Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
alama ma yau suka shiga Surar, dan fako yake karantowa cikin kwarewar larabci da taka tsantsan. Masallacin yayi tsit kowa yana saurarensa, sai da ya maimaita ayoyin daya karanta sau uku kafin ya d'ago idanunsa yana kallon d'aliban nasa da zasu iya kaiwa 40+, fuskarsa d'auke da murmushi mai sanyi. Cikin nutsuwa suka shiga maimaitawa suma, yayinda yake musu gyara a inda yaji kuskure. Har k'arfe 9 suna karatu. Sheirk Aliyu ya kalli agogon fatar dake d'aure a tsintsiyar hannunsa, ganin har tara da kusan kwata yay d'an gyaran murya alamar su dakata. duk kallonsa sukayi, yad'an murmusa yana fad'in ?Masha ALLAH, Inaga yakamata mu dakata haka, domin kowa yaje ya k'arasa Uzirinsa?. Duk sun amsa masa da to. Addu'a yay musu kafin kowa yatashi ya fito bayan sunbashi hannu duk sunyi musabaha da bankwanar tashi lafiya. Bayan fitar kowa ya tattare littatafansa yana zare farin glesses d'in fuskarsa sannan ya mik'e shima ya fito. Cikin gidan ya nufa, inda a zauren farko ya iske mahaifinsu malam Abdul-ra'uff da dattijan d'alibansa. Rissinawa yay ya gaidasu, dan yaga da alama suma sun gama karatun nasu na yau, har zai mik'e Malam yace, ?Ali inason ganinka kuwa?. Kansa a k'asa ya amsa da ?To Babah gani?. ?A'a ba ciki zaka shigaba? Shiga ka fito zuwa sannan Na kammala nima?. ?To?. Ya amsa yana mik'ewa. Da sallama ya shiga gidan nasu da a yanzu babu yawan hayaniya, saboda mafi yawan yaran gidan sunyi aure, wad'anda suka rage kuma duk sun mallaki hankalinsu, sai dai jikoki da wasu ke rik'o a matan gidan. Babu kowa a tsakar gida, sai wutar lantarki data haske ko ina kasancewar ba'a kashe gen... Ba saboda masu karatun dare. Kai tsaye k'ofar hajia bah-bah ya nufa uwargidan malam. Saida yay sallama a k'ofar d'akin aka bashi izinin Shiga sanna ya shiga da sallama. Hajia Bah-bah da wata matashiyar budurwa da yara biyu suka amsa. Yaran suka taso suna masa oyoyo. Hannayensu ya rik'e cikin murmushi yana fad'in ?A'a malam k'arami yau anan za'a kwana kaida Ai'shatu??. A tare suka amsa da e Kawu! Zamu kwana wajen hajia bah-bah ne, Ammin mu taje Kaduna. ?Masha ALLAH, ALLAH ya dawo da ita lafiya?. ?ya k'are maganar yana zama a kujerar kusa da k'ofa? Budurwar tace, ?Yaya ina yini? Wad'annan iyayen maganar sun tsareka da surutu?. Murmushi yayi sannan ya amsa da ?lafiya lau Ni'ima, ya makaranta??. ?Alhmdllh yaya?. Murmushi yayi yana maida hankalinsa kan hajia bah-bah dake kishingid'e tana murmushi tun shigowarsa. Cike da girmamawa yace, ?Hajia ina yini??. ?Lafiya lau Aliyu, har an tashi daga makarantar??. ?Muntashi hajia, saikuma ALLAH yasa muna cikin masu kaiwa gobe?. ?To ALLAH ya datar damu?. Hajia bah-bah tafad'a tana tashi zaune sosai. Yayinda Aliyu ya yunk'ura zai tashi, amma sai hajia Bah-bah ta dakatar dashi ta hanyar fad'in ?Aliyu abinci fa??. ?Alhmdllh hajia, dan yau nagaji barci zanyi da wuri, idan naci abinci yanzu zai takura min?. ?To shikenan, bandama dai kanason zama babban kwabo ai kawuce cin abincin gidanku saina matarka, yakamata dai a motsa hakanan Aliyu?. Murmushi yayi yana mik'ewa da fad'in ?Za a duba insha ALLAH