Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Haka ma Auwalu shima yayi Auransa yatare da matarsa a garin Abujah dake shi yana ha'dawa da aikin gwannati Jibiril ko San mata yasa agaba damuwar shi ya aikata xina da 'Yar mutane ya biyata Anan duk ku'din da yake samu suke qarewa yaqiyin Aure sam Jabiru ko neman ku'di kawai yasa agaba Shine siyan filaye gidaje da dai sauransu gashi dasan yasaka hannun jari a garuruwa Ananan ananan wata rana yaje saudiya dan sauke farali Anan ya ha'du da Khamsa'u balarabiyar qasar Harif Kallo 'daya sukama juna sukasan sun kamu da qaunar juna Dake wayayyune anan kowa yabaiyana kansa ga 'dan uwansa Khamsa'u dai 'yar Sarkin garin harif ce Ita ka'dai Allah ya bashi Baqamin so mahaifinta yake mata ba Saidai yanada burin samun 'da namiji Mahaifiyarta mah 'yar sarauta CE kuma itama ita ka'dai agun iyayanta Lokacin da tasamu Cikin Khamsa'u alokacin ne iyayanta suka mutu sakamakwan wata cuta da tashiga garin iyayan nata wanda takashe rayuka da dama Hakan yasa dukkan wata dukiyar mahaifanta tadawo hannunta Ta haifi 'yarta Khamsa'u suka raini abinsu har girmanta Wanda ayanxu take shekara ishirin da uku Sunxo sauke faraline saudiya shine Jabiru yaga Khamsa'u suka fa'da qaunar juna Tun aranar iyayan Khamsa'u suka San da Jabiru Da sun qita dashi Amma ta bijiremusu Sam Haka suka rabu da ita bayanda suka iya Soyayya tayi qarfi tsakaninta da jabiru har magana tayi xafi iyaye suka shiga xancan Dan koyaushe Jabiru yana hanyar garinsu Harif Daqar magana tayi qarfi har Allah yasa Khamsa'u taxama mata ga Jabiru Iyayanta sukace baxai kawo musu 'ya Nigeria ba Saidai ya xauna da ita a qasar Saudi dan tafi kusa da qasarsu Dake Jabiru ya mutu kan Santa haka ya yarda yasai gida aqasar saudiya suka tare da Amaryar tasa. Tunda Jibiril yaje yaga maxaunin qanin nasa Jabiru yaga sai hankalinsa ya tashi maqin cikinsa yaci karfinsa nan yafara tunanin Hanyar da xaiyi ya kashe Jabiru danya mallaki dukiyarsa Lokacin ko idan Jabiru yaqara wayewa dan shiga qasashe da yakeyi shida matarsa Khamsa'u Nan yasa hannun jarinsa a qasar Kuwait yasaka a England yasaka a American Wa'yannan qasashe uku dayasa hannun jarinsa sune silar qara ha66akar axxiqinsa Mutum ne me San temako me ibada da San Allah da Manzansa Hakance tasa yaware kasu mafi tsoka daga dukiyarsa yaba yayun nasa Naziru da Auwal ne kawai sukayi farin ciki da kyautar suka dinga murna dasama qanin nasu albarka Jibiril najinsu yajah tsaki Yace wai murnar mesukeyi dan yabasu 'yan ku'din dabai taka kara ya karya bah Duk da kallan mamaki suka bishi dashi kana suka hango tarin baqin ciki da hassadace take damun yayan nasu Wata rana iyayan Khamsa'u suka shirya kawo mata xiyara. Sai dai basuxo gareta ba jinginsu yasami matsala sukayi mummunan hatsari Wanda duk nacikin jirgin yarasa ransa dan babbakewa sukayi Sanda Khamsa'u tayi shekara kafin mutuwar tasaketa Alokacin ne kuma tasamu ciki..... Wai xokuga murna gun Jabiru Kowa ya tayashi murna da samun