Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta shigo, dukda dai cin masu aji ake masa bana karuwaiba, Afrah ce kawai a k'asa zaune, amma Nawwas da Namrah duk a kujera suka zauna kusama da juna, hannun Nawwas akan Na Namrah wadda ke sanye da wando da Riga masu bin jiki, sai siririn mayafi data yano, shima saida mamansu Tamata magana, kanta yaci uban kitson gashin doki, daka gantadai kaga wayayyun wannan zamanin. Shiko Nawwas wandone irin Na babansa iya gwiwa, sai singlet ruwan d'orawa, askin kansa abun takaici da kuka ga al'ummar musulmai, dan an saisaye gefe da gefe da k'eya, anbar gashin iya tsakkiyar kai sannan akai masa k'itso kalba (Dada) daga kasan gashin bak'i, sama kuma k'arshen kitson Brown. Duk a cikin mintuna kad'am su Malam Aliyu suka nazarcesu. Dady yace, ?Malam ga iyalin mawa, d'ayane babu a ciki autansu, yana jami'ar legas yana karatu, kwannan ma yatafi, wannan itace matata mahaifiyar yarana, sai babban Nawwas mai shekaru 27 a duniya, yagama p.h.d d'insa, watansa shidda kenan, yanzu haka yana aikinsa. Sai Afrah, tagama degree d'inta itama kwannan, muna mata shirin zuwa masters, sai Namrah tana jami'a tanan jos L200 yanzu?. Masha ALLAH su malam Aliyu suka fad'a a tare, da d'orawa da addu'ar fatan alkairi. Daga Nana malam Aliyu ya d'ora da fad'in ?Dalilin zuwanmu nan gidan shine yarinyarka Afrah?. Atare suka kalli Afrah da kanta ke a k'asa. Malam Aliyu yacigaba da fad'in ?Wani sak'o daya kasa barin zuciyata ta turamin, harma naji nakasa hak'uri saina dangane da wannan family, Afrah indai ban shiga huruminki ba inason ki kuma maimaita abinda kika turamin domin Na tabbatar?. Hawayen dake d'iga a kumatunta ta share, kafin tace, ?Dady da mah-mah Ku gafarceni, yau Zan bud'e sirrin daku baku saniba, saidai har a yanzu ina tambayar kaina Sakacinku ne kokuwa ak'idar boko ce? Da wautar barin tarbiyyar addinin islama?. Har yanzu zuciyata ta Gaza amsamin tambayar, amma ban saniba ko idan Na fad'a yanzu amsar zata fito?. Ba k'aramin fad'uwa gaban Nawwas yayiba, dukda baisan mi Afrah zata fad'aba yaji ya tsargu. Mik'ewa yay niyyar yi amma dad ya tsaidashi da Ido, dole ya koma ya zauna yana wani kumbura baki. Afrah takuma fashewa da kuka sannan tafara jawabi dalla-dalla kamar yanda taima malam Aliyu a sak'o, harma ta k'ara da abinda bata sanar masaba. Gaba d'aya falon jikin kowa ya mutu murus, Dady da mah-mah ma jikinsu rawa yakeyi, hakama Namrah datayi wani tsalle zuwa k'asa saboda tsorata, bata ta6a zaton wani mahaluki yasan suna tarayya da Nawwas ba, sannan bata ta6a zargin yanayin abinda yakeyi da ita da Afrah ba. Gani kawai sukayi Dady ya kifo k'asa, Mah-mah ma data mik'e domin zuwa garesa saita yanke jiki ta fad'i. Nawwas kam dukya rikice, yarasa ina zashi ya 6uya saboda kunya da tsantsar tashin hankali. A tsorace su malam Aliyu duk sukayo kan Dady, yayinda Afrah tayi kan mah-mah d'insu. *bayan awa biyu* su Dady suka dawo a hayyacinsu, saboda kiran likitansu da Namrah tayi, annan yake sanarda jininsu ne yahau sakamakon jin abinda ya tsoratasu. Bayan tafiyar doctor da nitsawar komai, malam Aliyu yafara magana a matuk'ar sanyaye da k'unar zuciya. Ya Fara dajan ayoyin alkur'ani da hadisai, sannan ya d'ora da nasiha Mai girgiza zuciya.  