Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
toothpaste sponge da soap na wanka da na wanki da omo. Gaisuwarta ta sannu da zuwan da take yi mishi ya amsa, kasancewar a gajiye yake sai da ya d’an huta tukunnan yake gaya mata “Ya tambayi mai restaurant d’in nasu ita ta had’a shi da ogan su kai hotel d’in, so ya tambayeshi ko zasu iya zama a d’akin sai a dinga cira a cikin albashin shi? Mutumin ya yarda amman kasancewar idan an cira zai yiwa albashin gib’i sosai yasa aka d’auke room service, dai an basu d’akin ne amman su za suyi komai…” Abinci suka fara ci yana ta bata labari, yau kam ta d’an sake ba laifi, haka nan suka sha hirarsu sosai. Sai da suka gama tace zata yi wanka daga nan ta wanke toilet, so tana so ya bata omo, amman k’iri k’iri yace “taje tayi wankan ta, idan ya shiga shi zai wanke toilet d’in har kayan data cire ma ta barsu a ciki zai wanke!.” Babu yadda bata yi dashi ba amma ya k’i, hakanan ta je tayi wankan, kamar ya sani bayan 10 minutes ya mik’e ya shiga aikuwa ya kama ta tana shirin wanke kayan, sai da yayi da gaske tukunna ta barshi ta fito har inner wears d’inta saida ya had’a ya karb’a, ba yadda ta iya. Tukunna yayi wanka ya wanke toilet ya wanke musu kayansu. Tana zaune tana karatun Al’Qur’ani, ya fito. Sai da ya shirya sannan yazo kusa da ita ya zauna ya kamo hannunta yasa a cikin nashi. Bata kulashi ba sai da ta kai aya sannnan ta juyo bayan ta ajjiye Quranin da d’ayan hannun damanta a gefe,tace “Abba amman kana ganin Mahaifin ka zai hak’ura?? sannan maiyasa baka gaya min haka yake ba? Taya za’ace Yaranka ba zasu shiga familyn Baban su ba? A Ina aka tab’a yin haka?” Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan yace “Maryam, i don’t want to lie to you or give u any false hope! Maganar gaskiya ba lalle ya hak’ura ba!. Ai wannan abunda yayi fa bai ma yi komai ba. Idan na fara baki labarin halinsa, ba lalle ki yadda da wasu abubuwan da yake yi ba. Kuma kinga a case d’innan fa laifi nane, nine na tab’o shi To be sincere I was expecting more than this from him.” B’ata rai tayi sannan ta fara k’ok’arin zare hannunta a cikin nashi kafin tace “yanzu ka kyauta mini kenan??? Abba ba wai fata nake yi ba amman ba a san gawar fari ba!! Yaran mu nake dubawa anan…” Rik’e hannunta yayi sannan yace “Maryam idan akwai abinda zan iya rantse miki akai shine ‘ko bayan taina na san sai dai Yaya da mahaifin mu su raba gari, suyi baram baram indai akan Y’ay’a nane, dan Yaya ba zai tab’a k’in kula Y’ay’ana ba, sannan ga d’ayan Yayan nawa shima na san ba zai yi abandoning Y’ay’ana ba ko da ina raye talkless of ba na raye’. Kawai dai one thing is for sure, na san zan had’a rigima ne, da kuma fad’an da ni kaina ba zan iya kuncewa ba, because..definitely mahaifinmu zai so hana brothers d’ina kulani su kuma ba za suyi mishi biyayya ba when it comes to that! Bar ganin Yaya ya k’i kulamu yanzu, I assure u ba za ayi 3 months ba zakiga ya zo ya fara bibiyata.” With surprise Maryam take kallon shi kafin tace “Amman ka san da duk wannan mai yasa kayi taking risk d’in to? Why do you want to tear apart your own family??.” Murmushi yayi sannan ya matso kusa da ita sosai