wannan cikin musamman da akayi scanning aka gano 'yan biyu kuma Dukka maxa Lokacin Naziru yana da 'yarsa Saudat Auwal kuwa Saida cikin Khamsa'u yakai wata hu'du Matarsa tasamu ciki Hmmmm Jibiril yasamu qannansa Naziru da Auwal Yace yanaso subashi ha'din kai su kashe Jabiru da matarsa Khamsa'u dan Su mallaki dukiyarsu Idan suka mallaki dukiyarsu ya tabbatar wani ikwan Allah ne xaisa suyi talauci arayuwarsu Sam Naziru da Auwal sukaqi yarda da hakan dan sunasan Jabiru abin duniyarsa bai rufe musu ido bah Yace toh shikenan shi xai aikata kuma Wlhi suka fidda wannan xance saiya hallakasu suma Naziru Yace ai Yaya bame harnakawa sai Allah haka kuma baxai baka damar cin galaba akansu ba Auwal Yace hakane kam Murmushin mugunta Jibiril yayi Yace xaku gani Da ido suka bishi Suna mai addu'ar Allah yayaye mishi Baqin ciki Ana saura wata 'daya Khamsa'u ta aihu tadanqama mijinta Jabiru dukiyarta me tarin yawa Tace yajuya mata Wata qanwar babanta Amme Salima wacce take Aure anan qasar saudiya da Naziru da Auwal Yayun shi jabiru sune suke da shaida akan mallaka mishi dukiyar tata da tayi Nan yasa mata Su a hannun jari na qasashen da yake harda Kuma duk dukiyar tashi da tata yasaka musu Suna 'daya dashi ne mutum yake da damar mallakar wannan dukiyoyin ko bayan ransu Wato wannan sunan shine sunanta Wato ( *Khamsa'u* ) Indai bada wannan sunan kayi amfani ba kaje kar6ar wani ku'di a American England Kuwait toko in aka kamaka 'daurin rai-rai ne dan ansan ba naka bane Toh Jabiru ya ke6e da 'yan uwansa biyu wa'yanda ya da'de da sanin SOYAYYAR gaskiya suke masa Wato Naziru da Auwal Dan haka yagaya Komai akan dukiyarsa data matarsa Sun jinjina masa kuma suntabbatar masa bamaijin wannan sirrin nasa . Ranar ta kasance Asabar mummunar ranah ga masoyan Khamsa'u da Jabiru Dan Jibiril ya samu nasarar harbe Jabiru qiri qiri acikin gidansa lokacin Khamsa'u tafuta tirenin 'din masu cika nan kusa da gidanta Aiko tana dawowa taga gawar mijinta alamar kasheshi akayi. Nan tashin hankali ya sata na'kudar dole 'Yan aikin gidannane suka kaita asibiti Annan ta haifi RAMADAN da RAMADAN junior Bayan aihuwarsu da tayi da minti biyu tace ga garinmu nan. Rai yayi halinsa Kuka Sosai Naziru da Auwal sukayi ganin gawar 'dan uwan nasu da matarsa Abin takaici Jibiril ya tabbatar musu da cewa shiya kashe Jabiru Basuyi mamaki ba dan sunsan dama tunda Yace saiya kasheshi ikwan Allah ne xai hanashi aikatawa Amme Salima tanemi da Jibiril da Auwal Naziru subata 'yan biyun nan Amma sukaqi musamman Auwal dayace shixai 'dau 'daya shi kuma Naziru ya 'dau 'daya Haka tanaji tana gani suka qi batasu Amma sun bata tabbacin xasu dinga kawo mata Su tana Ganinsu Tayarda da hakan Bayan sun rabu ne akan hakan Jibiril ya bu'de musu wutta akan Saidai subashi yaran Sukuma suka mishi Jan wiya akan baxasu bashi suba ya kashesu Daqar yasamu kansu suka bashi 'daya bayan yayi musu rantsuwa akan baixai cutar da yaran ba Su temaka mishi xaisamu me shayarwa ta shayar