Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
baki d'aya, sannan Ku tayani da addu'ar samun damar yin adalci a tsakinku, dan ina tsoron ranar da za'ace gani natashi cikin mutane masu shanyayyen jiki saboda rashin adalci a tsakanin iyalina. Daga k'arshe ina kuma rok'onmu dan ALLAH muji tsoron ubangiji adukkan abinda zamu aikata a wannan zaman, karmu zama cikin masu shiryama juna makirci ko jifan juna da sharri koda Na maganane, karmu biyema duk Wanda zai kawo 6atanci a zamantakewarmu, koda kuwa acikin makusantanmu ne, karmu biyema sharrin zuciya ta sak'a mana abinda zamu dawo muna Dana sani, muringa tinawa a kowanne motsinmu akwai mala'iku dake biye damu rik'e da alk'alaminsu, kuma Ubangijin al'arshi yana jinmu yana ganinmu, ALLAH yay muku albarka yabamu zaman lafiya da kwanciyar hankali Na har abadan?. Kowacce ta amsa da amin, zukatansu duk sai suka kuma raunana dayin sanyi, aganinsu minene abin zafafawa akan wannan gajeruwar rayuwar da bakada tabbacin kaiwa safiya....... Aliyu ya katse musu tunani da fad'in ?Maimunatu mizakice??. 'Dan murmushi tayi na k'arfin hali tana had'iye hawayenta da suka cika mata ido, ?Duk abinda Zan fad'a Yaya ka fad'eshi, sai dai nace ALLAH yabamu zaman lafiya da hak'urin jure yau da gobe, dan itace mai wahalar, insha ALLAHU zaka samemu fiyema da yanda kake tunani, kamar yanda kafad'a hak'uri shine jigon komai Na rayuwa, ALLAH ya bamu mai amfani, yakuma baka k'arfin gwiwar adalci agaremu, dukda Alhmdllh kakai ayaba maka, dan nidai Zan iya bugar k'irji ako ina nace mijinmu adaline, ya banbanta da maza da yawa dakan wulak'anta matansu aduk lokacin da zasu k'ara aure, sannan kuma bakaimin romon bakaba nacewa k'addarace ta sakaka k'arawa badan kasoba, kafito kanka tsaye kasanarmin sonta kakeyi shiyyasa zaka aurota, kaga hakan dakayi ka k'ara Mata kima da daraja a idona, sannan baka tozartaniba yanda Zan kalli k'ara aurenka a matsayin gazawata ba, kabi dukkan sharud'a da matakan da kowanne musulmi adalin magidanci yakamata ace ya d'ora gidansa akai, dan maza da yawa suke gur6ata zaman lafiyar gidansu tunkan aure da bayan shugowar amarya, harga ALLAH ina k'aunar y'ar uwata a matsayinta Na musulma kuma Mace, abinda zai k'ara sakamin ita arai kuma shine zamantakewarmu cikin aminci babu cutar da juna ko k'untatawa, ALLAH yabamu zaman lafiya yakuma k'ara mana tsoronsa koda gujema azabar wuta?. Amin, jiddah da malam suka fad'a. Sannan ya d'ora da fad'in ?ALLAH yaymiki albarka, yakuma k'ara muku k'arfin gwiwa bisa k'yak'yk'yawar niyyarki?. Nanma Jiddah ta amsa da amin. Ya maida kallonsa ga Jiddah itama, ?Jiddah fa mizakice??. Kai Jiddah ta girgiza, cikin sanyinta tace, ?Duk abinda yadace kun fad'a, fatana ALLAH yabamu k'warin zukatan aikatawa da hak'uri, sannan nima harga ALLAH Aunty tashiga raina saboda k'yak'yk'yawan halinta da awannan zamanin yay k'aranci ga mata, akanyi dogon bincike kafin asamu mace irinta, wadda miji zai k'ara aure sannan ta kar6i matar da hannu biyu dakuma zuciyar musulinci, nagode sosai aunty, halayyarki na gari da ya sanarmin tunkan shigowata gidannan tabbas