Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Yace kika mutu ainima binki Xanyi Taqara harararsa da cewa bawani nan Kama huta. saikaci gaba daga inda ka tsaya Yace Wlhi my Luv na rasaki binki xanyi ina miki wani so Wanda yafi qarfin akirashi da MASEEFAR SOO Tace toh naji gayamin Yace mefah Tace gayamin 'yan matanka nawa kuma bayan ni wacece kakeji aranka Qura mata ido yayi kafin yayi Murmushi dan ya hango kishin natane yau yatashi. Abin takaicin wai dan tagirmeshi shine take neman mishi wayo Ya qarayin Murmushi aqaro nabiyu Yace ni bani da 'yan mata yanxu dan tunda nasameki kika shafe Komai na jikin wata bana ganin kyansu sai naki bana jinsu sai jinki bana ganinsu sai ganinki Tace hmmm toh ita wacce nagunku fah Yace pls my Luv ki barni haka dan Allah mana Tunda kika ganmu naji na tsaneta Sam. Kuma nagaya mata bani ba ita Xatayi magana yayi saurin rufe bakinta da hannunshi Yace sanyi nakeji my Luv dama mun xama masoyan gaskiyan inji 'dumin ko nasamu nutsuwa. Yafa'da da janye hannunsa yana jifanta da wani irin kallo Aiko nan take jikinta ya mutu dan kallan daya aika mata dashi Tace hmmm Yasan dama hmm 'din xatace dan haka ya tashi yana cewa yau kin hanani xuwa skull. Tace ni. Yace eh mana. Dan ko naje ba abinda xan 'dauka a kwakwal wata Tayi Murmushi Tace gobe saimuje tare Yace tarayo miki kenan Tace eh Yace hmm in xaki tsaya kiyi karatu kitsaya kiyi inba haka ba Wlhi na mallakeki ba qaramin mamaki xan baki ba Tace ko Yace Sa wasa kiganshi gabanki Tace Allah ya kaimu lokacin Yace AmEEn my Luv Ni xan tafi sai Allah ya kaimu anjima ko Auntyna Tace hmm saura ka fara xuwa gunta...... Yayi Murmushi da ficcewa daga falan yana cewa nidai bance ba kuma ba ruwana..... 'Dankin RAMADAN ya koma Yana shiga yaga RAMADAN junior da senior da FAWAS Junior yana yana canjah Kaya dan har Dady ya shigomai da kayansa Ganin yanda ya qame shi yasa RAMADAN senior ya dafa kafa'dar shi Yace 'dan Uwa nane mu 'yan biyu ne. KHAMIS Yace bar fa'damin dan Allah Tunanina nayi gamo ne😳 RAMADAN yayi dariya yana qara mishi haske akan lamarin Nan hankalin KHAMIS ya kwanta yace Koda Naji. Nayi farin cikin kasan cewarshi garemu dafatan mun xama 'yan uwa Junior yayi Murmushi Yace Sosai mah Yace amma kamanninku yayi yawa. Bafah Wanda xai gareku Junior qara kallansa yayi Yace xaku dinga ganemu mana. FAWAS Yace ta ina Komai naku 'daya Yaqara yin murmushi yayi Yace nan gaba ka'dan xakuce na gaya muku KHAMIS Yace toh kai me sunanka Yace RAMADAN..... Suka kallesa dukkansu har senior... FAWAS Yace RAMADAN kuma Har sunan naku 'dayane Yace eh kai Sai dai shi Senior ne nikuma Junior KHAMIS Yace Yauwa gwara daka babbance mana FAWAS ya tashi yana fa'din bara inje office 'din Dady na dawo KHAMIS Yace nima Momy ta ha'dani da wani aiki wai inje in gaida wata yarinyar qawarta Ameera batajin da'di an sallamora daga asibiti. koni ina ruwana dasai naje gaisheta oho Senior yayi Murmushi