Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kiranta yana shigewa bedroom yabar Umma a falo. Sai dai kuma har wayar ta tsinke bata d'agaba. Kuma kiranta yayi. Hajia Hindu dake kallon wayar taja guntun tsaki sannan ta d'aga. Ko sallama babu tace, ?Alhaji kana inane??. Dukda tambayar tabashi haushi saiya danne, saikace wani yaronta. Amma a fili sai yace, ?Haba Maman kalifa ko gaisuwa ma babu??. Dogon tsaki taja, a harzuk'e tace, ?Kaga malam nifa ba wannan ya sakani kiranka ba, yara suncemin tun jiya baka gida, gashi yau sun tashi motarsu ta zuwa makaranta babu mai........? Cikin nuna damuwa da 6acin rai yace, ?Amma driver d'innan d'an iskane, shine bazai kirani a waya ya sanarminba?, to lallai bazan yarda da wannan iya shegenba......? Hajia Hindu ta katse masa magana da fad'in, ?Aiba laifinsa bane shi kad'ai, inda jarabarka bata motsaba katafi wani waje ka kwana hakan zai faru? Kamayi duk yanda zakayi kakaimin yara makaranta kafin su makara?. Kafin yayi magana ta yanke wayar. Ya dafe kansa saboda takaicin yanda Hindu ke datsa masa magana tamkar boyi-boyinta. Da hanzari yahau shiryawa, dukda ba zaman gidan yakeba yanada kaya a gidan. Lokacin daya fito Umma na k'ok'arin had'a masa shayi da kayan tea d'in da Nafisa ta kawo musu. Ganin zai fice tayi saurin fad'in ?Abban Nafisa ina kuma zakaje ga Karin kumallo ina had'a maka??. ?Kinga barshi Yagana, su kalifa zanje nakai makaranta karsu makara, motar da ake kaisu makaranta babu mai?. ?To?. Kawai Umma tace masa taja bakinta tayi shiru. Shikuma ya ajiye dubu uku a hannun kujera yay ficewarsa batareda yayi bayaniba. Ko motsi Umma kasawa tayi a wajen balle tasamu damar d'aukar kud'in. (Nace,  Humm =?A?). ('('('('('('('('('('(' Lokaci da Aliyu ya fito daga cikin gida malam ya shige falonsa da k'ofar ke a zaure Na biyu. Sallama yayi ya amsa masa tare da bashi izinin shiga. Malam dake kishingid'e bisa lallausar dardumar dake wani sashe Na falon ya d'ago ido yana kallon Aliyu bayan ya rufe littafin dake hannunsa. Zama Aliyu yayi a gefen dardumar, malam yaymasa alama daya matso kusa dashi. Matsawa yay yana guntun murmushi. Saida suka nutsu malam yace, ?Aliyu!?. Cikin sanyinsa yace, ?Na'am baba?. ?Aliyu ina muka kwana akan batun aure? Nazata a shekara d'aya da dawowarka yaci ace kazomin da zancen samun Matar aure, amma sainaji tsit, mike faruwane??. Kansa a k'asa ya kasa kallon malam, cike da kunya yace, ?Baba ai har yanzu......?. Saikuma yay shiru. ?Har yanzun mi??. Cewar malam yana kuma tsareshi da idanu. Aliyu yakuma k'asa da kansa. ?Baba har yanzun banida tabbas akan samun......?. Nanma ya kasa k'arasawa. Murmushi malam yay, dan ya fahimci inda Aliyun ya dosa. ?Ali kenan, to ai a ganina auren shine zai banbance mana hakan ko? Zamanka haka babu aure a matsayinka Na babban mutum mai koyar da ilimi da yad'ashi ko kusa bai daceba, aure shine cikar kamala Na kowanne d'an Adam, duk girmanka da mulkinka da addininka saika saka rigar aure kake kuma daraja a idon jama'a. Yakamata ka nemo Matar aure hakanan, idan kuma ni Na nemo maka to shikenan. Ni dai nabaka watanni uku idan ALLAH ya kaimu, daka dawo daga tafiyar nan da zakayi kafara shirin aure, inason kafin azuminnan mai zuwa ka ajiye