Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Tace Wato barin ba yanxu ba. Dan nasan xaku 'dau shekara goma Sha biyar nan gaba kafin kuyi Auran dan ayanxu bamai hankalin daxai baku mata Ya sheqe da wata dariya abinda ya bata mamaki dan tasan Murmushi ne abokin tafiyarsa Ya kama hannunta tare da kallan kwayar idanta Yace hakane Auntyna Kin san na rabu da Amina jiya Tace ayya yarinya me hankali ta tsaya 6atama kanta lokaci akanka. Me ya ha'daku Ya kwashe Komai ya gaya mata yaqara da cewa Wlhi Auntyna taban tausayi Tace kwarai Ko nima Yace yau sha'daya muke da lectures Tace ni baxanje ba fah Yayi shuru yana kallanta can ya shafi gefan fuskarta Yace nadena matsa miki akan hakan my Aunty Tace kadena ta6amin fuska ni sa'arkace wai Yace abin ya xaman min jiki ne Auntyna ko shima kinajin xirrrr 'din 'din ne Ta gallamai harara Tace ko 'daya nidai...... Ya katseta da cewa nadena shikenan Tace inaso kakaini gidansu XEE yau daga can kakaimu gidan Saudat tana ta kirana bansan ko lafiya bah Yace toh kishirya yanxu na kaiki kafin nagama shirin makaranta nasan kungama sai nakai gidan Aunty Saudat 'din mubarki acan in muntashi daga skull sai mubiyo mu 'daukeki Tace itama XEE baxa taje ba Yata6e baki Yace hmm Allah ya ganar daku sanin mahimmancin ilimi Ta harareshi ya futa daga kitchen 'din Takira wayan XEE tana CE mata gatanan xuwa. XEE Tace ki temaken kuxo da KHAMIS dan Allah dan SOYAYYARKI da manxan Allah Jikin SAILUBAH yayi sanyi Tace toh Nan takira RAMADAN Tace dama suje da KHAMIS Yace toh bara ya gayamai yaxo yasa memu Tace Yauwa Riga da siket tasa na atamfa 'dinkin ya amsheta Sosai tayi kyau ba'dan ka'dan ba RAMADAN ya dinga 'daukarta a hoto Bayan sun fitoh ne Yace Amma fa kayan nan sun matseki Tace toh yake nan Yace danine ke da hijab xansa Tayi dariya Tace tab toh bakai bane ni KHAMIS Yace Aunty LUUVAH kinyi fah Ta tallesa sosai eh da gaske KHAMIS na miji ne kuma kyakkyawa amma ita bataga abin so a jikin qaramin yaro ba Tace Kullun haka kuke cewa KHAMIS Yayi Murmushi Yace ai hakanne Haka RAMADAN yaje ya xakulo wata motarsa da yada'de bai hautaba Suka bar layin nasu Samarin layin suka dasa gulmar su. Wai RAMADAN yasamu SAILUBAH yanda yakeso Bayan sunyi parking a Gidansu XEE suka shiga gidan kansu tsaye A falo sukaga mamah da ita XEE 'din Nan suka gaida maman tayi kitchen KHAMIS Yace Aunty XEE Tace yane Qanina RAMADAN Yace naga kin fa'da tsakanin jiya da yau lafiya Tace hmm ganinan dai RAMADAN so yanasan haukatar dani SAILUBAH tagalla mata harara Yace toh Allah ya kawo Sauqi Amma ciwan so maseefa ne. Tace AmEEn hakane wlhi SAILUBAH ta xungureta akan tadena kafe KHAMIS da ido haka Itama ta harareta abayyane Tace Wlhi baxaki hanani ganin abinda ya hanani bacci ba SAILUBAH Tace toh tashi muje 'daki Tace qaramin minti biyu in sami nutsuwa dan Allah Cikin Baqin ciki SAILUBAH tarabu da ita Tana