gadon.
A hankali ta shiga gayawa Ummu abinda ya faru har Ja’afar yayi mata wannan aika aikar…
Share kwalla Ummu ta yi sannan tace “Gaskiya Mama ni kam zan d’auki Huda mu tafi gidana da ita, koda kuwa Hajiya Shuwa zata yi fushi. Dan naga alamar burinsu Sadiya su kashe ta ne, wannan wanne irin abu ne??
Ana sallamrta za mu tafi tare ba za su sake ganin ta ba.”
Da sauri Mama tace “a’a Bilkisu, kar kiyi haka, dan Allah. Fushin Hajiya Shuwa bashi da dad’i ni zan fad’a miki wannan, ba zan so saboda ni ki samu matsala da ita ba.
Kawai ki barmu a yadda muke, Allah yana sane da mu...
Wani irin tausayin su ne ya rufe Ummu, ganin tana shirin fashewa da kuka yasa ta yi saurin mik’ewa tana cewa
“Bara inje inda Sakina ta barmu in jirata, kar tazo tayi ta nemanmu bata ganmu ba.”
Tana gama fad’in haka da sauri ta fita tana sakar kukan daya taho mata babu shiri.
Murmushi Mama tayi dan sarai ta gano k’anwar tata.
A hankali ta fara shafa kan Huda wasu zafafan hawaye suna tsiyaya daga idanunta sakamokon kwakwalwarta da ta fara tariyo mata wasu shud’ad’d’un al’amura da suka wakana shekaru ashirin da shida baya.........
………………..
Alhaji Muhammad Madu shine asalin sunan Mahaifin Mama, Mahaifin sa Babarbarene gaba da baya, Mahaifiyarsa kuma y’ar jahar Yobe ce, Fune, Jajere .
Ya fi kama da Mahaifiyarsa domin idan ka kalle sa yanayin farar fatar sa da siririn jikinsa komai nasa irin na fulani ne.
Iyayaensa shi kad’ai suka haifa, sannan sun rasu ne tun yana Yaro.
Mahaifin Anum (Hajiya Shuwa ) shine ya d’auke sa ya rik’e shi kamar d’an sa.
Bashi da d’a Namiji, Shuwa da yayunta mata biyu Allah ya bashi, shiyasa ya rik’e Madu a matsayin d’ansa, sannan an yi zaman mutumci a lokacin da iyayenshi kafin su rasu.
Mahaifin Hajiya Shuwa da Mahaifiyarta gaba d’aya dangin su Shuwa Arab ne.
Mahaifin ta ya kasance Malami Babba a Maiduguri, domin babu inda zaka tsaya a lokacin ka ambaci sunanshi ace ba a sanshi ba.
Shekarun Madu suna d’an ja suka fara zazzafar soyayya shi da Anum. Mahaifin ta yana fahimtar hakan kuwa, ya tsaida wata biyu aka d’aura musu aure, dukda Mahaifiyarta ba wani so take yi ba, dan Anum d’in a wannan lokacin shekarunta 13 kuma tafiso y’ay’anta duk su yi aure a k’abilarsu, gashi Anum d’in tana da masoya sosai a cikin y’an uwa, dan duk Yara masu shekarunta a wannan lokacin babu mai kyau da gashinta, shiyasa ma sunanta ya b’uya daga Anum kowa yake kiranta da Shuwa.
Shikuma Mahaifin Anum, hazak’a da k’ok’ari irin na Madu ya gani dan kaff cikin d’alibansa babu wanda ya taka sawunsa kamar Madu.
Daman chan tun kafin Mahaifinshi ya rasu ya d’aura shi a kan ilimin addini, yanzu kam kusan tare suke tafsiri a masallatai, gashi da k’ok’arin neman na kai.
Ana d’aura musu aure ya nemi zai tafi Kano tare da iyalinsa… domin akwai business kala kala da Abokin sa yake kwad’aita masa ya zo su yi.
Tare suke kasuwanci shi yana chan kuma yana ganin idan yana kusa harkar zata fi bud’ewa.