Wlhy iyaye Ku farka=?-?, karku d'auki wancan zancen matsayin labarin littafi kawai, wannan fitinace data shigo acikin wannan al'ummar, Uba kaga yana Neman y'ay'ansa, Uwa ta nemi d'anta ko abokin d'anta, ko abokin mijinta, ko makwafcinsu, Yaya da k'annensa suringa Neman junansu, Yaya da kanwa su ringa aikata mad'igo, ko Matar uba da y'ay'an miji=?-?, aboki yaringa zina da d'iyar abokinsa, k'anin uwa ya ringa zina da Y'ar k'anwarsa ko yayarsa, k'anin Uba yana zina da y'ay'an d'an uwansa, shin dan ALLAH wad'anne irin al'umma muke son zamane? Anya kuwa muna tsoron mutuwa da kwanciyar kabari da hisabi? Muna tuna duniya tak'aitaciyace? Innalillahi wa inna'ilairaji'un, wlhy kaiconmu da toshewar imani dana zuciya=?-?, k'iri-k'iri munason barin dokokin addininmu muna aro Na yahudanci da tsantsar tsagwaron kafirci a matsayin wayewa, *MUTUM DA DUNIYAR, y'an uwana YA DACE MU GYARA KANMMU* dai tunkan lokaci ya k'ure mana, wlhy tunkan muga kayinmu cikin WUTAR JAHANNAMA mu farka daga wannan barcin asarar, duk yanda muke kallon mutuwa a nesa damu saitazo garemu, domin a kullum k'ara kusantomu take a kowacce safiya, mimuka tanada mikuma zamu tarrar??. Malam ya k'are maganar hawaye Na cika idonsa, malam mustafa da malam Mahmud Kansu jikinsu Yakuma yin sanyi lis da maganar malam Aliyu. Kafin kacemi kuka ya 6alle a tsakanin wannan ahali, kowannensu yana kaico da koyi da al'adar yahudanci da barin tafarkin addininsu bisaga rud'in duniya da wayewa Mara amfanii a duniya da lahira. Duk Wanda ya kallesu saisun bashi matuk'ar tausayi. Har kusan magrib su malam Aliyu Na gidan, saida sukaga komai ya natsa sannan suka wuce, sukabar wannan ahali cikin tsantsar rud'ani da nadama. Gaba d'aya da zazza6i Malam Aliyu ya kwana a ranar, washe garima haka suka tafi kano baida lafiya, koda suka dawo har k'arin ruwa yasha, saboda azababben ciwon kai da damuwa sun kasa barin zuciyarsa, komai kallonsa yake tamkar ba gaske ba ma. Amma dole zuciyarsa ta tilasta masa gaskatawa tunda yaje yaga zahiri. ('('('('('('('('('('(' Sai da jarabawar su Jiddah takai kwanaki hud'u sannan sakamako ya fito. Cikin amincin Ubangiji Jiddah taci ita da Mariya Ibrahim wata y'ar ajin, sosai suka shiga farinciki da wannan nasara, nanfa y'an aji suka shiga tayasu, dukda zukatan wasu babu dad'i akan rashin nasarar. Da tsantsar farin ciki Jiddah ta iso gida, ta kanand'e Umma dake shanya kayan da take wanki. ?An dace kenan??. Umma tafad'a tana dariya bayan ta juyo ta kalli Jiddah dake mak'ale da ita. ?Alhmadllh Umman mu naci wlhy, kai ina cikin farin ciki?. ?Alhmdllh Jiddon Uncle, ALLAH ya sanya albarka da nasara tagaba?. ?Amin Ummana . Su Zarah na shigowa gida Umma ta taresu da wannan farin ciki suma, tuni sun