Yace kaje dai kaga matar da sukesan baka KHAMIS yawaro ido 😳 cikin tsoro Yace what FAWAS ya shege da dariya Yace wai kai nan baka gane manufar xuwan naka ba. Yace Wlhi ban gano ba😳 Junior yayi Murmushi Yace ya toh xakayi da Aunty XEE Duk suka kalleshi atare sukace kasanta ne Yace na santa mana sanadinku Suka cika da mamaki dan basusan yasan rahotan kowa a cikinsu ba KHAMIS Yace na rantse da Allah akarabani da Aunty XEE mutuwa Xanyi Bansan yaushe Santa yayimin mugun kamu bah Senior Yace kata addu'a ba abinda xai faru FAWAS Yace hmm Allah yasa KHAMIS Yace kai barama naje yanxu dan tabbatar da maganarku Atare FAWAS da KHAMIS suka fitta Senior RAMADAN ya xauna daf da 'dan uwan nasa Yace xanso kaban labarinka Junior yayi Murmushi Yace ahannun Dady Jibiril nataso Saidai duk Wasu abubuwana a waje nake yinsu Senior Yace kana nufin Kaine 'dan uwan da momyna take gayamin yana wajan Dady Jibiril Junior ya gya'da mishi kai Yace watoh 'dan Uwa akwai cakwakiya acikin tarihin rayuwarsu Xakaji Komai Amma lefin nan bara naci abinci muyi Sallah idan na hutta na baka labari ko da dare ne Senior Yace Owkie Suna xaune kan dining Suna cin abinci Amma banda Senior RAMADAN Dan danne dannansa kawai yakeyi awaya Junior ya kalli kwayar idan Dady Yace ba da'dewa Xanyi ba. Kwata kwata sati uku ne ya ragemin in koma skull Senior RAMADAN Yace nayi tunanin kadawo garenine gabaki 'daya Yace eh haka ne Dan nabar hannun Dady Jibiril kenan ko Baku Dady ya ajiye cokalin hannunsa Yace da gaske kakeyi Yace gaskiyar kenan dad Tunda nagane akwai wani abu aqasa Wanda kuka da'de da 6oyewa shikenan fah naji banisan qara xama kusa dashi Cikin sanyi Dady ya kalli Momy alamar ya shiga damuwa Daidai nan 'din junior ya tashi yana yana goge baki da tishu ya ficce daga falan xuwa part 'din senior RAMADAN Momy Tace akwai matsala Dady Yace damuwata kaddai ya gano Komai Senior RAMADAN Yace Dad kaban haske bai kamata ka6oyemin abubuwa haka ba Ace inada 'dan Uwa Amma sai yanxu naganshi. Me yake faruwa ne Dady yajah numfashi Yace kayi hakuri my son banyi maka hakan daniya bah Tashi RAMADAN yayi ya bar falan xuwa ga Qanin nasa Shida da Momy suka bishi da kallo Momy Tace lokaci yayi daxaku fayyace musu Komai dansu fuskanci rayuwa Dady ya kalli Momy Yace Wlhi yanda nake san yarannan ko 'ya'yana bana jinsu kamarsu Momy tayi Murmushi Sam mijin nata bai iya 6oye gaskiyarsa ba Shiyasa take qara sanshi Idan abu ya kasance gaskiyar shine baya damuwa da ranta ya sosu ko karya sosu fa'da mata kawai xaiyi Tace nima ina matuqar sansu Allah ya dubesu ya rayasu Yace AmEEn Senior Yace pls 'dan uwana gaya min Komai Junior ya tashi ya bashi diarys 'dinnan biyu Yace ka karanta nidai hutu nake nema brother Da sauri senior ya kar6a yana cewa tnx..... Sosai junior yake bacci hankali kwance yayinda senior yagama karance diarys 'din nan tsaf Hawaye ne kawai yake sauka afuskarshi Na Farko abinda ya sashi kuka na