiyar zuciya yace “Adama akwai matsala fa, don sun sake yin wani fad’an da granpa har ya ma fi na last time, sannan shi kuma ya sakawa kanshi damuwa over gashi yanzu har ya kusan shiga next stage.” “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”shine abinda Mom tace idanunta suna kawo kwallah kafin ta kalle sa sosai tace “To ai ni da ka bari Auwal d’in ya ji ya fad’a ma granpa d’in watak’ila hakan ya sanya shi ya d’an sauk’o daga fushin. Na ga kwana biyun nan ma ai kamar yad’an yi sanyi ai ba kamar da ba,ko?” D’an murmushi Daddy ya yi tukunna yace”babu fa abinda ya chanja daga halin granpa,kawai dai kwana biyun ba a samu wanda ya tab’o sa bane ba shiyasa kika ji shiru…d’azun fa malan iliya ya kirani ya ke ce mini Auwal ya fatattake sa,da na tambayi drivern granpa d’in yace mini shi granpa d’in ne yace a kori mallan iliyan d’azu daga dawowarsu daga meeting,wai dan ya bar bakin main gate ya tafi siyan agwaluma.” “Allah ya kyauta” Shine abinda Mom tace, sannan ahankali tace “wai menene ma to abunda ya taso da fad’an nasu shi da Abban?? daa fa har muna murnar almost 2 years lafiya k’alau tsakaninsu,shima kuma Abban ciwon nasa ko tari babu.” Sai da Daddy ya d’an furzar da numfashi tukunna yace”Wai mafarkai yakeyi da Maryam! da jariri a hannunta,tana kuka tana cewa ya zo ya taimaketa, abun ya kai 3 months yace kullum in ya kwanta sai yayi shinefa ya d’aga hankalinsa… Da farko,Dad ya samu ya fad’a mishi. Shikuma Dad yace mishi ya yi ta addua kawai… shine fa tsabar ganganci kawai ya je ya tunkari granpa da maganar.. akan wai yana so yaje ya ganta,ya tabbatar babu Yaro a tsakaninsu,saboda mafarkan da yake ta yi.” Ba shiri Mom ta zaro ido waje sosai kafin ta yi k’asa da murya tukunna tace”me granpa d’in ya ce??” “Cewa za ki yi me ya yi masa,ba me yace ba! In banda abun Abba kai da ka san mutumin nan yanata fushi da kai for morethan 24 years ko ga miciji ba kwa yi da shi, amma shine zaka kwashi k’afa ka je ka tunkare sa da irin wannan zancen? Ni wallahi Adama nima na fara tunanin ko dai asiri ne matar nan ta yi masa,saboda ki duba kiga yadda he’s willing to risk everything just to talk to her again. Dukda irin bak’ak’en maganganun da ta dinga rubuto masa har da fa threatening nashi da kotu fa ta yi… Daga k’arshe fa idan ta aiko da sak’o ba ya nuna mana! daina nuna mana yayi ni da Dad Allah kad’ai ya san irin maganganun da suke a ciki Shikuma a wannan lokacin kullum cikin bata hak’uri yakeyi yana aikawa. Da kyar granpa ya samu ya rabasu, shine yanzu yake son tada zaune tsaye, shi ko ta jikinsa da lafiyarsa ma bayayi, gashi yanzu granpa ya yi masa horo mai tsanani….. ..Kinga da farko ya sallame shi a duk wani company da kika sani namu a yanzu babu Abba a ciki,sannan ya hanashi share d’inshi. Kuma ya bashi notice akan ya bar masa estate d’inshi kar ya k’ara ganin shi ko y’ay’ansa. Yace kuma duk wanda ya bashi hak’uri sai ya had’u da tsananin b’acin ranshi,hatta gramma.” “Ya subahanallah” shine abunda Mom ta fad’a sannan a hankali tace “bara inje wajen Zainab.” “To” kawai yace mata ya juya ya nufi dining area ya nemi guri ya zauna ya fara zuba abinci, kana ganin fuskarsa ka san yana cikin matsananciyar damuwa. Fitowa ta yi tana zancen zuci ta k’arasa bakin gate sannan ta fita ta k’aramar k’ofa,ta nufi d’aya daga cikin gidajen tana d’an sauri,tana isa tayi knocking,kamar