hajia?. Bayan fitarsa Ni'ima tace, ?Wlhy kuwa hajia yakamata Yaya Aliyu yay aure, yanzufa kaf gidanan shikad'ai ya rage baiyi aureba a maza, gasu yaya Mahmud da Yaya Usman harsun cika wata hud'u da aurensu, shiko ko maganar ma bayayi, yakamata ya cire Asma'u a ransa, tana gidan mijinta hankali kwance harda yara biyu da cikin Na uku shiko ya zauna?. Hajia bah-bah batace komaiba, amma fuskarta ya nuna alamun damuwa da tausayin Aliyun. Shikam d'akin iya habi ya shiga itama bayan yayi sallama an bashi izinin shiga, ita kad'aice kawai a d'akin, dan dukta aurar da yaranta, sai yarinyar k'anwarta da take rik'o mai suna Maimunatu, itama budurwace, dan zatakai sa'ar Ni'ima. Iya Habi ta tareshi da fara'a kamar yanda ta saba, dan ita mace ce mai yawan barkwanci, cikin tsokana tace, ?Tuzurun gidanmu har an tashi daga karatun??. Fuskarsa d'auke da murmushi ya zauna, cikeda sanyinsa ya gaidata, shi mutumne da bashida yawan magana, shiyyasa ko Ana tsokanarsa bai iya ramawa. Maimuna data fito a d'aki tawani washe baki, a rayuwarta tana k'aunar Aliyu, amma shi yanda ta lura matanma basa gabansa kokuwa duk malantarce oho. ?Yaya Aliyu barka da dare?. Idanunsa yad'an d'ago ya kalleta kad'an ya janye sanann ya amsa da fad'in ?Yauwa Maimunatu, ya makaranta?. ?Alhamdllh yaya, d'azun a islamiyya nazo dubaka a office amma saina tarar ka fita ma?. ?ALLAH sarki?. Abinda kawai yafad'a kenan yay shiru da bakinsa, saima ya mik'e yayinda Maimuna ke shirin zama kusa da kujerar da yake zaune. ?Iya bara naje sai ALLAH ya kaimu?. ?ALLAH ya tashemu Aliyu kaji?. ?Amin iya?. Maimuna da takaici ya isheta kam batama amsaba, tarasa yanda zata shawo kan Aliyu kanta. Iya Habi Na kula da ita, murmushi kawai tayi ta d'auke kanta, tuni ta fahimci Maimuna nason Aliyun. Aliyu kam yana d'akin gwaggo itama suna gaisawa, itama mace ce mai yawan sakin jiki da mutane, nanma ya gaisa da k'annensa biyu dasuka rage a d'akinta basuyi aureba, Asiya da Fatima, sanan ya fito zuwa kiran malam. ('('('('('('('('('('(' Jiddah dake fitowa daga d'aki cikin shirin fita ta kalli Umma dake zaune a tsakar gida tanajin redio, su kad'aine a gidan, su walida sun wuce islamiyya.  Umma bara naje Na duba Maman Sadiq daga nan zanje na duba sa'adatu sulaiman ta islamiyyarmu ance batada lafiya yau ko islamiyya batajeba?. ?To jiddah saikin dawo, amma a dawo dai da wuri?. ?To Umma insha ALLAH?. A k'afa ta taka har zuwa gidan Uncle yahaya, dan basuda wani nisa mai yawa, ta iske gidan shiru, su Sadiq duk sun wuce makaranta, Maman sadiq dake wance a tsakar gida ta d'ago Kai tana murmushi da amsa sallamar Jiddah. ?Yau malama ce a gidan namu??. Jiddah ta zauna gefen tabarmar tana yaye nik'ab d'inta, fuskarta d'auke da murmushi ta fara gaisheta. Maman sadiq ta mik'e zaune itama tana amsawa. ?Maman sadiq yanaji gidan shiru??. ?k'annen naki duk suna islamiyya Jiddah, yasu Zarah??. ?Suna lafiya, suma idan sun dawo islamiyya zasu biyo dubaki?. ?ALLAH ya dawo dasu lafiya?, ?Amin mama?. Jiddah tafad'a tana mik'ewa tsaye, hijjab d'inta ta cire ta d'auki tsintsiya ta share tsakar gidan. Duk wani aiki daya dace tayisa, ta dafa musu taliya bisa Umarnin