dasu Sam sukaqi Daga baya dai suka bashi 'daya Wato junior RAMADAN qaramin ciki kenan Yaran sunci suna kamar haka Muhammad da Sadeeq Muhammad shine RAMADAN 'din SAILUBAH Sadeeq kuma shine RAMADAN junior Sai Naziru ya 'dauki RAMADAN nasa ya ha'da shi da 'yarsa Saudat Daga baya yasamu khairat Jibiril dama bashi da niyar kuma kashe junior RAMADAN dan Hakka kawai Allah ya jarrabeshi dasan yaran Abinda yakeso dai yasamu Danya samu dukiyar Jabiru Dangin Su gidajan da filiyan da yasiya a nan gida Nigeria sudai ya samu Dan baisan da wancan hannun jarin da Jabiru yake dashi a American England Kuwait ba Tafiya tai tafiya har ya cinye komai. To dama hakkin marayuu ina xai kaisa Ganin haka yasa yayi wani rikakken 'dan fashi Anan ya shige harkar Aikowa yaxama wani Babba a harkar Tunda ya kar6i junior RAMADAN bai ta6a kawoshi kano ba Haka 'yan uwansa Auwal da Naziru suke mishi nacin ya kawo musu shi Kullun saidai yadinga turo musu da hotansa Wata ranah Amme Salima taje gidan Jabiru dan tunawa da 'Yar 'dan uwan nata Tana binciken kayanta sai kawai taga diarys biyu nan ta karanta na farko taga na Khamsa'u ne Ta karanta nabiyu saitaga na Jabiru ne Dan haka saita kaima Alhaji Jibiril har garin Abujah Tace ya ajiyema Su RAMADAN xai musu amfani wata ranah Toh tunda ya kar6a ya bai ta6a tsayawa ya dubawa ya karanta bah Saidai yana ankare dasu dan yalura junior RAMADAN 'din yanasan karantawa Gashi kuma yanasan rigashi karantawa shiyasa Sam yake hanashi 'dauko idan yaxo 'dauka Shima yana mamakin yanda akayi yakasa tsayawa ya karanta kuma xuciyarshi tahanashi barin junior RAMADAN ya karanta Alhaji Jibiril ya sakama junior RAMADAN sunan RAMADAN 'din SAILUBAH ne dan in rana ta6aci masa a Nigeria aka gano fashin 'dan nasa yabar garin Abujah Sannan ya rubuta leta mah jami'an tsoro ajan suje garin kano wanda suke nema yanacan Toh sai Allah ya 6abunta al'amarin Yabama junior RAMADAN ilimi da kulawa shiyasa Sam junior RAMADAN yataso a shagwa6e saidai akwai aiki da hankali da ilimi Yana karatu a qasar England inda yakesan xama cikakken doctor Duk lokacin dayaxo hutune Alhaji Jibiril yake turashi yin fashi da makami Dan ayanxu mah hutune ya kawoshi Abujah shine Alhaji Jibiril "din ya turashi fashi gidan Dadyn shahuda. πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘― *SAMAREEN BANAH* πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘― *TASU SALAN SOYAYYAR* Junior RAMADAN yaja numfashi dan kammala karanta diaries 'din da yayi Kanshi ya 'dau caji yagano tabbas mahaifinsu ba mutuwar Allah da Annabi yayi Bah. Kasheshi akayi..... Kuma yana xargin Alhaji Jibiril da kisan Dan rubutun mahaifin nasu yatsaya mai a inda ya gayama yayunsa biyu akan hannun jarin da yasa a qasashe uku sukace bawanda xaiji wannan sirri nasa Ya qara jan numfashi yana San sanin ya akayi mahaifunsu ya mutu da mahaifiyarsu Dole yaje ga Dadyn brother 'dinnan nasa yaji ya abin ya kasance Wanka yayi yayi. Sallah kana yabi lafiyar gado da tunanin Yayan nasa RAMADAN ko yanxu an sake shi ko ba'a sakeshi ba oho Koma miye yabarma awa 'daya kacal...