mutuwar iyayan nasu dan yasan da mahaifinsu yana nan dole ya bayyana garesu Toh ya akayi ya mutu kasheshi akayi ko haka kawai ya mutu Tabbas xaiso yaji wannan Na biyu kuma yanda Dadyn shi Alhaji Naziru yanunamai qauna fiye da 'ya'yansa Baya ha'da soyayyar da yake masa da kowa agidan Tabbas yanuna mishi qauna ta qarshe Yana nuna mishi SOYAYYAR DA BATA DA QARSHE 😀 Ya maida kallansa ga junior da yake baccinsa hankali kwance. Sai yaji wata masifaffiyar qaunarsa takamashi Nan yaci gaba da kukan nasa Sosai. Awannan yanayin ne junior ya tashi ya gansa Ya kalli agogo yaga kusan shidda da rabi Yace Ya Allah banyi sallar La'asar ba Senior yaqi kulashi Junior yayi Murmushi ya matso kusa dashi Yace yane brother Kuka haka Kamar wanda xai rasa dukkanin farin cikinsa Kar damu in haka ne kana dani Ni kadai na isheka Hmmm nasan xaka fini shiga Baqin ciki idan ka karanta Soboda koda wasa Dady bai ta6a nuna maka cewa bashine ya haifeka ba. Saidai nafika shiga baqin ciki ayanxu dan nagano na rayune ahannun Wanda ya kashemin mahaifina Senior ya kallesa da sauri Yace katabbatar Dady Jibiril ne ya kashe mahaifinmu Yace ko shakka babu dan bashi da imani Na sanshi fiye da tunanin me tunani Allah ya jarrabeshi da sona ne danya nuna mishi qarshansa Karka damu brother xansan yanda xanyi dashi Senior yayi saurin cewa aa banasan kayi yunqurin yin Komai idan na isa dakai Junior yayi murmushi Yace duk abinda kasani Xanyi haka dukkan abinda ka hanani xanqi yinshi Yace Yauwa 'dan uwana naji da'din wannan furucin naka Yace kai ka'dai nake dashi in banyima ladabi ba. baxan ta6a yafema kaina ba. RAMADAN ya rungumeshi Yace kasoni pls inajin maseefar sanka araina Junior yayi Murmushi hawaye yaxubo mishi Yace nasoka tun kan ka ganni..... (Wato shidai "dan uwa da'dine dashi) bayan sunsami nutsuwa Toilet senior yashiga yana cewa ai nima banyi sallar ba. Dan haka saina rigaka Alwala Junior yayi Murmushi Yace idan kada'de Saidai kasameni akan sallaya dan swn yanxu in rigaka...... Bai qarasa furucin nasa ba tashigo kamar an jefuta SAILUBAH kenan Junior yayi mata kallo 'daya xuciyarsa na bugawa fat fat fat Ai bai ankareba yajita kusa dashi. Qamshinta ya bigeshi ya lumshe ido cikin basarwa Tabishi da kallan shagwa6a ta kama hannunsa Tace Abban nan nawa kamar mai aljanu kaga yacanja tsarin nasa yanxu wai wata biyu yaban nafito da Wanda nake so. Tunda wancan bai 'doramin idda ba. Nufinshi yajanye wata takwas 'din da Yace kenan Wai inda nafitoh da Wanda nakeso hankalinshi xaifi kwanciya Koda baxa'ayi bikin nan kusa bah Pls ka temaken Qanina ya xanyi. Taqarashe kamar xatayi kuka Yanda take mishi maganar ba qaramin hargitsa mai kwanya takeyi ba Dan haka ya xare hannunshi daga nata ya tashi Tace kaji dani mana Cikin rashin kunya da raini ya watsa mata harara Yace Karki qara ta6amin hannu malama Kantayi magana senior ya fitoh daga toilet. Yace Auntyna😁 Tawaro ido 😳 Tace me nake gani RAMADAN Yace 'dan uwana ne. Mu 'yan biyu ne. 