Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Balu da taita yanka Mata habaici ita da Gajiram, sai da Umma ta tsawatar musu da harshen kanuri, duk dariyar dakecin Zarah da walida basuyiba, dan wannan ba tarbiyarsu bace saka Kansu a hurumin manya, tun suna k'anana Umma bata ta6a basu damar cin zarafin hajia Hindu ba ko Mata rashin kunya, koda kuskure kayi hakan kuwa ranar zakaci uwaka wajen Umma. Tsakanin su Umma dasu kalifa kuwa babu ko gaisuwa, hasalima d'auke Kansu sukai suna cigaba da kallon ball d'insu da hayaniya da uhu kamar basu ga su Umma ba. (Sun manta Ubansu Na kwance=?F??)? ('('('('('('('('('('(' A washe garin d'aurin auren Aliyu bai samu shigowa wajen Jiddah ba, saboda zazza6i da amai da Maimuna taita fama dashi, saida aka maidata asibiti aka k'ara Mata ruwa sannan tad'an samu k'arfi-k'arfi. Kwana biyu da d'aurin auren ya Kira Uncle yahya ya sanar masa zaizo. Dan haka Uncle yahya shima yaje ya sanarma Jiddah dakeshan gyara itama. A gida kuma ya saka Maman Sadiq ta shiryama malam Aliyu abin tarba dukda yace zuwan dare zaiyi. &&&&& Da taimakon Maimuna dake fama da kanta ya shirya, dan yanzu tarigada ta shagwa6ashi da komai sai an masa. Yayi matuk'ar yin k'yau cikin boyal blue mai duhu sosai, hakama hularsa blue sai takalmi bak'i, sosai Maimunatu ta zazzage masa turarurruka har saida ya kwace yana fad'in ?Malama ya isheki haka, sokike ki karyamin tattalin arzik'in turare ne??. Cikin dariya Maimuna tace, ?Haba dai Yaya, yada saurin karaya haka? Indai turarene zamu saka maka a lefe nida k'anwata Jiddah, kasanfa mu maza Na had'a lefe to mu mune zamu had'a maka wannan karon tsabar kaid'in d'an gatanmu ne?. ?A haba dai tawajena da gaske? To kinga k'ara zazzagamin kawai?. ?Yay maganar yana mik'a Mata kwalaben turarurrukansa?. Dariya sosai Maimuna ta sanya masa, ?Oh ni Yaya, ashe dama malamai sun iya son bati suma??. Murmushi yayi har hak'oransa Na bayyana, ya damk'i hannunta yana matsawa yanda zataji zafi ?Sake fad'e naji?. ?Wayyo Yaya ALLAH da zafi, idan ka tsinke hannun maga Wanda zaima girki a gidannan, dan k'anwatama bazata makaba?. ?Ahaf yarinya, basai naje Na auro Nana Hafsat (miss Xoxo) ba, dama kullum saitamin massage Na soyayya safe da yamma, dukda nace Mata matana biyu tace ko uku ne zatazo ata hud'u dan tsabar k'aunar da takemin?. Cikin had'e fuska Maimuna tace bazazzage zaka zama kenan? To ALLAH kama fad'amata ta kiyayeka, kai d'in mijin mace biyune kacal insha ALLAH, dan naji su Yaburra har suna yad'awa a gidan Alhaji khaleel mai mota dakaje duba y'arsa Islam cewa zaka auri Hafsat d'in, damadai shiru namaka naga gaskene??. (Zazzagawa bayinmufa akwai son Mata da gaske uwargidan malam=???