kowanne gida nan ma mai gadi ne ya zo ya bud’e mata,ya gaidata ta amsa sannan ta shiga. Tana shiga ta hango wata k’atuwar moving van ga jakankuna a ajiye a waje da boxes, sannan ana ci gaba da fitowa da wasu. K’ara saurin tafiyar tata ta yi ta nufi hanyar k’ofar shiga main parlourn wadda ke nan a wangale anata shige da ficen kwashe kaya. Da sallama a bakinta ta shiga, tana shiga ta hango wata farar mata zaune a kan 2sitter na d’aya daga cikin jerin kujerun falon,matar ta zabga uban tagumi,kana ganin ta ka san tana cikin damuwa sannan tayi nisa a tunani. K’arasawa Mom tayi kusa da ita sannan ta dafa ta,ganin kamar ma ba ta san ta dafa tan bane ya sanya ta kira sunanta”Zainab!“ Firgigit!! Ta yi ta juyo,suna had’a idanu da Mom kuwa kamar jira takeyi ta fashe da kuka,sannan ta kamo hannayenta duka biyun kafin ta fara jujjuya kai ahankali tana kallonta tace “Adama inata kiranku yau kwana biyar wayanki baya tafiya,komai ya zo mini k’arshe kashina ya bushe!! I never saw this coming!! Shikenan na san yanzu zai yi finding out kum......” Mom bata bari ta k’arasa ba ta yi saurin zare hannunta wanda ta rik’e ta yi amfani da shi wajen toshe mata baki sannan ta juya tana kallon falon tana rarraba ido cikin fargabar kar wani ya jiyoso. Ganin da ta yi ba kowa a falon masu kwasar kayan ma duk sun gama na k’asa sunyi sama ne ya sanya ta kamo d’ayan hannaunta da har yanzu yake cikin nata ta mik’ar da ita sannan ta jata suka nufi d’aya daga cikin d’akunan parlour. Sai da Mom ta tabbata ta saka key,tukunna ta juyo tace “Yanzu menene abun yi?” Share kwallarta Zainab ta yi sannan tace “Granpa ya koremu shiyasa kikaga anata kwash..” “Na sani“ Mom ta katse ta sannan tace “Daddy ya fad’a mini komai.” Shiru Zainab tayi, sannan ta jingina da bango ta d’aga kanta sama ta rufe idanunta a hankali tace “In dai muka bar gidan nan,kin san cewa babu abunda zai hana Abba bibiyar Maryam ko? Saboda ya kasa yarda da takarda har yau,kin san cewa ko a kwanakin baya dama na gaya miki Ina ganin kokwanto a fuskarsa….ita kuma mayyar gashi yanzu har a mafarki zuwar masa takeyi.” Bud’e idanunta ta yi ta kalli Mom sannan ta ci gaba da cewa “4 days ago fa yana tashi yace shi wajenta zai je, ya gaji da wannan mafarke mafarken,da ya je wajen granpa suka yi fad’an nasu da suka saba,dan bai samu an goya masa baya ba shine tun a chan ya zube,sai kwasar shi aka yi ,akai asibiti da shi. Kwanan mu d’aya da wuni bai san inda kanshi yake ba ana fama.” Shiru ta yi kafin ta ci gaba da cewa “Adama granpa shi kad’ai yake iya takawa Abba burki akan Matar nan yanzu ya bashi freedom!!Saboda wannan abun fa da akayi da granpa da mutane ne suke ganinshi as punishment amman a wajen Abba freedom ne. Can u imagine in 2 weeks time fa granpa yace “mu bar gidan nan amman Abba a jiya da sassafe ya kira masu penti aka fara pentin gidanshi na kundila yanzu kinga yau da safe yace mufara parking, na tabbatar ko kammala pentin ba a yi ba. Atleast ai ya jira ya dawo daga asibiti ko? Ya samu ya d’an warware maybe b4 then ma granpa ya saukkk’o.” Murmushi Mom ta yi kafin tace “Haba Zainab,ke har yanzu ba ki san waye uncle d’inki ba ne? If there’s one thing that I’m sure of shine granpa ba zai goge decision d’inshi ba sai dai in ya sassauta,yanzu mafita itace abar nema ba wai wannan dogon labarin ba Dan ba ke kad’ai ba hatta ni da Mammy sai mun raina