Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a tab’a Huda ba, nan ta samu abunyi… Saboda ita aka cire Huda daga makarantar islamiyyar da suke yi aka chanjamata boko kuwa sai da suka san yadda suka yi k’iri k’iri aka hanata zuwa.. Junaidu tun yana dukan Jalila har Sadiya ta bud’e mishi ido ya daina. Haka kurum sai su rufe Huda da duka babu laifin tsaye babu na zaune.. Maryam bata samun sauk’i a kaf fad’in duniyar nan sai in tana karatun Alqurani ko kuma idan Bilkisu da Yaranta sun zo Sakina itace Babba watanni uku Hudan ta bata amman irin Yaran nanne masu garin jiki shiyasa ta zama kamar ma ta girmi Hudan, sai k’anwarta Sumayya. Sakina irin Yaran nan ne da basa barin takwana, takan zo wasu lokutan tayi weekend a gidan itama Hudan takan je musu, ammanfa duk ranar da Sakina tazo sai an kwashi y’an kallo ita da Jalila duk da kuwa Jalilan mugun duka take yi mata amman takanci nasara itama akanta itama wasu lokutan. Akwai ranar da suka yi wani dambe! Jalila tayi mata duka ita kuma da taji zafi ta rarumi dutse ta bugawa Jalilan a kai wanda har saida ya kaita ga suma. Ya Usman da Sadiya kuwa suka d’aukowa Sakina y’an sanda, su kuma y’an sanda da son banza suka zo zasu tafi da ita. Suna shirin sakata a mota kenan daman Babansu ya taho d’aukarsu kuma Mama ta kirasa dan haka ya k’araso a rikice. Ya ji haushin abun sosai dan haka fad’an ya koma na manya akai baram baram da shi da Ya Usman. Tun daga nan suka hana Yaran su zuwa gidajensu. Shiyasa ko lokacin da Bilkisu tace zata d’auki Huda Shuwa ta hanata a cewarta ba zata bari matsalar Maryam ta shafi aurenta ba................. ……………………………… Mama bataji shigowar Sakina da Ummu ba, dafa ta d’in da Ummu tayi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin data lulaaa.. A hankali ta juyo gareta tana kallonta fuskarta sharkaf da hawaye. Numfashi Ummu ta fesar kafin ta tsugunna a gabanta sannan ta shiga share mata hawayen har sai da taga tayi shiru tana sauk’e ajiyar zuciya… Motsa hannun da Huda tayi ne ya katsewa Ummu maganar da take shirin farawa. ..A hankali take bud’e idanuwanta da suka chanza kala suka k’ank’ance. Tana gama bud’ewa hawaye suka shiga zubo mata. Rad’ad’i take ji har yanzu a wajen da Ya Ja’afar ya daketa da katako ga ciwon kan da take ji kamar zata mutu!. Sakina ce ta hau kan gadon ta zauna ta wajen kanta kafin ta kamo hannunta ta kuma shiga share mata hawaye tana cewa “ta yi hak’uri tayi shiru karta k’arawa kanta ciwon.” Da kyar dai itama Hudan tayi shiru. Bayan Likita ta shigone ta chanja mata d’aurin ruwa sannan tayi mata wasu allurai tace “ba zai yiu a sallamesu yau ba sai dai gobe” Kasancewar dare yayi sosai hakan ya sanya Mama ta lallab’a su Ummu suka wuce gida. Ya junaidu kam sai da ya tabbatar sun kintsa ya nemo musu duk abun buk’ata tukunna ya wuce shima. Washegari da sassafe su Ummu suka zo musu da breakfast, bayan sun biya gidan Hajiya sun ajjiye Sumayya dan itama jikin nata sai a hankali. Kamar jiya yau ma har dare Ummu tana wajensu, saboda zazzab’in da ya sake lullub’e Hudan ya sanya Likitocin suka fasa sallamarsu aka kuma k’ara mata allurai masu nauyi da magunguna ta wuni tana barci. Sakina Ummu ta sake aikawa taje gida tayo musu girki ta dawo. Suna zaune wajajen 8 daman kamar Mama ta sani tana ta cewa Ummu ta tashi su tafi sa dawo gobe amman tak’i! Kawai sai ga kiran Hajiya Shuwa, Ummu na d’auka ko gaisuwarta bata amsaba ta hau zazzaga mata bala’i tana cewa “taya zata tafi ta bar mara lafiya haka!? Tabi duk ta wani d’aga hankalinta akan wata Huda, koma meye ya sameta ai sune suka jawa kansu! Tayi maza ta dawo yanzun nan idan ba hakaba ranta sai ya b’aci!”