πŸ‘ŒπŸ» Idan yatashi yaji komai..... Yusra CE take yunqurin shiga gidansu Wani saurari ya tareta yana fa'din sannu 'Yan mata Tace Yauwa Yace dan Allah dama RAMADAN anan gidan yake Tayi Murmushi kun san Yusra da surutu nan tafara mai xuba kamar kanya Tace ayya Ya RAMADAN ai 'dan kano ne ya kawoma Momyna da Dadyna da kuma wata Auntynsa SAILUBAH xirayane Ina sanshi Sosai Yace ayya haka kawai naji ina sanshi nima inasan inyi abota dashi ko xakiban adireshin Sa na garin kano Tayi dariya Tace Sosai mah. Ina lefin me sanka Nan taxage tagaya mai Komai akan RAMADAN Wanda ta'dan sani Tana cewa Wlhi xakaji da'din abota dashi dan yanada hali mekyau Yace Allah qanwata Tace Wlhi da gaske Yayi Murmushi dayi mata godiya har yana cewa in tashiga tagai sheshi kuma tace mishi zaixo anjima Ta gya'da kai Tace toh ta shige ciki Kana ya tafi yana mamakin magana irin nata Senior RAMADAN na bacci Yusra ta tadashi Yace matsala ya akayi Tace hmm wani ne ya tareni daxan shigo gida wai Yana sanka yana San yayi abota dakai Na bashi bayanai akanka Sosai Yace me kika sani akaina Tace abubuwa da yawaπŸ˜€ Yayi Murmushi Yace ko Tace Sosai mana Yace angaisheki jeki ha'damin Lipton Tace aha Yayana Tafita. Yabita da kallo Batafi minti uku ba saigata da Lipton 'din Yace nagode Tace dame fah Yace haka dai Tace Allah bana so ka dinga min godiya idan na maka abu Yace dalili Tace nima hakka dai Ya mata Murmushi kawai batare da Yace Komai ba Junior RAMADAN ko yana tsaka da baccinsa yaransa suka tasheshi Yace dafatan kun gano min shi 'Daya daga cikinsu Yace eh Amma ba dukkan labaran ba dan wasu sai sunkai gobe Ayau Inuwa ya tafi garin da yake Kano Dan ya sami bayanai agun wata yarinyar gidan daya sauka anan Yusra Ta tabbatar mishi sunansa RAMADAN kuma agarin kano yake da xama awata unguwa Fage Na tabbatar maka xai gano maka ko shi Waye Yace gud... Hakka nakesan jiii...... Wani acikinsu Isma'il Yace oga naganshi 'daxu akofar gidan Alhaji Aminu Junior RAMADAN Yace Waye kuma shi Yace wani 'dan kwungiya ne ba abinda bayayi Cikin mamaki junior ya tashi Yace toh meya ha'da 'dan uwana dashi Yace eh toh. Idan kana buqatar sani yanxu xan binkicuma Yace dako naji da'di Haka Isma'il yaje ga megadin gidan Alhaji Aminu Yacika shi da ku'di akan yanasan yasan me yakawo RAMADAN gunsa 'daxu Yace aidama sunansa RAMADAN Isma'il Yace eh Nan ko megadin ya gayamai Komai akan 'Yar uwarsa Alhaji Aminun yake Aure kuma ya hanata jin kowa nata Nan dai da Isma'il ya samu abinda yakeso yayima megadin sallama ya tafi Shiko yanata murna yau sai samun ku'di yake Direct Isma'il ga junior RAMADAN yaje Anan yagaya mai Komai Junior RAMADAN yayi Murmushi Yace aha Yana San ya futar da ita daga gidan ne Dan shi da ita sungano ko shi Alhaji Aminun Waye Isma'il Yace idanko haka ne ya kamata kasa mishi hannu oga dan baxai iya fidda ita daga wannan gidan bah Yace Hakka Amma ya xanyi in gansa shi Alhaji Aminun Isma'in yace nasan wani hotel da yake xuwa cin abinci qarfe takwas na dare Junior Yace gud...