Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da kai mishi wani wawan naushi abaki Ya saki wani qara dan atake haquranshi hu'du nagaba suka xube. Bai ankareba ya kuma kai mishi wani naushin ta qafa. Ya sauka a gabansa. Wannan karan qarar daya sake tafurgitasu gabaki 'dayansu Dan yana yinta ya fa'di sumamme Cikin xafin nama wanda ya fara magana ya kawoma junior naushi Baisan duk a ankare yake dasu ba Dan haka bai samu nasarar samunshi bah Amma shi junior yayi nasarar bashi wani naushi aciki tawajan sunkuyawar da yayi wajan kare kansa da yayima naushin daya kawo masa Bai barshi hakaba sanda ya qara bashi a gefan kunnansa Nan ya saki tashi qarar da durqusawa a qasa cikin rikicewa Ganin haka yasa sauran biyun suka afku masa???? Ai nan take fa'da ya kaure. Ji kake maxaje na nishi Abbas yayi shuru kawai yana kallan yanda junior yake basu wahala Yasan idanma yayi fa'dan dayafi haka daidai ne dan baya wasa da xuwa wajan koyan tirenin Sam a skull ( junior kenan ) Ba qaramin doka suka Sha agunsaba Abin daya dinga basu mamaki 'daya ne yanda duk yake kaucema dukkanin dukan da suke kai masa Abbas ne ya janye junior xuwa mota da janta cikin sauri ganin mutane sun fara taruwa Ya kalli buduwar Yace inane unguwarku Tace bacirawa Yace me yashigo dake nan Tace naxo gidan qawata ne Shinefah daga fitowata suka dinga bina wai tsaya Niko na tsaya sanda naga 'dayansu yana Neman ha'da ni da jikinsa shine nayi yunqurin gudu Shine fah suka fara bina Abbas ya ta6e baki Yace Allah ya temakeki Ta maida kallanta ga junior nan taga danne danne mah yake awaya Tace nagode da temakwan da kayimin Allah ya saka Shuru junior yayi mata. Ganin haka yasa Abbas cewa AmEEn Haka suka sauketa akan layinsu Tace mah Abbas dan Allah ban number naka mana Baiyi musu bah ya bata dan yana lura da mayataccen kallan da take bin junior dashi Sanda tajuya junior yabita da kallo kana yajah tsaki Yace kagafah shigar da tayi badole 'yan iska suji sha'awarta bah Abbas dai jan motar tasu yayi yana cewa hmm sai ahankali Ya kuma jan tsaki Yace Mai dani gida pls.... Abbas Yace tajama yawanmu kenan Shuru junior yayi masa ????????wayyo ni Rahamat???????? Wa'yannan yaran da junior yama duka yaran manyan mutane ne Wa'yanda gwamnati takeji dasu Hakan yasa ko cikakken minti biyu basuyi agun bah labarin dukan da junior yayi musu yaje garesu Da tashin hankali suka ibi yaran nasu xuwa asibiti Suna mai fatan Allah ya ha'dasu da junior Su hukuntashi Taqar akasamu Mubarak ya farfa'do Wanda yafara cin mugun duka a hannun junior Yo dole nace mugun Duka tunda bugi biyu yayi masa yasashi sumewa?? Sauran ko ansami kansu cikin sauqi Har suke maidama iyayan nasu yanda abin ya kasance Jin basu da gaskiya yasa 6acin ran iyayannasu sauka ka'dan Mahaifin Mubarak yasa ayima Mubarak 'din Duba na musamman cikin qanqanin lokaci dan tabbatar da lafiyan gabansa Likitoci sun gano mararshice tayi bala'in buguwa Amma bugun bai ta6a gabansa bah Ba mahaifin