Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
like her, ba!. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 34 A meeting point d’in da suka yi zasu had’u… A nan suka tarar da Khadijahn tana jiransu. Ba tare da b’ata lokaci ba Aslam ya zaro blank check ya mik’a mata yace “Ta rubuta ko nawa take so muddin ta san zata fad’i gaskiyar abunda ta sani game da case d’in Arshaad.” “Mai yasa kake so ka sani” Ta yi musu tambayar tana mai kallonsu. Fahimtar da Aslam yayi za ta yi taurin kai ne ya sanya kawai yace mata “Ko ta fad’a ko kuma ya d’auke check d’in ya hanata kud’in kuma dole in za a shigo court sai anje da ita dan sunanta ya fito! Dan Auwal ya ambato sunanta a cikin case d’in.” Cikin tsanannin tashin hankali da b’acin rai tace “Auwal d’inne ya ambato sunana? Sannan abun naku har da court daman?”. Arshaad ne, yayi mata bayanin komai sannan ya d’aura da cewa “ina da recording d’in wayar da muka yi da Auwal lokacin da ya ambato sunanki a ciiki” Saboda haka ki taimaki kanki ki taimaki Auwal ta hanyar fad’in gaskiyar iyaka abunda kika sani. If not zata rufta da ke da Auwal d’in, duk ranar da aka zauna a kotu…. Domin kuwa shi Auwal yana tunanin yayi mini sharri! Sai dai kuma bai san iyaka wannan evidence d’in na voice call ya isa ya d’auresa tamau!! Kuma dole abun ya shafe ki. Jikinta har rawa yake yi tace “Dan Allah….zan gaya muku komai amman kar ku gayawa Auwal ni ce na fad’a!” ….Nan ta hau zayyano duk abunda suke da buk’atar ji da zai taimaka wajen wanke Arshaad! Daga k’arshe tace “gobe da sassafe su had’u a nan, zata kawo wasu takardun duk akan bayanan da zasu taimaka wajen wanke Arshaad d’in ne..” Sannan ta sake rok’ar su akan dan Allah dan Annabi kar su bari Auwal ya san itace ta fad’a musu, dan in dai ya sani to sai ya koreta a aiki bayan wulak’ancin da Allah kad’ai ya san kalar wanda zai yi mata… Sanann su yi k’ok’ari kar a shiga court kar sunanta ya fito dan ta san nan ma zata samu matsala da CEO! Bayan an yanke mata hukunci kuma kora ta biyo baya.. Da wannan aikin ta dogara su uku ne a family d’inta Ita , mamanta, sai k’anwarta Babanta ya dad’e da rasuwa ita take providing a family d’in su taimaketa! Dan Allah. Ta k’arashe maganar cikin had’e hannunwanta alamun rok’o!. “Thankyou Khadijah!.” shine kawai abunda Aslam yace mata daga nan ya mik’e tsaye yana cewa “Nayi miki alk’awarin ‘sunanki ba zai fito ba’.” Kafin yace “Rubuta kud’in da kike buk’ata za mu wuce. Da farko cewa tayi su barshi kawai. Sai da Arshaad yace “Ai alk’awari suka yi mata tun farko kuma ta fad’i abunda sukeson ji don haka dole su cika mata alk’awarin da suka d’auka.” Tukunna ta d’auki blank check d’in ta rubuta 300k! Sukayi signing mata suka wuce… Suna yin gaba Aslam ya zaro wayarshi a gaban aljihun rigarshi ya katse video d’in da ya saita tun kafin su fito daga mota. Basu samu sun je wajen Auwal a ranar ba! Saboda busy d’in da Aslam da Abba suka shiga har ma da Arshaad dan so suke su yi su gama shirye shirye su samu su bud’e company d’in nasu soon. Around 9:00 pm washegarin ranar bayan kowa ya dawo a office an yi dinner da isha suka nufi gidansu Auwal.. Da Mom suka fara cin karo a k’asa tana waya. Faram faram ta karb’esu bayan y’an gaishe gaishe Arshaad yace “Auwal yana nan?”