'Daxu yaxo Tace kut😳 Amma shine Komai naku 'daya Xama yayi kusa da ita lokacin junior ya shige toilet Yace kema kin tabbatar ba abinda ya rabamu ko. Tace eh Amma wannan bashi da kunya Yace me yayi miki Tace sanda nagama mai xuba yawani yimin rashin kunya RAMADAN yayi Murmushi Yace toh kiyi hakuri Tace kai dashi Waye Babba Yace nine Tace toh kaja mishi kunne ni Auntynka CE Yace toh my Aunty Tace naga xakayi Sallah bara inje. In ka idar kanemeni ko awaya ne Yace angama my Auty Har xata tashi sai kuma taxauna Tace toh meyasa baka ta6a gayamin cewa Ku 'yan biyu bane Yace kiyi hakuri dama inasan yimiki baxata ne Kamar yau da kika gansa kika xata nine Ta 6ata rai Tace karka sake Yace shi ka'daine nawa kinga sakewa bada niba... Tace Yauwa baka gayama momy tare muka dawo bane Yace eh Tace kamar nasani nafara xuwa gareta anan naga Dady mah Ta kallan da mamaki da San jin ya taganni Shine nake gaya mata Komai Dady Yace aiya mantane bai gaya mata ba Amma sunyi xancan da Abbana da safe. Yayi min Nasiha Sosai RAMADAN Yayi Murmushi Cikin wani yanayi ya qare mata kallo Yace kinyi kyau Auntyna Takalli kanta. Wata rigace dogowa tasa sai qaramin gyane data yane kanta Tace banyi fah wankan yamma bafah. Yace aiko bakiyi wanka ba kyau kike Xatayi magana junior ya fitto bai kallesu ba ya shinfi'da sallaya zai hauyin Sallah senior Tace am 'dan uwa gafah Auntyna ta Kaina inaji da ita over kaso pls dan zanji da'din hakan.... Cikin maseefa SAILUBAH Tace karma yasoni mana Junior ya kalleta araini Yace gaskiya brother na rainata. Ma'ana baxan sota ba Dan banga abin San bah Cikin sauri senior RAMADAN Yace bafah wancan san ba. Junior yayi Murmushi Yace ai in wancanne tayimin yarinya Ina nufin baxan sota bane kwata kwata dan bakai nabata kowane irin matsayi na so ba...... Ya qarashe da tada abbara cikin halin ko in kula. Kut😳 SAILUBAH Tace ta kalli senior. Yayi saurin marairaice murya cikin kunya da nadamar gabatar da ita gareshi Yace am sorry my Aunty karkiji Komai aranki dan furucinsa Wlhi qarya yakeyi ke abar San kowa ne Tace Amma wannan akwai 'dan iska mara mutunci shege Nixai kalla Yace baiga abin so ba Ni sa'arsace Shuru senior ya mata dan yasan ta shaqa kuma baisan me xai kuma CE mata bah Itama shurun tayi tana jiran ya idar ta tsefeshi tamkar senior yasan me take saqawa saiya kama hannuta Yace kanya idar xo in nuna miki wani abu da Dady ya siyamin Batayi musu ba tabishi har harabar gidan Yace am sorry my aunty Ki yafe mishi banasan tashin hankalinki Xan mishi magana Sosai akanki Yasan girmanki daatsayinki Tace dama wayo kamin dankar in tsefeshi Yace aa ni na'isa in miki wayo. Fatana dai Kiyi hakuri dan Allah Tace toh naji Wlhi saina mishi rashin mutunci baxan hakura ba Dafe kai RAMADAN yayi. Yayi shuru dan ya hango rashin hakurin nata axahiri Ita ko ganin shurun da yayi yasata cemai Meya samu idanka kamar kayi kuka. Tun 