Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K’AI. So da Buri Free Book 01. 3 years ago..... A cikin garin kano,a unguwar gandun albasa,cikin wani d’an matsakaicin gida… kana ganin gidan kai tsaye za ka kirashi da na mai k’aramin k’arfi…daga waje k’ofa ce idan ka shigeta zaka biyo ta wani k’aramin soro,a soron akwai k’ofar d’aki mai band’aki a cikinsa kafin ka karaso cikin tsakar gidan wanda babu ko siminti rairayi ne a malale wanda ya ke nan a share dukda yanada d’an girma amman hakan bai hana an share shi tsaf ba! Daga gefe guda akwai d’akuna guda hud’u a jere,daga chan ta wajen k’arshen tsakar gidan kuma akwai bayi wanda aka sakaye shi da k’ofar langa langa duk tayi tsatsa,sai kuma opposite d’inshi kitchen ne da ko k’ofar langa langar ma shi babu amman baka iya hango cikin kitchen d’in saboda duhunsa sakamokon bangon da duk yayi bak’i wuluk ta dalilin girki da itace. Wata y’ar matashiyar budurwa da ba zata gaza shekaru 14 ba ce a tsakar gidan sai uban zufa takeyi,ta yi kneel down ta d’aga hannayenta sama,a kan tafukan hannayen nata kuwa wasu maka makan takalman ball ne d’aya a kowanne hannu… D’an motsi ta yi wanda hakan ya sanya takalmin dake kan hannun hagun ta ya kusan fad’uwa,tsabar yadda duk ta rikice ta fita a hayyacin ta ga rana ga tsoron bulala ne ya sanya ba ta san lokacin da ta yar da na hannun daman nata tai saurin rik’e na hannun hagun nata ba… ai kuwa bata k’arasa rik’ewa ba ya d’aga zabgegiyar bulalar dake rik’e a hannunsa ya zabga mata a kan hannayen nata,hakan yasanya ta k’arasa zubar da takalmin itama ta zub’e a nan k’asan saboda ba kad’an ba dukan ya shigeta. Kamar jira yake yi kuwa ya rufeta ta duka! Babu ji babu gani… ihu takeyi sosai tana kwala kiran “Mama!, mama!!,mama!!!” Mama da ke a d’aki,wadda tun farawar abun take jin su, ta runtse idanunta hawaye na gangaro mata tana adduan Allah ya kawo wanda zai ceci y’ar tata. Kamar daga sama ya ji an fizge bulalar,juyowa yayi a fusace zai yi masifa suka had’a ido da wani kyakkyawan saurayi!mai manyan idanuwa..yanada cikar gashin kai da na gira da dogon hanci sannan bakinsa bai cika girma ba…skin colour d’insa chocolate ne me d’an haske da shek’i,dan ko kad’an ba za ka kira sa da Bak’i ba..... cikin b’acin rai Junaidu yake kallon yayan nasa wanda suke mugun kama da juna bambancin kawai Junaidun ya fi yayan nasa kyau da manyan idanuwa da haske,sannan lips d’insa bai yi duhu ba kamar na yayan nasa da suka yi bak’ik’irin instead nasa shi light pink ne….. tun cikin bacci yake jin hayaniyarsa a tsakar gida sama sama har ya kaiga farkawa ya watstsake yafara jiyosu sosai. Kallon kwayar idanunsa Junaidun yayi…a zuciye ya yar da bulalar a k’asa kafin ya doka wani uban tsaki sannan yace”yanzu fisabillillahi ya Ja’afar abinda kake yi ya dace kenan??idan za ka hukunta Yarinyar nan ka dinga hukunta ta a lokutan da kake cikin haiyyacinka mana!!! kalla fa idanunka! ka je ka yi high!!kawai ka zo sai jubgar y’ar mutane ka ke yi so kake ka illatata?? kuma zan iya dafa Qur’ani akan cewa ba wani laifin kirki ta yi maka ba…a kan laifin da bai taka kara ya karya ba ka zo kanata dukanta haka! me ta yi maka??” Ya yi masa tambayar still yana tsare shi da manyan idanuwansa. Mitsi misi ya