kallanta tanata Satar kallan KHAMIS Shiko basan tanayi ba Ashe tayi shukar sirri akan idan RAMADAN Dan haka yace aransa bara ya tabbatar da xarginsa Yace Aunty XEE xamu tafi Nan fah tanuna tashin hankalinta akan subari sai anjima SAILUBAH kamar ta kwasheta da mari haka taji Tace xasu skull muba xuwa xamuyi ba akanme zakice suxauna Ta harari SAILUBAH idanta akan na KHAMIS ita kanta tsintar kanta tayi da shagwa6e mai fuska Tace dan Allah kubari sai 'dan anjima Yace Aunty XEE kiyi hakuri Kuba san karatu kuke ba. Muko munaso kibari in aka tashi maxo. Yafa'di hakan cikin kulawa RAMADAN ya kalli XEE Sannan ya maida kallansa ga KHAMIS ya kalli SAILUBAH sai yayi Murmushi tagallamai harara. Haka suka tashi suka tafi badan XEE taso ba RAMADAN na tuqi ya kalli KHAMIS ka'dan Yace ka ankare da Aunty XEE fah Cikin sauri KHAMIS ya kalli RAMADAN Yace ban gane ba pls ganar dani naji gabana ya fa'di RAMADAN ya ta6e baki Yace idan budurwa taga 'daya daga cikinmu tana so. kuma 'dayanmu ya gano hakan ai da wannan kalmar muke gayama juna dan ya ankare da ita ko ka manta ne Sakin wayar hannunshi KHAMIS yayi ya kama kansa da hannu biyu Yace innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un RAMADAN Yace xaku dace Sosai 😆 KHAMIS yayi shuru..... Xuciya cike da tunani da tashin hankali Can Yace Aunty XEE wayyo Allah na ina toh Surajon nata RAMADAN Yace tsuntsun yatashi daga kansa ya dawo kanka pls kashare kawai kahuta abokina xata kula dakai sosai cikin rayuwar Auranku👌🏻 Shuru KHAMIS yayi duk hankalinsa ya tashi yarasa wane tunani xaiyi Yana cikin wannan halin yaga kiran meenat a wayarsa data fa'di qasa RAMADAN Yace saki ranka ka 'dauka pls KHAMIS ya kallesa Yace kasan me Naji Yace aa Yace Wlhi ji nayi inhar na'dau wayannan Aunty na kallona RAMADAN ya sheqe da dariya Yace naga alamar Aunty XEE 'dinnan ta har gitsa maka kwanya. Cikin fusata Yace ba itace ta har gitsamin kwanya ba kaine. Daka ankarar dani ita. Ya fa'da dajan tsaki RAMADAN yayi Murmushi Yace ka kwantar da hankalinka pls dan Allah Yace narasa tunanin da Xanyi RAMADAN Al'amarin ya shigeni Sosai Kuma bansan ta'ina ni da ita xamu fara ba. RAMADAN Yace hmm ka fita sanin ta inda xaku fara ai Tunda bayau nasa ba baku Satan amsa ba ka share kawai abokina. Dan Akwai hanyoyi da dama....... Ni Wlhi ban ta6a ganin Mara sanin abinda ya dace kamarki ba Akan wane dalili xakiso qaramin yaro dan xubar da mutunci Toh ai gashi nan alamu sunnuna RAMADAN ya gano Ki. SAILUBAH tafa'da cikin 6acin rai Cikin wani yanayi XEE Tace ban damu da RAMADAN ya gano Sirrin xuciyata ba. Ni dai nariga da nayi tunanin xuciyata takamu dasan KHAMIS batun yanxu ba Gwara ma da RAMADAN 'din ya ganoni nasan ba'abinda xai hanashi temakona SAILUBAH Tace Amma....... Cikin fusata XEE ta katseta da fa'din duk abinda xaki fa'da min Wlhi baxai shiga xuciyata ba SAILUBAH. Dan narigada na gama