Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
akan yadda Aaima da Arshaad suka yi ta d’awainiya da Yaran nan.” K’ura mata ido Baban Sakina yayi har sai da ta d’an sunkuyar da kanta, kafin ahankali yace “Ki bari ba yanzu ba tukunna ko?” Sannan ya d’aura da cewa “Yanzu dai a halin da ake ciki yana buk’atar zuwa wajen su Madu ne, dan yace mini in dai suka gama daidaitawa da ita Hudan to baya so auren ya d’auki lokaci mai tsayi.” Murmushi Ummu tayi sannan tace “Allah ya tabbatar mana da alkhairi, abun nan yayi min dad’i Baban Sakina, ko ba komai hankalin Mama da ita kanta Hudan zai kwanta zata rabu da masifar su Sadiya, ita kanta Mama kullum fargabarta kar a aurawa Huda Junaidu, to dai yanzu babu wannan zancen, tunda gashi Arshaad zai ruga Junaidun zuwa. Murmushi Baban Sakina yayi sannan yace “Kuma yace min maganar karatu har sai tace bataso, duk inda take so shi kam zai kaita tayi.” “Alhamdulillah” Ummu tace cike da farin ciki sannan ta k’ara da cewa “Yaron nan d’an albarka ne, Allah ya tabbatar da alkhairi sannan Allah ya had’ata da surukai na gari inda zata huta ta samu cikakken kwanciyar hankali da kulawar da bata samuba a baya…” A hankalii Baban Sakina yace “Ameeeen” Tattaunawa suka d’an yi kafin Ummu ta mik’e ta hau tattare kwanukan tana mai cewa “bara inje in sanar da Mama, yaushe kace mishi yaje wajen su Kakan? Ko sai an tuntub’e su tukunna anji?” “Eh” kawai yace mata daga haka ya mik’e ya nufi toilet ita kuma ta k’arasa kwashewa ta fice tanata murna....... Arshaad yana kwance da waya a hannunshi….yayi dialing number Mama ya kashe before ya fara ringing yafi sau biyar! Yana cikin wannan yanayin ya fara jiyo sallamar Aaima a falonsa hakan yasa ya ajjiye wayar ya mik’e ya fita. Kusan karo suka yi a k’ofar d’akin, tana k’ok’arin fara knocking. Baya taja tana cewa “ai na d’auka ma kayi bacci.” Girgiza mata kai kawai yayi alamar ‘a’a’ sannan ya wuce cikin parlourn, kujerar 3 seater ya nema ya zauna, kusa dashi Aaima taje itama ta zauna sannan ta fara gaidashi.. A hankali ya amsa yana mai dafe kan shi daya ji yana neman fara ciwo. A hankali cikin kulawa tace “Ya Arshaad baka da lafiya ne?” Jinjina mata kai yayi sannan yace “it’s nothing serious kawai kai nane ke min ciwo.” Da sauri ta hau tambayr shi “tun yaushe, mai ya faru ,ya sha Magani??” Ganin yadda duk ta rud’e ne ya sanya yayi murmushi kafin yace “Yanzu auta wacce tambayar kike so in fara amsa miki, um?” D’an murmushi tayi kafin tace “Yaya to baka da lafiya kuma sai ka na zaunawa a d’aki? Na tabbatar ko Mammy ma baka gayama ba, tunda yanzun nan muka rabu da ita tana tambayata ‘kana Ina?’.” Murmushi ya sake yi sannan yace “Ban sha magani ba tukunna sai nazo bacci. Mammy kuma bana so ta ganni a situation d’innan ne, sai mun gama settling in shaa Allah!” Sai da ya furzar da numfashi tukunna ya ce “d’an k’awarta ne ya kunno min wuta! Banaso mu zama silar b’ata musu friendship. Idan munyi settling before Monday tou Alhamdulillah, in kuma bamu yi ba, i don’t know ya abubuwan zasu kasnce gaskiya.” A hankali Aaima ta ke kallon shi sannan tace “Fad’a kuka sake yi kai da Ya Auwal??” Arshaad bai b’oyewa Aaima komai ba, nan ya hau gaya mata yadda sukayi