. Sarai Mama taji abinda Hajiya tace saboda wayar Ummu irin mai volume d’in nan ce amman sai ta nuna kamar bata ji ba. Ummu kam jikinta duk yayi sanyi ko tambayar jikin Huda Hajiya bata tsaya yiba tace a taho a barsu su suka sani. Haka nan dai jiki duk ba kwari, ta d’auki jakarta bayan ta tabbatar ta biya komai kuma tabar musu isheshshen kud’i a hannu da alk’awarin gobe da sassafe za su dawo In sha Allah. Suna shirin fita Junaidu kuma yana shirin shigowa da ledoji a hannunshi. Gaisawa suka yi da Ummu sannan yayi mata sai da safe ya shigo. A gefen gadon wajen k’afafunta ya nemi waje ya zauna bayan ya gaida Mama. A hankali yake kallonta yana jin wani zafi a ranshi kafin yace mata “ya jikin?”. Sai da ta gaisheshi bata damu da rashin amsawar shi ba tace masa “da sauk’i” Shiru d’akin yayi babu mai cewa komai kafin a hankali Hudan tace “Mama zan yi sallah.” “To” Maman tace sannan ta mik’e ta fara k’ok’arin d’aga Hudan wadda azaba tasa ta fara yin wani kuka mara sauti abin tausayi. Runtse ido Junaidu yayi kafin yace “Mama idan ba zata iya ba gara kawai a nemo kwano da ruwa, tayi alwala anan tunda daman yanzu jikin nata zai yi tsami sosai.” Hakan kuwan akayi da kyar ta iya zama sannan ta samu tayi alwala tayi sallar. Bayan ta idar ne ya janyo ledojin da ya shigo dasu ya fara bubbud’ewa…. D’ayan fresh milk ne da su maltina, sau d’ayan kuma gasassun kaji ne mai yawa, da zafin su sai maik’o da kamshi suke yi. Mik’ewa yayi ya d’auko plate da cup, kazan ya fara zuba mata kamar rabi, har ya d’auko fresh milk zai zuba mata sai kuma ya d’ago manyan idanuwanshi ya kalleta yace “Me zaki sha??” Cike da jin kunya, dan ya kamata tana kallon kazar daya zuba mata ta nuna mishi Maltina. Murmushi yayi sannan ya ajjiye fresh milk d’in ya d’auki Maltina ya zuba mata kafin ya sake mik’ewa ya dawo kusa da ita ya ajjiye plate d’in akan cinyarta, cup d’in kuma a kan drawer gefen gadon, shi kuma ya tsaya a kanta kafin yace “Bismillah” Har ga Allah so yake yad’an zauna kusa da ita amman kuma yana jin kunyar Mama. Da kyar ta iya cin rabi, daga nan tace masa “ta k’oshi” dan ji tayi cikinta har ya cika taf! Amma da farko lokacin da yana zubawa kamar tace masa ya juye duka. Gyara tsayuwar shi yayi sannan yace “ko ta cinye ko ya d’ura mata!” Ba yadda ta iya haka ta dinga turawa saida yaga tana k’ok’arin yin amai tukunna ya kyaleta. Gaba d’aya Mama itama a takure take, kayana kunya da nauyi duk ya kanainaiyeta. Har ga Allah idan aka tsareta ba zata iya nuna makusa guda d’aya a tare da Junaidu ba. Yaron yana da hankali, gashi yayi karatun shi yanzu haka ma masters yake yi, part time. Yana kuma sana’a dan yana da zuciyar nema, sanna ta san yana son Hudan