Shuwa sai a lokacin ta yi kukan Aure saboda ita da a tunaninta a gida za su zauna tunda ta auri Yayanta.
Haka suka tarkato suka yo Kano tana kuka da kyar ya lallasheta a hanya.
Suna isowa Gandun Albasa suka nufa, domin
nan ne Unguwar Abokin kasuwancin nasa ‘Bashir’ wanda suka had’u
shekaru biyar baya a wani zuwanshi da ya yi Maiduguri shi da uncle d’inshi saro huluna…a lokacin Madu ne Yaron shagon ya yi musu sauk’i sosai, dan haka da suka ji dad’i, suka rik’esa…. Ya kan yi musu aiken sak’on
ma wani lokacin, daga baya su bada kud’in, ko huluna aka yi sai ya fara zab’ar musu tukunna ake fara saidawa jama’a, wannan karamcin nashi yasa Bashir wanda yake tsarar shi shima duk wata hanyar samu sai ya san yadda yayi ya sako Madu a ciki(dukda kuwa k’aranci na shekarunsu a wannan lokacin).
Daga nan kuma sai Abota mai k’arfi ta shiga tsakani.
Shima Bashir ya kan tura musu kaya daganan Kano idan farashinsu ya fi tsada a chan domin su saida su samu tasu ribar suma su Madun haka.
Tun a lokacin Madu yaso dawowa kano, dan farashin kaya suna d’an fin hawa anan kamar su huluna da shadda zai a na turo musu daga Maiduguri
sannan akwai business kala kala da Bashir d’in ya kwad’aitawa masa a Kanon.
Mahaifin Anum shi ya hanashi a wanchan lokacin saboda k’arancin shekarunsa, sannan bai kammala secondary ba,yafi son at least ya samu certificate d’insa kafin ya fara tafiye tafiye, kar ya ji dad’in business ya k’i karatun boko….
Suna isowa direct gidan Bashir suka nufa, A lokacin shi ya dad’e da yin aure ya na tare da matarshi Aisha wadda ake kira da talatu da Yaransa biyu maza Jamilu da Usman, Jamilu shekarshi uku sai Usman wanda bai gama rufe d’aya ba.
Alllah sarki Bashir a gidan sa ya bawa Madu da Shuwa d’aki suka zauna na y’an wasu lokuta har Madu ya samu ya tara kud’in haya.
A layin ya kama haya tukun suka tashi, sannan ya sayi wani d’an Fili a gefe kad’an duk cikin layin, ya fara gininsa shima.
A wannan lokacin layin nasu dogo ne sasai kuma Babba amman kwata kwata gidaje hud’u ne a layin ragowar kuwa duk filaye ne. Gidan farko a layin shine gidan K’asimu yana da mata d’aya Khadijah ana kiranta da Laraba da Yaranshi uku Salmanu Umaru da Hansa’u.
Sai gidan Audu da ya yi aure watanni uku da suka wuce da amaryarsa,sai Bashir sai Madu.
K’asimu,
tun lokacin da Madu ya zo basu samu good start ba, hakanan Madun bai kwanta mishi ba saboda shi K’asimu irin mutannen nan ne masu kishi hassada da kyashi.
Madu yana zuwa layin akwai wani masallaci a bayan layi aka bashi ladani, daganan kuma ya koma Limami, sannan ga gida ya kama haya ga kuma fili yana gini ga karatun daya ci gaba na boko (daman ya gama secondary school tun a Maiduguri)ga kuma kasuwanci, hanya bud’e mishi take yi ta ko Ina, gashi kaff layin matansu basu kai tashi kyau ba.
Waennan abubuwa su suka taru suka k’ara rura wutar k’iyayyar Madu a zuciyar K’asimu, saboda shi tunda ya yi aure yau Yaran shi uku amman yana fama da gidan haya, sannan ya so a bashi wani matsayi a masallaci amma an k’i, gashi kasuwancin ma har yau Yaron shago ne shi Amman shi Madu daga zuwansa ko shekara biyar bai yi ba kalli yadda ya zama shahararre kusan kowa ya sanshi d’aukaka ta ko Ina ya sameta.