kamar yanda ya gama fad’awa Aslam d’azu. Allah sarki Aaima har da kukanta! Da kyar ya iya lallashinta tayi shiru kafin yace “in shaa Allah ba za muje court d’inba, kud’in suna accnt d’ina, although i don’t know tayaya suka shiga kuma ko alert ban gani ba sai da nayi checking balance tukunna na gansu. Zamu je mu samu granma mu bata kud’in ita kuma ta bashi ta taya mu kuma bashi hak’uri, Allah yasa ya hak’ura.” Cikin sake share hawaye tace “Allah ya isan ka Ya Arshaad, ban san mai yasa Ya Auwal yake wannan abubuwan ba.” Murmushi yayi kafin yace mata “MT mana! Saboda kud’i ne Aaima, duk dan kud’i ne, so yake ya had’e komai, sannan ya zama superior akan kowa, ta yadda za aga capability’s d’inshi a mallaka masa MT! Nothing more than that. Shiyasa idan ya ga wani yana shirin yin sama a company d’in ko kuma yana k’ok’arin ganosa yakeyin sauri ya had’a mishi tuggu, just like wat he did to me! Da idona fa naga ya saci more than 5 hundred million a cuwa cuwa da wasu ways d’inshi! Bana son issue shiyasa kawai nayi shiru…” Da sauri Aaima tace “to ai Ya Arshaad kaima da sai ka fad’a kace ga abinda yayi” Murmushi kawai Arshaad yayi sannan yace “You know what Aaima, just forget all this, let’s talk about reason d’in da yasa na kiraki. D’azu da muna dawowa, you look disturbed Mai ya ke damunki?” Shiru tayi ba tare data bashi amsa ba ta fara wasa da y’an yatsunta tana kallon k’asa. Gaba d’aya nutsuwarshi ya tattaro kafin yace “i just finish sharing my problems with you, ki fad’a mun ko mene yake damunki, ko kina da wanda zaki fad’ama apart from me and Aslam??” A hankali ta girgiza kai kafin ta zayyano mishi halin da suke ciki itada Auwal…. Shiru yayi yana kallonta for some minutes, kafin yace “Do you love him?” Shiru tayi hakan yasa ya fahimci amsar ta! Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya kafin a hankali yace “Aaima kiyi ta addua nima zan taya ki, Allah ya cire miki sonshi a rai. Auwal ba Mijin aure bane ba. Not because of wai bana shiri da shi yasa bana son aurenku Not at all! Kinga na farko Auwal bai san mutuncin mutane ba, both Babba da Yaro, hatta mahaifiyar shi baya ganin girmanta! All that matters to him is money, dukiya da abun duniya, kuma zan iya rantse miki ba abunda ba zai iya aikatawa ba domin ganin ya tara. Secondly, humanizer ne first class, yanzu haka a company d’innan inda muke ni da shi, za a iya samun mata morethan five da za suyi testifying haka a kanshi. The last and worst shine bai damu da addiniba dan zan iya ce miki tun dawowa ta daga Dubai ban tab’a had’uwa dashi koda a hanyar masallaci ba! Sannan munafuki ne, ke kin san haka dan tun muna Yara abunda ya fara had’ani fad’a da shi kenan, Auwal ya kan shiga tsakanin d’a da mahaifi ya had’a su fada na har abada.. Idan nace zan tsaya lissafo miki munanan halayenshi zamu jima anan, all I’m saying is ki yi k’ok’arin rabuwa dashi kuma kiyi ta addua Allah ya yaye miki sonshi saboda Aaima is not the type of man da nake miki fatan kiyi spending the rest of your life with, ba.” Aaima, ita kam waennan halaye na Auwal sun sake tabbatar mata ba sonta yake yi ba, wato yana tare da ita ashe yana chan da wasu y’an matan amman kullum k’arya da yake shirga