Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zo ta gaishesu. Sai a lokacin ma Ya Usman ya lura da ita, Abokin ne ya amsa yana cewa “uwar gida ya gida?” Da kyar tace “Lafiya” Dan in Abokanan Ya Usman suka ce mata uwar gida duk sai taji wani iri, shiyasa bata tsaya biyewa tsokanarta d’in daya shiga yi ba tayi wucewarta cikin gida. Ta isa k’ofar Baaba Talatu kenan har zata tura taji suna magana, sai da ta kara kunnenta tukunna ta gano ita da Ya Jamilu ne…mamaki da murna takeyi a ranata tace “yaushe ya dawo?”. Har ta fara k’ok’arin shiga sai kuma taji maganar da yake yi daga ji ran shi a b’ace yake dan yana maganane cikin d’aga murya… “Habaa Baaba! Yanzu abunda za a yi an kyauta kenan??? Shi fa Usman d’in da kansa yake ce mini tace ‘bata sonshi’! Garin son sake k’ulla zumunci sai kunje kun yi abinda zai tarwatsa komai!! Ku kanku fa kun san halin Maryam tun tana Yarinya tanada mugun taurin kai!! Ya kamata ku fahimci tunda har tace muku a yanzu wanchan Yaron take so to shi d’in take so a yanzun! Amma baku tsaya kun yi nazari ba, tashi d’aya kun rabota da shi sannan kuma kawai rana tsaka kun zo kun ce zaku d’aura mata aure wannan juma’ar ita da Usman?? Idan wanchan Yaron ne bakwa so kwata kwata ai at least dai kwa bari idan ma auren ne ita da Usman d’in ya kamata a bari su sake fahimtar juna, dan wallahi idan aka yi auren nan bata sonshi a haka a wannan yanayin da take ciki to ba zata tab’a son shi ba.” Baba Talatun ce itama ta rufeshi da fad’a tana cewa “To ubana!!! wanda ya san salon so! Yaushe aka haife ka ne Jamilu?? Bari kaji….rud’u ne yake damun Maryam amman ba wani Abba da takeso ni na san Usman take so, kuma bari kaji, ko da ace bata auri Usman ranar Juma’ar nan ba to tabbas Abban ta zai aurar da ita a sadaka ranar dan yayi wannan alk’awarin, furucin nasa ne ma ya sa Babanku yace ‘ga Usman’ to kaga ai taimakon tama zai yi! Wai dan ma ban ce d’a na ba zai auri ragowar wani ba!?” “Haba! haba!! Baaba, bai kamata ku yarda da zancen su Zainab akan Yarinyar nan ba fa, idan y’an layi suna yamid’id’i kema sai ki biye su? Maryam fa kamar y’a take a wajen ki, kuma kin san basa shiri da Zainab dama.” Da sauri Baaba ta karb’e tana cewa “Ai Maryam bata d’aukeni uwa ba tunda gashi k’iri k’iri tana so ta guji Usman. Kuma kana nufin dan basa shiri da Zainab d’in za ta k’ulla mata sharrine??” Ji tayi Ya Jamilu yaci gaba da magana “Ni dai in za ‘a j....” Maryam kasa tsayawa ta cigaba da jin maganar tasu tayi. Zuwa yanzu ta fahimci komai, tuni fuskarta ta jik’e sharkaf da hawaye da uban gumi…nan da nan ta fara ganin dishi dishi! Da gudu ta fita a gidan ko bi ta kan Ya Usman da yake kiran ta bataiba! Taya mahaifinta wanda yake masifar sonta zai yi sadaka da ita??? lalle kuwa zata kashe kanta, wato sun yarda da maganar mutane akan ta kenan?