βœ” Ina san gobe da qarfe takwas 'din muyi ram dashi dan wlhi saiya saketa dan ubansa..... Isma'il Yace angama oga.. Washe gari ko kusan qarfe biyu RAMADAN yayi parking 'din motarsa a 'kofar gidan Auntyn tasa..... Kamar yanda megadi yace mai xai jira xuwansa hakance ta kasance Yace Barka da ranah me baba Yace barka dai samari RAMADAN yamiqa masa ku'di da wani abu acikin Leda Yace wannan xaka bata Yace Amma ku'din yau yafi na jiya RAMADAN yayi Murmushi Yace aikai ka buqaci aqara maka farashi Ya washare baki Yace ashe baka manta ba samari Yace ai dama bai dace na manta da hakan ba dan ayanxu ba abinda yafika mahimmanci arayuwata kamarka Dan kaine kake sadani da abinda yafi min Komai arayuwata Megadi yayi Murmushi Yace kanasan yayarnan taka Yace fiye da Komai mah Nan dai megadin ya shige...... SAILUBAH na xaune tana kallo lokaci lokaci tana kallan agogo addu'arta Allah yasa taji qanin nata yanxu Kamar yanda take fata ko sai ganin megadi tayi Tace yanxu naketa sake saken xuwanka Yamiqa mata ledar hannun nasa cikin ladabi Ta kar6a jiki na rawa Tana bu'de ledan taga wata qaramar wayar RAMADAN ce Farin ciki kamar ya kasheta Tace shikenan babah megadi jeka Yatafi yana Murmushi har yaxo ga RAMADAN. Yace nabata samari Yace Yauwa toh sai anjima Yace gobema xaka dawo Yace eh toh bandai saniba amman karka damu Yace toh nidai ina saurare Murmushi RAMADAN yayi yaja motarsa Yana tuqi yanata ganin kiran Auntyn tashi Amma yaqi 'dauka dan yana san sai yakai gidan kawun nasa ya 'dauka yafi jin da'din magana da ita Yana kaiwa ko ya shige bet room ya baje agado. Xai kirata kenan Amar ya shigo 'dakin Yace brother ya kamata yau mu 'dan xaga gari Yace toh bara inji nutsuwata sai muje Amar yayi dariya Yace toh kafito lafiya Yace Allah yasa Kiranta yayi Yace Auntyna Tace naji dadi Sosai Wlhi Yace nasan xakiji da'din yanxu bani labari Tace farkwan labarin shine kaci abinci Yace eh toh bandaici na yanxu ba Amma naci na safe Cikin sanyi Tace kaci pls Yace Wlhi Auntyna konasaka agaba inna tunoki kasaci nake Tace wayyo Qanina kaci dan Allah kasanfa bana san xamanka da yunwa Yace nasani Kinga nasami wata mafuta guda 'daya.... Tace toh fa'di inaji Yace mexai hana ki'dan roqeshi ya kaiki ko gidan matar abokinsa ne Kinga daga nan sai musan yanda xamuyi yanda bazaki koma gareshi ba Tace Yauwa kakawo shawara. Amma matsalar 'dayace ko ganinsa bana san yi natsaneshi bana qaunarsa. RAMADAN yaja numfashi Yace kidaure my Aunty Wlhi nayi missing 'dinki sosai ina buqatarki kusa dani Tace nice nake buqatarka RAMADAN. Ka shagwa6a ganina da ganinka. Ba abinda nakeso ayanxu kamar in ganni gani gaka Qanina Dan Kullun sai nayi mafarkinka. Yace Allah Auntyna Tace Wlhi Qanina Yace toh kiyi abinda nasaki Tace toh kaci abinci pls Indai kanaso nasami nutsuwata Yace angama my Aunty bye-bye den luv u Tace love you more my futuna..... Da