tsakaninsa da Allah,sosai. To amman matsalar d’aya itace iyayen shi, da ace Junaidu ba d’an Sadiya da Usman baneba da ita da kanta zata tsaya tsayin daka ya auri Huda. Tsakanin d’aa da uwa sai Allah dan ta d’auki lesson akan Jalila, duk runtsi wata rana dole yabi maganar Mahaifiyar shi kuma itama Hudan dole ta yiwa Sadiya biyayya tunda uwar Mijinta ce……ta san Huda ba k’aramin wahala zata sha a hannun Sadiyar ba… Ita kuwa tana ganin wahalar da Huda ta sha daga yarintarta kawo yanzu yaci ace ta samu kwanciyar hankali a gidan aurenta! Apart from all this ma, ta san Sadiya da Usman ba zasu tab’a yadda da auren ba sai dai wani tsananin rabo.. Sallamar Baba Bashir da Baaba Talatu ce ta katse mata tunaninta..ta yi saurin d’agowa tana kallon k’ofa......... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 21 Murmushi Mama tayi kafin ta mik’e ta shiga yi musu ‘sannu da zuwa’. Baba Bashir ta jawa kujera ya zauna, Baaba Talatu da d’an gidan Ya Jamilu mai sunan Madu su kuma ta shimfid’a musu darduma. Bayan sun gaggaisa ne Kaka (Baba Bashir) ya ke tambayar Mama “mai ya faru?,d’azu Bilkisu ta kira take ce musu Hudan na asibiti.” Shiru Maama tayi dan ita harga Allah bata san ta ina zata fara ba, gashi tanajin kunyar su. Junaidu ne yayi gyaran murya, ya hau zayyano musu duk abunda ya faru. Ai kuwa nan Kaka ya hau fad’a! Ta inda yake shiga bata nan yake fita ba A take ya sa aka kira mishi Baba yace masa “yazo yanzun nan yana son ganinshi a asibitin da aka kwantar da Huda.” Bayan kamar minti biyu Baba ya kira Junaidu ya tambayeshi “ko ya san sunan asibitin?” nan ya fad’a mishi harda number d’akin. Suna zaune Baaba Talatu itama tanata bawa Mama baki Baba ya turo k’ofa da sallama a bakinsa ya shigo. Tun kafin ya zauna Kaka yace “Wato Usman ban isa da kai ba ko? Wato na hana su Sadiya zaluntar Yarinyar nan shine ka b’ullo ta hannun Ja’afar ko!? Tayaya ma zaka bari shi da ba ishashshiyar nutsuwa garesa ba ya bugi Yarinya haka?! Haba Usman, katako fa mai k’usoshi a jiki ya maka mata, a ciki!!!. Yaro gaba daya duk ya bi ya haukace? Yo hauka mana, idan ba hauka ba wa zai yi wannan ta’asar saboda Allah? Sannan ku kuma kai da uwar sa sam baku son kuji laifinshi. Lokacin da yake hannun Maryam ai tun farkon fara lalacewar shi sai da ta nutsar da shi amma tun dawowar Sadiya gaba d’aya ya sake tab’arb’arewa! Daga ya saci akuya sai ya saci kaza! Shekaran jiya sai da aka kawo mana k’arar sa akan ya saci zakara!. Kuma abun haushi naira ashirin ko talatin yake saidawa k’arshen tsadar d’ari ko d’ari da hamsin. Mai unguwa da kanshi yace mini ‘dan kawai ya ga jikanmu ne shiyasa yake d’aga mishi k’afa. Usman kai ka san a irin unguwar da muke Abu kad’an suke jira a fara gustiri tsoma! Dan haka tunda kun kasa tsawatar masa ni zan dauk’i mataki! Tun kafin yaje ya janyo mana maganar da tafi wannan in dai baku tashi tsaye a kanshi ya shiryu ba to wallahi kaji na rantse ‘Ni da kaina nan zan kaishi gidan mahaukata!!’