kaure da murna suna k'ara yima yayar tasu adduar nasara. Itama Aunty Nafisa suka takura saida Umma ta kurata ta gumtsa Mata. Sosai tayi farinciki itama. ('('('('('('('('('('(' Yau gaba d'aya Malam Aliyu a busy yake, saboda tafiyar da tazo masa babu shiri, dukda dama yasan da tafiyar, amma bai tsammaceta cikin wannan watanba. Muhimmancin abinda zashiyine ya sakashi shiryawa babu wata damuwa da zuwan tafiyar a yanayin rashin shiri. Ko d'alibansa bada kowa ya samu damar yin sallamaba, sai sak'on ban hak'uri daya barmusu, da d'ora malam Mustafa matsayin Wanda zai cigaba da yimusu karatu harya dawo tafiyarsa ta watanni uku zuwa hud'u insha ALLAH. Cikin gida ya Shiga yayma matan Malam sallama, y'an uwansa kuma dukya kirasu ta waya musamman Ruk'ayya da Siyama daya dad'e yana waya dasu domin yin sallama, yaso su had'u kafin ya wuce, amma ina lokaci yariga da ya k'ure sosai. ('('('('('('('('('('('  Haba hindu, fushinnan ya isa haka mana, tunda kika dawo kink'i saurarena, minene amfanin dawo da abinda akayi ya wuce, kuma nabaki hak'uri?. Shiru tayi tamkar bata jisaba, tacigaba dacin abincinta, shiko ya k'ura Mata ido yana juya nasa cokalin akan filet. A haka su Hussain suka fito suka samesu, kowanne kujerar Dani d'in yaja ya zauna, ko sallama basuyima iyayen nasuba. Kalifa daya zauna kusada Abba ya kallesa yana fad'in ?Abba wai sai yaushe zaka cikamin alk'awarina?, ALLAH wayarnan bana sonta, Su Faisal duk an canja musu ni bandani, harma kunyar zuwa school nake da wayata?. Murmushi Abba yayi ya shafa kan kalifa, ?Haba babana ka kwantar min da hankalinka mana, aina fad'a maka Zan sake maka, yanzu wasu abubuwane suka d'an tushemin, amma kabani nanda k'arshen watannan insha ALLAH taka wayarma duksai tafi tasu, dan nayima Nabel magana ma ya za6o maka mai k'yau?. Washe hak'wara kalifa yayi yana rungume Abba da fad'in ?Kana birgrni Abbana......? ?Abbanmu dai?. Cewar Hassan cikin jin haushi. Kallonsa Hajia hindatu da Abba sukayi, yayinda kalifa ke antaya masa harara kafin yaja tsaki da fad'in ?Jealousy?. Hassan ya ta6e baki shima yana hararar kalifan ?Jealaus d'in Ubanmi za'a maka, gaskiya Abba muma ka siya mana phones, nidai nafasa sai munkai js3 d'inma, ai gashi Aisar nan suna dashi?. Hajia Hindu dake dariya tace, ?Y'an biyun Abba da gaske dai kishin kukeyi da babban Yaya?. ?ALLAH ya kiyaye wlhy Mom, kibarma hura masa wannan k'aton kan nasa?. ?Kai dan Uwarka waye mai k'aton kan??. Kalifa ya fad'a a fusace yana mik'ewa zai kaima Hussain dayay maganar duka. Amma sai Abba yay nasarar tarewa. ?Haba yaran Abba minene abin fad'a anan, ya Isa haka to abar maganar, kowa za'a saya masa indai wayace. Kai Auta mikake buk'ata??. ?Abba ya k'are maganar da kallon Munner daketa kallonsu kawai?. ?Abba ni sonake ka siyamin motar da muka gani ni da mom ranar, nace ta sayamin saitace kud'inta bazai kaiba?. Jinjina kai Abba yayi yana maida kallonsa ga Hajia Hindu. Da ido tai masa alamar anyi haka. Murmushi yayi, ?To Auta mom zata