Murmushi ya waro ido😳 Yace nine futuna ko Tayi Murmushi cikin sanyi Tace ko yanzu ganin bani kusa ka dena ne Yace idan kika dawo xan 'dora akan inda natsaya Tace aha. Bana gajiya da hira dakai Qanina Yace nima haka Auntyna Tace kaci abinci yanxu bayan ka gama muci gaba Yace Owkie Da misalin qarfe biyar inuwa ya kawoma junior RAMADAN rahotan Komai na RAMADAN Da yanda yake dasu KHAMIS da FAWAS da yanda ya shaqu da Auntynsa SAILUBAH Komai dai sanda junior RAMADAN yaji Yayi Murmushi kawai Qarfe takwas ko nayi na dare junior RAMADAN sukama Alhaji Aminu dirar makiya Yana Cikin 'dakin da Yakama a hotel 'din Junior RAMADAN da Isma'il suka buqaci ma'aikacin wajan daya gaya musu wane 'daki yake Da farko Yace dokace ba'a fa'din inda mutum yake a hotel Amma dayaga ku'di ai bashiri Yace musu yana 'daki mai number goma Sha shidda Haka ko sukaje gareshi Kofarma abu'de take Sai kawai suka shiga suka dannama "kofar key Alhaji Aminu Wanda yake cin abinci ga wani saurayi najiranshi yagama sufa'da masha'a. Sai kawai yabi junior RAMADAN da kallo Cikin mamaki Yace RAMADAN meya kawoka nan Junior RAMADAN yayi Murmushi ya 'dora qafarshi 'daya a table 'din da yake cin abincin yana juya bindiga Yace abu 'daya ne ya kawoni Cikin tsoran yanda yake juya bindiga Alhaji Aminu Yace miye shi kuma meyasa naganka cikin wannan yanayin bayan nasan kaime nutsuwa ne gashi kamar ba imani atattare dakai Junior RAMADAN Yace au haba shege Alhaji dama kasan imani kake kashe qananan yara kake 6ata maxaje da ma'digo Kake cikin kwingiya shan jini Alhaji Aminu yayi shuru ya bishi da ido da mamakinsa da kuma tsoran yanayinsa Junior yaci gaba da fa'din. Toh dan ubanka idan kana iskanci mu asamanka muke Duk da bama ko 'daya acikin abinda kakeyi Amma nafika iskanci Wlhi So nake kasaki SAILUUVAH....... Sai kuma ya kalli Isma'il Yace Hakka sunan yake ko Da Murmushi Isma'il Yace eh haka yake oga Saidai naji da'din yanda a ambaci sunan da alama kafi kowa iya fa'dar sunan Ya tabe baki da maida kallan ga Alhaji Aminu Yace nima haka kawai naji sunan yayimin idan na ambaceshi inajin da'dinsa abakina Sosai Alhaji Aminu Yace baxan iya sakinta ba............. Aikam ya qarasa furucinsa junior RAMADAN ya sakar masa harsashi 'daya a kafa'da Nan Alhaji Aminu yasaki wata furgitacciyar qara yadafe gun tare da tashi yajah baya cikin tashin hankali da tsoro Junior Yace Shege angayama ana yimin musu ne acikin wannan yanayin da nake ciki Kayi kuskure Tayaya xa'ayi ka Auri yarinya ka ajiyeta batare da kana mata amfanin Komai ba Ko An gayama ita 'din bishiyace da xata rayu haka bajin 'dimin mijinta kusa da ita. Cikin maseefar tsoro Alhaji Aminu Yace na roqeka da Allah karka kasheni inasan rayuwa ban gaji da ita ba. Yace toh naji Yanxu so nake kasaketa Cikin daran nan Gobe kuma kinji barinta gidanka da misalin qarfe goma Idan ba haka ba Wlhi kaji na rantse yanda nabaka wutta a kafa'darka haka xan qara baka a cikin xuciyarka Ya fa'din haka ya fitta daga 'dakin