. “Eh, yana sama har ya kwanta ma. Wai ya gaji yau sosai.”Ta basu amsa, a tunaninta za su bari ne amman sai taga Aslam ya mik’e yana cewa “yana nan a side d’inshi na daa har yanzu ko?” “Eh” ta sake basu amsa. “Muje” Aslam ya cewa Arshaad, daga haka suka nufi saman. Mom ji take yi kamar ta bisu ta lab’e taji meyene ya kawo su dan tabbas ta san ba lafiya ba! Tunda dai Auwal ba shiri yake yi da either of them ba. Tana shirin mik’ewa Daddy ya shigo! Kamar ta kurma ihu haka taji, haka nan tana ji tana gani ba yadda ta iya…ba dan ta so ba ta hak’ura da lab’en data shirya yi. Kamar yadda Mom ta fad’a musu, Auwal d’in har ya kwanta! Har cikin bedroom d’inshi suka shiga Arshaad ya lalubo switch ya kunna!. Baccin nasa bai yi wani nisa ba shiyasa yayi saurin farkawa yana mitsi mitsi da idanuwa. Da mamaki yake kallonsu kafin ya mik’e ya zauna a kan gadon yace “Lafiya! Zaku tashi mutum yana bacci? Infact baku san babu kyau invading privacy ba?”. Murmushi Arshaad yayi ya k’arasa inda yake ya zauna a gefenshi kafin yace “Ai baka taki zaman lafiya da kwanciyar hankali ba! So ka cire bacci a agenda d’inka for now and start worrying about yourself.” Tsaki kawai yayi ya fara k’ok’arin komawa ya kwanta. Dai dai nan Aslam ya k’araso yayi masa playing video d’in da suka yiwa Khadijah jiya ba tare da ta sani ba. Jin muryar Khadijah ya sanya ya d’ago yasa hannu ya karb’a dan da farko k’in kallon wayar ma yayi. Sai da video d’in ya k’are tukunna Aslam ya jawo stool ya zauna a kai yana facing Auwal d’in! A hankali ya fara magana “Auwal da kai da Arshaad ba ku da bambanci a wajena amma i have to sopport wanda yake da gaskiya! Ka taimaki kanka ka taimaka mana mu kashe case d’innan if not kai kanka ka san ba zatayi maka kyau ba! In ka yarda kayi sopporting d’in mu Ni na san ya yadda zan yi in rufa maka asiri In rufawa ita Khadijah asiri Case d’in ya mutu ba tare da sunan either of you ya fito ba! Amman if you try to act stubborn and rude to bani da wani choice d’in daya wuce In saki video d’innan! And the first person da zan turawa shine ‘Granpa’ Followed by su Dad Daga nan su Mom After them kuma har a MT estate da company sai kowa yaji kuma ya gani! Wallahi. Shiruuu, Auwal yayi yana lissafi… Duk ta inda ya duba ya zagaya ya zagayo bashi da mafita! Dan haka kawai ya yanke shawarar hak’ura. Amman fa sai ya gasawa Aslam aya a hannu wallahi! Zai san ya tab’o shi.. But first zai bari komai ya lafa zuwan nan da kamar 2 ko 3 months haka A lokacin zai san wayene Auwal! And he will make sure yayi takunshi da kyau ta yadda ba za su samu damar kamashi ta ko wacce hanya ba…. “Kai muke jira!” Ya ji muryar Arshaad. Ajiyar xuciya ya sauk’e sannan yayi murmushi ya d’ago ya kalli Aslam kafin yace “Selfish bitch!! Kar in sake jin kace ‘da ni da Arshaad d’aya muke a wajenka!’ Bana son munafurci gara kawai ka fito a mutum ka bi bayan brother d’inka ka bar yin wasu kwana kwana..” Mik’ewa kawai Aslam yayi ya cewa Arshaad “muje! He’s not ready to negotiate.” Sai da Auwal ya runtse idanunsa da k’arfi! Yana mai jin takaicin abunda zai fad’a, tukunna a hankali yace “Truce accepted!” Murmushi Aslam yayi ya juyo yace “Good boy! First of all.. Zaka kawo takardun da kace ka had’a na wasu laifuffukan da zaka sake d’aurawa Arshaad idan an je court. Sannan Akwai papers d’in da nake buk’ata ka yimin zuwa nan da 24 hours.. ( nan ya zayyano mishi abunda takardun za su k’unsa) “Zan had’a tare da na Khadijah In kaiwa Granpa Once yayi accepting, shikenan case ya mutu! Daga nan sai ka sameni ni kuma zan goge video d’innan a gabanka har wanda na tura a laptop duk zan goge.” “Sounds fare” Shine abunda Auwal yace daga nan ya juya ya kwanta yace “Ku kashe min bulb in kun tashi fita.” Har zasu wuce Aslam ya juyo yace “Ina so kayi promising d’ina ‘ba zaka yiwa Khadijah komai ba’ Saboda na riga nayi mata alk’awarin kareta ta ko wacce hanya.” Sai da Aslam ya kira sunanshi tukunna yace “To!!” Ba tare da ya juyo ya kalle su ba. Arshaad ne ya fara ficewa sannan Aslam bayan ya kashe mishi bulb d’in ya jawo k’ofar d’akin, suka wuce. Suna fitowa a d’akin Arshaad yace “Thankyou! Case zai mutu ba tare da sunan kowa ya b’aci ba.” Murmushi Aslam yayi sannan yace “ka fahimceni kenan.. Gara hakan ai dan ni a ganina idan muka had’ashi da Granpa rigima ce babba da Allah kad’ai ya san k’arshenta. Ni da in da ace za a bi ta tawa To da an bar maganar bada company d’innan a mutum d’aya da Granpa yake son yi! Rivalry kawai hakan zai janyo da bitterness d’in da Allah kad’ai ya san k’arshen shi.......” Da safe kamar yadda Khadijah ta fad’a, haka ta kai takardu. Auwal ma 24 hours suna cika ya cika alk’awari….. Da mamaki a kan fuskokinsu suka dinga kallon sharrin da Auwal ya k’ukk’ulawa Arshaad kala kala! Wanda tabbas idan takardun suka fita to da wuya in Granpa ba zai saka Arshaad ya k’are rayuwarsa a jail ba! A take suka yaga takardun sannan Aslam ya had’a da na wajen Khadijah da ragowar takardun daya had’a yake kuma buk’ata Ya nufi wajen Granpa da su. Sai da Aslam ya tabbatar Granpa ya yarda kuma ya hak’ura sannan case ya mutu! Tukunna ya dawo ya goge videos d’in Khadija a gaban auwal kamar yadda yayi alk’awari.. Sai dai kuma Auwal d’in bai kai ga barin wajen ba ma Message d’in Granpa ya shigo wayarshi../ “He’s not serious, ba shi da lura he’s reckless!! Shiyasa aka samu har kud’i masu yawa haka suka shiga account d’in Arshaad instead of account d’in turawan da ya kamata ace an tura.. Gashi yanzu sun yi loosing contract d’in! Saboda haka gobe yana zuwa office ya kwashe kayanshi daga office d’in md ya maida ground floor.....”. Da kyar Auwal ya iya jan k’afafuwan shi yana ganin dishi dishi ya fice daga side d’in nasu ba tare da ya cewa d’aya daga cikin su uffan ba! Ikon Allah ne kawai ya maidashi gidansu. Yana fita ba da dad’ewa ba Message ya shigo wayar Arshaad shima.. ‘An maidashi aiki But ya samu demotion kamar Auwal A ground floor zai koma aikinshi.’ Murmushi yayi bayan ya gama karantawa, ya turawa Granpa d’in “Thankyou Granpa A lot.” Sannan ya mik’awa Aslam wayar yana mai cewa “Da babu gara ba dad’i.” Kwata Kwata Aslam bai ji dad’in hakan ba! Ganin haka yasa Arshaad d’in yayi ta mishi nuni da ‘daman ya san sai an hukuntashi ko da ace an yafe mishi, so shi a ganinshi babu wata damuwa.. Dama shi burin shi case ya mutu kuma ya mutu! Dan haka Alhamdulillah Ya san k’ark’ari a rage mishi salary wanda shi salary d’in da ake biyan shin ma kamar bonus ne saboda company d’in shine ja baya a harkoki daban daban d’in da yake yi wajen kawo mishi kud’i! Kuma yanzu ya san tunda a ground floor yake to duk inda 3 tayi ya tashi! Hakan zai bashi dama wajen focusing a kan ragowar businesses d’in da yake yi…’. Sai da yaga Aslam d’in ya fahimceshi tukunna ya kyaleshi haka suka fad’a wata hirar. Tun a Daren ranar Granpa ya gama deciding sannan ya rubuta ‘Kujerar md ta koma hannun Aslam!’ Daga nan ya kira Baban Auwal yace “ya ci gaba da managing branch d’in ‘Mai Turare’ na Uk ko wata wata ne ya dinga lek’awa saboda ya san a anan ma akawai wani company d’in su daban da yake kula dashi. Tunda yanzu Aslam ya dawo nan to shi zai zama MD na nan, saboda Arshaad da Auwal wawaye ne basu san aiikin ba! Sannan baya buk’atar Aslam d’in ya sake komawa UK! Ya isa haka.. Maganar Mahaifiyarshi kuma in shaa Allah yana sa ran dacewa dan yayi booking appointment da ‘best neorologist in the world’ za a kaita ta ganshi, in shaa Allah akwai alaman nasara.. So ayi arranging papers na change of position d’in da aka samu da office In shaa Allah gobe shi da kanshi zai yi introducing Aslam as their new MD na wannan branch d’in! Next week kuma sai suje UK d’in nan ma a yi y’an tsare tsare………” Yana gama fad’an haka suka yi sallam bayan Baban Auwal d’in ya nuna mishi fahimta da amincewar hakan 100%. Yana ajjiye wayar ya kasa juyowa ya kalla inda Mom take dan tun lokacin da ya fara wayar yaji ta mik’e ta zauna a kan gadon. Sarai ya san ko bata ji komai ba to ta fahimci wani abun! Bai san ta ina zai fara yi mata bayani ba, dan in dai a kan Auwal ne to gaba d’aya yanzu notikan kanta za su kwance! Shi kuma har ga Allah bai shiryawa hakan ba cikin daren nan, kanshi ciwo yake yi besides kuma yana tunanin rik’e manyan company’s har biyu! Dan bayan ‘Mai Turare’ company na oils d’in da yake rik’e dashi is the second largest a family d’in…. Yana cikin wannan tunanin ya ji lallausan tafin hannunta a kan kafad’ar shi. Shiruuu, yayi bai kulata ba, hakan ya bata daman fara magana.. “Ka san dai na fahimci akwai matsala, ko? Rashin sanar dani da yin shirun ka sake saka zuciyata cikin zullumi zai yi! Dan Allah ko menene komai d’acinsa ka fad’amin, please Mijina.” Tayi maganar tana amfani da tafin hannunta wajen shafashi. Juyowa yayi gareta ya kamo hannun ya rik’e sannan ba tare da b’oye b’oye ba, ya hau fad’a mata yadda suka yi game da ‘zai koma MD na branch d’in Uk, tunda Aslam ya dawo..shi kuma Aslam d’in an bashi MD na nan!’ Tun kafin ya k’arasa rufe bakinshi tace “Auwal fa?” Ajiyar zuciya ya sake sauk’ewa kafin yace “Ya samu demotion! Da shi da Arshaad Granpa yace ‘they are not capable’….. Mom wadda ranta ya b’aci hankalinta ya tashi bata san lokacin da ta manta da duk wani karatun kissar ta ba tace “Zancen banza kenan!!! Daga bakin mutanen banza, wallahi ba zai yiu....” Tsawar da Daddy ya daka mata ce ta sanya ta d’an seseta hankalinta ya d’an dawo “Bana son raini fa Adama!!!! Ni ne mutumin