& @&) Hannu yakai zaikuma damk'ota ta gudu bayi tana fad'in  Wlhy katafi k'anwata Na jiranka, inba hakaba nakirata nace karta baka ruwa mai sanyi . Dariyar dabai shiryaba yad'anyi, kafin ya juya ya fita yana d'aura agogonsa da fad'in  Habawa yarinya Zan kamakine, saikinmin bayani dalla-dalla idan Na dawo ai . Zuciyarsa cike take da farin ciki dakumajin k'arin k'aunar Maimunatu a ransa, gefe d'aya Na zuciyarsa Na ayyano masa yanda zai iske amaryar tasa mai idon kuka............. '?)?>???#?=??=?F??:?_* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*=?-?=?O????-?. Su Zarah sukai Mata rakkiya gidan Uncle yahya, lokacin harma Aliyun ya iso, dan haka Maman Sadiq batabar Jiddah tama zaunaba tace tacire hijab ga gyale ta sanya. Idanu Jiddah ta gwalalo kamar zata fasa ihu, cikin sanyinta daya had'u da rawar muryar son Fara kuka tace, ?Mama dan ALLAH ki barni naje a haka, ALLAH bazan iya........?. Uncle yahya daya shigo ya katse Jiddah da tuni kwalla sun cika idonta, ?Wai mikuke jirane kuma? Tun d'azu yana jiranta haka babu k'yau ai?. ?Yi hak'uri Abban Sadiq yanzu zata tafi?. ?Maman Sadiq tayi maganar tana cirema Jiddag hijjab da kanta. Gyalen ta yafo Mata tana d'an harararta, murya k'asa-k'asa yanda Uncle yahya dasu Walida bazasujiba tace, ?Saura kije kimasa dososo wlhy, ki Saki jikinki komi ya nuna yanaso kibarsa, dan wlhy wata yabaro a gida kema kin sani?. Kai kawai Jiddah ta d'aga Mata tafita tana gyara gyalen zuwa saman kanta, abinda bai dametaba a rayuwarta kenan, wato saka gyale, zama ta iya rantsewa tunda ta mallaki hankalinta bata ta6a saka gyale tafita anguwaba. Da wannan tunanin ta k'arasa k'ofar seat room d'in, saida taja gyalen sosai takuma rufe jikinta da fuskarta sannan tayi sallama a hankali. Malam Aliyu dake tsaye akusan tsakkiyar falon ya amsa Mata cikin sanyinsa da zumud'in ganinta, gaba d'aya fitinannen turarenta ya dabaibaye hancinsa tunkan ta shigo, saida taja wasu seconds kafin ta d'aga labulen ta shigo kanta a k'asa, dama gashi gyalen ya rufe Mata fuska, amma tana ganinsa saboda gyalen babu kauri. Shima yana hango fuskarta kad'an dukda tayi k'asa da ita, dan falon kwanyar yake da wutar Gen... Da Uncle yahya ya tayar. Sassanyar ajiyar Zuciya Aliyu ya sauke, kafin ya bud'e dukkan hannayensa alamar tazo gareshi. Ina Sam Jiddah bazata iyaba, dan haka takoma jikin bango ta mak'ure tana kumayin k'asa da kanta, yayinda bugun zuciyarta ke k'aruwa. Murmushi yay mai sauti yana takowa a hankali gareta, duk wani takunsa kuma tsulmata a tsoro yake, dan ta gama lura da gaske kanta yayo. Daf da ita yazo ya tsaya, k'amshinsu yagama gaurayewa waje d'aya yana fidda wani sirri na musamman saboda iskar fanka dake kad'awa tana kuma gaurayeshi. Kallonta ya tsayayi daga sama har k'asa, dukda tana sanye da gyale hakan bai hanashi yaba halittar Ubangiji ba, shikam yadace da mata masu k'yak'k'yawar sura, dan Maimunatu ma masha ALLAH. Sosai Jiddah takejin idanunsa na yawo a jikinta, dan haka takuma k'ank'ame jikinta waje d'aya. Murmushi yakuma saki yana d'an rankwafowa kanta yanda hartakejin fitar numfashinsa, cikin sassanyar muryarsa yace, ?Lallai wannan amaryar mai