fa'dawa tarkwan sonsa Naga alamar bakisan rayuwa ba. Tunda bakisan miye so ba Tashi SAILUBAH tayi tashiga toilet can tafitoh. Tace yanxu xa muje gidan Saudat 'dinne. ko sai anjima. XEE ta harareta takawar da fuskarta Murmushi SAILUBAH tayi kana taje ta dafa kafa'darta. Idan baki xama matar KHAMIS ba ai Al'amuran baxa suyi kyau ba Kuma yanxu ne naga dace warku ke da shi Ina san Kibi Komai ahankali dan in kikayi gaggawa abin baxai xo miki da kyau bah Wlhi na fahimceki duk da gorin da kike yimin akan bansan so ba Xanyi qoqari insan ya yake XEE tayi Murmushi cikin jin da'din furucinta Tace nagode ma Allah dayasa kika fahimceni Wlhi baxan 6oye miki ba. Damuwata ta qasu kashi biyu ne. Da qin fahimtata da kikayi da maseefar son KHAMIS Naji sanyi araina ta 6angaranki. Yanxu yaxa muyi da KHAMIS SAILUBAH tajah numfashi Tace inaso kirage xagewa akan san nashi Tace ni Kaina bansan lokacin da xuciyata ta shagaltu da kallanshi 'daxo ba. Wlhi SAILUBAH bansan ya akayi nakamu da sanshi ba. Ban sani ba. Ina da aji inada kamun kai. Ke kin sani Amma lokaci 'daya na burkice. Tafa'da hawaye na xubu mata. Yanxu ne SAILUBAH taji tausayinta. Tayi shuru tana tunanin ta'ina xasu fara Can dai Tace bama rasa mafuta XEE kwantar da hankalinki Can da yanma sukayi gidan Saudat rijiyar xaki inda suka tarad da ita Cikin damuwa XEE Tace ya naganki cikin damuwa kina amarya Tace ke dai bari. Ashe Auran mijin da yake da mata maseefa ne Atare SAILUBAH da XEE sukace lafiya Tace ba lafiya ba Kunsan tunda aka kawoni gidannan ban qara ganin idan Mijina ba SAILUBAH Tace kamarya Tace Wlhi SAILUBAH Saidai inji muryarshi da shewarshi a 'dakin kishiyar tawa XEE tawaro ido Tace duk soyayyar daya nuna miki SAILUBAH Tace tab kuma sai kika xuba musu ido Tace toh ya xanyi Tana dai xuwa ta kawomin abinci tajuya tatafi........ Kan SAILUBAH tayi magana sai sukaji muryan Megidan nasu shi dasu RAMADAN Da 6arin jiki yake CE musu kushiga tana ciki Su RAMADAN sukayi cikin falan da sallama Gaban XEE ya fa'di dake idanta na qasa batayi gigin kallan KHAMIS ba Da murna Saudat Tace qannena KHAMIS Yace Aunty Saudat ina wuni Tace lafiya RAMADAN ma ya gaidata Yaqara da kallan Auntyn tashi Yace kutashi mutafi ko. Ta hararesa da cewa toh yanxu mukaxo Yace toh xamu tafi kwa tawo Tace haba mana 'dan Qanina dan Allah bamu mintina saimu tafi Shuru ya mata Saudat Tace kunga yayi shashinta ko SAILUBAH Tace eh gashi nan kam Ko shigowa nan baiyi ba Tace Wlhi xuwa anjima xakuji shewarsa shi da ita SAILUBAH Tace hmm inda nice ke duk ubansu xanci wlhi. Dan saina dafasu ta cikin ruwan sanyi Shawara 'daya xan baki itace kifuta daga har karsa kwata kwata Sannan ita kuma ki sake da ita dan bakisan abinda tataka ba. Sai kin shigeta xaki gane Komai. Daga wannan lokacin saiki San tawace hanya xaki 6ullo mata Kina tashi da safe kigama aikinki da wuri sai kije kitchen 'dinta kice