Ja’afar d’in yayi da idanuwansa da suka yi jazir sannan ya yi baya kad’an ya d’an yi tangal tangal kamar zai fad’i sai kuma ya dawo daf da Junaidun ya tsaya ya zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa sannan ya zuba masa idanuwa kafin yace “Kai,dan uwarka ni sa’anka ne?” Shiru Junaidun ya yi yana kallon shi kafin a hankali ya d’an sassauta murya yace “yi hak’uri,mai tai maka??” Tsaki ya Ja’afar d’in ya yi sannan yace “Akan gyaran d’akin da suke yi mini it da Jalila ne,Jalila ta yi mini bayanin ta ta wuce, Ita wannan makirar sai ta tsaya shara wai Umma ce ta sakata sharar tsakar gida, abun haushin da na shiga d’akin nawa fa ko tsinke ba’a d’aga ba komai yana nan a yadda na barshi…” shiru Junaidu yayi don in dai zai iya tunawa to jiya da shekaran jiya duk ya ganta tana gyaran d’akin ya Ja’afar,kuma a ka’idarsa shi ya Ja’afar d’in kwana bibbiyu sukeyi itada jalilan…to ya za a yi kuma yau ma yace still itace zatai mishi gyaran d’aki… Juyawa yai yana kallon hanyar d’akunan gidan kmr yana neman wani abun kafin da k’arfi ya fara kwala kiran “Jalila!Jalila!!Jalila!!!” Ya jafar ne ya d’an tab’o hannunsa sannan yace masa “kai ta tafi jarabawa fa” juyawa Junaidu ya yi ya kalle sa kafin yace “ya Ja’afar yau a ka’ida waye zai yi maka gyaran d’aki???” shiru yayi kafin cikin maganarsa ta y’an shaye shaye yace “Kagane ko! a k’a’ida Jalila ce,to ita wannan makirar sharar da ta yi jiya da shekaran jiya duk basu fita ba kai gyaran ma kwata kwata bai yi ba shiyasa yau sai d’akin yayi kmr ba a tab’a gyarawa ba sannan Jalila jarabawa ta tafi,shine na shigo na ganta tana shara kuma Jalila ta sameni a waje ta ce mini ta rok’eta ta gyara d’akin ita ta makara amman ta zazzageta har da marin ta fa tayi!!! ita dan uwarta a gidan ubanta ba a alfarma ne eh? Shine fa na shigo na sameta tana kwashe shara,ni kuma na d’auki alwashin sassama mata kamanni a yau d’innan tunda ta raina ni,ai ba Jalila ta zaga ba ni ta zaga tunda d’akina ne,kai marin ma ni ta mara tunda ai dai duk akan d’aki na ne” Junaidu da ya fara fahimta makirci ne kawai Umma da Jalila suka had’a saboda sunga an kwana biyu ba a jibgi baiwar Allah n ba,sannan su Baba ya hana su dukanta shine suka biyo ta hannun ya Ja’afar tunda sunga shi in dai ya bugu to ba iya gane gaskiya da k’arya yake yiba sannan ko baya ga hakama daman chan shi ya tsani Yarinyar…. Sunkuyawar da ya ga ya Ja’afar nayi yana k’ok’arin sake d’auko bulalar ne ya dawo dashi daga nazarin daya tafi,da sauri ya rik’e hannun ya Ja’afar ya shiga lallab’asa akan ya yi hak’uri ya barta za a gyara masa d’akin nasa,amman fur ya k’i hak’ura… k’arshe dai naira ashirin Junaidu ya d’auko daga aljihu ya basa tukunna ya hak’ura ya karb’a yana murmushi yace ta bar gyaran d’akin ma gobe sai ta yi,idan kuma Jalila bata da jarabawa goben sai ta bari jibi ta karb’i aikinta. Juyawa ya Ja’afar ya yi yai hanyar fita daga gidan shikuma Junaidu ya juyo yana kallonta anan a durk’ushe tana kuka tana ajiyar zuciya ta kifa kanta a k’asa…. A hankali ya sunkoyo kanta,kafad’unta ya kama duka biyu ya juyo da ita sannan ya sa hannunsa a hab’arta ya d’ago fuskarta. Da sauri ta runtse idanuwanta da suka yi luhu luhu fuskarnan tayi jawur tsabar kukan dataci..shiruu