nagansu a yanzu a gareki, ALLAH yabani ikon koyi da nagartarki?. Murmushi Aliyu yayi sannan ya amsa da amin. ?To Alhamdullahi matana nagodema ALLAH Na gode muku, sai maganar kwana, Yaya kuke ganin za'ayi??. Itadai Jiddah k'asa tayi da kanta, dan a ganin wanan ba huruminta baneba yanzun. Maimunatu tayi murmushi tareda d'an kallonsa ta kauda idonta. ?Nidai a 6angarena banida matsala, akan kwana hud'un a marya Na k'ara muku shida, wannan shine gift d'ina agareku na aure, sannan aganina kwana bibbiyu Alhamdllh, amma k'anwata ya kika gani??. Shiru Jiddah tayi tana sunkuyar dakai. ?Kiyi magana k'anwata, dan kema kinada hak'in fad'ar ra'ayinki?. ?duk yanda kikace yayi?. Maimuna zata sake magana Aliyu ya dakatar da ita, ?Yanda kika fad'ad'in yayi, sannan kuma maganar kwana shida da kika k'ara mana mun amshi uku kawai, mun gode?. ?Kayi hak'uri babu jayayya a tsakaninmu, idan kukak'i amsa sainaga kamar kun rainane?. Harara yad'an zabga Mata sannan yace, ?To mungode?. Itadai Jiddah Uffan batace dasuba. ('('('('('('('('('('(' Abba tun yana zama Abuja da shauk'i harta fita aransa, gashi sai cinye y'an kud'insa yake wajen biyan hotel da abinci, kullum ya zagaya gidan Alhaji Sammani sai mai gadi yace ai bai dawoba. Yauma dai yana tsaye a bakin gate sai hucin 6acin rai yake saboda abinda mai gadin yamasa Na wulak'anci da jifansa da Kalmar maula, da girmansa da mutuncinsa a kirasa d'an maula?, horn d'in mota ya sakashi saurin d'agowa, dad'i ya kamasa domin ganin Alhaji Sammani, ajiyar zuciya ya sauke tareda ambaton Alhamdullahi. Har driver zai shige Alhaji Sammani ya dakatar dashi saboda ganin Abba dake jingine a jikin motarsa, ya sauke gilas lokacin da suka tsaya dai-dai saitin Abban. ?Wanake gani haka kamar Alhaji Zakari yaro??. Abba yay dariya mai cike da tsantsar farin ciki yana matsawa jikin motar Alhaji Sammani, ?Wlhy nine kuwa abokina, inata zaryar ganinka amma hakan yaci tura?. ?Ashsha Alhaji zakari, wlhy banda wannan labarin, gashi kuma kullum ina gari, yanzu dai shigo muje ciki?. Jikin Abba Na tsuma ya bud'e motar ya shiga kusada Alhaji Sammani, sai wani dad'i yakeji dajinsa a sama, jiyake yagama da matsalar Alhaji garba ma kawai. =?9?=?9?>?+?Abba=?? ('('('('('('('('('('(' Koda Alhaji garba yadawo gida baiko dubi sashen Hajia deluwa ba balle tasan da dawowarsa, itako tanacan tana cika da bunk'asa har yanzu, yayinda Bala da Ashir keta kuma tunzurata da tsinema amaryar Uban nasu, har suna fad'in tabasu dama su lakad'a mata duka yanda gobe zata tattara da k'afarta tabar musu gidansu. Kumbura Hajia deluwa ta sakeyi, dan ita tafison Alhaji yadawo sufara cashewa kafin tabi takan waccan banzar, dan bak'aramin iskanci k'awayen Amaryar suka 6ararba yau a gidan, gud'a da habaici babu irin Wanda deluwa batajiba, gashi sun fita yawa, tanajin tsoron ta fita su lakad'a Mata duka. Hakanne yasata mak'alewa akan cewa da Alhaji zatayi badasuba. Shikam baimasan tanayiba, yanacan yasamu tarba ta musamman ga amarya, tunima ya manta dawata banza hajia deluwa, Amaryarsa kawai yakeji da gani, yayinda ta gama kasheshi da dabaibayeshi da soyayya