kanmu idan zance ya fito…. Na san granpa Hates Maryam with passion But what we did is something da bai kamata ace mu bari a kamamu da laifinshi ba!.” Ajiyar zuciya Zainab ta sauk’e kafin ta juyo ta kalli Adama sannan ta kama hannuwanta biyu tace” ki taimakeni… at any cost kar mu bar gidan nan,you always come out with the perfect solution, do something. Har yau ban samu soyyayyar Abba ba,I’ve been trying my best wajen ganin na yi winning nashi kuma na san I’m almost there but in dai matarnan ta dawo cikin rayuwarsa komai lalacewa zai yi.” Shiru Mom ta yi tana d’an tunani ta kusan 5minutes sannan ta yi murmushi tace mata “kawo kunnenki kiji wata magana” Matsowa ta yi sannan ta fara rad’a mata maganar….. Da farko juyowa ta yi ta kalleta da alamun mamaki mamaki sai kuma ta juya ta ci gaba da sauraronta ahankali ta fara murmushi.... “Ummi!Ummi!!Ummi!!!” Suka ji murya ana kwala kira a parlour. Da sauri Zainab ta juyo tace inaga ga su shuraim sun dawo d’azu suka tafi asibiti.” Har ta kai bakin k’ofa ta murza key d’in za ta fita sai kuma ta juyo ta kalla Mom tace mata “Kin tabbata babu matsala?” Murmushi mom ta yi sannan ta d’aga mata kai,alamar’eh.’ Juyawa tayi ta fita itama ta biyo bayanta suka fice a d’akin. Wani Yarone yake shigowa cikin parlourn fari tass da shi kyakkyawa,suna had’a ido da Zainab ya kalli sama yana kallon d’ayan Yaron da ba zai wuce 10 years ba yanata hawa Bene yana kwala kiran “Ummi!!” , da d’an k’arfi ya ce “Sudais!” Da sauri wanda aka kira da sudais d’in ya juyo yana kallon d’an uwanasa wanda juyowar da ya yi ne zai sanya ka fahimci ashe twins ne dan komai nasu iri d’aya ne. Nuna masa Zainab ya yi sannan yace “ga Ummin nan.” Da saurin sa kuwa ya sauk’o ya zo ya rungumeta kafin ya d’ago kai yacee mata “Ummi Abba ya dawo,Dr yace ya warke!suna waje shi da ya Arshaad yanzu zai shigo da shi.” bai gama rufe bakinsa ba kuwa Arshaad ya shigo Shi da wani mutumi kyakkyawan gaske,dogo d’an kakkaura amman bashi da k’iba kwata kwata,fari tas da shi, kyakkyawar fuskarshi cike da tsananin kyau haiba da kwarjini ‘ABBA’ ya rik’e hannun Arshaad d’in na dama shikuma Arshaad d’in ya ruk’o kafad’arshi da dayan hannun for support suna tafiya a hankali,kana ganin mutumin ka san bashi da lafiya. A hankali suka k’arasa Arshaad ya kaisa har kan d’aya daga cikin kujerun parlourn ya zaunar da shi tukunna ya juyo ya kalli su Ummi ya gaida su. Sai da suka gama gaisawa sannan Ummi ta k’araso kusa da su tace “Abba ya jiki? Yaushe aka sallameka? Mai yasa baka kirani ba?” D’an gyaran murya Arshaad yayi, saida ta d’ago ta kalle sa sannan a hankali yace “Ummi Dr yace kar a dameshi fa,and yana buk’atar Hutu,sosai!.” Juyawa ta yi ta kalla gefe ta d’ayan staircase d’in yadda aketa sak’k’owa da kaya ana shige da fice kafin tayi murmushi tace “To Arshaad yanzu daka kowoshi ka ga alamun rashin hayaniya anan d’in? Kalla fa parking aka hau yi yau d’innan gadan gadan,nima Ina dawowa daga asibitin na tarar da su suna jirana a gate da na tambaya sukace wai Abban ne yace su zo su fara kwashe kaya suna kaiwa sabon gida, yanzu saboda Allah idan bai ji da lafiyarsa dan kanshi ko ni ba,ai ya duba Yaran nan”ta yi maganar tana nuna su Sudais tare da share kwallar da ta zubo mata. A hankali Abban ya yi d’an tari sannan ya gyara zamanshi tukunna yace “Arshaad.” “Na’am Abba.” Arshaad d’in ya fad’a cikin