mata ‘Bashida kowa sai ita’ A hankali tace “in sha Allah, Yaya.” Dan ita kam har ga Allah ko son Auwal zai kasheta ta fita a hanyar shi kenan har abada m. She can’t live with this type of man as a husband… Arshaad ne ya katse mata tunani ta hanyar cewa “Sai maganarmu ta biyu, it’s about Huda.” Da murmushi ta d’ago tana kallonshi kafin tace “what about her?” Murmushi yayi sannan yace “kin san taste d’inta? As in abubuwan da takeso. Ina so in d’an yi mata shopping ne, kuma Ina son siya mata waya.” Murmushi Aaima tayi sannan tace “Tou na farko dai tana son perfumes, da abaya da rings and her favorite colour is blue, irin royal blue d’innan. About the phone kuma ko jiya da taga wayana sai da tayi ta yabawa tana cewa wayan yayi kyau, tun ranar farko data fara gani time d’in munje musu visiting tayiya juya wayan ta dinga game tana kallon pics, tace min ya burgeta sosai.” Kallon wayan Aaima yayi mai k’irar iphone 12 mini kafin yace “Aiit, shikenan iya abunda takeso? Abaya perfume rings is that all?” “Gaskiya i think shine dau abunda tafi so but u can add abunda kaga ya kamata, ko?” Cewar Aaima. Hamma Arshaad yayi kafin yace “No p. Gobe In Allah ya kaimu sai ki rakani muje muyi mu kai mata ko?”. “Owk” shine abinda Aaima tace tana murmushi. Mik’ewa Arshaad yayi yana mik’a sannan yace “Sai da safe bacci nake ji.” Sallama itama Aaima tayi mishi….har zata fita sai kuma ta juyo ta ce “Ya Arshaad ka samu lawyer ne? Naga baka wani shiri, gashi ance Monday.” Murmushi yayi sannan yace zan ga lawyer, Aslam yace zai yi mishi magana so zan ganshi gobe around 11 na dare. In sha Allah ma ba za’a shiga court d’inba, ki dai taya ni da addua.” “In sha Allah” Aaima tace, tana kallonshi har ya shige bedroom sannan itama ta juya ta fita ranta ba dad’i duk tayi laushi tanata tunani.. A Haka ta fito daga corridor d’in side d’in nasa. Kwata kwata hankalinta bai kai kan main parlour ba, ta nufu hanyar staicase d’in da zai sadata da side d’inta. Muryar Mammy ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da take, jin tana cewa “Ke Aaima wai bakya ji ne? Tunanin me kike tayi ne haka?“ Da d’an k’arfi. Da sauri ta juyo….da kyar ta iya janye idanunta da suka sark’e cikin na Auwal wanda ya wani hakimce akan kujera gefen Mammy yana binta da kallo. D’auke kai tayi sannan ta k’arasa cikin parlourn ta nemi waje ta zauna a ranta tana mamakin guts irin na Ya Auwal! Despite abunda ya yiwa Ya Arshaad kalla yadda ya zo ya baje a parlourn su yana hira da Mammy tsabar tsaurin ido! Wata zuciyar ce ta hau tunzurata ta fad’awa Mammy halinda ake ciki, sai kuma ta tuna da Anty Adama, da kuma yadda shima Ya Arshaad d’in yayi shiru yana hoping a yi settling case d’in b4 Monday..kar taje ta had’a gurmi kuma azo case d’in ya mutu amman fad’a tsakanin iyayensu bai mutu ba…. Muryar Mammy ce ta dawo da ita daga wannan tunanin jin tana cewa “Auwal gaskiya tou akwai matsala tattare da Aaima, bafa jin ka takeyi ba, ke wai me yake damunki ne? Ina Arshaad d’in yake? Daga fitowa daga wajenshi duk kin yi sanyi haka sai tunani? lafiya dai yake ko? Umm bara dai inje In ganshi kawai.” Mammy ta k’arshe maganar tana mik’ewa direct ta nufi hanyar side d’in Arshaad, ko