Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sauran nutsuwa harya fice, amma haka take dakewa da yawan Addu'ar samun kwarin gwiwa harya fice. Duk dokokin da Aliyu yace ta kiyaye Alhmdllh tana iyakar k'ok'arinta, dama can ita bamai wasa da irin abubuwan nan baceba, zaman sihiri jikinta kawai k'addarace daga ubangji Mai jarabtar Bawa aduk sanda yaso, akuma lokacin fayaso. ('('('('('('('('('('(' Shirye-shiryen tafiya gasarsu ya kankama, dukda duk wannan hidimar da akeyi Abba bai saniba, rabonshi da zuwa gidan kusan watanni hud'u kenan, kuma yana zaune a garin babu inda yaje. Ganin yarage saura kwana biyu su Jiddah su tafi Uncle yahaya yaje har gida ya sameshi da maganar. A harabar gidan ya iske su kalifa na ball, kallo d'aya sukai masa suka d'auke Kansu tareda cigaba da kwallonsu. Murmushi Uncle yahaya yayi kawai shi yana k'arasawa garesu da fad'in ?yarana kuna lafiya??. Cike da rashin kulawa suka amsa suna cigaba da harkar gabansu. ?To ALLAH ya k'yauta? uncle yahaya yafad'a yana kamo hannun kalifa domin tambayarsa. Amma sai yaron yay azamar janye hannunsa yana wani 6ata fuska. Uncle yahaya baice komaiba sai tambayarsu Abba nanan da yay. Muneer kawai ya amsa da eh, amma Hassan da Hussain da kalifa tunima sun koma kan hayaniya akan cin Ball. Haka Uncle yahaya ya k'arasa ciki yana tausayin yayansa akan wad'annan yaran marasa tarbiyya, acikinma Hajia Hindu yatsine-yatsine taita masa, tana shirin cewa Abba baya gida saigashi ya fito saboda jin muryar d'an uwansa. Zama yay suka gaisa Uncle Yahaya ya fad'a masa abinda ya kawoshi. Kallonsa Abba yay rai a 6ace, ?Yahaya kace min dama wannan shine dalilin dayasa kuka kashe Mata aure??. Uncle yahaya yay murmushin takaici yana gyara zamansa. ?Yaya ba wannan maganar bace ta kawoni please, nidai yanzu amincewarka kawai da addu'arka muke buk'ata?. ?Yo inda amincewarsa ake buk'ata Aida tini amfad'a masa basaida lokaci ya k'ureba?. ?Hajia Hindu tai maganar tana gatsine-gatsine?. Murtike fuska Uncle yahaya yayi yana watsa mata wata muguwar harara, ?Kinji na sakoki a cikin zancena Maman kalifa? To ki Kama kanki wannan ba huruminki baneba, kibari idan mungama Na wuce saikiyi keda shi?. Harara ta watsa masa tabar falon tana jan tsaki. Shima Uncle yahaya tsakin yayi ya mik'e. Abba yace, ?Ni wlhy ina mamakin yanda kokad'an kaida Hindu bakwa zama inuwa d'aya, nasan dai yagana ce kawai ke rura wutar k'iyayya a tsakaninku kullum tamkar kuna ganin hanjin juna?. Baki Uncle yahaya ya ta6e kawai, ?Yaya nawuce ni?. Uncle yahaya bai sakebi takan Abba ba tundaga ranar har yau dasu Jiddah ke shirin tafiya k'asa mai tsarki, jirginsu zai tashi k'arfe tara Na darene. &&&*  ALLAH Yaya Jiddah harna Fara kewarki tunma da rana . Harara Zarah ta zubama Walida Mai maganar, ta d'auki kwandon wanke-wanke data gama tana nufar kicin, ?To Uwar iya, kema kad'ai kike kewarta kenan??. Dariya Umma da Jiddah dake zaune kan tabarma sukayi, Jiddah ta janye albasar datake yanka wadda zasuci awara tana fad'in ?Oni Hauwa, wlhy Zarah yanzu kinzama jarababbiya, wannan harar da kike Mata ai saikisa ta rud'e ta tsulma cikin rijiyar?. Daga kicin Zarah tace, ?Yo Yaya Jiddah abunne da haushi, inama laifin tace munfara