tsadace, indai sayen fuskane nasiya da farashi mafi daraja Hauwa'u-Jiddah?. Ya k'are maganar yana saka hannayensa duk biyu ya d'age gyalen data yane fuskarta ya saukeshi kan kafad'arta. Da hanzari ta d'ago idonta daya gama tara kwalla ta kallesa, tuni idonsu ya shige cikin na juna, Jiddah tayi azamar janyewa da k'ok'arin duk'ewa k'asa saboda mazarin da jikinta yakeyi sosai, dan tunda take bata ta6a samun irin wannan kusancin dawani d'a namijiba, ko alhaji garba da aka d'aura musu aure bai ta6a koda rik'e mata hannuba, dan haka a yau takejin lamarin da girman gaske...... Kafin takai k'asa itada tunaninta tuni Aliyu yayi azamar ruk'o kafad'unta ya maidata tsaye, kafin tasamu damar yin maganar da take k'ok'arin yi tuni ya sakata a jikinsa ya rungume. Rikicewa sosai Jiddah tayi, ga jikinta Na wani irin tsuma da rawar mazari, abin ya had'e Mata uku, sabon al'amari, lalurarta, gargad'insu Maman Sadiq dasu Balu. Sheikh Aliyu kam lumshe manyan idanunsa yayi yana karanto addu'ar godiya ga Ubangiji ayayinda kasamu wata ni'ima daga garesa, 'DR-NER/O DDGP 'DNQ0PJ (PFP9REN*PGP *N*PEOQ 'D5NQ'DP-N'*P . *_ Alhamdu lillahil-lazee bini imatihi tatimmus-salihat ._* _Godiya ta tabbata ga ALLAH wanda saboda ni'imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika._ 'NDR-NER/O PDDGP 9NDNI CODPQ -N'DM. *_ Alhamdu lillahi ala kulli halin ._* _Godiya ta tabbata ga Allah a cikin kowane hali._ Jin d'umin hawayen Jiddah a k'irjinsa ya sakashi d'agota da hanzari, raba idanu ya shigayi akan fuskarta wadda sai a yaune yasamu yimata kallon tsaf, masha ALLAH tanada k'yawunta dai-dai gwargwado, baiyi magaba sai hannunta kawai daya kama zuwaga kujera, yana k'ok'arin sakata ta zauna a kujerar tai saurin zamewa k'asan carpet ta zauna. Fuskarsa d'auke da murmushi shima ya zauna a k'asan kusa da ita daf, k'afarsa d'aya a tankwashe d'aya kuma a zaune ya d'ora hannunsa Na haggu akai, yayinda yarik'o hannun Jiddah Na haggu Dana damarsa. ?Sannu da zuwa, ina yini?. ?Tafad'a hawaye na sauka a kumatunta?. Jikinta kuma har yanzu rawa yakeyi. ?Ya salam *_Khairunnisaa_*, minene ya sakaki kuka haka? A zatona yau farincikinki bazai musaltuba kamar yanda nakasa kwatanta nawa nima, kisaka a ranki insha ALLAHU babu wani shaid'ani dazaiyi cigaba da tasiri a kanki a halin yanzun, indai kina k'arfafa ranki zakibarma jin wannan tsoron kwata-kwata kinji?. ?Yay maganar yana d'ago da ha6arta da hannunsa na Haggu, Na damarma kuma yana rik'e da hannunta har yanzun yana murza yatsun a hankali. Lumshe idanunta tayi, dan bazata iya had'a ido dashiba, sosai takejin kunyarsa irin wadda bata ta6ajinta gawaniba tunda take, dan abinda yake Mata babu wani mahaluki daya kwatanta yimata bayan alhaji garba da d'ansa, sukuma nasu ya banbanta da nashin. Kanta ta d'aga amasa alamar amsawa. Shi Aliyu duk zatonsa lalurartace takawo hakan, danshi kallon bazawara yake mata, shiyyasa bai kawo a ransa wannan shine Karon