.” Da sauri Baba ya d’ago ya kalleshi.. “Kwarai kuwa!” Shine abinda Kaka ya fad’a kafin Baaba Talatu itama ta d’aura da cewa “Yo ai Usman dole a kai sa gidan mahaukata, domin kuwa kwata kwata Jaafar baya yin abun masu hankali, kuma gashi kun barshi a gida yana shirin yin kisan kai!! Idan k’ungiyar masu kare lafiyar d’an Adam taji maganar nan Ina mai tabbatar maka da ‘su zasu fara kaishi kafin mu mu kaishi’! Shekaran jiya fa da Jamilu da iyalinshi suka zo… ga Abba k’arami anan ka tambayeshi kaji ‘a bakin kwata suka sami Jaafar ya tsugunna yana ta shak’a!’ Babbar kwatar layi mai uban d’oyi. Yau Huda ya yiwa zamu iya rufa asiri, gobe ka san wa zai yiwa?? Gaskiya ce muke gaya maka tun wuri kusan abunyi kai da uwarsa da bakwasan jin laifin shi….” Shiru d’akin ya d’auka, a hankali Kaka ya mik’e ya isa inda Hudan take…..shafa kanta yayi yai mata sannu sannan ya cewa Abba k’arami ”su taso su tafi.” Baba talatu ce itama ta mik’e tana mai cewa “Yanzu inda ace Jaafar mai hankali ne ai da tuni shima ya tara iyali Kalli Abba shekara d’aya aka haifesu amma shi y’ay’ansa biyu…. Idan kuka bari so ya rufe muku ido zaku yi dana sani a gaba, dan gaba d’aya rayuwarshi kuke neman lalatawa ba tare da kun sani ba.” Tana gama fad’in haka itama ta yiwa Mama sai da safe sannan tayi hanyar fita tana cewa “ita kuma Hudan idan ta warke ki turo min ita inji waye wannan Yaron da suka ce ya sakota a napep d’in.” “To in sha Allah” Shine abinda Maama tace tana mai sake yi mata “sai da safe” Har zata fita sai kuma ta juyo tace mata “Sadiyar sun zo??” Shiruuu Mama tayi nanma ta kasa magana. Girgiza kai kawai Baaba Talatun tayi tace “Hmmm” Daga haka ta sa kai ta fita. Jikin Mama har rawa yake yi, dan a tunanin ta Baba zai sauk’e mata buhun masifa ne amman sai taga kawai ya juya shima yabi bayansu ya fita. Junaidu ne yace “Ai da idan ina magana akan Ya Ja’afar gani suke yi abin kamar wasa ne.. Gashi yanzu daga anyi zancen ‘gidan mahaukata’ hankalinsa duk ya tashi! Tun ba a je ko’ina ba.” “Allah ya kyauta” shine abinda Mama tace sannan suka d’an shiga tab’a hira ita da Junaidun dan already Hudan tayi bacci. Sai wajen 10:30 tukunna da kyar Mama ta lallab’a shi ya tafi dan daa cewa yayi “a wajen zai kwana” Ita Mama da farko ma dariya ya bata sai da taga dagaske yake tukunna ta nuna mishi ba zai yiu ba…. Washegari da safe wajen k’arfe sha d’aya aka sallameta bayan su Ummu sunzo da Sakina harda Sumayya wadda ta ji sauk’i. Ya Junaidu shima ya zo tare suka zo da matar Ya Jamilu da safe, su suka kawo musu abun kari, bata dad’e ba tace “ya mayar da ita saboda su fara shiri anjima zasu koma.” Ya tafi maidata dake motar mijinta sukai using, bai kai ga dawowa ba aka sallamesu. A motar Mijin Ummu aka mayar da Huda gida, bayan sun siya mata duk magungunanta. Suna zuwa a bakin k’ofa suka tarar da Jalila tana zance da malamin maths d’insu, ko kallonsu bata yi ba haka ma ta nuna kamar bata san dasu a wajenba..da Ummu da Mama ne suka kamo Hudan tana tafiya da kyar, sai da suka zo daff da su kawai Jalilan da doka tsaki ta tofar da yawu a daidai inda zasu taka su wuce su shiga cikin gidan! Sakina ce ta yunk’ura zata tanka mata amman Ummu ta daka mata tsawa tace “ta wuce tayi ciki!” Ba yadda ta iya dolenta tayi shiru, kamar zata fashe ta shige ciki tana gunguni… Haka nan suka wuce ciki ko bi ta kan Jalilan basu yi ba. Tun safe su Ummu