Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
rawa bai saketaba, saima bakinsa daya d'ora saman goshinta ya sumbata kafin yace, ?wannan lalurar taki batamin adalciba, dolene kafin ki tare da izinin ALLAH na nemo mafita?. Yana gama fad'a ya sumbaci la66anta sannan ya saketa. Dukda halin datake ciki Na gushewar nutsuwar wucin gadi hakan bai hanata yomasa rakkiyaba kamar yanda Gajiram ta gargad'eta. Tun a bakin k'ofa ya Danna key d'insa motarsa takawo haske day'ar tsuwwa, bud'ewa yay yashiga yana d'ebo ledojin gefensa ya mik'o Mata. K'in kar6a tayi tana shirin juyawa. Da hanzari ya damk'o hannunta yana fad'in ?Hajiyata tunadai miji nake ba saurayiba?. Dariya maganarsa ta bata, ledojin ya zura mata a hannu yana sumbatar hannun, ?Kiyi mafarkina daga farkon dare har k'arshe?. Kanta a duk'e tace, ?Nagode ALLAH ya k'ara bud'i na alkairi, yakaika gida lafiya?. ?Amin *Qurratul ain*, maza shiga gidan dan bak'aramin k'ok'ari naiba barinki fitowa nan da wannan gyalen, danma kawai Darene kuma mota ta kare?. Murmushi tayi tana d'an risinawa da fad'in ?saida safe?. Harta shige idonsa k'yam akan bayanta, ajiyar zuciya mai k'arfi ya sauke tareda jingina da kujera yana lumshe idanunsa, yakai hannu yana shafa gemunsa Na sunnah kafin ya maida hannun ga cikinsa, a hankali ya furta  Kunun aya yafara aiki kenan . Bud'e idonsa yayi yatada motar a kasalance yabar anguwar tamkar bayason tuk'in. ('('('('('('. Duk a falo Jiddah ta iskesu har Uncle yahya dasu Sadiq da basuyi barciba, gaba d'aya suka zubo Mata idanu, hakanne yasakata yin kasa da kanta tana sakin ledojin hannunta a k'asa, gani take kamar duk sunsan miya faru tsakaninta da Sheikh Aliyu. ?A'a Jiddodo yada sakin ledoji haka??. Uncle yahya yafad'a fuskarsa a washe da murmushi. ?Babu komai Uncle?. ?To Alhamsullhi, ya tafi ne??. ?Eh?. ?To ALLAH ya tsare, basaikin zaunaba kumuje Na rakaku gida dare yayi?. Ledojin Jiddah ta d'iba takaima Maman Sadiq. ?A'a Walida d'aukar Mata, wannan nakine ai?. ?A'a mama bafa nawa baneba?. Uncle yahya ya katse zancen da fad'in ?Kinga walida d'auka Mata kumuje?. Babu Wanda yay masa musu sukabi Umarninsa. Jiddah ta d'auki hijjabinta ta saka suka fita sunama Maman Sadiq dasu Mageed saida safe. Har k'ofar gida ya rakasu, saida yaga sun Shiga sannan ya juya batareda yashigaba shi. Su Umma duk suna zaune basuyi barciba suna jiransu. Balu ce ke fad'in ?A lallai wannan d'an nawa ya iya zuwa, amarya mikika samo mana??. Fita Jiddah tayi takoma d'akinsu takasa bata amsa, nanfa suka shiga yimata dariya da tsokanarta, tana jinsu amma tak'iyin ko tari, sai abinda ya faru tsakaninta da Aliyu keta dawo Mata kamar wata almara ko shirin film. A can kuwa Gajiram ta bud'e ledojin dasukazo dasu. Kayan marmarine sai ice-cream da kaji guda biyu, sai kuma kwalin waya harda Sim card. Nanfa suka shiga godiya ga Aliyu da fatan alkairi dana zaman lafiya garesu. Gajiram tace walida ta d'auka takaima Jiddah, amma sai Umma ta dakatar da ita. ?Ba haka ya kamata ba, ki raba kowama ya samu, wannan shine dai-dai?. Gajiram tasan halin Y'ar uwarsu da k'yak'yk'yawan tsari akan yaranta, dan haka tabi umarninta, kaza d'a aka ajiyema gidansu Uncle yahya, kayan marmarinma aka d'iba musu, ice-cream aka ajiye roba d'aya, ta raba komai nasu tabama su Jiddah rabi suma su uku suka d'auki rabi. 