iyali, kaje kayi shawara, zaka nemo kona nema maka kafin ka dawo?, idan kuma kanada wadda kakeso saika sanarmin, dan nikam nagaji da ganinka haka kana yawo babu aure?. ?Amin afuwa baba, insha ALLAH Zan duba, abinda Na yanke zakaji zuwa Safiya idan ALLAH ya kaimu, ALLAH ya huci zuciyarka?. ?To Alhmdllh, ALLAH ya kaimu lafiya, kenan kanada wadda kakeso??. ?A'a baba?. ?To shikenan, kaje ina saurarenka zuwa safiyar. Akwai wasu littatafai da Malam Salis keso, nace masa Zan tambaya masa ko kana dasu?. ?To Baba wannene??. ?Yafa bani a rubuce dama dan karna manta, duba littafincan ko ciki Na saka takardan?. Mik'ewa Aliyu yayi zuwa inda kantar buks d'in malam take, ya bud'e littafin dake a jiye a k'asa da malam ya nuna masa. A shafin farko yaga k'aramar takarda dan haka ya d'akko yana nuna masa. Kai malam ya jinjina alamar eh itace. Aliyu yay masa sallama sannan yazo ya fice domin zuwa makwancinsa.. K'aramun gida dake jikin masallacin malam nanne gidan da yaran malam maza duk suka zauna kafin aurensu, ayanzu haka Aliyu ne kawai a ciki sai idan malam yayi bak'i ai musu masauki anan. 'Dakinsa dake can k'arshe ya bud'e da key ya kunna fitilar wayarsa sannan ya shiga da sallama, d'akine babba dake malale da kafet ruwan makuba (oxblood) sai k'atuwar katifarsa irin wadda ba'a sakawa a gado, sai firij da kantar litatafai da k'aramar wardrobe ta kayansa, d'akin babu wani tarkace dan mazaunin cikinsa ma'abocin tsaftane a koyaushe. Fitilar wayarsa ya kashe ya kunna wadda yake amfani da ita idan babu wuta, dandanan d'akin ya gauraye da haske. Wata k'ofa danake k'yautata zaton bayice a d'akin naga ya shiga. Kusan mintuna 30 saigashi ya fito da alama wanka yayi. Bayan malam Aliyu ya kammala dukkan uzurorinsa yazo ya zauna a gefen katifarsa yana jawo lap-top d'insa, yanar gizo ya Shiga domin duba sak'wannin jama'a Na neman fatawa da masu gaisuwa. Ahankali yake binsu d'ai-d'ai yana dubawa, wata fatawar ta tausayi wata ta mamaki, wanima takaici ne tsantsa a ciki. Wasu yakan basu amsa, wasu kam wucewa kawai yakeyi. Wani sak'o dayaja hankalinsa matuk'a ya nutsu yana kuma dubawa. *_Assalamu alaikum. Malam barka da warhaka, malam wlhy inada damuwa ne, kuma Na rasa Wanda Zan tunkara da ita. Mu hud'u iyayenmu suka Haifa, mata biyu maza biyu, nice nake bima babban wanmu sai k'anwarmu sai kuma autanmu, to malam yanayin rayuwar da muka tashi ta ak'idar boko saiya zamto ta6a jikin juna irinsu runguma da zama kusa da juna hakan ba komai bane nida y'an uwana, wannan kusancin mai tsanani saiya kaimu ga fara wuce iyaka har yayana yafara kwanciya dani, iyayenmu basu ta6a saniba konace ak'idar data lullu6e zukatanmu bata ta6a kai tunaninsu da zarginmu ba, malam yanzu haka maganar da nake maka inada ciki wata hud'u kuma bansan da shiba sai kwanaki 6 da suka shige, hankalina yatashi na nufi d'akin yayana danna sanar masa saina taddashi yana irin abinda yakeyi da ni da k'anwarmu dake bimin. Malam narasa yazan fassara wannan halin dabbancin namu, sakacin iyayenmu ne? kokuwa d'aukar ak'idar da bata dace da addininmu ba?, wlhy jinake tamkar Na kashe kaina malam, nayi nadamar rayuwata data y'an uwana, malam ka taimakeni da shawara dan ALLAH=?-?=?O???????

Chapter 4 of 31