kinxo tayata aiki. Duk yanda tayi dake akan kibari karki bari Ki kwantar dakai kimata ladabi da biyayya tanan xaki kasheta Ya kasance Ki lixamci 'dakinta da xinmar kinxo tayata hira. Tanan Xaki gane inda tasa gaba Shi kuma ko yaxo ya sameki a 'dakinta gaisuwace kawai xata shiga tsakaninki dashi kina gaishe shi kibar 'dakin dace musu sai da safe Shi xai shiga cikin damuwar abinda yakeyi bai dace ba kuma me yake sashi yin hakan Yayinda ita kuma xataji da'di aranta ta'dauka cewa ashema ke mijin baya gabanki. Kinga daga nan saita qara sakewa dake. Ke kuma aidama ba xuwan Allah da Annabi kikeba sai kiyi saurin sanin Komai daga nan saiki 6ata mata shiri cikin ruwan sanyi. dan dama kin riga da kinsan Komai saike cafke mijinki tunda kinsan matsalar daga ina take Amma fah kiriqe Allah a lamuranki bamai miki saishi bamai hanaki saishi Tace hmm Nagode sosai Xanyi qoqari in gani Allah yasa mudace (AmEEn) Dako kin temaki kanki dan Wlhi inda nice Sai dai axo rabamu dan ubanki xanci tunda mjin ba naki bane ke ke 'daya. Cewar XEE KHAMIS ya qura mata ido na'dan daqiqu RAMADAN ya kalli Saudat Yace Wlhi Aunty kima mijinki ladabi da biyayya karki biyema Auntyna Kinsan ita 6ata abu take Sam bata iya gyarawa ba XEE ta kallesa Tace ai xata mishi biyayyan SAILUBAH Tatashi tana cewa saita biyemun. kuma ban iya gyaran ba. Kasanni she'daniyace. Wlhi RAMADAN kafita daga idona in rufe. Suma tashi sukayi harda XEE RAMADAN Ya ha'da hannuwansa biyu Yace iyi hakuri toh Ko kulashi batayi ba tafita daga falan. Har waje Saudat tarakosu RAMADAN Yace Aunty XEE da mota biyu muka xo kinga..... Xaki shiga tawace in kaiki gida ko KHAMIS ya kaiki. Da sauri KHAMIS Yace kaji ka da wani kwa'du. Aunty LUUVAH xaka 'dauka tunda layinku 'daya ko nace gidanku 'daya ko ba haka ba Aunty XEE ni saina kaiki gidan. Ya fa'da da kallanta cikin murmusawa SAILUBAH tayi Murmushi tana fa'din aranta Lalle yarannan sun raina musu hankali. Yanxu haka sungama shirya abinsu xasu kawo musu wani alaye. Tace hakan shine daidai. Tafa'da da shigewa motar RAMADAN Ahankali XEE tashiga motar KHAMIS RAMADAN ya 'daga mishi gira. KHAMIS yayi Murmushi ya shige shima natare da Auntys 'din nasu sun ganosu bah Sanda suka fita daga layin RAMADAN ya tada tasu motar. [3:01PM, 17/11/2016] Rahamat Nalele 👯: Suna tafiyar cikin nutsuwa RAMADAN ya kalli SAILUBAH ka'dan Yace Auntyna ki dinga gyara abu pls kidena 6atawa Tayaya xa'ayi Ki gaya mata tashare mijinta. SAILUBAH Tayi mai banxa Shi kuma yanace sai tayi magana ya qara kallanta Haba mana dan Allah Auntyna ki dinga gyara ki dena 6atawa ki dena xiga mutum yanxu kin xigata akan ta yaudari 'Yar uwarta inkece aka xoma ta wannan hanyar...... Da fusata ta katseshi da cewa. Waiwa ya gayama ni xugata nayi shawara na bata wacce ta dace da ita. Tafa'da da 6acin rai Shuru yayi mata dama so yake tayi magana kuma tayi Har suka qaraso