ya yi yana kallon ta..tun daga kan lafiyayyan gashin gaban goshinta wanda suka kwanta sukai lub lub akan farar fatar ta,zuwa kan gashin girarta masu kyau da shape kamar ta yi cavn da madaidaitan idanuwanta, zuwa kan dogon hancinta wanda yai kmr M daga k’arshe amman ba sosaiba da dan mitsitsin bakinta…. Cikin seconds d’in da ba su fi uku ba ya yi mata wannan kallon..a hankali ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya kira sunanta“HUDAN”saurin bud’e idanunta tayi ta kallesa! kamar kuma wadda ta tuna wani abun sai ta yi saurin ture hannunsa daga jikinta ta tashi da gudu tai hanyar d’akin Mama. Shiru ya d’an yi,chan kuma a hankali ya mik’e tsaye, ya juya da niyyar komawa d’akinsa. Juyowar da zai yi ya ga Umma a tsaye tana kallonsa sai kuma Anty zainab wadda ke tsaye a chan bakin k’ofar gidan tana d’an lek’a waje da alama bayan Ja’afar wanda ya fita yanzun ta ke bi da kallo.Daga gani ka san basu dad’e da shigowa cikin gidan ba dan ga lullub’i a kanta da kuma jaka a hannunta,itama anty zainab dake bak’in k’ofa haka amman tabbas ta gansa tare da Huda dan gashi ranta a mugun b’ace yake! Cikin in inar da bai san yana da ita ba yace “um um umma dddagaa ina ku ke?” K’arasowa ta yi gaban sa ta tsaya sannan cikin b’acin rai tace”daga gidan ubanka nake!!….”. Shiru ya yi ya sunkuyar da kansa yana sauraronta tana fad’a baki da kumfa,Anty Zainab da ta k’arasa shigowa yanzun tana tayata , Umma ce tace”wato da ka d’auka ba yanzu zan dawoba ko?shine kaje harda wani d’ago ta kana kallon ta,idan za ta had’iyi zuciya ta mutu Junaidu ina ruwanka da damuwarta?? Ka ga ta inda Ja’afar ya fi ka ko?Yaron nan ko kyalle ne indai nace banaso to kuwa shima ba zai so shiba,anya ni na haifeka kuwa?a ce Yaro kwata kwata baya kishin uwarsa!!anbi an lashe ka an shanye ka to wallahi ba’a isa ba,ni naci uwar boka ma ballantana malami…ka ci gaba da b’ata mini rai har sai ka ja nai maka baki tunda baka jin magana ta dudda dai na san ba yin kanka baneba.” Anty Zainab itama tace “ke kuwa Yarinya ta yo gadon munafurci ai ba zai tab’a ganin laifin taba,mu mun buga da wadda ta haifo ta ma ta hak’ura ta barmu,ballantana ita…..” Ta inda suke shiga ba ta nan suke fita ba hakanan suka yi ta habaici a tsakar gidan babu wanda yace musu ci kanku sukayi suka gama suka shige d’akin Umma suna huci,anan d’in ma maganar sukaitayi,da suka gaji Umma ta bawa anty zainab sak’onta ta mik’e tai mata sallama ta fito ta tafi,har ta fita a gidan mamakin Junaidu takeyi…ba irin yadda ba su yi ba akan ya fita harkar Yarinyar tun bata kai haka ba amman a banza Ajiyar zuciya ta sauk’e a ranta tana adduar Allah yasa Junaidu dai ba gadon wahala ya yo daga wajen ubansa ba . Chan d’akin Mama kuwa Hudan ce kwance akan gado ta d’aura kanta a kan cinyar Mama tanata kuka,Mama bata hanata yin kukan taba sai da taji ta d’an sassauta kukan nata tukunna a hankali ta shafa kanta tace”Huda ba na hanaki shiga harkar Junaidu ba?? Dukda a cikin y’an gidan nan shi kad’ai ne baya zaluntarki yake kuma kare ki amman na san kin san cewa banason alak’ar ku ko? Yanzu duba ki ga irin zagin da kika ja mini da ke kanki”. Shiru Hudan tayi da kukan da takeyi kafin ta dago kanta ta share hawayenta ta kalli mama sannan