Mubarak ba hatta Mubarak sanda yayi hamdala ga Allah Amma yasa aransa baxai bar Junior ba Wlhi saiya nemosa duk inda yake yayi mishi fin abinda yayi mishi Wannan kenan Tafiya suke 'dagwas 'dagwas Cikin yanga da Jan aji Kallo 'daya xaka musu kasan sunha'du Kaso mallakar 'daya daga cikinsu SAILUBAH da XEE kenan Suna hanyarsu ta dawowa daga gidansu Maimunan da sukaje kamun nata Wani Mustafah yayi parking motarsa gabansu Yafitoh Yana Murmushi wani ma ya biyo bayansa daga cikin motar Ameer Mustafah ya kalli SAILUBAH Yace 'yan mata jima Ta 6ata rai Yaci gaba da fa'din sunana Mustafah. Wannan abokina ne Ameer Mun ganku munaso Da fatan xaku bamu ha'din kai dan kar muyi rashinku mata masu ajii da hankali SAILUBAH tajah tsaki taci gaba da tafiya Ameer yasha gaban XEE Yace kima Allah da Annabi kitsaya Ki bamu numbarku da gaya mana gidanku dan darajar Allah Tace kaci ko darajarsu Amma kasani duk ba taku anan Mustafah Yace eh munji Haka tabasu numbar wayar dayi musu kwatance kana tacinma SAILUBAH tana cewa shegiya Qawata kina neman miji dan kar aha'daki da wanda bai dace bah Amma kina wani Jan aji Tace aiko nayi sai sun bini Kinga ko gwara naja musu dan Susan darajata Tace da wannan dan wannan Amma...... Bata qarasa ba wani Alhaji ya tsayar da tashi motar agabansu yafitoh yana nuna maitarsa akan SAILUBAH Sam sukaqi kulasa Suna tafiya yana binsu a baya Magiya yake musu akan Su shiga ya rage musu hanya Sam sukaqi Can da sukaga 'dan naci ne sai suka ha'kura suka shiga Gidansu XEE ya fara xuwa ya sauketa kafin yaje ga gidansu SAILUBAH ya sauketa itama Sam qin bashi damar maganarta tayi Yace dan Allah in dawo anjima Cikin gajiyawa da nacinsa Tace saidai gobe da safe Xaiyi magana tayi cikin gidansu Yayi Murmushi kawai ya tada motarsa Akan idan senior RAMADAN da junior aka sauketa Dan suna sama wajan barandar gidan nasu Dan haka kowa da abinda yake kissimawa aransa Dama senior kunsan tirketa zaiyi akan Waye ya sauketa Yayin da junior zuciyarshi ta'dau xafi kamar yaje ya na'da mata dukan tsiya dan nashi ganin bai dace tashiga motar qatan qarden mutum kamar wannan qaxamin bah..... Ya jah tsaki Senior Yace wani abu???? Ya kallesa ka'dan Yace no iz Owkie Senior Yace okay. Bara naje na'danga Auntyna ka'dan Junior yayi Murmushi Yace brother kenan xaka ka tirketa ko Yace kamar kasani...... Junior yabishi da kallo har yabar gidan Ilai kuwa. SAILUBAH na xaune tabaje a falo tana shan ice-cream senior ya cimmata Ya xauña kusa da ita Yace my Aunty Tace na'am 'dan Qanina Yace waye ya saukeki Ta kallesa ka'dan. Ta watsar batare da tace mai Komai bah Yaci gaba da fa'din ki gayamin mana Auntyna Cikin fusata Tace wai RAMADAN me yake damunka ne. Saika dinga sani agaba kamar wani abana kana tirkeni akan samarina. ina ruwanka dasu Yayi mata shuru Taci gaba. Toh saurayina ne Yace yaushe kuka ha'du Ta galla mishi harara Tace yanxu Yace wai meyasa Sam Aunty bakya jama maxa ajii ne Daga kin ha'du da mutum yace