Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yace “Taya kuke waya to? Ko bakwa yi kwata kwata?” Girgiza kai tayi alamar ‘a’a’ kafin tace “Ai ina saka layi na a wayar Umma lokaci zuwa lokaci.” D’aya daga cikin wayoyinshi ya zaro….wadda bai dad’e da fara anfani da ita ba! Gf d’inshi ce ta bashi ranar birthday d’inshi. Bincika wayar yayi sai da ya tabbatar bashi da wani abu important a ciki kafin ya cire sim d’in shi ya mik’a mata wayar sannan yace “Idan kin shiga sai ki saka layin naki a nan.” Kallonshi tayi sai kuma ta kalli wayar kafin ta sa hannu ta karb’a… D’an zuba mata ido yayi alamun jiran godiyarta yake yi amman sai yaga ita murmurshima take ta yi tanata dudduba wayar tana juyawa Ganin dayayi batama da shirin yi mishi godiya ne yasa kawai ya share ya zaro card d’inshi ya bata yace “ta kirashi ga number shi” Kafin ya sake zaro y’an bandir d’in 5hndred ya mik’a mata yace gashi “ta saka kati!” This time around ko d’an jinkirin da tayi first time na karb’ar waya ma bata yi ba da saurinta ta sa hannu ta karb’a tana murmushi. Shi kam kasa daurewa yayi hakan yasa ya ce mata “Ba ko y’ar godiyar nan?” Kunya ta d’an ji sai kuma ta sunkuyar da kanta k’asa kafin tace “Na gode.” Murmushi yayi ya d’an kalli agogon hannunshi kafin yace “Bara in wuce sai naji kiranki ko?”. D’aga kai tayi ta juyo ta kalleshi tana murmushi. Shima murmushin ya mayar mata sannan ya d’an yi waving nata yace “bye” kafin yad’an matso ya bud’e mata marfin motar.. Sai taji kamar kuma kar ta fita saboda bata son barin sanyi. A hankali tasa k’afarta ta fita sannan ta d’an juyo tace mishi “sai anjima.” Har zata fara tafiya taji yace “Remember, don’t talk to him about me yet!” “To” kawai tace kafin ta juya ta wuce cikin gida. Binta yayi da kallo yana mamakin ‘me Arshaad yake planning akan Yarinyar nan? Da farko da yaga gidan ya d’auka maybe ko saboda kyau ne! Da kuma ya ganta, thou se is beautiful but not to the extend da zaace a guy like Arshaad yayi laying down level d’inshi yazo nan ba Sai ya fara tunanin may be nutsuwa da hankalinta da tarbiyya ne ya jawo hankalinshi gareta! But in less than 1 hour ya fahimci kwata kwata Yarinyar bata da nutsuwa da kalan tarbiyyan da ya kamata ace Arshaad ya sota!. So wat is he up to? Saboda ya san ko giyar wake yasha ba zai tab’a tuntub’ar Granpa a kan auren Yarinyar nan ba! Sai dai idan ko yayi secret marriage ko ya siya musu gida b4 the wedding Ko kuma ma kwata kwata ba aure ne ya kawoshi wajenta ba! Dan ya lura Yarinyar in dai za a bata kud’i to da alama zata yi komai ma! A ranshi kuma sai ya ce “But ai Arshaad is not a humanizer” Wata zuciyar ce tace mishi “Kai dai kawai kaga mutum ka kyaleshi, baka san me yake aikatawa behind closed doors ba!”.’ Murmushi yayi kafin yace “Koma dai menene, na san cewa its important to Arshaad! Ni kuma nayi alk’awarin sai na lalata komai in sha Allah. But Yarinyar nan anya kuwa zan iya tolerating d’inta ko dai kawai mu dinga waya ina turo mata kud’i dan gaskiya she is not my type! Amman kuma anya zata yarda da ni yadda nake buk’ata? Ba tare da ina zuwa muna had’uwa ba kuwa?......” Da waennan tunane tunanen ya ja motarshi yayi gaba.... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 31 Cike da farin ciki Jalila wadda take ji kamar an tsundumata a Aljannah ta shiga cikin gida! A tsakar gidan ta tadda Umma da alama ita take jira.. Ko k’arasowa Jalilan bata yi ba Umma ta hango wayar hannunta da kud’in! Tana zuwa ta bud’e baki zata yi magana kenan Umman ta rufe bakin, ta jata d’aki. Har da rufe k’ofa bayan sun shiga wai duk dan kar a jiyo su! Abunda bata sani ba ‘su Sakinan su kam ba ma sa cikin gidan’ dan tun safe Khadija ta kira su tace “dan Allah su zo ita da Huda su taya ta zab’ar kayan da zata yi amfani dasu da bikin nata.” Suna shiga d’akin k’asa k’asa Umma tace “Ya kuka yi da shi?baki yayi??” Tayi maganar tana kallon hannun Jalilan kafin ta sa hannu ta karb’i wayar ta hau jujjuyawa. Ajiyar zuciya Jalila ta sauk’e sannan ta jefar da mayafinta a kan gado ta nemi guri kan kujera ta zauna kafin tace “Ba Arshaad bane ba! Wai k’aninsa ne, sunanshi Auwal!”. Da mamaki Umma take kallonta kafin tace “Ikon Allah, me ya ce miki tou? Me ya kawoshi? Arshaad d’inne ya turo shi?”. “A’a, wai ce mini yayi wai Arshaad d’in aure zai yi, wai an zab’a mishi wata a gida…Shi kuma Auwal d’in wai yana sona ne zai aure ni! Sannan wai in yi shiru kar inyi magana da Arshaad d’in de komenene dai ni dai ban gane ba gaskiya.” “Ikon Allah!” Shine abunda Umman tace kafin ta sake cewa “Tou ai Alhamdulillah.” Nufar wardrobe d’insu tayi mai b’allalliyar k’ofa. Wajen kayanta ta hau bincikawa da alamun akwai abunda take nema… Cike da son jin k’arin bayani Umma ta matso kusa da ita tace “Jalila ki juyo ki yi mini bayanin da zan gane dan ni sam ban fahimci zancen ki ba.” A d’an razane kuma sai ta tab’ata sannan tace “Ince dai ba Hudan zai auraba ko? Shi Arshaad d’in!”. “A’A” Jalilan tace, kafin ta sake cewa “Kina jina fa nace miki ‘a cikin danginsu aka zab’ar mishi mata! A yadda na fahimta kamar ma fa bai gayawa ita Hudan ba har yanzu.” Wata kalar dariyar mugunta Umma tayi sannan tace “Allah shi k’ara! Sai wani faman hura hanci suke yi su a dole y’arsu zata auri mai kud’i! Ai ga irinta nan.” Sai da ta d’an yi shiru kamar mai tunani kafin ta sake cewa “Ikon Allah, wani hanin ga Allah baiwa ne…Kiga fa babu yadda ban yi dake akan ki fita ku had’u da Yaron nan ba amma Allah bai yi ba! Yanzu fa da tuni ke zai yaudara ya gudu yaje ya auri wata kinaji kina gani. Daman nifa an dad’e ana gaya min cewa ‘In kwantar da hankalina, ba Mijinta bane ba!’. To Amman shi wannan d’in in ce dai mai kud’i ne sosai shima, ko Arshaad d’in ya fishi?”. Juyawa Jalila wadda ta nemo layin ta da kyar a k’ark’ashin hargitsatstsun kayanta, tayi, tana murmushin tambayar! Sai da ta amshi wayar daga hannun Umma ta k’arasa ta zauna a kan yagalgalalliyar kujerar d’akin ta fara neman inda zata saka layin a wayar tukunna ta fara magana “Ai Umma, ba wai Arshaad d’in ne mai kud’in ba Inaga kamar Babansu ne mai kud’in! Domin kuwa shima wannan Auwal d’in yadda kikaga Arshaad tou haka yake.. Da had’add’iyar motar da gayun da yanayin turancin duk! Kina gani kin san ya tsumu a naira! Kinga fatar jikinshi kuwa? Tafin hannunshi laushi kamar.....” Shiruuu, Jalila tayi ta daina k’ok’arin