a hankali cikin sanyi tace”Maamaa ni fa ban kula shi ba Allah,kawai dai ya karb’e bulalar da Ya Ja’afar yake duka nane ya bashi hak’uri amman ni bance masa komaiba.” Shiru Mama tayi tana kallon y’ar tata kafin tace”to ke Huda mai yasa da Jalila tace ki gyara mishi d’aki kika k’i kika hau shara??” Raurau Hudan ta yi da idonta kafin tace “Mama jalila k’arya ta yi mini, daman jiya akan ya Junaidu ya hanani wanke mata uniform d’in makarantar ta tace mini wallahi sai ta saka ya Ja’afar ya zaneni, wai tunda na shiga tsakaninta da d’ayan yayan nata bara sai ta sa d’ayan ya zaneni.” Shiru kawai Mama tayi tana tunani….ko ba a fad’a ba daga yanayin fuskarta ka san ranta a b’ace yake. Gaskiya ita dai hak’urin ta ya kusan k’arewa,taya still za a mayar mata Yarinya kamar wata jaka,dan ma ta samu sauk’i tun lokacin… ………. Da ta je wajen Kaka (Baba Bashir) ta kai masa k’orafi akan su Umman da jalilan. Ran kaka ya yi mugun b’aci a lokacin hakan yasa ya kira Baba ya ja masa kunne akan yayi musu gargad’i mai zafi dan in har ya sake jin ko da marin Hudan ne anyi a tsakanin Umma ko Jalila to bai yafe masa ba. Baba ya shiga rud’u a wannan lokacin domin kuwa a duniyar nan idan akwai abunda yake jin tsoro to shine b’acin ran Umma amman kuma yanzu ga abunda mahaifin sa ya fad’a wanda ko hauka yakeyi ba zai bari Allah ya isan iyaye ta hau kansa ba,hakan yasa yana dawowa gida ya rufe ido ya tara su a d’akinsa ya cewa Umma da Jalila “kar su k’ara dukan Huda,sannan kar a sake d’aura mata talla,wankinsu su dunga yi da kansu ko sukai gidan wankau,sannan wanke wanke da wankin band’aki tsakanin Huda da Jalila duk ranar da mamanka keda girki kai ne zaka yi,indai har kuwa aka k’etare abunda ya fad’a to a bakin auren Umma Abunda kawai ya yarda aikin Huda ne parmanent shine sharar tsakar gida domin ita Jalila nazuwa makaranta.” Umma a wannan lokacin kusan daskarewa ta yi tsabar mamaki..mutumin da ko maida mata magana baya iya yi shine yau harda ik’irarin cewa ‘a bakin aurenta!!’ Tabbas da sake, kasa yin shiru tayi dan haka ta yi gyaran murya sannan tace “Alhaji ka bani mamaki matuk’a amman ba zan yi jainja da kai ba a gaban Yara,abu d’aya wanda na sani shine kana dab da b’ata tarbiyar Yarinyar nan kai da uwarta dan ba zai yiu ace kab gida Yaro babu mai kwab’arsa ba,ga yayunta nan maza amman an nuna mini iyakata,Alhaji ance babu mu ba Huda ko? Saboda ita shafaffiya da mai ce? ni za ka yiwa haka akan wad’annan mutanen???” Ta yi maganar tana dukan k’irji da kafe Baba da manyan idanunta waenda yake hango tsantsar b’acin rai a cikinsu. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 02 Shiru Baba yayi yana tunanin ta hanyar da zai bi ya d’an kwantar ma da Umma hankali…chan ya yunk’ura yai gyaran murya kafin yace “Sadiya ni bance harda yayunta maza ba,dokar iyaka kanki ne ke da Jalila shima kuma saboda Kaka yayi mini kashedi mai zafi shiyasa, ko kina so Allah ya isan shi ta hau kaina?? yayunta maza sunada ikon hukuntata indai ta yi laifi kuma ai....” “Aikin banza ma kenan!!!”tsawar Umma ta katse shi Kafin ta ci gaba da cewa”ai kaga wannan matar” ta yi maganar tana nuna Mama wadda tunda aka fara maganar bata ce uffan ba. Cikin huci ta d’aura da cewa”tabbas in dai baka taka