yayi cupping face d’inta a cikin tafukan hannayensa sannan yayi mata light peck a forehead d’inta… a hankali da idanunsa a lumshe ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace mata “This is worth it!” Tana k’ok’arin janye face d’inta yayi mata wani a kan hanci a hankali ya sake furta “And this” Bai jira d’aukar lokaci ba dan ya fahimci so take ta kwace fuskan nata yayi mata a lips d’inta yace “And this….” Daga nan kuma Maryam ta ji Abba kamar ba shi ba! Duk wani k’ok’arin ta na ganin ta karb’i kanta kasawa tayi, bata tashi sanin abun nashi na gaske bane ba saida taji azaba na shirin d’auke ranta. A b’angaren Abba kuwa yaso suyi sallah kafin komai amman duk yadda ya k’ok’arta hana kanshi sai ya gagara, domin kuwa tun a karan farko shikam ya manta hanyar garinsu ma balle azo kan maganar hana kai! Shiyasa duk kalar kuka da magiyar Maryam d’in tashi ya zamana ba jinta yayi ba...... Ahankali yake shafa kanta yanata murmushi kafin ya janyota jikinshi ya rungume a haka bacci ya kwashesu, ita baccinta na wahala ne shi kuwa na cikar farin ciki da nutsuwa ne. Kiran sallar farko ya tada shi, jikinta yaji yayi zafi da alamar zazzab’i. Wanka ya fara yi ya taimaka mata itama tayi, sannan yaje ya siyo musu abinci da maganin zazzab’in ta! Dariya taso ta bashi dan kwata kwata tak’i kallonshi gashi sai kumbura baki take yi ita ala dole fushi take dashi amman kuma komai idan zata yi sai da taimakon shi. Sai da ya tabbata komai ya kimtsu sannan bata buk’atar komai tukunna ya fita aiki, sai dare ya dawo….yau ma kamar jiya Abba bai kauda kai ba… Maryam tun tana k’i harta daina….. Idan ta ce Abba yana son ta, to tama ragewa soyayyar da yake yi mata a zamansu daraja, dan kalmar so tayi kad’an wajen fasaltawa. Duk wani abu na kulawa da k’auna shi yake gwada mata, ko tsinke baya bari ta d’auka saidai In a bayan idonshi ko In baya nan tayi sauri tayi, ta yadda idan ya dawo aikin ba zai zama dayawa ba. Shi zai yi shara yayi moping ya wanke toilet yayi wanki, sannan duk abinda tace tanaso sai ya nemo mata. Zaman nasu gwanin ban sha awa, yadda yake kyautata mata itama haka take yi mishi biyayya….. Idan aga Maryam indai ba bakinta ta bud’e tayi maka Hausa ba to bazaka tab’a cewa ba balarabiya bace ba…tayi k’iba ta k’ara fari tayi freshi da kyau abinta. A hankali ya siya musu d’an electric gas da d’an kayan abinci suka ajjiye a d’akin, wai ko da wani lokacin tana sha’awar yin girkin gida, amman kuma the funny thing is ‘ya hanata yin girkin’, kasancewar a restaurant yake yanata koyan girki kala kala,idan tace bana sayarwa take son ci ba to yana dawowa break ko kafin ya fita ko bayan ya dawo a aiki zai zage ya girka mata!. Zaman lafiya da k’aunar juna kankat, shine zaman da Maryam da Abba suke yi a Madina. Abu d’aya yake damun Abba rashin tsayayyen aiki, ya kai takardun shi wajaje mabanbanta amman bar yau shiru, bai san daliliba. A kwana a tashi har suka yi 4 months. Yau ma kamar kullum yana wajen aiki, wasu bak’i suka zo Larabawa, da alamun manya ne dan yaga yadda managern nasu yake ta rawar kai, ya jere abinci wajen kala goma yace duk a fitar musu… Tray d’in farko ya fara d’auka ya nufi table d’in