kewarki, amma saita wani ware kanta?. ?Kishi kike da autata kenan Zarah??. ?Cewar Umma tana dariya?. ?Umma barta ai Zan rama wlhy?. Zarah da Jiddah suka sanya dariya, yayinda Walida ta kwa6e fuska tana dangwarar da gugan hannunta tadawo kusada Umma ta zauna tana kumbura baki. Jawota Umma tayi jikinta itama tan danne dariyarta dak'yar saboda baki da Walida ta kumburo. ?Kinga auta barsu kinji, saina rama miki nima bazan bar saita kwanaba?. ?Yauwa Ummana shiyasa nake sonki?. Ha6a Jiddah ta rik'e tana fad'in ?To a'a mu tsintomu akai madam, wato Ummanki ma ke kad'ai?. Gwalo Walida tai musu, yayinda Zarah takai Mata dundu Umma ta tare. ?ALLAH Zarah kika dokarmin yarinya saina rama mata?. Jiddah tace, ?Umma harda fad'in ALLAH??. ?To tadaketa tagani?. ?Yaya Jiddah barsu, badai an waremu ba, yau kina tafiya gidan Uncle yahaya Zan koma nima?. ?Haba dai y'ammatan Umma wasa muke muku?. ?Umma da walida suka had'a baki wajen fad'a?. Dariya suka sanya suduka. Haka suka cigaba da hirarsu har bayan isha'i bayan sungama cin Awara, daga nan Jiddah tahau shiri dan Uncle yahaya yakura Umma yace ta shirya malam mustafa yace zaizo d'aukarsu. Karfe takwas da rabi kuwa sai gashi shida Uncle yahaya, alokacin kuma kuka yatashi a tsakanin su Jiddah, Umma ma dai tana dannewa ne kawai, suduka gidan sukai mata rakkiya har airport. Wannan dai shine Karon farko na zuwan Jiddah da ahalinta airport, dan haka sukaita zuba k'auyanci, Jiddah dai tanata kalle-kalle amma bata cewa komai sai dariya da take musu itada Uncle yahaya da malam mustafa. Saida kuma aka fara shelar matafiyan jirgin Saudia sannan jikinsu yay sanyi, su Zarah aka fara matse hawaye. Sunaji suna gani aka kira sunan Jiddah a bayan Na Uncle yahaya da malam mustafa. A d'arare ta shiga jirgin ga wani tsoro daketa kuma mamaye zuciyarta, Addu'a tafara karantowa a zuciyarta, indama ALLAH ya taimaketa kusada wata Mata malam mustafa ya nuna Mata ta zauna. Cikin k'ank'anin lokaci sabo ya shiga tsakanin Jiddah da Matar Mai yawan fara'a, da taimakonta Jiddah ta dake kewar y'an uwanta ta ragu Mata a zuciya. Ubangiji ya saukesu lafiya, inda Jirginsu ya sauka a Jidda, itadai Jiddah tanata tsarkake sunan ALLAH a zuciyarta, lallai duniya akwai abubuwan kallo, gaba d'aya saita koma cikakkiyar bak'auya zam, shi kansa Uncle yahaya sai tsarkake sunan ALLAH yakeyi, yau gashi sanadin d'iyar zumu yazo inda baiyi tunaniba (danshi baita6a zuwa makka ba) jiyay yana k'ara k'aunar Jiddah har k'asan ransa, wato zuminci babban abune da mutane ke wofantar dashi bisaga son zuciya, da mutane zasu nutsu su fahimci muhimman zuminci da sun rik'e, shidai babu abinda zai cema ALLAH sai godiya............... '??=ض????#?), sundake sai sayen jarida suke suk'ara ganinta, su Zarah ma har Umma suka sayomawa, aiko tasaka k'asan gado ta 6oye bayan sungama Karantawa, wai zata adana tarihi=??>?-?. Zumud'in dawowar Jiddah garesu dukya cikasu. Lokacin da aka nuna Jiddah a labarai Abba da Hajia Hindu suka gani Hajia Hindu rud'ewa tayi, shikansa Abba yau saiyaji wani iri, yarinyarsace a tsakkiyar manyan mut?ne da duniyar musulinci ke ji dasu, duk surutan da Hajia Hindu kemasa baibi takantaba yatashi yashige d'akinsa

Chapter 13 of 31