Maman sadiq d'in. Bayan ta kammala komai taima Maman sadiq daketa kwarara Mata addu'a sallama ta tafi. Daga nan napep ta hau zuwa gidansu Sa'adatu sulaiman d'in. Bata wani dad'e a canba takuma hawo napep zuwa gida kasancewar yamma tayi lik'is, gab ma ake da kiran magriba. Tunda ta fito a napep d'in gabanta ya fad'i domin ganin motar Abbansu a k'ofar gida, jiki a sanyaye ta mik'ama mai a daidaita hamsin d'insa tanufi k'ofar gidansu, kamar kullum saida tayi addu'ar shiga gida sannan ta shiga da sallama. Tunkan ta k'asara shiga take jiyo sautin muryar Abbansu Na magana a zafafe.... Batada ikon juyawa dan haka ta ida shiga. Umma Na zaune a kujera y'ar tsugunno, yayinda Abba ke bisa tabarma da Umma ta shinfid'a masa. Yaye nik'ab d'inta tayi tak'arasa gabansa ta durk'usa, cikin rawar murya tace, ?Abbah ina yini??. Harara yakuma zuba Mata, wadda dama tunda ta shigo yake mata ita. ?Daga ina kike k?, nifa bazan d'auki wannan iskancin nakuba, wlhy duk wadda tajawo min magana saidai ya k'arema uwarku, ke ko kunya bak'yaji kiyita yawo gand'an-gand'an cikin anguwa domin kuji dad'in tozartani a dinga nunaku Ana y'ay'an Alhaji zakari ne ko? To lallai bazan lamunta ba, kodai ki fidda Mijin aure kokuma wlhy Na baki duk Wanda yaymin, itama Zarahn tazo ta fidda miji dan banga amfanin wannan karatunba, kuma da kukeyi bazai amfaneku da Komaiba balleni dake wahala daku?. Cikin share hawaye Jiddah tace, ?Abbah kayi hak'uri, wlhy ba wani waje najeba, gidan Uncle yahaya naje Na duba Maman Sadiq batada lafiya?. ?Wannan kuma ke kika sani, nidai nafad'a miki?. Umma na zaune tana saurarensu, duk k'ok'arinka baka isa gane yanayin da take cikiba, dan fuskarta gwanace wajen shanye damuwa da 6acin rai. Koda Jiddah ta tashi ta shige d'akinsu tana hawaye da kallo kawai Umma ta bita, bayan shigewarta ta d'auke idonta tana maidawa ga Abba. ?Alhaji nikam inason na tambayeka wani abu?. Banza yay bai tanka mataba, sai dai ya nuna alamun yana saurarenta. Bata damuba itama ta cigaba da fad'in ?Shin wani yata6a nuna maka illar abinda kakeyi a rayuwarka kuwa? Baka tsoron ranar da zakayi nadama akan wannan ak'idar taka ne? Kokuwa dan kaga dai ina maka shiru akan lamarin yarannan? Lallai Ubangiji adalin sarkine, domin adalcin mulkinsa ne yasa shi fidda rayayye a cikin matacce wlhy, lallai ina jiye maka ranar dana sani?. Umma Na gama fad'a ta tashi ta shige d'akinta. Cike da tsantsar takaici Abba ya bita da kallo, sai dai kuma ya had'iye abinsa ya mik'e domin bin bayanta. Umma dake zaune a bakin gado tayi tagumi ta d'ago idanu ta kallesa kafin ta janye. Zama yay kusa da ita a bakin gadon yana fad'in ?ke dad'ina dake Yagana rashin fahimta, to miye Na yankamin wannan maganganun??. Murmushi kawai Umma tayi, dan hakan da yayi yakuma tabbatar Mata da zarginta. Ta d'an kallesa a kaikaice, ?Halan yau amarya ta murd'a kanbunta na doguwar tafiya? Shiyyasa aka taho ga juji??...... Da sauri ya saka hannu ya rufe mata baki. ?Nidai karkimin sharri, a yaushe na ta6a cemiki juji??. Nanma murmishin Umma tai kawai ta d'auke kanta tana had'iye wani Abu mai d'aci. Lallai rayuwar wasu mazan wanan zamanin Na d'aure