…. Da wannan tunanin ta isa gida tana shiga falon sukai kicib’us da Madu wanda yake shirin fita .. Goge hawayenta tayi sannan ta durk’usa a gaban shi ta hau magiya “Abba dan Allah ka yi hak’uri, na rantse da Allah sharri aka yi mini, wallahi Abba bana son Ya Usman, kar ka aura mini shi dan Allah…” Zagayeta Madu yayi ya wuce ya fita ba tare da yace mata komai ba. Mik’ewa ta yi ta nufi Shuwa wadda ta fito daga kitchen yanzu itama ta fara yi magiya tana “Hajiya dan Allah ki kulani yau, ki yarda dani wallahi sharri aka yi mini, baba son Ya Usman kar ku yi mini auren dole, wallahi k’arya su Zainab aka yi mini! Yanzu kin yarda da abinda suka ce??” Da sauri Shuwa tace “Na yarda!!! Duk wani abu da aka fad’a na yarda, ko da ace zuciya ta tana son k’aryatawa, to zan tirsasa mata in tilastawa kaina in gasgata hakan ne. Tunda har zaki iya k’etare umarnina! Maryam a nan” Ta yi maganar tana nuna k’ofar kitchen, sannan ta ci gaba “A nan na zaunar dake nace miki ki rabu da wannan Yaron, kika nuna mini kin amince, amman saboda kin raina ni, ban isa in baki shawara ki d’aukaba, kuma ki nuna ban isa dake ba shine kika ci gaba da kulashi!! Jiya principal d’inku duk sai da ta fad’a mana komai har yadda yace “yana son ki a gaban kowa da yake shi bashi da kunya ke kuma kika biye masa bayan kin san da zancen Usman!! Daman na riga na gama yanke shawarar ko ba a kore ki ba to baza ki ci gaba da zama a makarantar ba! Maryam kin bani mamaki matuk’a wallahi, banyi tunanin haka daga gareki ba sam, kuma nima zan baki mamaki, dan wallahi idan baki tsaya kin auri Usman ba to ki saka a ranki babuni babu ke! Idan taurin kai kike tak’ama dashi ina so ki san cewa a wajena kika gada! Da ni dake aga wanda zai janye.” Kuka Maryam ta sake fashewa dashi, ita kuwa Shuwa ta wuce tayi hanyar d’akinta ta barta a wajen…Bilkisu ce ta zo tayi ta lallashinta har aka samu ta d’an yi shiru ta tashi suka tafi dakinta. Haka ta wuni har dare sukuku, tana d’akin taji Baaba Talatu ta shigo tana tambayarta, wai “Usman yace mata d’azu taje ta lab’e mata ita da Jamilu” Shuwa ce tace “Ai yanzu Maryam komai ma akace tayi ba zan musa ba, kiji fa har da lab’e ta koya, tabbas ta yi kam dan nan ta shigo tana ta faman yi mana haukan k’arya….” Nan dai Shuwa ta hau labarta mata yadda sukayi d’azu… “Allah ya kyauta” Baaba Talatu tace. Daga nan suka hau shirye shirye. Bayan sun gama ne taji Baaba Talatu tana cewa “bari ta lek’ata kafin ta tafi, da mugun sauri ta shige bargo ta hau barcin k’arya, tana jinta ta lek’a har fuskarta tana cewa “Ashe ma tayi barci” Ita dai bata kula taba har ta juya ta fita, dan ita yanzu Baaba Talatu ta fara bata mamaki, k’iri k’iiri take nuna son y’ay’anta, sab’anin su Shuwa. Da daddare tana daki ta idar da sallah abun duniya ya mata yawa, ita ta rasa ta gudu ne ko ta tsaya bama ta san ta Ina za ta fara ba amma idan akawai abunda yake da yak’ini akai shine ‘ko sama da k’asa zasu had’e ba zata tab’a yarda da auren Ya Usman ba!!’ Idan ta yarda kenan tama karb’i laifin sharrin da aka k’ala mata ta yarda ta yi d’in kenan!!!Shigowar Shuwa ne ya katse mata tunani. Da sauri ta mik’e ta hau gaisheta, bata amsa mata ba kawai ta juya tace “kije parlourn Abban ku yana son ganinki.” Daganan ta sa kai ta fita. Ninke sallayar Maryam tayi ta bi bayanta ta nufi parlourn Abban nasu. Tana shiga ta sameshi yana shan shayi, da Al’Qurani a hannunshi…sai da ta jira ya kai aya ya rufe sannan ta gaida shi…cikin kulawa ya amsa mata kafin ya ce “Maryama.” A hankali ta amsa kanta a k’asa. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya fara magana cikin nutsuwa… “Ki sani ko da ace duk duniya zasu yarda da abinda akace a kanki ni ba zan tab’a yarda ba.” Da sauri ta d’ago kanta ta kalleshi wasu hawayen farinciki suna gangaro mata, bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba. Gyad’a mata kai yayi sannan yaci gaba “na san halinki na san tarbiyyar ki, fiye da kowa. Amman Maryam ya zama dole a d’aura miki aure ranar juma’ar nan!!”. “Innalillahi wainna ilaihir rajiun.” Shine abunda Maryam ta fara maimaitawa, tana hawaye sannan tace “Abba yanzun fa kace ka yarda da ni.” Jinjina kai yayi alamar ‘eh’, kafin yace “Tabbas Maryam na yarda dake amman kuma auren shine mafi alkhairi a tattare dake, makarantar nan da kika yi sananniyar makaranta ce, yanzu sun baki expel!! Ko kin san cewa babu makarantar da zata d’auke ki da saninsu? Sannan mahaifiyarki tace ‘ba zaki k’ara komawa makaranta ba!’ Zaman me to za ki zauna yi?? Sannan abu na biyu, ban san ya akayi zancen nan ya zagaye gari ba, amman jiya har meeting aka had’a da dattijawan unguwa, saboda ke!! Abun takaicin anan shine ba zan iya kare ki ba saboda all evidences are against u, abunda nake tsayawa tsayin daka dan ganin al’umma basu fad’a ciki ba, yau nine ake zargin y’ata da shi... Maryam da ace kin yi abunda ya kaiki makarantar kawai baki tsaya kula Yaron nan ba da duk haka bata taso ba, yanzu idan shekaru suka yi gaba, ba lalle ki auru ba domin kusan kaf layin nan maganarki akeyi, kuma kin san idan miji ya fitowa mace a wajen y’an unguwar su da makarantar da tayi ake bincika halayenta wanda inada tabbacin ba zasu bada shaida mai kyau a kanki ba! Maryam hakan zai fi yi mini ciwo fiye da aurar dake da zanyi a yanzu, ko ba komai hankalina a kwance yake da Usman, na san zai kula dake matuk’a. Ki yi hak’uri, wanda ya riga ka zama dole zai riga ka tashi, ki rungumi k’addararki, baki da wayo shiyasa aka yi saurin k’ulla miki sharrin da ba zaki iya fitar da kanki ba….” Kukan da Maryam take yi ne ya sanya shi sak’k’owa daga kan kujerar da yake, ya shiga lallashinta da fad’a mata kalamai masu kwantar da hankali har sai da yaga tayi shiru tukunna ya sallameta, jikinta a mace haka ta tashi ta fita. A hankali ya saka yatsarshi ya d’auke kwallar data taru a idonshi, sannan ya koma ya zauna ya jingina da jikin kujerar had’e da lumshe idanuwanshi……. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 13 Maryam tana shiga d’aki ta fad’a kan gado ta fashe da wani mugun kuka…ta kusa awa d’aya tana abu d’aya, idanuwanta duk sun kumbura fuskarta tayi jajawur!!! Sai da tayi mai isarta tukunna ta hak’ura ta shiga sauk’e ajiyar zuciya akai akai…. Kamar wadda ta tuna da wani abun ta mike zumburr!! ta nufi wajen kayanta, k’asan ta d’aga ta zaro wata farar takarda..tun ranar da Abba ya bata takardar bata duba ba, warewa ta shiga yi a hankali, tana gama bud’ewa idanuwanta suka sauk’a kan wasu y’an nambobi a jere waenda ko ba a fad’a mata ba ta san number landline d’inshi ce. “Lalle ma Abba!! wato ma nice zan