SHARE PLS.
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
09
Tun K’asimu yana b’oyewa har ya zo ya fara nunawa a fili…daga ya je chan ya tsugunna ya zagi Madu sai ya je chan ya tsugunna ya yi masa sharri. Babu inda zai zauna ya tashi bai zage sa ba, shi kuwa Madu harkar gabansa kawai yake yi sam baya bi ta kan K’asimu dan ya lura ko sallama idan yayi masa ba amsawa yake yi ba.
Tsananin tsanar Madu bata sake tabbata a zuciyar K’asimu ba sai a lokacin da kud’in hayar shi K’asimun na wajen shekaru uku ya taru, anyi anyi ya biya ya k’i biya, gashi gidan na marayu ne suma suna fama da yanayin rayuwa…jin labarin sabon limamin da a ka nad’a ba da jimawa ba mai aiki da addini gashi yayi karatun lauyoyi duk unguwa ana girmamashi ne ya sanya waennan Marayu suka garzayo wajen Madu akan ya taya su fad’in gaskiya a basu hakkinsu, ai kuwa Madu bai yi k’asa guiwa ba sai da ya tabbata ya karb’a musu hakkinsu har saida ta kai ga tirsasa K’asimu siyar da y’an dabbobim shi ya biya su hakkinsu da kud’in….
Jarumta da tarin ilimin Madu ne ya sanya aka nad’asa ‘mai unguwa’ a lokacin shekarar sa goma da zuwa garin Kano.
Sai kuma a lokacin ne Allah ya bawa Shuwa ikon samun ciki.
Kusan a tare suka haihu ita da matar Bashir da matar K’asimu.
Matar kasimu itace ta fara haihuwa,ta haifi y’arta mace aka sakamata Halimatus Sa’adiyyah sai matar Bashir ta haifi y’arta itama mace Zainab
Shuwa itama ta haifi mace, Maryama.
Duk a tsakanin haihuwar watanni bibbiyu ne.
Murna a wajen Madu kuwa ba a magana, saboda daman shi akwaishi da son Yara, shiyasa su Usman da Jamilu sunfi sakewa ma da shi fiye da Mahaifinsu dan idan ba sani ka yi ba ko fad’a maka akayi ba to ba zaka tab’a cewa Madu da
Bashir ba y’an uwa baneba
saboda tsananin shak’uwa da k’aunar junan dake a tsakaninsu, gashi yanayin jikin su iri d’aya….
Maryama ta taso cikin gata saboda tsananin so da k’aunar da Mahaifin ta yake nuna mata, ga kuma yayyunta guda biyu Usman da Jamilu dan wani lokaci har fad’a akeyi wajen d’aukar Maryam tsakanin Jamilu da Usman dukda kuwa ga Zainab k’anwarsu.
Idan Maryam tace tana son abu nan da nan Mahaifinta zai nemo sam baya bari ta sake tambayarshi a karo na biyo dukda kuwa ba wani k’arfi ne da shi ba, Law ya karanta a lokacin albashinsa ba wani yawa ne da shi ba amman idan kaga Maryama ko y’ar gidan wani hamshak’in mai kud’in sai haka, suturar jkinta kad’ai abun kallo ne.
Tana isa shekara hud’u Madu ya had’ata da Zainab ya saka a makaranta, a wannan lokacin har sai da Talatu ta bawa shuwa shawarar a nemawa Maryama maganin baki da mayu saboda babu inda zata je ba a tankataba…Yarinyar chubby da ita gata fara farin ta irin mai yellow d’innan, gashin gira da idonta a ciccike ga gashin kai har gadon baya mai sulbi, idan ka kalle ta dole ka k’ara.
A haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Maryam da Zainab suka kai shekaru goma a duniya, sai a lokacin ne kuma aka saka y’ar gidan K’asimu (Sadiya)a makaranta da kyar!