itakuma. Har kusan 11 babu Alhaji babu labarinsa, hakanne yasaka su Ashir fitowa zasu sashensu, mamakine ya kamasu ganin motar Abbansu, Bala yakasa hak'uri yaje yana tambayar mai gadi ko Alhaji ya shigo. Mai gadi yace, ?Ah tun kusan takwas da rabi ai Alhaji ya shigo gidan ai?. Idanu bala ya zaro, sannan cikin sassarfa yanufi sashen Hajia deluwa ya shaida mata. Wata uwar ashar ta lailayo ta dire, kafin ta fisgi waya tahau kiran Alhaji, amma harta k'araci ringing ta katse bai d'agaba, saida tayi Kira kusan goma sannan aka d'aga. Cikin masifa tace, ?Sannu munafiki, to ALLAH ya tona asirinka kadaw......? A wata irin muryar kwarkwasa Hajia bariki ta katseta, ?O madam kekuma haka naki salon yake babu tarbiyya da girmama miji? Please kid'an jinkirta yana sunnah ne, zuwa safiya zaki iya ganinsa bye?. Bata tsaya jin zagin da Hajia deluwa ta antayo mataba ta yanke wayar tana dariya. Zubewa kawai a k'asa hajia dealuwa tayi ta daddage ta kwad'a ihu>?+?=?9?>?#?............. '???#?>?#?ho Abbanmu). Nadai tak'aice muku bayani aranar Abba yabaro Abuja ya kamo hanyar kano, sai surutai yake a mota tamkar sabon kamu.=?? ('('('('('('('('('('(' Sai gabannin la'asar Aliyu ya tashi, wanka yayi danyaji k'arfin jikinsa, barcin dayayi yasaka jikinsa nauyi sosai. Jiddah kam barcinta bai wuce Na awa d'aya ba ta farka, Tasha mamakin yanda akai takoma tsakkiyar gadon, tana sakkowa taci Karo da kayan abincin da Aliyu ya ajiye, tashitai taje ta duba ganin abincine saita rufe tafara shiga bayi, bayan wasu mintuna tafito, zama tayi taci abincin, dan dama yunwa takeji. Bayan ta kammala d'akkowa tai tadawo falo, tana zama Ana maido wuta, taji dad'i sosai, saidai kuma matsalar ma ba'a had'a Mata kayan kallonta ba, koma fiddasu a Kwali su Yaruwaiya basuyiba, komawa tayi cikin kujera ta kwanta tafad'a duniyar tunani. Har aka Kira sallar la'asar tana falon, daga bisani takoma d'aki domin yin sallah. Bayan an idarne Aliyu ya shigo, sanye yake da yadi mara nauyi kalar shanshanbale mai duhu, kansa da hula kamar ko yaushe. Kan Jiddah a k'asa tace, ?Sannu da dawowa?. ?Yauwa amarya, ya bak'unta??. Murmushi kawai Jiddah tayi amma batace komaiba. Shima saiya zauna a bakin gadon yana fad'in, ?Naga kin kirani d'azu a waya, nasakata a silent na kwanta barci, sai dana tashi nagani, mike faruwa??. Kallonsa tayi da mamaki, ?Aini wayarma bata wajena, na mantata a gida?. ?Tofa, to kosu Zarah ne dai??. ?yay maganar yana Ciro wayar a aljihun gaban rigarsa?. Jiddah tace, ?K'ila sune to?. Baice komaiba yashiga k'ok'arin kiran Number tata, amma kuma a kashe yanzu, kallonta yayi yace, ?wayarkuma a kashe ai?. ?k'ila babu cajine, ni nazatama zasuzo yau amma babu Wanda yazo saikace basa sonama?. ?Tak'are maganar Idonta na cika da k'walla?. Fuskarsa d'auke da murmushi yace, ?Malama waya fad'a miki dama ana zuwa gidan amarya irin wannan ranar??. Matso hawayen tayi sannan ta saka gefen hijjab ta share. Shi dariyama tabashi, yacire hularsa yana ajiyewa gefen gadon, ?Kincika shagwa6a da sonyin kuka, kuka yana miki matuk'ar sauk'i hajiyata, toyi hak'uri insha ALLAH nasan zasuzo