yana sanki sai kawai Ki lamunce masa sai kace wacce take neman kai da kanta Ran SAILUBAH ya6aci Tasan ko xaginsa tayi indai akan samareenta ne bayajin komai Dan haka tajah bakinta tamai shuru Shiko ya nace saitayi magana Dan haka ya ta6e baki Yace baiyi bah Sam bai dace dake Ina xaki kaisa da munin nan nasa Tayi dariya Tace ina sanshi haka. Komin muninsa yayi min Shikenan ko Ya harareta ka'dan xaiyi magana wayarta ta'dau qara. Tana jinta har takatse taqi 'dauka Can kiran yaqara shigowa. Ta'dauka da fa'din hello Daga can me kiran nata Yace Mustafa ne Tace ayya ya akayi Yace muna 'kofar gidanku dan Allah karkice baxaki fittoba Tace aiko baxan sami fitowa bah Dan Allah kayi hakuri kaxo gobe Tana fa'din haka ta kashe wayan gabaki 'daya RAMADAN daya gama jin Komai Sai yayi kalar sanyi Yace Aunty Ta kallesa Shi kuma wannan Waye Tace Mustafah A ina kuka ha'du 'Daxu. Tabashi amsa Yace kut😳 Ta kallesa da mamakin yanda yaxaro ido Tace menene Yace ina xaki kai maxa biyu alokaci 'daya SAILUBAH tagyara xama Tace kaga wannan Mustafan kyakkyawa ne kuma da alama me ku'dine gashi nutsattse na lura baxaiyi girman kai ba.... Naji ina sanshi da gaske RAMADAN wannan shine maganar Gaskiya Katayani da addu'a Allah yasa mutumin kirkine na tsaidashi amatsayin mijina. RAMADAN yayi wani shegen Murmushi Yace ai daga jin muryarsa nasan wannan ha'daddene Tace Ashe kaji Yace Sosai mah. Amma baki bashi lokacin daxaixo goben bah Tace inna kunna wayata anjima ya qara kira na gaya masa Yace Yauwa inkin gaya masa saiki gayamin dan nagansa SAILUBAH takallesa Tace aa basai ka gansa bah Yace Allah ba abinda xai fa'ru bayan namiki alqawari ko kin manta ne Tace hmm ban yarda dakai ba kabarni kawai Yace haba Aunty yanxu yadace wanda yakesan Auntyna yaxo naqi xuwa gaidashi Tace hmm makircinka nake jin tsoro RAMADAN Indai akan samarina ne kota ina 6ullomin kakeyi. Gwara kawai kasha xamanka Nagode Ya matso kusa da ita da 'daukar ice-cream 'din nata ya fara bata tana Sha Yace Allah Auntyna wannan karan ba abinda xanyi kiyarda dani. Tace ka'dau alqawari Yace eh Tace toh shikenan Sanda ya gama bata tas Sannan Yace toh shi wannan daya saukeki yaushe xai dawo. Tace nadai CE mai da safe RAMADAN yajah numfashi Yace bara naje nayi Sallah in rokwan miki Allah ko Tace yauwa Qanina Ya shafi gefan fuskarta Yace Aunty fuskarki da'din ta6awa Ta harareshi Yajanye hannunsa yana cigaba da cewa ina sanki Auntyna Tace nima haka 'dan Qanina Ya tashi Yace toh bye bye Tace kaci abinci fah Yace toh da ficcewa Tabishi da kallan jin da'di Shiko yana fittowa yaga Jamila Tace ashe Ku 'yan biyu ne Yace eh Tace toh Kaine RAMADAN 'dina ko wancan👈🏻 tanuna mai junior dake barandar har yanxu Dake Senior baya buqatar magana ayanxu sai Yace mata wancan ne nakin Tace oho nagode Yace aha bye bye da shigewa gidan nasu Ya kalli junior dake danne danne a waya Yace nadawo 'dan Uwa Yace ta gayama Waye shi Yace ai dolanta Yace toh Madallah Senior Ya 'dan