girmamawa ya d’an rankwafo ta saitin shi. Sai da ya kuma yin tari sannan yace “Ka duba moving van d’in dake a waje akwai boxes da Ghana most go a ciki ka d’auko empty ones d’in dayawa,ka shiga parlourna da d’akina duk wani abu ka had’a su ka tattare,sannan ka rubuta sunan items d’in da suke ciki a jikin kowanne box da makar saboda kar ya bada wahalar tantancewa idan anje chan. Ka yi sauri idan ka gama za su shiga yanzu su kwashe furnitures, naga har sun kusan gama chan side d’in.” Ya k’arashe maganar yana d’an tari. “To Abba” shine abinda Arshaad yace,daga haka ya nufi waje domin d’auko boxes d’in. Juyawa Abba yayi ya kalla su Sudais sannan yace “kuma ku je ku d’auko ku had’a naku kayan.” Har ya gyara zaman ya d’an jingina ya lumshe idanunsa, sai kuma ya d’ago ya kalli Ummi sannan a hankali yace mata “Za ki bimu ko a nan za mu barki!” Yunk’urawa ta yi za ta yi magana ranta na sake b’aci, Da sauri Mom wadda ke a bayanta ta rik’o hannunta ta d’an matse alamar ta yi shiru. Shurun kuwa ta yi sannan Mom ta yi gaba tace “Abba sannu da jiki, Allah ya sa kaffara ne. Bara muje saman in taya ta had’a kayanta. Idan kana buk’atar wani abu muna sama sai ka kiramu a waya....” D’aga kanshi ya yi alamar ‘to’ sannan ya mayar da idanunsa ya lumshe ya koma ya jingina a jikin kujerar. SHARE PLS. BULAMA✍️ So da Buri Free Book 05 Jan hannunta Mom ta yi sannan suka yi sama,suna shiga d’akinta tace “Adama ba fa inda zanje sannan suma babu inda za su je.” “Na sani” Shine abinda Mom tace sannan ta fara dube dube kamar tana neman wani abu. Drowern gaban mudubi ta kai hannunta ta bud’e,aikuwa ta ci karo da abinda take nema..da sauri ta d’auko littafin da ta gani da biro sannan tace “oya d’auko mini takardar gidanki wanda ya baki in kalla signature da wani note haka da ya tab’a rubutawa.” D’an tsayawa Ummi ta yi tana kallon ta da alamar tsoro a fuskarta. Ganin haka ya sa Mom ta kawo gabanta ta tsaya sannan tace “I’m just trying to help,ba mu da ishesshen lokaci,ki daina dogon nazari. Besides har yanzu ukune akan ki so don’t worry about one ballantana ma bashi da masaniya,so babushi a lissafi. Kowa ya sani a estate d’innan kece weakness d’in granpa,ki duba ki ga abubuwan da yake yi just to make sure u stay happy..I can assure u ba zai bari Abba ya tafi ko Ina ba idan ya ga wannan.” tayi maganr tana nuna mata takardar da ta yaga daga jikin book d’in. Shiru Ummi ta yi kafin tace “Adama I love my husband, banaso in shiga tsakaninshi da mahaifinsa..” Wannan karon tsaki Mom ta yi sannan tace”Zainab kin fara bani haushi wallahi zan yi tafiyata, shiga tsakani kuma na nawa?? Waye ummulaba’isin fad’an nasu?sai da abu ya zo gangara za ki fara tunanin tsame hannunki? To bari kiji! ta inda akabi aka hau ta nan ake sauk’a sannan na san Dr Abba farin sani If things get out of control zan yi paying nashi ya maka masa case na memory loss, a ce yayi for a day ne, a time din kuma yayi ta misbehaving,sai mu ce a lokacin ne yayi shi kansha kenan bai san yayi ba. Dan mutumin da ya kwana ya wuni bai san inda kansa yake ba ai zai yi morethan this,kuma babu wanda ya isa ya musa.” Da sauri Ummi tace”ok ok”sannan ta nufi wardrobe d’inta ta d’auko key a k’asan tulin kayanta sannan ta saka key d’in a jikin wani d’an k’aramin locker wanda yake nan ata k’asan kayannata ta murza mukullin ya bud’u. Wani suitcase ta d’auko ta yo