Don a lokacin duniya ta yi masa zafi, yanayin rayuwa sai a hankali kuma shi ya dage ba zai sakata a makarantar gwamnati ba, a dole ta kud’in da su Maryam da Zainab suke zuwa nan itama zata je, a cewarsa ‘ai tare aka haifesu’
Bayan shi basussukan da suke kanshi kad’ai ma abun mamaki ne,dan idan aka gaya maka zaka rasa Ina yake kai kud’in,
abu guda d’aya dai shine ko takalmi ne idan Madu ya sauya yau to tabbata sai ka ga irinshi sak a k’afar K’asimu washegari, duk wai dan ya nunawa duniya ‘ai Madun bai fi sa kud’i ba’ (a cewarshi), sai dai kuma duk inda aka yi sati 1ko2 nan zaka nemi takalmin ko suturar ka rasa saboda ya siyar ya cinye kud’in a banza. Yaransa duka uku babu mai zuwa makaranta da kyar ya saka Sadiya.
Layin nasu zuwa yanzu ya cika sosai dan a k’alla gidaje sun kai sha biyar, Bashir ya sayi filin jikin gidanshi ya had’e ya kuma yin wani had’add’en gini, Madu shima ginisa a layin gwanin ban sha’awa daman shi filin sa tafkeke ne ya siya, amman shi K’asimu har yanzu yana wannan gidan haya na marayu wanda k’arfi da yaji yake so ya danne ya mayar da gidan nasa.
Matarshi ta so ta had’u da Talatu da Shuwa amman tunda ta so had’a su fad’a Allah ya taimaka sukai saurin ganewa munafuka ce, sai suka yi saurin
ja baya da ita, amma duk da ja bayan da suke yi da ita hakanan sai ta yi ta nanik’e
musu. Inda Allah ya taimake su sai wata dillaliya ta tare, nan ta koma suka jone, aikuwa tun daga wannan lokacin in dai ka ji hayaniya da fad’a a layin to ko daga gidan dillaliya, ko gidan K’asimu dan basa barin takwana, ko kallo ne kayi musu bai musu ba nan za su fara surfa ruwan bala’i, ga rashin sanin ya kamata da munafurci......
Wata rana cikin azumi K’asimu yana zaune a bakin titi…duk magidanta da samarin unguwar suna masallaci ana sauraron tafsirin Modu amman shi ya k’i shiga tsabar bak’in hali, saboda baya shiri da Madu kuma akwai maza guda hud’u a cikin masallacin waenda yake gaba da su, dan haka ya gwammaci ya zauna shi d’aya har lokacin shan ruwa ya yi yaje ya amshi abun sadaka yayi gida domin dashi suke karya azumi….ko kwayar shinkafa babu a gidanshi.
Suna cikin masallaci sukaji kamar k’arar jiniyar y’an sanda, sunan nan zaune suka ji k’arar tana ta matsowa. Kasancewar lokacin addu’a ya yi ya sanya suka rufe sukai addua
masu son yin alwala suka mik’e suka yi waje…suna fita kuwa sukaga Yara sunata gudu sunayin titi,wani a cikin su ne ya tare wani Yaro ya tambayeshi “mai ya faru” shine Yaron yake ce musu ,
“wai motar sojiji ne mota uku, da na y’an sanda suka zo za su tafi da Baba K’asimu.”
Da sauri wasunsu suka yi bakin titin wasu kuma suka koma cikin masallaci domin sanar da ragowan mutanen.
Waenda suka yi bakin titin ne suka hango K’asimu ana ta k’ok’arin dannashi a motar y’an sanda yana tirjewa,yana bada hak’uri amman kafin su k’araso wajen har an tafi da shi.
A bakin Yaran gurin suka ji cewa wai “Kud’in wani kurtun soja ya amsa ya sayi mota tun watanni biyar baya, kuma yace zai biya kud’in amman har yanzu be biyaba.”
Cike da tarin mamaki suka koma masallaci domin lokacin shan ruwa ya yi, suna isa suka bud’a baki da dabino da ruwa akai Sallah kowa yayi gida domin karyawa.
Basu samu lokacin bin bayan K’asimu ba sai da suka idar da asham
Da Madu da Bashir da wasu mak’oftansu guda biyu (Kabiru da Nafi’u)suka tafi a motar Madu.