jah tsaki ka'dan Yace harsy biyu ne fah...... Allah yasa gobe bamu da lectures kaga na 6ata mata Komai 🙅🏼 Junior yayi Murmushi Yace kai brother nalura akwai ka da kishi Yace hmm ba'dan ka'dan ba Danta shagwa6ani da soyayyarta kagako dole na haukace akan kishinta Junior ya kallesa yajah numfashi Yace wai danma kanada nutsuwa ne shiyasa har yanxu takasa ganoka. Yace kai dai bari. Ina ganin harsai na mallaketa nayi ram da ita xata ankare da soyayyata Junior yayi Murmushi Yace mai xai hana in gaya mata dan tadena cutarmin dakai Yace barta kawai mutafi ahakan xan gyara mata tunaninta Junior yayi dariya Sosai Yace wayaga LEEKITAN ZUCIYAH Senior ya camke da sauri Yace inji AUNTY RAHAMAT tace yaxo ya gyara tunanin NUFAISAT da TAUDAT. A tare suka bushe da dariya😂 Washe gari KHAMIS ne yafitoh daga wanka yasaka kayansa wa'yanda suka kar6esa ya shafah mai 'dinsa me da'din qamshi. Ya feshe jikinsa da turare Kana ya kalli agogo yaga kusan sha'daya 11:00Am haka kawai yakeso yau yaga taurayuwar tasa yanxu...... Cikinsa ne ya mur'damai da sauri ya fitoh falo ya addu'ar Allah yasa yanxu mum 'din tasa ta ajiyemai breakfast 'din nasa Yana duba dining ko yaga Komai da xafinsa yaxauna yaci ya koshi. Sannan ya nufi falan mum 'din...... Kaga Dadyn KHAMIS mukai sadakin yarinyar nan kawai amasa Auran nan da wuri in yaga haka ya ha'kura da Zainab 'din Dady Yace shashaba bah. Ko ina xaikaita oho Momy tayi dariya Tace hmm bar yaran nan Dady kana rainasu sai subaka mamaki Yace ai na hango hakanne shi yasa hankalina ya tashi akansa sai ya iya jamin abin kunya Tace aikuwa Yace toh yanxu xanje gidan Yayan Madi na gaya masa Komai ko xuwa gobene sai akai sadakin ko Cikin murmusawa Momy Tace hakan shi yafi....... Wani qara KHAMIS yasaka ya shiga 'dakin da sauri da durquwa gaban iyayan nasa Yace pls mum Dad kutemakeni Wlhi bana santa nidai Aunty XEE nakeso.... Momy tajah tsaki Tace kafita saga idona fah KHAMIS in rufe Aiko sai yafe da kuka Sosai yana fa'din nidai Wlhi bana Santa Zainab nakeso kuma aka 'daura min Aure da wannan narantse wahala xataci aguna.😰 Momy da Dady suka xubamai ido ganin irin kukan da yake. Sam sai suka kasa cemai Komai Can dai Dady Yace sai dai kabata wahalan dan saimun aura maka ita Kuma Aure tsakaninka da Zainab babu shi Tashi KHAMIS yayi hankalinsa tashe ya bar 'dakin Yayinda jikin Momy yayi. Batasan abinda xaisa ma KHAMIS 'dinta kuka Amma duk da haka itadai batasan Auransa da XEE Yana xuwa 'dakinsa ya fa'da gado Nan ya kira RAMADAN Yace abokina mum da Dad sunsani agaba fah yanxu haka wai gobe xasu kai sadaki gidansu wannan shegiyar yarinyar RAMADAN yayi dariya Yace shine kayi kuka KHAMIS yayi tsaki Yace kaifah 'dan iskane. Ya xa'ayi baxanyi kuka ba Kasan wane irin so nakema Aunty XEE Yace toh Sowie yanxu mu ha'du xuwa qarfe 1 KHAMIS yajah tsaki Yace Allah RAMADAN suka rabani da Aunty XEE akwai tashin hankali. RAMADAN Yace karka damu Dan baxa sukai nan gurinba xasu hakura Yace