kan gadon da shi,a tare suka hau bincikawa har sai da suka d’auko wani file da wata envelope. File d’in takardun gida ne, envelope d’in kuwa da suka bud’e ta wani had’add’en rubutu ne ya baiyana a cikin da alama wasik’a ce . Zama Mom ta yi a kan gadon sannan ta saka wannan wasik’ar a gaba ta yi shiruu…ta kai kusan 2 minutes tana k’are mata kallo kafin ta ajjiye ta a gabanta tukunna ta hau rubutu akan wannan blank papern data yago….exactly handwriting d’in irin na wannan wasik’ar takeyi. Ta d’auki y’an mintuna tana rubutawa kafin ta d’auki dayan file din ta bud’o dai dai wajen signature ta kalla da kyau sannan ta ajiye ta yi irinta a k’asan takardaar da ta gama rubutu a kai. Tashi tayi daga kan gadon sannan ta juyo ta kalli Ummi tace mata “Done!!” Mik’a hannu Ummin ta yi ta karb’a ta karanta sannan ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “Yanzu ta Ina zan wuce?? kin san fa yana falo.” “D’auko mayafinki” inji Mom. Cikin wardrobe d’inta ta bud’e wajen mayafai, sannan ta jawo abinda hannunta ya kai kai . Warewa ta yi tana shirin saka hijabin Mom tace a’a bani nan zan saka a cikin nawa maya fin in fita in yaso sai ki sak’k’o daga baya ki yi kamar kin shiga kitchen,ni kuma zan jiraki a k’aramin compound ta baya,sai ki fito mu wuce.” Har ta juya za ta fita,sai kuma ta dawo ta k’ara rad’a mata wata magana sannan ta fice. Yadda Mom d’in ta tsara hakan kuwa akayi… Bayan sun fita daga gate d’in gidan suka nufi na granpa. Suna zuwa daniel ya gaidasu suka shige suka isa k’ofar main parlor. Suna shiga kamar kullum sukaga ba kowa,shiruu sai k’arar ac Ganin hakane ya sa suka nufi kitchen a tunanin su ko za su ga granma ta yi musu iso,amman nan d’in ma ba su sameta ba,sai masu aiki. Ganin suna b’atawa kansu lokacine yasa Mom ta d’auko wayarta, ta kira gramma,bugu biyu ana ukun ta d’auka. “Assalamu alaiki, Adama.” Aka fad’a daga d’ayan b’angaren. Cikin girmamawa mom tace “Ameen wa alaiki assalam,Ina wuni gramma” “Alhamdulillah” Shine abinda gramma tace. Cikin ladabi Mom tace”daman yanzu Zainab ta zo ta sameni akan wata magana,shine muke son ganin granpa,ban sani ba ko yana nan?.” “Yana nan.”Ta ce,daga haka ta katse kiran. Kusan mintuna talatin suka yi a kitchen d’in, har sun fara gajiya sukaji k’arar bud’e k’ofa. Da sauri suka fito a kitchen d’in dai dai k’ofar da take kallon kitchen d’in aka bud’e sosai wata farar tsohuwa ta fito,bata da tsayi sosai amman tanada k’iba,idanunta sanye cikin medicated eye glasses, tana sanye cikin wata royal blue d’in atamfar super xclusive ta yi d’aurinta irin na tsoffi. A hankali take tafiya tana tunkaro k’ofar kitchen d’in tana yin mitsi misti da idanu alamun so take ta fahimci su d’inne a wajen domin kuwa dudda glass d’in ba kasafai take iya hango abu idan yayi nesa sosai ba. Gane hakan da suka yi ne ya sanya suka yi saurin k’arasawa inda take sannan suka d’an rissina suna sake gaida ita. Cikin kulawa ta amsa sannan tace “ina fata dai abu mai muhimmanci ke tafe da ku ba shirme ba,dan kar ku je ku yi ta shiririta,kun san ba yawan son surutu yake ba,yanzu hakan ma da kyar ya yarda zai ganku..” Takardar hannunta kawai Ummi ta mik’a mata. Kallonta gramma ta yi sannan ta sa hannun ta karb’a takardar ta fara dubawa….gyara glases d’in idanunta ta yi da kyau cikin zaro ido kafin ta d’ago ta kallesu sannan tace “Shi Yakubun ya baki wannan???yaushe!??” K’asa Ummi ta yi da kanta sannan a hankali tace “Shekaran jiya” Cikin fad’a gramma tace”kuma to me kika tsaya yi tun shekaran jiya baki zo nan ba? Ai cewa yayi ki tafi wajen iyayenki,ko kina da iyayen da suka fi mu ne?”