gida bai qara magana ba Yana parking tafuta daga motar da xafin rai. Yabita da kallo yayi Murmushi itako tana xuwa 'daki tasaka key dan tasan ba barinta xaiyi ba KHAMIS da XEE ko shuru kakeji acikin motar bamai magana acikinsu Saima XEE ce da lokaci lokaci takan kalli KHAMIS 'din dan xuciyar tata hanata daurema kallansa Da yayi parking a 'kofar gidansu ya kalleta cikin wani yanayi ya sanyaya murya Yace my Aunty mun'iso Duk da XEE tasan sun iso hakan bai hanata kallansa cikin sauri ba. Dan muryar da yayi amfani da ita wajan yi mata maganar ta shigeta ba'dan ka'dan ba. Ya lura da hakan sarai. saiya futa daga motar yaxo ya bu'de mata motar kamar yanda masoyi yake yima masoyiyarsa Tafi toh xata 'dau jakarta sai kawai yayi saurin 'dauka yana cewa da alamun gajiya atare dake my Aunty xanso in kai miki har gida idan kin amince min. Yafa'da da jifanta da wani kallo mesaka Sarki yayima Bawansa ladabi. Da sauri Tace na amince. Ya qura mata ido Tace lafiya kike kallona haka Yayi Murmushi yace Wlhi wani tunani na shiga. Tunda nake dake Aunty XEE ban ta6a jin da'din muryarki irin tayau bah....... Da'di kamar ya kashe XEE Tace sai yau ka ta6aji Ya waro ido Yace kinga xan 'daure Kaina. Ai Kullun muryarki acikin da'din sauraro take Tace toh Nagode Ta shige gaba yana binta abaya yana qare mata kallo har suka iso falan gidan Yace mamah bata nan ne. Tace gashi dai daga dukkan alamu Ta ibo drink taxuba mai a cup itama tasaka ma kanta kana Tace xanso kasha Qanina Ya kar6a da Murmushi Yace banso shaba dan banajin shan Komai saboda damuwa Amma tunda kinaso nasha ba'abin da xai hanani Sha Sanda ya Sha ka'dan Tace meya sakaka cikin damuwa Yace Wlhi Aunty wata nake So❤ saidai ta girmeni ban san ya xanyi bah Da sauri ta furzar da drink 'din da yake bakinta ha'de da sakin cup 'din ya fa'di qasa...... jikake tass ya fashe Tayi saurin xamowa daga kan kujerar da take cikin tashin hankali Tace wa kakeso kuma Da sauri ya matso kusa da ita da ciro hankicif 'dinsa cikin nuna tsoro ya kama hannunta taji wani shock shima yaji Amma ya share ya fara goge mata hannun nata da gefan bakinta Yana cewa am sorry Aunty XEE na tada miki da hankali ko. Karki damu nasan baxata soni bah. Sai dai Wlhi baxan ta6a Auran wata mace ba in ba ita ba. Ya qarashe maganar da sake mata hannun nata Aiko saiga hawaye ya xubo mata cikin kuka Tatashi xata bar falan. Yace baxan ta6a yafema kaina ba idan har kika tafi cikin kukan nan kika barni batare da kin gayamin dalilinki nayin shiba Juyowa tayi ahankali Tace KHAMIS nakamu tasan wani yaro wanda na girme masa gashi kaima kakamu dasan wacce ka girma. Ganin da nayi matsalarmu 'dayace shi yasani rikicewa har nayi wannan kukan KHAMIS yajah numfashi ha'de da lumshe idansa yanajin kukanta har cikin ransa kana ya bu'de idan Yace ki dena bana so bana san jin kukanki yana damun xuciyata pls kitsai dashi karci