toh Allah yasa AmEEn RAMADAN Yace suka ajiye waya Junior Yace soyayya tana wahalar daku brother Senior Yace hmm duk acikin mu nafi tausayama KHAMIS tunda bai samu goyan baya agun Dad 'dinsa ba Junior ya kalli agogo Yace ya kamata muje baranta dan ganin ko wannan qatan saurayin Auntyn naka ko yaxo Da sauri Senior yatashi Yace kuma fah. Haka suka haura farandar saman gidan nasu suka kafama gidansu SAILUBAH ido da 'kofar gidan nasu Aiko ko cikakken minti biyu basuyi ba saiga wannan Alhajin daya sauke SAILUBAH jiya yaxo yayi parking motarsa a'kofar gidan nasu Suna kallo yaciro waya yayi kira kafin ya ajiye Aiko kamar yanda suka xata ita ya kira hakanne. Dan sai Ganin SAILUBAH sukayi tafitoh tana bah me gadinsu Amarni ya bu'de get tana da baqo. Nan tajanyo kujerun roba da suke harabar gidan tasaka Su a'inda ya dace kafin takoma cikin falansu Senior yayi Murmushi yace wannan ya samu shiga da yawa Junior ya ta6e baki Yace kar dai ka barta ta xaqe da yawa dan komai xai iya faruwa Senior Yace ban gane bah Junior ya kallesa da kyau Yace idan kabari hirarsu tayi tsayi. Ina tabbatar maka xata baka mummunan labari Senior Yace ko Yace ko shakka babu. Da maida kallansa cikin harabar gidan wanda har SAILUBAH tafitoh cikin kyakkyawar shiga tajera abin Sha agaban Alhajin wanda ya kame akan kujerar rubar kana ta xauna tana fa'din Barka da safiya Alhaji Yace barka SAILUBAH da fatan kintashi lapia Tace lafiya lau Ya akayi kasan sunana. Kuma kasamu number ta Yace nasani ne lokacin da qawarki XEE tace miki toh SAILUBAH Allah ya tashemu lapia. Number mah agunta nasamu dan jiya daga nan gidansu nakoma Tace ayya Yace wato SAILUBAH agurguje nake akan San da nake Miki Ina sanki sosai. na yaba da tarbiyarki da halayanki. dan nasamu bayanai akanki Sosai tsakanin jiya da yau. Sai Naji naqara kwa'dai tuwa daki xama mata agareni. Sunana Alhaji Auwal me katifah Inada mata biyu. Xanso ki xama ta ukunsu idai kin iya da al'amurana to shikenan kin rufe musu qofah ba xuwanta hu'du Ina da yara goma cif..... Da sauri SAILUBAH ta xaro ido😳 Tace tab Yace wani abu Tace aa kawai naji yaran naka ne Yace sunyi ka'dan a wayan shakaruna ko Tace Sosai Yayi dariya Yace inasa ran kibani goma daga gareki SAILUBAH Tace hmm Allah ya kawo masu albarka Yace AmEEn Junior Yace yanxu me kakeji aranka brother agame dasu Senior Yace Wlhi ba abinda banaji Yace toh maixai hana ka turani in bashi tsoro dan nalura ya fara tafiya da ita bakaga har Murmushi take ba. Xuwa anjima xata fara dariya Kaga daga wannan lokacin xuciyarka xata iya samun matsala Senior yayi tsaki yana bin SAILUBAH da muguwar harara batare da tasan yanayi ba....... Hmm sunfa fara 'daukar lokaci fah. Junior ya katseshi da fa'din hakan Senior yayi murmushin yaqe Yace yanxu idan naturaka mai xaka mata Yace abu mai sauqi aguna Amma agunta me xafi Yace toh jeka. Junior yayi murmushin jin da'di ya juya yabar barandar Senior ya bishi da kallan qauna Yana kallo ya shiga