Aaima wadda take ce mata “he’s fyn” bata tsaya sauraraba. Mammy tana shigewa Auwal ya taso ya zo kan handle d’in 1 seater n da Aaima ta ke zaune a kai, ya zauna. Yana zama tana mik’ewa da sauri ko bi ta kanshi bata yi ba ta wuce tayi hanyar sama… Da sauri ya sha gabanta yana k’ok’arin kallon kwayar idanunta amman tak’i bashi had’in kai. Hab’arta ya kama da k’arfi ya d’ago fuskarta har sai da tayi Kara kafin yace “Ban son raini, wannan attitude d’in fa?” Dukkan k’arfinta ta saka ta buge mishi hannu itama sannan tace “Out of my way, zan je d’aki, i have better things to do!!” K’ura mata ido yayi na y’an mintuna chan taga ya fashe da dariya har da d’an rik’e ciki. Sai da ya d’an tsagaita sannan ya d’ago yana kallon hanyar side d’in Arshaad yana murmushi yana shafa lallausan sajenshi a hankali yace “Arshaad! Arshaad!! hmm..” Kafin ya juyo ya ce mata “ya min spilling beans ko? Me yace?” “Ban sani ba!” Shine abunda Aaima tace sannan ta yunk’ura zata wuce… Da k’arfi yasa hannu ya fisgota ta dawo gaban shi kafin yace “bamu gama maganaba dan haka you are going nowhere, idan kina so ki tafi you better drop this attitude and talk!!”. Ya k’arashe maganar yana mai had’e rai. Mamaki kawai take yi yadda ya juye mata lokaci d’aya kamar ba Auwal d’inta mai lallab’ata ba. Tabbas ta kusan tafka babban kuskure a rayuwar ta, Allah ya taimaketa data farga da wuri! Kwallar da taji tana shirin zubo mata yasa ta ja vail d’in doguwar rigarta ta hau k’ok’arin sharewa. Binta ya fara yi da kallo from head to toe… chaaan! Ya ja akiyar zuciya ya sauk’e sannan a hankali ya matso ya dafa kafaf’unta yace “Baby this is all your fault…kiyi hak’uri to na fisgo ki kinji don’t cry, unhm?” D’aga kai kawai tayi ba tare da tace komai ba. Ahankali ya saki wani killer smile sannan yace “yauwa dear. To yanzu about that kiss” Ya fad’a yana kallonta da murmushi a kan fuskarsa.” Da sauri ta d’ago tana kallon shi, a zuciyarta taji tabbas it’s about time da ya kamata ta yiwa Auwal wankin babban bargo dan ta lura bayan mugayen halayenshi har da tab’un hankali ma yana damunshi. Sai da tayi murmushi sannan tace “It’s clear abunda kake so daga wajena, Auwal ya kamata ka farka ka daina deceiving d’in kanka, dan ba sona kake yi ba wallahi!! Kuma abunda kake buk’ata daga wajeni ni Aaima ba da niba! Mai zai hana ka tafi wajen y’an matan ka, i’m pretty sure za suyi maka wanda yafi wannan without any hasitation, and please kar ka sake shigowa gidan mu, tunda har zaka iya yiwa Ya Arshaad abunda kayi to i don’t think kayi deserving any love or kindness from his family, and yes Allah zai fitar dashi daga tuggun daka had’a mishi… Ka sani mai gaskiya kullum shine a sama!! Look at u, akan abun duniya you have turned into a monster, baka da aikin daya wuce ka had’a wannan da wannan ka had’a wanchan da wanchan duk saboda kud’i! Alhamdulillah! Mu ba wannan ne a gaban mu ba. And one more thing Allah ya isa na deceiving d’ina daka dinga yi, i tot you love me truly ashe kai chan wani shirme ka kake tunani… I’m like a sister to you, so ba zan ce maka na tsaneka ba but inaso ka ajjiye wannan at the back of your mind ‘ko ni da kai kad’ai muka rage a duniyar nan ba zan had’a ko wanne irin relationship da kai ba!’