A cikin motar ne su Kabiru suke hira da Baba Nafi’u wanda yake tambayar “shin wai yaushe K’asimu ya sayi mota ne shifa bai tab’a ganin motar ba.”
Nafi’u ne yace “ai tun watanni shida da suka wuce lokacin da Madu ya sayi mota shima ya tada hankalinshi ya dinga bi yana tambayar bashi kusan kaf layin duk wanda baya gaba da shi saida ya tambaya bashi aka hanashi.”
Nafi’un ya d’aura da cewa “nima sanadiyyar ya tambaye ni aron kud’i nace masa bani da kud’i ya sanya ya fara gaba da ni har da ce mini ‘wai ni ba makwafcin gaskiya bane ba, Ina yi mishi bak’in ciki….’
To dai na ganshi da mota after one month kuma ina kyautata zaton a wajen wannan kurtun ya karb’a Aron kud’i dan bai dad’e da tarewa ba a bayan layi lokacin.”
Kabiru Yace ”Ikon Allah to ai ni ban tab’a ganin motar ba.”
Dariya Nafi’u ya yi yace”Ai motar ba ta kwana ba inaga damfarar sa masu siyarwan suka yi. A ranar da ya siyota ya kawo ya zo yayi parking, haka nan ta dunga hayak’i ta cika unguwa saida athmar d’in Laraba ya tashi…nifa da na fara ganin hayak’i wallahi na d’auka gobarace ta tashi a gidan nasa, lokacin dawowa ta kenan daga kasuwa ko gidana ban shiga ba na ce bara in duba gidan nashi inga, Ina lek’awa kuwa na hango shi da salmanu da Umar sunata bulawa motar k’asa don k’ok’arin kashe hayak’in. Hansai kuma tanata kuka ita da Sadiya suna jijjiga mahaifiyarsu wadda ta sassank’are tana numfashi da kyar. Ban bi ta kansu ba naje da kyar na nemo abun hawa aka kai Laraba asibiti, shikuma ya tafi kai mota gyara…kusan duk d’an abin hannunshi saida ya k’are a wajen gyaran motar nan.
Daga karshe ya maidawa wanda ya saya a wajenshi shi kuma ya ce an kwak’ule motar a wajen gyara bata da wani amfani, inaga a dubu hamsin ya saida motar da kyar,ya amshi kud’in, dan ta tashi a aiki....”
Madu ne ya katse musu hirar su ta hanyar ce musu “Mun iso!!”
Suna shiga kuwa sukaci sa’a inda suka je d’in aka kaishi, bayan sun buk’aci ganinsa ne aka fiddoshi
Har an fara sauya mishi kamanni. Da farko ya so yayi tirjiya da b’oye b’oye,amma da yaga ba sarki sai Allah sai kawai ya hak’ura ya gaya musu gaskiya “kud’in kurtu ya karb’a ya sayi mota kuma shi yanzu bashi da halin biya.”
Madu da Bashir su suka had’a kud’i sukai belling shi, bayan ya dawo gida Modu da Bashir suka bada rabin kud’in mota, shima K’asimun d’an kud’in hannun shi ya tattaro ya had’a da adashin Laraba aka had’a duk amman dukda haka kud’in bai cika ba…Da kyar da taimakon wasu makwaftan aka had’a ma kurtu kudinshi dan cewa ya yi “Wallahi bai san Asara ba!.”
Bayan sun dawo gida ne da washegari, Modu ya samu Baashir yace masa “su taimaka su had’awa K’asimu kud’i su bashi ya ja jari ya daina yawon neman bashi,tare aka taso bai kamata su barshi a haka ba.”
Dama shi Bashir da kyar ya yarda, ai kuwa!!…..a cikin azumi suka bashi kud’in lokacin yanata murna yayi ta godiya har da rungume Madu. Bayan Sallah tana yi K’asimu ya rangad’a sabon Aurensa, ya auro baffulatana Yarinya y’ar k’arama shekara d’aya Jamilu ya bata.