gidansu SAILUBAN Alhaji ya gyara xama Yace yanxu kin kar6eni a matsayin wanda xaki tsaida matsayin Mijinki....... Shuru SAILUBAH tamai ganin junior Yana nufusu cikin Murmushi tunaninta senior ne Yace Barka dai Alhaji Yace Yauwa barka SAMAREE. Junior ya kalli SAILUBAH Yace Aunty Waye shi Tace ban sani bah Yayi Murmushi yana wani kallansu qasa qasa Yace Alhaji in gayama wata Gaskiya Yace eh SAMAREE Junior ya nuna SAILUBAH da yatsa Yace Wlhi tana da miji..... Atare SAILUBAH da Alhaji suka waro ido 😳 Alhaji Yace Miji Junior Yace kwarai da gaske Alhaji ya kalli SAILUBAH data sake baki da tana kallan junior wanda ko kallanta bai qara yi bah Yace Amma a binciken danayi banji ancemin tanada miji ba. Junior yayi murmushi Yace Toh a ina xasu gayama Bayan jiyannan aka 'daura Auran Ita kanta sanda kasauke ta jiya Abbanta yake gaya mata Nan take tanuna furgicinta da nuna rashin amince warta. Kuma kawuna ne mijin nata Yanxu haka yana kan hanyar xuwa nan gidan Aure ne Wanda dukkansu basuyi xatonsa bah Maganar gaskiya Alhaji ina santa da kawuna Dan haka dan Allah katashi kabar gidan nan tunkan tsautsayi ya hau kanta mahaifinta ya ganku yayi mata baki ko shi mijin nata ya ganka ya xargi wani abu Kuma nima idan ina ganinka xan iya yin Komai dan qetarar da Auran kawuna daga tanga'din da takesan yayi Alhaji Auwal me katifah yagoge gumi ya tashi yana kallan SAILUBAH Yace kima iyayanki biyayyah hakan xaisa kidace duniya wala hira Yana fa'din hakan yanufi barin gidan SAILUBAH na kallansa harya ficce daga gidan cikin damuwa Kana takalli junior Wanda duk tunaninta senior ne Tace mexance maka Ya 6allah mata harara dayi mata kallan raini kamar yanda yasaba.. Yace oho miki Nan ta tsaida idanta akansa Sosai taga 'dan iskan nata ne. Ashe ba senior bane Tatashi cikin 6acin rai Tace meye ha'dinka dani da xaka..... Yayi saurin katseta da cewa kinga malama dakata Karki wani gayamin magana nima sani akayi Da mummunan 6acin rai Tace Waye yasaka Yace kidinga min magana cikin sanyin rai kar ranki ya6aci da yawa dan temakwanki nayi narabaki da qaxami mummuna Tace ko buri ne shi na buqaci hakan ne Ya xuba drink yana Murmushi ya miqa mata Yace Sha Auntyn brother kiji sanyi aranki hakan xaisa ranki yayi sanyi Ta kar6a ta 'daga sama ta xuba mishi aka. Ya kalleta Yace biyu kenan Wlhi bashi kikaci xan rama alokacin da ranki xaifi haka 6aci Tajah tsaki Tace kai innalillahi Ya xanyi daku ne ni SAILUBAH Wancan ya kasance makira Kai kuma ka kasance 'dan iska Waini sa'arku CE Junior ya kalli sama inda senior yake. Yaga yana nan yana kallansu Hakan yasa ya mayar da abinda xuciyarsa ta kisa masa yayi mata ayanxu Amma yasa aransa Wlhi saiya aikata mata shi da ita. Qila daga wannan ranar tadena kiransa da 'dan iska. Yace xan hukuntaki ne saina baki mamaki wawiya kawai me tunanin jarirai Ya qarashe da nuna mata senior da hannu Cikin raini yaciga da cewa shiya turoni Aiko SAILUBAH Suna ha'da ido da senior yayi saurin ha'de