neman inda zata saka layin a wayar, kamar tana tunani…. Mik’ewa ta yi taje inda Umma take tsaye kafin tace “Amma Umma gani nake yi kamar d’an iska ne wannan d’in, ina shiga motar fa ya hau rik’e min hannu! Gaba d’aya ma ni kasa sakewa nayi da shi sosai. Kuma ni Umma har ga Allah Arshaad nake so! Inaga gara kawai ki san yadda zakiyi kawai a fasa auren nashi! Dan ni ya fi kwantamin a rai, shi wannan Auwal d’in gaskiya jinina bai wani d’auke shi ba! Watak’ila mafa kinga d’an iska ne!. Idan ya zo kar In sake fita ko? Harda fa matsa mini hannun ya dinga yi!.” Kallonta Umman tayi na y’an dak’ik’u, kafin tayi k’asa k’asa da murya tace “Jalila anya kin san ciwon kan ki kuwa? Idan kika kuskura kika yi wasa da damar ki Wallahi ki kuka da kanki! Tayaya aka samu kika yi saurayin ma?. Kiga fa Yaron nan wannan shine zuwansa na farko amma kalli abun arzik’i!” Tayi maganar tana nuna waya da kud’in da Auwal ya bayar sannan taci gaba da cewa “Su su Hudan kika san me suke yi?. Ni dai a ganina dan dai rik’e hannu a wagga Yaro mai arzik’i ba laifi bane ba. Yanzu fa rayuwar ta sauya ne gaba d’aya…. A matsayina na uwarki! Ina mai baki shawara ki samu a lallab’a ko ta halin k’ak’a ne a samu ayi auren nan! Muma mu samu muji dad’in rayuwa a dama damu.. Kina gani dai ga yayanki chan a kulle wanda na tabbatar inda ace mu wasu hamshak’an masu arzik’i ne wallahi da tuni sun sake shi. Ki tashi ki tsayawa kanki Jalila, Junaidu yanzu sai ta Allah wanda kin san shi ne yake taimaka mana da kud’i, kuma na san kin san ba don kud’in da yake bani ba da tuni yanzu bana cikin gidan nan! Jiya banyi ishashshen bacci ba tunani kawai nake yi ta yadda zan biya malan Yusuf kud’in aikin da yake bina dan har ya fara yi mini tuni! Sai gashi Allah ya dubamu ya kawo mai bamu amma shine kike k’ok’arin yi mana bak’in ciki ko? Ni dai ban ce kije kiyi abunda bai dace ba amma a iya tunani na da wayo ‘Rik’e hannu ba matsala bace ba’.” Tana gama fad’in haka ta hau dudduba d’akin… Chaan! Ta rarumo mayafinta tana cewa “Bari ma kiga in tashi inje gida! Akwai maganar da ya kamata muyi da Baabaa Laraba. Kin san ance da zafi zafi a kan daki k’arfe.” Shiruu, taga Jalilan tayi kamar mai tunanin wani abu hakan ya sanya ta koma ta zauna a kusa da ita ta dafa ta tace “Ki kwantar da hankalinki, komai zai tafi dai dai. Ki cire wani Arshaad a ranki Allah na tuba me za kiyi da mayaudari? Abu na biyu kuma Kin ga masu kud’in nan sun fimu iya shige shige Idan muka ce zamu raba aurenshi da wachchar y’ar uwar tashi tsaf sai y’an kud’ad’enmu sun kare tass!! Dan haka kawai kiyi abunda yake mai sauk’i, kin ji ko?”. Har zata mik’e sai kuma tace “Yanzu shi wannan d’in a ina yace ya ganki? Sannan shi Arshaad d’in ya aka yi yayi mishi maganar ki? Ni fa ban gane komai ba gaskiya ki fahimtar dani ta yadda zan iya yiwa Baabaa Laraba bayani dalla dalla.” Tsaki Jalilan taja sanann tace “Wallahi Umma yadda baki fahimta ba nima hakan take. Sam sam ban gane me yake nufi ba!.” Da d’an fad’a Umman tace “Kuma baki damu da ki tambaya ba!? Kan ki yanata rawa…” “Umma wai so kike yi in disga kaina ne? Na fad’a miki da turanci yayi ta bayaninshi kuma irin mai saurin nan! Kina