kirashi!! despite the fact that na yi mishi kwatancen gidanmu!! he didn’t even bother to come. Sannan kuma all this time already yanada wadda zai aura ya tsaya b’ata mini lokaci……Allah ya isanaa!!” Ta fad’i hakan a cikin zuciyarta cikin d’aci da zafin zuciya. Jin zuciyarta tana shirin fashewa ne yasanya ta duk’unk’une takardar ta jefar da ita ta koma ta zauna a kan gado ranta yana sake b’aci. Gaskiya Shuwa ta fad’a da tace mata “b’ata mata lokaci kawai zai yi amma yanada wadda zai aura.’ Dan kuwa gashi ashe Abba yaudarar ta yake yi ita bata sani ba, dan inda ace son gaskiya yake mata ai da zai lek’o ta. Ganin zuciyarta tana shirin fashewa tsabar takaicin abinda take tunanin yayi mata gashi zaai mata auren dole kuma duk shi ya ja amman bai ma damu da ya san halin da take ciki ba, kuma duk yadda ta k’ok’arta ta kasa rabashi da zuciyarta! Hakan ya sanya kawai ta yanke shawarar ta d’auki number ta kirashi, ta fad’a mishi ta fa san yaudararta yayi, at least zata rage wani b’angaren na damuwa takaici da tashin hankalin da take a ciki!! kwana biyun nan. Sai dai kuma Allah yasa yana gidan, dan ta san maybe a time d’innan yana school yanzu…. Da wannan tunanin ta mik’e ta isa inda ta yar da duk’unk’unanniyar takardar….da kyar ta iya bud’ewa dan har sai da ta d’an yage tsabar yadda ta d’unkuleta ta jefar d’azun…Haddace nambobin tayi a kanta sannan ta nufi falo. Kamar ko da yaushe landline d’insu yana kan tebur kusa da tv, kamar munafuka haka ta lek’a kitchen ta tabbatar Shuwa bata nan maybe ko ta fita ne Itada Bilkisu dan gidan shiruu, a hankali ta isa ta murza nambobin ta d’aga ta kara a kunnen ta…ba‘a wani dad’e ba aka d’aga. “Hello who is there?” Taji ance mata A hankali tace “please i want to speak with Abba.” “Ok! hold on, let me tell him.” Mutumin yace sannan taji yana magana “Sir, someone wants to talk to you.” Daga chan nesa taji muryar Abba yana cewa “Who’s it?”kamar bashi da lafiya Jin muryar tasa kuwa da tayi , sai taji kamar rabin damuwarta ya kau, dukda haushin sa da take ji. Mutumin ne ya sake tambayar ta “Ma’am pls what’s your name?” “Maryam” Ta bashi amsa. Tanaji mutumin yace mishi “Maryam.” Kafin kace kwabo muryar Abba har ta iso cikin dodon kunnen ta, da alamun har ya k’araso ya amshi wayar, muryarshi har wani rawa take yi taji yana cewa “Maryam! da gaske kece? Ya kike? how is everything? Zan zo soon, in shaa Allah…i missed you a lot!” Ya fad’a kamar zai yi kuka wanda hakan yasa Maryam ta ji tausayinshi a d’ayan b’angaren zuciyarta kuwa tana ganin rainin hankali irin na Abba wai ‘he missed her!’ amman kuma shine ya kasa zuwa ya ganta?. Murmushin takaici tayi sannan tace “Ai ba zaka damu ka zo ka ganni ba tunda kana da wadda zaka aura, Abba I just call saboda Ina so in tambayeka dalilin da yasa ka tsaya b’ata mini lokaci, bayan ka san an yi maka mata??” Tayi mishi tambayar ranta yana sake b’aci. Murmushi taji yana yi, kafin yace “Even your anger sounds sweet to me Maryam, i‘m just happy Ina jin muryar ki yanzu..” Maryam zuwa yanzu ranta ya b’aci sosai kamar ta fashe da kuka haka take ji… Jin tayi shiru yasa yace “Maryam kema idan kin