mata burki ba tunda ta samu Kaka yana goya mata baya zata sake komawa wajen shi ta kai k’arar su Junaidun suma..tunda naga kamar ma tsoronta kafara ji.” Ta k’arashe maganar tana huci. Shiru Baba yayi kafin ya d’ago kanshi ya kalli Mama “MARYAM” ya kira sunanta cikin kakkausar murya.D’agowa Mama ta yi ta kalleshi kafin a hankali tace “naam” Nisawa yayi sannan ya ce “kin kai k’arata wajen mahaifina,an yi miki abunda kike so ko? To nima ga nawa sharad’in, Indai Huda ta yi laifi kika hana su Ja’afar hukuntata kema a bakin aurenki,don kamar yadda Sadiya ta fad’a ba zai yiu ace Yaro babu mai kwab’arshi a gida ba, Ita dai da Jalila ga sunan sun bar miki y’ar ki.” Yana gama fad’in haka ya d’ora da cewa “Shikenan kowa zai iya tafiya na riga na gama magana.” Ahaka aka tashi kowa yai d’akinsu . Umma sam ba haka ta so ba,dan ta san daman auren Baba ba wani d’ad’a Mama yayi da k’asa ba,kawai dai saboda Hudan yasanya take hak’uri take zaman gidan. Hakanan ranta babu dad’i suka k’arasa d’aki tanata k’ulla ta inda zata b’ullo wa alamarin a ranta. Mama atunaninta sauk’i zai zowa y’artata sai dai sam abun ba haka yakasance ba domin kusun kullum sai ansan sharrin da aka had’a mata an saka Ja’afar yai mata shegen duka,sannan sharar tsakar gidan da aka ce shine aikinta kullum,tofa a rana sai Umma ta sakata ta yishi sau uku ko fiye da haka duk kuwa da girman shi,da gangan Jalila za ta jefar da abunda bai taka kara ya karya ba ace sai ta share duka ai daman yayi datti. Sauk’i d’aya zuwa biyu ta samu shine na talla da wankin su,amman ko wankin band’aki ranar na Jalila kwara ruwa kawai takeyi kusan ita ce za’ace take wanke band’akin duk ranar yinta....... ………………. K’arar buga k’auren ne ya dawo da Mama daga duniyar tunanin da ta tafi K’arar bata gama barin dodon kunnenta ba ta ji an shigo gidan ana wak’a,ko ba a fad’a mata ba ta san Jalila ce. Huda Mama ta juya ta kalla tace “kikace bata ce miki ki gyara d’akin yayanku ba ko?” Kai Hudan ta d’aga mata alamar ‘eh’ Mik’ewa Maman tayi ta juyo ta kalli Hudan tace mata “zauna kar ki fito” daga haka ta yi waje. wata budurwa ce take K’arasowa tsakar gidan…ba za’a kirata da bak’a ba sannan kuma ba fara bace fat!!shekarunta ba za su wuce goma sha shidda ba,tanada manyan idanuwa da d’an matsakaicin hanci sannan bakinta ba k’arami bane ba kuma k’atoto bane ba yayi dai dai da yanayin fuskarta kallo d’aya za ka yi mata ka kirata da kyakkyawa sannan yanayin shigarta zai tabbatar maka da irin y’an matan nanne marasa kunya…tana tafe tana wak’a had’i da taunar cingum wanda hakan yabawa gefen kumatunta damar lotsawa. Uniform d’in jikinta koren wando ne da farar riga da farin hijabi wanda hakan ke nuni da makarantar da take zuwa ta gwamnati ce…da alama tanada wani muk’amin a makarantar tasu domin d’an kwalin kanta yellow ne ba Fari ba ba kuma kore ba,ta zaro shi daga cikin hijabin nata tayi daurin ture kaga tsiya ta saman hijabin….daga makaranta take amman ta rambada uban jan jambaki,sannan ga idon nan yasha kwalli ya sake fitowa rambad’au!!!! tubarkalla,y’ar k’aramar jakarta da ba za ta ci littafi biyu ba na sakale a gefen hannun damanta. Ido suka had’a da Mama wadda ta gama fitowa daga d’akinta yanzun hakan yasa ta jan wani dogon