'Dauka su Zarah sukai da wayar Jiddah suka nufo d'akinsu zuciyarsu wasai dakumajin lallai yanzune Y'ar uwarsu tayi aure. A tsanake sukaci komai sukai gidiya ga ubangiji, kafin su dasa fira da k'ok'arin had'a wayar Jiddah dukda babuma wuta. Suma su Umma dai hirar tasu duk akan tariyar jiddahrne, sunayi sunacin abin arzik'in da ya sheikh Aliy ya kawo. ('('('('('('('('('('('. A haka ya lalla6a hanyar gida bayan ya tsaya yasayama Maimunatu abin motsa baki itama. Dukda dare yafarayi hakan bai hana ya iske tsirarun mutane a bakin masallacin k'ofar gidansaba, dayake akwai wuta a anguwar tasu su, dukda yabaro anguwarsu Jiddah babu kuwa. Wani saurayine dasuke a bakin masallacin ya tashi ya bud'e masa gate, bayan yashiga ya rufe, saida ya tsaya Aliyu yafito a mota ya gaidashi sannan yafito yana masa saida safe. Aliyu kuma ya kulle gidan danya shigo kuma kenan, tsarabar Maimunatu ya d'iba yanufi cikin gidan duk a matuk'ar kasalance, Wanda kallo d'aya zaka masa ka tabbatar da bashida kuzari ko kad'an, dukda shi mutumne mai sanyi dama amma saiya kuma narkewa yanzu. A yanda Maimunatu dake zaune a falo taji sallamarsa kawai saida ta d'ago da sauri ta kallesa da k'yau............. '???)??& @&. ('('('('('('('('('('(' Gaba d'aya Abba zakari a takure yake, yasaba harkokinsa Na kasuwanci a kullu yaumin, amma anzo nan an ajiyeshi wai dan ya huta, anyama kuwa wannan ba tsarin Yahya baneba? Zumbur yamik'e saboda amsar da zuciyarsa ta basa, lallai wannan haka yake, akwai munafinci a wannan lamarin, tunda dai ai shine ya kawo likitan, to waima miyasa yagaza tariyo yanda suka k'are a Station ne?, shiru yay nawani lokaci, kafin babu shiri ya lailayo wani ashar ya dire a k'asan tayis, a lallai yahya yagama ganin gadon barcinsa, yanzu kuwa zaije ayita tak'are wlhy. Batareda jiran likitaba ya had'a inasa-inasa ya nufo gidansa da Hajia Hindu ke a ciki. ('('('('('('('('('('('. Hajia deluwa hakimce a falonta Na alfarma tana waya da hajia Hindu akan auren Jiddah, sai dariya take kwasa tasamun nasara, dan yanzu sakayau takejinta tamkar an sauke Mata kaya a Kai, Alhaji Garba datun farkon fara wayar yashigo yay tsaye tamkar gunki yana saurarenta, dawowarsa kenan daga tafiyar da yayi, cikin zumud'i yanufo sashenta saboda shigar bazata yay mata batasan da dawowarsaba yau, amma saiyaci Karo da abinda ke Neman fasa masa zuciya. Jiddah tayi aure bashiba, mahaifinta ya yaudaresa, matarsa itace ta ruguza masa dukkan shiri ta k'ark'ashin k'asa. A fusace ya fisge wayar ya ratsata da k'asa akan tayis, nan take tayi kwatsa-kwatsa. Hajia deluwa data mik'e a fusace tuni mamaki da tsoro ya baibaiyeta, dan batasan da shigowarba ko kad'an, amma dayake manyan matane sunsan takan duniya saita dake tana kallonsa hankali a kwance. ?Alhaji lafiya kuwa? Ya daga dawowa sai fushi haka? Mi wayata Tamaka??. ?Ban saniba Yahanasu, yanzunan kece da kanki zaki aikata shed'anci Na ruguza auren sunna? Dama son aurena da Jiddah dakiketa nunawa da farko munafuncine Ashe? Lallai yau nakuma yarda makircin mace yafi Na shaid'an girma, anyama kuwa bakece kika kori Jiddah daga gidannanba??. ?Yo Alhaji kaga laifinane? idanma ni d'ince?. ?No ya za'ayi inga laifinki, ban ganiba wlhy? yay wata dariya ta basawa, kafin ya nunata yana cigaba da fad'in ?Kijira sakamakon aikinki Na ruguzamin auren Jiddah da