san kina da wanda zaki aura mai yasa kika tsaya kulani??” Jin tayi shiru yasa shi sake maimaita mata tambayar. A hankali tace “Ni bana sonshi, tun farko” Da sauri yace “nima haka wallahi & Inaso ki san cewa ‘ni Abba na yi miki alk’awarin ke! Zan aura duk runtsi, ko menene zai faru after that I don’t care, i‘ll choose our happiness akan koma.......” Kukan da ta fara yi ne ya saka shi kasa k’arasawa.. nan ya fara tambayarta “mai ya faru??” Cikin sheshshek’ar kuka tace “Abba duk wannan ba shi da amfani yanzu, da ace ka zo ka lallab’a Abban mu da duk hakan bata faru ba, amman ya....” Cikin tare numfashin ta yace “Maryam Yayana ne yayi grounding d’ina for 2 weeks!! Ya ma k’i ya tsaya ya saurareni kwata kwata, gaba d’aya baya kulani… Bayan tafiyar ku ya zo nema mini transfer, shinefa wannan matar ta tisa shi a gaba ta dinga yi mana sharri…Amman kar ki damu, duk fushin da Yaya zai yi dani na san 2 weeks d’innan yana cika ya huce, kuma zai saurareni, daga nan zan zo in sha Allah.. Yau sauran 5 days ai kwanankin su k’are.” Ya fad’a sounding so relieved. “Kafin nan an d’aura mini aure” Ya ji Maryam d’in ta fad’a.. Ba abinci ko ruwa yake sha ba amma wata muguwar kwarewar da yayi sai da ta d’auke shi kusan minti uku yana tari tukunna ya dawo dai dai. Cikin tsananin tashin hankali yace “kiyi mini wasa akan komai Maryam amma banda wannan!! me hakan yake nufi???” Yayi mata tambayar da kakkausar murya… Duk abinda ya faru daga dawowarta zuwa yanzu babu abunda Maryam ta b’oye mishi. Ga mamakinta bai ce mata komai ba, kawai taji ya ajjiye wayar. Ta kai kusan minti d’aya da kan wayar a hannunta, tukunna ta share hawayenta ta ajjiye ta juyo da nufin komawa d’aki suka yi ido biyu da Shuwa. Gabanta ne yayi mugun fad’uwa, cikin rawar jiki da na murya mai cike da in ina ta k’arasa inda Shuwan take ta hau kame kame “Da da ddmn kawai nn ccemishi bai kky…” Wani wawan marin da Shuwa ta kwasheta da shi ne yasa ta kasa k’arasawa, bata dawo dai dai ba ta k’ara mata wani wanda yasa har sai da ta kai k’asa tana shirin tashi ta rufeta da duka….. Sai da Shuwa tayi mata lilis!! kamar ba ita ta tsugunna ta haifeta ba, dan har sai da takai bata iya kuka tsabar azaba, tukunnan ta kyaleta tana mai cewa “Tunda na lura kin daina fahimtar yaren magana watak’il ki fahimci wannan!. Gani kike yi yanzu kinfi k’arfin kowa ko? To ni da ke mu zuba mu gani.” Tana gama fad’in haka ta wuce ta isa wajen landline d’in, ta gwada yafi sau nawa amman dai ko ba’a d’auka bane ko kuma bai tafi ba. A haka tazo ta wuce ta tsallake ta, ta tafi ta barta a kwance a falon tana kukan wahala.. Ganin ba zata iya taimakawa kanta bane yasa kawai ta hak’ura, a wajen baccin wahala ya kwasheta. Kamar a mafarki taji ana tab’a fuskarta ana haskawa da tochila, bud’e idanuwanta taci gaba da yi, bata ganin komai sai hasken fitilar…sama sama take jin muryar Ya Usman yana cewa “Abba ba sai ka kira Likitanba, ta farfad’o. Da sauri Madu ya k’araso yana tamabayarta “mai ya faru? Mai ya sameta?” Bata ida bashi amsa ba Shuwa wadda ke shigowa yanzu tace “Ni da itane.” Da mamaki ya mik’e ya juya yana mata kallon tuhuma kafin yace “ke da ita? ban ganeba.” “Dukanta nayi” ta fad’a tana k’ok’arin wucewa. Da sauri yace “mai yasa??dakata mana!! Ina zakije ana magana! Mai ta yi miki?” Ya fad’i hakan yana k’ok’arin hanata wucewa. Da mamaki Shuwa take kallon shi dan bai tab’a yi mata haka ba. Kallon Maryam d’in tayi da take k’ok’arin zama, sannan tace “Kamata nayi ta kira wanchan Yaron na makarantarsu, tana cewa za a yi mata auren dole… shiyasa na zane ta! tunda kunnenta ya daina jin magana watak’il idan aka tab’a lafiyarta zata fi fahimta tun……” Madu bai bari ta k’arasa ba ya rufeta da fad’a, shi kanshi ya manta rabon da yayi mata fad’a hakan suna a su kad’ai ma, ballantana a gaban Yara. Sai da yayi mata tatas tareda kwakkwaran kashedin kar ta sake dukar masa Y’a, tukunna ya juya ya fita ranshi a mugun b’ace! Shi a ganinshi yanzu Maryam ai ta wuce mari ma ballantana irin wannan dukan, kuma abun haushin ta tsallaketa ta barta ko bi ta kanta ma bata yiba, idan ma mutuwa zatayi bata damuba kenan.! Sai da yaje masallaci ya zauna shi d’aya, daga baya yayita karatun Qur’ani tukunna ya d’an samu zuciyarshi tayi sanyi. Shi kanshi ya san idan akwai abu mafi soyuwa a rayuwar sa to Maryam ce, bayajin akwai uban da yake son Y’arshi a duniyar nan kamar yadda yake son Maryam, shi yasa idan ya tuna ranar Jumaar nan zai aura mata wanda bata so sai yaji gabanshi yana ta fad’uwa, amman bashi da yadda zai yi ne shiyasa, hakan it’s the right thing to do. Ita kuwa Shuwa da kyar ta fita daga shock d’in data shiga na fad’an da Madu ya rufeta da shi, aikuwa akan Maryam itama ta zazzage nata fad’an, kafin ta juya tayi d’akinta. Maryam mamakin yadda Shuwa ta juya mata baya lokaci d’aya take yi, ita kam zata yi k’ok’arin yin yak’i da zuciyarta ta rabu da Abba dan taga abun nasu yana shirin tab’a har zaman lafiyan iyayenta. Muryar Ya Usman ce ta katse mata tunani, da sauri ta d’ago ta kalleshi…a hankali yake ce mata “Ya jikin?” “Da sauk’i” tace dashi, tana k’ok’arin kawar da kanta daga kallonshi, dan bata son ganin fuskarshi! Gani take yi shine ummulabaisin haddasa mata duk wata fitinar da take ciki a yanzu. Sake fuskantar ta yayi ya d’an tsugunna a gabanta sannan yace “Inane yake yi miki ciwo?” Chan k’asa a hankali murya ciki ciki tace “Babu ko ina.” Ta fad’i hakan tana turo baki tana k’ok’arin tattaro ragowar k’arfinta domin ta samu ta mik’e. “Mai kike buk’ata??” Ya sake tambayarta. “Ba komai.” Tace dashi a d’an hassale sannan ta mik’e da sauri dan so take ta bar wajen. Mik’ewa shima yayi, sannan yace “Maryam!”. Tsayawa kawai tayi ba tare da ta amsa ko ta kalleshi ba, dan zuwa yanzu ta fara tunanin anya su Ya Usman basu had’a jini da mayu ba kuwa?