Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dai shi malam dayasan yanayin d'ansa tuni ya hango farin ciki tattare dashi. &&&&& A ranar da yamma kayan gadon Jiddah suka iso, kayane masu k'yau da tsari dakuma tsada gwargwadon k'arfin Uncle yahya, kowa yagani saiya yaba, saidai idan mak'iyi kuwa. Ganinfa abin da gaskene sai jikin Jiddah yakuma sanyi, ga Yaruwaiya tadage sosai take kuma gyarata da tsumata a k'amshi. Sheikh Aliyu yana kiran Jiddah su gaisa, yakuma bata hak'uri akan bazai samu sake shigowaba, dan yayi busy da yawa, ga shirin tarewarta ga walimar musabik'ar dataje Saudia wadda malam yace za'a had'a data aurensu. Ita hakanma sai yay Mata dad'i, dan dama batason yazo yaga taji ciwonan Na hannunta, sannanma dai tafison su zauna nesa-nesan, shiyyasa jitake inama su Umma zasu yarda a kuma d'aga tariyar. Daka ganta kasan tana tare da damuwa, datasamu ke6ewa ita kad'ai sai kuka, ita kanta Umma dauriya kawai takeyi, su Zarah kam duk sunyi wani sukuku dasu suma, kewar Y'ar uwarsu Na matsuk'ar damunsu. Washe gari aunty zulai dasu Aunty Saudah, hannatu suka iso, dan haka aka rankaya gidan Aliyu yoma Jiddah Jere. Tarba ta mutunci suka samu dagasu aunty Ruk'ayya da Maimunatu, dan bazama kata6a cewa itace kishiryar Jiddanba, yanda taketa hidima dasu abun gwanin birgewa. Dukda gidan Alhaji garba yafi Na Aliyu komai hakan bai hana gidan Aliyu k'ayatar dasuba, dan ba arzik'in bane abin birgewa kawai, zaman kafiya da kwanciyar hankali shine abun buk'ata ga kowacce d'iya mace. Tsarin gidan babu ruwan kowa da kowa, dan kowacce kamar 6angarenta daban zamuce, sai dai bawani k'atun k'atunbafa, dan bawani katafaren gida baneba, yanada dai girmansa gwargwadon hali, kuma tsarin yayi, iri d'ayane da sashen Maimuna, babu wani banbanci saina kayan d'aki, komai Na Jiddah pink and White ne, iya gwargwadon iko dolene a yabama Uncle yahya, kayan gadonta d'aki biyun duk aka zuba, kicinma kam Alhamdllh, saidai mak'iyi. Dayake sunada yawa dandanan suka gama, dan zuwa magriba sun dawo gida, sunata zuzuta tsarin gidan, sun nunama Umma video recording d'in da sukayo, itama sosai ta yaba, dad'i kuma ya kamata, dan yanzune hankalinta ya kwanta da auren d'iyarta. Koda suka nunama Jiddah k'in kalla tayi, saima ta fashe musu da kuka. Aiko dariya suka sanya Mata, ganin da gaske takeyi duk sai jikinsu kuma yay saniyi suka shiga rarrashinta. Washe garifa dangi suka Fara sauka, zuwa yamma gida yayi taf, dangin Umma danasu Abba, kamar taron farko wannan karonma sai rabuwa sukayi saboda gidan Umma yamusu kad'an. A ranar da yamma kuma aka kawo lefen Juddatulkhair daga angonta Sheikh Aliyu maina, suma ammusu tarba ta girma da mutuntawa, kuma kowa ya yaba da lefen Masha ALLAH, dan saidai mak'iyi kam, abin tamkar bana bazawara ba. Jiddah dai ko tarinta bakaji a gidan, koda su aunty siyama suka buk'aci ganinta k'in yarda tayi, dole suka hak'ura suna fad'in ai dai gobe iyanzu takusa shiga gidansu. ('('('('('('('('('('(' A yayinda ake shagalin tarewar Jiddah kuma shima Alhaji garba yanacan yana shagalin tarewa da sabuwar amaryarsa da aka d'aura aure yau hajia deluwa bata saniba, sai wajen tashin hantsi taga anzo ana kwashe kayan 6angaren Jiddah, dariya tayi sosai tana fad'in ?Badole ka kwasheba, da kabarsu su shekara dan itadai tatafi kenan har Abadan?. A wajen kwasar kaya masu kwasar sukaci Karo da abinda Hajia deluwa ta sakama Jiddah. Basuyi k'asa a gwiwa ba suka Kira Alhaji garba suka shaida masa.. Mamakine ya kamashi, babu jimawa yadawo gida bayan an d'aura aure, kai kawai yake iya jinjinawa saboda takaici, ko tantama bayayi wannan aikin deluwa ne, wato wannan shine yasaka Jiddah haukacewa idan tagansa, shine kuma yasatake masa wari?. Sakasu yayi suka k'ona, itakuma bai Mata maganaba dan yanzu bashida lokacinta, ta amaryarsa yakeyi wadda takasance gogaggiyar Y'ar bariki, dan hajia bariki ma ake kiranta, tafi hajia deluwa komai, idanma kud'ine itama ta Tara, tadad'e tana nunama Alhaji garba so amma yana shareta, hajia deluwa kuwa sosai ta tashi hankalinta lokacin dataji hajia Rahina bariki Na sonsa, dan shige-shigen malamai taitayi dan kar hajia rahina tashiga zuciyar Alhaji garba. To a yanzu kuma gashi tashigo batareda ta saniba, ko wane irin zama za'ayi=?9? kuma=?F??-??