Isma'il yabi bayansa Iya tsorata Alhaji Aminu ya tsorata da junior RAMADAN Jikinsa na rawa ya sallami wannan saurayin dan badamar aikata abun nasu yana cikin jini. kana ya 'dora suwaita akan rigarsa shima ya fitoh dan xuwa ga doctor ya cire mashi harsashin Bayan angama mishi Komai ya xauna hutawa kafin ya nufu gidan nasa. Junior RAMADAN ko da qarfe goma Sha 'daya ya kwanta dan jiyayi kansa nayi masa ciwo Baiyi nisa a baccin bah yaran nasa suka tashe shi Ya qare musu kallo ba Isma'il aciki Yace kunxo kashe ninne kamar yanda yasaku ranar Suka kalli junansu Kana sukace ka yafe mana oga mun amsa mishi da xamu aikata hakan Saidai baxa mu iyaba musamman idan muka tuna halaccinka garemu Yace gud ashe Ku 'ya'yan halak ne. Kunyi kyan tunani duk da ban ta6a kisa ba. Da ace bakuyi wanna tunanin ba dako nafara kisan akanku Kuje gareshi kuce mishi baxaku iyaba shi yaxo da kansa ya kashenin Haka ko suka juya suka fitta Yabisu da kallo Alhaji Jibiril 'din yana falansa suka gayamai baxasu iyaba Yajah numfashi Yace hmm nasani baxaku iyaba. musamman idan kuka tuna alkairan da yakema iyayanku. Kuje karku damu xansan yanda Xanyi dashi. Alhaji Aminu Lokacin da ya'isa gidansa qarfe 'daya ne na dare A bet room yaga SAILUBAH tana Sallah Ya xauna harta idar Tabishi da mugun kallo Tace lafiya Yace itace takawoni Dama 'dan uwanki Shegen Yaro ne Tace duk da bansan wa kake nufiba nasan ko kusa bashi da kwatankwacin hali irin naka. Karka qara kiran wani nawa da shege. dan kaine shegen. 'dan iska. Fasiqi. mugu axxalimi. Mara imani me kashe qananun yara batare da tausayawa ba..... Yace na sakeki saki uku Da sauri SAILUBAH Tace Alhamdulillah Nan Tatashi da sauri Tace muje ka fuddani daga wannan qaxamin gidan naka Ya tashi Yace xaki fitta Amma sai gobe da qarfe goma Yana fa'din haka ya fitta SAILUBAH tajah numfashi taxauna takira RAMADAN dan bashi labari Saidai taji wayan akashe bayan yanxu suka gama waya tata6e baki da tura masa message Kana takwanta bayan tatufe ko ina da addu'a Washe gari ko tun qarfe 6:00pm tayi wanka taxauna xaman jiran qarfe gomah Alokacin ne RAMADAN yaga sakwanta Cikin farin ciki ya kirata ta'dauka Yace Auntyna da gaske Tace Wlhi har yana cewa qarfe goma xai barni na tafi. Yace alhamdunillah Yanxu kinga bara nafara shiri sai na musu sallama daga nan sai naxo kawai mu wucce Tace toh ina jiranka Qanina Yace Aha my Aunty Kana ajiye wayan ya kalli Amar Yace yau xantafi fah Da mamaki Yace mai yau Yace yah. Da barin 'dakin Amar ya bishi da kallo Anan falan ya tarar da Momy da kawun nasa Yace dad mum kumin afuwa yau xan koma gida Suka CE lafiya Yace Wlhi qalauπŸ˜€ Auntyna CE xata gida yau shine naga dacewar mutafi tare Sukace Amma bamuji da'di Yace hmm aixan qara dawowa ne Dad Yace kan kadawon ai saika ibi shakaru Mum Tace qilama sai Auransa in munje ma gansa kawai Yayi Murmushi Yace kai mum Tace eh ai gaskiya ne Yace toh bara naje in sharya xuwa 9:30am nakesan tafiya Mum Tace toh Allah ya nuna mana lokacin