sakani cikin wani dan Allah Ahankali XEE ta qaraso gabansa Tace shin abinda kafa'da haka yake Yace akan me xan miki qarya. Yafa'da yana mai goge mata hawayan Kawai ki share my Aunty xan kiraki anjima kiban shawa'a akan ya xan 6ulloma da ita budurwar tawa. Sannan kema kinemi shawarata akan wanda kikeso. Tunsa kinga mu SAMAREEN BANAH ne xan iya baki shawara yanda xakiyi dashi kema Kinga kyabani shawarar yanda xanyi da ita Shuru tayi masa Shiko har yakai 'Kofa ya juyo ya dawo dan yana so ya hanata bacci Ya shafi gefan fuskarta Yace kimin alqawarin xaki cire damuwa aranki my Aunty Tace idan na iya cire ko wacce damuwa araina ai baxan iya cire damuwar SO ba Ya lakuce mata hanci Yace insha Allah xaki kasance da wanda kikeso dan shima yana MASEEFAR SONKI Tace ya akayi kasan hakan bayan..... Ya katseta da cewa saboda ko makawone yaji wuccewarki kawai yanasan Allah yayi halittar kyakkyawar mace anan Tayi Murmushi Tace yanxu kai ka tabbatar da hakan Yace Wlhi ayanxu bawanda ya kaini tabbatar da hakan koda ko Ya Surajo ne Ta 'daure fuska xatayi magana Yace bye bye sai munyi waya Ya fitta Tabishi da kallo Sallar magriba SAILUBAH tayi tafa'da tunanin wani Alhaji Aliyu da ya kirata 'daxo wai abikin Saudat ya ganta dan Allah dan annabi tabashi dama yaxo gareta. Yanda yake rokwanta ne yasata bashi ixinin yaxo Tana tunaninsa ne zaizo bayan Isha'i ne ko xaixo gobe bata sani ba To ganin yanxu mah taji wayanta na ringing sai tayi tunanin shine Ashe bashi bane wanine kuma wai Alhaji Aminu Duk dai abikin Saudat ne suka ganta. Yana gaya mata dan Allah taso shi Yana Santa yana garin Abuja da xama. Baida mata. Kuma da maganar Aure xaixo gareta dan Allah tabashi dama yaxo gareta Dan yanxu haka yana Cikin garin kano dan gobe yake san komawa Abuja Toh fah😳 kunsan SAILUBAH da Alhazawan garin abuja ba qaramin so take musu ba dan ku'dinsu nan take taji ya wanta mata arai dan muryarshi nada da'di Amma danta gwada shi sai Tace hmm banajin yau xaka ganni dan nagaji da yawo sai gobe Kamar xai mata kuka yake mata magiyar tayi hakuri ya ganta dan Allah Tace toh kaxo Amma kasani minti biyar kacal xan baka Yace angama ranki ya da'de Bayan tayi sallar isha'i. Kyalliya tayi Sosai RAMADAN Yace Auntyna wannan kwalliya haka. Sam ta manta sunyi fa'da 'daxo taje takama hannunsa ta sakarmai kiss a kumatu Tace yau burina ya fara cika nayi saurayi 'dan abuja anjima xaixo Da tsoro RAMADAN ya waro ido cikin wani yanayi Yace pls Auntyna Karki soshi dan Allah Ta galla mai harara tare da sake hannunsa tana ta6e baki Tace Wlhi saina so shi Kuma na ranshe da Allah kakorar min shi saina maka dukan tsiya Yayi Murmushi Yace wasa nake miki baxan koreshi ba Sam SAILUBAH bata yarda da murmushin da yayi ba. Dan tasan halinsa sarai fa'danta da cika bakinta baya hanashi korar mata su. Dan haka sai Tace suje 'dakin shi xata gaya mishi wani Abu Haka ko