Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya mik’e tsaye ya gaida Granpa cikin girmamawa. Bai amsa ba sai tambayar d’azu da ya sake jeho mishi!!. A hankali Auwal ya goge wata zufa da ta karyo mishi a goshi sannan yace “Eh, I think so, amman bb ba bamu yi maganar wasu za suzo da ita ba!”. Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin yace “I’m leaving, kazo muje gida sai ka kaisu wajenta! Su yi abunda ya kawosu su wuce.. Make sure basu dad’e ba ka san bana son kwashe kwashe!.” Wani yawu mai mugun d’aci da tauri Auwal ya had’iye kafin yace “Ok Granpa.” Sannan ya bi bayanshi suka fice tare a office d’in hankalinshi a masifar tashe!! Tabbas ya san ba y’an uwan Mom bane suka zo! Ummi ita kad’ai ce cousin d’inta tunda mata biyu kacal kakarsu ta haifa! Da maaman Ummi da Maman Mom Su kuma suka haifi mata d’aya d’aya Ummi da Mom. Sai dai In ko relatives d’in kakar tasu, amman ya san Mom ba huld’a take yi da su ba dan tun tana y’ar k’ank’anuwarta ta kwaso kayanta ta dawo wajen Ummi Gramma ta had’asu ta renesu tare.. Sannan har gobe sai anyi da gaske tukunna take zuwa k’auye wajen Mahaifiyarta ta d’anyi kwana biyu ta dubota ta dawo sam bata son k’auye Sannan Maman nata irin matan nan ne masu fad’in gaskiya da tsananin imani acewarta kenan (mom d’in) D’an mistake kad’an Idan tayi nan zata had’u da fushinta! Hakan ya sanya da taga tafiyar su ba zata zo d’aya ba sannan ita kuma (Mahaifiyar tata) ta k’i zaman birni, ta ajjiye ta a k’auyen ta siya mata gida take tura mata kud’i duk wata, waya ma suna yi amman ba sosai ba. Zuwa kuwa sai tafi shekara bata lek’a ta ba…… Yana wannan tunanin suka k’arasa wajen da suka yi parking motocinsu! Granpa ne ya juyo ya cewa mai gadin da yake tare dasu yana yi musu rakiya “Ina bak’in??” Sai da sojan ya d’an rissina tukunna yace “Suna waje bara inje In shigo da su.” “Okay hurry” Shine abunda Granpa yace yana mai gyara tsayuwar shi a jikin motar. Wasu zufa ne suke tsatsafowa Auwal ta kowacce b’ular gashin dake jikinshi… Da ace Granpa zai lura dashi da kyau to da tabbas a tashi d’aya zai karanto tsananin tashin hankali tsoro da rashin gaskiyar da suke tattare da shi!. Tabbas ya san kashin shi ya bushe yau!! Saboda bashi da tantama wata a cikin y’an matan shi ce ta zo! Duba kuma da irin yanayin halayyarshi tabbas!! Ya san ba alkhairi ne ya kawota ba…. Wata idea ce ta fad’o mishi dan haka da sauri yasa hannu a aljihu ya zaro wayarshi ya shiga message…. Yana gama sending message d’in dai dai su Umma suna k’arasowa wajen tare da wasu masu gadi da suka tayasu d’ibar kayansu. Da mamaki yake kallonsu especially Jalila wadda yaga ta chanza! Itan ma shi take kallo ido cikin ido Tana mamakin yadda ya nutsu a gaban wannan tsohon, kamar ba shin ba. Umma ce ta gaida Granpa wanda taga yana yi musu kallon k’urilla!. Ba tare da ya amsa ba ya cewa Auwal “Did you recognize them?” Sai da ya d’an russunar da kai tukunna yace “No Granpa.” “Call Adama” Granpa ya bashi umarni. Wani sanyi Auwal yaji ya na ratsashi a hankali yace “Ok” kafin ya danna kiran Mom. Ya san ta d’auka amman bai saka wayar a handsfree ba Sai kawai yayi shiru chaan kuma ya kashe! Ya bada kamar minti d’aya dan ta samu ta karanta sak’on nashi sannan ya sake kiranta. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya kalli Granpa yana d’an murmushi yace “Sai yanzu wayar ta shiga inaga ba network ne.” “Umm” kawai Granpa wanda ya fara gajiya da tsauwar yace mishi. Tana d’auka yasa a handsfree a hankali ya gaisheta kafin yace “Ga wasu bak’i nan sunzo wai daga wajen Innaa Ta san da zuwan su?”. Tun kafin yayi shiru tace “Eh! Sun yi chattn da Innar ta gaya mata zuwan su Yarinyar distant relative d’in Innar ce, so za a yi mata aure suna buk’atar kayan d’aki Shine zata d’anyi aikace aikace a gidan kafin lokacin aurenta ya isa! Su biya ta ta tafi.” “Ok tam shikenan.” Auwal d’in yace daga haka ya katse kiran ya juya yana kallon Granpa. Lumshe ido kawai Granpa yayi ya bud’e daga nan ya jinjina kai. “Thankyou Granpa “ shine kawai abunda Auwal yace Daganan ya yafito wasu cleaners ya umarcesu dasu kwashi kayan Jalila su kai motarshi sannan ya zaro kud’i a aljihu ya mik’awa Umma yace “gashi tayi kud’in mota ta koma” Kafin ya kalli Jalila yace mata “muje ko” A hankali ta d’an kalli Umma, da ido Umman tayi mata sign d’in ‘ta bishi’ Kamar ta kurma ihu haka taji amman ba yadda ta iya hakanan ta wuce suka nufi motar tashi… Sai a lokacin Granpa ya juya shima driver d’inshi ya bud’e mishi mota ya shiga yaja suka nufi MT estate.. Motar Granpa na gaba tashi na a baya haka suke tafiya har suka isa makeken gate d’in estate d’in Daga shi har Jalila ba wanda ya kalli wani babu kuma wanda yacl cewa wani uffan! Jikin Jalila har rawa yake yi da aka bud’e musu gate d’in suka danna hancin motar cikin aljannar duniyar da idanuwanta suke gani… Kasa hak’ura tayi kawai ta hau jujjuya kai tanata faman kalle kalle! Tana ganin motar gaban su ta nufi gidan da yafi ko wanne girma aka bud’e ta shige.. Su kuma suka nufi d’aya daga cikin jerin gidajen estate d’in suma aka bud’e musu gate suka shige… Bata san lokacin da tace “woow” tana kallo tana murmushi ba! Tsakin da Auwal ya jaa ne ya d’an dawo da ita hankalinta! A hankali ta d’an muskuta ta gyara zaman ta. Har suka gama ya bud’e motar ya fita bata sake yin motsi ko tace komai ba. Ganin ya fita ne ya sanya itama ta bud’e motar ta fito ta bi bayanshi a ranta tana cewa “Aljannar duniya! Ma shaa Allah.. Wai tab!! Dukiya tana inda take.” K’ofar da taga ya shiga nan itama ta bi ta shige.. A tsaye ta ganshi da wata mata fara y’ar kyakkyawa mai matsakaicin jiki da tsayi suna magana… Tana shigowa duk suka jiyo suna kallonta! A hankali ta tako ta zo inda suke itama ta tsaya: Runtse ido Auwal yayi da mugun k’arfi! Kafin ya juyo inda take tsaye ya d’auke ta da wani mahaukacin marin da saida ya kaita ga kaiwa k’asa!! Bai damu da yadda yaga numfashin ta yana shirin d’aukewa ba! Ya fara k’ok’arin kwance belt d’in wandon jikinshi… Ko takan Mom wadda take ta k’ok’arin tsaidashi bai bi ba Haka ya ture ta gefe ya hau zulawa Jalila belt d’in da ya samu nasarar zarowa daga k’ugunsa! Sai da yayi mata uku tukunna Mom ta samu ta tureshi gefe da kyar!!! Cikin fad’a tace “Baka da hankali? baka jin yadda take kurma uban ihu sai wani yaji ya shigo?” In banda huci ba abunda yake yi, tare da da aikawa Jalila wani k’ask’antccen kallo wanda yake cike da tsana! Dai dai nan Ummi ta shigo. Kallonsu take tana mamakin yadda Auwal