da akace suna nan… Tun kafin ya k’araso yaga d’ayan ya kafe shi da ido, yana k’arasowa ya d’an gaidasu kafin ya ajjiye ya fara niyyar juyawa dan ya d’auko musu wani yaji ance “Ya’akub!” Da sauri ya juya jin wannan balarabe ya kira sunan shi rad’au. Suna had’a ido dashi ya tuna shi Abokin Yayansa ne sosai dan yana yawan zuwa gidansu na nan idan sunzo. Sake maimaita sunan balaraben yayi, da d’an murmushi Abba ya amsa sannan ya sake gaishe shi. Amsawa yayi sannan da mamaki yace mishi “aiki yake yi anan!” D’aga mishi kai kawai Abba yayi. D’an jimm!! balaraben yayi kafin ya hau bawa Abokanan tafiyartasa labarin waye Abba. Da mamakinsu suma suka dinga kallonshi kasancewar duk sun san Yahaya MT. Wannan balaraben yake gaya musu irin tarin alkhairan da Yahayan yayi mishi kafin ya juyo kan Ya’akub d’in yace masa “bai yi karatu bane? Maiyasa yake aiki a matsayin waiter?” Da murmushi yace “yazo k’asar ne yayi sabon aure kuma bai san kowa ba shiyasa.” Da d’an fad’a mutumin ya fara cewa “ya za a yi suna garin nan amma Yahaya ya bar k’anin shi haka? ai ko shi waya d’aya kawai zai yi a dauki k’anin shi a aiki, bara yana komawa gida zai kirashi…” Abba bai b’oye musu komai ba yace “Ya d’an samu matsala da Mahaifinsu ne, so idan Yahayan ya taimaka mishi, zai iya involving nashi a case d’in shiyasa.” Cike da gamsuwa balaraben yace “Ina credentials d’inshi? ya kwaso ya zo su tafi yanzu ba sai anjima ba.” Cike da farin ciki ya nufi d’aki, yana murna, ya isa d’akinsu. Yana shiga ya tarar Maryam tana bacci, yaso ya tashe ta ya fad’a mata amman kawai sai ya barta ya kwashi abubuwan da yake buk’ata ya fita a hankali gudun kar ya tada ita. Yana zuwa ya tarar har sun mik’e abincin kad’an suka d’an cachchalkala shi kawai suke jira, shiyasa yana zuwa suka wuce. Bai sha wahala ba kasancewar companyn Baban d’aya daga cikin mutanen da Yayan nashi ya tab’a taimakawa ne, da Mutumin da Baban nasa ne suka yi mishi interview, Allah sarki mutumin da alama yaji dad’in abinda Yahaya yayi mishi dan a wajen ma yanata gayawa Mahaifinshi ai k’anin Yahaya ne. A take ba b’ata lokaci bayan an gama interview aka d’auke shi aiki. Har da ardrobe allowance aka had’a mishi. Sai wajen 5 tukunna ya dawo, da mamaki Maryam take kallonshi yadda ya shigo cike da fara’a..yana shigowa yayi hugging d’inta ya d’agata sama yana juyawa. Sai da ya ajjiyeta yana dariya ya shiga bata labari, ba k’aramin godiya ga Allah da farin cikin tayi ba, ahankali ya sake hugging d’inta yace “Maryam ke good luck ce, kiga fa a yadda muka shigo garin nan amman ko wata biyar bamu yi ba yau nine harda office, sannan ko daidai da rana d’aya bamu tagaiyyaraba.” Cikin murmushi itama ta sa hannu ta rungume shi, suna a haka sukaji knocking!! Mik’ewa yayi yaje ya bud’e aikuwa yana bud’ewa suka yi ido biyu da manager, ko gaisuwarshi bai amsaba ya hau sirfa mishi bala’i yana cewa “Ya bar bak’i d’azu bai k’arasa kai abinciba sai cook d’inne ya kai da kanshi, saboda tsabar yana so ya nuna hotel d’in bashida tsari ko? Sannan tun d’azu aketa neman shi baya nan, ina yaje?” Bai b’oyewa manager d’in ba nan yake gaya mishi “ai aiki ya samu!”