basu tafi ba sai daff da Magriba..haka wuni sunata hira ana wasa da dariya a tsakaninsu, d’an uwa mai dad’i! Gaba d’aya sai Mama da Huda suka nemi damuwar su suka rasa…… Haka rayuwa taci gaba da tafiya…. Har Hudan ta warke a tsakanin Sadiya ko Jalila ba wadda tace mata ci kanki! Gidan kuwa haka nan ya koma kacha kacha dan Jalila ba gyarawa take yiba tace waec take yi itama bata da lokaci. Ranar asabar da yamma Hudan ta dawo daga islamiyya kenan, Yaro yayi sallama yace “wai ana son ganin Hudan a waje” Da k’arfi Jalila wadda take m cin abinci ta kware, sai da tayi kusan minti d’aya tana tari idanunta harda hawaye da kyar ta dawo dai dai. Maganar da Yaron ya sake yi ne ya sanya Mama fitiwa tacewa Yaron “kaje kace inji wa?” Fita yayi cikin k’ank’anin lokaci ya dawo yace “Yace wai ace mata Arshaad ne” “To” kawai Mama tace sannan ta koma ciki ta shiga tambayar Huda wadda take chanja uniform d’inta “Waye Arshaad?” Shiruuu! Hudan tayi kamar tana so ta tuna wani abun chan ta d’ago ta cewa Maama “wannan mutumin da ya bani handkerchief d’inshi ne, ranar da su Ya Jalila suka aikeni siyo zob’o.” Ajiyar xuciya Mama ta sauk’e sannan tace “ki maida mishi handkerchief d’insa sannan kice mishi baki fara zance ba!” Zaro ido Huda tayi tace “Mama bafa zance muka yi ba ranar ba ma, kuma yau ma ba zance yazo ba, ba saurayina bane ba.” Kallonta Maman tayi sannan tace “kije ki gaya mishi haka ki dawo da wuri!.” Tana gama fad’in hakan ta juya ta fita zuwa kitchen ba tare data tsaya sauraron amsar da Hudan taketa nanatawa ba akan “itafa ba zance aka zo wajenta ba.” Yaron ne ya sake dawowa da same sak’o! Hakan yasa Hudan ta zira hijabinta ta fito. A soro ta hango Jalila, ta kasa tsaye ta kasa zaune, da alama lek’en sa take yi amman tana ganin Hudan sai ta baasar kawai tayi cikin gida. Arshaad, yana cikin mota a zaune, Abokinshi wanda ya rakosa yanata tsokanarshi, yana cewa “Yanzu Dude!! Saboda Allah a nan kayo matar da kabi ka isheni da ‘kayi mata’ take? may be ma ba right kwatance bane gaskiya, tunda kaga fa har yanzu bata fitoba! Kaga kawai mu juya, kai kanka kace Yarinya ce, maybe ma ba zance take yi ba! Kar ka sa yayanta ya biyo mu da sanda.” Murmushi Arshaad yayi sannan ya juyo ya kalli Jamil wanda shima shi d’in yake kallo! Nuna kanshi yayi da yatsa sannan yace “Ni, In juya?? Hmm tab!! Ai ba wannan zancen! Ka shirya kwana a nan dan yau za aga naci!!.” Dariya Jamil ya kwashe dashi kafin yace “So makaho! Yau ga wanda y’ay’an senators da governors suke hauka akai ya mato akan y’ar gidan Malan shehu!.” Duka Arshaad ya kai mishi sannan yace “Bana son rainin wayo…you beta learn on how to talk about my in-laws dude! And you b……” maganar tasa ce ta sark’e sakamokon hango Hudan da yayi ta fito tana d’an duddubawa da alamun neman wanda aka ce yana neman nata take yi. Motar ta kalla sannan ta d’auke kai tana kallon d’ayan gefen dan ba da motar da suka had’u da shi waccchar ranar yazo ba. Sai da ya duba fuskarsa a mirror d’in gaban motar tukunna ya sa hannu zai bud’e marfin motar ya fita yaji Jamil ya rik’e mishi hannu. Cikin dariyar mugunta Jamil d’in yace “haba Man! Ka d’an ja aji mana..” Fisge hannunshi