farko data samu kusanci da wani d'a namiji irin haka ba, da bazai zo Mata kaitsayeba, zai bita mataki-matakin dazata fara sakin jiki dashine. Goshinta ya sumbata kafin yadawo ya sumbaci la66anta ma da tun d'azun hankalinsa ke wajen. Wani irin zirrr Jiddah taji a jikinta, Wanda harya sakata saurin ja da baya. ?O, ALLAH. A kulani mana, ai najawu sosai hakanan Amarya?. Yanda yay maganar sai Jiddah duk taji babu dad'i a ranta, dan haka tace, ?Kayimin afuwa dan ALLAH, ni....ni...wlhy...?. Saikuma tayi shiru takasa k'arasawa. Rank'wafowa yay saitin kunnenta cikin rad'a sosai yace, ?K...k...mi? madam! Ke a bari saikinje can gidan ko??. Batare data shiryaba ta d'ago idonta ta kalleshi jin ya canja mata magana. Ganin yanda ta waro ido saiya bashi dariya, amma baiyiba yasaki lallausan murmushi yana fad'in ?Maida idon karki sakan Na kasa gane hanyar gidana hajiya?. Gyalenta taja ta rufe fuskarta, Kafin tabashi amsa Walida da Zarah sukayi sallama a k'ofar d'akin. Shine ya amsa yana mik'ewa ya koma saman kujera ya zauna, tareda nasu Izinin shigowa. Kallo d'aya sukai musu kowacce tai k'asa da kanta, yayinda tuni kunyar duniya ta taru akan Jiddah da itama tai azamar matsawa baya tunda su Walida sukai sallama, amma Aliyu ya zauna jikin kujerar data matsa, harma k'afarsa Na gogar jikinta . Kayan hannunsu suka ajiye, suka durk'usa suna gaisheshi. Cike da kulawa da fara'a ya amsa, yagane Walida, Zarah ce bai saniba, dan haka ya tambayi sunanta itama ta fad'a masa, daganan yacigaba da musu tambayoyi suduka akan karatu suna amsa masa. Sosai suma suka birgeshi, dan ya yaba da tarbiyyarsu d'ari bisa d'ari. Sallama sukai musu suka fita. Suna fita yay shirin dawowa k'asa kusa da ita, amma sai tayi azamar fad'in ?Dan ALLAH kayi hak'uri karka zauna a k'asa kuma?. Kansa yad'an langa6e gefe yana narke Mata murya ?Sai dai idan kema zaki dawo nan?. Yay Mata nuni da cinyarsa. K'irji Jiddah ta dafe irinna tsorata d'innan. Sheikh Aliyu da dariyar abinda tayi ke cinsa yace, ?Oh bazaki iyaba ko? Aiko saina fad'ima matata?. ?matarka?!? tayi maganar tana kuma waro idanu akansa sosai da bud'e baki tana fad'in, ?Rufamin asiri?. Kasa hak'uri yayi yanzunkam saida ya dara kad'an musamman dayaga idonta harya kawo ruwan hawaye. ?To shikenan nafasa tunda kin karaya, ammafa ki d'auka 1-0, nine nayi winning kenan?. Gefen gyalen tasaka ta share hawayen da suka cika idonta tana fad'in ?naji ba komai?. ?Lallai wannan amaryar tawa shagwa6a66ace, Ashe aiki ya samemu nida Maimoon?. Baki tad'an turo masa batareda ta saniba. Lumshe idanunsa yayi yana sauke ajiyar zuciya, datasan turo bakinnan abinda ke sakashi data daina, amma zaiyi maganintane inhar bata bariba kafin yabar gidannan. Itakam batasan yanayibama, tuni tamik'e takoma gaban tiren dasu Walida suka kawo tafara zuba masa kunun aya mai sanyi daketa tashin k'amshi. ?Bismillah?. Tafad'a cikin sanyinta. Bud'e idonsa yayi yana d'ago kansa