. A tunanin Abba managern zai taya shi farin ciki amman sai yaga sab’anin haka dan daga k’arshema cewa yayi ya kwashe kayanshi ya nemi waje tunda ya samu aiki, ai daman ba k’aramin discount suka yi mishi ba, wajen 49%! Dan haka indai yana son yaci gaba da zama to saidai ya ajjiye wanchan aikin yaci gaba da yi musu aiki, yabashi 30 minutes yaje yayi making up mind d’inshi.” Yana gama fad’an haka ya juya ya fita. Tuni Abba ya yanke shawarar barin wajen ya kama haya tunda da d’an kud’i a hannunshi, amman dai sai da ya sake neman shawarar Maryam wadda itama tunaninta ya zo daidai da nashin. Dan haka a mintunan da basu gaza 20 ba sukayi parking komai nasu suka fito. Managern yana ganinsu da kaya ya fahimci decision d’in Abba na barin wajen nasu ne kenan, dan haka ya kuma b’ata rai ko godiyar da Abba yake yi mishi bai amsaba. Shi dai Abba bai damu ba yayi mishi sallama suka nufi cikin kitchen d’in dan ko ba komai ba zai manta da manager ba, kuma idan an d’an kwana biyu in sha Allah zai d’an dinga lek’owa suna gaisawa. A kitchen d’in daman sun tab’a hirar apartments masu sauk’i da cook d’in da suje shiri dan haka ya tambayeshi “inane yake ganin zai fi dacewa ya zauna?” Cike da farin ciki cook d’in yace “apartment d’in da yake zaune akwai security a estate d’in! Ya bashi 3 minutes ya chanja kayanshi ya zo suje sai ya rakashi har gidan mai estate d’in, daman Neighbour d’inshi bai dad’e da tashi ba sai ya karb’i gurin.” Cook d’in yanata murna da taya Abba murnar samun sabon aiki, a haka suka d’unguma, saida suka biya apartment d’in cook d’in, 2 bedroom da parlour da kitchen, anan suka ajjiye kayansu, sannan shi da Abba suka tafi gidan mutumin, aka bar Maryam da matarshi mai mutunci tanata janta a jiki Yaransu uku. Kamar yadda cook d’in yaso kuwa, apartment d’in gefen su aka bawa Abba, bayan ya biya kud’i ya cike duk wani abun buk’ata. Sai wajen 1 suka gama settling…har moping sai da mutumin nan da family d’inshi suka tayasu sannan suka yi musu sallama suka tafi nasu gidan. Washegari da safe Abba ya nufi wajen aiki. Da kyar Abba ya yarda Maryam ta fara aikin kitchen, shima sai da ta saka mishi kuka, saboda ba fita take yi ba sannan ba aikin da take yi, shiyasa gaba d’aya kafafunta har wani kumbura suka yi. Sai da yaga dai rashin exercise d’in ka iya yi mata illa tukunna ya yarda, amman dai shara wannaan aikinsa ne idan ya dawo, wankin toilet kuma kafin ya tafi office da safe tare sukeyi idan sun shiga wanka, wanki kuwa yanzu sunada washing machine abunsu............ Kano, Nigeria. 5months ago… Da mugun gudu Sadiya ta shiga cikin gidansu Maryam bayan taga tashin motar Abba, tana shiga takaici ya rufeta ganin babu kowa. Gidansu ta koma ta sanarwa Baaba Laraba halin da ake ciki dan ta d’an jiyo maganar Maryam d’in da Abba sama sama…Baaba Laraba kuwa sarkin y’an tsurku nan ta zari mayafi tayi waje…Gidan aminiyarta dillaliya ta fara lek’awa ta fesa mata. …Wannan gayawa wannan, kafin awa d’aya labari ya baza unguwa ‘Maryam ta gudu da saurayinta wanda aka kamasu a makaranta suna lalata!’. Har majalisar maza zancen da akeyi kenan, magana har ta kai kunnen tsofaffin unguwa ana ta cewa “Y’ar gidan mai unguwa kuma Limami ta gudu ta bi saurayinta!’