yake tsaye da belt a hannu yana ta faman huci, ga kuma Yarinya a kwance a k’asa tanata faman kuka!! Wanda ta tabbatar ihun ta take jiyowa tun a compound. A hankali Jalila ta fara k’ok’arin tashi… Hannu Ummi wadda ta k’araso yanzu ta saka ta d’ago ta ba tare da ta kalletaba tace musu “Lafiya? Mai ya faru?” Tayi maganar tana kallon Mom. Mom ta bud’e baki za tayi magana kenan Jalila wadda ta k’arasa inda take ta d’auketa da mari!!! Basu gama fita daga wannan shock d’in ba kawai suka ga ta wage baki ta fara kwala kiran “Granpa” da mugun k’arfi!!!!. “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”shine abunda Ummi ta hau maimaitawa kafin a gigice tace “Adama wacce mahaukaciyar Yarinya ce wanna?? Meye haka take yi? Ku yi mini magana mana!! Ke yanzu tsabar rashin d’a’a wannan bata haifeki ba?!” Ummi duk tana maganar ne cikin tsananin tsoro da firgice dan yadda Jalila take kiran Granpa tabbas in dai wani ya zo wucewa ta gefen gidan sai ya jiyota ta!! Gashi estate d’in tsit!! So definitely muryar ta zai iya fita koina ma. Cikin tsananin tashin hankali mamaki da firgici da tsoro Auwal ya k’arasa inda take ya mata wata wawuyar shak’a!! Ba yadda su Ummi basu yi ba amman suka kasa kwatar ta a hannunshi… Ita kanta Jalila hannunta na a kan nashi da niyyar kwatar kanta amman ta kasa b’amb’are hannun nashi saboda ba k’aramin ruk’o ya yiwa wuyan nata ba!. Ganin yana shirin kaita lahira ne ya sanya ta tak’ark’are ta sa dukkannin ragowar k’arfinta ta d’aga k’afarta guda d’aya ta daki tsakiyan k’afafunsa da mugun k’arfi!! A rikice ya cikata ya durk’usa a wajen yana jin azabar da bai tab’a jin kwatakwacinta ba!. Ita kuma ta durk’ushe a wajen ta hau tarin wahala… A tsorace Ummi tace “Adama ku yi mini bayani dan Allah Ina kuka samo wannan y’ar dabar??” Mik’ewa Jalila tayi tana d’an tari kad’an kad’an tace “Y’ar daba ko? Ai gwara ni y’ar daba ce kuma a kan gaskiya ta sannan a wajen kwatar hakkina nake dabancin! D’anku fa? Shi baku ga abunda yayi mini ba? Baya ga dabancin daya gama nunawa a nan kunsan me yayi min? kun san ya alak’a ta take da shi???” A hankali Mom ta lumshe idanunta kafin ta bud’e su ta d’aura akan Auwal wanda ya mik’e yanzun nan tace “Auwal plss tell me you did not!!!” Ta fad’i hakan wani hawayen takaici yana zubo mata daga ido daya. A hankali ta d’an matsa gabanshi ta tsaya ta sake cewa “Dan Allah Of all people Auwal kar ka ce mini akwai wata mummunar alak’a tsakaninka da wannan Yarinyar!.” Murmushi Jalila tayi kafin tace “Tab!! Hajiya Adama ai kuwa ki tanadi drip mota mota dan na san hawayenki sai sun k’are tass kin buk’aci ruwa a wannan jikin naki! Bari kiji in gaya miki bayan mummunar alak’ar dake a tsakaninmu har da jika ko jikar ki nake k’unshe da a wannan cikin nawa da kike gani!” Tayi maganar tana shafa cikin. A zabure gaba d’ayansu suka juyo suna kallonta har Auwal! Kamar zaki haka ya sake fincikota ta matso daff dashi kafin yace “K’arya kike yi wallahi!! K’arya kike yi ki samu ciki da ni bayan magungunan da na baki kike sha kullum da safe for good 3 days!” Tunkud’e shi tayi cikin had’e fuska tace “Auwal in banda kai dak’iki ne! Taya kake tunanin zan ci ko in sha abun da ya fito daga hannunka bayan abunda ka yi mini a waennan kwanaki, ba