banzan ko mahaifina?? Hukuncine ya riga ya yanke kuma dole uban kowa ya bi! Idan kuma kina da ja na tabbatar kin san inda zaki iya samunshi. Ai tun Auwal bai kawo haka ba! Tun bai gagaremu ba nake gargad’arki… Yanzu gashi anzo gab’ar da bamu da wani choice d’in da ya wuce muna ji muna gani mu dinga take laifukanshi muna b’oyewa saboda rufun asirin mu baki d’aya! Ko kin san irin kalar b’arnar da yake tafkawa a office kuwa?? Baki da abinda kika d’orasa a kai tun tasowarshi kawo yanzu sai ‘ya bi duk wata hanya da zai bi don a Mallakaa mishi Mai Turare!’ Ko kina tunanin ban san me kike yi ba? Baki damu da kare mutumcinshi ba! Baki damu da d’orashi a kan addini ba! Baki damu..baki damu…baki damu ba da yawa, Adama!!!. Tarbiyyar ma ba bashi kika yi ba instead ina yi kina warware min! Gashi yanzu ya addabeni ya addabeki kuma kwad’ayin Mai Turaren da kike yi…due to yadda kika maidashi ya sanya yana abu kamar psyco psyco gashi yanzu instead of daga MD ya wuce CEO gashi an maidashi ground floor!!! Wa gari ya waya kenan?? Daga 10th maimaikon ya k’are yin sama amma instead ya dawo ground flour! Kinga garin neman gira an rasa ido……” Hakanan Daddy yayi mata tatass! Kamar ya ari baki.. Mom kam kasa danne bak’in cikin ta tayi haka nan ta dinga kuka wiwi har da majina kamar wata k’aramar Yarinya.. Ganin haka ya sa Daddy ya d’an sassauta muryarshi yace “Kiyi hak’uri Adama, da Auwal da Arshaad da Aslam duk abu d’aya ne! Koma waye aka bawa MT duk dai y’ay’an mu ne.. Kuma daman ni na dad’e da fahimtar Aslam d’in yake son bawa ko duba da d’umbin soyayyarshi a zuciyarsa da kuma tausayinshi… Auwal ya rainaki amman still mu muka haifeshi! Lokaci yayi da zaki fara nuna mishi dai dai duk d’acin ta da kuma akasin haka. Idan muka zuba ido a kansa especially yanzu da yaga Aslam ya dawo Ina jiye mishi kar yaje yayi wani shirmen da za a kwace gaba d’aya shares d’insa a duk k’ananan company’s d’in sannan kuma a koreshi gaba d’aya! Kina gani dai irin tarin soyayyar da Granpa ke yiwa Abba! Na san duk da abunda ya shiga tsakaninsu har yanzu yanajin shi a rai amma ki duba kiga yadda ya rufe ido ya tsameshi a kan komai yanzu.. Tou har gara Abba dan yanzu shirin ma bud’e construction company suke yi shi da Aslam Kisa a ranki Auwal aka yiwa abunda aka yi wa Abba Shin wacce sana a kike tunanin zai yi?? Gashi girma ya zo mishi, lokacin tara Iyali yayi.” Shiruuu, Mom tayi ta nutsu ta bama Daddy dukkan hankalinta tana sauraronshi.. Ba k’aramin dad’i hakan yayi mishi ba kuwa, dan haka ya gyara zama yaci gaba da yi mata nuni da abinda ya dace da wanda bai dace ba da kuma yadda zasu had’u su gyara d’ansu tare da neman had’in kanta… Sun dad’e suna tattaunawa ganin ta aminta da hakan ga kuma nadama k’arara a kan fuskarta dan har hak’uri ta bashi tare da alk’awarin yin amfani da shawarwarinshi.. Hakan yasa ya janyo ta yayi hugging d’inta zuciyarshi fes! Cike da farin ciki, ba abunda yake buri a yanzu sama da ya ga Auwal d’insa ya nutsu ya zama kamar su Aslam shima. A haka ya jata suka kwanta yana mai karanto addu’o’in bacci ya shafe jikinsu dashi, yana d’an shafa gashin kanta har bacci yayi awon gaba da shi. Ganin da Mom tayi yayi bacci yasa ta share hawayen da suka zubo mata sannan ta mik’e ta zauna ta galla mishi wata uwar harara a ranta tace “Sakarai kawai! Ana nuna maka Annabi kana runtse ido, ko su y’an uwan naka dakake ta tak’ama kana nuna y’ay’ansu nakane bari kaga ranar da za a bawa wani Mai Turare a nan zaka sha mamaki! Infact shekaru ma suna ja nan zaka fahimci da mai shi ake yi!”