.” Tana kaiwa nan ta watsa mishi harara sannan ta ce “Humanizer irin ka.” Da mamaki yaketa kallonta tun lokacin data fara magana tana dasa aya ya hau tafi!! yayi kusan sau hud’u sannan yace “What a great speech, Aaima. Hope you are done saboda now it’s my turn. Abu biyu kawai zan iya fad’a miki yanzu First You are right, bana sonki, you are not my type, sometimes idan muna zance ji nake kamar inyi kuka tsabar takaici, kawai daurewa nake yi, ke to be sincere ni ko irin soyayyar y’an uwan takan nan ma bana yi miki!! Dan haka don’t even think of wai kinyi rejecting d’ina ne Aaima i never loved u you day one….kuma kin da wayo fa for that i salute u sannan Allah ya taimakeki da kika gano gaskiyar lamari, and Yayanki shima yayi playing role wajen ceton rayuwarki because i was planning in yi using naki ne sannan nai dumping saboda Ina so in koyawa Yayanki hankali akan takura min d’in da yake yi. Abu na biyu Kinga ba sonki nake yi ba ko? But abunda Arshaad yayi min ya min ciwo, so ga sak’o inaso ki bashi from me to him, yadda ya rabani dake to kar ya bari in had’u da girl d’insa.” Yana gama fad’an haka ya juya fuuu, ya fice kamar zai tashi sama. Aaima a wajen ta tsugunna ta fashe da kuka, so kawai all this time yana kallontane as a fool?! Sai kuma ta fara maimaita ‘Alhamdulillah’ da Allah ya tseratar da ita. Gabanta ne ya fad’i da ta tuna da abunda ya gama fad’a a kan Huda yanzun, a hankali tace “Allah yasa kar ya yiwa Huda komai.” Tana gama fad’in haka ta mik’e tana goge hawayenta wanda hakan yayi dai dai da fitowar Mammy daga side d’in Arshaad. Salati Mammyn ta saka sannan ta k’araso wajen Aaima ta rik’eta tana “Me yake damunki? wani abun ne ya had’a ki fad’a da Auwal d’in? Mai ya faru???” Murmushi kawai Aaiima tayi kafin tace “ba komai Mammy abune fa ya fad’a mini cikin ido.” Cikata Mammy tayi sannan tace “ke wallahi zan ci Uban ku! Daga ke har Arshaad d’in shima tun d’azu nake ta fama dashi akan ya fad’a min damuwarsa sai k’arya ba komai yake min kuma kina ganinshi kin san yanada matsala! Sannan kema yanzu kin ce min ba komai, kunada wata uwar da ta fini ne??” Share hawaye Aaima tayi tace “Mammy ba komai fa, dan Allah kiyi hak’uri, zan je in kwanta kaina ke ciwo.” “Ba fa inda zaki je sai kin gaya min matsalarki yanzun nan!” Mammyn ta fad’a tana sake rik’o Aaima wadda take k’ok’arin wucewa. Ahankali Aaima tace “Tou shikenan Mammy i promise zan fad’a miki, amman sai gobe da safe plss Dan Allah yanzu kaina ke ciwo.” Cika ta kawai Mammy tayi tace “Allah ya kaimu.” Da alama ranta ya baci dan fuuu ta juya ta nufi nasu hanyar staircase d’in. Sai da Aaima taga shigewarta sannan itama ta kama hanya tayi sama…. Dank’areren parlournta ta wuce ta shige bedroom wanda shima girman sa ya kusan parlour d’in, a hankali ta k’arasa k’ofar toilet ta kama handle dinner ta bud’e, sannan ta shiga…had’add’en band’akin ne mai d’auke da different wajen wanka har uku, shower normal bathtub da wani makeken jacuzzi sai wani had’add’en closet da aka warewa waje shima daban kana hangowa ta toilet d’in. Wayar ta kawai ta ajjiye a kan doguwar drawer gaban k’aton mirror d’in dake cikin toilet d’in sannan ta nufi