tare da na san ingancin su ba?? Lura ne baka yi ba amman ko abinci ko ruwa idan ka kawo sai na tabbatar da kaci na gani a gaban idona tukunna nake ci nima… Saboda haka Duk wasu magungunan da kake tunanin ka bani fakar idonka nake yi in b’oye a k’asan pillow sannan inyi kamar nasa a bakina Kana fita nake yin flushing d’insu a Masai! Dan haka In Akwai wadda zakace ba zata yi ciki ba to Masai ce! Amman ba dai ni Jalila bint Usman ba!!!” Dafe kai kawai Auwal yayi ya lumshe idanuwanshi! Wani kalar sarawa yake ji kanshi yanayi bana wasa ba! Shi? Jininshi? Da na Jalila? Inaaaa, ba zai yiu ba wallahi!!! Yana cikin wannan tunanin yaji tace “Idan kuma baku yarda ba Kuna iya zuwa muje akwai wani test da akeyi wani abu ‘NA’ haka dai.. Na san ku kun sanshi Sai muje ayi a tabbatar muku amman kafin nan inaso ku nanamin d’akina in d’an shiga In huta in yi wanka! Dan gaba d’aya ilahirin jikina ciwo suke yi, sam! Ban saba da duka ba… Sannan a had’o min abinci mai rai da lafiya dan....” A fusace taga Auwal ya k’araso inda take, cikin tsananin b’acin rai yace “Kin san Allah? In kika kaini bango zan kasheki In kashe banza wallahi!! Banza dak’ik’iyar Yarinya!! Bari kiji in gaya miki ko taku d’aya ba zaki sake yi forward ciki gidan nan ba sai dai backward!! Sannan cikin nan yanzun nan za aje a zubar da shi! Ko kinaso ko bakya so wallahi!! Daga nan ko suna na kika sake kira by mistake ma, sai na datse miki harshe.” Wata dariyar rainin wayo ta saka wanda hakan ba k’aramin sake k’ular da Auwal yayi ba. Sai da ta d’an tsagaita sannan tace “To shikenan! Naji ba zan shigar muku gida ba amma inaso ka sani Billahilazim Wallahi Tallahi! Na fita daga nan direct gidan da naga wannann tsohon wanda naga kana mugun jin tsoro ya shiga nan!! Nima zan nufa Kuma idan naje sai na fad’a mishi komai!! Sannan ince ayi test da jininka dana d’an da yake cikina aga idan k’arya nake yi” Tana gama fadin haka ta juya zata fita. Da sauri Ummi ta ruk’o hannunta… Fincike hannun nata tayi kafin tace “Ai ke kad’ai ce naga alamar kina buk’atar sulhu amman da shi da uwarsa sam basa buk’ata! Dan haka daga nan gidan Granpa na nufa..” A hankali taji Mom tace “Tsaya” Da sauri Auwal ya juyo yace “Mom! Wannan Yarinyar shed’an ce Ki barni da ita i can handle her wallahi ba zata.....” Cikin katseshi Mom tace “I think you have done enough Auwal!! Zaka barni in gyara kuskurenka? Ko kuma in barka kaci gaba da lalata rayuwarka??” A hankali Ummi tace “Wuce kaje kawai Auwal za mu san abun yi kaji ko?” Ji yake kamar ya rufe Jalila da duka har sai yaga bata numfashi tukunna ya barta. A hankali yaji Ummi ta sake cewa “Kaje kawai, kaji?” Sai da ya sauk’e wata k’akk’arfar ajiyar zuciya tukunna ya dallawa Jalila wadda ta tsareshi da manyan idanuwanta harara! Ya saka kai fuu!! Ya fice daga gidan ko belt d’inshi bai tsaya d’auka ba. Tab’e baki kawai tayi ta d’auke kai “Muje in kai ki d’akinki” Shine abunda Mom tace mata ta juya tayi gaba. A k’asa ta nuna mata guess room amman Jalila furr tace “wallahi ba zata zauna a k’asa ba! Ya za ai tana ganin gida mai bene har biyu amman a ajjiye ta a k’asa?” Ba yadda Mom ta iya haka tasa masu aiki suka kai mata kayanta d’akin sama na bak’i! A chan gefen side d’in Auwal. Sannan suka gyara