'daxo nakesan tambatarka. Tafa'da dasan kawar da damuwar da tagani a fuskarsa Yace kuka nayi Auntyna Tace waya samin kai Yace nayine dan ganin 'dan uwannan nawa SAILUBAH tata6e baki da gallamai harara Tace hmm toh karka sake dan ba irinsu akeyima kuka ba...... Kai bakaga idanshi tsaf na marasa kunya bane da tarbi....... Da sauri senior ya tufe mata baki Yace kibar shi haka mana Aunty baxai qara yimiki rashin kunya ba promise Tace hmm imma xaiyi ina daidai dashi Nan dai RAMADAN ya rakata gida yana lallashinta ya dawo Sanda yayi Sallah ya fuskanci junior Yace 'dan Uwa ka.... Katseshi junior yayi Yace baxan qara yimata Komai ba... Senior yayi Murmushi Yace Yauwa 'dan Uwa ka lura pls Yace karka damu...... Wannan dare Sam RAMADAN bai bar qanin nasa ba yana tare dashi yana nuna mishi tsantsar qauna FAWAS ko sha'awa suka dinga bashi KHAMIS ko damuwa da tashin hankaline yayi mishi yawa dan ya tabbatar da xancan senior RAMADAN akan Ameeran da Momyn shi Tace yaje dubata Shegiyar yarinya qiri qiri tafitoh tace tana sanshi Yanxu haka bayan Isha'ine xaune yake a 'dakinsa sai saqa yake yana kwancewa Shidai Aunty XEE ce aransa ba wata mace Sam agabansa........ Momy da Dadyn shi suka shigo 'dakin Aiko ya 'daure fuska Dady Yace me yake damunka Yace haba Dad meyasa mum xatayi min haka Ni fah nayi qarami a Aure Yace ko Yace Wlhi Yace toh saurareni dakyau kaji Wlhi Aure xan maka da ita Ameeran Ko kana tunanin bansan me kakeyi bane na futan dare Kuna yawan xuwa club Kullun dare Me kukeyi acan iye Hakanne yasa nagane Aure kakeso dan haka acikin satinnan xancan sadakinka gidansu Ameeran Ko kanaso ko baka so mutumin banxa kawai......... Wani ihu KHAMIS ya kwalla🙆🏼 ha'de da wani tsalle ya dire agaban Dadyn nashi Yace Dady kamin rai Wlhi bana santa. Ina skull Dady pls karkamin haka Dadyn yayi murmushi irin nasu na manya Yace Wlhi baxaka jawomin abin kunya ba saina maka Aure tunda kanuna shi kakeso Yace wayyo Dady ina da wacce nakeso Wlhi. Momy Tace wacece ita Da sauri Yace Aunty XEE Momy da Dady suka waro ido😳 cikin mamaki har Suna ha'da baki wanjan cewa Zainab.... Dan sunsanta Sosai. Ya 'daga musu kai cikin tsoro Yace Wlhi ita kawai nakeso kuka rabani da ita mutuwa Xanyi Gauuuuu Momy ta falleshi da mari..... Atarihin KHAMIS tunda yataso da wayansa bai ta6a ginin ranar da iyayan nasa suka dakesa ba Amma yau sanadin masoyiyarsa yasha mari agun momynsa Ya kalli Dadyn nashi cikin sanyin yanayi. Dadyn ya 6alla mishi harara Yace kamin magana saina qara maka wani Marin Shashashan yaro kawai Ina xaka kaita yarinyar data girme maka da shekaru kusan biyar ko shidda Toh kasani ko xaka mutu baxan Aura maka ita ba Yana fa'din hakan ya ficce daga 'dakin cikin 6acin rai Momy Tace Wlhi idan ina raye baxaka ta6a Auranta ba. Sakarai kawai Ina xaka kaita yaxakayi da ita kana 'dan qaraminka.... Aikan tafuta KHAMIS yasa mata kuka fa'di yake mum ina Santa Wlhi kuka rabani da ita