. Ana cikin haka Madu da su Shuwa suka dawo, har da Ya Usman wanda jikinshi ya d’anyi sauk’i dan a asibitin a gabanshi aka yanke shawarar aura mishi Maryam da zarar an dawo gida!. Duk da sun san ba a neman aure cikin aure amman zasu je su yiwa Yayan Abba bayani su nemi alfarma a wajensu. Baaba Talatu ma da farin cikin ta ta dawo. Tun kafin su shigar da mota gida K’asimu ya tsayar da motar da yaga Madu da Bashir a ciki, parking Madu yayi a gefe dan ya bawa motar da Ya Jamilu yake tuk’awa damar wucewa, bayan sun fito, ko gaisawa K’asimu bai bari sun yi ba ga y’an unguwa da ganinsu yasa suka k’araso suma domin suji k’arin bayani….ba tare da tauna zance ko lafazi mai kwantar da hankali ba K’asimu ya shiga koro musu bayani kamar a gabanshi aka yi, har da cewa “sai da Maryam da Abban suka gama rungume rungume ma tun kafin su shiga motar su gudu.” Ba tare da Madu ya kula kowa ba ya kamo hannun Baba Bashir suka nufi cikin gidan Baba Bashir d’in, tun kafin su k’arasa shiga ya fara jiyo kukan Shuwa, suna shiga tsakar gidan ciki suka tarar da Baabaa laraba da dillaliya suna ta kora mata bayani tana kuka!. Ya Jamilu ne yace “dan Allah ya isa haka!!” Sannan ya cewa su Sadiya “an gode, ku je, za muji da lamarin!.” Suna fita kamar jira Shuwa take yi ta mik’e ta fara yiwa Madu bala’i kamar ba Mijinta ba, gaba d’aya laifin ta d’aurashi a kansa, a cewarta “Ai shi ya shagwab’a Maryam d’in ,ba dan shi ba da duk haka bata faru ba! Sannan saboda rashin lissafi yaje ya bawa Yaron da bai gama sani ba Y’arsu, gashi yanzu ya gudu da ita!! Wannan wanne irin abin kunya ne, da wanne ido zata kalli jama’a??? Mai zata ce wa mutane?. A yanzu haka Innaa tana kasuwa taje siyowa Maryam kayan d’aki! Shin ta Ina zata fara yi mata bayani idan ta dawo? Mai zata ce mata???” kuka take kamar ranta zai fita tana cewa “Madu ya cuceta duk shi ya jawo mata.” Baba Bashir ne yace “suje gida su duba koina, a dudduba sosai.” Dan shi bai gama yarda da maganar su Sadiya ba......... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 18 Babu inda ba a duba ba, amman babu Maryam babu alamar ta, gaba d’aya hankalin kowa a tashe yake, tunba ma da Innaa ta dawo daga kasuwa nik’i nik’i da kayan d’aki ba!. Babu kalar zagin da bata yiwa Madu ba, Mallan shima yana k’arasowa ya iske mummunan labari. Har dare basu zauna ba domin shi Madu ya dage akan ‘bai yarda Maryam guduwa tayi ba!’. Sune har police station da daddare bayan sallar Isha……..da kyar suka iya cin abinci tun safe….. Suna zaune a gidan Madun, Inna tana ta yada magana tana cewa “Madu ya janyo musu abun kunya! Itakam Allah ma yaso ta tunda idan aka bi tsattso ba a jikinta ya fito ba!! Kuma kowa ya san Shuwanta bata da laifi…”waye waye…. Har sai da taga ran mallan ya b’aci ya fara yi mata bala’i shima, tukunna tayi shiru. Sallamar da aka yi da Madu ce ta katse mata guna gunin da take yi akan ‘itafa shiyasa tun farko bata so auren Shuwa da Madun ba’….. Cikin mutuwar jiki Madu ya mik’e Baba Bashir yana binshi suka fita tare domin amsa kiran da ake yi mishi a waje!. Suna fita suka tarar da dattawan unguwar, da sauri Madu ya k’arasa ya shiga basu hannu yana tambayar su “ko lafiya??” Dan shi a tunanin sa anga Maryam ne. Amma sab’anin hakan sai yaji wai ‘su meeting d’in gaggawa suka zo ayi saboda guduwar da y’arsa tayi, domin kuwa y’an unguwa sunce ya kamata a chanza sabon Limami.!’ Da mamaki yake kallon su, shi yana ta neman y’arsa, su kuma suna ta muk’ami! shiyasa ba tare da b’ata lokaci ba ya sanar musu da ‘ya sauk’a!’. Amman hakan bai sanya sun barshi ba saida suka jashi akaje wajen meeting d’in. Suna zuwa yaga dubban mutane, su kawai ake jira.! Sai a wannan lokacin Madu ya san ba K’asimu kad’ai ba ne mak’iyinsa a layin!! Harda waenda yake ganinsu Abokanan sa duk cikinsu babu ya bi bayanshi.. Mutum uku ne kawai suka bi bayan Baba Bashir wanda Allah sarki dudda halin da Usman yake ciki bai sa ya juyawa Madun baya ba. A lokacin mutanen gurin rabuwa sukayi kashi uku Kashi na farko ‘sune su Baba Bashir su hud’u!’ Kashi na biyu ‘sun ce, y’ar Madu tayi laifi kuma shi ya janyo tunda shine ya shagwab’ata kuma baya son laifinta, amman bai kamata ace laifinta ya hau kanshiba, har a kai ga sauk’e shi ba’. Kashi na uku kuwa (su K’asimu) sunce ‘ai laifinshi ne y’arsa ta gudu yawon karuwanci, tun farko shine ya yi mata lagalaga ya shagwab’ata, baya tsawatar mata duk abinda takeso baya hanata! Haka k’iri k’iri aka koreta a makaranta saboda abunda take yi amman ya rufe yak’i gayawa kowa idan an tambayeshi sai dai yace chanza mata makarantar yake son yi! Ai y’an unguwar da aka taso sama da shekaru ashirin da biyar tare ya kamata ace yanzu an zama d’aya dan haka su ba zasu dinga bin mutumin da yake ha’intarsu! Sallah ba. Su idan matsala ta taso a nasu gidajen tuni sunzo sun saki baki dan neman shawara da yarda da juna, amman shi y’arsa daya kamata ace tun kafin abun ya kai haka a taka burki yak’i yarda ya bada k’ofar yin hakan kuma shima ta bangarenshi bai yi ba, gashi yanzu ta tafi tabi saurayi. Saboda haka.. Su baza su bi uban karuwa ba a masallaci har ma da unguwa.’ Harda cewa ‘ci yake yi da addini.’ Nan suka fara jidar kaya za suyi zanga zanga! Dattawan unguwa na ganin haka suka hau basu hak’uri, sannan a take aka sake sauk’e Madu daga matsayinshi na mai unguwa ma gaba d’aya! Dan a samu a zauna lafiya. Babu kalmar da ta fi b’atawa Madu rai irin na kiran ‘Maryam karuwa da aka yi’ Shiyasa tun baya mayar musu har ya zo yafara mayar musu da martani, da kyar Baba Bashir ya janye sa suka bar wajen sukayi gida. Dishi dishi kawai Madu yake gani, bai san ta Ina zai fara ba, Da kyar ya iya kai kanshi gida. Yana shiga Inna ta tisa shi a gaba da tata mitar, harda d’akko mayafinta tace ‘sai ya kaita gidan Yayan Abba! Ai sunce sun yi bincike dan haka ya kaita ko wajen wani nashi ne…’ Madu kuwa tun rana, suke ziryar zuwa ganin Alhaji Yahaya amman mai gadi yace musu wai yace ‘kar a barsu su shiga!!’