sukayi gidansu dayin part 'dinshi Suna shiga 'dakin tacire key 'din 'dakin nashi tafita da gudu ta kulle shi ta baya tana ai nasan maganinka Ta window ta leqo tasheqe mishi da dariya Tace in yaxo ya tafi xan dawo in bu'deka. tana fa'din hakan tabar gun Shuru RAMADAN yayi yana tunani Gaskiya ta shamma ceshi dan yasa aransa ko ganinsa baxatayi ba xai koreshi Ashe ta ankare dashi Yayi kwafah da fa'din ni da ke har abada muna tare da juna Auntyna SAILUBAH na shiga gidansu saiga Alhaji Aminun yaxo Sanda tashafe minti goma Sha biyar Sannan taje gareshi Yace ina wini tauraruwa me haskake taurari Tace lafiya da fatan kaxo lafiya Yace lpy lau Tace toh Madallah Nan ya qara fa'da mata shi ko Waye Wai yana Saida 'dan kunne da tsarqa na xinare ne a Abuja iyayansa 'yan nan kanone sana'ar tasa ce takaisa Abuja Sosai mutumin ya tafi da imanin SAILUBAH dan ganinshi da tayi kyak kyawa ga xaxxafar motar da yaxo da ita Ta'dan dai bashi dama haka Yace Yaji da'di xai turo iyayansa suxo dan bai ta6a SOYAYYA ba bayasan yaudarar mata Kuma komai xa'ayi shi da sauri Tace toh itadai saita xanta da mahaifinta tabashi labarin yanda sukayi Yace duk da haka xai turo iyayansa gobe Daxai tafi saiya bu'de mata wani qaramin akwati Yace ta ibi iya adadin ku'din da takeso Nan cikin SAILUBAH ya mun'da dan ganin yawan ku'din kuma duk 'yan dubu dabu ne a ciki cikin wani yanayi Tace ka barshi Nagode Yace aa fah ina San Ki 'dauka ko ku'din xai sami farin jini aguna kisa mai albarka dan Allah Tace aa dai ka barshi 'Daukar wata leda yayi yasaka mata bandir 'din ku'dinnan guda goma😳 miliyon 'daya kenan a ha'duwar farko. Ya saka mata akan cinyarta Yace nasanki da temako duk xaki iya bayar da wa'yan nan Amma dan Allah ko naira biyar CE kici aciki hakan xaisa inji da'di. Ga wannan cikakken bayanai ne akaina kiba Abbanki nasan mah xaisan mahaifina Shuru SAILUBAH tayi tafuta daga motan da ku'din a hannunta. Tana kallansa yafita da motar tashi yana 'daga mata hannu Bayan 6ace warsa tayi cikin gidansu da gudu tayi 'dakinta ta xaxxage ku'din a gado. tana murna sai watsa ku'din take sama tana ta dariya Can ta tuna da RAMADAN. Aiko da gudu ta'dau kin 'dakin nasa tafitoh xuwa Gidansu ko gyale babu ajikinta sai 'dan kwalinta data rufe kanta dashi xuwa kafa'darta Da sauri take bu'de 'dakin tana bu'dewa takama hannun RAMADAN tana jansa har cikin gidan Sanda sukaxo 'dakinta taja musu burki Tace kalli gadona RAMADAN ya xaro ido cikin tsoro Yace Auntyna wannan ku'dinfah Tayi dariya ta 'dane gadan ta watsa ku'din sama Tace aikin Alhaji Aminu ne Sai kuma tasauko ta ta tsaya agabansa Kaga burina xai cika xan xama matar Babban mutum. xan mallaki ku'da'de masu yawa. xanje gidan marayu inbata tallafi. xanje asibitoci nakai xiyara......... Ya isa da Allah Ki mayar masa da ku'dinsa Cak ko ta tsaya da maganar tata Tace kut...... Na lura ba qaramin Baqin ciki