Arshaad yayi sannan yace “na bar maka ajin yau, ka had’a da naka idan kaje wajen taka sai kayi.” Daga haka ya murd’a hannun murfin motar ya fita. Fitarsa tayi dai dai da sake juyowar Huda, aikuwa suka had’a ido. Tana ganinsa ta gane shi…. Yana sanye da blue jeans mai kyau da wata bak’ar riga mai k’aramin hannu data d’an kama jikinsa, ga wani takalmi sau ciki kamar canvas da bak’in agogo a hannunshi Yayi kyau sosai.! “Me kuma ya kawo shi? oho!” Shine abunda ta fad’a a ranta sannan ta ci gaba da tunanin “Lalle, da ace Mama taga wannan da ba zata ce zance ya zo wajena ba! Wannan ko a mai aiki ba lalle ya yarda ya d’auke niba.” Tunawa tayi da handkerchief d’inshi mai kyau, da Mama tace ta kawo mishi abinshi, wata k’ilan shi ya biyo dan haka ta fara tunanin kalar hak’urin da zata bashi dan ita bata san inda yake ba…… Sallamar da yayi mata ce ta katse mata zancen zucin da take yi. A hankali ta sannan tace masa “ina wuni” tana mai shak’ar wani nutsatsen k’amshin turare da yake tashi daga jikinshi. Murmushi yayi kafin yace “Lafiya Huda, ya gida?” A hankali ta sake cewa “lafiya” dan ji take kamar k’amshin turarensh za sanyata bacci. Ganin tayi shiru yasa yace “Tun last two weeks naso zuwa, amman sai nayi tafiya. Jiya na dawo inata Allah Allah in zo, but sai naga kamar I’m not welcome..” Kamar an fisgi maganar a bakinta tace “Kayi hak’uri ya b’ata ne”. Da mamaki yake kallonta kafin yace “Me??” “Handkerchief” ta bashi amsa. Dariya ma ta bashi….tabbas ya san ya bata handkercheif amman shi yama manta dashi, dan haka kanshi tsaye yace “bashi na biyo ba ai, wajenki na zo.” Still yanzun ma kamar an fizgi maganar a bakinta, tace”Mama tace ince maka bana zance” Sai kuma taji kamar ta nutse a k’asa, taya zata ce mishi haka? bayan ta tabbatar ba wannan ne ma ya kawo sa wajenta ba. Jin shiru yasa ta d’ago kanta cike da jin kunya. Tana d’agowa kuwa suka had’a ido dan shima itan yake kallo yana murmushi…. kafin ya sauk’e ajiyar zuciya yace “To sai yaushe zaki fara zancen??” “Nima ban san lokacin ba” Ta bashi amsa. “To yanzu ya za ayi kenan?” Ya sake tambayarta. Shiruuu, tayi dan ta rasa bakin magana yanzu kam. A hankali yace “ko sai kin tambayi Mama?” Da sauri ta d’aga kai alamar ‘eh’. Murmushi yayi yace “Yaushe zan dawo to inji me tace??” Da sauri tace “a’a bara in shiga In tambayo ta.” This time around sai da yayi dariya kafin yace “No, ki bari jibi zan dawo sai inji me tace, ko?” “To”kawai tace. Ganin yak’i tafiya yasa tace mishi “sai anjima”. Murmushi yayi kafin yace mata “bye” sannan ya fara tafiya da baya yana waving d’inta, har ya kusan motarsa tukunna ya juya ya isa ya bud’e ya shiga. Ita ma ta juya tayi cikin gida… A soro suka kuma cin karo da Jalila, ita dai Huda bata ce mata k’ala ba tayi wucewarta. D’aki ta wuce direct dan bata hango Mama a kitchen ba. Tana zuwa ta fad’a mata yadda suka yi dashi.. Sai da Mama ta d’anyi jim!! Tunkunna tace mata “ta tashi taje da d’aura ruwan miya” dan already Maman ta tuk’a tuwon tun kafin ta dawo a makaranta. Tana fita Mama ta janyo waya ta hau kiran Ummu….. Bayan sun gaisa ne, Cikin d’an rage murya dan taji kamar akwai mutum a k’ofar d’akinta! Ta fad’a mata