suka goge aka wanke band’akin. K’iri k’iri tana zaune Mom ta sanya cook tayi mata Girki Bata ce musu ba zata ci ba sai da cook d’in ta kawo ta ajjiye sannan tace “Allankatafir ba zata ci girkin kafira ba! Sai dai Mom ta dafa mata da kanta… Cikin tsananin b’acin rai Ummi wadda take tolerating d’inta tun d’azu da kyar tace “Wannan ne kuma baki Isa ba wallahi sai dai ki kwana da yunwa!” Jalila ta mik’e kenan zata fara zuba tujara sukaji sallamar Daddy Ganin da tayi su Mom sun maida hankalinsu gaba d’aya a bakin k’ofar ne ya sanya itama ta juya tana kallon wajen. A hankali Mom ta runtse idanuwanta da suka yi jaaa ta bud’e tace “zan yi miki” sannan ta nufi wajenshi. Da mamaki yake kallonsu yana kallon Jalilan dan bai gane ta ba! Kuma kamar y’ar hayaniya ya jiyo suna yi, hakan ya sanya ko gaisuwar Mom bai amsa da kyau ba yace mata “wacece wannan?” Yayi maganar yana kallon Jalila da itama ta nufi wajen su. Da sauri Mom tace “Yarinyar wata distant relative d’in inna ce! akwai y’an aikace aikacen da zata tayani, zuwa k’arshen watannan sai in biyata in sallameta saboda suma suna buk’atar kud’in, aure zata yi so suna buk’atar na siyan kayan d’aki!.” Murmushi Daddy yayi kafin yace “Shine kuma har sai tayi aiki? Ko ba relative d’in Innaa naji kin ce ba?. Kamar nawa ne ta fad’a miki suke buk’ata d’in sai a bayar ai ko? Besides muna da masu aiki enough ai wanne kuma zata yi?”. A hankali tace “Muje ka huta kaci abinci ko? Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya amsa gaisuwar Jalilan sanann ya wuce sama. Babu yadda Daddy bai yi da Mom akan ta maida Jalila ba amman k’iri k’iri ta dinga kaucewa tana kawo mishi wasu silky excuses d’inta.. A gajiye yake shiyasa kawai ya rabu da ita. Ba abunda yafi d’aga mishi hankali sai yadda yaga d’akin Jalilan a sama gefen side d’in Auwal! Da daddare bayan Jalila taci ta sha tayi wanka ta zo kwanciya Ta kira Umma.. Tun daga lokacin da suka rabu ta kwashe komai ta gaya mata sannan tace “Umma in gaya mikii jikan Mai Turare ne Unguwa ce dasu guda! Ina ga shida y’ay’an shi ne da jikokinshi.. Anan gidansu Auwal d’in yake. A bakin gate d’in shiga unguwar tasu an rubuta Mai Turare.” Cike da tsantasr farin ciki Umman tace “To ai hakan yayi dede, kai amman naji dad’i sosai! Yanzu abunda neke so dake shine ‘karki kuskura ki raga musu! Da shi da uwarsa da wannan wadda kika ce aunty d’in nan nasa’ Ina fatan kin fahimci rashin tsoronsu d’in da kika nuna shi ya kwace ki har ya kaiki ga ci gaba da zama a gidan?” Da sauri tace “Tabbas kam hakanne” Ajiyar zuciya Umman ta sauk’e kafin tace “To inaso ki tashi ki tsayawa kanki nima kuma Ina nan Ina tayaki! Sannan duk bayan sati biyu ki saka mishi saiya dinga biyanki kud’in kayan kwalliya da buk’atun yau da kullum. Sannan ki tashi ki tsaya ko yaya za suyi dake ki nuna musu ba zaki tab’a yarda ki zubar da cikin ba! Ni na san yadda zan yi daga k’arshe..” A hankali Jalila tace “Umma to ya za muyi da Baba?” “Kar ki damu! Zan ce masa kin bi Hansai Daman ya san da zancen za tayi tafiya Inta kama ma Kaka zan saka yayi mishi magana Yadda ba zai iya cewa a’a ba Kar ki damu na san me zan yi. Sannan abu na gaba Kar ki damu in shaa Allah zan tsaya miki ki auri Arshaad bi’izinillahi Ta’ala Tunda yanzu