Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Shima duk fuskarsa ta Nuna alamun damuwa yana tausayama Maimunatu matuk'a. &&&& Bayan sunsha fruits d'inda saida yasha fama da ita sannan yasa ta had'a masa Shayin, koda yace taci naman daya kawo catai ta k'oshi, bai takurataba ya kammala shan tea d'insa yamik'e yana fad'in tayi alwala kafin ya dawo . Bai jira amsartaba ya fice, kwashe kayan tayi cike da tsarguwa tafito, tabud'e abinda tasan zai iya lalacewa dan batada firij. Umarninsa tabi, bayan tayi shirin barci ta d'auro alwala, duk yanda su Yaruwaiya suka koyar da ita wajen saka k'amshi da tsaftace bakinta saida tayi, kafin tasaka hijjab ta zauna zaman jiransa. Bai wani jimaba can sosai ya dawo cikin jallabiya ruwan k'asa. Kallonta yay damata alamar ta tashi, itadai duk jikinta yayi sanyi, addu'a kawai takeyi a k'asan ranta ALLAH yasa ba zargin datake baneba. Sheikh Aliy ya jasu salla raka biyu kafin suyi zaman addu'ar, yaja addu'a mai tsayo tafatan zaman lafiya a tsakaninsu da sauran al'umar musulmi kafin su shafa ya juyo gareta. Cikin tsareta da idanu ya jeho Mata tambaya.............. '????

Chapter 23 of 31