. Da sauri Ummi ta girgiza kai tana share hawaye. Cikin tausayawa,gramma ta kamo hannunta ta rungumeta tana bubbuga bayanta,sai da ta yi shiru sannan tace su je wajen granpa d’in. Ta cikin parlourn da gramma ta fito suka shiga,suka bi ta wani had’add’en staircase suka isa wani tafkeken parlour sannan suka sake bin bene kafin su iso wani had’add’en parlour. A tsaye suka hangosa gaban wani k’atoton glass wanda gaba d’aya bangon wajen glass d’in ne ya cinye…ya juya baya yana kallon glass d’in wanda ta cikin k’atoton glass d’in kana iya hango har compound d’in estate d’in. Waje gramma ta nuna musu sannan ta k’arasa gabansa ta mik’a mishi takardar,kafin ahankali tace”ga abinda yake tafe da su”. Ya kusan 2 minutes tukunna ya ce “Read it loud” Cikin nutsuwa grmma ta fara karantowa. “Ni Yakubu Umar Farouk mai turare, na saki matata Zainab Umar Farouk mai turare,saki d’aya…dalilin kuwa Ina gudun shiga hakkin aure domin na kasa bata kulawar da ta kamata da waje a zuciyata ta koma gidan iyayenta ta ci gaba da zama,nima zan tafi nawa gidan, idan ta samu miji ta yi aure.” Shiru kakeji d’ip! Kamar ba halitta a parlourn. Da farko tari Ummi ta fara a hankali,chan kuma sai ta farayi da k’arfi har da kamar kakarin amai kafin a hankali ta sulale daga zaunen da take akan kafet ta kwanta a wajen. “Ya subahanallah jini!!!” shine abinda suka ji Mom ta fad’a….da sauri gramma ta yo kansu,itama tana zxuwa ganin alamun jini jini a cikin bakinta yasa a rud’e ta ce “Adama mai ya faru?innalillahi wa inna ilaihirrajiun, maza d’auko ruwa ga firij chan ki zo ki yayyafa mata…” Ruwa aka d’auko aka fara yayyafa mata amman a banza sai ma jinin da yake ta biyo yawu yana dalala a k’asa….da sauri gramma tace maza kira wani a cikin samarin nan ya zo a taimaka a kaita asibiti,da sauri mom ta mik’e sai kuma ta tsaya tace “gramma duk basa nan na manta,amma d’azu naga Dr ya zo duba Abba,in kirashi??” Da sauri gramma tace “Eh kirawoshi,Allah ya kawo sauk’i ma ai.” Nan ta fita gramma kuma ta cigaba da jijjiga Zainab tana tofa mata addu‘o’i. Cikin mintunan da basu gaza ashirin ba Mom ta dawo Dr na biye da ita,suna zuwa aka gyara wa Ummi kwanciya anan kan kafet din Dr ya shiga duba ta da kayan aikin da ya shigo da su. D’agowa ya yi ya kalli Mom sannan yace”tun yaushe ta fara?” “Bata tab’a suma irin wannan ba gaskiya,sai dai tarin jini kuma ba ya zuwa sosai kamar na yau.” “Tun yaushe ta fara?” Doctor ya sake jeho mata tambayar ba tare da ya kalleta ba dan ya duk’ufa ya tarkata hankalinshi duk a kan Ummi burinsa kawai ya ga ta farfad’o. Kwanaki ta yi a gaba na har sau biyu,na yi mata magana tace “wai ta je absibi ance ba komai.Yau kuma sau uku kenan har da wannan,shima da naga ta yi ta sakeyi na tamabayeta tace mini ba komai fa.” “Unhm“ Shine abunda Dr yace yana zuk’o wani ruwan allura sannan ya saita jijiyan hannun Zainab d’in ya juye mata shi a ciki ya ci gaba da bata taimakon da ya kamata. Bayan wasu y’an mintuna… A hankali take bud’e idanuwanta waenda suka yi jazir…da sauri gramma ta k’araso gabanta ta fara k’ok’arin mik’ar da ita tanata faman jera mata sannu,Allah sarki

Chapter 3 of 32