. Shiyasa ma abun ya kuma dagule musu, amman dai basu fad’awa kowa ba suna so suyi settling ne a tsakaninsu, shiyasa yanzu furucin Inna ya sake rikitashi!. Ba yadda ya iya hakanan kawai ya sanya Jamilu ya jasu a mota suka nufi gidan, dan bashi da wani sauran energy. Har da Inna da Mallan aka tafi, suna zuwa, daidai motar Alhaji Yahaya tana k’arasowa. Da sauri Madu ya fita ya isa gaban motar tashi ya tsaya!. Alhaji Yahaya ganin an ritsa shi yasa kawai ya fito dan babu yadda zaiyi, a hankali ya k’arasa inda Madun yake wanda isar tashi tayi daidai da k’arasowar su Inna wajen. Duk da rikicin da Madu yake a ciki hakan bai hanashi tsayawa suka gaisa da Alhaji Yahaya wanda ya kasa had’a ido dashi ba. Inna ce ta matso sannan tace “Kai Yaro!! Ina kuka saka mjni jikata?? fito min da ita dan tun yanzu anan zan fara cin uwar ta kafin mu k’arasa gida.” Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan ya juyo ya fuskanci Madu ya fara kwararo masa bayanin duk abinda ya faru tun daga safiyar yau har kawo yanzu, hatta furucin da granpa ya yiwa Maryam akanshi da Shuwa da Bilkisu duk bai b’oye ba. Sannan ya k’ara da cewa “Shima dalilin da yasa, yaketa dudging karsu had’u shine ‘mahaifinsu yace indai ya yarda ya sauraresu to ranshi sai yayi mugun b’aci, kuma sai ya kulle zuri’ar su Madu gaba d’ayansu!’.” Yace “Mahaifin nasu yace ‘babu su babu duk wani abunda ya shafi Maryam da Abba’.” Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan yace “A tunanina zamu iya shawo kanshi, amman ranar da nazo gidan ka bayan mun koma naje na sameshi, b’acin ran dana gani a fuskar shi tabbas yayi matuk’ar tsoratani, shiyasa na cewa Abba ya hak’ura! Amman Yaran zamani kaga abunda suka je sukayi… Ni ban san ta Ina zan fara baka hak’uri ba, amman yanzu dai Ina rok’on ka da kuyi saurin barin nan, mahaifin mu yana da c i ds da yawa especially ma yanzu da case d’innan yake going! Idan yaji labarin na ganku akwai babbar matsala.” Yana gama fad’in haka yayi saurin komawa cikin motarshi ya danna horn mai gadi ya bud’e mishi ya shige ciki da gudu. Da kyar Baba Bashir da Ya Jamilu suka ja Madu suka saka shi a mota, dan daskare musu yayi a wajen kwata kwata yak’i motsi. Duk tsauri da k’ok’arin Madu sai da hawaye ya zubo ta idonsa….. Yanzu wannan itace kalar rayuwar da Maryam d’insa zata yi? Da irin wannan mutumin a matsayin suriki?? Wanda d’an cikinsa ma daya haifa bai sarara wa ba ballantana ita karan kad’a miya!! Gashi k’iri k’iri ya nuna ya tsane ta! Tabbas Maryam guduwa tayi amman aure tayi! Abu d’aya daya sani shine idan zai had’iyi AlQurani yana rantsuwa yana fad’awa mutane Maryam aure tayi babu wanda zai yarda. He is very disappointed in Maryam! Sam bai tab’a tunanin zata iya aikata haka ba! Bai ankaraba yaji fuskarshi ta jik’e sharkaf da hawaye!!! Baba Bashir ma tausayinshi ne yasa ya share tashi kwallar da yake ta k’ok’arin b’oyewa saboda yanaso nunawa Madun kwarin gwiwa. Inna ma duk surutunta tayi shiruuuu! Kamar ruwa ya cinyeta, tabbas ta san Maryam bata kyauta ba, amman ko da irin wannan surikin aka barta hukuncinta yama yi yawa. Haka Mallan shima da Ya Jamilu suma duk sun yi shiru….motar shiru baka jin sautin komai sai na sauk’ar ajiyar zuciyar Madu. A haka suka k’araso, suna shiga suka tarar dasu Baaba Talatu sunyi cirko cirko, nan suka hau tambayarsu, Innaa ce ta fara labarta musu…… Salatin da Shuwa tasa tare da kuka a lokaci daya ne ya juyo da hankalinsu kanta, aikuwa da gudu suka k’araso , sakamokon ganin Madu a k’asa wanwar kamar babu rai a

Chapter 14 of 32