…. Maganarshi ce ta katse mata tunani “Ba kya sona ko?” Yayi mata tambayar yana isowa dab da ita. Shiru tayi bata ce komai ba. A hankali ya fara magana.... “Maryam ko baki fad’a ba na san bakya sona a yanzu! Amman inaso ki san wani abu guda d’aya! ‘Ko da ace bana sonki, auran had’i za ayi mana, kika yi wannan tawayen, kika nunawa duniya bakya sona kika zab’i wani a kai na to tabbas ko sama da k’asa zata had’e wallahi sai na aureki!! Ballantana kuma Ina sonki! A yanzu bani da burin da ya wuce In aureki saboda abu uku: ‘Soyayyata a gareki ‘In nuna miki kuskuren ki ‘sannan inaso ki gano soyayya ta da take a cikin zuciyarki wadda wanchan Yaron yake k’ok’arin binnewa… Dan haka shawarata a gareki itace ki daina d’aga hankalinki kina k’ok’arin hana abunda ba zai tab’a hanuwa ba’.” Yana gama fad’in haka ya juya ya fita. Maryam bata samu daman tafiya d’akin da tayi niyya ba, hakan ta koma ta zauna a wajen taci gaba da kuka, har sai da Bilkisu ta zo tayita lallashinta tukunna ta mik’e ta isa d’aki tayi ta jero nafilfilinta.. Dan sai a lokacin ma ta lura ashe dare yayi. Washegari da safe taga anata shirye shirye, zuwa k’arfe d’aya motocin y’an Maiduguri suka fara sauk’a, sai a lokacin ta tabbatar tabbas aurenta za ayi, kuma tayi alk’awari idan son Abba zai kasheta ba zata sake kiranshi a waya ba, dukda ta karb’i uzurin shi da ya gaya mata, kuma ta yadda ba son Yarinyar yake yi ba amman mai yasa zai kashe mata waya? kuma bai ma fad’a mata magana mai dad’i ba da zata d’an kwantar mata da hankali….. Tana wannan tunanin wata cousin d’inta ta shigo ta, suna ganin juna suka hau murna, dan ba laifi suna shiri sosai da Maryam d’in. Bayan sun d’an gaisa tace “turota aka yi ta kirata” Tayi sauri ta je kafin fushin Inna ya k’aru…. Tunda Maryam taji an ambaci inna gabanta ya hau fad’uwa! Haka ta zari gyalenta ta fita jiki ba kwari, cousin d’in tata na biye da ita. Tun kafin ta k’araso Kakar tasu ta fara surfa mata fad’a, da yaren Shuwa da Hausa duk had’awa take yi, dan kaf Shuwa ta labarta mata halin da ake ciki…….tana yi sister’s d’in Shuwa suna tayata, ahaka dai suka yi mata tattass sai kuma aka koma nasiha ana cewa “ta bi zab’in da iyayenta suka yi mata, ta kyale wanchan Yaron waye waye….” Ita dai Maryam tayi shiru tanata kad’a kai kamar k’adangaruwa, sai da suka gama tukunna suka hau yi mata gyaran jiki, bayan nan akace taje tayi wanka anjima akwai kaulu. Nan suka shirya kayayyakin Al’ada da su tabarma wai zasu kai gidan ango, Shuwa kam sai ce musu take yi “ai da sun bari, dan babu wani shirin aure da akayi, babu ma fa tambaya ba komai kawai dai Madu yace jumaar nan zai aurar da ita ga koma waye shi kuma Baban Usman yace ga Usman nan, to maybe sai a masallacin gobe za ai komai a lokaci d’aya kuma a d’aura auren” Amma su dai basu biye taba sai da suka kai kayan tukunna hankalinsu ya kwanta, a cewarsu ai wannan dolene dan ma babu lokaci ne da duk wata al’ada sai sunyi….. Gyaran jikin da aka yiwa Maryam na iya wuni d’aya yayi masifar karb’arta, tayi kyau sosai!! Tana zaune gaban mirror tana shafa mai fitowarta kenan daga wanka, cousin d’inta ta d’azu ta sake shigowa tace mata “Wai Shuwa tace tayi sauri taje parlourn Madu yana nemanta yanzu yanada bak’i.” A gurguje ta shirya ta saka doguwar riga y’ar kanti ta zumbula uban hijabi kalar blue black, ta fita da niyyar idan ta dawo sai tayi shirin Kaulun. Kowa ya kalleta sai ya k’ara, ana ta yaba kyawun da tayi haka tazo ta wuce su ita dai bata cewa ‘k’ala’ sai dai murmushi. Tunda aka ce mata Madu yana kiranta haka nan gabanta yake fad’uwa, tana

Chapter 11 of 32