kashe mana aure?. Yana gama fad'a yay ficewarsa, mamakine ya kama hajia Deluwa, tafara safa da marwa Na tunanin to mizai Mata? Miya shirya? Kodai sakinta zaiyi?. Gabantane yay wata mummunar fad'uwa, jikinta Na rawa tabi bayansa. Amma saita tarar ya gark'ame k'ofarsa, duk Nokin d'in datai masa bai kulataba. Kuma yana jinta sarai, dan yanama zaune a falonsa yana k'ok'arin kiran Abba Zakari a wayane. Abba datunda yabaro gidan doctor yadawo gidan hajia deluwa ta tareda da farin cikin samun lafiyarsa, dukda tagansa awani tsume alamun zuciyarsa a kusa take hakan bai hanata tarairayarsa yay wanka yaci abinci ba, harzai fita gun Uncle yahya ta dakatar dashi da maganar kalifa daya shigo gidan yanzu babu jimawa sannan Abba yana wanka. ?Kin dakatar Dani, bakice komaiba kin zubamin idanu?. ?A'a Abban kalifa, bafani nakar zomonba, dama kalifane aka koro daga makaranta sunyi fad'a dawani yaro akan budurwa ya fasa masa Kai, yanzuma haka abinda ake ciki iyayen yaron sunce bazasu yardaba, shiyyasa aka koro kalifa yazo yaje da mahaifinsa yana d'akinsu, Wanda aka turosu tare kuma yana a bakin gate yana jiranka?. Zugudi yayi yana kallonta, bakinsama yamasa nauyin daya gaza furta komai, harma yaushe Kalifan yagama balaga dazai fasa kan wani akan mace?, ina wannan sharrine kawai za'aima yaronsa, dan haka babu inda zayi yanada matsalar data girmi wannan shirmen........ K'arar wayarsa daya kunna babu dad'ewa ta katse masa tunani. Wata mummunar fad'uwa gabansa yayi saboda ganin mai kiran, yanda ya gwalalo idanune yasaka hajia Hindu lek'a wayar, itama saida ta fiddo ido kafin tace, ?Abban kalifa ka d'aga mana?. Kallonta yayi awani yanayin data kasa fassarawa, wayar Na tsinkewa aka sake bugowa, amma Abba yakasa d'auka. Hakanne Yakuma fusata Alhaji Garba daga can, a matuk'ar harzik'e yakuma dannoma Abba Kira. ?Alhaji ka d'auka mana? hajia Hindu tafad'a tana nuna masa wayar, ganin bashida niyyar amsawa ita saita amsa tana saka masa a kunne. Yanda Alhaji garba yay magana dagacan a harzuk'ene yasaka Abba kwarewa da yawu yahau tari. ?A lallai Alhaji zakari, ni zakaima d'ibar albarka, k'in amsa wayata da kayi kawai ya isa bani shaidar kana kan sani ka aurar da y'arka, to ni bazan zauna 6ata lokacina akan hayaniya dakaiba, saidaifa ina mai tuna maka maganar kud'ina miliyan hamsin cif nanda wata d'aya kacal wlhy, dan wannan shinema adalcin dazan maka, sannan kuma namik'a komai a hannun d'ana Ashir dashi zakuyi nabarka lafiya?. Wani haushine ya turnik'e Abba, Dama ga zuciyarsa a kusa take, jira yake a ta6osa ya fidda fushinsa, cikin tsantsar bala'i shima ya dakatar da Alhaji garba dake shirin katse kiran. ?To naji d'in saime, ank'i a baka auren Nata, waishin kasheni zakuyi da haukankune?, shin da wanne zanji? Kama tambayeni yanda akayi mana amma saika hau kaina saboda wata banzar miliyan hamsin, Kai da mutuncinafa babu Wanda ya isa ya takani?. Tsaki Alhaji garba yayi ya yanke wayarsa. ?Amma Abban kalifa da bakai masa hakaba ai, gara ka lalla6ashi ko Zarah saika bashi madadin Jiddar ko??. Wata uwar harara ya zuba Mata, kafin yasaka hannu ya hankad'ata baya, tareda tad'e k'afarta dake hanyar dazai wuce, a take k'ashin k'afar yay k'arar samun rauni. dukda k'arar wahala data saki baibi takantaba ya tsallaketa yafuce a fusace. Turk'ashi=?F???

Chapter 18 of 31