tsaki had’i da tofar da cingum d’in bakinta kafin tace”Ni fa na tsani kallo.” Sannan ta yi hanyar shiga d’akin Ummansu. “dakata Jalila, magana za mu yi dake” Mama ta fad’i hakan tana k’ok’arin K’arasowa inda take. Juyowa ta yi ta zuba mata ido ta gyara tsayuwarta tare da nad’e hannuwanta akan k’irjinta irin ina jinki d’innan. Kallon ta Mama ta yi sannan tace”yanzu Jalila saboda Allah dukan da kike sakawa yayanku Ja’afar yana yiwa y’ar uwarki ba tare da hakkinta ba kina ganin ya dace kenan? Ke kenan kullum ba za ki ja k’anwarki a jiki ku zauna lafiya ba? Ki duba fa saboda Atule d’in fa da kike sakawa Yara suna yi mata kullum hakan ya sanya dole Babanku ya chanza mata islamiyya aka maida ita ta dare da asabar da lahadi na safe. Yarinyar da ta taso da k’aunarki acikin ranta kina k’ok’arin maida mata rayuwa kurkuku?Meyasa kike hakane Jalila?mai ya faru kika chanja?” Umma ce ta hankad’o labule ta fito daga dakinta cikin masifa tace “Kawai kinga munafuka ki fito fili b’aro b’aro kice tunda na dawo gidan nan na chanjata,akan wanne dalilin za ki tasa mini y’a a gaba kina wani cewa ta chanza hali? To bari kiji in gaya miki Allah ne ya tsameta a cikin munafukai ya dawo da ita cikin masu gaskiya,kuna abu simi sumi da ke da y’arki nankuwa kunfi kowa iya munafurci da cin dunduniyar mutum!.” Juyawa Mama ta yi ta kalli Jalila wadda ta ga ta yi shiru tana kallon gefe kamar bata wajen,a tunanin Mama nutsuwa ce ta zowa Jalilan, Juyawa tayi ta kalli Umma wadda har yanzu take fad’a baki da kumfa tace mata “kinga Sadiya ba dake nake ba, ya Ina shirin shirya tsakanin Yara ke kuma kina k’ok’arin kiga kin b’ata?ki daina shiga fad’an y’an uwa fa dan wataran za ki ji kuny.....” “In sha Allah ke ce za ki ji kunya ba dai Ummana ba!” maganar Jalila ta katse ta, “kuma da kike ta cewa wani wai y’an uwa da ni da Huda shin wai Ubanta ne d’an uwan Baba? ko kuwa ke uwarta ce y’ar uwar Umma???” Shiru Mama ta yi tana kallon Yarinyar da ta rena ta goya a bayanta ta ci kashinta taci fitsarinta tana rera mata rashin kunya. Cikin son fahimtar da ita Maman tace “Jalila ai ko babu y’an uwantaka ke kin san Hudan k’anwarki ce.” “Chan ki je ki nemo y’an uwanta wallahi ba dai ni ba.” Jalila ta fad’a cikin d’aga mata Hannu kafin ta d’aura da cewa”kiganni nan kaf y’an uwana na dangin Ummana da Babana suna da nasabarsu kuma suna amsa sunan iyayen su!…da za ki ce wani Ummana za ta ji kunya dan kawai ke kinji kunya shine za ki so kowa ma ya ji?kinje kin Haifo shegiya kin kawo ta cikin gidanmu still za ki yi ta lak’aba mini ita kina wani y’ar uwartace ita? Idan ba tsoroba ki nuna ubanta mana ki kaita wajenshi Yarinyar da ko sunanta Babanta ba ya so yaj.....” Jalila bataga k’arasowar Mama daff da ita ba sai kawai wani haske da ta gani sakamokon marin da Mama ta d’auke ta da shi,ai kuwa batai wata wata ba itama ta d’aga hannunta za ta mari Mama. Ji ta yi an rik’e hannun hakan ya sanya da sauri ta juyo,nan suka had’a ido da Junaidu ya had’e rai. Matse hannun nata yai da k’arfi sai da tayi k’ara sannan yace mata “baki da hankali Mama za ki mara?” Nan Umma daga bakin d’akinta toyo wata super tayi kan Junaidu ta rufe shi da duka tana cewa”saketa ta rama ka saketa nace!!” duk irin

Chapter 1 of 32