Ai kuwa gidan nan nasa ya sake hargitsewa, gashi shi
ba wata tsayayyiyar sana’a garesa ba dan haka kowa zuciyarsa a kusa! kullum cikin fad’a, daman itama amaryar irin marasa kunyar nan ne, kowa baya ragawa kowa.
Yadda basa ragawa junansu hakanan y’an waje ma ko kallo ka yiwa d’aya daga cikin Yaran In bai musu ba duk girman mutun haka zasu zuba maka tujara, shiyasa ake yiwa gidan Lak’ami da
‘Gidan marasa tarbiyya,’
sun kuwa tsani sunan idan sukaji sunan a bakin wani tofa ranar rigima sai inda k’arfinsa ya k’are.
A wannan lokacin ne kuma Shuwa ta sake d’aukar ciki, Maryam da Zainab da Sadiya sunada shekara goma a duniya.
Murna a wajen Maryam da Zainab ba’a magana dan har sun fara shirya kalar party d’in da za su yi idan Shuwa ta sauk’a lafiya.
Kullum kuma cikin addua suke Allah yasa k’anwa za a haifa musu don su dinga yi mata kitso suna yi mata kwalliya.
Wani abun mamaki, Zainab k’awar Maryam ce sosai a da amma tunda ta fara zuwa makarantar su sai suka had’ewa Maryam kai, ita Zainab ashe dama tuntuni tana d’an jin haushin Maryam saboda su Ya Jamilu sun fi sonta, da taimakon zugar Sadiya kuwa k’iyayyar Maryam ta samu waje a zuciyar Zainab, daman chan ita Sadiya ta tsani Maryam domin kuwa ita ya’yan masu kud’i ta so yin huld’a da su amma sam basa kulata Maryam suke so da k’awance duk da ita kuma Maryam d’in bata kulasu sosai dan bata da hayaniya.
Duniya ta fara yiwa Maryam zafi a lokacin da k’awarta kwalli d’aya ta juya mata baya. A yanzu ko kaisu makaranta Zainab bata yarda a yi tare balle a d’aukosu, ta gwammaci ta biyawa Sadiya su tafi a k’afa su dawo a k’afa! Wanda har su je su dawo kuwa basu da aiki sai na zagin Maryam ita ba amma ta san suna yi ba. Ana cikin haka ne Shuwa ta haihu, ta samu y’arta mace ranar suna taci suna ‘Bilkisu’ , bayan suna Maryam ta had’a party duk wani Yaro saanta ta gayyata ana I washegari amman Sadiya sai ta hana Zainab zuwa sannan ta sakata ta sato kud’in Babanta da ya ajjiye, abinda bata taba yi ba.
Haka nan dinga bin Yara suna raba musu kud’i akan ‘ “kar su je Partyn Maryam’ wai ta saka guba a lemo, su jira su gani babu wanda zai je saboda bak’in jini ne da ita.”
Ai kuwa hakan akayi ko wanne Yaro ya karb’i kud’i yak’i zuwa party kar ya je a bashi guba.
A ranar Maryam kwana tayi tana kuka, tun daga ranar kuwa bata isa fitaba sai Yara su fara mata wak’ar ‘mai bak’in jini’ Sadiya ta kafa ta tsare duk wanda taga yana shirin fara yin k’awance da Maryam nan da nan za ta saka Zainab ta je ta sato kud’in mahaifinta ta bawa Yaran tace su zab’a ko kud’i ko k’awance da Maryam.
Bashir tun baya fahimta har ya fara fahimtar ana d’aukar masa kud’i…
A haka shekaru suka yi ta shurawa abun tun yana damun Maryam harta hak’ura ya daina damunta da taimakon Shuwa.
Ranar wata Juma’ah Baba Bashir ya tafi masallaci aka y rashin sa’a ya manta bai d’auki darduma ba kuma ya makara don Madu yayi tafiya so ba tare za su tafi ba, hakan ya sanya ya dawo…yana shiga
d’akinsa kuwa ya kama Zainab dumu dumu, ai kuwa ta daku a ranar kuma ya titsiye ta sai da ta fad’a mishi komai plan d’insu da Sadiya ba abinda ta b’oye…..