kake yimin bah. Wlhi inxaka mutu baxan mayar da wannan ku'din bah Ban da haka me xaisa na mayar masa da ku'dinsa Tambayarka nake kaban amsa. RAMADAN yaja numfashi Yace saboda ba sanshi kike ba ku'dinsa kike so Yanxu ya dace Ki yaudare shi Tace eh ai rayuwace Qila indan na Auresa naji ina sansa Yayi Murmushi Yace toh Allah ya tabbatar da alkairi Tace AmEEn Amma kadena min baqin ciki Sannan inaso gobe kaxo ka rakani gidan marayu da wajan almajirai Kamar ya tsinka mata mari haka yaji Yace gaskiya baxan 'dauke ki da wannan qaxan taccan ku'din ba, ma'ana baxanje ba Tace toh shi kenan karka kar kaje. Ainima nakusa yin mota xanje ko ina da kaina basai nane mi ka kaini ba jeka nagode....... Da mugun kallo yabita kana Yajuya ya futa xuciyarsa nayi masa xafi SAILUBAH ta bishi da kallan harara. Kana ta ha'de ku'da'danta tanemi guri ta adana Sannan tanemi kiran XEE. RAMADAN juyi ya dinga yi akan makeken gadansa duk ya rasa nutsuwarsa Can yatashi yana safah da marwah yana tunanin ta inda xai biyoma Auntyn tasa Yasan tashiga da yawa. Da gaske wannan karan saiya bita ahankali Yana cikin tunaninne FAWAS ya shigo 'dakin nasa shi da KHAMIS FAWAS Yace lafiya naganka Cikin damuwa Yace Auntyna ce ta jefani cikin damuwar kun santa da ku'di yanxu tayi wani tsinanne wai daga Abuja. Ni damuwata yanxu na sanshi. FAWAS Yace tokai mexai dameka Yace kun kasa ganewa har yanxu KHAMIS yayi Murmushi Yace hmm Aunty LUUVAH kenan Ni dai tana burgeni Sosai. Tana burin ta mallaki ku'di masu yawan gaske. Kuma ta temakama marasa shi Wannan burin nata yaba tsumani ba'dan ka'dan ba FAWAS Yace toh wai me xai dameka akan hakan Bayan kafi kowa sanin wannan burinta ne RAMADAN Yace dole Komai ya dameni akanta. xaku gane ne nan gaba. Ya dafe kansa na mintunoni Can ya saki murmushin mugunta dan tuno da wani abu wanda in yayi mata xai bala'in 6ata mata rai har Tace ta hakura da Alhaji Aminun ya kalli KHAMIS ya 'dora da fa'din ya Aunty XEE... KHAMIS yayi dariya Yace tana nan qalau na burkitata kamar yanda tayi nasarar burkitanin daga ankarewa da ita. Wlhi RAMADAN banajin ko wacce mace arai ayanxu kamar Aunty XEEE Ya abin xai kasance idan kunya ta hanata furtamin Kalmar SO Ha'da ido FAWAS da RAMADAN sukayi atare kuma suka saki Murmushi Shege yaga cikakkiyar mace Ai dole kaso ta. Dan ta ha'du tako ta'ina Kagaya mata pls karki dinga hargitsata. dan nasan ka'dan da aikinka ka tarwatsa mata kwanya....... Cewar FAWAS KHAMIS yayi dariya Yace aina rigada na tarwatsa mata kwanyar dan Wlhi yau nayi alqawarin saina hanata bacci Yanxu haka nasan tana cikin damuwa dan na jefata cikinta RAMADAN Yace ya isa haka dan Allah Pls karka wahalar da ita da yawa Dan bana san tashiga damuwar da har tasata jefamin Auntyna aciki. KHAMIS ya tashi yana dariya Yace Aunty LUUVAH ka sani kawai. Itace damuwarka karka damu baxan bari she'daniyar xuciyata

Chapter 4 of 33