dai babu maganar aurenshi da kowa in ba Hudan ba Huda kuwa k’aramin alhaki ce dan karki damu ki bar mini komai a hannuna kinji?” Cike da farin ciki Jalila tace “na gode sosai Ummana” Murmushi Umman tayi suka d’an yi hirara su Jalilan tana ta bata labarin bahon da tayi wanka aciki da gadon da take kai da d’akin da komai… Daga baya suka yi sallama bayan Umman ta gaya mata itama gobe da safe zata wuce Kaduna biki. ..... Washegari da safe sai wajajen goma ta samu ta farka. Sai da tayi wanka tukunna ta fito parlourn k’asa. Kamar masu meeting haka ta tarar da Mammy Ummi da Mom sun had’a kai ko sauk’owarta ba su ji ba! A ranta tace “guda d’aya ta k’aru kenan!” Bata ko kalli inda suke ba ta tako ta zo ta wuce su zuwa dining.. Kamar daga sama taji Mammy tace “Baki iya gaisuwa ba?” Da sauri Mom tace “Ki rabu da ita kawai mana! Bana son rikici da safen nan wallahi.” Cikin b’acin rai Ummi tace “Ai dama na gaya miki!! It’s like kamar fa tsoronta ma take ji! Ni kam ba zan iya zaman ganin abun takaici ba! Sai anjimanku.” Tana gama fad’in haka ta mik’e tayi hanyar fita. Jalila tana ganinta amman tak’i matsawa Ita kuwa Ummi tana zuwa tabi ta kan k’afarta ta wuce “Da sauri ta ruk’o mayafinta Sai kuma ta durk’usa a wajen ta kurma wani uban ihu!!! A razane Mom ta taso.. Mammy kuwa tsaki kawai taja tanajin tsanar Jalila na sake shiga ranta! Mom tana k’arasowa wajen Jalila ta mik’e a fusace tayi hanyar fita. Da sauri tace “tsaya Jalila tsaya dan Allah!” Dan ta san abunda take shirin yi. Juyowa Jalila tayi tana musu wani kallon wulak’anci Da kyar Mom ta samu ta danne abunda take ji yana taso mata ta k’arasa gabanta ta tsaya tace “Kiyi hak’uri Itama kuma zan yi mata magana!! In sha Allah ba zata sake ba.” Ummi ji tayi kamar ta d’aura hannu a kai ta kurma ihu!! Yayinda Mammy take ji kamar tayi super ta shak’o wuyan Jalila. Murmushin renin wayo Jalilan tayi kafin tace “Kinga Adama!!! Ta sake ko kar ta sake wannan duk ba damuwa ta bace ba! Kawai abunda nake buk’ata shine tazo ta durk’usa ta bani hak’uri! In ba haka ba to babu abunda zai hana ni yin abunda nayi niyya!!” Tana fad’an haka ta fara k’ok’arin juyawa.. Ruk’o Jalilan tayi da sauri jikinta na d’an rawa tace “Tsaya zata baki hak’uri!” Sannan ta juya da sauri ta koma wajen Ummi ta kamo hannunta… Tun kafin tace wani abun Ummi tace “Adama baki da hankaline? Hak’urin kike so inje In durk’usa In bata ko me? To bari kiji ‘Ba zan bayar ba!!’ Sai dai duk abunda zai faru ya faru!!” Cikin b’acin rai ta kalli Jalilan tace “Idan baki san hanyar gidan nashi ba kizo muje ni zan rakaki!! K’aramar mara kunya kawai!!” Murmushi kawai Jalila tayi kafin ta d’aga kanta ta kalli agogo tace “Na baku minti uku!!”. Kamar Mom za tayi kuka haka ta fara lallab’a ummi tana rok’on ta Allah Annabi amman furr!!! Ummi tace “ba zata bawa k’ask’antacciyar Yarinya kamar Jalila hak’uri ba!” Mammy ma bayan Ummi ta bi d’ari bisa d’ari!. Ganin ba zasu bata had’in kai cikin sauk’i ba! Ga lokacin da Jalila ta bayar ya cika ya sanya kawai ta koma gefe ta tsaya tace “Duk ku biyun nan ba don ni ba da ban san halinda kuke ciki a yanzu ba! A tunanina ko mahaukaciya na d’auko a bola nace ku bata hak’uri saboda rufin asiri na ni da d’ana to za kuyi. Amman ba komai