ji kin san irin na turawa ne, shiyasa nace miki shima akwai arzik’i dan daga ji ba a k’asar nan yayi karatu ba… Yanayin nasa kalar turancin ba irin nasu Ya Junaidu bane ba. Gashi shima kyakkyawa fari tass kalar hutu.” “Tam shikenan, bara inje mu gani.” Umma tayi maganar tana gyara mayafinta sannan ta d’auki wayarta tana cewa “Alhamdulillah wayata zata huta! Shegen malamin maths mai son bati, saura kuma inji kin kirashi da wannan wayar, ke! Ni kima fita a harkar shi dan yanzu kam kin fi k’arfin shi.” Dariya Jalila tayi itama ta mik’e tana cewa “Wallahi kuwa Ummata.. Bari nima ki ga yanzu inje gidan su Jidda sune masu manyan wayoyi in basu su sakamin sim d’innan dan na kasa. Sannan In d’an saka charji inaga ya manta bai had’a min da charger ba, anjima ina kiranshi zan ce ya taho min da ita idan zai zo, kar in manta.” Haka nan suka fice a gidan, Umma tayi gidansu Ita kuma Jalila ta nufi layin gidansu wachche ta kira da Jidda. Umma tana zuwa gidansu ta tarar ana fad’a da Baaba Laraba da K’asimu da Anty amarya… Ganin kalar zagi da cin mutuncin da K’asimu yake yi wa Baaba Laraba a tsakar gida gaban Yara da ita kanta Anty amaryar ne ya sanya Umma ta jaa Baaba Laraban suka shige d’aki suka bar su sunata rashin mutuncinsu!. Umma ji take kamar tayi super ta dira kan Anty amarya taci ubanta, amma kuma gudu da tsoron karta janyowa uwarta saki yasa kawai ta ja bakinta tayi shiru…..ta san duk bala’in ta K’asimu ya dama ta ya shanye! Yanzun nan zai yi musu abunda basu tab’a tsammaniba. Suna shiga Baaba Laraba ta sa kuka, cikin kukan take cewa “Sadiya wallahi uban ki ba d’an halak bane ba!. Saboda Allah dan yaga yanzu amarya ke bashi kud’in kashewa shike nan ni sai in zama bola? Wanne irin gata ne ban yi mishi ba? Shifa ya karyani a sana’ar tawa saboda yadda nake bashi kud’ad’ena kyauta da bashi! Amman yanzu dan yaga bani da shi shikenan na zama banza kenan?? Da gangan fa Yarinyar nan zata takalo ni da fad’a ina tankawa shikenan zai shigar mata su tisa ni gaba da cin mutunci tsofai tsofai da ni.” Ajiyar zuciya Umma ta sauk’e kafin ta matso ta share mata hawaye sannan tace “Kiyi hak’uri, ki kyalesu, ki daina shiga harkar ta, komai zata yi miki ki kar ki kulata. Ki kwantar da hankalinki in dai na haifu y’ar halak to wallahi sai ta bar gidan nan!! Dama ai babu ce tasa muka barta muka zuba mata ido ko? To yanzu Allah ya kawo mana mafita .......” Nan ta zayyano mata zancen Auwal da Jalila, da kuma maganar auren da Auwal d’in ya zo dashi, da maganar auren Arshaad!! Duk bata bar komai ba. Murmushi Baaba Laraba ta hau yi sannan tasa hannu ta goge ragowar hawayen fuskarta kafin tace “Yanzu ba gwara hakan ba? Ai sai sun fi jin ciwon hakan yanzu akan ace an rabasu tun farko! Abunda nake ta gaya miki kenan tun lokacin da aka ce mana ‘ba Mijinta bane ba’ Wannan ranar nake kwad’ayi gani! Ke kuma duk kika bi kika d’aga hankalinki kika gaza nutsuwa ki fahimceni…akan yana kawo mata abubuwa kuma ita tana fita Jalila tana zaune.. Yanzu tou ba gashi itama Jalilan Allah ya kawo ba?”