Kunya! kamar k’asa ta tsage Bashir da Talatu su shige haka sukaji…mutumin da yake biya mata kud’in makaranta bai tab’a nuna gajiyawa ba shine take yiwa y’ar sa haka??.
A lokacin suna aji biyu a js amman babu shiri aka siya mata form ta yi junior waec , aka fara shirin tura ta boarding. Madu yana dawowa Bashir ya rok’esa yace “yanaso zai had’a da Maryam ya kaisu makarantar kwana, anfi karatu dan kwata kwata Zainab bata karatu”.
Sam Madu bai so hakaba don baya son yayi nesa da Maryam amman kawai sai yayi kawaici ya amince, Bashir a tunanin sa Zainab da Maryam za su shirya ne idan an kaisu boarding tare tunda daman chan k’awaye ne, kuma yana kyautata zaton Sadiya ce ta had’asu fad’a. Sai dai kuma ko da akaje boarding d’inma, farin jinin da Maryam take da shi a wajen Malamai da d’alibai sai ya sake jawo mata bak’in jini a wajen Zainab, sannan Yayanta Usman sai ya zo makarantar sau da yawa wajen Maryam amman ita sai dai ya bada sak’o yace a bata, kuma sai ya cukowa Maryam leda da kayan kwad’ayi amman ita sai ya bada kad’an yace a bata..
Abunda ba ta sani ba a ko da yaushe sai Maryam d’in ta k’ara mata a kan wanda Ya Usman d’in ya bayar yace bata.
Haka kurum sai ta daina kulata ko ta hau yada magana idan ta ganta, shirin da akeso dai su yi bai yiwu ba domin kuwa alamarin k’ara tab’arb’arewa ma yayi don kwata kwata Zainab da Maryam basa shiri,duk mates d’insu sun sani.
Har sai da Zainab ta kai Maryam bango duk kuwa hak’urinta sai da ta tanka mata sukayi wani damben da suka jiwa kansu ciwuka har aka kai ga kiran iyayen su, sai a nan ne Madu ya ji abinda ya faru har Bashir ya kaisu boarding duk dan ya samu daidaita tsakaninsu.
Ganin k’ok’arin Bashir na ganin zaman lafiya ya wanzu ya kuma tabbata a tsakanin Yaran nasu ne ya sanya kawai shima Madu ya barsu sukaci gaba da boarding d’in.
Wanda bayan sun dawo hutun gama ss1 ne Ya Usman ya zo da zungureriyar wasik’ar shi ya bawa Maryam ta inda ya ke bayyyana mata cewa shi fa sonta yakeyi tun tana y’ar k’aramar ta….
Ita dai Maryam ba zata ce bata son Ya Usman ba saboda Yayanta ne kuma ya kula da ita sosai, amman a gaskiya so na soyayya sam bata yi masa kwata kwata. Ko da ta gayawa Umma Talatu da Hajiya Shuwa..kalar murnar da ta gani a kan fuskokinsu ne ya sanya kawai ta amince suka fara soyayyarsu ita da Usman gwanin ban sha’awa.
Zainab kuwa (duk da kaita boarding school d’in da akayi hakan bai saka sun rabu da Sadiya ba, don indai aka aike Zainab to sai ta biya wajen Sadiya a b’oye).
Ai kuwa tanajin labarin soyayyar Maryam da Usman,
Sadiya ce kawai ta fad’o mata a rai, dan ba zata iya irga adadin wasik’un da Sadiya ta bata ta bawa Ya Usman ba..tun tana y’ar shekara sha d’aya take son Ya Usman,
shi kuma Ya Usman idan akwai wadda ya tsana a duniyar nan to Sadiya ce! Idan ka kalli Sadiya sam ba zaka tab’a ce mata mummuna ba, ba doguwa baceba amman tanada manyan idanuwa da matsakaicin hanci bakinta dai dai misali ga dimples a fuskarta sai dai bak’a ce
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 32