halin da ake ciki sannan ta k’ara da cewa “Na san cewa Hudan tayi Yarinta yanzu, amma akwai abubuwan da na hango nakeso in taka musu burki tun kafin su zo su fi k’arfin mu. Kinga na farko.. Furucin Baba da yayi na ‘zai aura mata mallan iro mai kayan miya’ nake jin tsoro. Ga su Sadiya su kuma kinga kar su k’ulla mata wani sharrin da zai sanya hatta su Kaka suma su zuciya su bada goyon baya a aura mata mallan iro. Mutumin nan matanshi uku kin sani, kullum ana bala’i a gidan sa ga asirce asirce a tsakaninsu, sannan uwar gidanshi kin san k’awar su Laraba da dillaliya ce, abun ba zai zo da dadi ba! Ni ba wai arzik’in shi na raina ba wannan shine dalilina. Sannan yayi mata girma har ga Allah. Na san su Kaka ba lalle su yarda su bata malan iro ba amman fa munafuki ko d’akin mahaifiyarka ya riga ka shiga to sai ya had’a ku, su Sadiya sunga ta d’an fara tasawa kinga ai har sun fara k’ulla mata sharri, Allah kad’ai ya san me zasu ce a gaba, Ina tsoro kar a b’ata mata suna a zo hatta su Kaka su daina goyon bayanmu! Mai gata ma idan sunan shi ya b’aci ya yake k’arewa? ballantana ita da Mahaifin nata ma cewa yayi kar a fad’a mata ko da sunan shi ne. Abu na biyu kuma shine Junaidu! inaso tun kafin yaje ya samu su Kaka da maganar son auran Hudan, ya zaman ace tanada tsayayye already.. Dan naga take takenshi kenan kwana biyun nan. Harga Allah ba zance miki ga laifin Junaidu ko makusarshiba amman idan Hudan ta auri Junaidu ban san wacce kalar rayuwa zata yi a hannun Sadiya ba, yes na san Junaidu shine Mijin amman ina gudun sharrin Sadiya kina gani fa yanzu yadda ta mayar da Ya Usman sai fa abinda tace tukunna shi akeyi a cikin gidan nan ko b’acin ranta baya so ya gani. Sannan shi kanshi Ya Usman d’in ba son Hudan yake yi ba! Ba zan so ta zauna da irin waennan surakan ba na san zafin k’iyayyar suruki sam babu dad’i kwata kwata! Bana so Huda tayi irin rayuwar da nayi a baya, a wahalar rayuwa da Hudan tasha tun daga tasowarta inaso ace taji dad’i a gidan Mijinta. Sannan abu na uku.. Hudan fa tana zaune ne kawai Ita ba makaranta take zuwa ba ballantana ace tayi facing karatunta, duk wata hanya da suka san zata samu ci gaba k’ok’ari kawai sukeyi su datse. Kaka yana iya bakin k’ok’arin shi amman shima wani lokacin baya iya tankawa saboda halin sharrin mata, akan batun karatun Hudan yadda kika san an datse bakinsu shi da Baaba Talatu. In Allah ya taimaka ta samu mai kishin karatun sai ya barta tayi a d’akin ta, bana so Hudan ta k’are kamar ni kwata kwata… Waennan dalilan ne suka sanya da akace yana son ganin ta kawai na bata sak’on da amsarshi zata sanya in fahimci manufarsa a kantaZ Ni dai a ganina kawai a samu a bincika ko shi waye idan aka dace sai kiga komai ya zo da sauk’i.” 100% Ummu ta yarda da duk bayanan da Mama tayi, dan ji tayi ma kamar Maman ta shiga zuciyarta ne. Dan haka tace mata “Yanzu ya kike ganin za ayi?? Kina ganin idan yaje wajen su Kaka maganar ba zata jewa shi Junaidun ba?” Ajiyar zuciya Maman ta sauk’e kafin tace “Baban Sakina zaki yiwa magana. Yaron zai zo ya gaidashi.. In maganar tayi k’arfi muka ji manufarshi aka sanshi sai ya zo wajen Kaka, Tunda yanzu

Chapter 17 of 32