na gode gwara da Allah ya nunamin wannan ranar!!! Sai dai inaso ku sani Wallahi sai dai ta fashe da kowa! Dan k’afata k’afar Yarinyar nan! Tana gama zayyane bayaninta nima zan zauna In zayyane komai!! Dan ba zai yiu in share shekarun Ina taimakon ku ba yanzu kuma tashi d’aya ni in shiga problem ni kad’ai saboda taurin kanku!” Tana gama fad’in haka ta taka inda Ummi take tace “Gaki ga Jalila nan! In kinga dama ki bata hak’uri In kuma kin shiryawa fashewar boma bomai a cikin estate d’innan dan Allah kar ki bata hak’uri.” Tana gama fad’in haka ta koma kan kujera ta zauna ta d’aura k’afa d’aya akan d’aya tana girgizawa… Ummi ta jima tana tunani chan! kawai ta k’arasa inda Jalilan take tsaye ta d’an durk’usa kad’an tace “Jalila kiyi hak’uri nayi laifi ba zan k’ara ba” Bata bi ta kan kowa ba tasa kai ta fice da sauri.. Mammy ma tabi bayanta. Mom kuma ta mik’e tayi sama. Jalila kuma ta nufi dining tana tunani a ranta “menene haka sirrin da su Ummi basa so ya tonuu?”. BAYAN KWANA HUD’U!! (After four days!) Kamar yadda Mama tayi alk’awari haka nan yau ta shirya tsaf! Tun k’arfe takwas ta sanya atamfar ankon Khadijah da niyyar zuwa gidan Baaba Talatu. Tun bakwai suka yi waya da Ummu tace mata “sun fito tun tuni” So ta san duk inda tara tayi sun k’araso in shaa Allah. A kitchen ta fito ta samu Hudan tana d’an had’a musu abun kari da su da Ya Ja’afar dan shi ba a tafi da shi ba. Ganin da tayi Huda bata k’arasa nata shirin bane ba ya sanya tace mata “ta wuce taje ta shirya ita zata k’arasa aikin” Already ma Huda ta ida, zuzzubawa ne ya rage da had’a shayi…. “To” kawai Hudan tace daganan ta wuce d’aki. Mama na shirin zama taji kamar kira ya shigo ya yanke dan haka ta zaro wayar daga purse d’inta.. Tana dubawa taga Ummu ce! Ajjiye purse d’in tayi a gefe sannan ta gyara tsayuwarta ta hau kiran Ummun… Tayi mata misscalls sama da bakwai amman bata d’auka ba! Hankalinta ba k’aramin tashi yayi ba dan haka kawai ta yanke shawarar ta kira Shuwa tunda d’azu Ummun tace mata ‘a mota d’aya suke ita da Shuwa da Sumayya da Abba Madu da Ya Jamilu da suka je d’aurin aure a jiyan. Su Baba kuma suna tare da su Baaba Talatu.’ Bugu uku a na hud’un ta d’auka! Bata ce komai ba ta dai d’auka ta kuma kara a kunnenta!! A hankali Mama tace “Ina kwana Hajiya, Bilkisu tana kusa? Inata kiranta bata d’auka.” “Inaga wayar tana a silent ne” Shine abunda Hajiya Shuwa tace, daganan tayi shiru. A Ahankali Mama tace “Tam shikenan” Har zata kashe sai ta sake cewa “sai kun k’araso.. Muma gamu mun shirya yanzu zamu tafi gidan Baaba Talatu mu jira ku a chan.” Cikin yaren shuwa Hajiya Shuwa tace “Ku yi zaman ku kawai ba sai kun zo ba! Maryam Ina cikin farin ciki kar ki ja a b’ata mini rai kokuma a gaya min magana a yau d’innan!! Na gaya miki kar kuzo mana cikin taro da ke da y’arki amman kin k’i yarda ko?? Taurin kan naki da kika saba shi zaki gwada mini ko?” Cikin fad’a sosai taci gaba da cewa “Wallahi idan naga k’afar ki a inda nake ranki in yayi dubu sai ya baci!” Tana gama fad’in haka ta yanke kiran… Wayar Mama tana da volume sosai…dukda Huda ba wani yaren Shuwa take ji sosai ba amma tabbas ta fahimci abunda Hajiya take nufi… A hankali Mama wadda take jin kanta na masifar juyawa

Chapter 31 of 32