hannunsa biyu 👏🏻 alamar ban haku'ri da furta kalmar Sowie my Aunty Tagane abinda ya fa'dane da yanda ya sarrafah bakin nasa Tayi kwafah da cewa ka gaya masa inasan ganinsa Junior ya fara tafiya yana cewa baxan fa'da b. Idan kin matsu da San ganin nasa Ki kirasa mana. Ko angaya miki ni sakaran namjine da qaramar mace kamarki xata aikeni kuma naje SAILUBAH tayi Murmushi baqin cikin rainin dayayi mata Tasa aranta xatayi maganin rashin kunyarsa yau dan Wlhi saita nemo kyenkyaso tabashi gwale gwale dashi. Sannan tamaida kallanta ga senior Wanda har yanxu kallanta yake Ta shige cikin gidan nasu Senior ya kalli junior Yace me yasata xubama drink aka Junior Yace yayi Murmushi Yace Kaine brother Senior yayi dariya Yace alamu sunnuna tsowan ya tafi kenan Junior Yace inaga har abada bashi ba qara waiwayarta Yace naji da'di Sosai Junior ya 'dan bugi kafa'darsa yana cewa hakan nakeso ka kasance ako yaushe Bara naje na tsaftace Kaina ko Yace ba matsala. Nima bara naje wanke kaina Junior yayi dariya suka gangaro daga barandar tare Shuru SAILUBAH tayi tana naxarin yanda xatayi da senior da junior Tana Cikin tunaninne senior RAMADAN ya shigo Ta xubamai ido Ya 'dan Sosa qeya yana Murmushi qasaqasa Ya xauna kusa da ita Yace Aunty..... Taji sunan har cikin ranta. Amma bata da niyar amsa masa. Lura da hakan da yayine yasashi cewa dan Allah kiyi hakuri Aunty Wlhi baxan qara bah kinji Yafa'da dasan tayi mai magana Amma sam taqi Saiya marairaice mata kamar xaiyi kuka Yace Aunty yunwa nakeji Tace toh ina ruwana Yayi Murmushi dan dama maganar tata yake buqatar ji Yace haba Auntyna Tace kallesa dakyau nan tagano shagwa6ar tasace yau tamotsa. Tace nima yunwar nakeji Ya tashi yaje kitchen 'dinsu anan yaga kayan breakfast 'dinta dankali da kwai ne da farfesun kayan ciki sai ruwan tia yanda yaga gurin a tsaftace shi ya tabbatar masa da cewa da gaske batayi bah Kuma daga dukkan alamu ba ita taha'da bah Dan haka saiya dinga 'daukawa yana direwa agabanta 'daya Bayan 'daya har yagama Kafin ya xauna agabanta ya ha'da tia ya 'dauki dankalin 'daya Yace toh bu'de bakinki in baki Sam batayi musu bah yadinga bata Komai tanaci tana kallansa Sanda taji taqoshi Tace toh kaima kaci mana Yayi Murmushi Yace naci 'daxo Tace saika rantse xan yarda Yace narantse miki Shuru sukayi na'dan wani lokaci. Candai Tace nahakura da samari RAMADAN tunda na fuskanci har abada baxaka barni dasu bah Yace kiyi hakuri Auntyna xan samu miki daidai da xa6inki me kyau me ku'di me aji me meshakaru Kallansa kawai tayi Yaciga da fa'din hmm Auntyna... Tace menene Yace shi Mustafan da kukayi waya dashi jiya xaixo ne anjima Tace xaka koreshi ne Yayi Murmushi damarairai cewa Yace eh. Dan bana sanki da kowa Auntyna Janyo wayarta SAILUBAH tayi Tace tamiqa masa Tace xakaga Mustafah aciki daga nan saika 'dora makircin naka akansa Ya kar6a a sanyaye ha'de da jin tausayinta Haka yanemo number na Mustafah yakira Ringing 'daya biyu ya 'dauka RAMADAN