kanta, mace batada wani kima ko muhimmanci a garesu sai in zasu biya buk'atarsu. Takanyi wata bataga Abba a Idonta ba, badan tayi tsufan da bazata iya amfanar dashi ba, a'a sai dan kawai ita uwace ta y'ay'a Mata wad'anda ba sune tsarinsa ko ra'ayinsa ba, idan harka gansa yana yawan zuwa gidan to lallai yayi fad'ane da hindatu ko tayi wata tafiyar da bazai iya jurewaba shikuma, to lallai a wannan lokacin zai maida gidanta wajen zuwa, abinda ke 6ata ranta da zuwan nashi shine gushewar farin cikin yaranta, dan yata caccakarsu da jifansu da kalamai marasa dad'inji, badan sun masa laifin komaiba, sai dan kawai su ba abin sonsa baneba............ Katse mata tunani yay da jawota jikinsa, tai firgigit Na dawowa hayyacinta, sannan ta janye jikinta tana mik'ewa. Fuskar Abbah a d'aure yace, ?Amma kinsan hakan bakomai bane a gareki sai nemawa kai tsunuwar Ubangiji da mala'iku ko? Dan inada ikon nemanki a duk sanda Na gadama kuma nayi buk'ata. Wani murmushi. Takaici Umma tayi tana had'iye hawayen dake Neman cika Mata idanu, da k'yar ta iya furta ?Salla ake kira?. Tsaki yayi ya cire hular kansa ya ajiye a saman gadon sannan ya mik'e, babbar rigarsa ya ajiye itama kusada hular ya fita. Umma ta share hawayen fuskarta da bakin zani kafin tabi bayansa zuwa tsakar gidan. Yana zaune gindin rijiya a kujerar da Umma ta tashi, k'arasowa tayi ta d'auraye butar k'arfe data d'akko a d'aki sannan ta zuba masa ruwa ta rissina gabansa ta ajiye. Hakan yayi dai-dai da shigowar Zarah da Walida suna Y'ar dariya, amma ganin Abbansu Na alwala sai kowa tai azamar had'iye dariyarta, ko kad'an basu Lura da motarsa ba a waje su. Kallo d'aya yay musu ya d'auke idonsa, yayinda sukuma suka durk'usa suna gaisheshi. ?Lafiya?. Kawai yace yaci gaba da alwalarsa. Jiki a sanyaye suka maida kallonsu ga Ummansu. ?Umma barka da gida?. Murmushin kwantar da hankali ta sakar musu tana fad'in ?y'an makaranta an dawo??. ?Eh Umma?. Suka amsa murya na rawa, kafin su mik'e zuwa d'akinsu jiki a sanyaye. Jiddah dake kuka tun bayan tasowarta gaban Abbah ta mik'e da sauri jin maganar y'an uwanta, bata buk'atar su isketa tana kukan, dan haka tai azamar share Hawayenta. Yayinda suka shigo da sallama saita tarbesu da fara'a, harda tsokanarsu. ?y'an matan gidanmu yau kun makara, dolene ayi muku bulalar makara gaskiya?. Duk yanda taso 6oye musu hakan bai hanasu fahimtar tayi kukaba, sai gani kawai tai Walida ta fad'o kanta ta fashe da kuka, itama zaran saita had'asu ta rungume tana sakin Nata kukan. Daman sunsan zuwan Abbansu gidan tamkar zuwan 6acin rai ne a garesu da Ummansu abar alfaharinsu da sonsu. Umma data d'aga labulensu saboda Abba ya fita masallaci tace, ?Kukuma minene haka? Nifa kunsan banason wannan shashancin, kufito kuyi alwala, k Zarah tunda ba salla zakiyiba maza fito ki d'aurayemin kulolin Abbanku Na abinci?. Daga haka ta Saki labulen tabar wajen. Suma sai suka saki juna kowacce Na share hawayrnta, sunsan ita kanta Umman nasu k'arfin hali kawai takeyi. Umarninta sukabi suka fito waje, walida da Jiddah suka d'auka butocin al'awala, Zarah kuma ta shiga kicin d'akko kulolin................. '??

Chapter 3 of 31