rakani na saya maka insha ALLAH?. Sosai Munner yake murna shima. Haka dai suka cigaba dacin abincin kaya-kaya tamkar wasu kaji. Bayan sun gama kowa ya kama gabansa. Sayayyar da Abba yay alk'awarin yimasu Munner ce ta saka hajia Hindu sauka daga fishinta Na kwananda Abba yaje yayi a gidan Umma. Dan suna shiga d'aki ta rungumeshi. Sosai yaji dad'in, shiyyasa ya kudiri aniyar kokartawa ya siya musu duk abinda ya alk'awarta musu.................. '???#?zakuyi bayani indai aurene). Abubuwa da yawa ke saka su Jiddah kuka idan suka tuna zasuyi sure. Na farko rabuwa da juna da kuma Ummansu farin cikinsu. Na biyu wane irin miji zasuci karo dashi? Mai irin halin Abbansu ne kokuwa Wanda yafi nashi muni? Na uku tayaya Ummansu zataji dad'in rayuwa babusu a kusa? Tunda suka tashi sune take gani taji dad'i, k'aunar da take musuce tasakata hak'urin zama da mahaifinsu dukda munin halinsa da rashin k'aunar da yake nuna musu da ita kanta, to ta Yaya bazasu damuba a yayin da suka tuna zasu tafi su barta cikin kad'aici bayan ita ta zauna danta gusar da nasu kad'aicin a lokacin da suke matuk'ar buk'atarta. Haka kowaccensu taita sak'awa da kwancewa har dare yay nisa, ganin sun kasa barci Jiddah tace su tashi suje suyi alwala suzo suyi salla. Wannan shawarar sukabi, suka fito domin d'aura alwala, Umma dake sallar itama duk tana jiyo motsinsu. Godiya taima ALLAH daya bata y'ay'a irinsu Jiddah, dama akance Ubangiji baya had'ama bawa zafi biyu, idan ta k'untata wajen mahaifinsu saitaji sauk'i da farinciki a garesu, itako tayaya zata jahilci ni'imar Ubangiji buwayi gagara misali, shima dayake a cikin duhun kai ALLAH ya ganar dashi gaskiya. &&&& Washe gari duk sukuku suka tashi, gashi ranar lahadice babu makaranta, haka dai suka taimakawa jiddah ta shirya kayanta kala biyu sai Uniforms d'inta kala buyi suma (tafiyar ta kwana uku ce kacal, ko hud'u). Bayan sun gama Karin kumallo Uncle yahaya ya iso, dan tare zasu tafi, k'a'idar makarantar su Jiddah ce inhar tafiya irin wannan ta Kama saida muharraminka, basu yarda tafiya iya malamai da d'alibaiba, kowacce zatazo da muharraminta ne aje dashi, sauk'insu ma koda tafiya ta Kama ta k'etare to lallai makwaftan Najeriyane irinsu Cameroon, Niger dadai sauransu, mafi yawanci kuma duk tafiyace ta mota balle ace babu kud'in biyan jirgi. Har makaranta Zarah da Walida saukai mata rakkiya, sun iske malam mustafa da malam Bilal (kanin M. Aliyu) sai malam mika'il da sauran d'aliban da za'ayi tafiyar suma da y'an rakkiyarsu. Basu wani 6ata lokaciba suka shiga motar da za ayi tafiyar. Har suka fice su Walida basubar d'agama Jiddah da Uncle yahaya hannuba, itama Jiddah Na d'aga musu, yayinda Uncle yahaya suke k'ara birgeshi da k'arajin k'aunar yaran, dan tarbiyyarsu da zumincinsu Na birgeshi, sosai yayarda da maganar man ta bahaushe dayake cewa mace itace ginshik'in zuminci, dan inhar babu ita saikaga kan y'ay'anka kowanne da inda yayi. Wannan shine zuwan Jiddah Abuja Na uku, dan haka bata wani