daya jingina jikin kujera, hannunta da kofin ya had'a ya rik'e yana kallon abinda ke ciki, ?Madam minene wannan??. Batareda Jiddah ta kalleshiba tace, ?Kunun ayane?. ?Toke hajjaju dakika bani kunun aya matata Na fama da kanta yakikeson Na k'are??. Jiddah bata fahimcesaba, dan haka tad'an kallesa tana fad'in ?Baka sonshine??. Kallonta yay sosai, danta fara d'aure masa Kai, gaba d'aya yanda take masa sai yake ganin tamkar bata ta6a mu'amula dawani d'a namijiba da sunan miji, had'iye tunaninsa yayi saboda hannunta data motsa, saurin janye idanunta tayi dan satar kallonsa takeyi da. Shima saiya kar6i kofin yana gyara zamansa, ?Badan inada kishi mai tsananiba dana miki wata tambaya, amma bazanyiba, saboda ko'a tunani banason tuna kin ta6a auren wanina kafinni d'in. bara Zansha kawai, ALLAH ya fidda A'i daga rogo dai?. Jiddah batace komaiba itadai, dukda maganarsa ta d'aure Mata kai, dan batasan miyay niyyar tambayartaba. Kulolin tafara bud'ewa, tuwon shinkafane miyar ganye sai tashin k'amshi take. Tana k'ok'arin zubawa Aliyu dake shan kunun aya yace, ?Afuwan Juddatulkhair, danasan zakiyi abinci danace karkiyi, banacin abinci da daddare, wannan kununma ya wadatar dani, amma insha ALLAH zanzo darana kodan naci abincinki kafin kikoma kusa Dani gaba d'ayanki?. Kanta ta gyad'a a kunyace, kafin ta maida kulolin ta rufe, gefe takoma ta zauna sosai yanzuma kanta a k'asa, tace, ?Yaya auntyna??. ?tana gaisheki sosai itama, dan lafiya tamata k'aranci, shiyyasama kikaga tun ranar da aka d'aura aure ban zoba, alhalin hakan kuma ya cancanta, dan ALLAH amin afuwa?. ?ALLAH Sarki ALLAH yabata lafiya, yasa kaffarane, mike damunta haka??. ?Babienkune?. Yafad'a a wani yanayi daya kuma dulmiya Jiddah a kunya, harma tayi dana sanin tambayartasa. Murmushi kawai yayi ya canja firar. ?Kinga sarkin kunya da kuka, k'aramin kununnan tunda kin zurmani gara nasha dama hujja, amma Zan fad'ama auntynki duk ranarda zaki tare tayi kununnan aya itama danta rama?. ?Ni Hauwa'u, yin kunun ayar yazama laifi malam??. ?Niba malaminki baneba yarinya, amsarki kuma sai a nan gaba zaki samu, nidai k'aramin?. Tashi Jiddah tai ta k'ara masa, ita dai yau gaba d'aya bata fahimtar maganganunsa, sannan yana k'ara bata mamaki, batai zaton yana magana hakaba itakam. Haka yayta d'ora kunun aya yana Mata hirar da rabinta duk sakata kunya yakeyi, iyakarta murmushi ko e ko a'a. Goma da rabi nayi ya mik'e, ?To Juddatulkhair bara Na matsa ga Uwargida itama, zuwa talata insha ALLAH zankuma zagayowa gaisheki, a gaidamin Umminmu da k'yau?. Itama Jiddah tashi tayi tsaye, ?Zataji insha ALLAH, ka gaida aunty, ALLAH yabata lafiya?. Harya d'an Fara tafiya yadawo da baya kusa da ita sosai yana fuskantarta, ?Yanzu nan ba'amin oyoyoba, Na gaida gidanma bazan samuba kenan??. Yunk'urin ja tayi da baya yay azamar d'ora hannunsa a k'ugunta ya matsota jikinsa ya rungume, duk tsumar da jikinta yake da

Chapter 17 of 31