. Pillow taja ta saka a bayanta sannan ta kishing’ida a kan gadon dan ita bata ga ta bacc ba! Ai kuwa bata yi minti talatin ba idea ta fad’o mata! Murmushi kawai tayi sannan tace “Alhamdulillah” Tana mai ayyanawa a ranta ‘Gobe! Zata je ta samu Maman Aslam ta sanar da ita Aslam ya dawo! Bayan ta san yadda tayi ko ta halin k’ak’a ne ta d’auki video d’in Aslam da Arshaad ko dai wani a cikin estate d’in ba tare da an farga ba, ta yadda Maman nasa zata fi yarda idan ta gani.’ Juyowa tayi tana kallon Daddy wanda yake ta baccinshi.. Murmushi tayi tace “Yi baccinka Mijina! Auwal shi ke da Mai Turare, Bi‘izinillahi Ta ala.” Auwal, shi kam yana chan abun duniya yayi mishi zafi! Ya rasa ta Ina ma zai fara. Wayarshi ya zaro ya hau online wai ko zai d’an samu ya rage zafi! Sai dai yana hawa yaci karo da message d’in Jalila a sama sama da alamun yanzu ta turo.. Tsaki yayi ya jefar da wayar dan kwata kwata ya kasa fahimtar spelling d’in nata sannan ya gaza ganewa shin da Hausa tayi mishi magana ko da turanci!. Shifa ya kasa fahimtar alak’arta da Arshaad kwata kwata! Ya bugi cikinta shekaran jiya amman bai fahimci komai ba.. Ganin she’s not worth his time ya sanya kawai ya kawar da tunaninta gefe ya fara wanda ya san zai fishshe shi….. Gandun Albasa ! Yau kwana uku kenan rabon Jalila da Auwal Tun ranar da ya kirata a waya bata d’auka ba bai sake nemanta ba! Umma tana ankare da ita shiyasa da taga kamar basa waya kuma bataji tace mata zai zo ba ta tambayeta.. Jalila bata b’oyewa Umman komai ba, tace mata “Tun ranar da suka je shopping da ya kirata bata d’auka ba har yau ba suyi magana ba.” “Innalillahi wa innailaihirrajiun!!” Shine abunda Umman tace tana dafe kanta. Da sauri Jalila tace “Umma mai ya faru??” Cike da takaici tace mata “Ke kika faru! Mahaukaciya dak’ik’iya irin ki, banza kawai!.” Tura baki tayi ta koma gefe tana gunaguni dan sai yanzu ta fahimci dalilin salatin nata Cikin gunagunin nata tace “Umma nayi mishi magana fa a watsapp bai ce min komai ba.” Cikin tsananin b’acin rai Umman tace “Wallahi ko nice ba zan kulaki ba! Anya Yarinyar nan kin san ciwon kanki kuwa?” Tsabar bak’in ciki Umma kasa ma ci gaba da yi mata magana tayi, dan haka kawai ta mik’e ta fice a d’akin ta zauna a tsakar gida. Ganin yadda ran Umma ya b’aci sosai ne ya sanya kawai ta d’auki waya ta kirashi… A na farkon bai d’auka ba sai ana biyun! Shiru, yayi bai ce komai ba! Jin yayi shiru yasa tace “Ina wuni” “Lafiya” kawai yace mata. A hankali tace “Kwana biyu”. “Umm” Kawai ya sake cewa. Jin tayi shiru yasa yace “Kina da abun fad’a ne?”