mutuwa Xanyi Tace toh ka mutun mana.... Taficce Kuka Sosai KHAMIS yasa Toh yatake ne XEE 👯 matsala kenan👯 Haka yaci kukansa ya share hawayansa Kuma kamar ance mai karya kira 'daya daga cikin munanan nasa Sam bai kira kowa acikinsu bah Toh ga FAWAS ma hakan take Dan Ashe Dadyn KHAMIS ne yasami Dadyn FAWAS Dana RAMADAN suka tattauna akan matsalar yaran Toh FAWAS bayan ya rabu da RAMADAN senior da junior gida ya nufu A falo yaga iyayan nasa Momyn shi Tace xonan FAWAS yaje cikin ladabi Dady ya bashi wasu pix hotuna Yace kallesu dukka Cikin sanyin yanayi FAWAS yafara duba hotunan Kyawawan mata ne agani na fa'da Su goma cif FAWAS Yace Dady nagama gani Yace toh xa6i 'daya acikinsu Da sauri FAWAS ya kalleshi dan ya gane abinda yake shirin San faruwa Bakinsa na rawa Yace Dady ba wacce xan iya xa6a aciki Momyn shi ta harareshi cikin 6acin rai tace kafita daga idona tunkan raina ya6aci dakai kaxa6i 'daya acikinsu Yace toh momy miye ma'anar hakan Dadyn nashi ya fusata cikin tsawa yace Aure xan maka tunda kaxama 'dan iska ashe kullun yawan xuwa club kukeyi So kake kajawomin abin kunya agari ko Toh baka isa ba Wlhi Maxa xa6i 'daya acikinsu ko ranka ya 6aci Turo baki FAWAS yayi Yace ina fah da wacce nakeso fah Dady..... Gaskiya acikinsu ba wacce tamin. Ni HAMEEDA kawai nakeso Cikin sanyi Dadyn nasa Yace wacece HAMEEDA Yace a qauyan takai take ina Santa Sosai...... Cikin fusata momyn nashi Tace HAMEEDA a qauyan takai Yace eh Tace kana da hankali kuwa😳 FAWAS ya lalleta cikin sanyi Yace Wlhi ita nakeso kuma tama girmeni da kusan shekara hu'du Tana sona Sosai kamar yanda nake Santa Dan Allah Momy Dady karkuyi yunqurin rabani da ita Gauuuu Momy ta falleshi da mari Tace Lalle Dadynka ya shagwa6aka da yawa Toh bari kaji kayi gaggawan cireta aranka Dan Wlhi ba wanda xaije nema maka Aure a qauye Shashasha mara hankaki karasa wacce xaka nema sai 'yar qauye wacce ta girmemaka mah. Mara hankalin Yaro kawai Hawaye ne ya xuboma FAWAS Ya kalli Dadyn shi yaje ya kwantar da kansa akan cinyarsa cikin muryar rauni Yace dan Allah Dady karka bari momy ta rabani da ita Wlhi na rasata mutuwa Xanyi Dadyn da mamakin 'dan nasa ya hanashi motsi shafah kansa yayi Yace karabu da ita my son Yace ina Santa Dady Shuru Dadyn yayi Can Yace toh tashi kaje kayi wanka kaci abinci ka kwanta Ya 'dago da kansa Yace toh Dady baxaka rabani da itaba ko Yace sai nayi tunani. Yafa'da da shafa fuskarsa cikin kulawa....... Wani dogwan tsaki Momy tajah Tace Wlhi baxaka Aureta ba. FAWAS ya marairaice fuska Yace Dady kajita ko Dadyn yayi Murmushi Yace jekayi abinda nace ko Tashi FAWAS yayi yana bin Momy da kallo tana banka mishi harara Ahaka yayi part 'dinshi Daqar yayi wankan dan yasan Momyn tashi sarai bata fa'din abinda baya yuhuwa Gwara dadynshi yana da 'dan sanyi Abincinma daqar yaci Sanda yakira HAMEEDAN tagama mai shirmen soyayyarta yana jin da'di Sannan ya sami nutsuwarshi ka'dan😟 Senior