bathtub ta fad’a ko bathroom slippers d’in dake a k’afarta bata cireba… Ajiyar zuciya ta sauk’e sannan ta sakarwa kanta showern saman bathtub d’in. Ta dad’e a haka jin mura har ya kama ta yasa ta mik’e ta fito tana d’igar ruwa, da kyar ta iya cire kayan jikinta ta d’aura towel ta fad’a gado, tana yin addua ko minti goma ba’ayi ba baccin takaici yayi awon gaba da ita....... Washegari tana fitowa zata yi breakfast a main parlour Mammy ta hau tambayarta. Gaba d’aya ta rasa ya zata yi mata, suna a haka sai ga Arshaad shima ya fito nan ta had’a su tayi ta tambaya.. Aaima ce tace “Mammy bafa wani abun bane ba, kinga shi Yaya wani d’an fad’a suka yi da budurwarshi, shiyasa kika ganshi a haka kuma k’awata ce, shine nima ya had’a dani ya min fad’a wai ai laifi nane.” Da sauri Mammy tace “Wacece wannan d’in? a ina take?” “Huda” Shine abunda Arshaad yace yana mai k’ok’arin b’alle cuff links d’inshi sannan ya k’araso yazo ya kama hannunta yayi kissing kafin yace “Good morning Mammy” “Morning, wait Arshaad Hudan dai wannan d’ayar Yarinyar da Aaima ta tab’a bani labarin an kaisu school d’insu a scholarship har tana yi musu lesson??” “Yep” Shine abunda Arshaad yace yana mai k’arasawa dining table yana cewa Aaima “hurry kin san zamu fita Ina so mu k’arasa b4 12 dan zan je kd a yau.” “Ok” Aaima tace, itama tana k’arasowa dining dan yin break fast d’in. Da sauri Mammy ta k’araso tace “Arshaad wai me yake damunka? Ka san dai ba zan tab’a bari ka auro mini Yarinyar nan ba ko?? Ke kuma Aaima munafuka ai kin san da zancen amma shine baki tab’a gaya min ba!! To bari in gaya maka!! Ka san senator Bashir ai ko? To akwai dota d’inshi takwara tace tun kuna Yara idan zaka tuna Mamanta da sirikina take kiranka, ni a tunani na you are not ready for marriage shiyasa ban fara maganar ba ashe kai kana chan ka lik’ewa y’ar da ubanta ba kowan kowa ba!! Har da wani rashin lafiya jiya a kanta saboda kun yi fad’a!! Tou wallahi ka fita a idona in ba haka ba ranka zaiyi mugun b’aci dan ba zan had’a iri da talakawa ba wallahi!!!.” Murmushi Arshaad yayi sannan ya ajjiye spoon d’in ya mike yace “Mammy Hudan is not poor, ok? She’s is very rich! Kawai dai ban san dalilin da ya sanya iyayenta suka zab’i ta tafi a scholarship ba. Please Mammy dan Allah kar muyi haka dake mana! I luv her a lot so dan Allah kar problems su fara rising daga wajenki plsss. In kikai min auren dole da wanchan Yarinyar da kike magana akai tabbas zaku samu matsala ne dake da friend d’in taki, saboda I cant take care of her daughter tunda ba son ta nake yi ba!. I need your support a kan Hudan please Mammy dan Allah.” Kallonshi ta tsaya tana yi hakan yasa ya sakar mata murmushi yace “thanks, you are the best!!” Bai jira jin mai zata ce ba ya fice yana cewa Aaima “ta sameshi a mota da wuri!”. Da ido Mammy ta bisa har ya fice! Kwafa tayi sannan ta juyo kan Aaima…. Aaima tana ganin haka ta mik’e da gudu tayi hanyar sama tana cewa “Mammy bara in shirya In je kar Ya Arshaad yayi fad’a yace na shanyashi.” Bata wani dad’e ba ta sauk’o, ta d’auro abaya da vail akan English wears d’in jikinta.. Nan ma da gudu ta fita tana cewa “kinga Mammy Yaya har ya fara jera min misscalls, bara in je in na dawo zamu yi magana.” Sarai Mammy ta fahimci dodging d’inta Aaima take yi saboda bata son tayi mata maganar. Ta so tsayar da ita amman kafin ma ta lek’a tuni har an bud’e musu gate sun fice........ BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 26 Abun duniya duk ya bi ya taru ya ishi Mammy.. Hakan yasa ta mik’e, hijab d’inta kawai ta d’auka ta nufi gidan Mom. Tana shiga kuwa kamar had’in baki ta tarar da Ummi itama a falon. Sai da ta nemi waje ta zauna suka d’an gaisa tukunna tace “Alhamdulillah! Da na sameki a nan.” Murmushi Ummi tayi kafin tace “Me kuma ya faru yanzu?” Ajiyar zuciya Mammy ta sauk’e sannan tace “Aaima da Arshaad ne! Wai ace Yaran nan har sun san su had’e mini kai suna k’usk’us a tsakanin su?” Sai a lokacin tukunna Mom tayi magana, tace “Haba Mammy, ai abin farin cikine ma ace y’ay’anka sun had’e kai, kinga bakida matsala kenan dan babu mai iya shiga tsakaninsu!” Murmushin takaici Mammy tayi kafin tace “Na san da wannan Adama, amman abunda nake so ki gane shine ‘da ace abun kirki suke k’ullawa to da sai nafi kowa farin ciki !’. Kin tab’a jin labarin wasu Yara da Aaima take gaya min Arshaad d’in ya kai ya had’ata da su?” Shiruu, su Mom d’in suka yi kamar masu k’ok’arin tuna wani abun kafin chaan! Mom tace “‘Sakina’ kamar naji tace ko? Waenda take cewa d’ayar Yarinyar tana kama da Aslam.” “Allah yayi miki albarka Adama, su dai. To wai d’ayar fa yake so, shine suketa k’us k’us d’insu. Jiya Arshaad d’in inaga har kuka yayi wai ko tak’i d’aukar wayarshi ko fad’a sukaa yi, Oho musu dai.” Ummi ce tace “amman Yaron nan anyi ja’iri! Yanzu ya za muyi da maganar Khadija?? Kin san ko jiya sai da na had’u da Mahaifiyarta a wajen gyaran farce… Tanata tambaya ta ya sirikinta harma take gaya min next week khadijan zata dawo ta kammala masters d’inta.” “Banda Arshaad ma dai da abinshi, da class d’insa da komai amma shine zai je ya d’auko mana wachchar?? Daman wallahi ni jikina sai da ya bani. A yanayin labarin Aaima kamar fa har provision shi yake yi mata lokacin da suke makaranta.” Cewar mom Da sauri Mammy tace “Kinji ko! D’azun nan kuma ya gama cemin ‘ai she’s very rich waye waye kawai dai iyayenta sunyi choosing ta tafi a scholarship ne waye waye’.” Murmushi Mom tayi tace “k’arya yake yi! Aaima ai ta tab’a bawa Auwal Labari, tace Yaran ko ishashshen turanci basu iya ba, ita ta dinga yi musu lesson lokacin tana chan…da zata tafi ma sai da ta had’asu da wasu. Waenna Yara da suka samu good foundation a makarantar kirki ne za a ce basu iya turanci ba saboda Allah?? Kawai dai k’ok’arin watsa mana k’asa a ido yake yi.” Mammy kamar zata yi kuka tace “Ni ba wannan ne problem d’ina ba, dan bai auri Khadijah ba (ya watsamin k’asa a ido) shi ya sani!! Ni babban bak’in ciki na kar ya d’auko min Yarinyar da bata waye ba! Bana son had’a jini da su kwata kwata, zuciyata zata iya bugawa! Kuma yadda yake son Yarinyar nan, in dai ya aure ta to shikenan ni da shi sai dai kallo daga nesa! Dan na san janyeshi zata yi gaba d’aya, gata kuma y’ar matsiyata na san ta dinga sakawa yana yiwa iyayenta abubuwa kenan, a gindinsu kud’insa zasu k’are!”. Murmushi Ummi tayi sannan ta dafa kafad’arta kafin tace

Chapter 21 of 32