. Murmushi Umma tayi kafin tace “Ai dama Baabaa kin san ance duk abunda Babba ya hango Yaro ko kan dala ya hau ba zai ganiba. Yanzu menene abun yi? Dan idan mukayi sagegeluwar da su Maryam suka yi to fa muma hakan na iya faruwa da mu.” “Kud’in hannunta da aka bata kin taho da su?” Cewar Baaba Laraba. Baki Umma ta kama kafin tace “Niiiii? Kin dai san halin Jalila da shegen son abunta! Yanzun ma ina lure da ita sai wani kaffa kaffa take yi dan kar ince ta bani. Shiyasa na kyaleta sai munje kwanciya tukunna zan yi mata wayo In karb’a.. Kinga a ciki ma sai ki samu na jari.” “Ya kamata kam”. Shine abunda Baabaa Laraban tace. Daga nan suka hau k’ulla yadda za suyi da Auwal, K’asimu da Anty amarya........ BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 32 Tun azahar! Sai bayan sallar magrib tukunna Hudan da Sakina suka baro gidan Baaba Talatu suka nufi gida. …Tun azahar d’in suna tare da su Anty Zainab wadda suka zo ita da y’arta Khadijah (amarya) ana ta shirye shiryen biki… Yarinyar tana son Hudan sosai sai faman sakota take yi acikin lamuran bikin Anty Zainab ita kuma tana ta gwasalewa har sai da Baaba Talatu ta d’an tsawatar mata….. Ganin Hakan ne ya sanya Hudan ta mik’e ta shige d’akin Baaba Talatu ta barsu nan. Tana shiga ta hau video call da Arshaad, sai da aka kira Magrib tukunna suka yi sallama.. Suna shiga d’akin suka k’arasa da sauri wajen Mama sakamokon hangota da suka yi kwance a duk’unk’une cikin bargo! Dama sun fita sun bar ta tana d’an zazzab’i da ciwon kai!. Sakina tana zuwa tasa hannu ta tab’a goshinta! Aikuwa a rikice ta hau salati… kafin ta shiga cewa Hudan “ta zo maza maza, su fita su nemo adaidaita a kai Maman asibiti! Ko kuma su kira Ummu.” Dan jikinta ba k’aramin zafi ya d’auka ba wanda hakan ya sanya gaba d’aya suka rikice lokaci guda.! Da kyar Maman ta lallab’a su suka hak’ura suka bari akan ‘sai gobe da safe za a kaita asibitin’ A cewarta “ciwon nata, it not that serious.” Tsumman d’ankwali suka jik’o suka hau d’ad’d’aura mata a jiki… A hankali ta fara jin zazzab’in yana sauk’a, dan haka ta mik’e ta nufi bayi domin yin alwala.. Bayan ta idar da sallar ne ta juyo ta kallesu, kafin tace “Kika ce d’azu Arshaad zai zo kuma naga baku dawo ba.” Sakina ce ta karb’e ta hanyar cewa “Eh! Ya kira waya… wai Yayan nashi da zasu zo taren ne bashi da lafiya. So sai gobe za su zo, in sha Allah.” Kamar Maman ba zata ce komai ba, sai kuma tace “D’azu naji kamar Yaro ya shigo yana cewa ‘wai Jalila taje inji Arshaad!’.” “Around what time?” Hudan ta tambaya tana d’an kallon Mama.” “Wajajen biyar dai haka, zuwa, kafin Magrib naji ta shigo.” Murmushi Sakina tayi kafin tace “Iskancin su ne kawai! Maybe wani abun nasu suke son k’ullawa.. Amman ya Arshaad bai ma tab’a ganin Jalila ba! I don’t even think ya san ma tana existing. Ko kin tab’a gaya mishi akwai Jalila a gidan nan?” Ta k’arashe maganar tana kallon Huda.” “A’a” shine abinda Hudan tace Sannan ta d’aura da cewa “Tun wajajen hud’u da rabi ma muke video call da shi, sai da aka kira Magrib tukunna muka kashe.” Jinjina kai Mama tayi alamun cikakkiyar gamsuwa da zancen nasu! Daganan ta mik’e ta gabatar da sallar isha dan har an fara kira… Da kyar ta d’an tab’a abinci (‘ta zarcen’ da suka yi tun rana) shima kuma dan su Hudan sun takura mata ne daga nan