& @&), tayi k'yau harta gaji. Sai dai daka ganta kasan batada sukuni, magana kad'an za'ai Mata ta6are baki tana kuka. Y'an uwama saisuka koma tsokanarta, musamman abokan wasa, saisu Aunty Sauda ne ke kareta. ('('('('('('('('('('(' Abba dai duk wannan hidimar da akeyi baya gari, dan tun Randa aka fiddo kalifa daga station suna dawowa yahad'a kaya zuwa Abuja wajen wani Alhaji Sammani Moddibo, abokinsane amma yanzu ya haye dan d'an majalisane a Adamawa, Da Abba yabuga tunaninsa yagama yaga babu wajen mafaka, danya Kira Mijin y'arsa Sauda danya ranta masa kud'i ALLAH ya tak'aita wahala Sauda ta d'aga sannan wayar na agunta, saida yagama fad'ar buk'atarsa sannan tace masa ?To Abba ai nice, Ashe dama y'a mace nada amfani da Rana? Ai nazata bazakama ta6a tunamu a cikin y'ay'ankaba balle kabiyo mazajenmu da buk'ata?. Batajira cewarsaba ta yanke wayar taredayin blocking d'insama gaba d'aya, shinefa takira Uncle Yahya da Umma ta sanar musu. Wannan Abu da Sauda taimasa ba k'aramin Sosa masa zuciya yayiba, dan haka yashiga tsinarta yana had'a kaya, aranar yawuce Abuja. Harkuma yau da Jiddah zata tare bai dawoba, ya iske Alhaji Sammani bayanan, amma saiya zauna jiransa saiya dawo, dan ance tafiayar kwana biyar zaiyi, to aganinsa dayayi wahala biyu bai dawoba ai gara ya zauna ya jirasa kawai, yama huta da bala'oin daya baro a cikin kano. Auren Jiddah kuwa yana komawa yabiya Alhaji garba kud'insa saiya tsinkashi, danyayi alk'awarin tunda Yaruwaiya taci zarafinsa gaban y'ay'ansa saiya huce akan Umma, sannan saiya shukama Uncle yahya rashin mutuncin da ko'a hanya bazai sake nunashi a matsayin d'an uwansaba. >?&????-? Bai bartaba saida ya tabbatar jikinta yay sanyi da zuciyarta sannan ya kwantar da ita yana shafa matashin cikinta daya fara d'agowa. Addu'ar barci yafara karanto Mata, itadai tanata kallonshi da k'arajin k'aunarsa musamman da kishinsa, tanaji tana gani yau zasu raba shinfid'a, tunda tazo gidan hakan bai ta6a faruwaba sai dai idan tafiya yayi, amma yazatayi? Idan har takasance mai tsannatawa saidai ta saka kanta a musabar damuwa da rashin kwanciyar hankali, dan bata isa yin jayayya da hukuncin ubangiji ba. Bayan ya shafa Mata addu'ar ya kwanto jikinta, zatayi magana ya d'ora hannunsa saman bakinta alamar tayi shiru. Shirun kuwa tayi tana sauke ajiyar zuciya. Iska yafara hura Mata a kunne, ahankali tafara lumshe idanunta, saida yaga barci yafara cin galaba akanta kafin Yakoma Mata tausa, dand'in hakan yasaka nannauyan barci kwasheta, dama gashi gajiya tamata ligif. Saida ya tabbatar barcinta yayi nauyi sannan ya kuma tofeta da addu'oi ya gyara Mata kwanciya ya kashe fitilar ya fice yana murmushin dashi kad'ai yasan ma'anar kayansa. Nasa sashen yanufa, Wanda ya kasance a tsakkiyar nasu Jiddah, amma shifa falone kawai da bedroom, shima kuma yaune zai Fara amfani dashi, danda a d'ayan bedroom d'in sashen Maimunatu yake, bayan d'aura aurensa da Jiddah kuma ya gyara nasa, dukda bai ta6a kwanaba saikuma yau. Komai an saka, bakajin komai sai k'amshin sabon kaya Dana turaren da Maimuna ta saka. Baiwani 6ata lokaciba yashiga wanka ya fito, jallabiya Fara k'al mai gajeren hannu ya saka, yad'an saka turare ya fito, Gen... Yaje ya kashe, saima yaga an maido wuta wadda yake k'yautata zaton yanzu suka kawota, canjawa yay sanan ya doshi sashen jiddah. Garin yakumayin tsitt dan d'aya takusa, sosai ya yaba da k'ok'arin iyayenta, sai fad'ar ?Masha ALLAH yakeyi, komai yagama dacewa da sashen. Saida ya lek'a bedroom d'in farko yaga babu kowa, sai dai nanma komai tsaf yake, ga k'amshi mai dad'i yana tashi. 'Dayan ya nufa, inda ya hango Jiddah kwance a kan gadon, tawani takure waje d'aya. Bata dad'e dayin barci ba, dan fuskartama jik'e take da d'anyun hawaye daya kuma tabbatar masa hakan, sassanyar ajiyar zuciya ya sauke yana zama kusa da ita, yakai hannu ya d'auke gyalen dayad'an rufe mata fuska kad'an, babu wata kwalliya mai yawa a fuskarta, saima ruwan hawaye dake jik'e da fuskar, murmushi yayi aransa yana jinjina k'aunarta da kuka, akance yacika saurin kuka, amma yalura jiddah senior d'insace. Yanda jijiyoyin kanta suka tashi saiya fahimci batada isashshiyar lafiya, yakai hannunsa saman goshinta, hakanne yasaka Jiddah farkawa ta bud'e Idonta, da sauri ta tashi zaune jikinta yana 6arin tsorata. Saurin rik'o hannunta yayi dan ya lura tsorata tayi. ?Relax Hajiyar tsoro?. Dukda ta fahimci shine hakan baisakata nutsuwaba, dan bata Saba kusanci da wani namiji

Chapter 20 of 31