damu da 6ata lokaci wajen kallon hanyaba, hasalima ramuwar barci tashigayi, sa6anin abokan tafiyar tata dake hira a hankali, su Uncle yahaya dasu malam mustafa ma hirarsu sukeyi wadda ta danganci rikicin rayuwa da ta'addancin dake faruwa a duniya kullum Ana cewa musulmaine. Sun Isa Abuja k'arfe uku Na Rana, dan kokad'an basuyi guduba, tafiya sukai a tsanake babu wani cida zuci, sun tsaya a Kaduna masunyi salla, sunkuma dad'e kusan Awa d'aya da wani Abu. Tuni Jiddah ta tashi, dukda ba hira takeba tana sauraren hirar ta 6angarori biyu, y'an uwanta d'alibai da malamsu da iyayensu. Sun Isa Babbar makaranta ta Arabic da akeji da ita a ciki da wajen Nageriya, dan akwai d'alibai cikinta harda Na k'etare, sannan ta had'a k'abilu daban-daban. Makarantace da duniyar ilimin addinin Islam keji da ita matuk'a, dan duk Wanda yaje nan lallai yakai abin kallo da tutiya ga al'ummar musulmai, makarantace tundaga nursery har zuwa University, guda biyuce makarantar, ta mata ce a farkon shiga layin, sai ta maza acan k'arshe wanda nisansu yakai zaka iya hawa mashinma, babu yanda za'ayi namiji ya shigo sashen mata, hakama mata basuda hurumin shiga sashen maza, akwai tsaro sosai a makarantun mai ban sha'awa da tutiya ga al'ummar musulmi. wani taro dasu jiddah sukazo a makarantar suka sauka, amma lokacin anma d'alibai Hutu, sai y'an manyan kawai suka tarar y'an jami'a, amma wannan Karon d'alibai Na nan. Bayan y'an wasu abubuwa da suka gudana aka kai su Jiddah masaukinsu a cikin hostel. Tarba suka samu ta mutunci ga d'alibai y'an uwansu, sai kaf-kaf akeyi dasu. Hakama sauran d'aliban da suka halarci taron daga k'asashe daban-daban. Dukda wad'annan abubuwan hankalin Jiddah naga tunanin Ummanta da y'an uwanta, kad'an-kad'an saita ayyana ?komi sukeyi yanzu??. a zuciyarta. Yawan murmushinta yasaka wata d'aliba Mai suna kemi tambayarta cikin harshen larabci, (dan yoroba ce, bakuma tajin Hausa, ita kuma jiddah bajin turanci takeba sai tsinta-tsinta da ake koya musu a makaranta dakuma Wanda y'an uwanta ke koya mata). Murmushi Jiddah tai Mata, kafin tace, ?babu komai?. Badan kemi ta yardaba tabarta. Ranar dai haka suka kwana cikin d'alibai, inda da daddare aka gudanar da lecture mai ta6a zuciya da ruhi, wadda aka sakama suna *_TARBIYYAR MUSULMAI A YAU!!_*. sosai wannan lecture ta shigi su jiddah da sauran d'alibai, k'arfe sha d'aya aka tashi kowa ya nufi makwancinsa. Da k'yar jiddah tasamu tayi barci, dan kewar su Zarah ta addabi zuciyarta matuk'a. Washe garima bayan Sallar Asuba ankuma yimusu lecture, ita kuma Mai taken *_YAYA YAKAMATA MU RAYU A MATSAYIN MUSULMAI?!!_*. Itama dai tashigi su jiddah sosai, dan har kuka wasunsu sukasha saboda jin kura kurai da al'umar musulmai suke tafkawa a cikin zaman takewar rayuwa, wadda a yanzu mafi yawancinmu bama kare hak'k'ok'i da dokar da addininmu ya sharad'd'anta mana mu rayu, kowa gaban kansa yakeyi da abinda yay maisa a zuciya. (Ya rabbi ka gyaramu muda halayenmu=?-?=?O?

Chapter 6 of 31