yagyara xama idanshi Cikin nata Yace kana magana da Qanin SAILUBAH ne Yace ayya ai naga numbar tane mah RAMADAN ya ta6e baki Yace kana da sanin ansaka Auranta nan da wata biyu.... Cikin wani hali Mustafah ya furta kalmar ban sani ba Gaskiya Yace toh yanxu kasani kuma Auran xuminci ne xa'a mata dan haka kabarta pls Mustafah ya cije baki da kashe wayan SAILUBAH na kallo yayi blocking number nashin Sannan ya kalleta Yace akwai wani Mamaki Al'ajabi ya cika SAILUBAH tayi shuru kawai tana kallansa Ya matso kusa da ita. Kifa'da man Aunty Sam rasa me xatace mishi tayi Ganin da tayi ya kafeta da ido Yana yana aika mata da furgitaccen kallan nasa shiyasata cewa baga wayan ahannunka ba. Kaduba mana Yayi Murmushi da dora mata wayan kan cinyarta Yace aa basai na duba ba dan na yarda dake. Ya qarashe da dire kallansa a bakinta Tace RAMADAN Yace na'am Tace kashirya kalaman da xaka gayamin wanda xan fa'dama Abbana daxaran wa'adin daya saka min yacika Sosai ya qara matsawa kusa da ita yana Murmushi yasaka hannunsa yana shafa fuskarta Yace Aunty narigada na da'de shirya kalmomin da zan gaya miki kigaya masa Fatana dai kimin alqawarin kinbar kula kowane 'da namiji kenan Tace hmm aitunda Nace ma na hakura kaima kasan nasallami namarin kenan Amma kasani idan lokacin yayi baka bani gamsasun kalmomi ba. Kasani nabarka kenan har abada.... Yayi Murmushi Yace na 'danyi kissing 'dinki ka'dan Auntyna... Tace aa Ya marairaice mata dacewa dan Allah mana Aunty 'dauke idanta tayi daga kallansa danta hango harda iskanci yake ji bayan shagwa6a yau Ya qara matsowa kusa da ita yana cigaba dacewa Aunty.... Ta kallesa Yace inyi Tasan nacin RAMADAN sarai tunda yacire kunya ya gaya mata sai yayi xai barta. Dan haka tanunanai goshinta Tace oya Ya girgixa mata kai yana kallan bakinta Nan take tagane a inda yakesan yayi mata. Dan haka tamai banxa Shima shuru yayi mata yana qarema fuskarta kallo lungu da saqo Kunsan ance kallo gubana Dan SAILUBAH ji tayi duk jikinta yasake ta'dago suka ha'da ido tagalla mai harara Tace kafara damuna da kallo fah Yace toh inyi miki sai natafi. Banxa tamai Shiko yayi saurin kai bakinsa Cikin nata ya sakar mata shock kiss me tafiya da jinin mutum na wasu sakanni Sannan ya janye kansa daga gareta yana cewa bye bye my Aunty Da kallo tabishi harya ficce. Tasauke ajiyar xuciya Tace nashiga uku😰 ni SAILUBAH me yake damuna akan RAMADAN..... Wayarta CE tayi qara tana ganin XEE CE tayi saurin 'dauka Tana cewa Qawata XEE Tace abokin Mustafan nanne wanda muka ha'du dasu jiya shine ya kirani wai qaninki yakira mustafan Yace mishi wai Auranki nanda wata biyu Tace hmmm kadai bari XEE dan agabana RAMADAN ya kirashi yagama yimin qarya bayan junior qaninsa yagama yimin XEE tawaro😳 Tace qiri qiri agabanki Tace Wlhi XEE tamkar ya tofeni da addu'a Nace mai na hakura da samarin tunda na lura har abada baxai barni dasu ba. XEE tayi salati Tace Lalle an gaida ke. Yanxu ya xakiyi da Abban

Chapter 13 of 33