tabi gado, su Hudan kuwa basu kwanta da wuri ba! Dan bayan sun yi sallah sun ci abinci sai da suka d’an tattauna akan bikin Khadija wanda da farko Hudan tace “ba zata je ba!” Sai da Sakina tayi mata nuni da yadda amaryar take k’aunarta tukunna ta yarda suka bari akan zata je d’in amma ba zata je har Kaduna ba (dayake a chan za ayi bikin) Ta yarda dai zata je wunin da Baaba Talatu ta had’a anan (Kano) Saboda jama’arta bayan an kawota an dawo Kano, za kuma taje bud’ar Kai gidanta amma gaskiya ba zata je har Kaduna ba! Ta san Mama ma ba lalle taje chan d’in ba.. Dan haka za suyi zaman su idan an dawo Kano suje events d’in Kano…. Haka nan Sakina ta hak’ura, dan taga Huda ta riga ta kafe a kan bakarta. Kamar yadda Umma tayi zato! Bayan ta koma gida… Sai da suka kai ruwa rana tukunna Jalila ta yarda ta bata rabin kud’in shima kuma dan taji Umman tace ‘akan Auwal d’in yayi ta kawowa sannan ya turo da wuri za ayi aikin!!’ Ba dan hakan ba to da ba zata bayarba…. Daga nan ba suyi barci ba sai da Umma ta kokkoyawa Jalila d’abi’u da dabarun karb’ar kud’i a hannunshi. Arshaad yana gama waya da Huda, ya mik’e yayi alwalar Magrib ya fito da zummar zuwa masallaci. Ga mamakinshi a position d’in da ya bar Aslam a haka ya fito ya sameshi! K’arasawa inda yake yayi da sauri ya zauna a kusa da shi… Yana kallon yadda jijiyoyin kanshi suka firfito waje Idanuwanshi suka yi wani irin jaaa! Har abun tsoro. A hankali Arshaad ya shiga lallashinshi..yana kwantar masa da hankali yana bashi baki. Aslam, bai iya ce masa komai ba dan ya kasa magana ma! Ji yake kamar ya b’intike zuciyarshi da kan shi ya jefar sakamokon azababben ciwon da suke yi mishi.. Da kyar ya samu ya iya had’a sentence, yace “Jirani inyi alwala mu tafi mosque”. Yana gama fad’in haka ya mik’e yayi ciki. Bai d’ad’e ba ya fito. Daga nan suka fita a side d’in. Sai da sukayi sallar isha tukunna suka dawo. A parlourn k’asa suka samu Mammy Da kyar Aslam ya iya tsayawa ya gaida ita daganan ya hau jero mata tambayoyi “Tun yaushe?? Mai yasa basu gaya mishi ba??” Shiruuu, Mammyn tayi dan bata da amsar da zata bashi. Ganin haka yasa yace “Bari kawai ya je ya samu Granpa! Dan dole a nemo wani option din saboda ba zai yiu ace dashi da Mahaifiyarshi su d’auwwama a haka ba! Ba zai yiu ba!!” Duk ya bi ya hargitse! In ka ganshi muddin kana da saurin kuka to sai ka koka. Da kyar Mammy ta samu ta lallab’a shi ta hanyar ce mishi “Shima Granpa d’in bai gamsu ba! Yana nan yana ta shirin ganin best neorologiat na kaff duniya a dalilin case d’inta! Sannan Granpa yayi warning d’insu ne akan kar su kuskura su bari Aslam d’in yaji maganar Yanzu Idan ya san yaji ba zai yi duba da ‘Ai Auwal ne ya fad’a ba!’ Ta san had’a su zai yi gabad’ayansu yaci k’aniyarsu Tunda shi dai ya san iyakar parents d’inne suka san zancen so one of them ne ya fad’awa Auwal d’in kenan!. Yayi hak’uri ya kwantar da hankalinshi dan Allah Ko ya samu Granpa ko bai sameshiba dole ta san sai inda k’arfin shi ya k’are wajen nemawa Mommy lafiya Samun nashi kuma da yake shirin yi kawai matsala zai jawowa su Abba Dad Daddy da ita da su Mom. Ya yi ta addu’a a samu a dace adduar ce ta kamata ba wai tado