AmEEn dad Yace Yusra Tace gaskiya banji da'di Yace Karki damu qanwata ina tare dake ai Junior RAMADAN da Isma'il ko qarfe 9:00am dai-dai tayi musu ne qofar gidan Alhaji Aminu junior ya matsar da motar tashi can gaba yanda xaiga fitowar SAILUBAH da xuwan Yayan nasa Yace naxa'ku naqara ganinsa Isma'il Yace ai yanxu haka ma qila yana hanya Yace Wato Isma'il Wlhi kallo 'daya namishi Naji qaunarsa cikin raina Yace sai shima ya ganka na tabbata saiyaji sanka fiye da yanda kaji nasa Yace Allah yasa Haka suka dinga hira har xuwa lokacin da Senior RAMADAN ya iso Ya fitoh daga motar tashi yana kallan agogo Junior RAMADAN ya qura masa ido tabbas ya ha'du sai kace ba tashin Nigeria ba ya iya wanka Isma'il Yace hakane. Kiran Auntyn tasa senior RAMADAN ya hauyi SAILUBAH da take xaune xaman jiran lokaci ta'dauka ashagwa6e Tace kaga goman batayi ba ko Yace xatayi Auntyna fatana kina cikin shiri Tace eh Amma...... Bata qarasa furucin nata bah Alhaji Aminu ya shigo falan ya wulga mata takaddarta Yace asauka lafiya Tatashi da sauri ta'dauka tabi bayansa. Har xuwa wajan megadi Inda Alhaji Aminun ya bashi umarnin ya bu'de mata kofa tafitta. Tana fitowa tayi ido hu'du da qanin nata Aiko taje da gudu ta rungumeshi.......... Yace Auntyna atiti nefah😳 Tadaki qirjinsa ka'dan da dariya Tace ko a inane yanda nake cikin farin cikin nan Wlhi rungumarka Xanyi Tace toh sakeji dan najiki da yawa karna shiga wani hali in 'dauka budurwata CE Ta sake shi da harararsa Tace xamfah jimaka Yace idan kika jimin sai kiyi jinyata Tata6e fuska Tace yunwa nakeji Qanina Yace idan kikamin kuka xaki jefani atashin hankali plsπŸ‘πŸ» 'dan rage ragwa6ar ka'danπŸ‘ŒπŸ» Ya fa'da da ha'de hannunsa biyu alamar roqo da kuma rage mata ido 'daya Tayi Murmushi Tace kaiπŸ‘ˆπŸ» xaka fara kashemin jiki ko Yayi Murmushi da bu'de mata mota yana cewa abinda ya dace ne my Aunty Tashiga tana fa'din xanko hukuntaka Ya tada motan yana cewa ba damuwa ai indai hukuncinki ne nafi kowa buqatarsa Tace kaji dani pls Yace ina ji dake Auntyna. Ga wani dambun nama nan da mum tabani ha'de da cake kamar nasani nafitoh da drink 'daya Tace yauwa Qanina... Yanxu can muka nufah ko Yace eh Kanon dabo timbin giwa ba...... Ta kalleshi da Murmushi tanajin da'di Tace wannan motar fah Yace Kinsan jirgi nabiyo. Yanxu kuma nace Amar yaban motarsa kawai Dad Yace na'dau 'daya daga cikin tashi Tace lallekam motar tayi kyau..... Ya katseta da fa'din karkisa na riqe fah Tace ni bance bah Yace watoh har sake baki kikayi kika qara kyau acanko Tace toh yaxanyi dakai kaifa kabini qardin gwiwar hakan..... Dan Allah Auntyna kinutsu kigayamin komai cikin nutsuwarki. Ba haka kace ba. Ta qarashe da kallansa tana dariya Yabita da kallan jin da'di Yace kin manta da kuka kike cemin dan Allah kaxo ka'daukeni Wlhi kasheni xaiyi dan Allah Ni dai kaxo kawai ka 'daukeni..... Ya qarashe da kwaikwayan muryanta Ta kallesa ka'dan suka sheqe da dariya a lokaci 'daya☝🏻 Dai-dai nan suka wucce

Chapter 9 of 33