kinji?. Kanta ta jinjina masa, shikuma yay murmushi yana mik'ewa, ?Bara naje gadon k'aya na gaida malam dasu hajia, inaga sai dare zan dawo insha ALLAH?. ?Adawo lafiya, ALLAH ya tsare hanya?. ?Amin ya rabbi Khairunnisaa?. Harzai fita yadawo ya manna Mata Sumba a kumatu sannan ya fice. Ajiyar zuciya Jiddah ta sauke, harma tad'an fara sabawa da halayyarsa itakam. ('('('('('('('('('('(' Ihuntane yasaka Bala da Ashir shigowa aguje suna fad'in  Mami lafiya? Mi akayi mikine??. ?Ashir bazaku ganeba, zuciyata neman tarwatsewa takeyi, yanzunan har akwai ranarda dama kishiya zata fad'amin son ranta akan mijina? Ni ni Deluwa? Wlhy sai matarnan tabar gidannan koda zanyi yawo tsirarane kuwa, har abada dagani sai y'ay'ana zan rayu a gidannan?. Cikin fusata Ashir yace, ?Mami ki kwantar da hankalinki, wlhy idan kika bamu dama bazata cika satiba a gidannan zata Kama gabanta, narasa mike damun kan Dady, yarasa wadda zai kwaso mana sai wannan tsohuwar karuwar, ALLAH garama yarinyar nan Jiddah, dama ita kika hak'ura muka zauna da Dady bai kwaso mana wannan motar hayarba ai?. Hararsa hajia deluwa tayi, ?Kai dan Ubanka waya fad'a maka kishiya duk k'ank'antarta tanada sauk'i, dalla kuficemin anan kafin najuye muku takaicin dake kaina yanzunnan?. Kallon juna sukayi shi da bala suna ta6e baki, suka fice suka barta tana cigaba da borinta da zagi kwando-kwando ga Alhaji garba da amaryarsa.=?C?=?9? ('('('('('('('('('('(' Sai 10:30pm Aliyu ya dawo gida, tunda magriba ya dawo anguwar amma bai shigoba yana massalaci, bayan sungama karatun dare yakuma barin anguwar, sai dai baiwani dad'eba yadawo, Kai tsaye gida ya shigo, tsitt kakeji tamkar babu mutane, leda d'aya ya d'auka yanufi sashen Maimuna, kwance ya isketa harma tayi barci, ganin magani a durowar gefen gado yabashi tabbacin batada lafiya, zama yay kusa da ita yajanye bargon datake ciki yana ta6a wuyanta zuwa goshi, jikinta ringim da zazza6i, tausayintane ya kamashi, bai tadata ba ya tofeta da addu'a ya maida mata bargon sannan yafito. Kicin d'inta ya shiga yasaka Mata abin cikin ledar a firij sannan yadawo falo, tea d'insa da kayan fruits data gyara ya d'auka yafita yaja Mata k'ofar. Saida Yakoma mota ya d'auki d'ayar ledar sannan yanufi sashen Jiddah itama. Bai isketa a faloba, dan haka yawuce bedroom. Zaune take tana duba littafin Umdatul Ahkam, kanta ta d'ago tana amsa masa sallamar, ganinsa da kaya saita ajiye littafin tamik'e ta amshesa tana masa sannu. ?Yauwa Juddatulkhair, ya zaman shiru? Amin afuwa kinsan nid'in sai a hankaline?. Fusakarta d'auke da murmushi amma batace komaiba. Zama yay kan k'aramin kafet d'in gaban gadon ysna kallonta, itakam takasa kallon nashi, tana k'ok'arin aje kayan gefe tace, ?Aunty fa batada lafiya, amma tasha magani tun d'azu ta kwanta, zan kiraka amma ta hana?. ?Eh naje wajenta kafin nashigo nan, Mata kuna k'ok'ari, tunda tasamu cikinan haka taketa fama, nikaina bansan adadin ledar ruwan data shaba ma?. Cikin tausayawa Jiddah tace, ?ALLAH Sarki, ALLAH ya k'ara Mata lafiya, wlhy Na tausaya mata, dan d'azun daga cin abincin sai amai?.

Chapter 22 of 31