da case a kan case d’in rashin lafiyarta ba, mara lafiya baya buk’atar hakan.” Da kyar da mugun kyar Aslam ya hak’ura da taimokon kalaman Mammy masu k’arfafa guiwa sannan bata barshiba sai da ta bashi full hope akan samun sauk’in Mommy Bi’ixnillah Duk da hakan dai, bai wani sake sosai ba! Haka nan shi kad’ai sai ya zauna yayi ta tunani throughout abun tausayi… Wasan b’uya kuwa gadan gadan ya d’aura d’amarar yi da Mommy dan kayansa ma Arshaad ya sanya yaje ya d’auko ya kawo mishi gidansu side d’inshi (Arshaad) Saboda jikin nata ya motsa wannan karon sosai! Kamar ta san yazo wanda hakan ne yasa da Mammy tayi mishi tayin ya koma chan d’in kawai ya tattara ya koma za suke zama da Arshaad a side d’inshi. Gwaggo Asabe kwata kwata bata so hakan ba amman gudun kar ta sake d’aura mishi wata damuwar a kan wadda yake kai ya sanya kawai ta amince ta bishi da addu’o’i Bilaadadin. Yau da safe suna tashi ya shirya yaje ya gaida su Mom da Ummi da Granmma. Sai wajen 3:00 pm tukunna ya samu ganin su Daddy da Abba A hakan ma wai yau sun dawo da wuri kenan… Daddy aiki yayi mishi yawa har Sundays sai yaje office. Abba kuma akwai company d’insu shi da Aslam d’in da suke son bud’ewa wanda shine abunda ya fitar da shi, ya kuma sanya ya zama busy those days. Sun ji surprise d’in kuwa dan kawai ganinshi kawai suka yi. Sun yi matuk’ar jin dad’in hakan ba kad’an ba Daddy har da y’ar kwallar shi…. Bayan sun gaggaisa ne aka hau hirar yaushe gamo daganan kuma Abba da Aslam d’in suka hau tattaunawa akan company d’in nasu wanda za su bud’e nan da y’an kwanaki k’alilan. Su Daddy kuma suna taya su da wasu shawarwarin… Sai yamma suka rabu bayan sun yi sallar laasar tare. Da kyar da sid’in goshi Aslam ya yarda zai raka Arshaad wajen hudan bayan Mammy ta saka baki. Babu yadda Aaima bata yi akan aje da ita ba amman suka k’i. Haka ta haye sama tanata kumbure kumbure Mammy nayi mata dariya, tana ganin fitarsu tayi murmushi a ranta tace “Bara ku dawo, lokacin da zan bugi cikin Aslam ma ya fad’amin komai akan Yarinyar ba zaka sani ba Tunda naga Auwal ya kasa.” Arshaad ne yake tuk’in Aslam na gefe yana sanye da Top mai gajeran hannu maroon color da d’an ratsi ratsin blue black a jiki sai jeans, blue black . Yayi kyau sosai dukda kuwa simple dressing ne yayi. Arshaad kuma shadda ce a jikinshi yanayin d’inkin zamani mai mugun kyau! Kalar ruwan zuma, ya murza zanna bukar, wadda ta sake fito da ainahin kyawun fuskarshi… Da bak’in agogo da takalmin fata kalar shaddarshi. Kad’an kad’an yake jan Aslam da hira har sai da yaga yad’an saki fuska, dan idan akwai abunda baya son ganin shine Yaga Aslam a irin wannan mood d’in. A k’ofar gidan yayi parking kafin ya zaro waya ya nemo layin ta a recent ya kira yace “Suna waje” Da mamaki Aslam yake kallonshi, kafin yace “Arshaad kana da ishashshen hankali kuwa? Ba kaji shawarar dana baka ba ko? Karka cuci Yarinyar mutane ka b’ata mata lokaci! Kasan ko bayan ran Granpa ba lalle auren nan ya yiu ba dan na san Mammy ma won’t allow it I know her too well!!”. Murmushi kawai Arshaad yayi kafin yace don’t worry, I already have a plan.. Ka bari kawai lokacin yayi.” Da d’an fad’a

Chapter 27 of 32