RAMADAN ko sai kusan sha'daya yasami kiran Auntyn tasa Lokacin junior yana waya da wata wai Shakira yanayin maganar da ita tamkar yana mata ra'da dan sanyin murya Senior yayi Murmushi Bayan ya fuskanci qanin nasa yayi nisa a tafiya da kalamai Ya ta6e baki da fa'din nima bari naji da Auntyna aransa Lokacin SAILUBAH na chat awata sabuwar wayarta da XEE tasiyo mata 'daxu Tace yane Qanina Yace qalau my Aunty Da fatan ba abinda yake damunki kamar yanda nakeji araina yanxu Tace nifa Komai damuna yakeyi Ai kasani Yace toh gayamin menene Tace ya rage yawan watannin daya ban Kana tunanin xan iya rasa damuwa ne atare dani RAMADAN ya waro ido Yace da gaske Aunty ya rage😳 Tace da gaske mana Yace wayyo toh yanxu ya xamuyi Tace shine abinda ya kawoni 'daxu kenan mu tattauna Yace toh mubarma gobe ko Tace aidole Yace toh kihuta my Aunty Tace hmm kaci abinci Yace naci da 'dan uwana Tajah tsaki Tace kace da 'dan iskannan mara kunya Shuru RAMADAN yayi Tace kayi shuru Yace sai da safe Auntyna kiyi bacci me da'di da mafarkai.... Sai kuma yayi shuru Tace da mafarkai masu da'di ko Yace yes my Aunty bye bye. Ya kashe wayan SAILUBAH tajah numfashi fuskarta cike da annuri ta gyara kwanciya da cigaba da chat 'dinta RAMADAN mah gyara kwanciyarsa yayi. Yana sauraran junior Wanda har lokacin bai gama wayan nasa bah Can yagama ya kalli senior Yace brother dawa kayi waya Yace Auntyna SAILUBAH Yace naga alama kam Senior Yace alamar me kagani Yace nalura da farin cikin da nagani a fuskarka ne Yace Hakkane 'dan Uwa Idan ina tare da ita ina samun kaina Cikin nutsuwata Idan kuma ina waya da ita ina tsintar kaina cikin farin ciki Junior ya ta6e baki Yace kana Santa kenan Yace Sosai mah. Yace toh Allah yabarku tare😊 AmEEn Senior Yace kana ya'dora da fa'din wacece shakiran da kaketa wani amsa wayarta kamar bakaso Junior yayi Murmushi Yace kai brother har kariqe sunanta daga furtawa so 'daya Senior yayi Murmushi Yace sunan nata ne so sweet Junior Yace tnx Sunanta kenan Ban ta6a Santa bah Saidai ina more rayuwa da ita Sosai Dan tasan darajata Karuwace ada Amma ayanxu tawace ni 'daya Tana xama a Dubai balarabiyace ta gaske gata 'yar babba haka Dan ayanxu xata kai 26 years Senior yajah numfashi Yace idan na fahimceka kana harkar xinah kenan...... Junior ya katseshi da fa'din no no no no brother. ba Hakka bane .banayi da kowa sai da ita Kuma ban 'dauki hakan atsayin xina bah Tunda da ita kawai nake harka.... Senior ya katseshi da cewa xinah kake aikatawa 'dan uwana Dan duk mutumin da xaiyi harka da mace irin yanta ma'aurata sukeyi. Batare daya mallake ba. Ma'ana ya Aureta ba. Toh ba shakka xina yake aikatawa daga shi har ita Barama kaji 'dan akwai xinar ido ta kallo Akwai ta hanci ta wajan shaqar qamshi Akwai ta baki tawajan kalamai Xinar ido itace wacce........ junior yayi saurin katseshi da cewa karka damu brother Nasan xakamin wa'axinnan ne dan indena toh nadena shikenan😊 Senior yayi Murmushi Yace kamarko kasani shikenan kuwa Da tsakar dare junior na kallan senior RAMADAN yanata Sallah Abin yadinga bashi mamaki da sha'awa Harya kasa hakuri Santa ya tambayeshi da safe Yace brother Senior Yace na'am Yace kuma kullun kake tashi yin Sallah cikin dare Yace eh Sosai mah Yace Amma kana qoqari . Senior ya kallesa da kyau Yace kai bakayi ne Yace ko sau 'daya ban ta6ayi ba Amma ina lura da farillata Sosai. Bani barin ta wucce lokacinta Yace da kyau Amma Saidai da xaka daure kadinga yi xaiyi kyau Sosai Dan nafula tana tsare mutum daga dukkan kowane sharri Tanasa mutum ya samu kwarjini Tanasa mutum ya kasance Cikin nutsuwa. Tana hana baqin ciki yin tasiri a xuciyar mutum Tana 'daukaka darajar mutum Ata'kaice dai 'dan uwa yana dakyau mutum ya gyara lahirarsa kada yabari duniya ta ru'desa Inaso kaxamo 'daya daga cikin masu leman lahirarsu Junior yayi shiru Can Yace toh Allah yabani iko Kallansa kawai senior yayi Yace yau inada lectures qarfe tara Amma baxan jeba dan inasan baka lokacina Junior yayi Murmushi Yace bana wasa da karatu my brother ko ka'dan Idan lokacina yayi tafiya xanyi in Barka Inada wani aboki Abbas wanda mukaxo hutu tare Kanaji 'daxo da mukayi waya dashi yake gayamin yana Cikin garin nan a Nasarawa J:R:A. Kaji dai xaixo ya 'daukeni Banaso kayi missing wani abu daga karatunka Senior yayi Murmushi Yace toh Amma kace mishi yalura min dakai da kyau Junior yayi Murmushi Yace toh. Da kallan agogo Yace kaga taran ta kusa sukayi falan gidan Anan Momy taha'da musu breakfast bayan sun gaishesu Dady ya kalli senior Yace my son Yace yes Dady Yace inaso in maka Aure acikin shekarar nan....... Cikin sauri senior ya furxar da tia 'din da yake bakinsa Ya waro ido Yace Aure Dady Murmushi Dadyn yayi Yace eh. Naga kana so ne Yace Wlhi Dady bankai Aure ba Yace shine kuke yawan xuwa club Yace Wlhi ba abinda muka ta6ayi narantsema Yace hmm naji Amma baxan canja wannan tsarin nawa ba Adalci 'daya nayi maka shine kakawo min wacce kakeso acikin watannin nan Yace Dady😳 Yace my son Shiru senior yayi Can yatashi ba tare daya gaba breakfast 'dinba xai fita Momy tariqe hannunsa Tace katemaken kayi break 'dinnan. Kafah dena wasa da cikinka Yace hmm xanje gun Auntyna naci ne Tace toh me Aunty daga can xaka wucce ne Ya turo baki dacewa eh Tasaki hannunshi ya fitta.... Junior ya bishi da kallo da 'Yar dariya ka'dan Dady Yace kaima ina xuwa gareka Shuru junior yayi Can Yace Nagano Dady Jibiril ne ya kashe mana mahaifinmu....... Waro ido Dady yayi Cikin shaqewa Yace bashi bane my son Junior yayi Murmushi Yace Wlhi shine Ni naji da kunnena yana gayama wani Shuru Dady yayi Can Yace banasan kace xakayi wani abu akai Yace naso kasheshi nadai fasa dan bansan abinda Allah yake nufi ba da har yabari narayu ahannunsa ya kuma tusa masa qaunata Momy Tace kayi kyan tunani Allah yayi muku albarka Yace Amiien Dady Yace toh yanxu xansa

Chapter 11 of 33