. Taji zafin tambayar amman kawai ta daure tace “A’a kawai dai na kira mu gaisa ne.” “Hmm” Kawai yace daganan duk suka yi shiru. Kamar ba zai ce wani abun ba chaan! Kuma ya sauk’e ajiyar zuciya yace “Shekaran jiya baki ga miscall d’ina ba??” A hankali tace “Na gani.” “So?” Yayi mata tambayar a gajarce. Dabara ce ta fad’o mata dan haka tayi saurin cewa “Bani da kati ne, sai yau Umma ta saka min.” A hankali taji ya sauk’e ajiyar zuciya “Na d’auka kyaliya ce ai, shiyasa daa har nayi fushi.” Murmushi tayi sannan tace “Kayi hak’uri” Shima murmushin yayi daga nan yace “Ina aiki, zamu yi magana anjima.” “Allah ya taimaka” tace mishi. Daganan ya yanke kiran. Bai sake kiran taba har bayan kwana biyu… Yau ma Ummance ta tusa ta a gaba sai da taga ta kirashi ya amsa a kira a hud’u! Tukunna ta fita daga d’akin. Ya d’an sake yau ba kamar ranar ba…har d’an janta da hira ma ya dinga yi! Amman wata maganar idan ya fad’a sai taji kamar k’asa ta tsage ta shige ciki… Sai da suka kusan k’are wayar tukunna yace mata “ta shirya gobe zai zo da safe zata rakashi unguwa! Tunda weekend ne.” Sai da ya maimaita mata tukunna tace “Allah ya kaimu” Daganan sukayi sallama. Sun gama wayar kenan Umma ta shigo. Ganinta tayi zaune da waya a kunnenta amma kamar ba wayar take yi ba, da alamun tunani ta tafi… Sunanta ta kira dan haka tayi firgigit! Ta juyo tana kallonta kafin ta sauk’e wayar daga kunnanta tana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya. A hankali Umman ta k’araso ta zauna a kusa da ita kafin ta dubeta tace “Tunanin ne yau ma?” Wata ajiyar zuciyar Jalila ta sauk’e kafin tace “Wai cewa yayi zai zo in rakashi unguwa gobe! Da safe.” Murmushi Umma tayi sannan tace “kice kar inci d’umame da abinci rana gobe, ke har ma na dare ba zan ci ba.” Tana gama fad’in haka ta mik’e ta isa bakin wardrobe ta sunkuya ta d’auko ledar da su Huda suka kawo mata kwanaki ta zaro dandatsetsiyar riga tace “ungonan ajjiye ta a gefe ita zaki saka gobe.” Cikin rashin jin dad’i Jalila tace “Haba Umma! Daga yace in zo ni kuma sai kawai in bishi zungui zungui? Sati d’aya fa kenan yau d’in da had’uwa ta fa dashi. Sannan, kin ga dai bai gaya min inda za muje ba ko? Amman wallahi tunani na ya bani! A yanayin maganarshi da hirarshi ta yau sarai na fahimci inda ya dosa! Saboda haka gaskiya ni babu inda zan je!!”. Tayi maganar tana had’e rai sannan ta gyara ta kwanta a kan gadon rigin gine. Takowa inda take Umma tayi bayan ta ajjiye rigar a kan kujera Tana zuwa tace “Kin san Allah Jalila Wallahi sai kin je!!” A zabure da d’an mamaki a kan fuskarta ta mik’e ta zauna tana kallonta “Kwarai kuwa! Kin jini da kyau! Cewa nayi wallahi sai kin je! Idan ta kama in jaaa ki ne To ina iyawa In fitar dake!Muddin ya zo gobe kika yi taurin kai. Tunda na lura so kike ki kasheni da raina y’ar bak’in ciki Yarinyar da bata san ciwon kanta ba! Ana nuna mata Annabi tana runtse ido!.” Tana gama fad’in haka ta juya ta fice fuuu kamar zata tashi sama. Har dare Umma k’in kula Jalila tayi. Washegari da safe ma k’in kulata tayi… Ko tayi mata magana sai dai ta d’auke kai ta fara wak’a! Sanin abunda ya had’asu fad’a da Umman nata ne ya sanya kawai ta mik’e ta shiga wanka ta fito ta tsantsara kwalliya ta sanya doguwar rigar da Umman ta zab’a mata jiya.. Tayi masifar yin kyau kuwa kamar ka saceta ka gudu! Tana cikin rolling Umman ta shigo, tana ganinta

Chapter 29 of 32